Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya ne a kanki? Ga responsible mutum irin Bilal? Dan gidan mutunci da karamci, wanda kuma muka sansu suma suka sanmu?".

Gabadaya haushi yazo ya dabaibayeni wai me yasa ni ba zasu duba dalilina ba, zasu dinga concluding rayuwata kamar idan nayi auren su ne zasu yi min zaman auren ba ni ba? Na tashi zan wuce daki da sauri ina gunguni har da buga kafa a kasa.

Yaya ya daka min tsawa data gigita ni, tunda nake dashi ban taba jin yayi makamanciyar ta ba, musamman wa ni. Yace "dawo nan ki zauna Na'ilah tun kafin ranki ya baci wallahi!".

Ba shiri na koma inda nake zaune na zauna, hawayen da nake kokarin dannewa suka shiga zarya akan kumatuna.

Yaya ya kama baki, "ikon Allah! Kuka kuma kike yi? Lallai kin samu waje da yawa. Akan wannan yaro ne kike nema ki bata mana rai, me kika gani a jikinshi?".

Fatsu tayi caraf ta tare shi, "ni anya ma ba tsaface ta yayi ba? Naji ance wajajen nan sun kware wajen bin malamai".

Babu wanda ya tanka mata a tsakaninmu, Yaya ya cigaba da cewa "ni ba zan takura ki ba Illo, amma Allah ya gani zamu yi iyaka bakin kokarinmu. Amma tunda ke kina ganin hakan yafi miki, to sai kije kiyi tayi, babu wanda zai sake damunki. Sai dai ko mai zai faru, kiyi kuka da kanki". Ya tashi yana kakkabe jikinshi ya kalli Fatsu, "ni zan wuce gida Inna, sai da safenku!".
Tace "to Mudan, a gaida su yan biyu". Yasa kai ya bar gidan. Ya barni a zaune ina share hawaye.

Yana fita Fatsu ta juyo kaina, "wannan taurin kai naki, ban san daga inda kika kwaso shi ba. Ni dai duk tarihin danginmu babu mai taurin kai wallahi, balle kuma mahaifiyarki. Mace mai saukin kai, hakuri da ladabi da biyayya. Allah ya kyauta miki". Ta tashi ta hade kan kayanta ta shige daki.

Ni da Janan muka cigaba da zama a wajen, cikin ni da ita babu wanda yayi magana. Har na gama yan koke-koke na na share hawayena. Sai dana gama sannan ta kalleni, tace "kiyi hakuri, banyi zaton abin zai kai haka ba wallahi. Tambayata tayi, ni kuma I was just carried away, amma banyi da niyya ba".
Nasan halin Fatsu sarai da bugun ciki da iya manipulating, nasan kadan daga cikin aikinta ne. Amma ban tanka mata ba, nima tashi nayi na fada dakin, nayi shirin barci na kwanta abina.


*

Wato tunda nake zuwa Gashua, ban taba zuwan da bai yi min dadi kamar na wannan karon ba. Gabadaya Fatsu da Yaya sun dauke min wuta, kai hatta da Malam sai in ga kamar shima dai ya daina kula ni. Duk da cewa bai fito fili yayi min maganar ba, amma ta cikin hira da nasiha yakan sako zancen cikin dabara irin tasu ta manya. Shi yasa naji gabadaya na takura. Tunda farar safiya muke saka kafa mu bar gidan ni da Janan da muka shirya da ita a washegarin ranar da abin ya faru, ba zamu dawo ba kuwa sai dare yayi. Ta yadda da mun dawo, babu lokacin zama hira, zamu nemi makwanci.

Ranar Lahdi na zagayowa kuwa, yadda kasan na sauka daga kan kaya haka naji lokacin da muka fita daga garin Gashua. Nasan yanzu sai a hankali, sai nayi kokari sosai kafin in samu in shawo kan Fatsu da Yaya. Da wannan kudirin muka isa Zaria.
Cikin yan kwanakin kuwa na samu na shawo kansu din da kyar, duk da cewa har yanzu dai da suna dan tado min maganar musamman ma dai Fatsu, amma dai hakan yafi da.

Bamu yi cikakken sati uku da dawowa ba, muka tafi gida hutun sallah.















*☆⋆31⋆☆*




Komawata wannan karon naga alamun canji sosai a gidan. Misalin yadda na samu Anty Alawiyya cikin fara'a da walwala, tana ta shigi da ficinta cikin annashuwa. Su Ramata kuma ana zaune a kofar daki, an coge daurin dankwalin nan an kawo shi goshi, ana ta zubda ruwan habaici da bakaken maganganu kamar wata jikar mahauta.

Nayi sallama na shiga gidan, hannuna dauke da Auwal da muka hadu dashi a waje, sun dawo daga makarantar islamiya, ya gudu ya baro sauran. Anty Alawiyya ta amsa min sallamar da nayi cike da fara'a, tace "a'ah, mutanen Zaria ne? Sannunku da zuwa, ai bamu da labarin kuna kan hanya".

Nayi dan murmushi ni kuwa tare da gaidata, ta amsa tare da shigewa dakinta. Na juya na gaida Ramata, yau ko albarkacin amsa gaisuwar ban samu ba, ta cune baki waje daya, ta dauke kai daga kaina ta maida shi gefe. Na tabe baki na ciccibi akwatina na fada daki Auwal yana bina a baya.

Dakin a share a kimtse, abin har ya bani mamaki. Maryam dai ba irin masu son yin gyaran nan bane, saboda haka zuwa in ga daki a share a goge, yana kamshi, abin mamaki ne da tambaya.
Na zuge jakar hannuna na ciro cakuletin dairy milk dana siyo ledar guda saboda yara, na dauki daya na ba Auwal. Ya karba ya fita waje a guje, nasan sauri yake ya tari yan uwanshi ya basu labari. Nayi murmushi ina girgiza kai tare da tashi na hau cire kayan jikina.

Ina nan sai ga Alawiyya da gorar zobo da kunun aya, tace "ga mai dan sanyi ki kora kafin mu gama abinci, yanzu aka dora amma ba mai wahalar damuwa bane".
Allah sarki, sai naji abin wani banbarakwai. Duk da hakan bai hana ni jin dadin hakan ba, ko ba komi kasan cewa wani ya damu da kai a cikin gidannan, abin jin dadi ne da alfahari.
Na kai hannu na karba cikin murmushi, nace "babu komi ai, na ma ci abinci ai kafin in taho. Nagode sosai". Bata ce komi ba ta juya ta bar dakin.

Sai dana linke kayana na gyada su, sannan na sake fita tsakar gida, daidai lokacin yaran sun dawo, nan fa aka hau guje-guje da rige-rigen wanda zai riga zuwa wajena. Na taryo su gabadaya na rungume, sai da suka gama dokin su, sannan suka kyaleni. Na shiga bandaki na dauro alwala saboda yamma tayi sosai har rana ta kusa faduwa, na fito na sallami masu jiran tsaraba.
Na zauna kenan na fara shan zobon da Anty Alawiyya ta kawo min mai sanyi sosai, naji an fado kaina ta baya ana ihu. Muka fadi a tsakiyar dakin, gorar zobon tayi can nata waje, ni da Maryam da take kaina muma muka yi namu wajen.

Sai data ga barnar da tayi sannan ta tashi da sauri, ta fita ta dauko tsumma da mopper ta goge wajen da zobon ya zuba, sannan ta dawo ta sake rukunkume ni.
Tace "haba Yaya Na'ilah, ke kullum haka kike zuwa babu sanarwa? Me yasa ma kullum na kira wayarki bata shiga ne? Har a whatsapp bana samunki".

Tun ranar da muka yi waya da Yaya Bilal ta karshe, washegari na sayi sabon sim card nayi register. Kafin in ba Janan lambar wayar, sai data sha jan kunne da gargadi iri-iri akan kada ta kuskura, koda wasa Yaya Bilal yasan da zaman wannan lambar.
Amsarta a lokacin itace, 'kina tunanin zai damu da rashin samun wayarki ne bayan duk abubuwan da kika mishi?'.
Raina yayi rashin dadi da jin haka, amma sai na dake, nace "wani abu kuma na mishi?". Bata amsa ni ba, taci gaba da kallonta da take yi a lokacin.

Bayan nan kwata-kwata mantawa nayi da zancen Maryam, yawancin sauran abokanmu ma sai daga baya idan mun hadu sannan zasu yi korafin sun daina ji daga gareni, sai dai kawai in kawo wani dalili can in basu, muyi exchanging din numbers.
Na bata hakuri tare da cewa sim din aka yi blocking, na bata sabuwar lambata tayi saving.

Na kalli gorar zobon data ajiye a gefena, babu komi a ciki duk ya zube, na harareta nace "kin ga kin zubar min da abu, bayan ko sha ban yi ba".
Ta kyalkyale da dariya, "ai in dai ta wannan ne, baki da matsala Yaya. Ke da kika zo inda ake sarrafa zobon?". Ta tashi ta fita da sauri, ta dawo da wata gorar ta miko min, na amsa na bude tare da kafa kai.
Muna nan a zaune muna taba hira da ita, har aka kira sallah. Ita ta dauki wayata zata yi game saboda bata yin sallah, ni kuma na tada kabbarar sallah. Bayan na gama na amshi wayar, na turawa duk wanda ya kamata sakon na sauka gida lafiya, na dauki Al-Kur'ani mai girma na fara karantawa har aka kira sallar isha'i.

Sai bayan na gama sallar ne sannan na bude mata tata tsarabar. Takalmi da gyale da jaka wadda ake yayi ta yanmata irinta. Murna wajenta har ta rasa inda zata jefa ni, gefe kawai na koma ina mata dariya.
Bayan na tabbatar Baba ya gama cin abinci na yiwa dakinshi tsinke. Yana zaune matan sun dabaibaye shi, Alawiyya na zuba mishi hira, su Ramata kuma ana gefe ana ta cika da batsewa. Da alamu kambun a hannun Alawiyya yake wannan karon. Abinda yake faruwa kenan a gidan, su ganin walwalar miji a wajensu juyi-juyi ne. Wadda ta samu ta shawo kanshi, ko ta tsibbunta ko ta malaman, ta fa ita da 'ya'yanta su suke cikin jindadi, ita dayar kuma sai dai ta koma gefe ta kwashi takaici, kafin itama nata tenure din yazo.

Naja daga gefe na gaida shi, ya amsa fuska babu yabo babu fallasa. Nayi zaton zai yi min maganar Yaya Bilal, amma har na tashi na fita daga dakin, bai ce min komi ba. Duk da abin ya bani mamaki, amma naji dadin hakan.
Na shiga gidan su Kulsum, muka gaisa dasu Inna. Mun jima muna hira dasu, har wajen karfe goma, sannan na musu sai da safe na koma gida.

Kayan barci kawai na saka na lalubi shimfida na kwanta. Kamar wanda yake jira, ina kwanciya sai ga kiran wayar Dr. Na Abba ta shigo, dole na katse barcina ba don naso ba na dauki kiran.



*


Washegari kamar yadda na saba, nayi duk wasu abubuwa da yakamata inyi da safen nan. Kasancewar yara sun samu hutun sallah daga makaranta, yasa ban dora abin kari da wuri ba. Wajen karfe tara na gama, kowa ya amshi nashi kason. Na hada kan kayan na wanke, na share kicin din, sannan na koma daki nima nayi nawa karin. Gobe in Allah ya yarda ake yin hawan arfah.
Ina cikin cin abincin, Aliyu ya fado dakin kamar an jefo shi, tunda na dawo gida sai yanzu na ganshi. Yace "babbar Yaya, to ya ne?".
Nayi dan murmushi nace "lafiya lau Aliyu. Ya kake?". Nan muka dan sha hira dashi ya bar dakin.

Da yamma bayan na gama duk abinda zan yi, muna tsakar gida a zaune ni da Maryam muna hira, tana bani labarin zuwan da Yaya Bilal yayi gida.

"Har nan cikin gida fa Baba ya shigo dashi in fada miki.." take fada. Wanda hakan ya tabbatar min da cewa ba karamar tarba Baba din yayi mishi ba. Idan kaga yayi baki ya shigo dasu cikin gida, to ba kananun masu muhimmanci bane.
"... Su Mamarmu dubu goma ya raba musu, muma ya bamu dubu goma muka raba, shi kuwa Aliyu aka bashi dubu biyar".

Mamaki ya kamo ni, ban taba jin labarin hakan ba sai yanzu. Wato so yayi ya saye su da kudi ne ko me? Na godewa Allah daya kasance ba Gashua yaje yayi barin kudin nan ba.

Maryam ta dago ta kalleni, tace "amma da gaske ba zaki aure shi ba?".
Ban san yadda aka yi labarin yaje kunnensu ba, amma nafi kyautata zaton Baba ne ya fadawa iyayen, su kuma suka basu labari. Ban iya ce mata komi ba sai kafada dana daga mata.

Tayi pouting, "amma Yaya Na'ilah mai yasa? Kinga da idan kika aure shi, sai in zauna a gidanki idan naje Zaria karatu, kinsan nima fa can zan je". Na gyada mata kai.

Tsulum, sai ga bakin Ramata cikin maganar, da a daki take, bamu ma san lokacin daya fito daga dakin ba, "ke ja can sakaryar banza! Me ake da gidan mai mata? Ai wallahi kada ki kuskura ki yarda, kudin mutum su rufe miki idanu kiyi zaben tumun dare. Ke zaman nan gidan ma kadai bai isheki ishara ba? Kina dai ganin yadda muke fama, babu farinciki ko na anini sai akasinsa. Kullum cikin taraddadi da zullumin abinda makiya, makagauta zasu maka. Don haka wallahi ki auri dan saurayinki shi ya fiye miki kawai". Ta saurara tana kallona, ko amsa take jira in bata da godiyar shawarar data bani? Ban ce mata komi ba, amma a can kasan zuciyata sai da nace 'ishara ta nawa kuma?'.

Da dai taga bani da niyar tanka mata, sai ta kara gaba, tana fada tana kara nanatawa, ina amfanin auren gidan kishiya? Ina jin Anty Alawiyya daga daki tana ihun, "a hakan dai kuma ake zaune ake shuka rashin mutunci ba!". Babu dai wanda ya tanka musu a cikinmu, sai ma hirarmu da muka cigaba da yi.

Washegari muka tashi da azumin nafilar arfah a bakinmu.
Washegari kuma Baba yayi yankan layya. Dama kowace shekara, ya kan yanka raguna guda uku, daya matan su raba, daya nashi shi da abokai da yake yiwa rabo kasancewar shi mutum na mutane, dayan kuma na yara ne.
Kwananmu biyu muna aikin suya, aka kammala aka raba kowa ya dauki nashi. Wanda ranar rabon ma sai da su Ramata suka raba hali kamar za ayi dambe, sannan da kyar suka hakura.
Ni dai naci gaba da jindadin hutuna kafin ya kare.

Bayan sallar da kwana biyu, su Dr. Na Abba suka kai kudi can Gashua, wanda Baba ne yace hakan. Gabadaya suka kai kudin, aka kuma sanya ranar aure. Nan da watanni uku masu zuwa. Wanda yayi daidai da lokacin dana gama exams dina kenan.
Ban san a cikin wani yanayi nake ba a cikin wannan lokaci, abu daya kadai na sani, shine zuciyata bata maraba da wannan biki koda wasa.

Bayan kwana uku da kai kudin, na tattara na koma Zaria abina. Na hadu da angona to be, muka fara shirin yadda zamu gudanar da bikinmu. A gefe guda kuma na maida hankalina ga karatun exams din dake gabatomu nan da dan kankanin lokaci.






🙏🙏🙏🙏🙏








*☆⋆32⋆☆*






Kwanci tashi kamar yau ne a wajen Allah. Gashi har yau ya rage mana sati daya kacal mu gama da karatunmu gabaki daya. Hakan kuma yake nufin nan da sati biyu masu zuwa zan amarce. Kowa ya ganni a cikin irin wadannan lokutan, ya ga 'a walking zombie'. Kama ce ba wadda ake zaton gani a jikin amarya ba, amarya daya kamata ta zama mai kazar-kazar, da doki, da komi ma kai, ni kam komi nawa ya zama babu laka a jikinshi. A kowace matsowar rana, ji nake dama kara ranakun ake yi ba rage su ba. Amma babu wanda na ba wannan labari, na kama bakina na dinke babu wanda ya sani. Nasan duk wanda yaji kalar tashin hankalin da nake ciki, wanda babu wanda ya jefa ni ciki sai ni kaina, zai kira ni banza, sakara, kila ma har su kara da wadda bata san ciwon kanta ba. But I know better.
Kullum excuse dina daya, wanda nake kara ba kaina, cewa hidimomi ne suka yi min yawa ba wani abu ba. Zan wartsake, zan dawo daidai, abinda nake yawan ambatawa kaina kenan. Kodayake, naji ance dama yawanci haka amare suke ji idan aurensu yana gabatowa. Don haka it's normal.

Da Janan muke ta shigi da ficin harkar bikinnan, tayi ruwa tayi tsaki kamar yadda yakamata tayi, duk da cewa itama nata bikin nan da watanni hudu ne masu zuwa. Kasancewar Almunta ya tafi wani course kasar Germany na watanni biyar yasa aka saka ranar auren tasu bayan ya dawo da sati biyu.

Duk wasu shirye-shirye mun riga mun yi su. Rabon IV, daga gida Katsina, zuwa nan Zaria da kuma Gashua, duk wanda yakamata ya samu ya samu. Haka anko, kai da dai duk abinda ya dace, munyi sai sauran abinda ba'a rasa ba.

Yau muka zana jarabawarmu ta karshe a cikin Shika, nan da kwanaki uku zamu yi practicals din exams din, daga nan zamu yi induction, kamar graduating ne a wajen nurses ko kuma in ce oath-taking. Idan muka yi shi, za'a bamu nursing license dinmu, daga nan kuma zamu yi applying internship a inda muke so.

Bayan mun fito daga jarabawar, a gajiye muka koma dakina ni da Janan. Muka zube akan katifa muna ajiye numfashi da maida labarin yadda jarabawar ta kasance mana.
Saboda tsabar gajiyar dana kwasa cikin yan kwanakin nan, ban san lokacin da barci mai nauyi ya kwashe ni ba.

Kafin in tashi har Janan ta dafa mana jallop macaroni, lokacin dana tashi na gansu ita da Esther suna hira. Nayi mika tare da tashi zaune ina binsu da kallo, Janan ta kalleni "ki tashi ki wanko baki ki zo ki ci abinci. Ki gama muje wajen masu dinkin wancan mu gani idan sun gama mu amso".

Na tashi tsaye da kyar, ina jin jikina kamar an nada min dukan tsiya. Na dauki kettle na fita waje na daurayo bakina, na dawo na zauna a inda plate din abinci yake jirana. Na janyo abincin cikin mutuwar jiki na fara ci, ina ji suka ci gaba da hirarsu akan wajen da zasu je suyi nasu internship din, ita Janan a Kaduna zata yi, ita kuma Esther anan Shika zata yi. Nima dai nasan Shika dinne, don mun riga munyi maganar da Dr., ina karbar license dina zan mika mishi, zai yi applying internship din da kanshi anan Shika din.
Daga baya kuma sai hirar ta gangaro kan abinda zasu yi da abinda zasu saya idan suka dauki albashinsu na farko. Ina daga gefe ina jinsu, sai dai inyi dariya idan sun fadi wani abin daya bani dariya. Ko kuma in girgiza kai da jin absurdity din abubuwan da suke fada.

Ina gamawa, na maida kwanukan gefe. Esther ta jefo min wayata, nayi sauri na cafe. Tace "hubbynki ya kira lokacin da kike barci".
Na jefa mata harara cikin wasa, "shine kuma sai yanzu kika ga damar fada min? Kina so hankalin mijina ya tashi ne ko me?".

Ita da Janan suka yi dariya, tace "come on mana, nasan dana baki wayar nan daga tashinki daga barci, ba lallai kici abincin nan da wuri ba. Ko baki ga kokarina bane?".
Na daga baki zan bata amsa, aka amsa kiran dana dannawa wayar Dr., don haka na rufe bakina tare da kara wayar a kunne.

Tun kafin inyi magana ya riga ni, daga jin shi cike yake da doki da farinciki, "hey, guess what?".
Yanayin yadda yayi maganar kanshi ma, kasan cewa wani abu ne babba kuma muhimmi ya same shi, don haka naji na saki murmushi ba tare dana shiryawa hakan ba, nace "me ya faru ne?".

"Tafiyar nan fa ta samu, nan da sati biyu! Oh God!! I can't really believe this is happening!!". Ya karasa fada cikin karajin murya.

Naji na balle da murmushi nima kamar lebuna na zasu rabe biyu. Wani course ne asibitin zasu tura manyan doctors na department din su biyar kasar London duk bayan shekaru biyu, course ne na shekara biyu. Yace idan kaci sa'a, idan can asibitin da kaje yin course din suka ga kwazon ka, zasu iya daukar ka aiki kamar yadda suka dauki likitocinsu biyu aiki wadanda suka je waccan shekarar. Idan kuma baka samu aikin a can ba, idan ka dawo, zasu kara maka matsayi da kuma albashi anan. Wannan ba ma shine abin birgewar kadai ba, idan ka tafi can asibitin zasu dinga biyanka albashinka, su baka wajen zama, haka babu ruwanka da biyan kudin makaranta idan kaje. Tsarin shine, idan ka tafi yanzu, zaka yi wata takwas a makaranta kana daukar darasi abinka, a hakan ma kana da albashinka a hannu, bayan ka gama da nan zaka koma asibitin kayi aiki dasu na watanni goma sha biyu. Daga nan kuma sai su yanke shawarar yadda zasu yi da kai.
Yace min yanzu sau uku kenan yana applying ana hana shi, wannan karon ma kwata-kwata ya cire ranshi daga samu, sai kuma gashi yanzu babu zato babu tsammani, ya samu din.

Nace "Masha Allah, Alhamdulillah! Kai amma naji dadi wallahi, Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya albarkaci aikin wannan".
Yace "ameen ameen amaryata. Ni har na rasa wace kalar murna ma yakamata inyi, ji nake kamar mafarki nake yi!".
Na saki yar dariya, "right! Kawai ka kalli alkibla yanzu, ta nan kadai zaka nunawa Allah godiyarka. Idan ka bar nan kuma, sai kayi sadaka".
Yace "haka ne, nagode dear. Bari in tafi yanzu".

Na girgiza kai fondly, wani lokacin kamar yaro haka yake gudanar da dabi'un shi, wasu lokutan ya baka dariya, watarana kuma takaicinshi ya cika maka ciki kamar kayi me.

Wani tunani ya darsu a raina, nace "to amma ya zamu yi ne? Bikin ma nan da sati biyu ne, kenan hakan yana nufin tare zamu tafi kenan?".

Ya danyi jim, zuwa can yace "har yanzu ina kan wannan tunanin ne. Yanzu zan shiga gida in sanar dasu, zan kira ki zuwa anjima". Nace mishi "to ka gaishe dasu Hajiya". Yace "zasu ji", ya kashe wayar.

Na bi wayar da kallo, ko menene abin yin tunani a cikin wannan maganar? Na tabe baki tare da daga kafada.

Su Janan da tunda muka fara wayar suka katse hirarsu suke kallona jifa-jifa, suka zubo min idanu, na kallesu cikin murmushi, "dudes, London ta kira mu yanzun nan!".

Habawa, suka saki ihu da shewa tare da fadowa kaina, sai da muka fadi kasa.
Janan tace "da gaske?!".
Esther kam, "Oh my God!" Kawai take fada tana nanatawa.

Sai da suka gama ihun murnarsu sannan Esther ta tashi zaune, muma muka tashi. Janan ta sake sarkafo hannunta ta rungumo ni, "Na taya ki murna wallahi dear... Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Yanzu sai kiyi tafiyarki ki barni?".

Nayi dariya, "sis, maganar fa bata tabbata ba. Ni fa ina assuming abubuwa ne kawai".

Ta kai min duka a kafada, "maganar banza kenan! Ke yanzu kina tunanin zai tafi ya barki anan har na tsawon shekaru biyu? Wasa kenan. Balle ma, su da ana basu gidajensu acan, ai babu ma wani dalili da zai hana mu zuwa kai amarya kasar London". Ta kyalkyale da dariya bayan ta gama fadin haka, ni da Esther muna taya ta.

Sai wajen karfe biyar na yamma sannan muka fita zuwa amsar dinkin. Har Esther muka tafi. A hanya Janan take tambayata, "su fa kayan lefen da ba'a kawo ba har yanzu, ya za ayi dasu?".
Na kalleta, "ke da kika san zamani ya canza, yanzu lefe da zaki ga har ana saura kwana biyar daurin aure ba'a kai ba. Balle shi fa yace kamar haka al'adar gidansu take, sai bayan aure ake kai kayan lefe".

Janan ta jinjina kai, "haka ne. Mu dai ya taimaka ya kawo kafin mu kaiki, idan haka ne, bamu da damar daukar turamenmu kenan".

Na kai mata duka ina dariya, "ke fa baki da M wallahi, wawashe min kayan zaku yi kenan?".
Muna wannan hirar har muka fita waje, muka hau bus zuwa inda muka kai dinki.

Dancing Banana, nan ne wajen da muka kai dinki. Duk da wasu kayayyakin suna can Katsina, Maryam ta kai min su, kai wasu ma suna Kaduna. Wadannan wadanda Ummahn su Janan ne ta bamu, manyan atamfofi guda biyu iri daya, da wani lafiyayyayen yadi ni da Janan din. Da kanta ta kai dinkin, namu kawai tura measurement dinmu ne.
Wadanda muka kawo nan, wanda angon ne ya kawo, tunda ba'a riga an kai lefe ba. Na Katsina kuma, wanda muka fitar ne a matsayin anko.

Kai tsaye wajen wanda yake mana dinkin muka wuce, muka samu ya dinka kala na mutum daya, na dayan kuma ya yanka bai dinka ba. Esther ta fara fuming, dama ita ta hada mu dashi, "yanzu kana nufin kusan sati biyu wai har yanzu baka gama mana dinkin ba? Mike meye hakan wai?".

Yace "na fa

Please Login or Register in order to submit comment