Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu haka tana ciki tana dubata".

A raina naji abin banbarakwai. Nayi tunanin idan aka samu akasi irin haka, asibiti ake garzayawa? Amma sai na kame bakina nayi shiru. Na shiga daki na canza kayan jikina, na koma falo nabi layin jiran fitowar likita.

Banyi mintuna goma da zama ba, sai ga likitar ta fito. Duk muka tashi tsaye. A shekarance za'a iya cewa zata yi shekaru arba'in da wani abu, ta kalli yadda muka yi cirko-cirko cikin jimami, tace "sai dai hakuri, amma cikin ya zube saboda tsabar buguwar da tayi".

Hajara ta hau sallallami da salati cikin kuka, shi kuwa Yaya shiru yayi kawai yana kallon likitar, sai dai daga ganin yadda idanunshi suka kada suka yi ja, kasan cewa zancen ya shige shi sosai. Ban san a wani shafi nake ba, na bakinciki, jimami ko tausayi?.

Raheemah ta kama kugu ta fada karkada jiki cikin tsiwa, "hmm! Allah sarkin baiwa! Wadda aka bullo da ita kuma kenan? Ku dai kuka sani, nan gaba ma zuwa za ayi ace ta haihu an sace mata dan!".

Cikin nuna alamun gajiya Yaya yace "Raheemah...!". Amma bai karasa fada ba, kamar wadda maganar ta kakarewa. Da mai hankali ce, ko kuma da masifa bata rufe mata idanu ba da ta fahimci warning din da yake tattare a cikin muryarshi.
Maimakon tayi shiru sai taci gaba, "ai wallahi kaima tabewar basira ce ta same ka. Wadda aka tabbatarwa da cewa ba zata taba haihuwa ba, ita ce zata zo rana daya tace wai tana da ciki? Yo cikin abin banza ne ko kuwa a ruwa ake shan shi? Aikin banza, an rasa karyar da za ayi sai ta ciki. Ai wallahi dama jiran ranar da za'a haife muke yi mu ga uban abinda za'a kawo ace an haifa, sai kuma aka kare da bari. An kira likitar bogi ana wani kukan karya saboda an maida mu sakarkaru, to mun san komi ai wallah kuma idanunmu ba a rufe suke ba!".

Aikuwa sai Hajara ta shaka, nan da nan ta manta da kuka da salatin da take yi, tace "su waye kike cewa masu yin karyar ciki?".
Tace "ba ga ku nan ba! Makaryatan banza dana wofi!!".
Hajara kuwa tace "ke in ana zancen ciki ma har kin isa kiyi magana? Ke da ko batan wata ma baki taba yi ba? Idan fitsari kayan banza ne kaza ma tayi mana mu gani?!".

Wai! Ai sai Raheemah ta hau ihu, tana yi har tana hadawa da buga kafa a kasa, "ai wallahi na godewa Allah tunda abin bai kaini ga yin karyar ciki ba, kuma lafiyata lau, ina kuma da amfani ba ci nake ina kasayarwa ba!!".
Hajara tace "idan abin haka ne, me yasa ke baki taba yin cikin ba?".
Nan da nan falo ya rikice da hayaniya kamar zasu ba hammata iska, sai da Yaya ya tsawatar musu sannan da kyar. Raheemah ta wuce dakinta tana cigaba da zage-zagen.

Ya juya ya ba likitar hakuri, tayi murmushi tace babu komi ai. Ya tambayeta ko nawa ne kudin aikin da tayi? Tace ai kudinta suna cikin albashinta, Hajara ta taka mata ta mana sallama ta tafi.

Suna fita Yaya yayi dakin Ameerah, na bi bayanshi. Tana kwance akan gado tana barci. Idan ba fada maka aka yi ba, ba zaka taba cewa mai jinya ce ba wadda tayi bari. Babu paleness alamun rashin jini, babu alamar cuta ko kadan a tattare da ita. Ni dai na tabe baki a cikin raina, sai me idan tayi karyar ciki? Wannan ai matsalarta ce ba tawa ba. Matsalata ita ce matsalar dake tsakanina da mijina a yanzu.

Na samu kujera na zauna anan, babu mai uhm ko uhm uhm a cikinmu. Na kalli yadda ya dafe kai a zaune, har yanzu kayan aikine a jikinshi, bana tunanin ko sallar la'asar ma yayi. Na danyi gyaran murya nace "Yaya ko zaka je ka canza kayan jikinka ne? Zan kula da ita kafin ka dawo. Kayi sallah ma kuwa?".
Ya daga kai a hankali ya kalleni kafin ya girgiza kai. Tausayinshi ya cika min zuciya. Nayi takaicin cewa yau ba ranar girkina bace, da na faranta mishi rai, ta yadda zai manta da kowa da komi.
Nace "kaje kayi to, sai ka dawo".

Babu musu ya tashi ya bar dakin. Ni kuma naci gaba da zama anan har Hajara ta shigo itama.
Zuwa can Ameerah din ta tashi daga barci. Muka matsa muna mata sannu, Hajara ta taimaka mata ta tashi zaune. Na mata ya jiki, ta amsa tana wani yamutsa fuska. Ban kara ce mata komi ba, sai wani kallon dana jefa mata wanda ya sanya ta shiga taitayinta a take, ita tasan ni ba sakara bace, kamar yadda nasan itama ba sakarar bace, ta fahimci ma'anar kallon da nake wurga mata sarai. Nan na barsu na wuce dakina.

Washegari kuwa haka aka yi ta zuwa dubiya da jaje. Janan da Yaya ma sun zo. Bayan sun dubata, muka nutse daki ni da Janan. Tunda tazo take bi na da kallo cikin alamun tambaya, nasan hakan baya rasa nasaba da yadda nayi wuri-wuri ne, na canza kama. Muna shiga daki kuwa ta fara watso min tambayar lafiya? Nayi rashin lafiya ne?.

Na zauna a gefen gado ina kallonta, "lafiyata lau mana, me kika gani ne?".

Tace "ban gane ba? Baki ga irin ramar da kika yi bane? Kin kuma kara baki".
Na daga kafadata sama kawai, "halin rayuwa kenan dama, yau dadi gobe madaci".

Itama ta zauna a gefen gadon tare da dafa kafadata, tace "to Allah ya kyauta. Amma don Allah ki kwantar da hankalinki. Kada ki saka wata damuwa da bata kai ta kawo ba a cikin ranki ki janyowa kanki wata cutar. Komi zai zo ya wuce". Na gyada mata kai a hankali.

Sanin ba zata ji komi daga bakina ba, yasa ta kawo min hirar wajen da take yin internship. Duk mun kusa gamawa, nan da watannin da basu fi uku ba zamu gama, mu zama cikakkun nurses.
Daga karshe ma dai muka fita ni da ita. A motarta wata madaidaiciyar SUV Lexus UX ruwan toka, da mijinta ya sai mata. Da yake ta riga ta iya motarta tun kafin tayi aure, ita take kai kanta ko'ina, yanzu ma ita ta kawo su da Yaya.

Gidan Yaya Hafiz muka je, matarshi Hauwa, ta karbemu da far'arta. 'Ya'yansu maza biyu, mace daya suka zagaye mu suna mana sannu da zuwa. Da yake lokuta da dama suna leko mu, amma zumuncinsu yafi karfi da Ameerah, amma muna gaisuwar mutunci da ita.
Bayan mun dan yi kamar mintuna ashirin haka, muka musu sallama muka tafi. Muka nutsa cikin garin Abuja, shiga gidan wannan, fita daga wancan, yawancinsu duk gidajen kawayen Janan ne, wasu kuma gidajen yan'uwansu ne. Sai da Yaya ta kirata akan tana jiranta, sannan fa muka juya.

Bayan sun tafi na koma daki na zauna ina jiran a kira sallar magriba Nasan yau idan na kwanta sai nayi ciwon jiki saboda yawace-yawacen da muka sha.


⋆⋆


Kwana biyu, komi ya natsa, komi ya koma yadda yake, mun ci gaba da gudanar da rayuwarmu kamar da. Ameerah ma ta warware har ta karbi girki abinta.

Ranar Alhamis, ranar satina daya da zuwa Suleja. Abubuwa da dama sun ragu, ina kuma ganin canji sosai a tattare da Yaya, ya sauko sosai. Tunda yanzu mu kan zauna muyi hira cikin raha, muci abinci tare, duk da lokaci zuwa lokaci ya kan dan janye jikinshi, but am not complaining.

Aikin rana nayi yau, kafin in tafi nayi miya na ajiye a dakina, don haka ina dawowa na dafa cous-cous muka ci a matsayin abincin dare. Yau ko hirar da ake yi ban tsaya ba, ina maida kayan kicin, dakina na wuce nayi shirin kwanciya barci, na musu sallama na fada dakin Yaya na kwanta.

Ina kwanciya barci ya dauke ni, yau wuni muka yi akan kafafunmu, saboda haka jin jikina nake kamar wadda aka wa dukan tsiya. Ban damu da jiran Yaya ba, kamar yadda nace, mun dan koma normal ne, amma ba duka ba. Duk da hakan yana damuna, amma ban bari ya dameni sosai ba.

A cikin barcin naji shigowar shi dakin, da alama yau hirar bata yi tsayi ba, tunda ko cikakken minti goma banyi da kwanciya ba. Ina jin motsin shi a cikin dakin, da alama shirin kwanciya barci yake yi, amma saboda tsabar gajiya na kasa bude idanuna.

A hankali naji an zauna a gefen gadon, tattausan hannu ya shafo gashin kaina zuwa gefen kumatuna. Wata siririyar murya, very husky and soothing, take kiran sunana, amma daga can nesa nake jiyo muryar kamar a cikin mafarki.
"Na'ilah... Baby...!".

"uhm?", na amsa. Amma na kasa daga idanuna.
"Baby!!". Aka sake kirana, wannan karon desperately.

Don haka nayi kokari na bude idanuna da kyar, kuma a hankali.

Ban san me zan ce ba, saboda na kasa banbance tsakanin mafarki da farke. Shin wannan ma daya daga cikin mafarkan dana saba yi ne? Ko kuwa da gaske ne?!.

Ba kamar sauran mafarke-mafarken dana saba yi ba, kamar su dinne dai, amma ya banbanta. A maimakon silhouette din mutum dana saba gani, wannan karon sai nayi ido-da-ido da Yaya. Wanda ya saki wani irin tattausan murmushi lokacin da yaga na bude idanuna mun hada ido dashi.
Nayi scrunching eyebrows dina in confusion, mafarki nake yi?.

Ya kara shafa gefen fuskata, "I love you, baby na!".

Scratch that! Be it mafarki ko rashin mafarki, it doesn't matter. What matters is that, Yaya ne, mijina, nake gani zaune a gabana, yana furta min abinda na jima banji daga gareshi ba. Sanyin daya mamaye kirjina a wannan lokacin, Allah ne kadai yasan iyakarshi.

Sai dai barcin dake cikin idanuna ya rinjayeni, da kyar nake damben iya daga idanuna da suke komawa suna likewa kamar ana jona su da maganadisu.
Na dafa hannunshi dake kan kumatuna, "Yaya..!". Na samu na furta hakan a hankali, kafin barci ya sake daukata. Hakan bai hana ni jin warmness din da lebbanshi suka haifar akan goshina ba. Ban kuma daure murmushin daya subuce min ba duk da barcin daya ci karfina.

Kiran sallar farko a cikin kunnena. Na bude idanuna a nutse, a hankali kuma abubuwan da suka faru a daren jiya suka fara dawo min. Tunanina daya a lokacin, shin mafarki ne nayi?.
Sai dai daga jin dumin jikin daya kamo ni ya rukunkunme ni ta baya kamar wanda yake tsoron a dauke mishi ni, ina tantamar idan mafarki ne.

Murmushi ya fara kokarin subuce min, wani irin sanyi, aminci da salama dana manta rabon da inji kwatan-kwacinsu suka dinga kwararawa suna shiga cikin zuciyata. Marata cike take tam da fitsari, dalilin daya tasheni daga barci ma kenan, amma na kasa zame jikina daga nashi. Sai ma kara lafewa da nayi a kirjinshi ina jin bugun zuciyarshi.
Mun jima a haka, har zuwa lokacin da ya farka. Sannan na daga kai, tare da kokarin zame jikina daga nashi wanda sai a lokacin ne ya sake ni.

Sauka nayi daga kan gadon na shiga bandakin. Bayan na gama abinda zan yi, alwala na dauro sannan na fito. Ina fita, shima ya shiga bandakin.
Na gyara jikina tare da fara nafila kafin lokacin sallah yayi. Ina jin lokacin da Yaya ya fito shima, ya shirya ya fita zuwa masallaci.

Ina cikin nade abin da nayi sallar naji ya dawo. Ina jin lokacin daya maida kofar ya rufe. Nayi shiru a tsaye ina jiran in ga abinda zai yi ba tare dana juya ba, saboda ban san abinda zai faru ba. Kawai sai ji nayi an rungumoni ta baya. Ya lalubi kunnena yace "good morning, baby".

Naji kunya ta rufe ni, nace "ina kwana Yaya?".
Ya nutsa kanshi gefen wuyana yana humming, "lafiya lau baby na, kinyi barci lafiya?".


Na gyada mishi kai tare da juyawa ina kallonshi cikin murmushi, "sosai ma!".

Bai ce komi ba, sai kara ja na cikin jikinshi da yayi, ya kara saka kanshi a wuyana yana shakar numfashi. Abinda yake matukar kauna kenan. Mun jima a hakan, kafin ya dago ni yana kallona, "God, how I miss you!!".

Na daga hannu na shafo gefen fuskarshi, "I miss you too, Yaya na!".

Daga nan kuma abinda ya faru sirrinmu ne. Sai can, rana ta fito sosai sannan na raka shi ya tafi bayan na soya mishi kwai ya ci da shayi da biredi.

Ina dawowa daga raka shi din da nayi, naci karo da Raheemah a kofar kicin ta baya ta coge tana watsa min kallon tara saura. Na gaida ta fuska babu yabo babu fallasa. Ta kare min kallo tun daga sama har kasa, taja tsaki, "jarababbun banza da wofi!". Ta fadi hakan cike da tsana da dacin rai.

Ban ce mata komi ba, ban ma ji komi a cikin raina ba, farincikin da zuciyata take ciki a lokacin ya wuce tunanin mai tunani, babu abinda zan fari ya wargaza min wannan jindadin. Don haka na hasketa da murmushin tura haushi kawai na kara gaba.

Ina shiga kicin ta sake biyoni, "kina nufin yau da abinda zamu karya kenan?". Ta fada tana nuna flask din shayi da biredin da na ajiye akan dinning table, shekeke kamar wasu kayan kashi.
Nace "ehh mana, me suka yi ne?".
Kafin tace wani abu, Ameerah ta fado kicin din sanye da rigar barci ta leshi wadda ta tsaya mata a gwiwa. Ta kalli yadda muka yi cirko-cirko damu kamar wasu zakaru, ta dauke kanta ta hau dage-dagen drawers. Ni ce na fara gaida ta, sai data dauki gwangwanin white oats, sannan ta amsa.
Nima na dauki yoghurt daga cikin fridge na koma dakina. Bashin barcin da na ci na biya kafin lokacin tafiya aiki yayi.


***

Shikenan, muka shirya abinmu. Rayuwa taci gaba da tafiya, akwai lokuta da dama da sabani zai shiga tsakaninmu, hakan bai taba affecting rayuwar aurenmu ba. Bamu fari sabani ya kaimu ga bacin ran da zai hana mu jindadin rayuwar aurenmu ba.

A hankali azumi yana ta matsowa. Ranar nan kwatsam sai ga Yaya da albishirin zamu je umra dashi. Wayyo, murna har sai da nayi hawayen dadi. Na fara kiraye-kirayen wayar yan'uwa da abokanan arziki ina albishir.

Washegari sai rigima ta balle, a cewar Raheemah Yaya yayi rashin adalci. Saboda wancan karon ma da zai tafi tare da Ameerah suka tafi wanda hakan yake nufin wannan turn dinta ne kenan.
Yaya yace "wannan nima haka naji shi daga sama yadda kika ji shi kema, bani da alhakin kudin jirginta. Illa iyaka mun tafi tare, mun kuma dawo tare".

Da taji haka kuma sai tayi shiru ta fara kokarin nade tabarmar kunya da hauka. Wai "ai duk da hakan dai, ai..", Ta hau kame-kame. Yaya kuwa yayi banza da ita, ya juya yana kallon Ameerah yana gaya mata tayi list din abubuwan da zasu bukata kafin tafiyarmu, tace to.


*

Anyi haka da kwana biyu, sai ga Ameerah da nata biridin itama. Ranar assabar ce, lokacin saura sati biyu mu tafi.
Na tura Yaya falonshi yana karatun jarida, ni kuma na hau gyara mishi daki. Daga bandaki na fara, bayan na wanke shi tas na kyalkyale shi yana ta sheki da tashin kamshi, sai na koma bedroom.
Ban san lokacin da Ameerah ta shigo ba watakila lokacin ina bandaki. Ina jiyo sautin muryoyinsu daga nan.

Wai itama Daddynta ya biya mata umrah, da alamu kenan tare zamu tafi da ita. Tana fadar hakan tana yar dariya. Sai dai daga jin yadda muryar Yaya tayi a lokacin, abin bai bashi dariya ba.
Kai tsaye yace babu inda zata je.
Da taga tayi roko da magiya ya kafe, sai tace to zata bi yan gidansu kawai su tafi.

Yace "ba ina nufin ba zaki bimu bane, ina nufin babu inda zaki je, kina gida".
Murya na nuna bacin rai tace "kana nufin ayi asarar kudin da aka biya ne ko me?".
Yace "lokacin da aka biya kudin ai ba'a nemi shawarata ba, ko an nema? Kada ki manta kuma abinda ya dace ayi kenan tun daga farko. Ta inda ake hawa kuwa ta nan ake sauka".

Tayi shiru, can kuma tace "amma kasan duk shekara muna zuwa Hajji da umara ko?".
Yace "ba a taba tambayata ba, ko an taba? Nayi iyaka karar da zanyi, na kuma gaji. Saboda haka babu inda zaki je wannan karon, idan kuma zaki yi musu da nine, to mu zuba don Allah!".
Sai ta kame bakinta ta kulle. Na girgiza kai ina yin dan murmushi. Dama masu iya magana sun ce idan tura ta kai bango...!

Har na gama ayyukana ban sake jin duriyarsu ba, sai sautin karar talabijin ko kuma muryar Yaya idan an kira shi a waya.
Zuwa can na fito daga dakin hannu rike da basket da na matse bed sheets da kananun kayan Yaya dana wanke na wuce su a falon a zaune sunyi jugum-jugum.
Baya na fita na shanya kayan, na koma gidan ta kofar waje.
A kofar shiga falon muka yi karo da wata mata, muka kalli juna ni da ita, kamar na santa amma kuma na rasa a ina na santa. Na dakata ta shigo gidan kafin na rufa mata baya, sai da muka shiga falo naga tayi hanyar dakin Raheemah. Ni kuma na koma falon Yaya.

Lokacin dora girkin rana yayi na fita kicin na hau dafe-dafe, yam porridge nayi, nayi dambun cous-cous, da lemun cocktail.
Ina gama shirya abincin akan dinning Raheemah ta fito ta kwashi abincin da yawa ta koma dakinta, ban mata magana ba saboda bakuwar da nasan tayi.

Dakina na koma, nayi wanka tare da sanya kananun kaya, rigar blouse da dogon wando, na dora hular beanie na sanya silifas mai taushi na fita zuwa falon Yaya.
Ranar haka muka yini, Yaya bai leka ko nan da can ba. Sai can bayan sallar la'asar sannan ya fita.
Sai da yammar ne na fahimci cewa wannan bakuwar ba kowa bace face Haleemo. Na bita da kallo cike da tsananin mamaki, ta rame, tayi baki, duk wannan kwalisar babu ita, baka taba cewa itace Halimon nan. Kayan jikinta ma daga ganinsu sun ga jiya sun ga yau.
Ganin babu wadda tayi min magana a cikinsu, yasa nima na juya musu baya, naci gaba da yanka kabeji da nake yi a kicin. Amma kuma zuciyata cike take da tunanin abinda ya faru da ita, a iyaka sanina da ita Umar ta aura, to me ya faru? Ko sun rabu ne?.

Bayan na gama girkin, kasancewar lokaci ya kure tunda har an gama sallar magriba lokacin, yasa kayan ma a kan dinning na barsu gabadaya, na wuce dakina.
Wanka na fara yi, sai da nayi sallah sannan na zauna zaman shafa mai da hoda. Ina cikin shafar ne naji hayaniya ta fara tashi, na dan dakata, jin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa na dauki doguwar hijabi na zura na fita falo domin in ga abinda yake faruwa.

Raheemah na jingine da bangon falon, Yaya da Ameerah kuma na tsaye a tsakiyar falon sunyi cirko-cirko suna raba idanu kamar wasu zakaru.




*☆⋆47⋆☆*




Kallo daya zaka yiwa yanayin da mutanen falon suke ciki, zaka fahimci cewa babu lafiya.

Ameerah na tsaye nesa kadan da Yaya, in banda rawa, babu abinda ilahirin jikinta yake yi. A tsorace take sosai.
Shikuwa Yaya ya tsaya jimke da hannu, sai dana kare mishi kallo sosai sannan na fahimci cewa wata yar karamar farar takarda ce jimke a hannun nashi, wadda ya kama ya rukunkume har knuckles dinshi sai da suka yi fari, a gefe guda kuma jikinshi yana rawa cikin bacin rai.
Raheemah kam ta coge daurin dankwalin nan nata a tsakiyar ka kamar yadda ta saba, da alama itama hayaniyar ce ta fiddota zuwa cikin falon.

Hankalin Yaya gabadaya yana kan Ameerah, kallon da yake watsa mata kadai ya isa yasa duk girman kai da ji da kai na mutum ya saddakar masa ko da bai yi niyya ba kuwa. Ni kaina da nake gefe sai dana ji gabobin jikina sunyi sanyi. Ban taba ganin wannan side din na Yaya ba. Da alamu ma sam bai san da wanzuwarmu a falon ba, idan ma ya sani to yayi kokari wajen nuna cewa wanzuwar tamu anan bata shalle shi ba.

Ya nuna mata hannunshi da yake rike da farar takardar nan yana nuna mata, cikin wata irin murya da ta sanya ni na kara kallonshi da kyau domin in tabbatar da cewa da gaske shi dinne dai, he sounds deadly. Calm, but deadly. Kamar wani sabon mutum da ban taba gani ba, haka ya juye ya koma a lokacin.
Yace "care to explain, ko menene wannan kike kokarin zuba min a cikin abincina?". Jin abinda yace yasa na zare ido ina kallonsu, a lokaci daya kuma ina kara matsawa kusa dasu.

Ameerah ta dan ja baya da sauri, tsoron dake shimfide akan fuskarta da baka taba rabata da kwalliya, ya bayyana zane baro-baro, instead, shi ya zame mata kwalliyar yau.
Tace "don Allah kayi hakuri. Wallah na tuba, don Allah!".

Sai dai bai jira ta gama magiyar da take yi ba, ya daka wata irin gigitacciyar tsawa, "Don't you dare Ameerah! Tambayarki nayi, damn your sorrys don ba ita nake bida ba. Ki fada min, meye hadinki da shinkafar bera na tsinceta a hannunki kina kokarin sakata cikin abincin da zan ci?!".

Naji ana min wata irin kururuwa a cikin kunne, kaina yana juyawa kamar ana katantanwa dani, kafin wani irin duka a tsakiyar ka ya ziyarce ni kamar ana buga min guduma a ka. Ala dole na lalubi kujerar dake kusa dani na zauna babu shiri saboda rawar da kafafuna suka dauki yi.

Yanzu kam hawaye ne suke ta zarya akan kumatunta, daya bayan daya suna sintiri babu kakkautawa.

Yaya ya kura mata ido, "shikenan? Kaunar da kike ikirarin kina yi min kenan? Soyayyar kenan? At the end of the day kiyi sanadin raina?".

Kai ta hau girgizawa, "ba haka bane, wallah banyi da niyar cutar da kai ba, ka yarda dani. Sharrin shaidan ne!".

Yace "kada ki maida ni sakarai mana! Da idanuna na ganki kina zuba abinnan fa. Ko kuwa kina nufin ki ce sharri na miki, ko kuma idanuna ne basu gani daidai ba?"
Tayi shiru kanta a kasa, sai kai data girgiza kawai.

Yace "kina fa bata mana lokaci, ki fada min dalilin ki, ko kuwa kina so ne kice min gishiri ne wannan a hannuna?".

Ta daga baki da kyar tace "akwai antidote dinta, da kaci zan baka yadda zaka amayar da gubar da kaci. Wallahi ba zan taba yin abinda zai cutar da kai ba, na rantse da Allah!".

Sai dai ko kadan rantsuwar da take ja bata dada shi da kasa ba. Instead, sai kallonta daya tsaya yana yi. Babu mamaki tunani da lissafin gidan kula da masu tabin kwalwa mafi kusa yake so ya lalubo.
Da kyar ya iya kakaro sautin, "me yasa?", daga can kasan makoshinshi.
Bata amsa ba sai daya kara jefa mata tambayar cikin daka tsawar da tafi ta dazu gigitarwa.

Ta ja baya da sauri, "munyi zaton idan ka ci abincin zaka zargi ita ta zuba maka, sai ka sallameta!".

Na tsayin lokaci, duniyata sai ta tsaya cak. Bansan lokacin da hawaye suka fara zarya suna gangarowa kan kumatuna ba.
Wannan shine karshen kiyayya da wani mahaluki zai taba nuna maka a cikin rayuwa, shin ta tsani ganina har haka ne da abin zai kai ga laka min sharrin kisa? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!.
Yanzu da Yaya bai shigo ba akan lokaci ya sameta cikin aikata wannan aika-aika ba, mai zai faru? Da haka zan kare rayuwata da laifin attempted kisa, haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba. Da haka rayuwata zata kare, ina tsanar kaina da tuhumar ta yaya hakan ta faru? Yaya da yan'uwanshi da suka zama nawa yan uwan nima suna tsanata?
Me na yiwa wannan matar ne da zan cancanci haka daga gareta?.

Yaya bai ce komi ba sai pacing daya hau yi kamar mai fareti, cikinmu babu wanda yayi gigin yin ko motsi, sai ni da lokaci zuwa lokaci zan ja majina ko in share hawayen fuskata.
Ya dawo ya tsaya a gabanta, "what were you thinking you silly woman?", ya furta with venom a cikin muryarshi. Kafin ya juya ya cigaba

Please Login or Register in order to submit comment