Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hannuwana har rawa suke yi lokacin dana dauki wayar na karata a saitin kunnena. Nace "hello?", da kyar kamar wadda take koyon magana.
Yace "yanzu na karaso kofar hostel din, ina daga waje ina jiranki", cikin wani irin husky voice, deep and soothing a lokaci guda. Sai naji kamar yau na taba jin muryar. Naji wata irin rawar cikin jiki ta ziyarceni, kamar na fito waje cikin muku-mukun sanyinnan, na kakaro sautin "to", daga can kasan makoshi na kamar an shake ni. Na kashe wayar na ajiye a gefena ina maida numfashi da sauri da sauri kamar wadda tayi gudun ceton rai.

Sai dana tabbatar da natsuwata ta dawo cikin jikina, sannan na tashi tsaye, duk da haka sai da naji kamar zan kifa saboda yadda kafafuna suke rawa. Wani tray dana amsa wajen Esther, mai fadi ne ba laifi, da zanen manyan jajayen furanni a jiki. A cikin jug dinshi na zuba zobon da nayi, na yanka cucumber da kankana kanana a ciki bayan na cire 'ya'yan, su kuma kananun cups din jug din na kifa guda biyu akan tray din.
Na shirya meat pie din akan wani karamin plate, na kawo foil paper na rufe shi. Na dora lemun dana amso da ruwan akan tray din, aka yi sa'a ya kwashe duka.

Na kara duba fuskata a cikin madubi naga lafiya lau, na dauki gyale mai dan fadi nayi yafawar zamani, na kawo turaren fantasy na kara badawa a jikina. Duk wadannan abubuwa da nake yi, cikin takatsan-tsan da rawar jiki nake yinsu. Na dauki takalmi mai dan tudu baki na saka, sannan na dauki tray din wannan da wayata na fita.

Akwai wani karamin waje daga can gefen hostel din, yawanci dalibai kanyi karatu a ciki musamman irin group assignment da aka hada maza da mata a ciki, nan suke zuwa suyi karatun. Ko kuma idan wata daliba tayi baki nan take zuwa dasu idan maza ne. Nima can na fito da rana na samu wata yar kwana, inda babu yawan giccin mutane sosai na share na kuma goge kujerun da aka kera na sumunti a wajen da niyar nan zan jagoranci Muhammad din idan yazo.

Lokacin dana fito waje ban ga kowa ba, da alamu a can wajen gate ya tsaya, don haka na fara kai kayan hannuna wajen da zamu zauna na ajiye su, sannan na taka a hankali zuwa wajen gate din. Idan wani ya kalleni a lokacin, nasan babu bata lokaci zai ce tafiyar yanga ce nake yi, sai dai a zahirin gaskiya, tsananin fargaba da tsoro ne suka sa nake tafiya kamar wadda take jan kafarta. Ban san dalilin wannan sudden tsoro da naji ya dirar min ba, amma nafi danganta hakan da cewa kila saboda kawai haduwarmu ta farko kenan yau.

Na fita daga gate din, idanuwana suka fara karade ilahirin wajen da kallo, ina duba gefena na dama, na hango shi. Jingine da motar rav4 baka kirin, sanye yake da wata jikakkiyyar danyar shaddar getzner ruwan kasa mai haske, ta sha dinkin surfani na zare shima ruwan kasa amma mai duhu sosai, takalmin kafarshi shima ruwan kasar ne irin flats dinnan na maza, ko ba'a fada maka ba kasan ba karamin kudi da daraja zasu yi ba. Daga inda nake, babu abinda zan iya karaswa game da features dinshi, kawai dai nasan dogo ne, ya danyi min nisa, ban hangi komi a fuskarshi ba, musamman da yake a daidai wannan lokacin ya nutsa wayar tashi cikin wayar hannunshi. Sai hular kanshi kawai.

Na samu kaina da takawa a hankali zuwa inda yake, kaina a kasa ban iya dagowa na kalleshi ba saboda wani irin nauyinshi da naji ya dirar min, amma duk da kan nawa a kasa yake, ina jin zafin kallonshi a cikin jikina. Sai dana fara ganin kyawawan jerin dogaye kuma zara-zaran yatsun kafarshi da suka yi matukar kyawu cikin kyakkyawan takalmin kafarshi, sannan na iya daga kaina a hankali.

'Assalamu Alaik...", sallamar da nayi niyar yi mishi, ta makale a makoshina lokacin da na dago kai a lokacin, muka hada idanu hur-hudu dashi.
Fuskarshi bata nuna mamaki, al'ajabi ko rikicewar tunani kamar yadda na tabbatar suna zane akan fuskata ba baro-baro. A tsaye take kyam, maimakon hakan ma, sai wani tattausan murmushi daya bayyana akan fatar bakinshi.
Yace "wa alaikumussalam wa rahmatullah... Har kin fito?".

Na tsinci kaina da karkata kaina gefe guda cikin tsananin mamaki, can kasan zuciyata kuma ina maimaita kalmar 'har kin fito?', ko me yake nufi da hakan?.

Na dan duka cike da girmamawa nace "Yaya Bilal ina yini?". Gabadayan idanunshi fuskata suke karewa kaina kallo kamar yau ya taba ganina, yace "lafiya lau Na'ilah! Ya kike?".
Na gyada kai kawai, zuciyata cike da tambayoyi, yayin da a gefe guda kuma naci gaba da dube-dube ko zan hango Muhammad. Ya nake ganin kamar mu kadai ne a gaban hostel din? Ko kuma bai zo ba yace min yazo?.

Na furta tambayar da take ta ci min rai tunda naci karo da Yaya ne, nace "ko kazo wajen wata ne anan ko wani?", a raina nace ko dai wani auren yake nema ne? Na danyi shivering lokacin da tunanin abinda hakan yake nufi ya darsu a cikin raina.

Ya cigaba da jefa min irin wannan kallo da tunda muka hadu dashi yake jefa min, yana kuma gyada kai a hankali, "wata".
Na dan zare ido cikin mamaki, kafin nayi kokarin maida mamakina na kulle, sai anjima Janan zata sha labari, nace "uhmm, to. Dama nima akwai wanda na fito gani ne dama, tunda bai zo ba kuma bari in koma, ka samu wadda kazo ganinta ne ko kuma kana bukatar in dubo maka ita ne?".

Idanuwanshi na fitar da wasu alamu, awe and mischief, yace "a'ah, no need. Nagode. Na ganta ai, gata nan a gabana!".
Na dan juya bayana cikin tunanin in hadu da wadda take nufi din, sai naga wayam. Na girgiza kai kamar wadda take kokarin shaking din wani feeling, gabadaya abinda yake faruwa yanzu yana da matukar daure kai, na kasa banbance tsakanin karya da gaskiya. Ina bukatar in ganni a cikin dakina, in kwanta akan katifa inyi tunanin abinda yake faruwa.

Na gyada kai a hankali, a hankalin dai nace "to shikenan, zan koma ciki ni, a gaida gida". Kafin ma ya samu damar daga baki ya maido min amsa, maybe juya da sauri na daga kafata na fara tafiya.
Yace "Na'ilah, Muhammad ne fa!".

Naji na tsaya cak, kamar wadda aka kafe. A hankali na juya, zuciyata tana bugu da karfin masifa, cikin idanunshi nake kallo directly, ina laluben wani alamu da zai nuna wasa yake yi a cikin idanun nashi. Tunani nake, ta yaya aka yi yasan zance na da Muhammad? Ko dai yana daga cikin abokanshi ne? Haba, babu mamaki. Kila ma Muhammad din abokinshi ne, kila shi yasa zai biyo shi su zo tare ko. Na dauke idanuna daga kanshi zuwa cikin motarshi, so nake inga ko akwai alamun mutum a ciki, amma duhun gilasan motar ya hana in hango komi.

Kallon-kallo muka fara yi dashi, ganin bashi da niyar yi mun karin bayani akan wannan katoton al'amari, yasa ni na bude baki kamar wadda take tsoron magana, nace mishi "a ina kasan Muhammad? Ka san shi ne?".

Akwai wani nag feeling da yake damuna, daga can kasan zuciyata, wani bangarene yake jefo min tambayar, anya? Amma nake danne shi tun karfina, babu wata anya ko tantama, babu abinda yake faruwa. Yaya Bilal ba wani bane face aboki, ko kuma wani daya san zancena da Muhammad, and nothing more!.

Maimakon ya bani amsar tambayar daya min, sai ya daga kafa ya fara takowa a hankali har ya iso daf dani, ni kuma saboda tsabar rikici, na rasa ta yaya zan iya daga kafata inyi baya duk da cewa mun danyi kusanci dashi. A hakan ina iya shakar kamshin turaren daya fesa, kamar tufafin na nutsa a fuskata.

Ya daga yatsarshi manuniya yana nuna saitin kirjinshi, yace "ni nan, Na'ilah, nine dai Muhammad din da kike jira, Muhammad naki, wanda zai so ya ganki!".

Na kura mishi idanu kawai, idan banda bugun zuciyata babu abinda ya canza daga yanayin motsin jikina. Kila ma sandarewa nayi a tsaye ban sani ba. Ban san me yasa Yaya Bilal zai ji bukatar yayi min irin wannan wasan ba, halayenshi na kamewa da rashin son wasa yasa kwata-kwata na kasa yarda da cewa tsokana ce kawai kamar yadda nake nanatawa kaina domin karyata abinda zuciyata take fada min tunda na bayyana a gaban Yaya Bilal yanzu.

Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a haka, kawai ina kallonshi kamar wata bakuwar halitta. Na rasa gane a duniyar da nake, shin duniyar mafarki ce ko kuma ta gaske?.

Na samu kuzarin daga baki da kyar, bayan dogon lokacin nan, nace "wane Muhammad kake magana akai, Yaya?".

Ya saka hannu cikin aljihun rigarshi, ni kuma kamar sakara na bi hannun nashi da kallo har ya ciro wata kirar iPhone, fara kal da ita. Ina kallo yayi unlocking dinta ya fara danne-danne, ba'a dauki lokaci ba wayata ta hau kara da vibrating a hannuna. Sunan Muhammad ya fito baro-baro a jiki, yayin da a gefe guda kuma Yaya yake nuno min wayar hannunshi fuskata. Lambar wayata ce itama gata nan, da sunan 'baby na' a jiki, ga kuma hotona akai.

Yace "ko baki yarda da cewa nine Muhammad ba? Kina bukatar wata shaida ne daban?".

Na rikice, na rasa abinda zan tunana a cikin raina, me ke faruwa ne wai?!. Mafarki nake yi ne? Ko kuma kwalwata ta fara samun matsala ne? Ko kuma kwalwar Yaya Bilal din ce ta samu matsala?".

Kamar wata mahaukaciya sabon kamu, haka na fara ja da baya ina girgiza kaina, komi juya min yake yi, shi kanshi Yayan dake gabana bana ganinshi sosai. Da alamun hawaye ne suka ciko min idanu, naga lokacin da Yaya ya fara biyo ni shima, tun yana tafiya a hankali har ya daga kafa sosai ya tadda ni, ya kai hannu da niyar kamo ni yana mai ambatar sunana, "baby na!!".

Ko rufe baki bai kai ga yi ba, na juya na daga kafa a sukwane na fada hostel. Wani daga cikin security yana tambayata lafiya lau? Me ya faru?? Amma na kasa amsa mishi.

Tunani daya ne zuwa biyu a cikin raina a wannan lokacin, lallai na cika sakara mara tunani. Ta yaya aka yi duk tsayin wannan lokaci da muka dauka muna waya dashi ban taba daukar muryarshi ba, ta yaya idanuna suka rufe ne? Ta yaya nayi sake irin haka? Kuskure ne ko kuma rashin sani??.

_'Na sanki farin sani!...'_

_'Sunana M.B!...'_

_'Ina aikine da wani kamfanin buga takardu...'._

Of course ya sanni farin sani, Yaya Bilal ne shi fa after all. M.B yana nufin Muhammad Bilal. Yana aiki da kamfanin buga takarda, dama mutumin da yake aiki da daily trust ai dole ma ya sarrafa takardu.
Mai yasa ban taba yin irin wannan tunanin ba, sai yanzu da ta faru ta kare? Babu zancen komawa baya??!.
















*☆⋆22⋆☆*






A kofar daki muka ci karo da Esther ita kuma zata fito. Ta biyo bayana da sauri ganin yadda na wuceta a rikice tana jefa min tambayar lafiya? Amma na kasa daga baki in bata takamaimaimiyar amsa.
Na hade da gyalena da wayata nayi jifa dasu kan katifa, ni kuma na silale na zauna a tsakiyar dakin. Gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shin wai ko dai mafarki ne nake yi?.

Esther ta dafa ni tana dan shafa bayana in a comforting manner, tace "Na'ilah, me yake faruwa ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne?", na bita da kallo kawai, ban ma san me zan ce mata ba. Kai ko na daga baki ma bana tunanin magana zata iya fita. Don haka na cigaba da binta da kallo kawai.

Wayarta tayi kara, ta duba mai kiran, da sauri ta juyo tana kallona, "sorry Na'ilah, ana jirana a waje. Don Allah kiyi hakuri kinji? Bari inje in dawo yanzu". Ta fita da sauri.
Bayan fitarta na tallafo kumatuna da duka hannuwana biyu, na kurawa wayata dake yashe a kan katifata kamar ita zata bani amsar tambayoyina. Abin gwanin ban dariya gwanin ban haushi, yanzu ashe duk wannan waya da muke sha da shi, duk tsayin wannan lokacin, dama da Yaya Bilal muke waya? Haba, biri yayi kama da mutum! All those stolen glances idan muka hadu a karkashin rufi daya dashi wadanda daga farko na dauka ko ni ce nake wassafa hakan a cikin raina, kallon daya dinga jefa min ranar nan da nayi rashin lafiyar nan, har na dinga tunanin zafin zazzabi ne yasa nake ganin hakan, dama da gaske ne? Dama duk wannan lokacin, kallona kawai yake yi a dage, yana min kallon wata sakara wadda bata san abinda take yi ba? Da kuma maganganun daya dinga min a jiya, ba karamin godewa Allah nayi ba da bai sa giyar soyayya ta kwasheni na dauki alkawarin da ba zan taba cikawa ba. Yanzu da na amince mishi fa aka sa mana aure ko aka daura ba tare dana taba ganinshi ba? Nasan mutuwata ce tazo kawai.

Hankalina ya kasa kwanciya, duk inda na juya idanun Yaya Bilal kawai nake gani a cikin dakin, haunting me. Naji na fara damben warto numfashina da naji ya fara guduwa, ina warto shi da kyar.
Ban san lokacin dana rarumi wayata ba na dannawa Janan kira.

Ta dauka cheerily, murya cike da tsokana, "hey.., har Muhammadun naki ya tafi ne?!".

A rikice na hau kiran sunanta ina maimaitawa kamar karatu, "Janan... Janan...!!".

Nan da nan ta rikice, tace "subhanallahi, Na'ilah me ya faru ne?".
Nace "Yaya ne! Yaya Bilal ne... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau ya zanyi da rayuwata? Hasbunallahu wa ni'imal wakil!!".

Ai sai na kara rikitata, naji alamun motsa kaya daga can inda take, "me ya samu Yayan? Kun hadu dashi ne? Wai meke faruwa ne? Kiyi min bayani please!".

Na daga baki da niyar yin magana, amma sautin komi ya kasa fita.
"gani nan" kawai tace, kafin inji ta kashe wayar. Na koma na jingina da bango ina lumshe idanuna.

Abin kamar a almara haka nake jin shi. Yau da safe dana tashi, mafarki na farko dana fara tunawa wanda nayi ne akan Yaya Bilal. Maimakon abin ya bani mamaki, sai ma ya bani dariya. A tunanina meye hadin kifi da kaska? Tunanin Yaya Bilal da ni a waje daya, abu ne da bai taba, ina nufin koda wasa bai taba gittawa ta cikin raina ba, ko a mafarki ban taba ganin hakan ba sai a yau din. Shi yasa ko a dazun abin ya matukar bani dariya, saboda babu wani abu daya kamata inyi a wannan lokacin da yafi inyi dariyar.
Amma yanzu da naga abin yana shirin ya zama gaskiya, sai kuma abin yake shirin ya sanya ni kuka.

A yadda nake dinnan, a haka Janan tazo ta sameni. Ta tattagoni jikinta cikin tsananin nuna damuwa, ko bata furta ba fuskarta da idanuwanta sun nuna min hakan baro-baro. Hakan yasa naji jikina yana relaxing, na kwantar da kaina akan kafadarta, totally vulnerable.

Kusan mintunanmu biyar a hakan, kafin ta dago kaina daga jikinta, murya a tausashe, kamar wadda take tsoron idan ta dan kara daga muryarta zata saka ni kuka. Kodayake, hakan ne, ni nasan a yadda nake jina dinnan, zuciyata a wuya, to abu kadan da bai gamshe ni ba a yansu zai iya sa ni fashewa da kuka.

Tace "me ya faru ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne? Me kuma ya jefo Yaya Bilal cikin wannan magana?".

Na daga baki nace "Janan, Muhammad... Shi.. Yaya Bilal...". Nan da nan na fara hargitsewa. Tayi saurin taba kafadata, tace "kinga, nutsu kin gane? Yauwa, just calm down. Everything's good, ok?".

Na gyada mata kai a hankali, na fara jan numfashi ina saukewa a hankali har naji bugun zuciyata ya daidaita. A hankali na bude baki nace "Muhammad, Yaya Bilal ne! Yaya Bilal ne Muhammad Janan!!".
Naji wata zazzafar kwalla ta ciko min idanu, nayi saurin kokarin maida ta. Sai da na fadi maganar da karfi ta shiga kunnuwana, sannan naji gaskiyar lamarin yana shigata.

Janan ta zuba min idanu tana kallo, kamar wadda take jira in ce mata tsokanarta nake. To ai ni kaina jin abin nake kamar a mafarki ko a almara. Ni kaina na kasa yarda wai hakan ta faru.

Zuwa can tace "ta yaya?".
Nan na gyara zama na fede mata biri har wutsiya, ban rage mata komi ba. Tun daga fitata daga hostel, maganar da muka yi dashi har gudowar da nayi. Ban san cewa hawaye nake ba, sai dana sauke aya. Naja numfashi na ajiye, sannan naji lema tana bin kumatuna. Na sa hannu na share, amma ina dauketa wata ta sake gangarowa.

Na dora da, "Me yasa ni? Me yasa Yaya zai yi min haka? Me yasa hakan zata faru dani? Janan ya zanyi?".

Tace "mafita daya ce, kiyi hakuri ki danne zuciyarki, ki saurareshi kiji abinda zai ce".

Na tabe baki ina jinjina kai, "tab, lallai ma! In saurareshi ince mishi me? In gaya miki gaskiya ni da Yaya yanzu sai dai hange daga nesa, kai ko daga nesar na hango shi, zan canza hanya ne a sukwane ba tare da bata lokaci ba!".

Tace "amma kuma hakan ba mafita bace Na'ilah. Kika san ko yana da wani kwakkwaran dalili da yasa yayi hakan ne? Kada fa ki yanke hukunci cikin fushi Na'ilah, daga baya kuma ki zo kiyi dana sani!".

Nayi wata yar dariya da daga jinta babu digo ko alama ta farinciki a cikinta, sai akasin sa. Nace "wane dalili ne daya wuce ya muzanta ni, ya maida ni sakara? Da ba don nasan Yaya ba sosai, da sai ince baki ya hada da Umar ko wani akan suyi wasa da hankalina. Kodayake, ban san shi ba yanzu anymore!".

Janan ta kalleni, frowning. Tace "Ni nasan Yaya Bilal sosai, ba zai taba stooping that low to do something like this ba. Kamar yadda nace, da ace baya da kwakkwaran dalili, to ina mai tabbatar miki da cewa da ba zai taba ma bata lokacin shi tsawon lokutan nan ba!".

Na turo baki, "yanzu kuma kina bin bayan Yayanki ne, zaki yace min baya?".
Ta matso kusa dani da sauri, "koda wasa wallahi, haba, akan me zan miki haka? Ni fa shawarar da nake gani zata fissheki ce naki baki ba wani abu ba".

Na tashi tsaye, "whatever dai, ni dai an gama min wasa da hankalina, bana kuma tunanin zan iya tsayawa in sake sauraron shi".

Janan bata ce komi ba, ta zuba min idanu. Ni kuma na fara cire kayan jikina.

Idan da ace wani zai gaya min cewa a haka yinin na yau assabar zai kare min, da tuni zan karyata shi. Idan ma raina ya baci sosai, in kara da fada mishi bakar magana. Yau dana tashi da safe, ba haka na hango ni ba, ban taba tunanin akwai wani abu da zai zo yayi ruining yinin nawa na yau ba, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, yinin yayi bacin da ban taba tunani ba.
Na kalli kayan jikina dana cire, naji wani makokon takaici ya kawo ni wuya, ko linke su banyi ba na cukuikuyesu na jefa cikin kayana. Na dauki towel babba na daura a jikina. Ban cewa Janan komi ba, na dauki bokiti na sauka kasa na tari ruwa naje na watsa ruwa a jikina haka nan.

Ina cikin yin wankan naji an kira sallar magriba, don haka na daura alwala na koma sama.
Ina shiga dakin naci karo da Esther a zaune, da kayan dana baro a inda na ajiye. Ni na ma manta dasu. Daga ita har Janan suka bini da kallo.
Esther ce ta fara magana, ban san me Janan tace mata ba, amma naji bata tado min zancen dazu ba. Na dai ji ta tana mitar, "Ni wallahi nayi zaton ko accident ne suka yi ko wani abu a dazun, har na tsorata. Daga yace wani abu na gaggawa ya taso, sai ki wani rikice har haka? Lallai kina da babban aiki kuwa yarinya!". Ni dai na shareta ban ce komi ba.

Kayan dana ke sanyawa na shan iska na sa, na tada sallah nayi. Ina gamawa itama Janan ta shigo dakin, don haka na koma gefe na bata waje itama tayi. Tana gamawa Esther ta kallemu, tace "ni fa yunwa nake ji, kuma na rantse ba zanyi wani girki ba alhalin ga abinci nan ina gani a gabana. Idan ba zaki ci wannan abun ba, ki bani inci don ba zan so ayi asarar su ba gaskiya".

Nace "gashi nan kiyi ta ci".
Tayi tsalle ta rarumo kayan, Ina ji Janan tana itama a ajiye mata bari tayi sallah ta zo taci, nayi banza dasu su duka.

Ana kiran sallah na tashi nayi. Janan ma tana gama nata, ta zauna ta tada meat pie din da Esther ta rage mata da sauran drinks din. Dama guda biyar ne nayi babu yawa. Janan tana gamawa ta kalli agogo, tace "bari in tashi in tafi kafin Yaya ya dawo, yayi fada".

Ai jin an ambaci sunan Yaya, sai naji raina ya kara dagulewa. Na koma kan katifa na zauna, na harde hannuwa a kirji ina turo baki ina kallon Janan tana gyara zaman hijabin jikinta a wuyanta, ta gama ta juyo tana kallona, "mai kike jira ne, ba zaki raka ni ba?".

Na kara turo baki, "a'ah, ki gaida mutan gida!".
Ta daga hannuwa sama in mocking surrender, cam cikin idanunta alamun dariyar da take ta kokarin boyewa ne. Na harareta, ta kara yin murmushi, tace "yi hakuri ki maida wukar, ba ni na kar zomon ba kin gane? Bari in karasa gida ni kam. Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, kada ki bari wannan abin ya taba zuciyarki kinji?".
Na kalleta kawai, sanya abu a cikin rai na nawa kuma?
A haka dai ta mana sallama ta tafi.

Ina zaune ina kallon Esther data tashi tana hada kayan, tana cewa ita dai ba zata yi wanke-wanke ba fa, "Sai dai idan kin tashi gobe ki wanke kayanki amma ba zan iya ba".
Ta dai gaji da mitar ta tayi shiru ganin ban tanka mata ba. Tana gama abinda zata yi, tace min ta tafi class. Exam dinmu ranar monday ne, amma nasan ko giyar wake na sha ba zan iya yin karatu ba yanzu. Don haka na kwanta kawai ina ta faman saka da warwara a cikin raina.

Har wajen karfe goma sha daya na dare idanuna biyu kyar, babu alamun barci a cikinsu. Juyi kawai nake yi, ba tare da takamaiman wani abu da nake tunani a kai ba. Wayata ta fara kara, daga farko cak nayi a zaune, hatta da numfashina sai daya tsaya sakamakon jin kalar karan. A hankali na juya na kalli wayar, babu shakka sunan Muhammad ne, ko kuwa Yaya Bilal zan ce? Yake yawo akan wayata.

Ban iya motsawa ba har ta katse, tana katsewar aka sake kira. Na hau gyada kai ina kara girgizawa cikin tsananin mamaki, yanzu har Yaya yana da sauran kunyar da zai iya kirana a waya dama? Oh duniya ina zaki damu?!.

Na dauko wayar da niyar kasheta, hannuna ya silale ya taba answer and speaker button ba tare dana kula ba, sai dana ji muryar shi radam kamar a cikin dakin yake yana magana, "hello? Oh thank God! Baby kina ji na? Baby...?!".

Da sauri na danne wayar har ta mutu, na dafe saitin zuciyata data hau bugawa da sauri kuma da karfi. Jin muryar shi a yanzu, sai naji kamar an tado min wani tsumi. Ko ba'a fada ba, nasan yau munyi baram-baram ni da barci.




Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe don Allah. Jiya sai dana yi typing, nayi zaton na turo na goge, sai daga baya naga ashe ban turo ba.














*☆⋆23⋆☆*






Washegari na tashi da wani azababben ciwon kai wanda ban taba zaton wani mahaluki zai taba yin kamar sa ba sai a ranar. Ni dama nasan za'a rina, yadda jiya na kwana ina sake-sake, barci ma sai gab da sallar asubahi sannan ya daukeni. Dalili kenan da yasa na so in makara sallah yau. Ina yin sallar kuma dana koma barci ma, kasa komawa nayi, sai can rana har ta ma fara fitowa sannan nayi barcin.
Yanzu kam zaune nake akan katifata da misalin karfe goma da

Please Login or Register in order to submit comment