Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ki fadawa Janan, zata fada min. Sai anjima!".
Yasa kafa ya fita daga fadin haka, babu ko waiwaye.

I was too shock, ko hannu na kasa motsawa balle gangar jikina. Baki a dage, ido a bude akan kofa, haka su Janan suka shigo cikin dakin suka sameni. Wato ni za'a nunawa attitude? Lallai kuwa.

Janan ta fara tarkata mana kayan da aka baza a dan lokacin, likita ya shigo ya kafa min dokar cin abinci da samun barci isasshe. Ni dai jinshi nake yi, ya gama dogayen bayananshi, ya sallame mu muka kara gaba.

Da yake clinic din anan cikin unguwarmu yake, a kafa muka karasa gida.

Zuwa lokacin kowa yaji labarin yadda daurin aurena yazo da canjin yanayi, kuma canjin ango. Nan da nan mutanen da suka yi saura suka rufa a kaina da kalmomin 'sannu, ya jiki? Ashe abinda ya faru kenan? Sai ayi ta hakuri, Allah ya nufa shine mijin', wasu kuma har su kara da 'ai dama naji ance kun yi soyayya dashi, abin ya kwana gidan sauki ma', da dai sauransu.

Muka samu muka yakice su da kyar muka shige can kuryar dakin Anty Alawiyya, Allah yasa babu mutane sosai.
Na zauna a gefen gado, Maryam ta tafi nemo min abinda zan ci in sha magungunan da aka bani, Janan kuma ta zauna a gefena.

Nace mata "me ya faru da Dr. Ne?". Babu wanda naji ya sake tado zancenshi, ga yanayin yadda suke nunawa kuma, basu da alamun yi mun bayanin abinda ya faru.

Ta tabe baki, "hmm, mutuminki ba sai suka shanya yan daurin auren ba? Tun ana jira har aka gaji, babu wani dangin ango da aka gani a wajen daurin aure. Yaya Jameel ne da yazo daurin aure ya kira wani abokinshi yaje har can gidan su angon ya tambayo ko lafiya? Zancen da nake miki, ashe bawan Allah ya kwana ya huce a kasar London, ya bar sakon a gaya miki yana miki fatan alkhairi, amma idan kinga zaki iya jiranshi nan da shekaru biyun, to babu damuwa. Amma a halin yanzu ba zai iya daukar hidindimu masu yawa ba, liability yace. Shine su kuma cikin wadanda ya barwa sakon, daga abokai har yan'uwa, aka rasa wanda zai iya tako kafarshi yazo yayi bayani a mutunce kamar yadda aka faro a mutunce. To ana shirin sallamar mutane ne a basu hakuri, Yaya Jameel yace ba za'a yi haka ba, tunda an san da manemi a gida, ai kawai yazo ya biya sadaki, shine fa aka daga daurin auren zuwa yamma yadda Yaya Bilal yazo ya samu daurin auren".

Na jijjiga kai cikin sanyin jiki, wato har zabata aka yi akan abin duniya, aka kuma kirani liability? Allah kenan. Shi kuma Yaya Jameel, apparently shine makasudin jefa ni cikin ha'ula'in da nake ciki yanzu kenan?.
Janan ta dafa kafadata, "meye na wani abin damuwa anan? Ai in gaya miki ki kwantar da hankalinki Hajiyata, ki je ku kwashi soyayyarku wallahi. Shima Yayan fa ba karamin dace yayi ba, naji ance kusan mutane hudu suka nemi aurenki a take a lokacin".

Na ciza lebe kawai ban ce mata komi ba. A haka Maryam ta dawo ita da Kulsum, da kwanon abinci a hannunta. Haka nan saboda damun da suke yi min, na tuttura abincin ba don ina so ba. Kafin in gama an kira sallar magriba, duk muka yi harama suka yi.


*


Zuwa washegari gidan ya baje da yan biki, sai yan daidaiku da zasu tafi washegari. Shima Yaya Mudatthir a ranar ya juya. Janan tana makale a gefena, bana lekawa ko nan da kofar gida sai na sha fada da mita kamar itace mijin gabadaya.

Sai da safe dana je gaida Baba, sannan yayi min bayanin halin da ake ciki. A raina nace 'ihu bayan hari kenan'. Ya nanata min nan da sati daya za'a tafi dani, in shirya, nace mishi to.

Anty Halima taci gaba da zama damu, wani sabon gyara suka fara min ita da Anty Alawiyya babu kakkautawa. Anty Alawiyya ta kan ce, "zama cikin mata biyu musamman hamshakai yadda naji ana bada labarin matan mijin nan naki sai an dage Na'ilah. Don haka ki dage, ki kama kanki, ki taimaki kanki kafin ki zama saniyar ware".
Abinda bata sani ba shine, maganganun nan nata babu abinda suke kara min sai tashin hankali da taraddadi.

Wasu lokutan kuma haka zata zaunar dani tayi ta min nasihohi da maganganu, salo iri-iri na kissa da kisisina har mamaki take bani wani lokacin. Sai dai bana bin abinda take fada ko daya, kawai jinta nake yi. Mijin da ba'a so, gidan da ba'a so, meye na koyan makaman zama dasu? A ganina fa kenan.

Cikin dan wannan lokacin ban sake ji daga angon nawa ba, babu kira, babu text, babu komi. Wani lokacin ina ji zasu dinga yin waya da Janan, ya tambayeta ya nake, ko kuma akwai wata matsala ne? Haka zasu yi wayar su gama ya kashe, babu ko sakon gaisuwa.

Hakan ba karamin kona min rai yake yi ba, a ganina tun ma kafin aje ko'ina ya fara wulakanta ni, ina ga yaga na shiga gidanshi? Nima sai na shaka fiye da yadda yakamata, nayi watsi da al'amuranshi. Tashin hankalin da nake ciki ma baya barina tunanin wulakancin da yake yi min.

Kwanakin sai suka dinga wucewa kamar a cikin kiftawar ido da bismillah, kafin in ankare, lokacin barina gida yayi.
















*☆⋆34⋆☆*





Kafin zagayowar ranar tarewata, sai dana zama kamar wata matar Malam. Kullum ina fama da carbi da doguwar hijabi a jiki ina ja, cikin dare zan tashi tun daga farkon dare har karshen shi, washegari in tashi da azumi a bakina, addu'a daya ce nake yi ina maimaitawa; 'gidan Yaya Bilal, Allah ka tsareni da shiga wannan gida, Allah kamar yadda ka raba gabas da yamma, Allah ka raba ni da shiga wannan gida'.

Sai dai a kwana na biyar, dole na gama saddakarwa, na fara addu'ar neman ceto da taimako saboda babu alamu ta ko'ina mai nuna cewa zuwana gidan Yaya Bilal zai fasu. Ranakun kullum kara matsowa suke yi, hakan kuma yake kara saka ni cikin tsananin damuwa. Watakila dai karshen farin cikina ne yazo.

Tunda aka daura auren, na fara wasu irin mafarkai masu ban tsoro. Sai inyi mafarkin wata mata, fuskarta a rufe da bakin kyalle ta biyoni a guje da wuka a hannunta zata caka min, watarana sai inga nayi tuntube na fadi ta cimma ni, sai inga hannu ya zuro ya daukeni. Wani lokacin kuma haka zamu yi ta gudu, endlessly, babu kakkautawa. Haka zan tashi jikina sharkaf da gumi da zufa kamar an watsa min bokitin ruwa.

Don haka na dage kwarai da addu'a da kuma azkar, har su sadaka ban bari a baya ba.
Musamman Malam din su Kulsum, yayi rubutu ya kawo min ina sha safe da rana. Haka Anty Halima da Anty Alawiyya ma basu kyaleni ba, daga Gashua Fatsu ta aiko da sassake-sassake da magunguna iri-iri da addu'o'i, na lazimce su. Duk da cewa daga farko kin yin amfani nayi dasu, a wautata meye amfanin su to? After all, dama ba zaman gidan nake son yi ba.

Anty Alawiyya ce ta saka ni a gaba da fada da nasiha don ita Anty Halima cewa tayi ta gaji da lallashina, ta koma gefe ta kyalemu.

Anty Alawiyya tace "ke sakara ce wallahi, kina yin abu kamar wadda bata san abinda duniya ke ciki ba, ko kuma baki je kinyi karatun zamani ba. Don kina da kishiyoyi sai me wai? An gaya miki karshen duniya ne yazo? Ki shiga cikin kishiyoyi, ku buga ke dasu aga wadda zata sace zuciyar mijinta ta hanyar da manyan matan annabawa suka bi suka kwace zuciyoyin mazajensu, sai ki zama zara wadda tayi zarra. Amma ki zauna a gefe kina bata ranki a banza, wannan ai aikin kawai ne. Me zaki karas nan gaba?".

Nace "hmm, Anty sai ki dinga yi kamar baki san komi ba wallahi. Ki duba fa irin zaman da kuke yi da taki kishiyar a nan gidan. Sannan ki fa duba yadda yanzu aure yake mutuwa, abin har ya zama kamar yayi. Idan kuma kika yi duba, mafi yawa rabuwar auren kishiya ce take haddasa shi. To idan kishiya daya ta fitar da mace daga gidanta, ni da zan zauna da kishiyoyi biyu fa? Ai ko barbashin toka ta ba za'a gani ba".

Anty Alawiyya da Janan dake gefena a zaune suka kwashe da dariya, na harareta abinda nafi yi tunda aka daura min aure.

Anty Alawiyya tace "ke yanzu zaman gidan nan namu har zaki iya kiranshi zaman kishi?", ta girgiza kai, "ba zaman kishi muke yi ba Na'ilah, zamane muke yi irin na mutanen farko. Kafin hasken musulunci ya sauko, zama na rashin adalci, amma ba kishi bane. Ai ba haka kishi yake ba. Kishi shine inda zaki fito ke da kishiya, ku hada kirji ke da ita, ku rikita mijinku da ririta ta hanyar kissa, ladabi da biyayya, domin neman fada a cikin zuciyarshi. Kishi ba bin bokaye da malamai bane domin neman gurbi a cikin zuciyar miji, a kuma muzgunawa wadda ake zaune da ita, wannan jahilci ne."

"Ni kaina daga farko wannan shine tunanina akan kishi, sai daga baya na fahimci sam ba haka bane, ashe shirme ne. Shi yasa nake matukar kokarina wajen ganin cewa kin fahimci shi zama da kishiya, wallahi ba matsala bace, ba kuma damuwa bace. Matukar kina da gurbi a cikin zuciyar mijinki, kin kuma kama shi kam kin rike, to abinda kike bukata kenan. Me zai yi ruwanki da wata kishiya can? Ita dai ba ita ta zaunar dake ko take ciyar, da shayar dake ba. To menene abin tada jijiyoyin wuya? Yanzu baki ga yadda muke namu zaman ba ne? Ita ce babba, amma wa kika gani yana jan ragamar gidannan gabadaya yanzu?".

Nayi shiru ina jinta, da gaskiyarta. Yanzu ita ce take juya gidannan son ranta, har shi Baban. Ko hidimar bikin nan da aka yi, komi a hannunta yake, kowa ita yake nema idan wata bukata ta taso. Babu ma wanda yake wani tunkarar Ramata, dama bata saka kanta cikin hidimar bikin. Na kuma kula tunda na dawo gida hutun sallah dama kamar fadarta tayi kasa a wajen maigidan, har yanzu dai Anty Alawiyya ce take murza kambun mulkinta.

Tace "bana so ki bi hanyoyin da zafin kishi ya sanya ni bi Na'ilah, hanya ce halakakkiya mai halaka mutane, sai wanda Allah ya tseratar ne kadai yake tsira. Don haka ne nake so ki kwantar da hankalinki, ki tattara shi waje daya ki mayar kan mijinki, ki maida wata matsalar kishiya gefe, zaki ga duk su din ba wasu abubuwa bane, zaki kuma ce na fada miki watarana. Amma kafin nan sai kin kai zuciya nesa, kin kuma yi hakuri, amma da yardar Allah watarana sai dai ki tuno kiyi dariya kawai. Sai dai hakan ba zai faru ba, sai kin tashi tsaye, dole sai kin nemi taimako da tsari daga ayoyin Allah. Tsafi gaskiya ne, kuma a yadda nake jin labarin wannan kishiya taki, ba karamin dabi za'a sha da ita ba. Dole sai kin dage".

Wadannan maganganu su suka kwantar min da hankali. Na karbi kofin rubutu data bani, nayi bismillah na sha. Daga nan kuma naci gaba da amfani da sauran magungunan.

Cikin ikon Allah, kafin zagayowar sati, ni a karan kaina naji canji a cikin jikina sosai. Mafarkan da nake yi ba daina yin su. Haka naji a hankali idea din zama da su Raheemah da Ameerah ya daina terrifying dina sosai. Da idan na tuno yanzu sun zama kishiyoyina, kuma zan zauna dasu, sai inji har numfashi nake fitarwa da kyar. Amma a yanzu, sai inji idea don't is not that bad. Har zama zamu dinga yi ni da Janan muna hira a kansu, tace zata so taga expression din Raheemah lokacin da Yaya zai fada mata ya kara aure, kuma ba wata bace ya aura face ni. Ni kaina da nayi kokarin yin picturing yadda zata yi a lokacin sai naji ina fashewa da dariya. Muka hau kyalkyala dariya ni da ita kamar wasu sababbin kamu, sai da Anty Halima ta leko tana fada sannan muka dan saurara.

Ranar Alhamis aka yi min turaren jiki dana gashi, kasancewar wancan a kurarren lokaci ne, ba'a samu anyi komi ba. Bayan anyi turaren, wata kawar Kulsum tazo ta kama min gashi ta kitse shi sosai, karshen kitson sai data dinga sanya white gel tana kame min shi saboda kada ya warware da wuri. Ranar har dare muna tare dasu muna ta hira. Makitsiyar Nana, tana bamu labarin irin zaman kishin da aka buga a gidansu, su saboda tsabar damben da matan gidansu suka yi, gidan yan dambe ake kiran gidansu a unguwarsu.
"Amma yanzu gashi hakan ya zama tarihi, Anty ma Inna Hadiza take kiran babarmu yanzu". Duk muka kwashe da dariya. Haka dai muka wuni muna shan hirarmu da abokanmu.

Washegari kuma ranar Juma'ah, Anty Halima da Janan suka riga mu tafiya Zaria jeren kayan daki. Sun ce wasu ma guda biyu da zasu tafi da kayan daki daga Gashua zasu je can Zaria din, zasu hadu. Muka yi sallama dasu.

Ranar assabar, karfe tara na safe, motoci biyu suka fara danna horn a kofar gidanmu. Dama sun ce da safe masu daukar amaryar zasu zo.

Tun da safe Anty Alawiyya tasa nayi wanka, ta dauko wata doguwar rigar gown ta wani yadi na saka.
Tun bayan da aka daura auren, aka mayar da duk wasu kudi da kayan Dr. Na Abba dake hannunmu. Wannan rana rigar ta jikina ma, Anty Sa'a yayar su Janan ce ta kawo min ina washegarin daurin aure da tazo, kala biyar ne ire-iren su masu kyau. Dama tana kawowa Janan ta zare wannan rigar tace ranar da za'a kaini zan sanya ta.

Bayan na gama shiryawa, muka tafi dakin Baba yin sallama. Tun lokacin idanuna suka fara raina fata. A dakin Baba, nasiha yayi min sosai akan rayuwar aure da kuma muhimmancin yin hakuri a cikinta, ya rufe da yi min addu'a da fatan alkhairi a cikin rayuwar aurena. Tun ma kfin ya gama, na kuka sosai na tashin hankali.
Ya dauko kudin da aka biya na sadakina, dubu dari biyu cif babu ragi babu kari, ban ma san abinda zanyi dasu ba, kai kawai na girgiza mishi.

Yace "ba zaki amsa ba nufinki?"
Na gyada mishi kai, yace "ai ba za'a yi haka ba Na'ilah, hakkinki ne. Amma tunda kin nuna ba zaki amsa ba, zan turawa Yayanki kudin, ba za'a rasa abinda za'a sai miki dasu ba. Hakan yayi?". Na gyada mishi kai.

Yace "to madallah. Sai ku tashi kuyi haramar tafiya, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare. Allah yayi miki albarka Na'ilah!".

Hakan shi ya sa na kara fashewa da wani kukan mai sauti, tunda muke da Baba, sai yau ne na taba jin kalmar sanya albarka ta fita daga bakinshi. Ban san abinda zanyi ba a lokacin, da yafi inyi kuka.

Kafin in fita daga dakinshi, Maryam ta fita da akwatuna biyu da aka shirya min kayana a ciki zuwa cikin mota, da sauran tarkace. Jiya aka tafi da duk wasu kayan bukata, tun daga kayan gara, kayan kicin da sauransu.

Daga dakin Baba, ko dakina ban koma ba, aka yi waje dani. Sai da muka fita sannan muka ga Ramata cikin tawagar masu bankwana da amarya, na matsa muka yi bankwana dasu ita da sauran yara da suke ta ihun kukan sai an tafi dasu, Anty Alawiyya ce take ta aikin lallashi da ban baki.

Baba da kanshi ya bude min gidan baya, na shiga. Kulsum, Maryam da Hauwa cousin dinmu da tazo jiya daga Gashua, suka shiga cikin motar da nake.
Dayar motar kuma sauran masu zuwa suka shiga. Ana ta daga mana hannu da addu'o'i iri-iri, direba yaja mota muka tafi. Kaina yana cikin mayafin da aka rufa min, hawaye kawai nake sharewa babu kakkautawa cikin tausayawa kaina. Ina ji Maryam ta kira Janan ta sanar da ita tasowarmu kenan, amma ko daga kai ban iya yi ba a lokacin.

Har muka isa Zaria idanuna basu daina digar kwalla ba. At some point zan daina kukan da nake yi, sai dai da na tunano yadda rayuwata zata kasance a cikin gidan Yaya Bilal, sai inji wata kwallar tana zubowa babu kakkautawa. Ji nake kamar in cewa direban ya juya damu mu koma gida, zama gaban su Ramata da duk rashin kirkinsu ya fiye min rayuwar dake shirin tunkaroni, sai dai nasan hakan ba zai yiwu ba.

Wajen karfe goma sha biyu muka shiga gidan Yaya Bilal. Motocin suka yi fakin, duk muka firfito. Janan, Anty Sarah da wasu daga cikin yan'uwansu yanmata sa'anninmu, har dasu Harira, suka fito suka tare mu tare da mana jagora har zuwa sashena. Shine na kusa da na bangaren Anty Sarah, duk da haka babu nisa dana Raheemah.

Janan ta tura kofar, na shiga da kafata ta dama kamar yadda suka umarceni, bakina dauke da tarin addu'o'i. Suka ja ni har zuwa bedroom dina, daga nan kuma masu yiwa amarya sannu da zuwa suka fara shigowa. Masu shakiyanci nayi, masu maraba nayi, masu addu'a nayi.

Kayan dakin da aka jera min ba karamin kyau suka yi ba, babu abinda zan ce da Baba da yan'uwanmu sai dai fatan gamawa da duniya lafiya.
Bayan mun gama hutawa, munyi sallah, Janan dasu Harira suka daukemu zuwa tour din gidan. Dakuna hudu ne da babban falo, sai kicin da main toilet, sauran dakunan ma duk suna da nasu bandakunan, inda biyu daga cikin dakunan aka shake su da jeren kayana. Gado, mirror, closet, da dai sauran tarkacen kayan daki. Haka ma falon, ya sha saitin kujeru masu kyau, babbar plasma, dinning table, har da wajen hutawa daga can gefe. Aka shimfida tattausan rug carpet, aka watsa tuntuna da sofa kwara daya jal, sai katoton vase na fulawa.
Kicin kuwa ba'a ma yin magana, duk wasu kaya da ake bukata a cikin kicin an zuba min su, dangin su electronics da sauran kaya na nunawa sa'a. Ban taba tunanin haka gidan aurena zai kasance ba, a yadda Baba yake, nayi tunanin kila gado ma sai an kai ruwa rana zai sai min, dana gayawa Anty Halima haka dariya tayi ta min, wai bani da saiti.

Komi na gida dai yayi Alhamdulillah, sai godiyar Allah kawai. Daga nan kuma suka ja ni zuwa daya dakin na kusa da nawa, shi babu komi a ciki sai tattausan carpet da aka shimfida, katifa, da desktop table da kofofi. Daga gani babu tambaya nan ne dakin maigida Bilal. Nan suka nuna min akwatunan da aka kawo min, Janan tace "Yaya Sa'a ce zai fi a barsu anan kawai, in kin zo kiga kayanki tunda idan ma an kaisu can din hidimar kai da kawowa ce za'a sha". Na gyada mata kai cikin nuna fahimta.

Akwatuna ne irin na zallar leather dinnan, maroon, dai-daya har guda goma, kowanne shake da kaya. Tun daga na sawa, atamfa ce, laces, materials, yadika masu kyau da armashi, you name it. Kayan kwalliya kuwa kamar za'a bude shago. Harira da suke bude kayan, ta kalleni tana murmushin tsokana, "sai fa kin dage, mijinki mai dan banzan son kwalliya ne, ke kuwa naga alamu kwalliyar ba'a kanki ma take ba, kamar sauran taron matan can nashi daya ajiye dai. Idan kina so kiyi zarra, sai kin koyi amfani da kayan kwalliyar nan".

Nace mata "to waye yace miki so nake inyi zarra a gidannan?".
Tace "duh, lokacin da zaki fara shirin yin zarrar waya sani? Kawai ina baki head-ups ne idan lokacin yazo". Duk suka kwashe da dariya, ni kuma na bisu da harara.

Suka ci gaba da bude akwatunan, dangin jakunkuna, takalma tun daga vincci, gucci, chanels, LV, babu wanda babu. Turaruka, gyale, hijabai, babu abinda babu. Kada ma fannin fashion ear rings da sarkoki su ji labari. Kayan yawansu har yayi yawa, I was very overwhelmed. Yayin da masu ba idanu abinci suke ta zubo addu'o'i, idanuna cike suke taf da kwalla da hawaye, sai fakar idanu nayi na goge su.

Daga nan muka koma dakina, wasu kuma suka tsaya a falo. Aka fara shigo da tarin abinci kala-kala, muka zauna muka ci. Zuwa lokacin da muka gama cin abincin, aka fita da kwanukan abincin, karfe hudu tayi. Lokacin yawancin wadanda suka zo duk sun tafi, ya rage daga ni sai su Janan kawai dasu Maryam da zasu koma Katsina gobe.

Anty Halima ta sanya ni nayi wanka, na sanya riga da zani na atamfa, ruwan goro mai zanen manyan furanni, aka dora min babban gyale a kaina, na saka takalmi flat, muka tafi sashen Raheemah, a cewarsu kai amanar amarya.

Suna zaune a falonta ita da gang dinta, har ma da uwarsu. Taci daurin dankwalinta irin wanda ta saba yi na yan duniya, 'ya'ya sun zagayeta ana ta hira da shewa babu ko kunya.
Muka yi sallama muka shiga falon. Suka yi tsit, kamar ba su bane masu neman tada falon da hayaniya ba.
Babu wanda yayi mana masauku, suka nemi kujera suka zauna, ni kuma aka zaunar dani a kasan carpet. Kaina yana kasa cikin gyalena, naji su Anty Halima suna gaidasu. Babu wanda ya amsa, sai sautin "hummm" da "uhummmm" daya dinga tashi.

Basu daddara ba dai, Anty Halima tace musu "ga amanar diyarmu mun kawo muku, muna fata za'a rike mana ita cikin aminci da amana".

Sai da suka shaki iska, sannan naji muryar Adi, "to ku kunji fa, maciya amanan wai sun kawo muku amana".
Salame ta cafe, "Kaji ma wani rainin wayau fa anan wajen, Momcy. Sai da suka gama shuke-shuken munafurcinsu da kitsa rashin mutunci sannan wai suke kawo amana. Amanar me kuma? Ko roki a maida muku yar ku yadda kuka kawo ta mana, in one piece!".
Momcyn tasu kuma ta kara da, "ku ne ma kuka zauna wani yi musu karin bayani. Ku bari idanunsu su gane musu mana, kishi da ahalin gidanmu ba karamin aiki bane, kuma duk wanda yace zai ja da gidan iko, to ba jikinshi kadai ba, na uwatai ma da ubanai sai sunji labari!". Suka kuwa kwashi ihu har da sowa jin abinda tace.

Ganin abin yana wuce gona da iri, Anty Halima tace "to Allah ya baku hakuri, Allah ya gani mun sauke hakkin dake kanmu. Ku tashi mu tafi".

Sai lokacin Raheemar ta sanya baki, ta tashi tsaye tana wani jijjiga jiki, "hakkin banza dana wofi! Ku har wani hakki kuka sani? Wato dama munafurcin zuwa nan gidan da take yi, tsaface-tsaface take zuwa tana binne mana a gida. Sai da tayi yadda tayi ta tsaface min miji. To wallahi bari kuji, karyarku ta sha karya. Idan kuna cin kasa ku kiyayi ta shuri. An shigo gidan kudi ana ta bude daddaudan baki da ya sha miyar kuka, ana murna an auri mai kudi. To murnar ku zata koma ciki, gwanda ma tun kafin a maida muku diyarku a nakasce, ku dauketa cikin salama ku maidata inda ta fito, idan kuma ba haka ba... tammm!!".

Anty Halima tace "a'uzubillahi, mai kike fada ne haka? Allah ya tsaremuda aikata wannan danyen aiki. Mu ahalinmu babu masu aikata wannan danyen aiki, bamu taba ba, kuma ba zamu taba ba in Allah ya yarda".
Nan fa suka yo mana caaa! Da ihu kamar zasu cinyemu danyu. Nan dai muka samu muka bar musu falon, muka barsu suna barazanar sai sun koya mana hankali gabadayanmu.

Muna fita Anty Halima ta kama baki, tace "ikon Allah, Allah sarki mai halitta. Mutane ku sanya kanku cikin uku babu gaira babu dalili? Yanzu banda duniya ta zama abinda ta zama, me zai sako uwa cikin lamarin auren diyanta, har ka ganta ta taka kafa taje gidan surukai tayi dororo?".

Janan tace "Ai baki ga komi ba Anty Halima, idan har kina tare da mutanen nan, babu abinda zai dinga baki mamaki kuwa".
Hauwa tace "aikuwa dai Girma ya Fadi wallahi, ba'a ji dadin rayuwa ba. Ai in an girma sai asan an girma, a barwa yara yarinta".

Daga nan muka shiga wajen Anty Sarah. Nan kam tarba muka samu ta mutunci, aka gaisa a mutunce, aka bada amana

Please Login or Register in order to submit comment