Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka karba, daga nan muka koma sashen na.

Muna shiga na yaye gyalen kaina na haye can kuryar gado na lafe. Abinda ya faru a sashen Raheemah, ta tabbatar min daga cewa lallai sai na kara daure damara a cikin wannan gidan. Ina cikin wannan sake-sake su Janan suka shigo, dole na mike zaune muka kafa sansanin hira dasu.

Da dare ina daki na jiyo shigowar Yaya Bilal nan sashen, ina ji suna gaisawa dasu Anty Halima da suke falo suna hira. Na zauna a gefen gado sosai, ina jiran ya shigo ciki inji da kalar wadda yazo. Ba'a jima ba na ji hayaniyar gaisuwar ta ragu, sai hirarsu da suka cigaba da yi da kuma karar tv, wato fita yayi babu ko leke? Na kuta tare da komawa na kwanta abina.

Ba'a jima ba suka leko, wasu suka mana sai da safe suka koma daya dakin suka kwanta, wasun kuma kamar su Janan, suka kwanta tare dani anan dakin.








#F.W.A












*☆⋆35⋆☆*





Washegari muka karya da abinci mai rai da lafiya wanda aka kawo daga gidan Anty Sarah. Bayan mun ci munyi nak, muka yi wanka muka shirya.
Ina gaban mirror ina shafa man lebe a bakina, Maryam ta leko kanta dakin, "Yaya Na'ilah motar da zata maida mu tazo".
Na kalli agogo naga karfe goma, naji jikina yayi sanyi sosai. A sanyayen nace "tun yanzu? Nayi zaton zaku kai ko gobene".
Tace "haba, daga kawo amarya kuma? Mu daya kamata mu kauce tun jiya, mu ba ango damar cin amarcin sa?".

Na mike tsaye ina harararta, "yarinyar nan kin baci da yawa wallahi, baki da kunya yanzu".
Tayi dariya tare da maida murfin kofar ta fita bayan tace "kiyi sauri ki fito ke dai muyi sallama".

Na saka kaya a gaggauce na fita falon, ganin Anty Halima da kaya a gaba nayi turus, nace "kema yau zaki tafi?".
Tace "ehh mana, ko zaman daki kike so in zauna in miki?", duk suka kwashe da dariya.

Nayi narai-narai da ido kamar zanyi kuka, nace "yanzu ba zaku dan kara kwana bane?".

Huleirah tace "nop, not happening. Gwanda mu tafi tun ana ganin girma da mutumcinmu. Ko kuwa so kike angon ya kai ga korar mu ne?".
Na jefa mata harara, "dallah can yi mana shiru, waye ya sako bakinki anan?". Suka sake kwashewa da dariya.

Na shiga inda akwatuna suke, na cicciro kaya na fita na kai mika musu, Anty Halima tayi kir tace babu abinda zata amsa, "ce miki aka yi kyauta ake yi da kayan lefe ne? Mijinki kawo miki yayi don ki mishi kwalliya dasu ba wani abu ba".
Nace "to ai sanya albarkarku ne nake nema, don Allah ki amsa Anty".
Da kyar ta amsa, sannan suma su Maryam suka amshi tarkacen kayan kwalliyar dana basu, suna zuba godiya da sanya albarka.

Da yake a hannuna akwai kudin da Janan ta bani tace Yaya yace inyi hidimar biki dasu bayan an daura aure, babu abinda nayi dasu ma sai jikin jaka dana saka su. Na dauko na basu dubu dai-daya, Anty Halima kuma na bata biyar.

Tace "a'ah, har da kari? Kai Allah dai ya sanya albarka. Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki da zuriya dayyiba".

Na dan yamutse fuska cikin alamun tambaya, "karin me kuma?".
Tace "au, ashe fa kina barci lokacin daya shigo. Ai dazu da safe ya shigo muka gaisa shine ma ya sanar damu za'a zo a maida mu gida. Bayan haka kuma ya kara mana da kudin mota bayan shi ya bada motar da za'a kawo mu".

Naji wani abu a cikina ya tsinke. Yaya ya shigo dazu da safe? Kenan hakan yana nufin guduna yake yi ne ko menene? Sanyin jikina ya karu.

Cikin sanyin jikin muka fita zuwa waje, suka shiga motocin da zasu kaisu destination dinsu. Su Maryam Katsina, su kuma su Anty Halima Kano za'a kaisu su kwana gidan yan'uwanmu dake zaune a can, sai su wuce Gashua gobe.
Sai dana ga sun shiga mota har an tayar, sannan naji hankalina ya tashi. Na fara zubda hawaye. Maryam da Kulsum na ganin na fara kuka suma suka fara, dama tunda muka fara sallama suke sharar hawaye.

Janan ta janyo ni gefen jikinta tana shafa bayana a hankali, har aka ja motar suka tafi muna daga musu hannu.

Sai da muka ga sun fita daga gidan, sannan muka juya, ni, Janan, Harira da Firdausi zuwa bangarena.
Muka yi clashing da Salama da Adi sun fito daga sashen Raheemah, sun yi shigar su ta Ala wadai kamar yadda suka saba. Siket din da suka saka a jikinsu ya matse su kam kamar idan suka yi motsi mai karfi zai yage. Adi tana ta taunar cingam. Suka watsa mana kallon taro da sisi, suka ja tsaki suka wuce. Ko kallo babu wadda suka isa a cikinmu.

Su Harira suka zauna a falo suka kunna kallo, mu kuma muka wuce wajen kayana ni da Janan. Ta taya ni muka cire kayan da za'a kai dinki wasu kuma muka ajiye su sai a hankali tunda yanzu kayana masu dinki basu da yawa. Bayan mun gama, ta taya ni daukar sauran kayan muka je dakina muka shirya su a cikin wardrobe.

Bayan mun gama muma falon muka koma muka biyewa su Huleirah muna kallo.

A hankali yinin ranar yaci gaba da tafiya, muna ta karbar baki yan ganin daki. Tun daga kan dangin Yaya Bilal din, abokan karatunmu dake nan cikin Zaria da kuma makota.
Da rana aka sake kawo abinci daga gidan Anty Sarah. Da kanta ta shigo ta kawo mana abincin.

Na karbi jaririyarta da taci sunan Rabi'atul Badawiyya a hannunta, na dorata akan cinyata, Mimah kuma ta zauna a gefena tana jan kumatun yarinyar.

Ko bayan ta kawo mana abincin, zama tayi cikinmu aka sha hira da ita, har muka gama. Su Harira suka wanko mata kwanukan tas, sannan ta karba ta fita.
Yanayin sabuwar halayyarta ya bamu mamaki sosai, canjin halayenta da yawan shiga cikin mutane da take yi yanzu ba abinda muka saba gani bane a tare da ita. Ko bayan first tata, maganar da muka dauko kenan muna yi.

Firdausi tace "kin san fa dama can basa shiri da matar Yaya, sai in ga kamar dalilin da yasa bata shiga cikin mutane kenan sosai. Tunda kinga ai idan harkar dangi ta taso tana shiga ciki sosai".
Harira tace "nima na fi tunanin haka".
Daga nan muka karkata hirar zuwa wata daban kafin mu kai ga cin namanta.

Da la'asar Janan ta fita ta kai min kayana wajen dinki. Tana dawowa su Harira suka shirya suka wuce Kaduna, ita Janan zata tsaya ta kara hade kan kayanta zuwa gobe. Nan muka yi sallama dasu, suka tafi suna godiya, nima ina musu da sakon gaisuwa wajen su Ummah.

Bayan sun tafi, muka koma falona ni da Janan. Na kwanta akan doguwar kujera, ita kuma ta zauna a kasan carpet, Mimah kuma tana kwance a gefenta tana barci. Muna ta hirarmu da ita har Mustafanta ya kira, ta dauki wayar ta koma saman kujera ta lafe suna ta hirar su ta soyayya.

Nayi shiru akan kujera ina sauraronta, ina tuno wasu lokuta da hakan ta dinga faruwa dani da Yayan. Lokutan da zamu zauna mu sha soyayyarmu kamar babu gobe, wadannan muhimman lokuta da babu kamar su a cikin rayuwata.

Yanzu fa? Me yake faruwa ne? Me ya faru da tarihin soyayyarmu? Me ya faru da irin alkawurra na tattali da amintacciyar soyayya da yayi min idan munyi aure? Me ya faru da wannan kallon soyayya da yake yi min a duk lokutan daya samu dama da? Da kalmomin soyayya da basu taba barin bakinshi?.

Gashi yanzu na kula ko kallom inda nake baya so yayi balle a kai ga maganar arziki da wani kallon soyayya.

Shikenan kenan? Wadannan alkawurran sun zama empty promises? Dama dai zakin baki ne irin na Maza yake min, tunda kuma yanzu ya ganni a cikin gidanshi, ai yana da damar ya wulakanta ni son ran shi.
Nayi concluding hakan cikin raina ina maida kwallar data tarar min a cikin idanuna.

Har Janan ta gama wayarta, ban yi motsin kirki ba. Ina ji ta dawo gefena ta kwanta a inda take da, tana kiran sunana, nayi shiru kamar mai barci ban tanka mata ba.
Sai da aka kira sallah sannan muka tashi, lokacin Mimah ta koma sashen su. Muka yi sallah, na zauna akan abin sallar ina karanta suratul-Yasin, ita kuma Janan tana lazumi har aka kira sallar isha'i muka yi.

Naci gaba da zama akan abin sallar bayan na gama, har Janan ta kammala tata ta fita, bata jima ba ta dawo da kulolin abinci ta zuba mana. Duk da kamshin da abincin yake fitarwa, da dadin da yayi, kasa wani ci nayi da yawa, sai tsakura na dinga yi. Har sai da Janan ta kai ga tambayata lafiya? Nace mata bana jin dadin jikina ne.
A haka muka gama, ta wanke kayan ta fita dasu zuwa kicin.

Sai data dan jima, har sai dana tashi daga kan abin sallar na koma gefen gado na zauna, sai gata ta shigo. Ina so in bude baki in tambayeta ko Yaya yaci abincin shima? Amma na rasa ta yanda zan fara dauko maganar. Don haka nayi shiru, na bita da kallo har ta zo itama ta zauna a gefen gadon.

Tace "Yaya yace ki same shi a dakin Anty Raheemah yanzu".
Nace "ban gane ba? Ya shigo gidan ne?".

Ta girgiza kai, "a'ah, ya dai kira ni ne a waya".

Da wani haushi yazo ya tokare ni a wuya, duk yadda naso in danne kamar yadda na dinga yi cikin satin idan ya kirata instead of ni, ya bata wani sako kasawa nayi.
Nace, "wai ni meye amfanin wayata ne da ba zai dinga kirana ba sai dai ya wani bada sako a bani? Ko ban kai wannan matsayin bane kuma yanzu?".

Janan ta daga kafada, "to Hajiya, ni kuma ina zan sani? Shi ainihin maigidan naki zaki je ki tambaya, ni dai yar sako ce, na kuma kawo. Yana can kuma yana jiranki, kin kuwa san shi baya son jira don haka ki kwashi jikinki da kafafunki ki tafi tun kafin ya shaka".

Na mike tsaye ina guna-guni, "haka kawai sai a dinga wa mutane wani gani-gani da iko-iko? Ace kai da mijin aurenka wai sai an dinga wani kai da kawowa ana ajiye sakonni kamar a zamanin da?". Na ja tsaki.

Janan data kwanta dai-daya akan gadona, ta kyalkyale da dariya, "ku dai kuka sani!". Na wurga mata harara.
Na bude wardrobe na ciro hijabi doguwa, na saka.
Janan ta kalleni, "wai sai kace wadda zata je wani bikin gidan malamai, ba wajen mijinki zaki je ba da zaki wani kama hijabi ki zurma a jiki?".
Na kara jefa mata harara, "to wai ke ina ruwanki ne?".
Ta sake sakin dariya tare da sake mike kafa har da min gwalo. Na girgiza kai kawai ina dan murmushi. Na fita zuwa inda aka kirani.

Na tura kofar falon nata na shiga bakina dauke da sallama. Na kula da takalmin da na fi kyautata zaton na Yaya ne a ajiye a waje, da kuma wani hadadden bakin takalmi mai tudun duduniya daga ganinshi na mata ne. Ban kawo komi a cikin raina ba, na cire nawa takalmin nima na shiga cikin falon bakina dauke da sallama.

Sai dai ina shiga na danyi turus, ganin mutane a cikin falon. Mutanen da suka kasance uku, Yaya Bilal da matanshi.
Muryarshi kadai naji wadda ta amsa min sallamar, itama a hankali don da ba don shirun da falon yayi ba babu abinda zan iya ji.

A hankali na taka har zuwa tsakiyar falon, ina jin idanunsu a kaina suka biyo ni da kallo. Sai da naje tsakiyar falon, naja tunga na tsaya ina raba idanu a tsakanin kujerun falon da kuma matan nashi dashi kanshi, cikin tunanin inda zan zauna.
Shi zaune yake akan kujera mai daukar mutum biyu, Anty Ameerah kuwa na gefenshi kugu da kugu kamar zata haye kan cinyarshi, tazarar data bari a gefensu, idan aka samu mutum mara kiba tsaf zai yi fitting a wajen. Taci kwalliya kamar wadda zata je wajen biki, dama gata tubarkallah, kyakkyawa ce, kuma fara mai kyawun jiki, kayan data saka ma sun matukar karbarta. Ga mai karamar zuciya, tuni zata juya baya hannunta aka tana ihu, kallonta kadai a hakan nan kan iya tsoratar da mutum.

Ita kuma Raheemah ta zauna a daya kujerar dake gefenshi, itama dai tasha tata kwalliyar. English wears da suka matukar fitar mata da surar jiki. Kitson da aka mata da yasha karin gashin kanti, ya sauka har gadon bayanta da kuma saman kirjinta inda yayi matukar kokari wajen rufe shafaffen kirjinta da ko brazier acuci maza bata iya tado shi, tana ta wani kwarkwasa.
Idan har zan zauna kusa dashi, hakan yana nufin sai dai in zauna akan kujerar da Raheemah take, ko kuma in zauna a daya kujerar da take fuskantarsu, wanda idan nayi hakan ba zan samu damar jin abinda zai dinga fada ba sosai tunda sauran kujerun sunyi nisa da nan center table ya shiga tsakani. Sai dai kuma idan a kasa zan zauna.

Ina shirin neman wuri a kasar in zauna, naji muryar Yaya yana cewa "zo ki zauna anan".

Na daga kai na kalli inda yake, sai naga ashe ya tashi daga inda yake a zaune, yanzu yana tsaye ne. Na kalli inda yayi min nuni, kusa da Anty Ameerah da uncertainty, kafin na murje nayi ta maza naje na zauna. Sarai na kula da yadda ta matsa daga tsakiyar kujerar ta koma can karshe ta lafe, amma hakan bai dameni ba.

Yaya ya dauko kujerar dinning table guda daya, ya ajiye a tsakiyar falon yadda yake fuskantar mu gabadayanmu, ya zauna.

Da dai kamar inyi shiru yadda su ma suka yi, wani fanni na zuciyata dai ya tunatar dani ba haka aka yi min nasiha ba da zan taho daga gida, don haka na daga bakina da kyar na gaida su, idan sun amsa min, to ban ji ba har ga Allah.

Yaya yayi gyaran murya, tare da bude taron da salatin annabi. Ya janyo wasu ayoyi daga cikin Al-Kur'ani mai girma ya fassara, ya kawo hadisai, yayi sharhi, ya kare da nasihohi. Duk akan zaman aminci da zaman lafiya a tsakaninmu. Kaina a kasa, cikinmu babu wanda yayi motsi a cikinmu har ya gama.

Bayan dogon lokaci daya dauka yana bayanai, ya gabatar dani a matsayin matarshi. Sai lokacin daya ce ni din kamar yar uwa ce a garesu sannan naji Raheemah tace "tabdijam!", a can kasar zuciyarta. Ameerah kuma ta sake gyara zamanta. Duk yayi kamar bai ga ko ji abinda suka yi ba, yaci gaba da bayanan shi. Ya gama da cewa "kun fahimta?". Duk muka amsa da ehh.

Yace "good. Sannan maganar zama da zancen girki, ina so gabadayanku ku shirya, ranar wannan Ladin da zata zo zamu koma Abuja gabadayanmu. Komi an riga an tanada a can, saboda haka baku da bukatar daukar wani abu sai yan abubuwan da ba'a rasa ba. Any complain?".

Na daga baki cikin mamaki na kalleshi, Ameerah ma haka take kallonshi kamar wanda yace lahira zai kaita, ita kuwa Raheemah ta dan saki ihun murna cike da farinciki wanda bana tunanin tasan cewa tayi hakan.

Duk cikinmu babu wanda ya iya yin magana, sai Ameerah ce ta iya daga baki bayan lokaci mai tsayin tace, "amma ni fa Daddy bai san da wannan maganar ba, ka fada mishi ne?".

Ya kalleta kamar wata sabuwar mahaukaciya, yace "ni da Matata kuma, don zan zartar da hukunci a kanta sai na tambayi mahaifinta? Wai ma, me kike yi ne a Zaria? Ke ba aiki ba, ke ba karatu ba. Kada ki manta wancan karon da na miki maganar, karatunki kika kawo as an excuse, na kuma kyaleku har kika gama, amma baki sake tada min zancen ba. Na kuma kawo idanu na zuba miki, amma saboda baku san annabi ya faku ba, ko a jikinki. Shikenan ni kullum ina yawo da jele akan titi kamar wani mara galihu, an fada miki a kanki zan kare ne? To bari kiji, wannan itace magana ta karshe da zamu yi akan komawa Abuja, idan muka tafi wannan karon, babu abinda zai dawo dani Zaria sai dai idan wata hidima ta taso a cikin dangi don haka ki yanke shawararki".

Tayi shiru kanta a kasa, da alama bata ji dadin abubuwan daya fada mata a gabanmu ba, murya can kasa kamar wadda aka shake, tace "idan na tambayi daddy, zan fada maka duk yadda muka yi".

Ya tabe baki, da alamu abin bai dameshi ba, ko kuwa tsananin sabo ne? Yace "wannan kuma ku kuka sani, illa iyaka ina son ki san cewa idan na sanya kafa na tafi, kuma ba'a baki izinin biyo mu ba, kada ki saka ran zaki dinga ganina a Zaria kamar yadda kika saba don na gaji da wannan jigilar. Akwai wani me abin cewa ne kuma?".

Duk muka yi shiru, yace "idan mutum yana da matsala gwara ya fito tun da wuri ya fadi, bana son abinda sai daga baya za azo ana damuna da wasu kananun maganganu".

Ina so in tambaye shi maganar internship dina, tsoron abinda zai fita daga bakinshi ya hana ni daga baki. Idan ya yiwa ta gaban goshinshi fada irin haka, ina ga ni kuma da dama yake shake dani a wuya? Nasan kiris yake jira ya min wankin babban bargo. Don haka na ja bakina nayi shiru.

Raheemah ta daga baki itama cike da tsoron yin maganar, amma hakan bai hanata cewa, "uhmm.. har su Salama zamu tafi ne?".

Ba Yaya Bilal kadai ba, ni kaina sai dana kalleta baki a dage, meye hadin biri da gada kuma?

Yayan yace "a kan me kuma?". Tayi shiru tana muzurai.
Ya sake cewa "ba karatu suke yi ba wai? Meye na wani biyoki gidan aurenki? Ko kuwa tare aka daura muku auren ne?".

Sai ta kama in-ina, "dama.. wannan.. Adi nake nufi".

Ya kalleta sosai, "to wai ita Adin an miki wahayi da ita ne? Ko kuwa dole sai da ita zaki yi zaman aure ne? Wai bata da gidan iyayenta ne ita din? Ke kadai aka daura min aure da ita, ke kadai kuma nake bukatar gani a gidana. Don haka ke kadai zaki shirya ki bimu. Su Salama su koma gida mana? Dama can dalilin makaranta yasa suke zama anan, kuma ba zuwa suke yi ba, ita kuma Adin ta koma gidansu haka nan itama".

Sai tayi kus, tana gunguni can kasan makoshinta.
Yace "shikenan babu wani mai magana a cikinku kuma?".
Jin munyi shiru yasa ya gyada kai, ya rufe mana taro da addu'a.

Ya mike tsaye yana kallonmu mu duka, yana cewa, "don haka sai ku fara shiri. Ki tashi ki koma sashen ki, ke kuma zo in maida ki gidanki".

Ya fara tafiya, Ameerah ta tashi ta take mishi baya. Nima tashi nayi sadaf-sadaf na bi bayansu, muka bar Raheemah har yanzu a zaune a inda take babu alamun zata motsa.

Muna fita suka wuce wajen gareji, ni kuma na nufi sashena.

Janan bata nan lokacin dana koma dakin. Har na shiga bandaki na watsa ruwa, na fito na shirya cikin kayan barci, ban ji motsinta ba.

Na dauki waya na kirata tare da tambayar inda take, tace "makwanci mana".
Nace "ban gane ba, nayi zaton tare zamu kwana dake?".

Tace "rufa min asiri mana, in koma wajen Ummah na a yadda nake. Kinga, yanzu naji dawowar angonki, ki dauki jikinki ki tafi kije ki taro shi sai da safe".

Ta kashe wayar ba tare data bari nace wani abu. Na bi wayar da kallo, kafin na ajiyeta a gefen gado.

Shiru ina zaune ni kadai, ban ma san zaman me nake yi ba, daga karshe dai na fita na kaso wutar falo da kayan kallo, na koma na lalubi gefen gado na kwanta tare da kashe wutar dakin. Addu'ar kwanciya barci nayi na shafa a jikina, na lumshe idanuna.










#F.W.A





*☆⋆36⋆☆*





Ina rufe idanuna, naji an turo kofar dakin an sake kunna wutar dana kashe yanzu. Na bude idanuna da suka fara yin nauyi saboda gajiya da barci, na saukesu a bakin kofa.

Yaya Bilal yayi tsaye a bakin kofar hannunshi harde a kirji, da alama har ya dawo daga maida Anty Ameerah din. Kayan jikinshi ne na dazu har yanzu bai cire su ba, casual outpit ne, shigar da ban saba gani a jikinshi ba. Yawanci daga suits sai manyan kaya, riga da wando na shadda, watarana ma ko hula baya dorawa.

Muka tsaya muna kallon-kallo ni dashi, kafin ya maida kofar dakin ya rufe. Kai tsaye bandakina ya wuce, ina nan a kwance a inda ya barni, ina jin motsin ruwa dai. Ba'a jima ba, ya fito daga bandakin yana gyara links din hannun rigar shi. Na bi shi da kallo.

Sai daya kawo tsakiyar dakin sannan ya kalleni, "kin yi sallar isha'i?".

Wani kwarjinin shi ya cika min idanu, na kasa daga idanuna gabadaya in kalli tsakiyar nashi idanun. Kai na gyada mishi a hankali.

Ya sake cewa "kina da alwala har yanzu?".

Na sake girgiza mishi kai, alamun a'ah.

Ya tsaya yana kallona ba tare da yace komi ba, kusan tsayin minti daya, har sai dana kai ga dan dago kaina na kalleshi. Wani irin abu a tattare dashi dana kasa fahimtar koma menene, bugun zuciyata naji ya dauka da sauri da kuma karfi.

A hankali ya juya zuwa wajen da muke yin sallah, da alama dama an tanadi wurin ne saboda sallah.
Yace "ki tashi kiyo alwalar ko? Muyi sallah".

Ni wannan sabon attitude daya kirkiro na kasa fahimtar shi, kodayake ai dama can ba wani sanin shi nayi ba sosai, zata iya yiwuwa halin shi kenan. Na daga kafada tare da saukowa daga kan gadon. Kayan barcin dana saka a jikina dogon wando ne da riga karama top, wadda bata kama jikina ba. Na shiga bandakin na daura alwala kamar yadda ya umarceni.

Lokacin dana fito daga bandakin, har ya shimfida abin sallah. Na bude wardrobe na ciro doguwar hijabi na saka. Na karasa wajen da yake.
Ya tada sallah, na bi bayanshi. Raka'ah hudu muka yi dogaye, muka dora da shafa'i da wutiri.
Bayan mun gama, ya juyo ya dafa kaina, yayi addu'o'in da annabi S.A.W ya umarcemu da mu yi a lokacin da muka yi sabon aure. Neman alkhairan juna, da kuma neman tsari daga sharrin juna.

Bayan nan juyawa yayi, yaci gaba da janyo wasu addu'o'in, ni kuma na zauna muk'u a bayanshi, ban ma san kalar addu'ar da nake yi a cikin raina ba har ya gama. Ya tashi tsaye tare da linke abin sallar, nima na mike na nade wanda nayi amfani dashi na ajiye a inda muke ajiyewa.

Nayi tsaye anan kaina a kasa, ban san abinda yakamata inyi ba daga nan, it felt very awkward. Subhanallah! Haka kowace mace take ji idan aka barta da mijinta su kadai a dakinta, ko kuwa ni kadai ce nake jin haka?.

Shi kuwa gogan da alama ko a jikinshi, kamar baya jin komi, idan ma yana ji ba karamin kokari yayi ba wajen murje shi.
Yace "kin ci abinci? Kina jin yunwa?".

Ai ko ina jin yunwa bana tunanin wani abu zai iya shiga cikin cikina bayan numfashi, yadda nake jin shi dinnan yayi knotting da nerves, fargaba da rashin sanin abin yi. Na sake girgiza mishi kai. Ina tunanin dai na zama kurma yanzu, ko kuwa?.

Bai sake cewa komi ba, ya juya ya bar dakin. Na sauke numfashin da ban san na rike ba. Na jima a tsaye sosai, kafin na cire hijabin jikina na linke na maida inda take, na sake komawa na kwanta. Sai dai wannan karon ban kashe wutar dakin ba tunda bani da tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba.

Zuwa can, sai gashi ya sake dawowa. Wannan karon ya canza kayan jikinshi zuwa jallabiya fara kal, hannunshi kuma dauke da leda babba. Ya ajiye a tsakiyar dakin ya sake fita, can ya dawo da plates da kofuna guda biyu, ya janyo karamin carpet dake jingine acan gefe ya shimfida ya zauna.
Ya fara fitar da kayan ciki,

Please Login or Register in order to submit comment