Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katseta ta hanyar cewa, "daga ina kike?".

Ko kadan bata girgiza da tambayar daya jefo mata ba, tace "kasan cousin dina Mubeenah ko? Kanwar Mommy. To ita ce tazo ganin gida daga Switzerland, na fada maka ai ko?".

Yaya ya hade fuska iya hadewa, ban taba ganin zallan bacin ranshi irin na yau ba, ko lokacin da muke cikin je-ka-dawo kafin mu shirya kuwa.
Yace "zan kuma iya tuna abinda na fada miki a lokacin, ban yarda ki taka kafa ki bar nan gidan ba, ko ba haka na fada miki ba?".

Ta wani marairaice fuska kamar karamar yarinya, "amma Baby... Sai dana fada maka fa daddy ne yace inje mu gaisa da ita saboda mun jima bamu hadu ba. Kuma ma, kai da baka gidan, menene a ciki?".

Ran Yaya ya baci iyaka baci, ya tashi tsaye cike da matsanancin bacin rai, jikinshi har wata rawa yake yi, "akan meye zaki tsallake dokar dana kafa miki kamar wani sa'an wasanki, ko kuma wanda baki dauki maganar shi da mutunci ba, kodayake, dama yaushe kika taba girmama wani abu dana fada miki? Wai saboda Allah, ke nake aure ne ko kuma iyalan gidanku gabadaya?? Kwata-kwata an maida min rayuwar aure wasa, ni da matata, amma ban isa in zauna in gindaya mata sharadi ba tare da an san yadda aka yi, aka yi watsi da lamarin ba? Shin ni din ba mijinki bane? Idan ma baki sani bane, ki san cewa yanzu duk wata hidima da dawainiya da komi naki ya tashi daga hannun iyayenki, ya dawo hannuna. Baki da wani hurumin bin maganar mahaifinki ki tsallake tawa. Amma gabadayanku kun rufe idanunku, kuna abusing kalmar aure, saboda kun dauketa a ba a bakin komi bane ko me? Kin dauka rayuwar auren, abar wasa ce? Rashin sani ne yasa haka ko kuma rashin sanin yakamata??!".

Ameerah bata iya cewa komi ba saboda yadda taga ran nashi ya baci fiye da tunaninta.

Yaya yaci gaba da cewa, "na gaji da yadda kuke take min rayuwar aure haka nan. Ban isa dake ba, ban isa da komi naki ba. Saboda haka daga yau a gidannan, zaki zaba, umarnina ko kuma na mahaifinki? Idan har kin ce ba zaki bi umarnina ba, to tun kafin tafiya tayi nisa, ki koma inda kika fito. Idan kuma kin shirya yin zaman rayuwar aure kamar yadda yakamata, to daga yau sai yau, ban yarda ki taka kofar gida ba tare da kin nemi izinina ba Ameerah idan kuwa har hakan ta sake faruwa, duk abinda ya biyo baya, ki zargi kanki!. Zabi ya rage naki!".
Ya hada kan kayanshi ya wuce daki a fusace.

A hankali ta duka ta janyo akwatinta ta shigo cikin falon sosai, na mata sannu da zuwa, bata amsa ba, sai ma la'adar harara da nasha. Taja akwatinta ta wuce dakinta kamar tashin duniya, na bita da kallo cikin tabe baki. Meye laifina anan, ni da bani na kar zomon ba? Na sake tabe wani bakin.

Yaya bai fito ba sai da aka kira sallar magriba.
Kiri-kiri yaki cin abincin data dafa ranar, a gabanta ya kira wata hadaddiyar restaurant 'cloirassantz' daya saba yi mana odar abubuwan tande-tande, yayi placing order aka kawo mishi abinci, ya zauna yaci kayanshi ya wuce daki abinshi.

Washegari ina daki ina shirin fita ya leko dakin, na gaida shi. Yace min idan na dawo inyi girki, in kuma cigaba da yi har sai shi da kanshi yace min in ajiye. Ban iya cewa komi ba sai 'to', na kula hukuntata yake so yayi tun karfinshi.
Ban sanya bakina cikin fadansu ba, ko tambayarshi dalilinshi na damka min girki gabadaya ban yi ba.

Kwana biyu suna ta fadansu, fadan masoya hutu, ban san ta yadda ta samu ta shawo kanshi ba, naga dai sun koma sun dinke kamar tif da taya, nan ma ban ce komi ba, na damka mata girki taci gaba da yi.
Ya karbe motar hannunta yace ta maidata gida, ya kuma hanata yawan fita gatsar, dokoki sosai ya kafa mata, duk tace taji ta amince.
A haka Raheemah ta dawo muka cigaba da bugawa dai. Ta kawo mana souvenirs na bikin, ga hoton Haleemo nan da Umar ya sha uniform dinsu na sojoji radam a jikin komi, memo ne, jaka ce, calender ce, kai tarkace dai. Lokacin data bani, dariya nayi tare da musu fatan alkhairi na kai daki na ajiye. Ko tayi tsammanin haushi zan ji ko kishi??.



*


Cikin jikina yana ta tasawa cikin koshin lafiya, yanzu yana cikin satikan shi na goma sha daya.
Har yanzu muna cigaba da gwabzawa da matan Yaya, duk da cewa yanzu da Ameerah muke yi. Raheemah sam yanzu ba na ta tata, fada ne, bana biye mata.
Wata tsirfa data dauko ma sabuwa, haka zaka ganta a dakin Yaya ranar girkina tun da safe, ta kuma ci kwalliya ba ta wasa ba. Har magana sai da na yiwa Yaya akan haka, nace ya daina biye mata suna yin haka, suna shiga hakkin mai yin girki.
Amma maimakon yace wani abu, sai yayi dariya, wai "menene abin shiga hakki anan Baby? Mu da babu abinda muke yi sai hira kawai? Idan kika tafi yin girki, kadaici yana damuna, kinga tana taya ni dauke kadaicin".
Da naga dai bashi da niyar daukar mataki, sai na gyada kai nace "to babu laifi".

Da ranar girkinta ta zagayo, sai naci kwalliyata ta gani ta fada da safe, English wears mini skirt da wata vest, na gyara gashin kaina ranar ko hula ban saka ba, na yiwa dakin Yaya tsinke. Na samu gefen gado nayi daya kan daya, har tazo ta sameni anan, abin ya bata mamaki, amma bata yi magana ba.
Da dare ma da ya dawo haka ta faru, naje na musu zaune har dare ya tsala yadda ta saba yi min.
Zuwa karfe goma ta wani tashi tana mika, cibiyarta tana nunawa ta cikin half vest din data saka, tana wani fari da idanu da rangwada, tace "baby, muje mu kwanta ko?".

Yaya da yake shan dariyar hirar da nake mishi akan kiriniyar dasu Auwal suka sha lokacin da suna yara, ya kalleta yace "kiyi gaba, gani nan".
Ta turo baki cikin jin haushi, amma bata ce komi ba, ta shige uwar daka.
Muka kuwa cigaba da hirarmu, har sai da ta sake lekowa ta mishi magana, wai ai ita ta kasa yin barci saboda baya kusa da ita, lokacin karfe sha daya ta kusa.

Ina dariyar mugunta a ciki, nace "Yaya kaje ka kwanta mana, kasan fa gobe akwai aiki".
Yace "ke fa?".
Na girgiza kai, "bana jin barci, kaje ka kwanta abinka, idan na gama barcina zan je in kwanta. Sai da safe...", na dan juya ina kallon Ameerah da take tsaye a jikin kofa har lokacin, nace "sai da safe Anty Ameerah!".
Ta hadiye wani yawu da nafi kyautata zaton na takaici ne da bakin ciki tace "Allah ya tashe mu lafiya", ta juya cikin dakin. Yaya ya bani peck a kumatu tare da dukawa ya shafa cikina, sannan ya min sai da safe ya bi bayan matarshi. Na bishi da kallo ina murmushin mugunta. Matarshi tayi tsamnanin taci bulus ne? Ashe kuwa tana da sauran aiki a gabanta, domin kuwa ba'a buga irin wannan wasan da ni.

Washegari ma abinda ya faru kenan, hakan kuma yaci gaba da faruwa na wani dan lokaci.


Ranar Alhamis girki a hannuna yake. Tun da na dawo daga wajen aiki, nake shirya abincin dare. Dambun shinkafa nayi, mai kyau, na yanka hanta, carrots, kabeji, da sauran tarkacen veggies a ciki. Nayi sauce itama da na wadatata da su nama da kifi. Nayi lemun kankana da lemun zaki wanda na dan diga lemun tsami da zuma a ciki.
Lokacin dana gama girkin, yamma tayi. Don haka na bar miyar akan wuta domin ta karasa yi, na tafi dakina inyi wanka.
Ina cikin yin wankan naji dawowar Yaya daga wajen aiki, jin ina yin wanka yasa ya wuce dakinshi.

Daga bandakin na dauro alwala saboda lokacin sallah yayi. Na koma duba miyar, na ga har yanzu da sauran ruwa a cikinta, abin ya bani mamaki kwarai. Zan iya rantsewa akan cewa ruwan da na bari dazu bai kai haka yawa ba. Amma sai ban kawo komi a cikin raina ba, na kara rage wutar na koma daki domin inyi sallah.

Ina kan abin sallar, Yaya ya dawo daga masallaci, daga ganinshi kai tsaye dakina ya shigo. Na dago ina kallonshi cikin murmushi, "baby abinci... Abinci baby...". Ya fada a dan gaggauce, ya juya ya fita.
Na tashi tsaye ina dan murmushi, wato yau da yunwa ya dawo kenan. Na cire hijabin jikina na tafi kicin da niyar zuba mishi abincin.

Miyar dazu, ta koma kamar miyar tanade, ruwa tsululu kamar lokacin na fara dafa ta. Ban san lokacin da naji kwalla ta cika min idanu ba, na maida murfin tukunyar na rufe tare da kashe gas din. Na jingina da counter din kicin ina tunanin abu mai sauki da zan dafawa Yaya wanda ba zai dauki lokaci ba, sai dai duk abinda nayi tunani, sai in ga sam ba zai yiwu ba. Gabadaya duk wata idea ta dauke min, daga karshe dai na yanke shawarar kai mishi dambun a haka, tunda akwai komi a ciki, har maggi da mai sai dana saka a ciki, dama miyar don dai garnishing ne kawai.

Na ciccibi kayan na tafi falon Yaya dasu.

Tunda na fara zuba mishi yake kallona yana murmushi kwanannan abinda yake min kenan, idan na mishi magana yace ai cikin jikina ya canza ni ne shi yasa. Na tura mishi plate din gabanshi tare da tsiyaya mishi lemun a cikin kofi.

Ya ja plate din gabanshi, "yau kuma a haka zamu ci dambun?". Ya tambaya cikin alamun tsokana.
Na dan yi murmushi cike da fargaba, "uhmm, wani lokacin komi yana bukatar canji ai".
Yace "haka ne baby na". Yayi bismillah tare da kai cokalin farko bakinshi, take yanayin fuskarshi ya canza, da kyar ya hadiya. Naji gabana ya fadi cikin fargaba, nace "me ya faru?". Ban jira ya amsa ba na dauki cokali na kai bakina, yaji ya fara ziyartata kafin wani masifaffen gishiri mai rikita kwalwa ya biyo baya. Da sauri na kai lemun dana zuba mishi cikin bakina da niyar kora abincin dashi, domin ba zan iya hadiya shi ba. Nan kuma wani matsanancin tsamin lemun tsami daya min bismillah.

Ban san na tara kwalla a cikin idanuna ba, sai dana ji tana bin kumatuna. Da sauri Yaya ya kai hannu yana dauke min kwallar, yace "menene abin kuka kuma? Kada ki damu kanki, girki ai ya gaji haka. Bari yanzu in aika a sayo mana wani abincin".
Ban ce mishi komi ba, naci gaba da share kwallata. Yanzu duk wahalar wannan da naci ta tashi a banza kenan? Babu abin ban haushi da takaici ga matar aure, ace mijinta bai ci abincinta ba ya tafi neman na waje yaci.
Cikin kwallar da nake yi, nace "a'ah, bari in shiga in yi wani abu mai sauki".
Yace "inaa, ba zaki wahalar min da baby ba. Baki ji ance miki ba'a son ki cika yin aikin wahala ba? Maza daina kukan, kada ki sanya min baby kuka".
Duk yadda yaso inyi shiru, abin gagara yayi. Har aka kira sallah ya koma masallaci, raina a jagule yake.

Daya dawo sai gashi da ledar take away, har daki ya kaiwa kowa nata. Daya kawo min nawa ko kallonshi banyi ba saboda masifar bacin rai. Allah ya isa kadai nake ja ina karawa a cikin raina.
Muna zaune yana cin nashi abincin, nawa kuma yana gefe, sai ga Raheemah ta shigo falon. Ta kallemu ta tabe baki, "uhhum! Su yan gaban goshi masu juna biyu manya, wato yanzu abincin ma an daina yi sai dai a tafi a siyo na waje? Kwarai kuwa, Allah muma ya azurtamu da namu cikin dai!".

Kwata-kwata yau bana cikin jin zama in saurari korafe-korafen data saba, don haka na mike na wuce dakina, ban san yadda suka kare da ita ba. Sai wajen karfe goma sannan naje na kwashe kayan da muka bari. Ranar haka na kwanta zuciya a cunkushe.

Cikin dare fa barci ya gagareni, yunwa kamar zata kashe ni. Allah yasa na sanya abincin da Yaya ya kawo min cikin microwave, na zame jikina daga na Yaya a hankali na fita daga dakin. Kusan karfe biyu da rabi na dare lokacin. Shiru gidan, baka jin motsin komi.
Na shiga kicin, maimakon in kunna wuta, sai nayi amfani da hasken fitilar wayata. Na kunna microwave din, na koma falo na zauna akan dinning ina jiran abincin ya dumama. Fitilar na kashe, naci gaba da zama a cikin duhu, a zuciyata ina ta saka da warwara akan wannan sabuwar matsala data tunkaro ni.
Zato zunubi, amma da sai ince ga wadda ta aikata min wannan danyen aiki, sai dai shi zargi bashi da kyau. Kawai dai yanzu zan dinga yin takatsantsan ranar girkina kawai, shine mafita.

A hankali naji an turo kofar daki an fito, na daga kaina daga zuzzurfan tunanin dana fada. Raheemah ta fito itama tana haska fitilar wayarta tana taku sadaf-sadaf kamar barauniya, ganin ta wuce kicin kai tsaye yasa na dan yi murmushi. Da alama itama yunwar ce ta korota.

Ban yi motsin kirki ba balle ta ganni, na kara yin kasa da kaina ina wasa da yatsun hannuna.

Dare da baya raina abin ji komi kankantarshi, duk wani dan karamin motsi da zata yi ina jin shi, zuwa can naji tashin murya kasa-kasa alamun tana waya, hatta da daya bangaren data kira ina ji.
Cikin barci wadda ta kira din ta fara cewa, "ke wani irin shashanci ne haka zaki wani hau kiran mutane da tsakiyar daren wannan?".

Tayi kasa da muryarta sosai, "Momcy, na manta yadda zan sanya wannan maganin ne. Kin san kuma Malam yace idan ya wuce yau ba zai yi amfani ba".

Na zare idanu sosai, amma sai na kara lafewa ina sauraronta.
Sai da tayi hamma sannan tace "wanne daga ciki? Na turaren ko kuma na ci?".
Tace "na ci dai, ai na riga nayi na turaren tun yaushe...", ta ja dan tsaki, "... amma ni har yanzu ban ga yayi wani abu ba, anya kuwa ba asarar kudi kawai muka sake yi ba?".

Tace "ina, shi mai nema ai baya gajiya. Ba zamu gajiya ba, balle ina da tabbacin wannan din zai yi. Kin san fa aikin malamin nan kamar yankan wuka, kin dai ga irin aikin da yawa Halima. Ke kanki ba da taimakonshi bane kika shigo gidan ba?".

Tace "haka ne, kawai naga kwata-kwata aikin baya yi ne yan kwanakin nan. Duk inda muka je sai dai suyi ta cinye mana kudi. Shima wanda nake zuba mishi a abinci fa har ya kare, amma kinga har yanzu shiru kamar an shuka dusa. Bai sallameta ba, bai juya mata baya ba kamar yadda suka ce. Ranar nan ma fa har tambayata yayi me yasa abincin yake wani warin magunguna? Nace mishi maggi ne. Kada fa mu je ya cafko mu Momcy".

Tace "ke ja can matsoraciyar banza da ta wofi!! Dan ubanki ke har kin fara sarewa tun kafin aje ko'ina? To arr dinki, ni cikin yayana babu matsorata wallahi, ki kiyaye ni. Kina ganin idan kika zauna a gidan wannan tsakanin wadannan matan nashi, zaki ganu? Shi komi ba dan hakuri bane? Da sannu, su duka zamu yi waje dasu. Yanzu abinda zamu kokarta muyi shine mu ga cewa mun karkato da hankalinshi kanki tukun. Yanzu kije ki zuba maganin a cikin danyen nama, ya kwana, gobe ki soya shi ki mishi girki yaci, zaki ga abin mamaki. Amma kada ki kuskura ki kara bari inji kalmar karaya ta fita daga bakinki, kina jina?".

Cikin sanyin jiki tace "ehh Momcy".
Tace "to madallah, maza je kiyi aikin gabanki". Ta kashe wayar.

Na dafe kai da baki a lokaci guda. Kaji fa wata irin tabewar basira. Kai Allah dai ya kara rufa mana asiri, ya kuma sa mu dace.

Ban damu da cewa har yanzu tana cikin kicin din ba, na tashi nima na shiga kicin din. Wutar kicin din na kunna haske ya bayyana, daidai lokacin tana maida danyen nama cikin firjin. Da sauri, kuma a tsorace ta maida firjin din ta rufe, ta juyo tana kallona cikin zare idanu. Ban ce mata komi ba, na bude microwave na ciro abincin ciki, na koma kan dinning na zauna na fara ci.
Ta zo ta wuce ni cikin sanyin jiki kamar kazar da kwai ya fashewa a jiki, tana yi tana satar kallona.

Nima a sanyaye na fara cin abincin hankalina ya kasu gida-gida, har na rasa da wanne zan ji. Da alama sai na kara zagewa da addu'a ba akan kaina kadai ba, har shi Yayan.
Ina gama cin abincin, na je na dauke gabadaya naman dake cikin fridge na zubar. Na koma dakin Yaya. Bandaki na shiga na dauro alwala na fito na fuskanci alkibla ina jero nafilfili.


Washegari da safe ba sai aka maimaita yar gidan jiya ba? Na hadawa Yaya abincinshi na kari ya fara ci cikin nutsuwa, ya kai shayin dana hada mishi, kawai naji ya furzar dashi, a dan zafafe yace "meye haka Na'ilah?".

Daga farko tsananin mamakin ya kirani da Na'ilah ne ya kama ni, kafin mamakin abinda ya faru da shayin ya biyo baya. Bai ma tsaya yi min karin bayani ba, ya tashi ya bar wajen. Ina nan zaune cikin rashin sanin abin yi, sai gashi ya fito dauke da brief case dinshi, da kyar ya iya cewa "sai na dawo". A Karo na farko, ranar ya fita ba cikin rakiyata ba, kuma cikin rashin dadin rai.
Sai daga baya na fahimci cewa, robar sugar aka juye gabadaya aka zuba gishiri. Wannan karon ma kadan ya hana ni inyi kuka.

Saboda haka da girki ya sake dawowa kaina, na dinga bin kwakkwafi. Idan na shiga kicin, bana lekawa ko nan da can har sai na gama girkina, idan kuma na gama, tunda nasan na Yaya ne ake hari, sai in shige daki dashi in kulle har sai ya dawo. Duk da nasan cewa da gangan ake min haka, amma ban shirya neman kowacece ba, bani kuma da zuciyar ramawa. Nasan cewa dai, rana dubu ta barawo ce, daya kuma ta mai kaya.



*



Yau da yake ba ranar girkina bace, kuma ina off saboda evening duty dana gama, ban fito daga daki ba sai karfe biyu na rana. Yau da su kayan marmari ma na karya. Kwana biyu yanzu mangawaro kawai nake sha kamar babu gobe, kullum sai in sha fiye da guda biyar.
Yanzu ma abinda ya fiddo ni waje kenan, saboda mangwaron dakina ya kare ne. Yaya da zai fita yace za'a kawo wani.

Ina shiga kicin kuwa, na ganshi an kawo shi har kwali guda. Wani irin dadi ya ziyarceni. Na dauki guda biyu manya masu kyau, na wanke su na yanka. Ina cikin yi, Raheemah da take yin girki ranar ta shigo. Tunda abin nan ya faru, kusan sati daya kenan, bata ko yarda mu hada idanu da ita. Ko hira suke yi, idan taga na shigo waje, haka zaka ji tayi shiru ko ta ma tashi ta bar wajen.

Sannu kawai na mata ciki-ciki, na dauki mangwarona na koma daki.
Na zauna na tada mangwaron nan tas, na bi da ruwa mai sanyi.
Komawa nayi na kwanta naci gaba da barcina.


Wajen karfe hudu, wani irin masifaffen ciwon ciki ya tado ni daga barcin da nake yi.
Na tashi na fara murkususu. Tun ina yi akan gado, har na fado kasan carpet. Gabadaya ciwon ya gigitani, ban taba jin azababben ciwo irin wannan ba.

Da kyar na iya lalubo wayata na kira Yaya, yana dauka ya fara tambayar lafiya? Saboda yasan ban cika kiranshi idan ya tafi wajen aiki ba, musamman ma ranar da ba girkina ba. Ban iya mishi magana ba, sai gurnanin ciwo kawai daya dinga fita daga bakina. Nan da nan ya rikice, yace gashi nan zuwa.

Ina jin lema tana fita daga jikina, amma bani da kuzarin daga kai in ga ko menene. Ban ma san lokacin da Yaya ya dawo ba saboda hankalina ya gushe daga jikina.

Lokacin dana dawo cikin hayyacina, tuni cikin jikina ya zube.

Lokacin da wata likita daga cikin likitocin asibitinmu ta isar min da wannan sako, dauka nayi mafarki nake yi.
Sai da naga Yaya ya shigo, jiki babu kuzari, fuska very defeated, kawai na saki kuka ina jan Innalillahi...

Dr. Anita ta matso ta dafa kafadata tana lallashina har na dan nutsu nayi shiru, nasiha ta dinga yi min mai shiga cikin jiki da nuna min hakan ikon Allah ne, shi ya bamu shi dama tun farko, tunda kuma ya dauke kayanshi ba sai muyi hakuri ba. Sai da taga na daina kukan, sannan ta juya wajen Yaya shima ta mishi jaje, sannan ta barmu ni dashi.

Muna hada ido da Yaya, na sake barkewa da wani kukan. Ja na yayi cikin jikinshi kawai yayi yana shafa gadon bayana har sai da nayi mai isata, sannan ya dago kaina. Shi kanshi idanunshi sun kada sunyi jawur kamar wanda zai fashe da kukan. Nasan karfin hali kawai da jarumta irin ta namiji ce yake yi.

Ya taimaka min na tashi zaune saboda jikina babu karfi, likita tace ya bani abu mai ruwa in sha, a bani magani, amma sam na kasa cin komi. Sai da yayi kamar zai min kuka sannan na samu na dan kurbi yoghurt din daya kawo min. Ya bani maganin na sha.
Komawa nayi na kwanta, shi kuma ya zauna a gefena ya kamo hannuwana cikin nashi ya damke, wasu zafafan hawaye suke ta zirya akan kumatuna. Ya sanya hannu yana dauke min hawayen, cikin sanyin da muryarshi tayi, yake bani hakuri, yana kara yi min tuni akan yarda da kaddara.

Da alama maganin da aka bani har da na barci. Saboda ba'a jima ba barci mai nauyi ya daukeni.

Ban tashi ba sai washegari da safe. Ina bude ido, naga Janan zaune a gefena. Ban san lokacin da tazo ba, nan na sake bude wani shafin kukan tana aikin lallashi. Daga karshe nayi shiru, ta taimaka min na shiga bandaki nayi wanka. Na fito ta bani abinci na karya, na sha magunguna.
Tace Yaya ya zo da safe, yace zai kirani a waya saboda ana nemanshi a office ne, kai kawai na iya gyada mata.

Wajen karfe goma kuwa ya kira ni, na dauka muka gaisa. Dole na ware muryata sosai saboda kada ya karanci damuwar dake nake ciki. Nasan na kwallafa raina akan cikin jikina, amma Yaya ya fi ni. Tafiyar da yayi zuwa Niamey, haka ya dawo da kayan wasan yara kala-kala. Daki guda ya ware, yanzu ya kusa cika da kayan wasan yara dana sanyawa.
Ya tambayeni saukin jikina, nace mishi naji sauki. Nan muka dan sha hira dashi kafin muka kashe wayoyin da alkawarin zai sake kirana idan aka jima.

Yinin ranar cikin amsar waya da mutane yan dubiya muke, har yanzu na kasa yarda da cewa babu cikin jikina, amma idan na tuno hakan yana daga cikin kaddarar Allah, sai in kwantar da hankalina.
Matan Yaya ma sun leko zuwa rana, da dai-daya ma suka zo. Sai da Ameerah tazo ta tafi sannan Raheemah ta zo.

Zuwa can yamma, na dan warware daga jiki har zuci. Likitar data duba ni jiya, ta shigo ta sake duba jikina. Bayan yan tambayoyi data min na amsa, ta tabbatar min da cewa zuwa nan da kwana biyu ma zasu iya sallamata. Nace mata nagode.

Tace "amma barinki ya bani mamaki Nailah (haka yawancin mutanen asibitin suke furta sunana saboda basu iyawa), last time da kika zo muka duba ki, komi lafiya lau daga ke har dan cikinki, ba kwa fuskantar wata barazana. Kin tabbatar baki ci, ko sha wani abu da zai fitar da cikinki ta karfi ba? Saboda daga yanayin abin kamar da karfi cikin ya fita".

Na girgiza mata kai a hankali, nace "kawai dai kaddara ce Allah ya aiko".

Ta girgiza kai cikin nuna fahimta, "haka ne, Allah ya mayar miki da mafi alkhairi. Ki kwantar da hankalinki fa kinji? Kada ki sanyawa kanki damuwa".
Na sake mata godiya, ta mana sallama ta fita.

Tana fita Janan tayo kaina da tambayoyi, nace "ni fa

Please Login or Register in order to submit comment