Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaini da daukoni daga ranar. Ina daki sai jiyo tashin muryoyi na dinga yi, rigima suka yi sosai akan ya bada mota ana jigilar kaini wajen aiki.
Yace "kina nufin in barta tana kai da kawowa a cikin motocin haya ne, bayan ina da ikon da zan ajiye motar da zata yi jigilarta ne?".

Tace "ai wannna ma salon munafurci ne da rashin adalci. Ni me yasa baka ajiye min nawa direban ba sanda ina gidanka a Zaria, ka barni ina yawo a motocin hayar? Ko kuwa don ka nuna mana an shanye ka?".

Daga jin sautin tashin muryarshi a lokacin kasan cewa ranshi ya baci a lokacin, yace "aikuwa sai dai idan ke ce baki yiwa kanki adalci ba, amma clearly, zan iya tuna na ajiye miki da zai dinga yi miki hidimarki. Sannan kada ki manta, karatu take yi na aureta, kishin ki na banza da wofi ba zai sanya ni kasa sauke hakkin da Allah ya dora min ba. Babu yadda za ayi in bar matata ta dinga yawo a motocin haya a cikin garinnan, bayan ga motoci nan a cikin gidana Allah ya hore min. Idan ma abinda kike tsammani kenan, to sai ki daina!".

Cikin ihu tace "lallai ma! Wato kuma yanzu zagina zaka fara yi akan karatu ko? Wato saboda matanka suna da digiri, ni bani dashi, shine zaka fara zagina har matanka ma su raina ni ko? To wallahi ba'a isa ba!!".

Yace "zagi dai ke kika ji shi don ni dai ban daga baki na zageki ba. Karatu kuma bani nace ki barshi ba balle yanzu ki zo ki fara tada jijiyar wuya ki nemi ki tara min mutane ba. Wai ina dalili? Ba zaki taba barin rayuwata ta huta bane? Daga yanzu ki tado wannan, anjima sai ki kirkiro waccan?".
Tace "to saboda meye na katse karatun nawa? Ina jin saboda aurenka ne?".

Yaya yace "haka dai kike tunani, ni ban sani ba. Maganar direba ce dai, yana nan, kuma ai ba ita kadai na ajiyewa ba ko? Kema zaki iya aikenshi, zai kuma dinga kaiki duk inda kike son zuwa idan zaki tafi unguwa, don haka maganar wannan ta mutu!".
Ya bude kofar dakinshi a fusace ya shige, ya barta a falo tana masifa da mita, ni kuwa da nake kwance a daya daga cikin kujerun falonshi na kara lafewa akan kujerar, babu wanda ya kula dani.


Idan na tashi da safe ranar girkina, na kan hada abin kari mai rai da lafiya, idan muka ci, wani lokacin tare muke fita ni da Yaya, kowa ya wuce wajen aikinshi, watarana ya riga ni fita, ko kuma in riga shi. Karfe biyu na yamma nake dawowa, sai in dora abincin rana, shi Yaya baya cin abincin rana a gidan sai na dare, na kuma yi dashi akan in dinga dafawa ana kai mishi wajen aiki amma yaki, yace suna cin abinci acan.
Idan na gama abubuwan da nake yi da yamma, sai in dora abincin dare.

Sai ta fara mitar bana dafa musu abincin rana da wuri, ranar kuma da nake aikin rana ina dafa musu abincin rana da wuri, kafin lokacin ci yayi, abincin ya huce, ko ya saki, wasu irin excuses dai da daga jin su ma kasan rigima ce take nema kawai. Yaya yace to daga yau kowa ya dinga dafa nashi abincin da rana kawai.
Ba haka taso ba, maimakon ta bar maganar, sai ta fara masifar ita fa ta gaji da irin rashin adalcin da Yaya yake gwada mata, ya maidata saniyar ware a gida, ya biye min muna wulakantata, duk muka mata shiru dai. Data gaji da fadan, ta wuce dakinta fuu.
To yanzu dai a haka muke, yanzu ina cikin satina na biyar da dawowa Abuja kenan.

***
***
***

Dare ne sosai, baka jin motsin komi a cikin dakin, sai karan ac da kuma labulaye da suke kadawa sakamakon iskan da yake kadawa mai sanyi. Dakin babu haske, sai hasken farin wata daya ratso ta cikin tagogi da labulayen dakin.

Na sauke wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya a karo na barkatai, ni kaina bansan lokacin dana dauka a cikin wannan halin ba.
A hankali idanuna suka sauka kan sumar gashin dake saman kirjina. Tattausan numfashin da yake ja yana shaka yana sauka a saman fatar kirjina, rabin rigar barcin dana sanya yana saman ruwan cikina. Tun dazu numfashin ya fara saukar min da wani irin kasala, ya kuma haifar min da goosebumps a ilahirin sassan jikina. Sai dai duk yadda naso, na kasa samun zuciyar ture shi daga jikina, duk da ihun da zuciyata take yi min kuwa.

Cikin lokutan wadannan da muka yi munyi wani irin sabo ni dashi ba karami ba. Na sabar mishi da daddadan abinci mai rai da lafiya duk ranar girkina, tsabtar jikina da nashi, dakunanmu da kayan sanyawarmu, kamshin jiki, daki, da ma ko'ina, dadadan kalamai da sanyin hali. Ban taba daga sautin muryata tafi tashi ba a halin argument ko kuma hira kawai, ban taba tambayar dalilin wani umarni da zai bani ba koda kuwa ni abin bai yi min ba, shi yasa bana tantama yanzu har dokin zuwan ranar girkina yake yi, domin duk wani abu da zai sanya shi farinciki shi nake yi, bana yin abinda zai sosa ranshi koda wasa, sai dai cikin rashin sani. Sannan duk abinda zai yi ya bata min rai, ban taba confronting dinshi a gaban kishiya ba, kamar yadda naga tana yi ta kuma koya mishi, na kan bari sai mun shiga daki mu biyun mu sannan zamu kashe mu binne abinmu babu wanda ya sani.
Sannan duk runtsi, duk bacin rai, ban taba gigin raba mana shimfida ba, Anty Sarah tace kuskura na farko da mace zata yi wajen taimakawa balgacewa rayuwar aure mai armashi; raba shimfida da miji lokacin da ake cikin fushi.
Idan yanzu zamu yi fada, ko mu yini cikin fushi da juna, at the end of the day dai, zaka hangoni a dakinshi, akan gadonshi a kwance. Ko ban shige cikin jikinshi kamar yadda ya sabar min ba, zaka hangoni can karshen gadonshi. Sai dai da safe in tashi in tsince ni lullube cikin jikinshi, wasu lokutan daga nan zaka ga fadan ya wuce, watarana kuwa a nan kafin in fita dora abincin kari, zamu yi magana akan matsalar data taso mana, mu magance ta.

Matsalar daya ce dai har yanzu, mun kasa amsa sunan cikakkun ma'aurata. Tun yana kokarin yin wasanni dani a wasu ranakun, yanzu har ya ma daina attempting yin hakan.
Watarana haka na shiga dakinshi musamman, ciki da bai, har bayan dakin nashi, na fitar da komi na sharo har kasan gadonshi, true, na ciro layu, abubuwa iri-iri har cikin matashin kanshi naga abubuwa, naje can bayan gidan bayan Raheemah ta leka makotanmu gidan kawayen data fara yi, na kone su gabadaya.
Sannan cikin dabara da kissa irin tamu ta mata, na samu na lallabo kan Yaya Bilal, wani abokin Malam, babban Malami a cikin Suleja, yazo da dalibanshi suka yi saukar Al-Kur'ani Mai Girma a gidan, sannan duk sati yanzu ranar juma'ah yana bada rubutu a kawo mana, mu sha.
Sannan shi kanshi Yayan na dora shi akan hanyar sadaka ta ciyar da gajiyayyu, da marasa karfi. Yanzu haka duk ranar juma'ah, ana dafa abinci mai kyau a gidan su Ummah, a rabawa almajirai. Har Ummah sai data kirani a waya ta min godiya da haka, a cewarta hakan shawara ce mai kyau. Alhamdulliah, da alamun samun cigaba, tunda a hankali ya dawo da yan wasannin da yake min, duk da a yawancin lokuta na kanji dama kyaleni ya dinga yi, Yawancin darare haka yake barina cikin wani mawuyacin hali, darare da dama haka zan kare su cikin sharar hawaye. Sai dai ko a fuska, ban taba nuna mishi hakan yana damu na ba.
Yanzu dai ina cikin shakku ne, anya Yaya ba impotent bane? Musamman idan nayi duba da cewa, did shekarun nan da suka dauka da matan shi, basu taba haihuwa ba. Amma kuma ai Jan tace lafiyarshi lau, Allah ne bai kawo ba, but then, ba lallai Janan tasan yana da cuta ko baya da ita ba, tunda ba lallai ya fito ya fada mata hakan ba. Amma kuma da hakan ne, anya matan shi zasu yarda su zauna dashi? Ko kuwa? Abin har ya fara rikita ni.

Yau kam har na kwanta barci, wasu ayyuka ne suka sako shi a gaba a office kwana biyun nan, yanzun ma da kyar na janyo shi muka ci abinci, ya koma study room dinshi, wani dan karamin daki a cikin dakin nashi, nan yake gudanar da yawancin ayyukan shi. Har na gama duk wasu ayyuka da al'aduna, na kwanta yana kan desktop dinshi yana aiki.
Har wajen karfe sha daya na dare ina jiran ya dawo, naji shiru, na sake tashi na leka shi, he was so immensed a kan aikin da yake yi bai ma kula dani ba, don haka na maida mishi kofar na rufe, na kashe wutar dakin na kwanta abina.

Barci har ya fara daukata, ban san ko karfe nawa bane lokacin da naji ya hayo kan gadon finally, ya janyo ni cikin jikinshi.
Ina jin shi yana bin fatar jikina da shafa sensually, nasan dai karshen alewa kasa, wajen da muka saba tsayawa kullum dai nan zamu tsaya yau ma, amma kamar kullum, yau din ma kasa hana shi yin wani abu nayi. A haka ya taso ni na wartsake, ba'a jima ba naji nauyin kanshi a kirjina. A haka muka kasance tun dazun, na kasa koda motsa yatsa ne, na kuma kasa yin barcin.

Ban ankare ba, naji an fara kiran assalatu.
A hankali naji Yaya Bilal ya fara motsi, ba'a jima ba ya bude idanunshi, bakinshi dauke da addu'ar tashi daga barci.

A hankali ya dago kanshi ya kalleni, mamaki ya kama shi daya ga idanuna biyu.
Yace "tun yaushe kika tashi?".
Na daga kafada sama, "ban jima da tashi ba".

Ya kura min idanu kamar wanda bai yarda da abinda nace ba, na dauke kaina daga kallonshi kamar wadda take tsoron zai karanta tsantsar damuwar dake dankare a cikin raina. Sai dai ban tserewa hakan ba, ina jin ya karanci hakan, ko kuma ya fahimce ni.
A hankali naji ya sake janyoni cikin jikinshi, ya sake nutsa kanshi a kirjina kamar wani karamin yaro. Muka jima dashi a hakan, babu wanda yake kwakkwaran motsi, sai numfashinmu dake shiga kawai yana fita.

A hankali, daga can kasan makoshi, naji yace "am sorry baby!".
Na dan kalleshi in confusion, nace "saboda me?".

Ya tashi zaune sosai yana kallona, ni kuma nayi amfani da wannan damar na gyara zaman riga ta a jikina.

Ya kai hannunshi na dama ya kamo nawa dake kan ruwan cikina, ya damke cikin nashi yana murzawa a hankali, yace "for all of this, Na'ilah. Komi ma, tunda muka yi aure I was not able to... you know...!", ya ma kasa fadin kalmar, sai gesturing da yayi a tsakaninmu. Nima naji kunya, nayi kasa da nawa kan.

Yace "kawai ina so ki san cewa ba haka nake ba, ban san me yasa sai dake kadai bane hakan take faruwa, amma ina kan neman magani, don haka don Allah ki kara yi min hakuri, kinji baby na?".

Irin yadda yayi maganar da tambayar, helplessly, yasa naji wani irin tausayinshi ya rufe ni, haka naji wata irin soyayyar shi ta kara lullube min kirji.
Na kai hannuna daya na dora akan nashi hannun da har yanzu yake cikin nawa, a hankali, (don kunyar yin maganar naji sosai), nace "to ni menene na bani hakuri, laifin me kayi? Ko kuwa kaji ni ina complaining ne?".

Ya dan zare ido, idanunshi na nuna alamun mischievousness, yace "baki damu ba fa kika ce? Kenan ni kadai ne na damu, ina ta so inyi ajiya a nan!".
Ya kai daya hannunshi yana taba kasan marata. Na kai hannuna da sauri ina bige hannunshi, na kama idanuna na rufe, a lokaci guda kuma na juya fuskata na binneta cikin filo, "kai Yaya!". Na fada shrieking.

Ina jin sautin dariyar daya saki, ya mike tsaye yana cigaba da dariyar, "zaki sani ne yarinya, gwanda ma ki shirya tun da wuri, jikina yana bani soon, I mean very soon, wannan kunyar taki zata bar idanun nan naki da jikinki!".
Ban ce mishi komi ba har ya shige bandaki, sai da naji ya maida kofar ya rufe sannan na mike zaune ina ajiyar zuciya. A can kasan zuciyata kuwa, sai naji wani sanyi ya ziyarce ni. A raina nace 'at least dai lafiyarshi lau, sai dai mu kara kaimi wajen yin addu'a, idan ma wani abu ne, Allah ya yaye mishi'.

Yana fitowa daga bandakin, ban jira komi ba na fada ciki a sukwane.
Ina fitowa na ganshi akan abin sallah ya gama yin nafila, na dauki zanin dana shigo dashi saboda dorawa akan rigar barcin dana sanya idan zanyi sallah, na kalleshi, "yau ba zaka je masallacin da wuri bane?".

Yace "ina tunanin tsayawa muyi sallar mu ne a daki kawai yau".
Nace "ni dai na yafe, ka tafi masallacin ka kawai".
Yace "wai korata kike yi ne, baby?".

Na kama baki ina dariya, "ni ban wani koreka ba, kawai dai na fada mata ka tafi masallaci kaje kayi sallar ka ne a can, kasan yafi lada".

Ya mike tsaye, "ai shikenan, tunda abin ya zama haka, baby na ta fara gajiya dani har wani korata ma take yi daga daki".
Ban ce mishi komi ba, har ya fita daga dakin, sannan nayi murmushi na fara nafila kafin a kira sallah.



°•°•°


Ina kicin ina fama da yanka vegetables akan cutting board, Yaya yana dinning room akan daya daga cikin kujerun teburin, iPad dinshi ce a hannunshi, a cewarshi ayyukan jiya yake karasawa saboda a yau din ake so ya aika su, amma kuma hankalinshi baya kan wayar, duk motsin da zanyi idanunshi suna kaina.
Da yake yau ranar assabar ce, dukanmu muna gida.
Anty Raheemah har yanzu bata fito daga dakinta ba.

Har na gama hada abubuwan da zan hada, na kai kan table din na ajiye, Yaya yana zaune, sai dana gama hada komi sannan naje na buga mata kofa.
Ta bude kofar, har yanzu kayan barcinta ne bata cire ba, tana ganina ta hau wani yatsina, "menene?".
Nace "Yaya ne yace kizo mu ci abinci".
Bata ce komi ba, ta maida kofar ta rufe. Na tabe baki na koma inda Yaya yake.

Na zauna a gefenshi, na hau zuba mishi abubuwan dana dafa. A plate daya nake zuba mana komi, babu ruwana, tunda abinda yafi so kenan, to fa ni babu ruwana. Har muka fara cin abincin, babu alamunta.
Lokacin da tazo, daidai lokacin Yaya ya duka yana kwashe syrup din jam daya taba gefen bakina da harshen shi, sai sautin jan tsaki kawai muka yi.
Ta ja kujera ta zauna, babu ina kwana babu komi, ta mike kafa ta hau zuba abinci, shima Yayan bai ce mata komi ba, balle ni muka cigaba da cin abincinmu cikin shirun daya ratsa har muka gama. Ta tashi ta koma daki, shima Yaya ya koma dakinshi domin ya karasa aikinshi, ni kuma na dauki kayan da muka yi amfani dasu na wanke.

Tun jiya da dare Janan ta kirani a waya ta fada suna kan hanya ita dasu Harira da suka zo hutu. Da yake bikinta yana ta matsowa, nan da sati uku, suna ta aikin rabon katin gayyata da anko. Tace tunda aka kawo ankon, Yaya ya daukar mana ni da sauran abokan zamana, ina tunanin su ya basu nasu, don tace nawa kadai ya bada yace ta hada da nata a kai wajen dinki.

Tunda na shiga kicin din na hau hada musu abubuwan tande-tande da lashe-lashe da lemuka. Na saka lemuka cikin firjin domin suyi sanyi sannan na koma dakina ina jiransu.

Da wannna damar na samu na fara tunano maganganunmu da Yaya a daren jiya, nayi nisa cikin tunani, ban ma san lokacin dana dauko wayata na dannawa Sailu kira ba. Sai dana ji muryarta sannan. Nayi kamar in katse kiran kafin daga baya dai na daure na kara a kunne, muka gaisa da ita na tambayeta yan biyu, tace suna can gidansu.
Mun dan fara hira da ita, amma na kasa concentrating din komi. Da kanta ta fahimci ba lau nake ba, ta tambayeni lafiya? Da daga farko ce mata nayi lafiyata lau, kai tsaye tace karya nake. Ta fara watso min tambayoyi iri-iri, har sai data fara yin fushi, wai ban yarda da ita bane. Nace "wallahi ba haka bane Sailu, kema kin sani kuma".

Tace "to menene idan ba haka ba?".
Nayi shiru kamar ba zan ce komi ba, bata yi magana ba itama tana jiran taji abinda zan ce. In ina na fara, da kyar na iya rufe ido nayi summarizing din abinda yake faruwa damu tunda nazo gidan Yaya.

Tunda na fara take jan salati har na gama, tace "wannan ai babbar matsala ce Na'ilah! Kuma sai yanzu kike fada?".
Nayi shiru ina hararar bango kamar itace a wajen, nace "dama kika samu na samu kwarin gwiwar fada miki ko?".

Tace "kin taimaki kanki da kika fada da wuri kam, Allah kadai yasan abinda zai faru idan kuka cigaba da kasancewa a haka. Dole su Inna su ji labari!".

Na zaro ido, "mene? A'ah, don Allah kar ki fada musu".
Tace "to me amfanin fada min kenan? Ina dama don a nemo maganin matsalar ne a kuma maganceta?".
Nace "to amma fa yace shima yana neman magani!".

Tace "to sai me? Ba sai mu taya shi ba? Baki ji yan magana sun ce hannu da yawa maganin kazamar miya ba?".

Nayi shiru ina jinta amma hankalina bai kwanta da hakan ba, a tunanina da wani ido kuma zan iya kallon su Fatsu idan wannan maganar ta fita?.
Da lallami da nasihu ta shawo kaina na amince ta fadawa Fatsu ta fadawa Malam, sai da tayi alkawarin ba zata fadawa Yaya Mudatthir ba, amma nasan ko bata fada mishi ba, su Malam zasu fada sannan muka yi sallama da ita na kashe wayar.
Falo na koma naci gaba da jiran su Janan.

Sai wajen karfe sha daya da rabi sannan suka iso. Na fita waje na tarosu da doki na. Nan muka rungume juna muna juyi dasu, sai da muka gama dokin sannan naja su muka shiga ciki. Tunda muka dawo, sai yau suka zo. Baki a dage suka dinga kallon ko'ina suna santin gidan, sai dana musu tour din gidan suka gani sannan muka zube a kan kujerun falo. Na dauko cookies din dana musu da dambun nama da lemun kankana, lemun zaki dana yanka fresh strawberries a ciki, na ajiye musu. Kafin na leka dakin Yaya na sanar dashi sun iso, na koma wajensu.

Muna zaune muna ta hira ya fito, duk suka zame daga kan kujeru suna gaida shi. Ya amsa har yana hadawa da tsokanar su Harira suna ta dariya. Kujerar da nake zaune mai daukar mutum biyu ce, a tsakiyarta na zauna, fulullukan kujerar kuma a gefe da gefena, amma a haka ya kutsa ya zauna kusa dani. Na janye filo daya na kara matsawa gefe na bashi waje sosai.
A nutse suke hirarsu ta yan uwa wadda rabinta maganar makarantarsu ce sai kuwa zancen dangi da yan'uwa, bayan sun gama gaisawarsu, ya koma dakinshi bayan ya umarceni da shima in kai mishi cookies da lemun, nace to.

Bayan sun gama, muka koma dakina, sai da suka leka ta dakin Raheemah suka gaidata sannan muka wuce dakin nawa. Nan na barsu suna ta kara santin dakin, na koma na kaiwa Yaya cookies din, da kyar ya barni na koma wajensu. A cewarshi ba haka na sabar mishi ba. Nace "ni da zamu zo ma mu fita dasu yanzu? Ballema, na yau ne fa kawai!".
Ya wani turo baki har ya bani dariya. A haka dai na samu na zame na koma wajensu muka cigaba da hirarmu.

Tare dasu muka shiga kicin muka yi abincin rana, muna yin sallah azuhur muka fita rabon katin gayyata. Sai wajen karfe hudu muka dawo, don dama ba wasu gidaje masu yawa muka je ba, muna dawowa suka koma.

Washegari sai ga Fatsu ta kira, nasan akan maganar ce, da kyar na iya dagawa, kunya kamar kasa ta tsage in shige. Nan ta bani shawarwari da wasu addu'o'i da tace inji Malam tace mu dinga yi kullum daga ni har Yayan, ta maganin sihiri ce da sammu. Sannan tace akwai wani magani da za'a kawo mana hade da rubutun da aka saba kawowa, wanka ake yi dashi, mu gwada yin amfani dashi mu gani. Nace to, tare da mata godiya. Taci gaba da min nasiha game da rayuwar aure, tun ina jin kunyarta ma har nazo na daina don ita kam babu ruwanta. Mun jima sosai akan wayar kafin muka yi sallama.



A hankali bikin yana ta matsowa, kwanaki kuma suna wucewa. Na samu da kyar da jibin goshi an barni inje wajen biki inyi kwana hudu, daga can in wuce Katsina in musu kwanaki biyu. Zan dawo Abuja inyi sati biyu ko uku, sai in je Gashua. Duk yadda naso akan ya barni inyi ziyarar gabadaya, ki yayi, dole na hakura musamman da naga yana nema ya rufe ido yace bikin ma na fasa zuwa.

Ranar Laraba zasu fara shagulgulan biki, don haka nayi niyar tafiya ranar talata. Idan aka gama biki assabar, Lahdi in wuce Katsina.

Ranar litinin, ana washegari zan tafi. Ranar babu aiki saboda ranar hutun ma'aikata ce.

Da yake girkina ne yau, bayan mun gama karyawan safe, na koma daki na. Na cire kayan barcin dake jikina, na fada bandaki nayi wanka, bayan na fito na tsaya a gaban mirror na shafa mai, yau ko hodar ban shafa ba sai dan wet lips kawai, na bude wardrobe ina laluben abinda zan sanya.
Daga karshe dai idanuna suka sauka akan wata rigar atamfa, cikin dinkin da Janan ta kai min ne, ban taba sanyata ba sai yau.
Na fiddota tana ta tashin kamshin turaren kayan dana sanya a cikin wardrobe din kafin in shirya kayana.

Rigar doguwa ce, hannuwanta kanana ne da suka tsaya a damtsen hannuna, daga saman kafadar rigar an yi wani irin yanka ta yadda duka fatar wajen take a waje, haka daga bayan rigar ma anyi wani irin show me, rabin bayana a waje yake, daga tsakiyar rigar kuma daga baya, anyi tsaga tun daga kasa har tsakiyar rigar, idan na daga kafa ina tafiya tun daga gwiwata har kafafuna a waje suke.
Ni kaina dana saka rigar sai dana tsaya ina kallon kaina kamar ba ni ba yadda rigar ta fito da duk wata kira ta jikina kamar sai da aka auna ni, abin ya bani mamaki ya kuma kayatar dani.

Na kalli waje ta tagar dakin, naga yadda hadari yake ta kara gangamowa, tunda safe a haka muka tashi. Yanzu garin yayi luf, ya kuma dan yi duhu. Na dan sauke ajiyar zuciya tare da daukar comb na taje gashin kaina, na dauki dankwalin na daura kawai, gashina kuma ya tsaya a tsakiyar bayana yana ta sheki.

Ina cikin fesa turare, da niyar ina gamawa zan wuce dakin Yaya da nasan yana can yana jirana, sai naji an turo kofar dakin.,

"Bab...!"

Maganar daya fara ta tsaya mishi a makoshi. Na juya cikin mamaki na kalleshi, yana tsaye a bakin kofar dakin, baki a dage yana kallona, with admiration.
Na saki murmushi a tausashe, ko bai fada ba, nasan kwalliya ta biya kudin sabulu.

Na danyi juyi a gabanshi kamar wata wadda take fashion parade, na sake juyawa ina kallonshi, "nayi ne?".

Ya girgiza kai kamar yana shaking wani abu daga kan nashi, ya maida kofar ya rufe tare da takowa zuwa inda nake a hankali, ya tsaya a gabana. Hannu yasa ya kamo habata, na daga kai ina kallon idanunshi da suke karewa ilahirin jikina kallo, "Subhanallah! Just Masha Allah, baby na ba zaki gane irin kyawun da kika yi bane wallahi. Fatabarakallahu ahsana khaliqeen!! Dama haka kike, amma shine baki taba yi min irin wannna kwalliyar ba baby!".

Na saki yar dariya, "to yanzu ba gashi ka gani ba?".

Ya sake ni tare da ja da baya yana kara kare min kallo, ni kuwa nayi humoring dinshi ta hanyar sake yin wani juyin, na kara wani. Ina juyowa,

Please Login or Register in order to submit comment