Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ganin tana amsa min magana dai-daya yasa nayi shiru nima.

Tace "wannan likitan da kike biyewa, son shi kike yi ne?".
Na dan yamutsa fuska, "wace irin magana ce kike yi haka? Wani irin so kuma?".
Tace "to sai wani yage mishi baki kike yi kina dariya, me hakan yake nufi?".

Na girgiza kai, "don Allah kada mu ja maganar nan tayi tsayi. Ni babu wani son shi da nake yi".
Tace "to sai ki daina bashi fuska, a haka kina leading dinshi ne kawai ba wani abu ba!".
Na daga baki hangamgam, nace "to wai ke meye matsalarki ne? Idan na kula shi ko naki kula shi, meye damuwarki?".
Har ta daga baki zata yi magana, sai kuma ta fasa, tace "oho dai, ke kika sani!".
Muka yi shiru muka cigaba da tafiya, can kuma tace "ya labarin su Sailu?".
Muka karkata hirar zuwa can, wanda hakan ba karamin dadi yayi min ba.

Mun je ta sayi abinda zata ci, muka biya ta masallaci nayi sallah sannan muka koma ward. Acan taci abincin, muka cigaba da ayyukanmu har lokacin tashin mu yayi.
Janan ta riga ni tafiya saboda lokacin da aka tashi, wani yaro nake yiwa dressing. Faduwa yayi garin wasa da keke. Don haka ta wuce saboda a cewarta, zata biya kasuwa ta sayi wasu kayan bukatu kafin ta wuce gida.
Sai wajen karfe biyar da kwata na gama, na yiwa mutanen wajen sai da safe, na fita.

Sai dai cak! Naja na tsaya lokacin da nayi arba da abinda ban taba tunanin zan gani a daidai wannan lokacin ba. Yaya Bilal ne a tsaye kyam, tsayuwar sojoji, ya zube hannuwanshi duka biyu a cikin aljihun wandon kaftani dake jikinshi.
Kamar wanda aka ce mishi ya dago kanshi, karaf muka hada idanu dashi.

Abu na farko daya fara zo min a cikin raina, shine in fyalla da gudu. Sai dai da nayi tunani, sai naga meye na gudunshi to? Hakan ba wata mas'ala bace. Shawara ta biyu ita ce in tafi in raba ta gefenshi kawai in wuce, in nuna kamar ban san shi ba. Sai dai matsalar itace, kafafuna sun kasa motsawa balle har suyi tafiya. Don haka naci gaba da tsayuwa anan inda nake, ina kallon Yaya Bilal.

Ganin bani da niyar yunkurin yin wani abu, yasa ya tako cikin wani nutsattsen taku ya tunkaroni. Sai lokacin naji kafata ta motsa, na fara ja da baya, amma bai daina tunkarata ba. Da dai naga ya kusa cimma ni, sai na juya na sake fecewa a karo na biyu.

Can A&E na tafi, na shige can wani lungu da mutane basu cika bi ba na labe kamar wata munafuka. Na kwashe fiye da mintuna ashirin a wajen, zuwa lokacin nasan idan ma nema ne Yaya ya gaji ya kara gaba, don haka na fito daga maboyata.
Sai dana karewa wajen dana ganshi dazu kallo na tabbatar da cewa baya nan, sannan na daga kafa da sauri kamar wadda aka cilla daga jikin mashi, na dauki hanyar komawa hostel.

Sai dai da yake kwata-kwata yau sa'a ba a sashe na take ba, sai dana fara hango gate din hostel, har ina kara daga kafa, kawai sai ganin mutum nayi a gabana kamar wanda ya diro daga sama. Nayi tsalle nayi gefe daya a tsorace ina rafka salati, kafin in daga kaina in sauke su akan dodon nawa. Shi din dai da nake ta gudu.
Na sake juyawa da nufin ranta ana kare, ya sake shiga gabana, juyawar da nayi da sauri, da niyar bi ta wata hanyar, sai naji ni shame-shame a jikin bango. Shi kuwa yayi babakere a gabana, ya tsare gaba da baya, ta yadda babu yadda za ayi in tsere, sai dai idan bangaje shi zanyi. Ko kuma in ratsa ta jikin bangon dana jingina.
















*☆⋆25⋆☆*






Ga duk wata diya mace da take jin ta cika 'ya, mai cikar halitta da kamala, wadda zata shiga ko'ina ne a fadin duniyar nan kanta a tsaye, ta kuma amsa cikakken suna na 'ya mace, to ta cancanci gwarzon namiji kamar Yaya Bilal.
Irin mazajen nan ne da ake kira mazajen duniya. Wadanda Allah yayi wa ilhama da kuma rufin asiri ta kowane fanni.

Tun bayan rasuwar mahaifinsu, a lokacin yana ajinshi na shida a makarantar firamare, yayin da babbar yayarsu Yaya Sa'a take aji na biyar a sakandire, Jameel kuma yana primary three, duk da kankantarshi, Bilal bai yi kasa a gwiwa ba wajen zagewa tun karfinshi wajen ganin cewa ya tallafa musu. Wannan duniya da muke ciki ta riga ta zama abinda ta zama. Mutane basu san kowa ba daga kansu sai iyalansu, wasu ma iyalan nasu sai na kurkusa kawai. Mahaifinsu mutum ne mai rufin asiri daidai gwargwado, bayan rasuwarshi kuma sai rayuwa take nema ta zamar musu wata aba mai tsananin wahala.
Ummansu ta fara sana'o'i na hannu iri-iri domin ta samu ta tallafi ci da shan 'ya'yanta da karatunsu. To shima Bilal bai zauna ba, kananun sana'o'i na hannu babu wanda bai kama ya taba ba, kanikanci, dinki ne, bude karamar tired, da dai duk wata hanya daya san zata sada shi da samun halaliyarshi.

Duk da cewa yan uwa na iyaka bakin kokarinsu, sai dai kamar yadda nace, wannan zamani da muke ciki yanzu ya zama naka sai na naka. Koda suka fara abin daga farko kamar abin arziki, sai suka zo suka watsar. Shi kuwa yau a duniya, babu wani abu da yafi saurin zubar da mutunci da kima irin yawan bani. Ko iyaye gajiya suke yi balle kuma wadanda alaka ce kawai da bata kai ta kawo ba ta hada. Don haka suka kama kansu, idan an kawo musu abin amfani ko na tallafi, su karba suyi godiya, idan basu dashi, suyi kama-kama su rufawa kansu asiri.
Wannan gida da suke zaune, shi kadai mahaifinsu ya bar musu a matsayin gado, su ukun da kawunsu daya kasance kanin mahaifin nasu. Sai kuwa wata karamar gona da aka sayar da ita lokacin da Yaya Sa'a zata zana jarabawar fita daga babbar makarantar sakandire.
A cikin wannan lokacin ne mahaifinsu Janan ya fara neman Ummansu, lokacin matarshi bata jima da rasuwa ba. Kuma abokin mahaifinsu ne kafin ya rasu. Aka daura aure ta tare a Kaduna abinta.

Nan ya hade Bilal da Jameel din ya saka su a makaranta tare da sauran 'ya'yanshi suka cigaba, ita kuma Yaya Sa'a ya shige gaba, aka daura mata aure da wanda yake nemanta a lokacin bayan ta gama sakandire, taci gaba da karatunta a gidanta.
Bayan ya gama secondary, ya taho nan ABU Zaria yayi degree dinshi akan mass comm. Allah ya taimakeshi da taimakon Baban yara, ya gama degree dinshi da offer dinshi ta aikin jarida a hannu. Ya fara aikin a gidan jaridar Daily Trust da kafar dama, cikin dan kankanin lokaci ya samu karin matsayi, nan da nan yayi kaurin suna. Ya saye gidansu da suka gada a wajen kawunsu, itama Yaya Sa'a ya sayi nata ya bata kudinta. Yaje aka warewa Jameel nashi, ya tada gini abinshi. A cikin dan lokacin aka yi aurensu da Ameerah. Sun jima suna soyayya da ita, tun yana karatu a abu.

Har gashi a matsayin da yake tsaye a yau. Magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ilimi na musulunci da zamani ya gogar dashi. Yana fara aikinshi da Daily Trust, ya cigaba da neman kwalin masters dinshi ta online, bayan wannan bai dakata anan ba, yayi kwasa-kwasai da dama da suka kara mishi experience akan aikinshi, da kuma taimakonsu ne da taimakon Allah yake akan matsayin da yake yanzu a wajen aikinshi, Deputy Manager din Daily Trust.

Yana da wani irin hali na son yan uwanshi, zumunci da kyautatawa iyayenshi. Shi yasa har a kullum, Allah yake ta kara mishi budi da haske a cikin al'amuranshi. Allah ya wadata shi da haliita, zubi da kira irin na maza. Idan ka kalleshi sau daya, ba zaka so ka kauda kai ba. Irin halittar jikinshi halitta ce irin one in a million dinnan, kafin ka samu mai irinta sai ka dade. Sai kuwa alamun hutu da kasancewa cikin ni'ima ta rayuwa da suke kokarin boye yawan shekarunshi a duniya, wanda idan ba fada maka aka yi ba, mawuyaci ne ka iya cankar shekarun nashi kai tsaye.

Ta kowane fanni dai, Yaya Bilal irin mazan nan ne da idan mace ta samu irinsu, zata ce Allah ya karbi addu'arta, ya bata miji na kerewa sa'a. Idan kyawun ne, yana dashi, dukiya da rufin asirin ma dai Allah ya bashi, kyawun hali, kamala da nagarta, duk yana dasu. Duk dai wani abu da ake bukata a da namiji, miji na gari, kuma uban 'ya'ya na kwarai, idan aka zo kan Yaya Bilal dole a diga aya. Sai dai me yasa ni nake kokarin guje mishi tun karfina?!.


A yanzu daya zagaye ni ta ko'ina, duk inda na waiga babu abinda nake gani sai faffadan kirjinshi sai kuwa fuskarshi da sai na daga kai sannan zan iya ganin zagayayyun lebunan bakinshi, ni kuwa banyi wannan gigin ba. Kaina a kasa yake, ina kallon yatsun kafata kamar duk duniya babu wani abu daya kaisu kyawu.
Tattausan kamshin turaren da yake yi a karan kanshi, seems very inviting. Ji nake kamar wani maganadisu ne yake kokarin janyo ni zuwa jikinshi, domin inyi ta shakar kamshin kamar ba zan daina ba, kada ma kuma ayi maganar wannan managarcin kirjin nashi. Da na fara dago da kaina naga zan sauke idanuna akan shi, sai inyi saurin kara dunkufar da kan nawa kasa sosai.

Gashi a bakin hanya muke, mutane suna ta wucewa wanda duk da cewa kaina a kasa yake, amma na tabbatar kallonmu suke yi. Nan da nan nayi narai-narai, idanuna suka kawo kwalla.

Ina tunanin ya kula da hakan ne, ko kuwa wani abu ne na daban? Saboda da sauri naga ya ja da baya kamar wanda wutar lantarki ta ja, hannu daya soke cikin aljihun riga dayan kuma yana shafa bayan wuyanshi sheepishly.
Yace "God, don Allah kiyi hakuri. Amma meye na guduna Na'ilah kamar wani makiyinki?". Nayi shiru kaina a kasa.

Naji ya ja dogon numfashi ya ajiye, yace "ok..., na ji na kuma yarda ban kyauta miki boye kaina da nayi ba, sai dai bani da zabi ne Na'ilah, nayi tunanin wannan ita ce hanya mafi sauki da zata sa in saba dake. I was wrong ashe!". Yayi shiru yana kallona, ni kuma dana kasa iya hada ido dashi saboda tsabar kwarjinin da yayi min, nayi kasa da kaina.
Ya sake cewa, "kiyi min alfarma daya mana, ki zo muyi magana a nutse. Kinga nan a bakin hanya muke, sannan mutane suna wucewa ba zamu samu muyi magana a nutse ba!".

Gabadaya naji jijiyoyin jikina kamar an dauresu. Sai lokacin na dago muka hada idanu dashi, sanyin jikina ya karu, babu ma ta yadda za ayi in iya musawa wannan halittar da take gabana. Saboda haka na gyada kaina kawai, saboda a lokacin babu wata kalma da zata iya fitowa daga bakina.

Ya saki dan murmushi daya sa naji bugun zuciyata ya canza, na kara yin kasa da kaina. Yace "Masha Allah, bismillah!". Yana yi min nuni da tsallaken titi inda ya ajiye motarshi, ni sam ban ma kula da ita ba sai a lokacin. A hankali na daga kafafuna da nake jinsu kamar babu laka a jikinsu, na bi bayanshi har zuwa inda motar take. Muka jingina da motar, kaina a kasa ina wasa da yatsun hannuna, shi kuma yana ta aikin kallona. Bai yi magana ba, har sai da naji kamar inyi fiffike in bar wajen saboda yadda idanuwanshi dake kaina suka addabeni. Nan da nan naji babu abinda nake so a lokacin kamar kasa ta tsage in shige ciki ta rufe ni.

Sai da ya gama kare min kallo son ran shi, sannan yayi gyaran murya, ya kuma ambaci sunana cikin wata irin murya data girgiza gabadaya sassan jikina. Ban iya amsawa ba, sai daga kai kawai da nayi briefly na kalleshi wanda ko rabin sakan banyi ba na sake sadda kaina kasa.

Yace "Na'ilah kamar yadda na fada miki, ko kuma nake fada miki, takowa nayi musamman domin in baki hakuri. Na yarda cewa abinda nayi was not wise, kuma ba haka yakamata ace na biyowa abin ba. Na fahimci kina fushi, kina ganin kamar kawai ina yi miki wasa da hankaline wanda sam ba hakan bane. Saboda haka ne nake so ki bani izini, in bi ta hanyar data dace. Ina so ki yarje min, in gana da mahaifinki!".

Nayi gaggawar daga kaina na kalleshi sosai, kamar wadda aka bugawa guduma a ka. Wanda na tabbatar da cewa gurguwar shawara ce, saboda muna hada idanu dashi, I was a goner. Kamar maganadisu, haka na kasa janye idanuwana daga kanshi, ban san me kuma ya hana ni yin hakan ba. Gabadaya sai ma na manta da dalilin da yasa na daga kai na kalleshi har muka hada idanu dashi.
Shi ne ya fara janye idanunshi, sai a lokacin na hau kyafta idanu kamar wadda abu ya fada mata cikin idanu. Dole na saddakar, na ajiye duk wani abu da nake son fada a lokacin na tsaya ina saurarenshi.

Ya cigaba da cewa, "wannan yana daga cikin manyan dalilan da yasa na baro wajen aikina yau, domin ina so ne ace gobe in shaa Allah na hadu dashi munyi magana, mun tattauna an san da maganar mu. Tunda nan da watannin da ba zasu gaza shida ba zaku gama karatu, ina so kafin nan mu samu fahimtar juna a tsakaninmu, ta yadda kina gamawa ba za'a bata lokaci ba, sai kawai a daura mana aure. Ya kika ce?".

A raina naji wani banbarakwai. Abin dariya wai yaro ya tsinci hakori! Wato shi ana maganar son a san juna, shi ta maganar aure ma yake yi. Kodayake, yayi zancen fahimtar junan ai. Ganin na dauki lokuta ban tanka mishi ba, yasa ya sake cewa "ina saurarenki", cikin nuna kagara da son jin amsa daga bakina.

Ina so in daga baki ince mishi ni bana son shi, bana son aurenshi kuma bana son zama dashi, amma sam bakina ya kasa motsawa. Don haka na girgiza mishi kai kawai.

Yace "baki son aurena?". Na gyada mishi kai.

Ya dade yana kallona, har sai da naji na tsargu kafin ya nisa, yace "saboda menene? Na miki tsufa?".

Naji kamar into kwashe da dariya, wa yake ta wani maganar tsufa a halin da ake ciki yanzu? Balle ma Allah na tuba, wa zai dubi Yaya Bilal a yanzu ya kira shi da tsoho? Ai sai dai mara tsoron Allah.
Don haka na girgiza mishi kai alamun a'ah.

Yace "to idan ba wannan ba, menene? Baki so na?". Wannan karon ban ce mishi komi ba, a tsaka tsakiya nake. Kowace amsa na bashi yanzu, a tsakiya nake. Idan nace mishi bana son shi, na yiwa kaina karya. Idan na amsa ina son shi kuma, na karyata wani bangare na zuciyata kenan da yake so tun karfinshi ya nuna min bana bukatar shi a cikin rayuwata.

Nan ma ya jima yana kallona kamar wanda yake karanta ta, kafin ya sake cewa "saboda ina da mata ne har biyu?".

Nan fa ya sosa min inda yake min kaikayi, ba ko sake tunani na gyada mishi kai. Yace "me yasa? Matana zasu hana mu zaman aure dake ne, ko kuma kina tunanin ba zaki samu kulawar da kike bukata daga gareni bane saboda mata na?".

Ta wani bangaren har da wannan, sai dai wadannan duk sharar fage ne akan babbar matsalar. Wani abin mamaki kuma, sai a lokacin ne naji na samu muryata.

Nace "Babu ko daya, kayi hakuri don Allah. Ba zan iya abinda kake so ba!".

Yace "amma me yasa? Ina zamu kai son da muke yiwa juna?".

Nace "ai ana barin halas don kunya!".

Yace "wace kunya ce za'a bar halas saboda ita? Kada ki ce min wai saboda Ummah ne ko Janan, domin na tabbata su a garesu dauri ne zai tsinkewa mai kaya a gindin kaba. Bayan su kuma ban ga wanda zaki ce zaki zauna jin kunya ba. Idan ke zaki iya kauda kai, ki tuge son da kike min daga cikin zuciyarki, in gaya miki gaskiya ni ba zan iya ba! Don haka tun ma da wuri ki sake tunani".

Ni kuwa na sake baki kaina a kasa, kunya kamar kasa ta dare gida biyu in afka ciki. Tun da muke da Yaya, da duk sanin dana mishi, bamu taba doguwar magana mai tsayin gaske ba, balle har maganar so da aure ta shigo ciki.

A hankali na fara girgiza mishi kai, nace "ni fa duk ba wannan ba, kayi hakuri don Allah ka rufa min asiri, ka janye wannan maganar a tsakaninmu. Idan kai zaka iya, ni ba zan iya ba!".

Yace "babu abinda bawa ba zai iya ba Na'ilah, sai wanda kawai yaga damar ba zai iya din ba, sannan wannan magana da muke yi yanzu, babu wani abu da ba zaki iya ba. Zama da nine ba zaki iya ba, ko kuwa zama da kishiyoyin?".

Na girgiza kai kawai, Yaya Bilal ba zai taba ganewa ba. Ba zai fahimta ba, saboda haka nasan zama yi mishi wani bayani ma bata lokaci ne, don haka nayi shiru kawai.

Ya fara wasu dogayen maganganu akan yadda zai kama min gidana in zauna ni kadai ba tare da takura ba, da yadda zai kula dani. Har dai ya fahimci cewa ba fa saurarenshi nake yi ba, daga karshe dai yace in shiga cikin hostel, zamu sake yin magana.

Ni dama jira nake, na daga kafa da sauri na fada ciki, dama a kagauce nake. Bana so in mishi tsaurin ido ne, in tafi yana cikin yin magana kawai. Har yanzu da sauran mutuncinshi a cikin raina, ina kuma ganin girmanshi.


















*☆⋆26⋆☆*






"Wai ni wasu maganganu ne nake ji suna tashi a cikin ward dinmu game dake da Dr. Na Abba. Da gaske ne?".

Aisha, kawata take tambayata lokacin da muke kan hanyarmu ta dawowa daga cikin asibiti zuwa hostel a ranar juma'ah. Janan ta wuce gida abinta.
Na girgiza mata kai distractedly, "kin san mutane da son yayata abinda ba shi kenan ba, babu wata maganar azo a gani a tsakaninmu, har yanzu tangarda take yi".

Aisha ta gyada kai cikin nuna fahimta, tace "seriously, I shall warn you though, ana yawan fadin rashin kyawun halayen mutumin nan fa, duk da nima ba gani nayi da idanu na ba, ji nayi ana fada".

Na gyada mata kai kawai ina dan murmushi na yake, ba ita bace ta farko ba, ba kuma ba yau aka fara tarana da magana makamanciyar wannan ba, duk dai akan Dr. Na Abba. Cikin sati biyun da suka wuce, a kalla mutane fiye da shida, ciki har da Doctors da matrons, sunyi min magana ko ince sun buga min gargadi game da tarayya ta da Dr. Na Abba. Sai dai wani abu da basu sani ba shine, ni dai ba son shi nake yi ba. Ban kuma taba considering din maganar shi ba a cikin raina koda wasa. Saboda haka ni a ganina bata yawun bakinsu ne kawai suke yi, da kuma bata lokaci. Sai dai ban taba fada musu hakan ba, illa iyaka kawai duk abinda suka ce in tsaya in saurara, idan suka gama in musu godiya a wuce wurin.

Yanzu ma abinda na yiwa Aisha kenan, na mata godiya tare da tabbatar mata da cewa zan kiyaye kamar yadda ta bukata. Tace tayi farinciki da fahimtarta da nayi muka yi sallama da ita lokacin da muka shiga hostel, na haye sama ita kuma ta wuce sama dakinta.

Na saka key na bude dakin, kasancewar yau juma'ah, Esther ta tafi weekend, nasan cewa ni kadai zan dinga kwana a dakin daga yau har zuwa ranar sunday.
Na cire kayan jikina na rataye a jikin kusar da muke rataye kayanmu, na saka riga da wando cotton, na barci. Ba sallah nake yi ba, saboda haka lafiyar katifa kawai na bi na kwanta. Na janyo wayata na kunna, na hau chatting, bugs games, kallo, jin wakoki, har kokarin yin reviewing din project work dina dana kammala nayi, amma babu abinda ya dauke hankalina daga kan abu dayan nan da nake ta gujewa; Bilal Al-Qaseem.

Na rasa abinda zan yi akan mutumin nan, Allah ya gani, nayi iyakar kokarina, amma a banza. Gabadaya duk wata idea da tunanin yadda zan yakice duk wasu feelings da nake ji game dashi, na rasa. Duk wata hanya da zan bi, na bi. Amma a banza.
Kullum ta Allah ji nake kamar kara min so, bege, da kaunarshi a cikin raina ake yi. Na rasa kalar wannan masifar.
Wadannan yan lokutan, lokuta ne masu tsananin wahala da ban taba fuskantar irinsu a cikin rayuwata ba. Saboda haka ne na rasa yadda zan tunkari wannan al'amari.
Yaya Bilal ya zamo wata gagarumar wuta da take ci ganga-ganga a cikin raina, amma na rasa kalar ruwan da zai kashe min wannan wuta. Na kuma rasa yadda zanyi, saboda a kullum wannan wuta kara ruruwa take yi a cikin raina, tana kuma kona ni fiye da tunanina. Tana azabtar dani.

Yau dai kwanaki kusan goma sha uku rabon da inyi waya da Yaya Bilal. Tun washegarin ranar da yazo ya turke ni, ya kira ni. Lokacin muna cikin yin wayar, I snapped. Ban san lokacin dana mishi tsawa ba. Yana magana ne akan da gaske yana son aurena tsakaninshi da Allah, ya dage akan ba zai hada mu waje daya dasu ba, zai min nawa gidan daban. Ban san abinda ya shiga kaina ba a lokacin, su kansu kalmomin dana furta ban san na fade su ba sai bayan da suka fita daga bakina, nace "Wai ana dole ne? Ko kuwa ance maka ban san ciwon kaina ba? Dole ne? Ka kyaleni don Allah, nace maka bana son ka!!".
Nayi shiru ina sauke ajiyar numfashi kamar wata kumurcin macijiya.

Yaya Bilal shiru yayi a lokacin, kusan mintuna biyu tsakanin ni da shi babu wanda yayi magana. Sai sautin saukar numfashinmu dake tashi kawai. Daga baya ma sai ya kashe wayar shi, bai ce komi ba.
Daga wannan rana bai sake kirana ba, ban sake ganinshi ba.

Daga farko cewa nayi tafi nono fari tas. Sai dai me! Ba'a cinye kwararan kwanaki biyu ba, jikina yayi sanyi da jin yanayin shirun da yayi. Ban san me yasa na damu ba. Haka zan saka wayata a gaba ina kallo sau tari, ina contemplating din in kira shi ko kuma in kyale shi. Komi da yake faruwa a lokacin sabo ne a gareni, wanda ban taba experiencing dinshi ba a tsawon rayuwata. Ko rabuwar mu da Umar, ban ji kwatankwacin abinda nake ji a halin yanzu ba. Duba kuma da tsawon lokutan da muka dauka tare da shi, da kuma wanda muka dauka da Yaya Bilal, abin mamaki ne.

A kwanaki na hudu sai gani kunshe akan katifata cikin dare ina shakar kuka na fitar hankali. Kamar wadda aka sanarwa da wani babban jigo nata ya bar duniya. A lokacin kukan shine kadai abinda nake gani mafita ce mai kyau. Bayan nan barci ya kwasheni, wanda washegari na tashi da ciwon kai mai zafi da kumburarriyar fuska. Tun daga wannan ranar har yau ban daina yin wannan ciwon kan ba.

Janan, dama duk wani wanda ya sanni, ya san irin natural cheery behavior dina, yasan cewa wadannan yan kwanakin ba lafiya ta lau ba. Duk wanda muka hadu dashi sai ya tambayeni, lafiya?. Tun ina murmushi ina basar da maganar, har na gaji, idan ma an tambayeni sai dai kawai in kalli mutum blankly ko kuma kawai in basar in ki amsa tambayar, yaudarar kaina kawai nake yi, ba lafiyata lau ba. Ta yaya ma zan zauna lafiya bayan na ki ba zuciyata abinda take muradi?.

Yau Janan ta gayyaceni zuwa Kaduna mu yi weekend a can, sai dai kai tsaye nace mata ba zan je ba. Tunanina daya, idan fa naje muka hadu da Yaya Bilal acan? Me zan yi, ko kuma me zan ce mishi? Ita kanta Ummah ban san da wani ido zan kalleta ba idan naje, don haka duk da ina son zuwa, haka nan nace mata taje ni ina da abubuwan yi.

Please Login or Register in order to submit comment