Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujera.

Sai dai zaune a kasa, daf da kafafunshi, don idan ma wani ya kuskure zai iya cewa akan kafafun nashi take a zaune.
Amma ba ma wannan bane ya dauki hankalina ba, ba kuma dariyar dana tarar suna yi ba, kwalliyar data zabga ne kamar zata je gasar sarauniyar kyawu ta duniya, sai kuwa wani zagayayyen kyakkyawan ceramic plate da yake ajiye akan cinyarta shake da waffles da aka kwarara jam daya nutella akai, ga kuma fresh berries. Abin ya bani mamaki har na kai ga dan dakatawa.

Shirun da suka yi suna kallona ne ya sanya na dawo da hankalina kansu. Na danyi murmushi kawai tare da takawa na karasa wajensu. Sannu na mata ta amsa fuskarta da sauran fara'ar dake kan fuskarta lokacin dana shigo cikin falon.

Yaya ya kalleni lokacin da nake zama a gefenshi, akan kujerar kusa dashi, cikin murmushi.
Na gaida shi ya amsa, tare da cewa "har kin dawo? Ya asibitin?".

Nace "lafiya lau, yanzun nan na shigo. Dama lekowa nayi in ga ko kana bukatar wani abu kafin in gama girki sai kuma naga...", na kakare ina karewa plate din hannun Anty Ameerah kallo. Daga ganin yadda yayi fresh, kamshi yana tashi, kasan ba'a jima da gama yin shi ba. Probably bayan Yayan ya dawo daga wajen aiki.

Maimakon ya nuna wani abu, ko ita, sai naga yayi murmushi. Yace "ai Yayar ki ta hutar dake, sai ki sanya ranki a inuwa...", ya dauki daya ya sanya a bakinshi, ya gutsira ya tauna har da hadawa da lumshe idanu, "... kuma yayi dadi sosai. Bismillah, ki taba mana".

Na girgiza kai a hankali ina kokarin danne wani abu daya taso ya tsaya min a makogaro, kwacen girki kuma da rana tsakiya kiri-kiri?.

Nace "a'ah, na gode. Bari inje in karasa girkin. Anty Ameerah nagode fa!".
Idanunta akan allon talabijin tace "babu komi Na'ilah... Yiwa kai ne!".

Ban ce komi ba na tashi na fita daga falon.
Spaghetti na dafa, nayi warming miyar da nayi. Kafin Yaya ya dawo na kai mishi abincinshi falonshi. Su kuma matan nashi na ajiye musu nasu akan dinning table.

Daki na koma, na shirya kayan dana yasar, na gyara dakin nawa sannan na koma falon Yaya ina jiran ya dawo daga masallaci.

Yana dawowa na shirya abincin, na zauna a gefenshi na zuba mana muka fara ci. Yau abincin kadan yaci, a cewarshi Yayata ta cika mishi ciki. Murmushin yake kawai nake binshi dashi, saboda maganar gaskiya abin ya bata min rai. Akan me ni da girkina, ni da mijina, kawai tazo wai ta mishi girki? Ina so inyi magana, sai dai dole haka nayi shiru saboda bana son yace ina neman tada mishi zaune tsaye a gida, ko kuma bana son zama lafiya, ban godewa abinda ta min ba. Don haka nayi ta kauda maganar ina turata can bayan raina.

Ni kaina abincin yau haka nan dai naci shi cikin dauriya kawai. Mun saba idan muna cin abinci, haka zai yi ta yabon girkin da na mishi, wasu lokutan kuma yana ta tsokanata da yan wasannin shi.
Yanzun ma a hankali naji hannunshi yana min tafiyar tsutsa a bayana ta dan slit din da aka bari a bayan rigar dana sanya. Na daga kai na kalleshi a hankali, ya daga min gira challengely, cikin nuna alamun yana jiran yaga reaction dina.
Nayi dan murmushi, ina kokarin ganin cewa ban bari abinda ya faru yau ba ya hana ni samun farincikin raina dana mijina ba.

Don haka na biye mishi. Cikin kankanin lokaci munyi gefe da kayan abincin, sai gani a saman ruwan cikinshi ina kokarin daukar alewar bounty daya boye a bayanshi.

"Baby na.... Zaki karya ni fa, kinyi nauyi da yawa.. Baby, wayyo!".
Amma kuma dariya yake yi cikin shessheka, nima dariyar nake yi lokacin da naci sa'ar dauko sweet din.

Na koma na zauna a gefenshi ina bare ledar, shima ya tashi zaune yana maida ajiyar numfashi kamar wani wanda ya kwashi wani dambe.
Ina bare ledar na kai baki na hau taunawa, ya kalleni cikin zare idanu, "ba dai cinyewa zaki yi ki hana ni ba ko baby?".
Murmushin tsokana nayi tare da saka gabadaya sweet din cikin bakina.

Yace "kam, gaskiya ban yarda ba..".
Ganin yayo kaina gadan-gadan yasa nayi dan ihun tsokana naja da baya, amma duk da haka sai daya damko ni.
Yayi amfani da karfin jikinshi yayi trapping dina a jikinshi ta yadda babu yadda za ayi in kwace, bakina yake kokarin hadawa da nashi da niyar zakulo sauran alewar data rage a bakina, lokacin da aka turo kofar falon aka shigo.. Da sauri na daga kai naga Ameerah ce. Idanuna suka sauka akan agogo, naga karfe tara ce saura. Wani haushi yazo ya cika ni, kowa yasan a cikin gidan nan idan karfe tara ta gabato a cikin gidannan, kowa ya nemi makwancinshi, sai a bar mai girki ita da mijinta. To me kuma ya kawota yanzu?.

Kallon dana bita dashi baki a dage ne ya ba Yaya damar cikashe abinda yayi niyar yi. Sai lokacin ya sake ni, ya koma gefena yana tauna alewar a bakinshi.

Ameerah ta nemi kujera ta zauna, "sannunku da hutawa". Ta furta cikin fara'a.
Muka amsa mata, ni ciki-ciki, Yaya kuma yana dan murmushi, yace "baki kwanta bane har yanzu?".

Tayi wani fari da idanu tana rangwada, "wallahi kuwa baby, ban san me yasa na kasa yin barcin da wuri ba yau, shine nace bari dai in zo in rage dare anan".
Yaya ya daga kai distractedly, hankalinshi gabadaya akan tv, ana hasko wani labari akan wata sharia da ake kwasa tsakanin wani dan uwa da dan uwanshi.

Na mike tsaye ni kuwa na nade ledar dana shimfida mana na kaita inda ake ajiyeta a cikin falon, na dawo ina hada plates da kulolin, sai lokacin na dan saci kallon inda take, ta canza kayan dazu dana barci yanzu, riga da wando na cotton masu kyau da suka bi jikinta, ta dora hular beanie da tattausan silifas mai buzuzun gashi a kafarta. Nayi kwafa tare da kwashe kayan abincin na tafi kicin.

Ina gamawa da kicin na koma dakina. Na shiga bandaki nayi wanka, brush, na dauro alwala. Duk da cewa ina period, hakan baya hana ni kwanciya da alwala a jikina idan zan kwanta.
Bayan na gama, na dauko kayan barci masu kyau da bayyana surar jiki na sanya, na shafe ilahirin jikina da turaruka masu kamshi da nutsar da zuciya, na dora hijabi doguwa akan kayan nawa na fita daga dakin bayan nasa makulli na rufe dakin.

Har yanzu Yaya da Anty Ameerah suna falon suna hira, sai dai yanzu maimakon kujera, ta sauko kasa kusa dashi. Sunyi nisa a hirar da suke yi sosai, basu ma ji lokacin dana shigo ba.
Nima na lalubi waje kusa dashi na zauna. Ban yi kokarin tsoma musu baki a cikin hirar da suke yi ba, na kurawa tv da take ta aiki kallo ba tare da ina fahimtar komi da suke yi, ko suke fada ba.

Hirarsu suke tayi akan wani cousin dinta daya samu aiki da wani babban kamfani da yake kera motoci a kasar Germany, hirar ta gangara ta koma kan businesses da mahaifinta yake yi, har ta sake gangarowa kanta, wai itama tana so ta fara yin business, amma bata san akan abinda zata yi ba. Nan suka fara muhawarar abinda yakamata tayi.

Da dai naga karfe goma ta wuce, sai na tashi na musu sallama na wuce uwar dakan Yaya.
Anan dinma nafi kusan mintuna goma da shigowa kafin naji ya shigo dakin. Ina jinshi ya shiga bandaki yayi abinda zai yi ya gama, sannan ya dawo dakin. Ya kashe wutar, kafin ya hayo kan gadon inda nake, ya janyo ni cikin jikinshi.






*☆⋆42⋆☆*




Gidan shiru, baka jin motsin komi lokacin dana fito daga dakin Yaya na shiga kicin, duk da cewa karfe tara ne lokacin. Nasan hakan baya rasa nasaba da cewa yau din ranar karshen hutun mako ce.
Na tsaya a tsakiyar kicin din ina tunanin abinda yakamata in dora, daga karshe dai na kunna gas na hau aiki.

Sai wajen karfe goma da rabi sannan na gama. Na dauki na Yaya na tafi falonshi na kai na ajiye, sannan na dauki na matan nashi suma na kai falo na ajiye. Lokacin Raheemah har ta fito, tana zaune akan daya daga cikin kujerun falon tana waya da daya daga cikin kannenta.
Na leka dakin Yaya, baya kan gadon amma da alamu yana bandaki yana wanka saboda karan ruwa da naji yana tashi. Na karasa na gyada dakin tsaf, na kawo airfreshner na fesa. Sannan nima na koma dakina.

Kai tsaye wanka nayi, na fito nayi amfani da hand dryer na kafar da gashina, sannan na zauna akan dresser na fara bin duk wani lungu da sako na jikina da turaruka masu kamshi, wadanda nasan suna rikita min Yaya. Kamar kullum, yau ba ban wani tsaya yin kwalliya ba, bayan yar hoda dana goga, wani lip balm kawai na shafa a bakina. Mai kamshi da taste din strawberry. Wani zuwa da Anty Sarah ta taba yi nan, ta kawo min shi. Ban ma taba shafa shi ba sai yau. Na kalli kaina a madubi, nayi dan murmushi ganin yadda na fito tsaf a cikin kayan dana sanya. Riga da siket ne na wani material mai taushi, yanayin dinkin kamar wasu English wears. Rigar mai dogon hannu ce, amma an tsaga hannun tun daga kafada har tsintsiyar hannu, shima siket din anyi tsaga a tsakiyar shi ta yadda bayan kafafuna suke a waje idan ina tafiya. Nayi daurin dankwalina fanka, gashina dana kame a cikin band ya fito yana ta sheki da tashin kamshi. Na fita daga dakin.

Har yanzu Yaya bai fito ba, don haka na wuce dakinshi kai tsaye.
'oh please!!', na fada exasperatedly, lokacin idanuna suka sauka akan Ameerah dake zaune akan kujerar hutu dake fuskantar kofar dakin.

Yaya yana gaban dresser da ruwan tokar jallabiya a jikinshi, mai yake shafawa a sumar kanshi, gefe guda abin sallah ne a shimfide, da alamu tashin shi kenan daga kai. Kila sallar walaha yayi.
Yayin da matar tashi take sanye da riga da wando, English wears, kai babu dankwali balle hula, kitson da aka yi mata ya kkwanto har dokin wuyanta. Jarida ce a hannunta tana dubawa, Yaya kuma nata zuba mata hira.

Na girgiza kai a hankali ganin sun zubo idanuwansu kaina, Allah kadai yasan irin takaicin daya ciko min ciki, haka nan na daure na kakaro murmushi tare da karasawa cikin dakin. Yaya ya bini da kallo yana murmushi.

Na karasa gabanshi na tsaya, "Barka da safiya Yaya, har ka tashi?".

Yayi murmushin nan nashi mai burgewa, "na tashi tun dazu, har na gaji da jiran kizo ki taya ni shiryawa".
Nayi tunanin yanzu ma cewa zai yi an hutar dani, har na fara plotting irin rashin mutuncin da zan manna musu, nace "kasan fa girki na fita inyi, idan ka gama shiryawa kazo muje ka karya".
Ya gyada kai, "na kusa, gani nan zuwa. Kinyi kyau fa!".

Na kalli kayan jikina, kafin na sake kallonshi ina sakin murmushin saye zuciya, na manna mishi peck a kumatu tare da rada mishi thank you a kunne.
Sai dana juya zan fita sannan na kalli inda Anty Ameerah take, nace "oh oh! Anty Ameerah an tashi lafiya? Ashe kina dakin?".

Dan murmushin da yake kan fuskarta ya yaye, kafin ya sake dawowa, "lafiya lau Na'ilah. Wai ina dan taya shi hira ne ganin shi kadai ne a dakin".

Na girgiza kai cikin murmushi nima, idan duniyanci ne, gidan shi tazo, nace "babu komi wallahi, kin kyauta. Abinci ya kammala idan zaki ci".
Ta gyada kai tana murmushi, ni kuma na bude kofar dakin na fita.

Nayi zaton zata biyoni ne, amma shiru har na gama zubawa Yaya abincinshi, bata fito ba. Zuwa can sai gasu sun fito tare, hannunta damke cikin nashi. Na ciza baki cike da takaici da kuma mamakin matar, ina kula da lokacin da Yaya ya zame hannunshi daga cikin nata, amma duk da haka sai data sake yunkurin kamo shi, yayi saurin zama kusa dani. Ni kuwa na fara tura mishi abincinshi gaban shi.
Abincin dana zuba daidai wanda zamu iya cinyewa ne ni dashi, ina kallon yadda ta fara raba kallo tsakanin kulolin dana ajiye a bude babu komi a cikinsu, da kuma plate din gaban Yaya.

Ganin bata da niyar barin wajen, yasa nace mata "abincin a babban falo na ajiye".
Ga wani mutum daban, ko kuwa shi Yaya dake zaune yana durawa cikinshi abinda na girka mishi, zai yi zaton cewa tuni ne kawai nake mata, amma ita ta sani, nima nasan cewa ce mata nayi ta bamu waje.

Na kura mata idanu ina son tace wani abu, kamar tana son taci gaba da zama anan taga yadda ake fadin 'bar nan wajen', gatsar. Kowa yasan cewa ranakun weekend, har azuhur mai girki tana tarr da maigidanta suna hira ko duk ma abinda suka ga dama. Duk sai idan Yaya ya dawo daga masallaci sannan muke haduwa a babban falo, watarana kuma a falonshi, wani lokaci ayi hira, watarana kuma kowa yayi abinda yaga yafi mishi. To meye nata na wani zuwa ta dinga neman batawa mutane jindadin safiyarsu?.

Murmushi itama tayi, daga ganinshi bai kai ciki ba. Ta kalli Yaya tana wani firirita da rangwada, "babyyy... Kasan fa bana jin dadin cin abinci ni kadai musamman idan ina ganinka, gaskiya ni dai bari inje in zubo nawa sai inzo nan mu ci At least idan ina jin motsinku a kusa dani zan fi jin dadin abincin".

Yaya ya danyi hesitating, da alama shi kanshi bai yi maraba da hakan ba, sai dai sanin halin Yaya na rashin son disappointing mutane, ba zai iya cewa a'ah ba.
Ban ce komi ba, kaina a kasa ina tura abincin cikin bakina kamar bana ma jin abinda suke fada, sai dai gabadaya hankalina yana kansu ina jiran abinda Yayan zai ce mata.
Kallona yayi, yace "babu matsala?".

Na daga mishi kafada kaina a kasa, "wai ni? Noo, babu komi. Meye a ciki?".

Yaya bai fahimci yadda nayi maganar cike da dacin rai ba, yace mata "to ki je ki zubo din". Ta kuwa juya ba musu ta fita daga falon.

Na bita da kallo ina sake-sake a cikin raina, wata idea ta sauka a cikin raina. Nayi murmushin mugunta.

A hankali na matsa kusa da Yaya, na tabbatar kamshina yana kaiwa cikin hancinshi yadda na kamata, cikin salo na karairaya, ina kada idanu nace mishi "kasan wani abu Yaya?".

Ya dago kai a hankali ya kalleni, ina kula da yadda ya lumshe idanu yana kara shakar kamshin turarena, nayi murmushi. Kai kawai ya iya dagawa ba tare da yace komi ba, daga haka ma kadai nasan cewa ya shiga cikin wani yanayi.

Na kara matsawa saitin kunnenshi, "yanzu nayi wanka", na rada mishi a kunnen nashi.
Kallon daya watso min cikin zare ido yasa na kusa shekewa da dariya, na dai daureta, nayi murmushi, "da gaske?", ya tambaya breathless, kamar wanda yake dambarwa da numfashinshi, na gyada mishi kai.

Bai ce komi ba, ya ture plate din abincin can gefe, bai ankare ba naji an daga ni sama cimak, sai dakinshi. Na sheke da dariya ina kokarin zamewa, amma ina, ya maida kofar dakin baram ya rufe kamar tashin duniya. Bai min masauki a ko'ina ba sai akan tattausan gadonshi.
Tun ma kafin in gama tantance abinda ya faru, naji an fara zame min kayan jikina. Dariya kawai nake kyalkyalawa, gefe daya cikin farinciki, ganin yadda mijina ya rikice bayan dududu kwanaki shida ne kawai muka yi ba tare da juna ba, gefe daya kuma ta mugunta ce. Ina ta picturing yadda fuskar Ameerah zata kasance idan ta dawo cikin falon nan taga babu kowa sai kwanukan abinci kawai. Ko zata biyo mu taga abinda yasa muka tashi kuwa? Na sake sakin wata dariyar ina tunanin abinda zata yi idan ta shigo ta ga halin da muke ciki yanzu. Watakila daga yau ta shiga cikin hankalinta.


⋆⋆


Lokacin da muka sake fitowa daga dakinshi, tuni wasu masallatan suka gama sallar azuhur. Falon babu kowa sai kayan abincin da muka bari dazu, nayi murmushi ina girgiza kai. Yaya ya min sallama ya fita zuwa masallaci, ni kuma da yake na riga nayi tawa sallar a dakinshi, na hada kayan na wuce kicin.
Dukansu suna babban falo a zaune, Raheemah na kallo, Ameerah kuma tana wasa da kan wayarta. Na musu sannu na wuce kicin, babu wadda ta amsa min, sai Raheemah data bini da kalmar 'jarababbiya', ban ma nuna naji abinda tace ba na fada kicin.
In dai akan farantawa mijina rai ne, babu abinda ba zan iya yi ba, ban damu da duk abinda zasu ce ba, duk wadda taga zata iya jerawa dani, sai ta biyo bayana mu buga.

Yinin ranar haka muka yini, yau mu duka hudun muka hadu a falo ana ta hira, wadda yawancinta ni da Yaya ne muke yin ta, Raheemah bata saka mana baki sai idan harkar korafi ta taso, dama nan tafi auki, ita kuwa Ameerah, kokarinta kawai taga ta janye hankalin Yaya daga kaina, wanda ban bari hakan ta faru ba. Tana bukatar kara zage damtse sosai kafin hakan ta faru. Bata san cewa zaman nan da muka yi dasu ba, don dai ya zame min dole bane? Ni a son samuna, mu zauna mu biyu daga ni sai shi kawai, amma duk da kasancewarsu anan wajen, hakan ba zai taba hana ni yin abinda zai sanya mijina cikin nishadi ba. A haka dai yinin namu ya kare.


Yau ma da dare irin jiya ce ta faru, sai gata ta kwaso kwalliya, wai tazo taya mu hira. Sai dai maimakon wannan karon inji haushin haka, sai kawai nayi murmushi. Naci gaba da yiwa Yaya tausa a kafafunshi kamar yadda ta shigo ta same mu, muka cigaba da hirarmu dashi. Babu jimawa ma Yayan ya tashi yace zai je ya kwanta, muka mata sallama muka shige daki bayan mun bar mata sakon ta kashe wutar falon idan zata fita.

Washegari na fita daga girki, Raheemah ta amsa. Wani abin mamaki, sam Ameerah bata yi abubuwan data fara yi ba lokacin da nayi nawa girkin. Kenan hakan yana nufin ni ce dai take yiwa wannan shirmen? Idan kuwa haka ne, a shirye nake. Wannan shi na kira 'kishi'.
Kodayake, ban ga laifinta ba, Raheemah dai ba ruwanta da wani kula da tarairayar miji. Idan ta dafa mishi abinda ta dafa, wani lokaci yini take yi tana kallo a falo ko kayan da aka ci abinci bata dauke ba, watarana kuma gidan ma take bari. Saboda haka nafi kyautata zaton Ameerah gani take yi kwace miji a hannun Raheemah ba wani aiki bane, kuma da gaskiyarta. Sai ni kenan.


*


To rayuwar haka taci gaba da tafiya dai. Zaman da muka yi dasu a waje daya ya bani ikon fahimtar su sosai.

Ita Raheemah, tana da wani irin hali na daukar zuga da shawara. Babu abinda zata aikata ko ta gudanar, sai ta nemi shawarar kannenta. Sai ya zama kamar sune ma suke juya mata rayuwar aure gabadaya. Bata tsinanawa miji komi sai dan banzan mita, yawo da lalaci.

Ita kuwa Ameerah, ita ce ainihin ma'anar kissa da iya lallabin miji. Ta kowane fanni ba za'a kirata wadda ta gaza ba, ta iya kwalliya, girki, uwa uba iya kula da miji. Matsalar, bata san miji ya gindaya mata doka ta bi ba, sai dai tayi abinda taga dama kawai, babu ruwanta. Akwai lokuta da dama da zai hana ta fita, amma yana saka kafa ya fita, haka itama zata dauki makullin motarta ta fita Wata latest Benz da mahaifinta ya aiko mata da ita, da Yaya yace ta maida, a cewarshi me zata yi da mota bayan ga motoci nan ya ajiye mana? Sai tace mishi su duk gidansu, babu wanda yake tuka Honda da vibe. Ina wajen lokacin da hakan ta faru, sai na kama bakina kawai ina girgiza kai.

Akwai ma wata rana da zai tafi wata seminar ta kwana uku Gambia, tace mishi zata je gida kafin ya dawo, yace mata a'ah. Sai dai yana tafiya, sai ga wannan yar uwar tata data rakota ranar data dawo, da alama anan cikin Abujar take, suka fita babu ko sallama, lokacin itama Raheemah su Salame sun zo, sun shiga gari yadda suka saba, ban ce musu komi ba nima. Ashe Babanta da kanshi ne ya sai mata tikitin jirgi suka tafi kasar France wajen graduation din dan gidan kanin Babanta. Sai ranar da Yaya zai dawo da yamma, ita kuma ta dawo da safe.
Ire-iren wadannan abubuwan dai, ina kula dasu. Ban taba daga baki na fadawa Yaya ba, saboda na farko bana so ace ina tada rigima da zauni tsaye, na biyu kuma bana son ya kasance daga bakina ya fara jin wannan danyen aiki, nasan zai iya cewa kawai na fada ne, don haka na kame bakina na bame.

Tunda dai yanzu duk na karanci halayensu daya bayan daya, ina zaune da kowaccensu ta yadda ta bullo min. Na kan bi duk hanyar da zan bi wajen ganin cewa na kaucewa cece-kuce dasu, idan daya daga cikinsu ta min abinda bai kwanta ba, na kan san yadda nayi na maida musu da martani a aikace ba tare dana bari fatar bakina ta motsa ba.

Ameerah irin mutanen nan ne macizan sari ka noke, sai lokacin na fara yarda da maganganun Janan akan cewa gwanda zama da Raheemah akan Ameerah. Saboda ita Ameerah, sha yanzu ce magani yanzu, idan abu bai mata ba, zata fito tsab ta fade shi, koda cikin masifa ne kuwa. Ita din kamar budadden littafi ce, mai saurin karantawa. Ameerah kuwa ba haka take ba, baka taba fahimtar inda ta sanya gaba. Hakan kuwa yana da nasaba da halinta na danne komi da murmushin da bai idanunta ba, ita ba kamar Raheemah bace sam. Raheemah idan mutum bai mata ba, to kawia bai mata ba, ko kallon inda mutum yake bata yi balle kayi tunanin ta damu da kai. Yayin da Ameerah baka sanin tana son ka ko tana kin ka, sai dai kaga hakan a aikace kawai ba tare da hakan ya nuna a fuskarta ba. Hakan yasa mafiya yawancin lokuta Yaya ya kan yi zaton idan ta aikata wani abu, mistake ne, saboda haka baka da damar da zaka yi korafi.
To a kowani hali dai, haka muke gudanar da rayuwar tamu, yau dadi, gobe babu.


Tunda na fara internship dina sai wannan satin suka fara biyanmu, saboda yar matsala da aka samu wajen shigar da takarduna, amma yanzu komi ya gyaru.

Ranar da aka turo min kudin na gansu kamar a mafarki, har sai da nayi hawaye. Yau dai wahalhalun nan da muka sha, sun fara biya. Na shiga kasuwa, siyayya tun daga kan su Auwal, har matan Baba da shi kanshi, babu wanda ban ssiyawa abu ba, haka su Fatsu dasu Yaya.

Anyi hakan da kwana hudu, na tafi Gashua. Yaya ya sai min tiket din jirgi wanda ya sauke ni a Yobe, daga can na wuce Gashua.
Ba karamin jin dadin yadda na samu su Fatsu nayi ba. Yan biyun Yaya suna ta guje-gujensu da surutu. Sai lokacin naji cewa ashe bayan aurenmu, sau biyu Yaya yana zuwa suna gaisawa. Bai kuma taba gaya min ba. Yanzu ma da zan taho haka ya hado ni da kudin tsaraba wadda sai da nazo nan sannan na siya abubuwan da zan raba. Kamar kullum, a gidan Fatsu na sauka.

Kwana na biyu ina yawon gaisuwa da ganin dangi, ana uku ne muka je Kauyen Alkali wajen Anty Halima. Ba karamin murna tayi da ganina ba. Muka mata yini ni da Sailu da twins, sai da yamma sannan muka koma. A gidan su Sailu muka sauka, na zube akan kujera ina nishin gajiya. Tunda nazo

Please Login or Register in order to submit comment