Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya koya min mota.

   Gudu nake kamar zan tashi sama, muna isa gidan na fito da gudu ko kan faruq ban bi ba na shige cikin gidan dakin shi na wuce na daki kofar, zuɓewa nayi tare da fashewa da kuka, kamar raina zai fita.
"Bayan kashe min Uba da kika yi na rufa miki asiri yau mijina kika zo zaki haramta min shi! Mommy meye na miki da kika zabi sani kuka a rayuwata.

     Mommy Mijina ne fa! Me zaki yi dashi? Ashe tubarki bata Allah bace? Dama shiru  kika yi sai na saki jiki ki cutar dani,

       Toh ki dauki abinda ranki yake so ki bar min shi zan zauna dashi, naga duniyar da ba yawa ce da ita ba,  Allah ya baki dama dan ki gyara Kuskuren ki, amma kika shure, ina ji ina gani kika rufe min baƙi kar nayi magana akan mahaifina! Sannan da kika ga bai miki ba, kika yi ta wasan kura dani, daga nan zuwa nan Mommy nayi karuwanci saboda ke, don Allah ki bar min halwani.

         Shine abinda nake bukata a rayuwata, idan kin san Darajar Ubangiji ki bar min shi don Allah karki haramta mishin, idan kuma kika ji raina ya baci, toh ni bazan dauki mataki ba! Amma Ubangiji zai min sakayya."

    Matar nan tayi nisa, da kunya ina ganin wannan al'amarn, Uncle baya cikin hayacin shi, ban san ya kome ya faru ba.

Bata kulani ba, kawai so take ko ya-ya Penis din shi ya shiga jikinta, kuka nake ina ce mata.
"Don Allah fa! Karki min haka kinji don Allah, rokonki nake."

      Na rigada nasan zata aikata kawai nafice daga d'akin, na fito bakin kofar ina kuka.
"Shiiiiii!"
Sanyin da naji a gefen kafana ya sani fahimtar abinda yake shirin faruwa, maza na rike jelar shi a fusace ya juyo, lokacin su Faruq da kanen shi sun hauro.
Suka ce.
"Ummi!!"
Da mugun karfi sake jelar nayi tare da kallon shi.
"Mahaifiyata ce! Na hada ka da Allah karka mata kome, dama shi ba kaddarata bane, don Allah shuraihu, kaji don Allah."

        Cikin sanyin ya kuma sulalewa ya bar gidan, ihun Mommy naji tafito da gudu, a rikice na yo kanta.
    
Ganinta nayi a ƙasa tana birgima. Banyi ta kanta ba na wuce gurin mijina, nayi nayi ya farka bai tashi ba, dole na kira Mama Hussainah na gaya mata,  ita tazo ta ɗauki Mommy Suka tafi da ita, gurin su.

          Sannan Nakira Rahbeel, yazo muka nufi asibiti yaran muka ajiye su a gidan gurin Mamie.

    Idan ba tuna abinda Mamie tayi min sai naji bazan iya kuma kallonta as my mother ba, Amma idan na tuna, duk abinda ya faru akan soyayyar Abu daya ne! Uncle Ahmad Halwani! Sabida shi Mamie ta koma cruel muguwa, sabida shi ta koma kamar mahaukaciya, kawai sabida SO! Ta koma mara tsoron Allah tausayi babu, babu kome, ta koma kankarariya, kawai abinda take bukata ya zama nata ita ɗaya, hawaye ne ya silalalo min....
#Mai_Dambu ...
¹. Mik'ewa Nayi lokacin da Rahbeel, ya fito tare da sauke ajiyar zuciya yace.
"Ki kwantar da hankalinki! Ya farfaɗo har ya samu barci, dama kamar wani abu me ƙarfi aka watsa mishi.

.... kuma Alhamdulillah, ya farka yana barci ne!" Gyad'a kaina nai tare da zuba mishi ido, kafin nace.
"Toh nagode"
Na koma inda nake zaune na cigaba da zama,
"Zo ki shiga cikin dakin mana!"

Kamar bazan iya ba, kawai sai a shiga ko ba kome na mishi kallon karshe kafin mu rabu, tunda nasan Mommy ta rabani da shi, ina zaune ina kallon shi, ruwa na sauka a jikin shi.

... wannan lokacin bana bukatar taimakon kowa sai na Allah, dan haka bayan na samu nutsuwa nayi sallolin da suke kaina, na tashi tare da kiran Mama Hussainah! Na tambayeta inda suke.

             ....fita nayi daga dakin, sannan na nufi gidan, tunda na shiga na same su cirko cirko, Mommy tana ihu tare da gurnani.

     Tana fadar abinda ta aikata, tare da bin mijin Maryamu, Mama Hussainah, Kuka take tana kai karar Mommy,

    Juyawa nayi zan tafi na kuma komawa dakin na leka tare da cewa.
"Baki ga kome ba! Allah sai yabi mana hakkinmu!"

          Ina gama gaya mata haka na juya na bar gidan, ko asibitin ban koma ba, na shiga hada kayana, dole na bar shi ba dan.

Ina cikin hada kayana, naji ana cewa.
"Toh ina zaki? Akan me zaki bar shi?  bayan abinda kike zargi bai faru ba! Don Allah kije ki jinyanci mijinki, in ba haka ba zaki ga samu ki ga rashi.

     Ki godewa Allah, da kome yazo karshe, kuma kinyi nasara hakurinki yayi amfani. Ki godewa Allah, tunda gashi nan kina hana kowa kusantar inda ya ke."

         Zama nayi kuka ya kwace min, dan nayi sosai sannan na koma asibiti.

       A zaune na kwana, ko abinci na kasa ci, idan na tuna rayuwata sai naji na kuma tsanar Mommy.
.da asuba ya farka, a hankali ya miki min hannun shi, sannan na isa gare shi.

        Rungume ni yayi sannan yace..
"Kiyi hakuri! Ban san me ya faru ba!"
Rufe mishi baki nayi da hannuna, sannan na fara da bashi hakuri, sannan gaya mishi gaskiyar abinda ya faru.

                Kallona yayi sannan ya kuma rike hannuna yace.
"Daga ni har ke, bamu yi sa'ar iyaye mata ba, Mamie Abu biyu yasata hanani nononta Hajiya ta reneni, sabida ba a Sanya sunan mahaifinta ba, sai kuma dan karta rasa tsarin halittar.

    Ke kuma taki mahaifiyar ta kai karshe gurin son zuciya,"

   Haka yayi ta min nasiha, ina kallon shi ban iya magana ba.

    Bayan sati daya, duk wanda ya kalle ni sai yasan ina cikin damuwa.

    Dan haka ya kwashe mu da yaran muka tafi Umrah, alhamdulillah, na samu nutsuwa bai gaya min ya fara aiki a can South Africa, sai da muka baro saudiya, Muka dire a nan Cape town.
.ya same koyarwa a jami'ar su, ga kamfanin shi na kera-kere da yake garin.

       Tunda muka iso, garin hutun wata daya nayi sannan na fara karatu, karfi da yaji ya shagaltar dani tuna baya. Haka nake farin ciki na.

   Dake ya dauko Salim, tare muna zo yaron yafi sakewa damu, ba kamar sauran mutane ba.

          .......
Mommy hauka tuburan tayi kanta ya kunce, sai ihu take tare da niman guguwa, ranar juma'a tana cikin wannan yanayin wani tsaka ya sauko daga sama, ya cije ta a gefen wuyarta..

       Ai kuwa kafin gari ya waye, fuskarta ta yi wata irin kumbura, karshe bata iya kome sai fidda wani irin ruwa me hade da tsotsotsi, haka suka kaita asibiti tana wani.

            Suna zuwa aka yita fama da ita, sannan suka dawo, gida.
Bayan kwanaki wani abu ya shige gabanta, ihu take kamar zata mutu har ta samu sannan ya fito su Mama Hussainah ba ganin shi fuskar shi tayi jaga-jaga da jini,

         Wata irin ukuba take sha, wanda ya sanya ta kara kuncewa tana kiran sunan Omar, wato Abbanah, lokacin da nakira Mama Hussainah. Take gaya min abinda ya faruwa.

    Ban wani damu ba, kawai na turo masu kuɗi me yawa wanda zasu kula da ita.

     .........
Ina kwance a jikin shi, sai sake murmushi nake,
Gyara min kwanciya yayi yana kallon fuskana yace.
"Kafar Mamie za a kuma yanke mata zuwa gwiwarta."

Zubur na mike cikin tsoro, tare da rike bakina, dawo dani yayi sannan yace.
"Laifin da ta aikata ne yake bibiyar ta, da yau banyi hakuri da halinta ba da naga abinda zai wargaza min farin ciki na, Alhamdulillah."

      Haka na cigaba da zubda kwalla, ina jin ba dad'i.
Daga haka ban kuma cewa kome ba,

      Haka rayuwar mu tayi ta juyawa farin ciki, bakin ciki.

Amma daga ɓangaren Mommy kuwa azaba take ci, sai Allah tun tana haukar har ta dawo hankalin ta.

    Sai ga Mommy na rokon ta mutu ta huta.....

    ***
Bayan shekaru biyar..

Zamu je hutu Nigeria, hada kaya nake naji yazo ya rungume ni ta baya, tare da ce min Happy Valentine's day 14 February.

        Juyawa nayi na ganshi sanye da han shirt da farin trouser, haka takalmin shi ma, juyawa nayi sannan nace mishi.

" Ka manta yau zamu bar kasar nan shine kake wannan abun, idan Yarana suka gani kasa su.".

"Eheeeee! Ummi happy valentine day"
   Matsar dashi nayi na zuba musu ido da gudu suka fita na cigaba da abinda.

       Rungume ni yayi cikin nutsuwa yana cewa.
"Kiyi hakuri!"
Abinda naso tun tuni ya fada min bai fada ba, sai gashi a duk lokacin da nayi fushi, ina ganin tashin hankalin shi, duk sai ya gigice yayi ta bani hakuri.

   .... Ya kuma sa Yaran a gaba har d'akina suka bani hakuri, me yafi haka namiji ya koma mace kai ka koma boss, ba Wai Dan reni ba.

A'a sai dan Allah ya bani shi a hannuna ne, ba dukka ba. Dan bai hana idan halin Mazan ya motsa ya zabga min rashin kirki don ranshi.

    Mace zaki ga ta haɗu ta haɗa kome, duk yadda takai karshen haduwa wallahi sai kiga namiji ya kafta mata rashin mutunci.

             Bai fada min inda zamu fara zuwa ba, sai da muka shirya tsaf, muka fito, tare da shiga jirgi.
 
Karfe biyu na safiyar talata muna isa kasar korea, zaro ido nayi dan tun a can airport ya sayawa yaran shi manyan manyan kayan sanyi, muna shiga garin ya mika min nawa, da mayafi, muka kasa magana nayi ina kallon shi.

      Har muka shiga cikin sai ga Jim da Sheena, tare da yarinyarta. Da sauri muka karasa tare da rungume juna.

      Daga nan muka nufi gidan su, inda muka ga tarbar kamar babu gobe, bayan mun huta muna shiga dakin cin abunci. Muna gamawa muka fito.

          ........ Kwanan mu goma a can muka nufi, Yemen. Ban san dalilin shi na kawo mu ba, amma ina kyautata zaton sabida Salim me.
  Tunda muka isa bai yi wani yunkuri ba, sai kai mu guraren shakatawa, tare da mana sayayya, ranar da muka cika kwana uku.

       Salim da Anum sunfi shakuwa, Yayinda kullum suke faɗa da Anuam, kamar zasu cinye junar su dan fada, dariya Yake musu yace min.
"Wallahi bani ganin wani abu kawai abinda suke aikatawa kamar Kauna ce me tsafta"

    Share batun nayi, dan karshe sai da ya gaya min yana ganin son juna suke, dan a duk lokacin da Anum ta zauna kusa da Salim, Anuam zata iya tureta, shi kuma ya maketa ya gaya mata ai Anum abokiyar shi ce, idan taji haushi tace mishi.

      Ugly kawai, tana gaya mishi haka zai taso ya daketa, ban tab'a jin na hana shi ba, sabida kunsancin yayi dai-dai.

    Ita kuma Anum abokin fadar ta Ra'uf babban Yaron Aunty Sarinah, Wai ce mishi take ido huɗu, sabida yana saka glass dan.yana da laluran idanu.

      Wannan abin dariya yake bani, Kawai dan sun san abokan wasansu, Babana ne dai babu ruwan shi, babban mutum kullum zaka ganshi ya hard'e yana zuba iko, badan Ra'uf da Salim sun girme shi ba ban san ikon da zai yi ba, sak Uncle yake komawa, yayi ta zuba manyance, ko idan yana karatu kanen da Salim suka dame shi sai ya koma d'akina yayi karatun shi baya son fitina sam Ubana kenan, ai gado yayi.

       Mun shiga wata mall mun gama sayayya kawai naji Ihun wata mata, da sauri muka isa tana cewa.
Don Allah waye yazo mata da Muizzudin dinta, murmushi Uncle yayi tare da zuwa ya amshi hannun Salim, kunsan Halin larabawa da masifar son yaran su.

  Binshi take, har muka iso gurin biyan kudi tace kar a karbi kudin shi.

          Don Allah ya gaya mata wannan jinin sune?!

      Tausayi ta bani na tab'a Uncle.

   Kallonta yayi sannan ya mata.
"Ki same mu a masaukin mu."

Sannan ya fita da yaron, abin tausayi haka tabi bayan mu, har masauki sannan ta kira mijinta da sauran yaran ta, suka zo.

   Tunda muka fito da Salim yake kuka, dan yasan mika musu shi zamu yi.

        Nima daurewa nake, a hankali Uncle ya ciro abin hannun da Muizzidin yabawa Mah Liqah, sannan ya mika musu takardun shaida tarayya Dan su da Mah liqah, sannan yace.
"Kanwata ta rasu, ta bar salim, da sa ran zai hadu da mahaifin shi, daga ganin ku ba sai anyi magana ba, Salim jininku ne, amma bazamu iya baku shi ba, Dan muna tsoron kar mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mahaifiyarshi."

     "Don Allah! Karku hanamu shi, muma mun rasa mahaifin shi, a wani hatsarin da yayi. Amma kafin nan ya gaya mana, cewa yana da yaro da wata yar Afrika, yasan bazai tashi ba amma da ya nimo ta, don Allah ka bar mana shi wallahi muna kewar shi da mahaifin shi."

          "Zamu bar muku shi amma abisa sharadin, nice lawyer shi badan kome ba, sai dan karku hana shi zuwa ga dangin Mahaifiyar shi ga takardun saka hannu ku nimo mana lauyanku."

      Haka kuwa aka yi, sannan muka gaya musu zamu tafi Nigeria, domin muna zaune ne a South Africa, idan muka dawo zamu zo daukar shi sabida karatun shi. Babu yadda suka iya, amma wallahi suna haukar son yaron. haka suka saka hannun tare da amincewa.

  Sannan suka ce mu biyo su masarautar su na Yemen.

             Kai jama'a, yaro da fatan shi a maida shi maraya, dukiya iri na larabawa ba iya, dan haka har wani shirgegen daki aka ware mishi,

     Kome na jin dadin rayuwa sun ware mishi, tare da kai shi. Anan muka ci abincin dare da zamu tafi ya rike hannun Anuam.
"Yau babu fada ne?!"

        Girgiza kai tayi tace.
"Baka ganka a katon gida bane kamar castsly, idan nayi fada masu bindiga harbina zasu yi, kawai me zancewa Kaka idan muka je!"

       Dariya yayi sannan yace mata.
"Kice mata, Insha Allah idan nazo hutu zan kawo mata zinari da diamond, Tunda tace tana son Tayi kwalliya dashi."

          Shafa kanshi nayi tare da zuba mishi ido, nace.
"Karka yi abinda zai sa ace bazan mai daka gare mu ba, kayi kome da nutsa da kuma ilimi, idan kayi haka, ka kyauta min ka kuma burge ni. Allah yayi maka albarka idan kayi sallah kayi ta saka Amminka da Abbinka a cikin addu'a Allah ya jikan su da rahama."

   Dakyar muka bar gidan, sabida yaron yana da shiga rai.

...... washi gari muka koma, ina lura da yaran duk sunyi kewar shi, koda muka isa gidan Nigeria, kowa murna yake da zuwan mu sai tambayar shi aka muka gaya musu yana can masarauta su.

    
      Mun sha hutu da zaga dangin mu, Uncle ya hanani zuwa ganin Mommy, ƙamar zanyi kuka haka nake rokon shi. Dakyar ya dauke mu da yaran muka je.

                Lokacin da muka je, gaskiya Su Mama Hussainah sunyi namijin kokari, Bala'i ta kare ta koma abin tsoro, duk wannan dagawar  babu, sai tsantsan azaba da cutar kanta da tayi.

.... Kuka nake bawai na tausayin ta kawai ba, na tsoron Allah nake kawai saboda yadda Allah ya mai da mata sharrinta.

          Tunda muka dawo, zazzaɓi ya kamani, dama tun Yemen nake zargin ina da wani cikin, ban yarda ba sai da na fara zazzaɓi da ciwo sosai.

   ........ Sati biyu  muka tafi gurin dangin mahaifina, bayan naga abinda Uncle yayi musu na cigaba,  koda zanyi magana yace min bafa shi yayi ba, dukiyata na karuwanci ya dauka bayan ya tambayi malam ko zai iya gina masalaci da islamiyya shine aka ce eh.

         Dariya abin ya bani, kwanan mu daya muka dawo gombe.

           ......
Hajiya girma yayi mata rabga, dukda akwai Addinin a jikinta sai abin yazo mata da sauki babu kidimewa babu shiririta, sai ma ibadar da ta kuma mai dashi abokin hiranta.

    .ita dama addini da ibada, baka gane tasirin shi sai girma ya cimaka, duk dattijon da ya koma ba banza zaka samu bai gina zuciyarshi da kwakwalwar shi da ibada bace sai girma yazo kiga ana sake layi.

        Toh yaranta batayi kyau ba, amma aka gina farkon da tubalin  addini sai ka samu karshen tayi karko, itama Mommy abinda ta rasa kenan, da ta samu kyakyawan toshe karshen da zai yi kyau koda tsakiyar bata gyaru ba.

      Abinda ya kwaci Mamie ta gyara alakarta da Allah, shi yasa karshen bai mata muni ba, aka batar da datse sassan jikin ta.

           ......wata biyu cib muka yi sannan muka koma, SA. Bayan kakan Salim da Yan uwan baban shi sun kawo shi dan since ba sai mun bata kuɗin jirgi ba zasu kawo shi.

     Tunda ya dawo na fahimci, ya kwaso al'adar kakanni shi, murmushi nayi toh ya za ayi ai jinin sarauta ke yawo a jikin shi.

Sosai na sakewa yarana muna raba matsalar mu dasu, bamu takura su ba.

        Ko dawowar mun nan wai na hada master Uncle yake so, ga cikin da yazo ba zata.

     Yaran Khuwailah uku itama, Yaran Mah Naz, biyu.

          Yaran Dilshad uku,
Da Asood tana auren Ahmed dan gidan Baffa Ibrahim.

        ----
A can kuwa dangin Linah, Yan uwan baban su, ne suka tashi tsaye da addu'a akan Allah ya dawo musu da hankalin dan uwansu jikin shi bayan dama shima haka yake da mugun hali.

    Linah kan haka halinta ya tafi da ita, dan tana nan amma kamar bata san kome ba.

    Mamawo kuwa yawan jini domin yaranta sun sanya mata bakin ciki da damuwa, daya Yaronta an kama shi da kisan kai, aka rufe shi dayan kuma garin fada akan budurwa aka kashe shi.

      Sai wanda Linah take bi, yake dan shaye shaye.

Dole ciwon zuciya ya kamata....

   Dama wannan tabbatacciya, ce kana niman zuri'a ta gari ka samu mace ta gari, duk da nasan nima na tab'a bariki, toh amma kulluma addu'o'in nake akan yarana maza da matan, dan dukkan su laifi daya suke aikatawa.

Shi yasa kome suka yi nake bin diddingin suke yi.

        ----
Alhamdulillah wannan karon da kaina na haihu, inda na haifi da namiji, me kama dani, tunda Uncle Yayi min wayo, duk masu kama da shi nake juye mishi.

       A can  gida Gombe anyi suna a gurin mu kuma walima ya shirya mana.

    ....... Bayan shekara biyu abinda nake burin zama, ya tabbata cikakkiyar Lauyan me kare hakkin mata, kamar yadda nayi fatan na zama me cikakken nasara, da taimakawan mijina na zama jarumar mace, na kuma samu nasarar daukaka kimata Sosai.

      Dan ko da muka dawo, Mommy nacan na fama da azabar duniya,  watan mu goma da dawowa Allah ya amshin rayuwar Hajiya, mace me addini da sanin ya kamata, nafi kowa kuka.

     Yarana ban tsannanta musu ba, shi yasa kome ya faru zasu zo su gaya min Ummi kaza Ummi kaza.

     Duk wanda yake aikata sharri Allah ya mai da mishi abin shi, naje har Yola nayiwa Ammin Amrah godiya, sannan nace yanzun bana ganin Umma Zuljah, ta mika min godiyatabda Fatah Alkhairi.

        Mijina jarumi ne, wanda ya haɗa hakuri da sanin darajata, wata asabar mun je Super market, muka hadu da wata mata, tana bin yaran da kallo.

   Daga baya na Uncle ƴace.
"Dr Mayah Malik! Ga mata na, Brrst Yumnah Omar Ahmad da yaran mu, Faruq wancan, A'isha da Fatimah, Abubakar Sadeeq, shine karamin yaron mu."

  Tayi farin ciki sosai, sannan ta gabatar da yarta mai suna Seerat sai karamin da tasanya mishi sunan Uncle, Shima Halwani.

                  Bayan mun musayan Number ne, muka dawo gida.

             ----
Ina kwance a jikin shi, tare da rike hannun juna yace min.
"Saura me ya rage baki cimma ba?!"

       "Babu komai! Kawai ka yafewa Mommy da Linah abinda suka mana shine abinda rage min."

       "Toh Na yafe musu shikenan!"
" Ba shikenan bane baka ga yadda Allah ya mai dasu bane, wallahi nashi yafi su daraja, masu kula su, dan babu yadda zasu yi dasune amma da sun gudu, shi yasa nake biyan kudi a cigaba da kula min da Mommy, toh da ta koma sai Allah, wannan ai damuwa ce, da kanka ka kirkiro abinda zai kashe ka da ranka, gashi fatar mutuwa take amma taki zuwa."

.... "Eh ai gwara ta rayu amma cikin ukubar rayuwa,"

"Kai Uncle! Mamata ce fa!"
"Toh ita Mamie baki ga bana jin kome dan ciwon sugarta na cinyeta, da a lokacin da nake bukatar ta, ta bani kulawa wallahi da haka bai faru ba.

     Nono ta hanani, abinda yasa ma nake tausayin ta sabida dawainiyyar ciki da kuma Haihuwa, kinsan darajar nonon uwa ai, tunda kin shayar, me yasa idan kina Shayarwa mai damunki da akula min da Yarana.
.  Sabida na rasa nonon uwa, dan haka Malama bar wadancan matan abinda suka shuka suka gurba dai-daiwa dai-da."

     "Toh Allah yasa muyi kyakyawan karshe, rayuwar babu wata ma'ana da fa'ida, babu amfanin kayi abinda zai zame maka fitina a rayuwar ka, daga ni har kai mun ji jiki, da iyayen mu mata, Allah sarki Abbanah kashe shi tayi.

              Ko da hakkin shi ma ya ishe Mommy ganin Bala'i a rayuwarta. Gashi dai duniyar ta samu ya tafi a banza, ta tara ya watse bata ci ba, ya lalace. Ni da taso lalatawa gashi nice a rayen tare da zuri'ata.

     Ya Allah! make the Best of my life. The Last part.
And make my best deed last deed
  And My best day in which I mean"

"Amin Ya Allah,Amin Yumnah! Matar Tsoho da furfura."

  "Da gaske ka tsufa, toh bari naji Super J Dinka ko bazata yi aiki bane"

    Dariya muka yi baki, daya.

Rayuwa ba sauki, amma idan ka nemi sauki Ubangiji yana da sauki sosai.

   Salim dangin mahaifin shi na kawo shi, ganin mu ba laifi.

    Tako ina kome yayi daidai rayuwa baki dayanta hakuri ce.....

Alhamdulillah Nagode sosai a nan na kawo karshen Labarin Yumnah da Halwani...
Na fara rubutawa ranar 23/ July 2020/
Na gama 29/August/ 2020! Banda matsalolin da suka shigo da tuni na dire alkalamin.......

Allah ya had'a mu a karashin Kwarkwarah, Insha Allah...

Nagode sosai Mommys and Auntie's, na gode da bani kwarin gwiwa sosai, Ni kaina nasan bazan iya tafiya babu kune nagode 🤝 sosai Gaisuwa gareku Manyan MATA 😍🌹

Ku tanadi tissue da hanky..... Domin alkalamin kaddarar Jannart.....zai iya girgiza zukatan masoyanta....

#Mai_Dambujeeeee
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment