Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun kade har buzun su dan idan tafiyar karfe biyu ne, sai hudu zai fito, a haka ma wai dan ya gaya mata kenan.

Matar nan tasan sirrin saka miji a daki, shi yasa abokan shi suke gaya mishi ba zasu biyo mishi ba sai ya tambaye Babar shi.

Yan uwan shi kuwa sonta suke, sunyi sunyi ta auri kanin shi fir taki, tace. A'a, gashi basu haihu da Nura ba.
(🙄🤔🤭🙆🏻‍♀️Yanzun dan Allah matar da kuke son Baban su Halwani ya aura kenan! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Wannan mugun abun da me yayi kama! Duk kullunku ne😹🤣😜)

Tunda aka kawo kayan safiya, hankalin Mamie yashi, musamman da taji ana sanyawa Sarinah albarka, kamar tayi kuka, kallon kowa take as munafukin ta, dan haka ta kira Papa Tayi mishi wankin babban bargo, tace ya turo mata kayan fadar kishiyarta (😹🤣🙆🏻‍♀️🤦? Asha! Yau nayi typing har da dariya! This page make me laugh 😆🤣😂😁😝😛)

Haba me zai yi banda dariya, kamar zata yi kuka, haka tane jin shi bata ce kome ba.
"Toh nawa zai miki kayan?!"
Ya tambaye ta,
"20m!" Ta faɗa a masifance,
"Haba ranki shi dad'e, Kantun zaki saya baki daya, ina laifin 5m!"
"Ai dole kayi min haka ai, ba jikinka na rawa zaka ci sabon gindi ba, ai shikenan rike kudinka amma babu abinda 5m zai min kaje ka karawa ƙaruwar sojojin ka"

Wannan maganar ta bashi haushi amma dake ya manyanta, sai yayi murmushi yace.
"Kai wannan kalma gatsale! Ashirin yayi miki! Ai kema naki kullum sabuwa ce dal a leda, Turaina ai babu wata mace da zata shige min gaba tunda ina dake!"

Abinka da namiji take ya lallabata, ya turo mata kuɗin.
Babu godiya ba komai ta share batun shi.

Idan ta tuna labarin Safiya da aka bata, tana saka miji a daki, sai taji hankalinta ya kuma mik'ewa tsaye,(🤣😂😆😹 yau bani daya zan dara ba, har daku)

Wani irin bakin ciki ne, tasan halin mijinta jarababbe gindine, dan ma tana taka mishi birki an girma, amma tasan halinshi tsaf.

Dan haka ta shiga niman hanyar da zata kere safiya dan kar yazo ya wulakantata.

......
"Hello! Barakah shigo gidan!"
Inji Mamansu Khuwailah.
Shigowa matar tayi da alamu daga asibiti take.

Mushiga daga cikin. Ta fara mata bayanin.
"Kin san d'ab yau Kur'ani zamani, ban san taya aka yi ta sake suka yita mummunar alaka ba, tsorona daya kar yayi disvirgin ɗinta, dan na tambayeta tace babu abinda yayi mata.

But kuma suna kwana a guri ɗaya, ina son virginity dinta ya zama makamin da zan yaki Turai a ruwan sanyi ne!"

"Ok Aunty! Bari na shiga."
Abun tausayi, Khuwailah duk tayi wurijanjan, kamar am mata duka, sai share kwalla take, buga mata harara Mamanta tayi, sannan tace mata.
"Maza bude mata ta ga abinda zata iya gyara miki tunda baki san ciwon kanki ba, itama Dilshad dama nasan da ita, da ta gama barin wasu yan iska suka tsoma mata hannu a cikin gabanta.

Maza bude ko na miki shegen duka, har kin san ki zari jiki, kije gurin namiji ya kwana dake, maza bude min."
"Mama don Allah kiyi hakuri wallahi babu abinda ya tab'a min, ban barshi yayi min kome ba!"

Wata ƙatuwar harara ta buga mata sannan tafita.
"Wayyo Allah na, Aunty baraka ki rufe kofar wallahi bai min kome ba, kawai."

"Toh ya isa, hankalin Mamanki bazai kwanta bane sai ta tabbatar babu abinda ya sami gurin,"

Da sauri ta cire pant dinta, tare da kwanciya, a hankali Barakah ta haka wata yar karamar Torchlight, ta duba taga babu kome, a gurin sai kamshin miski da tayi amfani dashi. Dake Mamie tana saya musu, idan suna haila suyi amfani dashi.

"Aunty Uwani! Babu wani abin da ya sami gurin, wallahi."

Fita tayie tabar su, nan Aunty Baraka tayi mata nasiha, sosai kafin ta fita a dakin, tana ganin kiran shi kin dauka tayi gudun kar ya mata wani abu ta waya dan mamanta ta bata wuta.

Shima kamar dole, sai kiranta yake.
"Amma Aunty Wallahi ban ji dadin haka ba! Yarinyar tayi kankatane da wannan barazanar, wani kallon, da tayiwa Barakah nan tayi kasa da kanta, sannan tace.
"Kinsan sunar da Uwarshi takira min Y'a dashi karuwa fa! Idan na bar Turai ta cuce ni, sai na gyara yarinyar yadda zata gigita mata rayuwar D'anta."

Sosai Maman Khuwailah tayi shiri sosai, sannan ta kira wata Yar Yobe inda ta kai Khuwailah da Dilshad aka fara musu gyaran jiki na fitan hankali, domin kudi ta zubawa matar take gyara yaran.
......
---
Tsakanin Halwani da matar shi babu sauki dan burinta ta kashe shi, gashi ciwon bayan shi ya warke har ya koma bakin aikin shi a Japan,

Yanzun hankalin shi yana kan wani aiki da yake, duk wani kayan da ake bukata Sarinah yake bawa kudi ta saya musu shida Rahbeel.

Bashi da lokacin kanshi sai na aiki Allah sarki baby Yumnah, Yarinyar ta saba da Sarinah bata rikici, kuma bata da wata damu.

.....
Yau a gajiye ya dawo, tunda yaga Linah tana shige da fecce, jikin shi ya bashi wani mugun abu zata mishi dan haka ya shiga an karewa da ita, ina har ita farar hula tana basirar mishi ta'adanci, shi da yake jami'in tsaro ai dole ya gane abin harinta, dan haka kamar zai zauna a falon sai ya fasa. Ya koma dakin shi, can tazo tana buga mishi kofa.

Yana zuwa ya leka da wata yar kofa, kawai ya ganta rike da mai a frypan, murmushi yayi ya koma abinshi, ya zauna tare da kiran mahaifiyarta.

Bayan sun gaisa tace mishi.
"Ashe aure zaka yi, yaushe akayi bikinka da Kafaya!"

Dariya yayi sannan yace mata.
"Idan mace tana bawa namiji farin ciki, baya tab'a damuwa da matan layi ba.

Ma'am! Na kiraki ne a matsayin ki na Mahaifiyar kafaya na shaida miki zan saki Yarki, ciwon bayan da nayi nasan ta gaya miki itace ta watsa min ruwan zafi! Now zata kuma watsa min man gyada, toh wannan mai sauki ne!
Amma ina ganin ta dawo gida ta zauna. Idan na samu lokaci zan biyota da takardan sakinta, sabida"

"Ayi haka? Kayi hakuri kasan tana sonka shi yasa take kishinka, amma bazata dawo gida ba, me kake son yan jarida su faɗa akan mu, ga zab'e ya kusa, Please kayi hakuri don Allah na roke ka karka saketa."
.
"Bazan zauna da ita bane, bata gani na da kima, bata ganin duk na kusa dani da kima, taya bazan yi aure ba, na gaji sosai. Wata nawa ina kwance ba lafiya sabida ita about two months, Kawai taje idan naga zan iya zan dawo da ita idan bazan ita ba Allah ya hada kowa da rabon shi, bakanta farau ba."
Yana kai aya dan karta lallaba shi, ya kashe kiran duk wayoyin shi ya kashe yaki kunawa.

Kafaya na bakin kofa, rike da man da zata watsawa mishi, aka kirata tana dauka Uwarta ta rufe ta da fada, sosai sannan ta bar kofar dakin shi.

Wannan tashin hankali yayi yawa dan ta gayawa Mahaifiyarta, bazata fasa ba sai ya fasa auro Yumnah, shi kuma ya kira abokan aikin shi aka turo mishi maza, suka zo suka fita dashi bayan ya tattara kayan shi kaf, ya bar mata gidan ya koma gidan shi da ya sayawa Yumnah.

Bata nan kawai tana dawowa taga sako a bakin kofar.
_idan kin gama yunkurin kashe ni ki koma gida. Karki fara nima na_

Ihu da bala'i tayi shi tare da tsinewa Yumnah, tazo gidan Sarinah tayi mata wankin babban bargo ta koreta, bata hakura ba ta kuma zuwa tasa aka hanata shiga.

Ai kuwa ba shiri ta tattaro sai Gombe, bai damu ba tunda yasan karshen wata zai zai zo gombe.

Sun shirya kome shida Sarinah da kuma Rahbeel, dan haka ana saura sati daya, kawai suka hado kayan dasu kansu.

---
Ranar da suka isa aka kawo kayan na gani ina so da sadaki, nan aka kira ni, tare da tambaya na, na amince da kayan da aka kawo, idanuna cike da kwalla kaina a sunkuye nace.
"A'a kuyin hakuri! Ni bana son Uncle Halwani, Shima yayi hakuri da abinda m..."

"Tashi kije!"
Hardo yace min, ina tashi dake maza ne cikin natsuwa suka tattauna, sannan basu gaya musu abinda Mamie Tayi ba, Amma sun musu bayani akan abubuwan rayuwa da dai sauransu.

Haka suka dawo da kayan da ake kaiwa, babu shiri Uncle a ranar ya iso garin cikin dare, ya turo a kirani naki fita, tsabar damuwa a mota ya kwana, da asuba Hardo yaga motar shi, bayan sun fito suka gaisa, tare da tambayar shi yaushe yazo.

"Jiya nazo! Da dare!"

"Hmm! Baka yi sallama ka iso ba ko!"

Shiru yayi, bai bashi amsa ba, dan haka shima Hardo ya share shi dan yasan Jikanyar shi ce ta murda daga.

Wasa wasa kowa yasan da zuwan shi amma babu wanda yayi yunkurin mishi bayani, kawai an barshi dani ne.

Ni kuwa naki fitowa balle naga halin da yake ciki.

A wajen ya wuni, har dare Hardo Bai ce mishi cikanka ba, shima kuma bai yi fushi ba, sai da an damo mishi fura an kai mishi, nice dai naki zuwa.

.......
Bayan sallar isha yayiwa Hardo sallama, ya koma gombe.
Bayan tafiyar shi ina zaune a bayan dakin Yalwati ina kallon yadda dabbobi suke rayuwar su cikin farin ciki, ya zauna a kusa dani.

"Yumnatu! Kina kewar Amadu ko?!"
...kallon shi nayi fuskana dauke da murmushin takaici.
"Akan me zanyi kewar shi? Idan nayi haka mun ci sunan mu kwadayayyun kenan! Hardo. Idan naji kewar shi bani da daraja kenan!

Har abada bazai tab'a kambamani ba, gani na zai yi ina da saukin samu, koda zai same ni, sai ya wahala. Ya shiga yayi iri n rayuwar da kauyawa talakawa suke.

Ya fita yayi irin rayuwar hannu baka hannu kwarya, idan da hali ma, a kaina a dawo da al'adar mun ta shad'i, Idan yaga zai iya bismillah idan bai mishi ba babu dole babu wanda yayi mishi dole."

Murmushi dattijon yayi, yace wato.
"Kunje hura eso! Kunga anyi al'adar mu shine yabaki sha'awa, amma ai baki da wasu maneman! Sai shi?!"

Kallon inji waye? Nayi mishi. Sannan nace.
"Ai jiya dan ladi, na gidan liman yana cikin masu nima na, sai Yakubun Baffa dan Azumi. Kuma naga dukkan su mazaje ne"

Gyara zama yayi sannan yace.
"Idan suka cishi?!"

"Dama can Ni ba kaddarar shi bace! Amma indai ina cikin zanen kaddarar shi kamar yadda yake cewa, babu wanda zai same ni sai shi!"

Kina son shi kenan?!"
Murmushi nayi wanda yake nuna karfin hali na.
"Hardo! Ba wai bana so bane! So nake ya nunawa duniya ya wahala a gurin niman aurena! So nake ya nunawa kowa darajar da nake dashi a gurin shi, idan yayi min haka, Hardo zaka iya bashi nima sadaka!"

Kura min ido yayi, sannan ya mike tare da cewa.
"Tashi muje! Zamanki a irin nan babu dad'i, wani abu zai iya samunki bamu sani ba, dan idanun miyagu nakanki!"
Riko hannuna yayi ya kai ni dakin Mama ladi, ya tsaya tabani rubutun da yayi min d'azun nasha, sannan ya juya ya fita, ita kuma tasani nayi hayakin kaikayi .
. kwanciya nayi akan cinyarta, ina sauke ajiyar zuciya,
"Ki zama jaruma! Mai tsayawa akan kafarta, ki zama mai iya sarrafa kome karki yawaita zama cikin b'acin rai domin lokacin ake samun galaba akanka.

..idan ranki ya ɓaci ki zama kin nemi Alkur'ani a kusada ke, Insha Allah babu shaidanun da suka isa cutar miki, amma wunin yau ko abin baki ci ba, Yumnah, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace.
"Karku tsannanta k'iyayya, karku tsannanta Soyayya! Sabida kowane yana iya juyawa zuwa daya bangaren, son da kikewa Halwani tana iya cutar da Lafiyar da rayuwarki, don Allah a sassautawa zuciyarki bata da laifi sai na so!"

Nasiha mai haɗe da fata tayi min, sannan tasani nayi alola, sannan na kwanta, ita kuma ta cigaba da addu'a, har lokacin barci yayi.

---
Kanshi a saman cinyar Hajiya, idanun shi a lumshe, damuwa ce kawai tayi mishi yawa. Kalaman Hardo ce take dawo mishi.

_Malam Amadu! Kayi hakuri kaje kayiwa mahaifiyarka biyayya, itama Yumnatu zamu bata wani cikin y'ay'an mu, idan kuma akwai abinda ka kashe mata ka gaya mana, zamu biya ka, ga wannan ka kaiwa mahaifiyarka, sannan ka gaya mata inji Ni nace mutunci madara ce!_

Jin kalaman yake kamar an buga mishi duguma, bude ido yayi kan yan uwanshi da suke zagaye dashi, ya tashi ya jingina da kujeran da Hajiya ke zaune.

Kallon su yayi sannan yace.
"Mamie ta lalata min rayuwa! Ta lalata min kome nawa! Hajiya anya Mamie ce ta haife ni?!"

Shiru yayi bai kuma magana ba, amma yana cikin damuwa sosai.
Cike da tausayin shi, mik'ewa yayi ya haura sama, inda dakin shi yake, ya tsaya.

Haka kawai, yake jin a ranshi ina ma da Omar yana raye, yau yayi rashin amini bai san akwai ranar da zai zubda kwalla akan mutuwar Omar ba, sai yau, kallon yadda sanyin hunturu ke kadawa, yake.

"Broh! Kayi hakuri, nasan Mamie zata aikata abinda yafi haka"

"Sarinah har naje na dawo banji muryanta ba....
Paid before read.....
Sai maganin Gyaran na mata zaku iya tuntubana ta wannan Number! Idan Baki shirya ba karki min magana! Da Manyan mata nake abu na 08130269641

       ABU D'AYA.....muke so..
150 singul group! VIP 300 ta bank.Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga
        200 singul grp! VIP 400 katin MTN..
          Zaku iya tura shaidan biya ta wannan Number Zahran Addah Ramla +2347035133148 only Whatsp.
    
_ Idan kuma Alhubbih dayyia'n
Shima zaku iya biya ta Number! UmNass_
Acc No: 3051894647
Hajara Ahmad Hussain
Polaris Bank ga book din Alhubbi Dayyia'n zasu biya ta nan.... prize din iri daya ce, idan kuka biya ku tura shaidan ta gurin Zahrah+2347035133148
4️⃣3️⃣"Wallahi duk zaman da nayi da kwana ban saka Yumnah idanuna ba, ban san laifin da Mamie tai musu yakai haka ba sai da kakanta yake gaya min nayi hakuri nayiwa Mamie biyayya.

Daga nan na fahimci laifin mai girma ce, sai kudin da ya bani na bawa Mamie!, Tare da gaya min mutunci Madara ce!"

. kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta mai da idanunta, kasa ganin yadda Mamie ta shigo da farin ciki, tana tafiya tana murna, ta shiga babban falon gidan, da sauri ya juya tare da bari Sarinah,
Mamie na tsaye zata shige part dinsu, tana sauraron abinda Hajiya ke gaya mata.
"Me kika gayawa Iyayen Yumnah?"

Cikin rashin mutunci ta kalli Hajiya dakuma sauran mutanen da suke falon.

"Ce mata nayi indai iyayenta ba kwadayayyu bane, Kar ta aurar min d'a sannan dan na cireta daga rad'adi da zafin talauci na sayi soyayyar su da dubu dari biyu dan haka ina ga saura yar gidan Uwani itama haka zan mata gobe shegu kwadayayyun banza, kwadayayyun wofi."


"Garammmm!" Suka ji faduwar abu a bayan su, Sarinah tace.
"Yaya!!!" Da mugun karfi, kankace me gidan ya rufe, dole Rahbeel aka kira shi yazo ya duba shi tare da daura mishi ruwa.

"Hajiya don Allah kiyi wani abu! Wallahi damuwa tayiwa zuciyar shi yawa, shi yasa ya fadi jinin shi ya haura sosai,"

Shiru Hajiya tayi tana jin yadda kamen, har da wanda suke y'ay'an maza suna rokonta.

A jikin shi suka kwana. Kuma Hajiya ta haramtawa Mamie shigo mata Shashinta.
.washi gari.
Sammakon Hajiya tayi zuwa garin mu, ina kwance sabida zazzaɓin da yake damuna, ta shigo dakin.

Dakyar na tashi zaune ina gaishe,
Shafa kaina tayi tare da zuba min ido, kafin tace.
"Me yasa kika hana shi ganinki?!"

"Sabida iyaka tayi akan D'anta, kuma ta ambace ni da kwadayayya, ni da iyayena Hajiya it Uwa ce! Ni kuma matar da zai aura ce! Zai iya rabuwa dani, amma ita bazai rabu da ita ba. Kuma Hajiya ina ga kawai yayi hakuri inda gaske sona yake toh yayi min adalci, itace rokona dashi "

..abin gwanin tausayi duk yadda naso dakatar da kuka na, na kasa hayewa nake kawai, na kalli Hajiya da itama take kallona nace.
"Kin san Allah, Hajiya zan iya rayuwa dashi, amma bazan jure a wulakantani ko dangina akan shi ba! Duk da nasan bai da laifi ko daya amma ya san halin da mahaifiyar shi ta jefa shi ma rahama ce.

..hajiya ina son Uncle Halwani Sosai amma bazan iya daukar cin mutuncin ba, shi yasa na hakura da shi, tunda bashi ne autan maza ba"

Ina wannan maganar kuka nake sosai, itama shafa kaina take tana murmushi, sannan tace.
"Toh kiyi hakuri dan daraja na mana?!"
Kallonta nayi ina zubda wasu irin kwalla, sannan nace mata.
"Ki min adalci, a matsayin ki na kakar mu baki daya, yayi hakuri."

Mik'ewa tayi sannan tace "an miki adalci Insha Allah babu wanda zai kuma damunki da maganar halwani!"

Wani kukan ne ya taso min tana dariya tafito daga dakina da zata tafi aka kamo mata zazzaɓi da kaji, tare da Karyan man shanu, suka bata hakuri Baffa dan Azumi yace.
"Hajiya kuyi hakuri, Yumnatu yarinya ce. Kuma marainiya, bamu son muyi mata dole da zai saka tayi mana kallon dan ba mahaifinta bane, amma Insha Allah ni da Adam da kuma Jauro da harisu zamu lallabata, har ta amince,.idan kuma taki Allah ya gama kowa da rabon shi."

A haka tayi musu godiya sannan ta dawo gombe, ai kuwa yan koran Mamie suka shiga alakara tare da murnar an fasa auren shi da Yumnah, nan aka samu wata takira Kafaya ta gaya mata.

---
"Uwani kwaɗayin ki bai isa ki hakura ba, ai Kinga wacce tasan Darajar kanta da iyayen ta sun janye matakin aurawa dana kuma idan ba kwadayayyun ba, toh ahir din Yarki in ba haka ba zan wulakantata!"

Dariya Maman su Khuwailah ta saka gashi gidan an cika ana aikin biki. Kawayenta da Yan uwanta.
"Waye ya gaya miki ja da baya da rago yayi tsoro ne? Shirin aikata Alkhairi suke! Khuwailah da Yumnah kaman sun auri y'ay'anki kuwa.

Banda hauka da rashin kai, kina nan za a miki kishiya amma kina bin kan mutane da masifa, wallahi idan baki fita min daga gida ba zamu miki shegen duka."

"Ohooo! Yarki da ma ta gama karuwanci shine aka zo za a likawa yarona"

Fada sosai ya kaure, Khuwailah na Gidan gyaran jiki aka kirata aka gaya musu, babu shiri tazo taga yadda Mamie ke kora rashin mutunci, kiran Rahbeel tayi cikin damuwa da tashin hankali ya iso, yana shigowa yaga yadda ake dambarwa da Mamie.

"Kazo kayi waje da ita."
Takowa tayi gaban shi, tare da riko hannun shi har gaban Mamien. Wani irin takaici take ji, bakinta sai rawa yaƙe.

"Gashi nan! Ba dai Sharahbil bane? Ga d'anki nan! Amma yau bazaki bar gidan nan ba, sai ya biya ni matse ni da tsotse ni da yayi ko kuma wallahi na Bankad'a abinda baki sani ba akan Mah Naz da Mah Liqah."

Ta faɗa da mugun karfi sai da gidan ya dauka.
"Meye kika dauki Yaranki? Bugun aljanna ko? Mazan da suka fi dacewa da Y'ay'an masu kuɗi? Sune shafaffu da mai?"

"Hajiya kina abinda kika gadama, idan kin watsar da auren Yaranki toh ai bazaki iya watsar da na mijinki ba, Huwailah wuce daki, Allah ya kaso miki Manzon sauki Sharahbil, kuje babu kome Insha Allah biki yanzun haka fara, dan ta watsar da na Halwani sai take ganin zata iya wannan haukar.

Bata san cewa mu kaifi daya bane, Bama magana biyu. Zaki iya fita ranki shi dad'e Gimbiya"
Inji Baffa Nasir,

Cikin masifa ta juya gare shi zata fara yace mata.
"Wallahi yau ni na dakatar da Habu sake ki, Tunda yaji abinda kika yi akan Yar abokin Ahmad, Ni na hana ya sake ki, kuma kika Kuskura kika zage ni, tabbas wannan shine abinda zaki yi a tsakanin aurenku.
. Idan kina ganin karya ne, bismillah!"

Kwafa tayi tare da barin, gidan ita kuma Khuwailah ya tura aka kirata ita da Rahbeel, yayi musu nasiha tare da nuna musu bambanci halayyar shi da na sauran mutane wani bai tunzura shi ya fasa abinda yayi niyya, sannan suma sun je har garin su Yumnah, anyi magana da iyayenta sun fada musu gaskiya Mamie tace zata kashe Yumnah, kuma basu ga laifin su ba.

Dan sun san ita daya ce suka mallaka, tunda mahaifinta ita daya ya haifa, nasiha yayi musu mai shiga jiki.

Sannan ya bar gidan, dan dama matar shi Maman Sadeeq itace ta kira shi.

---
Kwanan Halwani biyu ya warware, basu sani ba ya dauki key mota daga shi sai kayan barci, sai garin mu.

Tunda yayi sallama, aka mishi iso zuwa dan wani daki a zauren gidan, ya zauna Hardo da kanshi ya shigo suka gaisa.
Sannan ya kalli Hardo.

"Nazo ne! Ka tausaya min,ka bani ita wallahi bazan tab'a zalintarta ba, kuma a duk lokacin da aka sami akasi, Insha Allah bazan juya mata baya ba, zan mata adalci iya karfina, Hardo bafa a gida daya zata zauna da Mahaifiyata ba, ba zata zauna a gida daya da kowa ba, daga ita sai ni, dan sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka min adalci ka bani ita, don Allah."

Yadda yake rokon Hardon duk sai yaji jikin shi yayi masifar sanyi, ga kaunar shi da yake da Yumnah, ga kuma amintar shi da Umaru. Mik'ewa yayi sannan yace.
"Ka kawo kuka inda ya dace! Bari na turo maka ita."

Ina kwance duk na gama hakura da zan kuma ganin shi Hardo ya d'aga labulen yace min.
"Bingel! Ki Kai min ruwa dakin zaure."
Dan yasan idan yace na kai mishi bazan fita ba, zuwa dakin matar shi nayi na amshi ruwan na kai dakin da sallama na shiga kamshin turaren Chor.

Yayi min maraba da zuwa ban ganshi ba, amma tabbas turaren shi ne, rufe kofar da aka yi yasani juyawa da sauri.
Sake ruwan nayi cike da mmki, nake kallon shi.


Sai zare idanun nake, tab'e baki

Please Login or Register in order to submit comment