Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Washi gari.
Tun asuba nake gyara gidan, ina aiki tana b'atawa har takai na mata magana tace min.
"Gidan mijina ne! Baki isa hanani abinda nayi niyya ba!"

Kallon ta nayi dan kamar da gayya ta fita ta dibo kasa, tazo ta watsa.

Cikin hauka, kasar ya shiga idanun Anuam, calla kara tayi kamar zanyi kuka ga shi ina aikin girki ne, nake gyara falona.

Dai-dai fitowar Abun kawai sai ganin maciji muka yi ya fito daga bayan Anum ya kasa Linah da mugun gudu. Nima tsabar na razana, daki na shige tare da rufe kofar, na bar yaran dan sakarci a waje.

"Dalla fita babu abinda zasu miki! Kofin su ce." Inji Wata murya yake fada min haka, ai ban san lokacin da na kuma fasa kuka ba.
"Amma Rabi'u baka kyauta ba, yadda kayi maganar zaka sumar min da Y'a yi shiru, dan uwanki ne babu abinda zai miki, ai tun fadawarki dajin nan idanun ki ya buɗe, amma idan kina so, za a rufe miki daga idon da kunnenki.

Amma bazaki ganmu ba, kawai sai dai mu bar miki sako."

"A'ah Ni kawai a rufe min yadda bazan ga wasu ba sai ku! Daga hakan ma ya ishe ni."

"Shikenan! Akwai kwali a cikin kayan kwalliyarki, ki saka baki da damuwa!"
Tace min, a hankali na fito, na karasa aikin, nan take bani shawaran na dauki yar aiki, ta taimaka min koda da sharar gidan ne.

Nace toh zan gaya mishi, idan ya dawo, sam na manta da batun Linah na kama yarana muka yi wanka na shirya su, dan suna yawo, sannan na basu abinci suka ci.

Kwanciya suka yi, karfe biyar na yammacin ranar ya iso, har sama na kai mishi brifcase d'inshi sannan na zo na taya shi cire takalmin shi, da safa,.

"Toh tsinaninya jikar matsafa, jinin karuwa, zaki koreta a gidan ta, sannu kwarkwasa, fidda me gida daga gidan shi, yar gaba da Fatiha, har kina turo mata da maciji zaki kash.......

#Mai_Dambujeeee
?. Kan uba, bata kai aya ba ta bugawa wata ihu, tare da tura kekenta suka hantsila.

    Wata ƙaton maciji, ne ta shigo ta kofar waje, kuma bai da kai,

  Keken Mamie yaje ya naɗe, sai da ya zubar da ita kasa.

                Abin dariya, haka macijin nan yayi ta bata wahala, koda na juya naga Uncle ya bar gurin, tunda ta fara zagina.

      Kwashe yarana nayi muka bar su a falon, suka ci-gaba da cin qaniyar su.

        Da sauri na ajiye su daki sannan nabi bayan shi, ina shiga na samu bai cire kome ba ya shiga ban daki, bin shi cikin ban dakin nayi, yana tsaye ya dafe bangon bayin, tare da lumshe idanunshi ruwa na zuba a kan shi.

    Zuwa nayi na, rungume shi ta baya.
"Kayi hakuri!"
Bai ce min uffan ba, na zaga ta gaban shi, ina kallon yadda idanun shi suka yi ja.

            A hankali na d'aga hannu na, tare da rungume, lasar labban shi na kasa na fara a hankali.

                   A hankali nake taune mishi ina hura mishi iskar bakina, rike wuyana tayi da hannun shi yana kallon fuskana.

    Sannan ya sanya harshen shi cikin bakina tare da lallubar harshena, tura mishi nai.

          Hmm, abin nima ya samu dama ya-ya lafiyar giwa balle tayi hauka, sai da yayi kamar zai cinye bakina, tun daga cikin ban ɗakin yake huce fushinsa akaina ban damu can ba, har muka dawo dakin.

     Dama jikina yayi laushi, ga gyaran da nayi, sosai ya shiga gurje ni. Ko nace muka shiga gurje juna, kamar ba gobe sannan muka fito, na shiga d'akina na shirya, tare da sakawa yarana wasu kayan sannan muka fito, na shimfid'a karamin capter.

               A hankali ya fara cin abincin yana bawa yaran shi, muna tattaunawa. Wayar shi ce tayi kara, zai dauka nayi maza na amshi  wayar na kashe.

"Lokacin mu ne, in da hali don Allah a dinga kashe wayar."

      Da wannan na tura mishi wayar shi, murmushi yayi sannan ya cigaba da cin abincin.

     Bayan mun gama, na shiga dakin shi na gyara mishi ko ina da ya b'ata, sannan na fito.

        ---
Alhamdulillah! Na samu dan nutsuwa da na fahimci mafi akasarin matsalata daga gare ni yake, sai gashi cikin ruwan sanyi na warware kashi sittin da tara.

                 Bayan wata biyu, Sarinah sun dawo gombe da mijinta, tana zuwa ta sake ni bana jin dadi aikuwa ta kwashi yaran dan nata yaran Uwar mijin ta ta kwashe su.

........ Dan haka na cigaba da kula da kaina, gashi wannan cikin ya hanani kome, haka Uncle zai yi kidar shi da rawan shi, hake ni yake son ranshin.

       .......
Al'amarin  Mommy kuwa shirin da take sai ta gama sai a lalata shi.
Karshe sau biyu Umma Zuljah, amma bata saurara ba.

    .....
Gidan mijina yanzun babu tashin hankali ko damuwa, sai ma soyayyar da muke zabgawa, me tsayawa a rai,
Ba gani ba, ba ga mijina ba, kowa ma kamar zamu cinye juna.

         A kullum idan Mamie da Linah suka taso zasu zo gidan mu, sai macijin nan ya hanasu shiga, dan dole suke komawa.

  ......muna cikin wannan yanayin Dilshad ta haihu, bayan taci uban azaba a hannun Zein, kafin ya rakota da zungurerriyar saki.

          Mun tausaya mata. A lokacin Aunty Safiyyah ta kuma Haihuwa na biyu, dukka maza Mamie sai da ta nuna b'acin ran ta,

     Hada sunan aka yi, tare da na Dilshad, Uncle yakira Zein yaki zuwa sai da ya tura mishi wani sako, cikin kwana goma sai gashi.
          Kebewa suka yi dashi.
"Allah ya baka duniya sannan ya kuma baka damar ka zuba rashin mutuncinka son ranka, amma baka san karshen rayuwar zata zo maka ba.

             Na san dole zaka wulakanta Dilshad, tunda ba sonta kake ba, na baka dama na karshe ka sauya ki kuma na dauki matakin karshe akanka, babu wanda yasan kaine kazab, ba.

   Amma Ni na san kai ne, don Allah domin Asood, ka ajiye abinda kake aikatawa, idan ba haka ba. Zaka iya tafiya."

Daga haka Uncle ya nuna mishi hanya ya fita.

   Bayan wasu watannin lokacin cikina yana da wata biyar, aka ce mana yayi hatsari jirgin sama, bayan ya tattaro dukiyar shi ya mallakawa Asood, dangin shi sun zo daga Saudiya, a basu yaron Uncle ya hana.

     A lokacin na bashi labarin Salim dan gidan Mah Liqah, ai babu shiri ya hada mana kayan mu sai Argentina, mun so fuskarta matsala, amma ya shiga ya fita, sai gamu a gidan Marayu.

      Muna shiga muka nufi Ofishin shugaban gidan Marayun.

        Muka mishi bayani tare da bashi takardun shaida yaron. A hankali ya ciro mana takardun yaron, sannan ya kira waya muna zaune aka shigo da yaron, wanda kana ganin shi kaga Balaraben Yemen, nuna mishi mu aka yi, sannan aka ce mishi.

"Ga Mamarka nan da Uncle Dinka!"

    Kallona yayi, hawaye na zuba daga idanuna, na bude Mishi hannuna a hankali ya shigo cikin jikina.

Wani kuka ne ya zo min, tare da k'amk'ame shi a jikina, tare da jin haushin Mamie yau tambarin da ta kirani dashi, gashi ya tabbata akan yarta.

Haka Uncle ya cike  wasu takardun sanan muka fita daga gidan, kwanan mu biyu a garin, bayan mun Mishi sayayyan kayan sawa muka dauki hanyar gida, tun a  jirgi nake tsara abinda zan gayawa mutane.

Ashe yallabai kan ya gama shirya kome, dan ya gaji da halin Mahaifiyarshi.

Muna isa gida da kwana biyu, ya dauki yaron bayan Yasaka anyi shelar general meeting.

      Inda aka hadu, bayan dogon bayani da yayi, sannan ya kirani yace na kawo Mishi yaron.
Ina shiga da yaron aka zuba.

Mik'ewa Mah naz tayi cikin kuka tace.
"Shine! Salim din Mah Liqah, dalilin cikin shi, muka yi sanadin da aka fasa auren mu.

   Tun lokacin da aka tura mu karatu, wallahi bamu da wata manufar lalata tarbiyyar mu, Mamie itace mutum na farko da tace mana.
"Kuna da kyau, kuyi amfani dashi ku nemi kudade a hannun maza, kuna da jiki mai Kyau shima jari ne.

          Tun daga ranar muka zama kamar wasu gwanjo wannan ya dauka ya ajiye wannan ya dauka ya dire, Mah liqah ta haɗu da Yarima Muizzidin, tun da suka haɗu ya hanata kula kowa.

   Dashi suke mu'amalar, har zuwa lokacin da ya gama abinda ya kawo shi ya tafi, daga nan ta fara ciwo, muna zuwa asibiti akace ciki ne da ita, mun yi iya yinmu cikin ya zube amma yaki fita.
.haka tayi ta zaman gida har ta haihu, daga nan muka dauka zuwa kasar Argentina, muka ajiye shi a gidan Marayu.

      Wallahi tana son Yaron dan itace tayi mishi huduba, kawai tana tsoron Papa ya ganta da cikin shege, lokacin da muka ji labarin abinda Kikewa Yumnah, sai mu zauna muyi ta kuka, kece kika lalata mu, kuma kina goranta mana, Papa don Allah ka yafe mana."

    Abun tausayi da jajjantawa, ashe bani kadai nake da ciwon muguwar Uwa ba, har dasu ma.

.....haka suka yi ta bani hakuri,  har muka tashi taron, tun a hanyar dawowa gida ya ce min.
"Thank You make feel Happiness."

          "Kwarin gwiwar daga gare ka na samu, dan haka babu batun godiya."

         Muna isa gidan, muka ci karo da Mommy, bayan shi na koma, cikin kuka da tashin hankali take rokon na yafe mata, raba gefen mijina nayi tare da shigewa gidan a guje.

Na manta cikin jikina, dan Bala'in tsoronta nake ji.

Tun daga ranar ta mai damin gida gurin zuwanta, kamar da wasa wai tana niman yafiyana,

Naki sauraronta haka tayi ta hadani da mutane ana zuwa ana min nasiha, ko a tare Uncle karshe ranar da aka tunzura shi yazo ya balbale ni da masifa shi na daina sawa ana mishi nasiha, haka yake hakuri da halin Uwar shi, nima na koya daga gare shi.

Banza nayi dashi, sabida wallahi bana jin Alkhairi a dawowar Mommy, haka suka zo har dasu Mamie, wai sunzo bani hakuri tunda na kwashi yarana na shige daki dasu ban kuma fitowa ba.

Har suka bar gidan, sai da Hajiya ta kirani tayi min nasiha, sannan na kula Mommy, shima sama-sama, bana tab'a barin ta ta taba min Yarana, ko sakewa da ita, kullum tazo ina baya baya da ita.

Gashi Umma Zuljah bata nan dan tace min zasu koma Nahiyar su, sai bayan na haihu zata dawo.

Dan haka nake baya baya da, ita, haka zata yo min sayayyar kayan lambu da abin kwaɗayi, tana kawowa zan yi mata godiya sannan zankira me aikina ta kai dakinta.

Tana tafiya zan ce ta kai bola, bawai dan ban yarda da Allah bane, kawai kiyayyewa ce.

Dan haka sosai na nutsu ina gasawa Linah aya a hannun. Dan bata dawo ba, amma idan muka hada a wasu abubuwan, tana gaya min magana zai rama, kuma na gaya mata naci dubu sai ceto.

.... Dan haka basu saduda ba, ita da Mamie suka shiga niman yadda zasu kawar dani su huta da fitinar da nake musu.

Duk inda suka je, abu daya ake gaya musu bazata mutu ba, sai dai ku idan kuka matsa. Dan haka Linah sai ta gayawa Mamie ta hakura, amma a bani hakuri na ta koma d'akin ta.

Nace tunda bani na koreta ba, zata nemi wani abu ai shirmen banza.

Haka ta dawo, tunda ta dawo na fahimci akwai abinda take nima, a dakin Uncle, tun ina basarwa har wata rana na kamata tana kokarin duba password din laptop dinshi, na shiga na rufe zata min magana na nuna mata hanya, dole ta fita tun daga nan kuma nima nasaka ido akanshi.

Ganin bazata dauki mataki akai na ba, sai ta koma gurin bokarta ya bata wani magani yazo ta saka mishi a cikin abun shan sa, zai mutu.

Ina kitchen abin mamaki sai ga macijin nan yayi gamo tare da tsare min hanya, cikin tsoro nace mishi.
"Don Allah karka cutar da ni, ka koma inda ka fito wallahi bazan saka a cutar da kai ba."

Warwarewa yayi ya fara haurawa step, sai ya juya ya kalle ni, sannan ya kuma haurawa. Sai ya kuma juyawa ya kalle ni, tsoron shi ya hanani fahimtar kome, can ya sake haurawa, kawai sai ya fasa kanshi, tare da sake harshen shi a kasa, kamar wacce aka bani umarnin na bishi, haka nayi ta bin bayan shi har zuwa dakin Uncle, yana shiga ya isa gaban friji din shi, ya saka kanshi a jikin hannun frij din.

Ya buɗe, kawai sai ga kome na ciki ya koma wani irin bakin ruwa, haka yayi ta saka bakin shine yana watsi da kome, cikin fusata, ya kama Bin bango yafita daga dakin, haka na kwashe kayan na zubar a waje, ina fita ko kitchen ban koma ba, na zube a kasar d'akina zazzaɓi ya rufe ni.

.... Dakyar barci ya dauke ni.
Shafa min kaina take, a hankali tana murmushi, tace.
"Ai gidan kun tsohon makabarta ne, kuma mijinki yayi ginin gidan a kusada gidan wani malamin mu, amma ya jima da barin gurin, tun bayan sayar da filayen, toh akwai wani jinsin aljanun da yafito daga can ƙasar sin, su siffar su na macizai ne.

Ba kamar mu da muke da dan kaho a gefe da gefen kan mu ba, iya haka kawai gare mu, amma kome namu na mutane ne,

Kuma mu cika fitar dashi ba, gaskiya, sai ya zama mun koma halittar mu.

Shi wannan sunan shuraihu, yana cikin gidan nan kafin a gine gidan, an dan sami matsala dashi, domin shima baya son zalinci, toh yaron shi Babba ya sari daya daga cikin masu aikin, suka bi shi suka kashe shi, koda suka kai mutumin da yaron shuraihu ya cika zuwa asibitin ya rasu.

Toh gaskiya ran kowa ni bangaren ya b'aci, domin Shuraihu ya tafi dan daukar fansa yaji labarin ai dan shi ne ya fara cizon marigayi dan tun farko sun so barin shi ya bar gurin. Har ya tafi ya dawo, ya ciji me kwasar block din.

Shine ya dawo, ya sami yaran yayi ta musu fada akan me basu gaya mishi gaskiya ba, da ya kuma Kuskuren da Armand yayi, dan haka ya hana yaran shi fita, har aka ce za a sare bishiyar da yake. Ciki da yaran shi da matan shi.

Toh kasancewar, ya san Halwani shine yaje yayi ta zuwa mishi a mafarki tare da Kawata mishi lambun can, dan kar a sare bishiyar, abar shi zai zamewa gurin abin kyau da ƙawa.

Tunda ya ga haka a mafarkin shi, shine yasa Ka bar itace, sanan aka gyara gurin ya gyara tsaf ya koma koma lambu, shima kuma ya hana ya ranshi fita idanun mutane.

Tun daga ranar da aka kawo ki, suka shigo taron mutanen kin tuna matar da yazo da yaranta mata guda biyu, har kike ce musu, ko zasu kwana ne mamar tace miki a'a, zasu tafi basu da nisa, ai sune.

Lokacin da aka cire miki Faruq, ai sun zo asibiti ko?"

Nan mamaki ya kamani, sannan take gaya min ai sabida Kafaya ta zuba guda ne a jikin kayan cikin firij din yasa, yazo ya fara zubda kome na cikin frij din.

......._Washa sunar wata😜🙆🏻‍♀?
#Mai_Dambu...
9/2/20, 12:22 PM - Ummi Tandama: ⁷⁰.Dan haka na kiyayye bani kadai bace a gidan, gudun kar ayi abinda zasu rab'e yarana.

   Sannan ta kuma karamin da cewa, nasaka ido duk wanda ya biyo ni da Sharri kanshi yake komawa, Insha Allah.

        Addu'a ta tofa min aruwa nasha, daga nan kuma tayi tafiyarta.

       ..... Bayan awa biyu naji ihu, tare da faduwar abu, da sauri na mike, har sai da bayana ya amsa, ma fito falon.

      Kafaya ce ke ihu, tare da niman ceto, riketa nayi cikin mamaki nace.
"Lafiya?!"

Jikinta na keerrma ta nuna min macijin nan, girgiza kai nai sannan nace mata.
"Me kika aikata yake binki? Haka kawai bazai ji a ranshi zai cutar dake ba!"

    "Wallahi ban yi mishi kome ba, na..."
"Kinyi mana! Idan baki fada ba taya zan dakatar dashi? Meye kika aikata?"

     .... Cikin mugun tsoro da ganin yana saukowa ta shiga fadar abinda tayi, zama nayi a kujera. Ina kallonta, juyawa yayi tare da barin gidan baki d'aya, itama kuma ta kalle ni sannan tace.
"Wato kin yi nasarar sani ma fasa abinda ke raina! Hmm! Am sorry."

       Kawai ta kai min duka a cikina, wani irin abu ne ya dira a kirjina, lokaci guda ruwa me zafi ya shaga zuba min da mugun gudu.
  Zufa ne ya fara karyo min.

   Ina kallon ta, ba ita nake kallo ba yadda macijin ya biyo bango, ya yana fakonta.

   "A'a karki kuma! Karki kuma Linah! Karki kuma!"
Yadda ta d'aga kafarta zata naushe ni, kawai sai ganinta nayi ta tashi sama, daga nan ban kuma sanin abinda ya faru ba.

      Sai bayan awa biyar, na farka naji an rike min hannuna, idanun shi yayi jajjur.

        "Sannun! Kin auna arziki, an cire yaron ba rai. Allah ya bi miki hakkin ki, sannu kinji!" Inji Hajiya.
          "Linah fa?!"
"Ke gafara can! Tana can ta haɗu da gamonta, duk me shirin aikata miki mugun nufinsa zai koma kanshi."

     Uncle bai iya magana ba, sai kallona yake, ya kasa magana.

        Lumshe idanuna nayi, tare da rike hannun shi sosai..
"Am sorry!"
.da sauri na bude idanuna, murmushi ne ya kwace min, nace.
"Da aka yi me?"
"Da ceton rayuwata!"
"Yaushe? A ina kuma?!"
"A koda yaushe!"
"Ai toh!"
"Nagode sosai!"
"A nawa?"
Murmushi ya sauke, tare da sumbatar goshina, yace.
"Dai-dai da kyautar faro!"

Lumshe idanuna nayi, tare da kawar da kaina, dan na fahimci abinda yake nufi.

           A hankali lafiya ya fara samu, sunki gaya min abinda ya faru da Linah Uncle ma idan na tambaye shi, b'ata rai yake, sai na daina. Kwana na uku Mommy tazo, Kawai daga shigowar ta naga Sharrin da ta kwaso, kafin ta zauna nace mata.
"Kije nagode karki ajiye min abinda kika kawo"

        Hankalinta ya tashi, ainun tare da zuba min ido, ganin yadda suka yi zuru-zuru, ina hararar ta, ya sata fita daga dakin.

    Ranta a b'ace dole ta kawo karshen Yumnah, a hanyar wucewa gidan ta haɗu da wata mata, an kawota cikin asibitin sai ihu take tana yagar gabanta, tare da fallasa abinda ta aikata.

        Dakyar ta gane matar Hajiya Zakiyah, tab'e baki tayi sannan ta ta wuce.

          Kwana biyu tsakani aka sallame ni, mun zo zamu fita na hango wata kamar na santa, can na kuma kallonta, Ummi.

Kallon Hajiya nayi, sannan na gaya mata, nasan Wancan mata,.kiranta tayi tazo tana gani na tace.
"Yumnah!?"

Sai kuma ta fashe da kuka, tana dariya tace.
"Alhamdulillah! Kullum nayi sallah sai na roki Allah ya saka kin kubuta, sannu. Baki da lafiya n?!"

Murmushi nayi na kalli kayan jikinta, abin tausayi.
"Shigo Mu tafi sai na baki labarin abinda ya faru."

Girgiza kai tayi sannan ta sunkuyar da kanta, tace.
"Bazan iya binki ba! Ina jinyar mijin Mahaifiyata ne da na gefa shi cikin damuwa, idan na sami lokaci zan zo, yanzun ma naje niman kudin magani ne ban samu ba, zan basu hakuri zuwa gobe! Yumnah rayuwa tayi tsada, kowa kaje niman taimako sai ya nemi sauke gajiyar shi a tare da kai.

         Insha Allah zan zo."

      Cikin tausayi nace.
"Toh muje gidan mana, sai na baki kudin magani, kece kika ce min nayi Kuskure komawa gidan Mommy! Tare da gaya min gaskiya akan abinda ta shirya min, dan haka meye amfanin bad'i ba rai, muje."

    Haka ta yarda ta biyo mu, ina bawa Hajiya labarin taimakon da tayi min,
 
Tun daga bakin get ta sake Baki, tana kallon gidan har muka shiga cikin gidan, dake gidan su Hajiya muka wuce, Uncle yaki magana, dan haushin mu yake ji nida hajiya.

Bayan an kawo mata abinci taci, sannan na turawa Uncle sako, harara na yayi, ya fita bayan minti arba'in ya dawo tare da mika min ledar na mika mata, tare da cewa.

"Gashi don Allah kiyi hakuri, sannan idan an kwana biyu zamu zo, mu duba shi."

    Kasa magana tayi tana share kwalla, tayi ta godiya, sannan ta tafi

.....hmm a wannan yanayin ina zan yarda ya kai ni gidan shi, dole sai gidan hajiya, domin balle ɗinkin zai yi na mutu, shine abin da ya bashi haushi wai mun hade mishi baki, dan haka shima ya dawo gidan Hajiya da zama sai an sallame mu tare.

    Hajiya tayi mishi fata-fata, muna shiga naga Hajiya Mamie, zaune tana bawa Anum Abinci a baki, Anuam tana hannun Sarinah, tana bata.

           ..... Al'amarin Mamie ya fara bani tsoro, dan ko shekaranjiya da tazo kuka take, tana tsinewa Linah, sunki gaya min meye ya faru bayan na suma,  sai da na samu guri na zauna, Mamie tace.
"Sannu!  Allah ya saka miki, Kinga rayuwa, wancan tsinaniyar Yarinyar Allah ya kwashe mata albarka."

        Nan ta kuma fashewa da kuka, tana bani Hakuri, nace ba komai.

......
Yaran sun koma hannunta, har da Faruq, Ni kuma Hajiya tana bani kulawa, ana cikin haka Aunty Taslimah ta koma gidan mijinta,

    Kwana na biyu Hajiya ke Bani labarin abinda ya faru.

Wato tunda macijin nan ya maketa da bindinshi, bai mata kome ba, sai watsa mata ruwan bakin shi a fusakarta, daga nan ta fara ihu, da niman taimako, tare da fadar abinda take shirin aikatawa.

      A wannan halin Uncle yazo ya same mu, shine ya kawo ni asibiti itama aka kawo ta, daga nan ya kira iyayenta suka yi gaba da ita, tare da gaya musu gaskiya shi fa ya jima da saketa,dan haka dama babu wani batun aure a tsakanin su...
            ...... Sai da na sami wata uku me kyau sannan na bar gidan Hajiya, muka koma gidan mu me cike da abubuwan.

        ........
A hankali muka shimfida rayuwar mu cikin amincin Allah, ina cika shekara daya da min aiki ya sani a makarantar. Na zana waec, dakyar ya barni nayi jarabawar, da katon sharad'i, bayan na gama ya kuma cika min jamb.

  Dariya nayi nace mishi.
"Wallahi zan fad'i!"
"Allah ya baki sa'a kika Kuskura sai na baki mamaki."

    Alhamdulillah, nayi jarabawar lafiya kuma sakamakon ya fito mai kyau.

       ..... Yau Faruq bai jin dadi dan haka na nufi asibiti, dashi kawai ina gaban likita Ina mkshi bayani sako ya shigo min, ina dubawa naga ance min.

_Idan kin isa ki dakatar da ni daga mijinki!_

       Ko takan likitan ban iya bi ba, na sabi faruq a kafada na. Muka fito da sauri.

             Motar da ya bani nake ja, dan karfi da yaji

Please Login or Register in order to submit comment