Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan da Haihuwa,kuma a nan gidan Hajiya take jego dan anan za ayi suna, sabida kishiyarta ma arufah tace zata kashe su.

Shi yasa aka dawo da ita, sannan duk wannan hidimar Mamie bata tako duba su ba, dan ta tace babu ruwan ta dasu.

.... Dan haka muka shiga hidimar suna, dan ma laulayi na damuna. Uncle kuwa ban kuma saka shi a ido ba, sai washi gari da yamma. Muna zaune ana min lalle, ja a yatsuna ya keta dandazon matan cikin familyn su, ya shigo dakin da yake cike da yan matan Danginsu, suna ganin shi suka fara wani iyayi da yauki.

Raina b'aci yayi ban san lokacin da sunkuyar da kaina ba, Musamman yadda suke gaishe shi, cikin iyayi da rawan kai.

Sanssanyar turaren shi ne, ya daki hancina, d'ago kaina nayi..muka yi karo dashi, dafe gurin nayi cikin jin haushi.

Narke min fuska yayi tare da hade goshin mu.
"Ko ko nime ni? Kika manta dani!"
Murmushi nayi tare da kawwar da kaina, ina kallon lallen da take zana min a yatsun hannuna.
Kallon yatsun yayi, sanan yacewa.
" me lallen nawa aka biya ki?!"

Kallona tayi sannan tace.
"Basu biya ba tukun!"

"Toh kuwa na biya miki! Umra sabida wannan tsanen yayi min kyau, kuma koda ya goge zaki na zuwa kina zana mata, yan tsirarun yatsunta."

Ware idanun nayi tare da tura baki nace.
"Wannan yabo ne ko zagi?!"

Zama yayi, tare da tankwashi kafar shi, yace.
"Ai kece mijin, Ni kuma matar! Ina gaya miki, yanzun kika ce min ayi girki sai naje na daura zani na fada kitchen."

"Wato goge laifinka kake son yi? Ba laifi bane dan ka kebe da mutanen da ka jima baka gani ba, amma kuskure ne ka manta da wacce take dauke da ajiyar ka, bar nan. Bani zakawa siyasa ba fita kafin na harba ma rashin kirki"
Na gaya mishi tare da zabga mishi harara.

Wani irin duba yake min, ban tab'a ganin wannan salon, ba domin rike kwalar rigarshi yayi, yana wasa da yatsun hannun shi, kanshi a sunkuye.

Zaro ido nayi cikin takaici, nace.
"Fitar min anan, bazaka guma min takaici ba, Uncle wai Ni kaje jin kunya ko yan dakin?!"

Fashewa da dariya duk suka yi, ya wani kamo hannuna yana fadin.
"Don Allah kiyi hakuri! Idan na kuma ki min horo a gaban mutane, kai idan na kuma na yarda kice min underwear dinki zan amsa amma banda fushin nan dan zai iya jawo yakin duniya.

Dan yanzun haka row sun...."

"Kam Bala'i wallahi basu isa ba, sai ma musu rashin mutunci,"

Mik'ewa nayi, ya riko ni, kamar da gaske, hango zobe nan nayi, a hankali na janye jikina tare da jin son zoben yayi min kyau.

Haka dai na koma na zauna, ina kallon zoben ana zana min lallen, tare da min hira musamman shi, din.

Sosai na maida hankali guri gudun kar wani ya dauka, koda aka gama min, ana yiwa wasu Ni kuma ina gefe Uncle ya fita, sai dariya suke min wai daga ni har shi, mun iya love drama. Ban ji kome ba burina lallena ya bushe dan har tafin kafana aka zana min, kamar ance min d'ago kanki, sakamakon ganin wata a kusa da gurin tsaye, kafin na d'ago har ta fita,.ina dubawa naga babu zoben.

Raina ya b'aci, amma na share meye najin ba dad'i.. amma wunin ranar naji shi babu dadi, har na cire lallen na wanke kafana da hannuna, ina fitowa.

Aka kawo min abinci, zama nayi ina bawa annur, a hankali ina rayawar cewa ina zanga zoben nan ne.

Wallahi ya shiga raina, mugun son zoben nake, Kawai sai naga zoben hannuna bai min yadda nake son wancan ba, kawai na cire shi na saka a jakar kayana.

Tunda aka gama lallen, ya ishe ni da aike dan haka nayi wanka tare da shiryawa cikin long sleeve floral gown, ash colour.

Turarukan Mai jego na shafa, sannan na gyara fuskana. Na yafe farin veil, na fito a hankali.

Falon da yan uwansu, suna gani na, suka saka shewa tare da tsokanata murmushi kawai nayi, tare da barin falon, ina fita na same shi a wata sabuwar Rover, maroon kafar shi daya a waje, yana dan daga ta tare da kad'ata.

Kallon wayar da Hajiya ta bani, d'azun nayi na duba naga akwai katin dari biyar a cikin shi, a hankali na tura mishi.
"Hi! Dan saurayi mijin yan mata kalle ni"

D'ago kanshi yayi cikin ranshi yana ƙara tasbihi ga Ubangiji tare da salatin taslima ga fiyayyen halitta Annabin Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, tare da Sahabban shi har zuwa ga ahlul baiti.

A hankali nake takowa, har zuwa gaban shi, na dan bude motar ta inda yake zaune. Cike da niman magana ya fara magana a waya.

"Don Allah baby karki Kashe kirana, kin san yadda nake jinki kuwa, toh kiyi hakuri bazan kuma ba."

Ware idanuna nayi tare da zabga mishi harara, nace.
"Wato ka kirani ne dan ka rena min hankali, shine zaka kira wata banza kana gaya min karta kashe kiranka. Bani wayar ko na zabga maka ihu yadda kowa zai fito yaga irin abinda kake min."

Mika min yayi tare da murmushi, na saka a kunne na, na fara da manyan jakar tsabar rashin mutunci.

Har ina kiranta kwartuwa, sai da na gama bala'i na bata amsa ba, can kawai tace min.
"Happy birthday Yumnah!"

Sake baki nayi, tare da cewa.
"Aunty Sarinah! Am..! Toh ai shi ne bai gaya min cewa kece a..a ..a layin ba, nagode sosai!"

Ma kashe wayar tare da take mishi kafar ci, cikin jin haushi. Dariya yayi sannan ya ce min.
"Kika taka min kafa sabida kawai naje yarinyar tace min bata yina.

Wallahi kika kuskura kika ja min bakin jinin yan mata bazan yarda ba, haka kawai. Zaki ja a daina yayi na, saurayi kamana"

Haushi ya bani naki magana, har muka isa gidan shi dake bayan layin gidan su Hajiya.

Har zamu shiga gidan ya kuma juyar da motar shi muka fita yawo, bude data nayi a hankali nake kallon kome na wayar wai sai na sabunta shi.
A hankali nayi Updating kome, sannan na fara duba Whatsp dina.

Wani group na ganni a cikin shi, Yan matan auren family members ɗin su suka bude, a hankali naga har Group uku daya na novel, daya kuma na irin nasiha da fadakarwa.

Sai daya Group din na tattaunawa ne a familyn baki daya manya da yara yan mata fa irin mu.

Ban tab'a karanta novel ba, gwara irin na larabawa haka, lokacin zuwana riyadh na fara, kawai wata mata tayi posting books da yawa, har naji Khuwailah tana tambayar.

Wani book wai tafi gabaruwa jima!, An kawo mata wani tace bashi ba wanda kungiyar hazaka tayi wato Beauty, Ummin Yusrah, Zeetty.

Ana bat naji tana cewa.
_Don Allah ku kara min da Bahaushiyah_
Dariya matar tayi, tare da cewa.
_Yasin kina ruwa! Toh me book din ta saka password! Amma gashi nan_

_🙆🏻‍♀️? Don Allah fa! Toh ku nima min Number ta! Ina son book din!_

_🤣🤣🤣 Kai Mrs Rahbeel! Kina jegon ma! Ba Zaki huta ba! Sai dai na baki Number Zahran Dan Naga ta gurinta ake biyan kudin Novel dinta._

_Toh kafin nan babu wani Novel dinta ne? Naji Yayata da take aure A Qatar ta bani labarin Wai matar So! Don Allah anyi soyayya a cikin shi, dan wallahi bana iya karanta book babu romance, Dan kin san ni yar soyayya ce._

_Toh naji gaskiya ana cewa yayi! Amma ga wannan book ɗinta da ciwo a rayuwata, ga kuma Yar gidan Yadiko_


_🤔🙄🙄Ke Maman Sadeeq! Nifa b kowani shirmen labari nake karantawa ba, bar min matar so din! Na sayi Bahaushiyah!_

Kamar zan mata magana sai na fasa zan rufe datar kawai naga wata tace.
_Maman Sadeeq Allah yayi miki albarka! Kamar kin san ina niman wadannan books din! Musamman Yar gidan Ya mayyer! Da kuma da ciwo a rayuwata, Hamma Sadeeq da Addah Amrah_

Wani stickers Khuwailah ta turo tare da lasar alewa tana fadin.
_Oho dai, bazan karanta su ba!_

Dariya matar tayi sannan tace.
_Dadi ya wuce ki, tunda bazaki ji labarin yadda ake rawan tankwal! Tare da akuyoyi ba, suna rawa suna kad'a bindin su._

_🤔🙆🏻‍♀️😲? Kai Haba! Kice akwai abin dariya da al'ajabi, na fasa matar so, bari na karanta wannan yar yadikon!_

Buɗe matar so nayi, a hankali na fara duba su, amma sabida sunyi kanana, ban iya karantawa ba na rufe Doc din, na zuba mishi ido.....
#Mai_Dambujeeeeeeeee
8/30/20, 9:41 PM - Ummi Tandama: ¹. Mai da hankalin shi yayi kan motar shi, da yake ja. Magana nake son yi Amma na rasa yadda zan mishi kawai dai na share batun tunda bamu jima da dawowa ba.

Kuma hankalin mu Bawai yana guri guda bane. Tunda ya isa inda za shi ya tsaya a gefen wani katin sannan ya sauke min glass din Motar tare da cewa.
"Naga kina hamma kar na fito na samu kinyi barci jirani."

"Toh, ga kasa nan ko? A fito lafiya!"
Nace mishi. Yana tafiya na bude datar wayana, ina kallon hirar da ake a group ya min dadi, amma bana jin nayi magana.

_Jama'a don Allah ku nimo min Inuwar Gajimare! Mana, sai kayi ta magana babu me kula ka_

Babu wanda ya tanka mata, ina kallon su,
_Don Allah! Ku bani novel masu zafi dan Allah wanda zan karanta nasan na karanta book, wanda ake cin Pussy kanar hauka, Kun gane_

_Toh ki nime bariki na fito mana, ko gidan Uncle, da adandi._

_Kai Ni bazan karanta su ba, kawai ku nima min wanda zan karanta naji dad'i sosai!_

_Toh ai kin ajiye mune sabida novel! Ki duba masarautar Jordan! Ko da ciwo a rayuwata! And naji kamar ana cewa akwai wani Book din da Marubuciyar zata yi karshen shekarar nan bayan ta gama HABEESHAH!_

Lashe baki matar tayi irin taji dadin nan
_😋😋 Don Allah! Wane kenan? Yaushe December! Gaskiya mai_Dambu ta karo wulakancin! Don Allah ya sunan Novel din?!"

_Eh toh nima a wani group nagani na Maryan Jumare! Wai amma cigaba Kwarkwarah ne! Dan naji shima ta kusan gamawa, tunda Kinga tasaka A gurguje!_

_🙄🤔😲 Ni wallahi na tsani haka! Kiji fa cigaban Kwarkwarah ne ma, toh don Allah ya suna Novel din? Dan na kagu tafara, Kwarkwarah ma Dan dai bamu da zuciya ne da mun ajiye mata labarinta, sau uku ina saka ran kome zai dai-daita tsakanin Kawu da Jannart sai naji shiru! Da alamu kuma itace kaddarar zai fada mata, gashi wannan last page din ta sani sai da naji kamar na kirata na kafta mata rashin mutunci_

🙄😲 _Amma baki da lafiya! Dama ya-ya kinsan kwayar mai_Dambu kuwa! Wallahi kina mata haka zata gama labarin a page d'aya 🤣😋 kuma abin haushi idan ta gama bata kuma bin takan shi, don Allah barmu mu lallaba abar mu, tasamu ta rasa mana, ai biyan bukata tafi dogon buri_

Matar ta faɗa, ina kallon su sai dariya nake, dama akwai mutane masu rikici haka a duniya? Na tambayi kaina, koni ina son Kwarkwarah, dazan samu zan karanta, amma cigaban shi nima nake son Jin ya Sunan yake?

....
"Sannun Yan mata!"
A tsorace na kalli mutumin tare da kallon shagon da Uncle ya shiga, cikin sauri na kauda kaina, dan tun daga nesa yake kallon mu cikin wutar kishi.

Jikina ne ya dauki rawa, baki na yana rawa nace.
"D..o..n ...don Allah ka tafi mijina."
Isowar Uncle Gurin tare da saka hannu ya bude kofar inda nake zaune, ya ajiye min kayan da ya sayo.

"Don Allah! Yallabai ka bani yar nan taka mana! Dan naga zata yi zafi!"

Bai kula shi ba, y a shigo cikin motar yaja abinshi, sai zare ido nake. Har muka bar gurin bai kalli inda nake ba, kawai abinda ya saka a gaban shi, yake.

Kallon shi nayi ina son yin magana babu fuska, juya mishi nayi ina kallon shi, tare.
"Uncle!"

A sanyayye ya amsa min.
"Na'am Yumnah!"
"Wallahi ban san shi ba!" Na faɗa cikin muryan kuka,
"Toh me nace miki?!"
Ya tambaye ni, cikin kulawa.

Rike hannuna yayi, cikin damuwa yace.
"Ina da kyakyawan fahimtar Kafin na zarta da Hukuncin, in dai zan kuma ganin shi dake bazan zarge ki dashi ba, sai a haduwa na uku toh nan ne zan mishi mugun duka.

Na karya kafar dan banza na tarawa iyayen shi a kofar gidan su, sannan na kuma bada kudin jinya a yi mishi magani, dan haka bar tunanin zan iya kullatarki akan wannan shirmen ba haka nake ba."

Murmushi nayi sai da kwalla suka zubo min, tare da sake dariya, yace.
"Kin zata Ni sakarai ne? Toh meye amfanin samunki da nayi a cikakkiyar mace Indai bazan iya bada shaidar wacece nake aure ba! Babu amfanin zama dake tun da bazan iya miki adalci ba.!"

Kallon shi nake, kamar bazan daina ba. Haka muka isa gidan muka shiga da motar, sannan muka nufi asalin cikin gidan, inda ya hadu babu laifi,

Wani daki ya rike hannuna muka nufa, muna zuwa bakin kofar, yasa min hannun shi ya rufe min fuska, muna shiga ya kai Ni har bakin gadon, sannan ya bude min fuskana, yana dariya.

Kallon kome nake a dakin kallon shi nayi cikin jin dadi da farin ciki, bude wani farin yard yayi wanda aka sanya shi a tsakiyar dakin.

Janye yard din yayi sai ga katon cake, kallon shi nayi, juyar dani yayi an saka wasu manyan balloon.

An rubuta, 17 juyawa nayi zan buga tsalle, ya rike ni.
"Don Allah! Haihuwa na biyu! Kin girma tsalle tsalle ba naki bane. Please a barwa Sahib"

Gyada mishi kai nayi Kawai, ina jin wani irin dad'i, fadar irin hidimar da Uncle yayi min babu iyaka, kawai dai nasan na ajiye son jiki da lalaci na barci yaci ni (🤣) a daren dan kamar ya samu tuwo hala yake ya kara, sai da yaga nayi laushi sannan ya kyale ni.

----
Washi gari na tashi da mugun zazzaɓi, haka na shirya tsaf dan zamu gidan suna.

Ina zaune a gefen gadon, na lallubi wayar shi, na shiga cikin gurin game, jin wayar shi a hannu na yace.
"Don Allah karki bincika min waya dan akwai Yarinyar da take turo min hoton pussy dinta."

Ajiye wayar nayi cike da jin haushi nace.
"Da zan kama hegiya sai na karya kafar ta, na kainata gidan iyayenta na watsar sannan tsabar rashin mutuncina bazan basu ko sisi na jinya ba"

Na karshe zancen da daurin fuska.
"Wayyo Allah! Kice idan Halwani baiyi da gaske ba, wata rana sai anyiwa baby Hanny wanka da hot water!"

Haushi ya bani nayi wuccewa ta na barshi a gurin, tunda na fahimci ba zaman lafiya yake nima ba, ina fita falon, na zauna ina kallon, hango zoben nan nayi cike da mamaki hadi da tsoro anya lafiyar zoben nan.

Domin ko jiya ina jin nayi mafarkin ana hanani tab'awa kamar yadda Uncle yayi, wata zuciya tace.
"Share kawai! Duk gizo ne!"

Na isa gaban home threath zan dauka.
"Babyh Zo dan Allah kiga wani abu!"

Buga kafa nayi tare da juyawa zuwa dakin shi, ina shiga naga baya cikin, d'akin.
"Amma dai! Uncle din nan ka kirani! Wayyo!"
Naji ya sunkuce ni sama, ajiyar zuciya na sauke sabida naji alamar damshin ruwa a jikinshi,!

"Naji zan karasa aikina amma kaima ai baka tashi da wuri ba, kuma nasan yanzun kowa ya hallara a can."

Juyowa ni yayi tare da zuba min ido.
"Kiyi hakuri! Kinsan me? Haka kawai nake ji a jikina zamu rasa juna! Shi yasa da naji haka na maza na kwala miki kira, jirani a nan har na shirya"

Haka na zauna, ina kallon shi, ya cire towel ɗin. Tare da saka boxes ɗin shi, murmushi nayi nace.
"Kana da jiki mai kyau! Shi yasa baka girma"

"Allah ko?"
Ban kuma magana ba, sai dai. Ce mishi da da nayi ina zuwa, da sauri na fita, ina zaune falo naga babu Zoben. Haka na dawo dakin na fara ji a jikina zoben babu Alkhairi a tare da shi, dan haka na cigaba da taimaka mishi ya shirya, muka fito.

Tsaf muka gyara ko ina dashi sannan muka fito, tunda muka nufi gidan sunan nake jin yin kuka, haka na fashe mishi da kuka sai da nayi ya isheni sannan ya bani abu na goge fuskana, muka nufi gidan dan tsayawa yayi nayi kukan.

Tunda muka shiga gidan ake mana tsiya, tare da zolaya ban damu ba na wuce dakin Hajiya wanda yake cike da Y'ay'an yan uwanta, anan wata mata take cewa.
"Wannan ba yarinyar nan da ta tafi karuwancin nan bane? Naga ta girma sosai!"

Kasa tashi nayi, tsabar tashin hankali, ina jin wata nacewa.
"Ai kazamar gado tayi uwarta sana'ar kenan, Kinga ai ba wani abu bane, dan ita tayi."

Wani irin kuka ne ya kuma kwace min, dakyar na nufi kofar ko gabana bana gani, ashe Hajiya na ban daki, lokacin da suke wannan maganar da sauri ta fito har tana Fad'uwa.

"Amma kunyi asara! Mugun asara ma, mugaye azzalumai marasa yarda da ƙaddara, maza ku fice min a gida ko na kira mijinta ya fidda ku, tunda ku Allah ya halicce ku baku da abin fada wani keda ita, kuke Allah ya bamu yawan rai da lafiya, sai kunyi kukan da yafi sautin ta, idan itace ya zanawa kanta zanen kaddarar ta, zaku gane idan kuma Ubangiji ne yake zanawa zaku gane.

Kufita kafin rayukan ku ya baci."

Ta faɗa haka tana jan haki, hawaye na zuba daga idanunta, haka suka fito basu ba hatta sauran yan uwansu sai da suka ji babu dad'i.

Ina fita, Aunty Marwanatu na min magana dan naga Annur a kafarta, shafa kanshi nayi ban iya bata amsa ba, shima gogan ya shigo gidan yaga nayi bayan garden da sauri, ya ke tambayar su.

"Lafiya me ya faru?!" Fitowar ƴaƴan yan uwan Hajiya suna mita tare da ganin laifin mutane biyub da suka aibanta Yumnah suke anan yaji abinda ya faru.

Da sauri yabi bayanta, amma sai me! Wayarta da takalminta tare da gyalenta duk suna gurin, amma ita kam babu, alamarta.

Da sauri ya fito yana haki, yace.
"Bata fito ba? Bayan shiga na,"

Kamar hadin baki suka ce.
"Wa????"

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Ya Allah idan barci nake karka bari wani ya taddani, Ya Allah karka farkar dani daga wannan mugun mafarkin."

"Halwani lafiya?!"

Kallon su yake kamar wanda ya tashi daga cutar makanta, a hankali yace.
"Da gaske bata fito nan ba?!"

Wani irin duka kirjina shi yayi daga nan ya zube akan gwiwar shi, tare da dafe goshinsa, kirjin shi kamar zata fashe zuciyarshi tayo waje, da sauri Aunty Taslima ta shiga garden din, itama gyalen da takalmi kawai ta gani tare da waya a can ya she.
Da sauri tafito tare da cewa.
."jama'a Yumnah tab'ata...... ..

#Mai_Dambu....
a: 6️⃣2️⃣. "Kamar Yumnah ta b'ata? Yarinyar da yanzun ta shiga gurin?!"

Kasa Magana Taslimah tai, kafin kace me gidan ya rufe da tashin hankali, aka shiga niman Yumnah.

Dakyar ya mike, tare da wani irin tangaɗi, gurin motar shi ya isa, kafin su fahimci me yake shirin aikatawa, tuni ya fada tare da fincikar motar.

...... A guje ya fita kamar wanda yake da yakinin ganinta a waje, gudu yake zubawa, mutane sai bashi hanya suke dan suna zargin ya shawo ne.

Bai tsaya a ko ina ba, sai gidan. Mommy mahaifiyar Yumnah, ranshi ya gama b'aci. Matakin da zai dauka akanta matukar ta rena mishi hankali ba na wasa bane!
.dan haka yana shiga ya same ta, tana zukar shisha.

.Gaban kayan kallon yaje, ya ciro wayar dake hade da wani receive, tana kallon shi ta zata ba zai iya abinda ya saka kanshi ba, kawai ya shiga zane ta.

Dukarta yake tare da ina ta kai mishi Yumnt, tsabar dakuwa. Sai da fuskarta ya farfashe. Taki magana waya yayi tare kiran yan sanda aka zo, suka tafi da ita.

Koda ya koma gida, kai tsaye part din Mamien su ya isa yana shiga, ya zuba mata ido.

A hankali yake takawa yace.
"Ina matata? Mamie ina kuka kai min Matana? Wallahi matuƙa baki yi magana ba! Na rantse zan yi abu!"

"Zane Ni! Kamar yadda ka zane Hassanah!" Kauda kai yayi cikin baƙin ciki.



Please Login or Register in order to submit comment