Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Har ya juya zai fita, ya dakata da cewa.
"Ince ni kika wulakanta Mamie? Kika raba ni da matana? Ba komai zan barwa Allah kome yayi ikon shi kamar yadda ya saba"

Bai sake magana ya fita daga gidan, duk yadda yaso jurewa sai da ya suma.

Asibiti aka kai shi, cikin gaggawa, nan aka shiga niman ceto rayuwar shi, dan zuciyarshi tana kokarin neman kin bugawa ne, sai da suka saka mishi bututun shaƙar numfashi. Kafin numfashin sa dai-daita.

Sai da aka share kwana uku, ana niman Yumnah babu ita babu labarin, hankali kowa ya tashi Hajiya ma tayi kuka tare da yin Allah ya wadaran ƴaƴan ƴan uwanta.

----
Tafiya kawai, take a cikin dokar daji tare mika hannuna kamar zata kamo wani, amma babu kowa, kafafuna sun kumbura, har suna tsagewa, tafiya kawai take. Ita kanta bata san ina take tafiya ba.

....kuma gata nan dai kamar mai hankali kamar ba me hankalin ba.

...... Ko ciwon kafarta bata ji, tafiya kawai take, idan ta gaji sai ta zauna a jikin bishiya, ta kwantar da kanta tana haki, dan barcine ya saceta, kamar wacce aka daka mata tsawa ta mike zubur ta cigaba da tafiya.

Hawaye na zuba a idanunta, tafiya kawai take, ga yunwa ga ƙishirwa, amma bata da ikon tsayawa.

---
A ofishin yan sanda kuwa Mommy ta sha mugun wulakancin, wanda bata tab'a tsammanin sabida Yumnah za a mata ba, domin CP Ibrahim yace kar a raga mata, idan bata fadi inda Yumnah take ba, ta zata wasa ne sai da suka fi dinga kwara mata ruwan sanyi tare da dukarta kamar mahauta.

Amma taki magana dan gani take, kamar zasu kyaleta amma suka ci-gaba da mata Izaya, gata da taurin kai. Suma suka nuna mata gaban samu,

....... Kwanan Halwani daya ya farka, cire karin ruwan yayi ya wuce ofishin yan sanda, tunda ya isa, ya kalli Mommy da taci wahala, kanta a cinyarta ta koma kamar marainiya.
"Ku sake!"

Haka suka bude mata ta fito, a sanyayye ya nuna mata hanya ta fita.
"Ki jirani a jikin motana"

Gyada mishi kai tayi tana dingishi.cika report yayi na ya janye tuhumar da yake mata, sannan ya kuma mika musu na goro.

Kin amincewa zuciyarshi yake, kawai domin yasan idan ya aikata haka, Yumnah bazata yafe mishi ba. Zai zama me mugun son kai.

Kasuwa ya wuce ya sayo igiyar da ake daure saniya, sannan suka shiga tafiya, sai da suka bar gombe kamar zasu nufi Yola, ya yanka da ita wani daji.

Da gudun gaske, har cikin tsakiyar dajin ya shiga da ita, ginin gida ne a cikin dajin, bai kalli inda take ba,. Ya fito da sauri.

Ya shiga gidan ya buɗe, sannan yazo ya mata jagora ciki, bayan ya kwashi kayan aikin shi.

Yana shiga ya wuce wani daki ya bude mata kome, sannan ya fito falon, ya shiga hada abinda yayi niyya.

Bayan shigarta da minti talatin sai gata sanye da wani irin rigar barci., Kauda kai yayi tare da zubawa igiyar da yake zargawa a saman fankar falon.

Yana gamawa ya juya ya zuba mata ido cikin murmushin takaici.
"Wowwww! You look sexy. Ka raso mana."

Da sauri ta karaso zata rungume shi yayi maza ya zamee tare da tura kanta cikin igiyar ya matse wuyarta.

Waje idanunta suka fito tare da tari, bai kulata ba, ya wurga igiyar sama, tare da zarge ta.
"Ina kika kai min mata na?!"

Dariya ta fara kamar Mahaukaciya, sake jan igiyar yayi da karfin tsiya, taji makogarinta ya matse.

Wani irin tsoro da fargaba ne ya shiga zuwa mata dan har idanunta sun kasa jajjur.

"Tambaya na karshe ina matana?!"

Sassauta daurin yayi, yana kallonta.
"Wallahi bata nan! Sannan ban san inda take..."

Matse igiyar yayi cikin fusata yace.
"Ki karkashe bayyaninki a can sauka lafiya."

Jan igiyar zai yi tayi maza tace.
"Tana can dokar dajin falgore, zata garin boka kafi Allah, don Allah kiyi hakuri karka kashe ni zan mika kaina ga yan sanda ma."

Kura mata ido yayi tare da zama, yana kallonta.

"Hassanah meye Yumnah tayi miki? Meye ta tsare miki? Anya kece kika haifeta kuwa?!"

Wani irin kuka ne ya kwace mata tana kallon shi, tana girgiza kai.

"Nice? Wallahi sabida son da nake makane nasa na juya mata baya, Halwani tun muna A.t.b.u nake sonka, ka fahimci ne ni!"

Nan ta shiga bashi labarin abinda ya faru, na soyayyar da take mishi, tana kuka tare da gaya mishi sirrin zuciyarta...

"Tabbas! Kinyi ƙoƙari amma ba Ni zakiwa wannan halayen ba, dan haka zan barki nan ki zauna sai naga Matana zan zo na fidda ke, idan ban ganta ba, kiyita zama. Har ki mutu asararriya, Ina sane da kece kika kashi Faruq! Yanzun kuma Yumnah. Na rantse da Allah idan ban sami mata na ba, zaki ga salon kisar da zan miki da ranki zanta yankar namar jikinki."

"Zanyi alfaharin wanda nake so shine ya kashe ni, kasan yadda zan koma!"

Make mata baki yayi, sannan yayi ficewar shi daga gidan,

Waya yayi cikin nutsuwa, can sai ga wasu matasa har su hudu suka iso gidan, bude motar shi suka yi tare da fidda kayan abinci suka shigar dashi gidan, sannan ya kalle su.

"Sau uku bata abinci, sannan karku fara nimanta, dan wallahi kuna ganin yadda take bazata rasa cuta a jikinta ba, idan kuma kuka ki ji babu ruwana."

Yana gama fadar haka yayi tafiyar shi, cikin motar shi. Kifa kai yayi yana mamakin wannan al'amarin, anya akwai muguwa irin Hassanah?!

.... Haka ya gama abinda zai yi ya koma gida, ko cikakken awanni bai yi ba, ya nufi hanyar bai gayawa kowa ba.

Haka ya tafi ya gama yawon shi bai gan me kamar Yumna ba.

Kamar zaiyi hauka, dawo gida cike da bakin cikin rayuwa da Hassanah ta wurga su cikinta.

----
Kwanaki sunyi tafiyar bazata! Sati na kara kutsawa, watanni na kara rubayyawa, haka wannan al'amarin ya kasance, cikin jikin Yumnah ya fito ita kanta tayi mugun rama, sai cikin da ya fito.

Ban da ikon Allah babu abinda yake dawainiyya da rayuwarta, tun daga nesa take hango rugaggen fulani, da sauri takara saurin tafiyar, dakyar ta isa wani ruga matasan Fulani ne a kofar gidan, zama tayi tana kallon yadda suke shan madara, sai had'iye yawu take.

"Zaki sha ne?!"

Gyada kai tayi, suka mika mata, jikin ta na rawa ta shanye, tana zare idanu. Alamun a kara mata.

"Rabi'u karo mata!"

Shiga cikin gidan yayi sai gashi da kindirimo, da ruwa a kwanon sha.

Ya ajiye mata, dauka tayi ta shanye rabin ruwan, sannan ta kuma kafanta a kan kindirimon.

Tana gamawa sha ta kwanta zata yi barci, dayan yace.
"Tashi mu kai ki cikin gidan, ki kwanta."

A hankali ta mike, suka shiga gidan. Tunda aka kaita wani dakin matar dakin farar ce Sosai, amma ta manyanta.

"Zo nan Y'ata, kwanta nan!"
Kwanciya tayi inda aka nuna mata. A hankali barci yayi gaba da ita.

Zama matasan suka yi, sannan Rabi'u yace.
"Ummi! Yanzun zama cigaba da zama anan kenan, kuma kin san yadda kowa ya gama saka ran zamu isa."

Murmushi tayi tare da jan casbi tace.
"Bazan bar yankin nan ba, sai na sadata ga danginta, kasan halin da mijinta yake ciki kuwa, sau uku yana zuwa nan dajin domin ita. Sannan da mun barta haka zata cigaba da tafiya har gurin wancan mushirikin.

Ai ko dan cikin jikinta ya kamata mu taimaka mata, dan haka bana jin zan barta ta salwanta a wannan halin, ka gayawa Karibullah yayi maza ya tafi, zuwa Kisra ya gayawa magaji...."

"Assalamu alaikum"
"Amin wa'alaikimun Salam warahmatullah! Barka da zuwa."

Mik'ewa yaran suka yi, tare da mishi Barka da zuwa, sannan suka fita.
"Zuljah!"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zabga mishi harara, sannan ta nuna mishi inda Yumnah take kwance.
"Zoben hannunta zaki cire! Don Allah taimaki bawan Allah irina mu koma kisra!"

"Imran bazan koma ko ina ba, aure zaka yi fa, auren ma jikar jikarka, Yo me zance maka, Naje gurin Sadeeq da Amrah, amma ya tabbatar min da aure zaka yi, kuma sai da muka yi alkawarin babu kishiya shine ɗan halinku na wulakancin maza kawai naji labarin aure zaka yi."

Zaro idanu Imran yayi cikin kasuwa ya jero mata tambaya haka.
"Injiwa? Yaushe? A ina matar take?! Don Allah waye ya gaya miki aure zanyi?"

"Waye banda Sadeeq! Kai bana Sadeeq ba, meye nufinka da gyaran gidan nan? Har dakuna sai da aka gyara fa! Wallahi Magaji ka cuce ni! Kaje bani son ganinka!"

"Wai ya kike son Mai da karamin al'amari babban al'amari ne? Na gaya miki ni ba auren zanyi ba, amma dole na zabgawa Sadeeq rashin mutunci, don Allah ko fahimce ni."

"Ka tafi ka bani guri!"
Ta nuna mishi hanya, zama yayi a gabanta, sannan ya fara magana.
"Uku ga watan muharram zaki cika shekaru dari uku da casa'in da tara, wanda yayi dai-dai da cika shekaru dari bakwai da zanyi! Shine yaranki suka ce a shirya miki maulidin karin shekarunki! Ashe ke nan kishi ya gama tafiya da ruhinki! Zuljah yaushe zaki fahimci ke daya nake so? Yaushe zaki gane nauyin soyayyanki a zuciyata.

Sabida son da nake miki, sai da aka kore ni na tsawon shekaru saba'in, don Allah ki bar biyewa Sadeeq, yanzun na yawo na samu ya jirgawa Amrah wannan bayanin itama ya gama turata cikin buhu wai zai kara aure, da jego na samu tana kuka, har tara mutane tayi wai a tambaye shi laifin da tayi mishi, mara kirki .

Ya kafe wai sai yayi auren,wato nima bari ya lalata min rayuwa, ta hanyar cewa zanyi aure."
.dariya ne ya kamata, tana kallon shi sannan tace.
"Toh! Ya zanyi da wannan Yarinyar?!"

"Eh toh ba sai ki kaita gurinsu Amrah, sai a hada mata magani, amma ai ba wani dogon sihiri bane, kawai akwai hatsari ne tab'a zoben, dole sai dan adam ne irinta zai tab'a, sabida asalin zoben na wani kasugurmin aljani ne, kuma boka ne zamanin shi, sace zoben shi aka yi kusan shekaru dari biyar da talatin kenan.

Dashi akayi tsafin, sannan yarinyar takan shagala da addu'a, duk da tana da ibada, Kinga ni ba wannan ba, ya zamu yi dan wallahi nayi hakuri, kuma hakurin ya kare, kisan yadda zaki yi dani!"

"Hmm! Ni fashin sallah nake!" Ta faɗa fuskarta a murtuke.

"Toh wallahi aure zan kara!"

"Ai dama nasan zaka aikata, kaje kuyi ta rashin kunyar ku, a gaban kananun yara, matsa ka bani guri na wuce!"

"Idan naki fa!"
Ya tambaye ta, tare da tsareta da ido.
Cikin sanyin murya tace.
"Rayuwar abin cikinta zaka Duba, don Allah mu kaita Yola daga nan ka cinye ni danye na amince."

"Hmmm!" Yace mata,
"Amma da Sadeeq ne ko wanin shi sai inda karfin shi ya ƙarfinka ya ƙare!"
"Abokin arziki ne! Itama bakin taimaka mata nayi ba, gani nayi kamar anfison yarinyar dani ne, tunda sabida ita kika yada zango anan dajin. Kuma Kinga mijinta na nimanta, amma kika hana shi."

"Toh idan ma na bashi ita bazata bishi ba dan shi baya ganin mu ita kuma tana ganin mu, kuma bazata tab'a bin shi ba, taya zamu bayyana mishi ba tare da ya razana ba, kaga muje kawai dan Ni ban cika son mita ba."

Ba tare da bata lokaci ba, ita ta gyara kayan jikin Yumnah, sannan ta dauketa suka bar dajin da ita.

....... Awa biyu, ya isar dasu forest din da yake bayan Mansion din Lamidon estate dake garin Yola domin jinyarta...
(Sorry na kawo muku Zuljah wa Imran!🤭)
#Mai_Dambujeeee
8/30/20, 9:42 PM - Ummi Tandama: ⁶?. Suna isa Sadeeq yana karasowa gurinsu, kallon Yumnah yayi da cikinta ya fito yace.
     "Sati biyu da suka wuce naga sanarwan ana nimanta, tab'a wata biyar da suka wuce, a ina kuka samota?!"

     "Toh gata nan Sharrin uwa yake bibiyar ta, dan haka sai ta zauna a hannun ka, muje ka haɗa mata magani, Kinga Zuljah taimaka ki dauketa, Dan Matar wani ce babu amfanin mu dauketa."

        Haka kuwa aka yi, suka dauketa zuwa dakin Amrah, wacce taci kuka har idanunta sun kumbura, kallon Zuljah tayi cikin mamaki.
"Daga ina kuke?"

Shimfid'a Yumnah tayi , tare da bata labarin abinda yake faruwa, ta tausaya mata sosai.

         Can suna tattaunawa, Sadeeq da Imran suka kawo maganin da za a fara mata amfani dashi, tare da zare zoben da ya matse hannunta sosai.

        ----
Yau ma kamar kullum, ya gama.

   Mamie sun gama hada munafuncin su kenan, zata haura sama, kawai ta taka abu koda ta duba sai ta ga ƙayar kifine.

   Tayi mamakin ganin shi a gurin dan haka ta cire, tare da hawa ta wanke kafarta tasa magani. Ta kuma cigaba da abinda yake gabanta tare da kiran Linah tana gaya mata yadda suka yi da matar Rahbeel.

     Bayan sun gama, ta kwanta.

      ...... Cikin dare zogi ya ishe ta tun tana barci taji kafarta yayi mata nauyi, dan haka ta mike tare da yayye bargon, me zata gani kafarta ta gani kamar bokiti  tsabar girman shi yayi bak'ikirin.

       Ihu ta tsalla gashi ita daya a cikin daki, ihunta dije taji ta hauro sama da gudu, tana zuwa kawai taga kafar Uwar dakin ta.
Ai a cikin abinda bai fi minti biyar ba, ta fita zuwa shashin Hajiya ya gaya mata, sai gasu tare da Halwani.

             A daren suka kaita asibiti.

Kamar mahaukaciya take surutun abinda zata aikata Khuwailah, tare da kara b'atar da Yumnah.

      Haka ya rike kanshi yana kuka, tsabar wahalar da take sha, har fadan abinda ta shiryawa Safiyyah, tare da rabata da Papa..

.Mugun Abu iri iri, sai da tafallasa kanta, da duk irin qoqarin da tayi gurin lalatawa Yumnah suna.
. alluran barci Rahbeel yayi mata domin abin kunyar yayi yawa.

Tare da tashin hankali, har kunyar fita waje yayi a cikin asibitin.

.....washi gari aka duba kafar ta lalace, a cikin kwana ɗaya tal, dan dole suka shiga da ita aikin gaggawa, domin sun fahimci tana dauke da diabetic, babu yadda zasu yi idan basu cire kafar ba, haurawa ciwon zai yi dan haka Halwani ya saka hannun, aka yanke kafar.

Papa kan cewa yayi babu ruwan shi, ta karata can.

----
Ga baki daya yan kungiyar Utta dashi, aka wayi gari sun kama da wuta, a gurin tsafin su. Har da Ammar, Hajiya zakiya ce ta sha bayan tayi ta tonawa kanta asiri. Haka akaita bugawa a jarida, dan haka da Uncle ya sayi daya.

Yaje har inda Mommy take ya wurga mata ya fita abinshi.

----
Bayan wata uku..
Lafiya na samu, sosai duk wanda yaga Yumnah zai sha mamakin yadda ta koma, sai dai bata magana, kuma koda ka tambaye ta daga ina tafito sai kuka.

"Yan mata! Zo mu shiga kitchen, kafin Abbi ya dawo." Inji Amrah.

A hankali ta mike sabida nauyin da cikin ta yayi, tunda suka shiga aka fara girkin.

"Kin gama makaranta ne?!"
Idanun tane ya cika da kwalla, ta girgiza kai.
"Toh me yasa?"
Kuka ne ya kwace mata, tana son magana amma babu bakin magana, dan haka ta kai hannunta gemunta, tare nuna alamar namiji tayi, sannan ta kuma sanya hannunta a kirjinta, alamun nono, ta kuma made hannun ta kama juya shi kamar me renon yaro, sannan ta fara bata labarin abinda ya faru..

Hatta kaita thailand da dawo da ita da Halwani yayi.

Kuka sosai Amrah take, dan tausaya mata, sannan take gaya mata, ita bayi sa'ar Uwa ba, sabida ta tsaneta, bata sonta rayuwarta take bukata.

Sannan ta kuma ce ta rabata da mijinta, yana sonta sosai. Ta kulla hannunta sannan tayi mata alama zuciya, tace.
Duk ya mallaka mata, zuciyarshi. Kuma baya fushi da duk abinda tayi, dan haka don Allah su maida ita gida ta haihu...

Don Allah karsu bari ta haihu basa tare alkawarin da yayi mata kenan.

Shigowa yayi cikin Kitchen din, ƴace.
"Wato kina son komawa wajen mijinki ko?! Bayan naga shi din tsoho ne!"

Girgiza kai tayi tare da raba hannunta tace. A'a da hannunta biyu, sannan ta zagaye fuskarta da tafin hannunta, alamun mijinta kyakyawan ne.

Tana murmushi, ta kuma ce mishi, yana da kirki, sannan yafi shi tsayi, wato Uncle Yafi Sadeeq..sannan yana da karfi alamar yana da kirar jiki me kyau.

Sannan baya da fada, yana da hakuri. Shi indai ba da ita bace baya magana don Allah su maida ita gurin shi, yana can a dame.

"Shi kenan! Zamu kai ki gobe Insha Allah, dama sabida lafiyarki muka barki tukun yanzu kan Insha Allah ba Mutum ba aljani ba bazai iya miki kome ba, kai hanyar da kika bi bazai bi ba."

Wani irin farin ciki ne, ya kamata sai godiya take musu, saboda zasu maida ta gurin Uncle..

----
Lokacin da Mamie ta farka, ta sami kanta a wani daki ne yaran zagaye da ita, zogin da take ji ne. Yasata tambayar su tayi tare.

"Me yasa mi kafata? Taya haka ya faru dani?"
Dakyar Uncle ya bata labarin, abinda ya faru aikuwa ta tsalla ihu, tare da suma.

Tun daga lokacin ta zama kamar mahaukaciya, haka suketa lallabata, har aka sallame ta. Banda Halwani babu me zama ya kula da ita, cikin kwanciyar hankali.

.....
Yana zaune na Office d'inshi nan, cikin gidan shi, aka mishi sallama yayi baki, cewa yayi a shigo dasu, falon baki, haka aka kai su can.

Kamar bazai fita ba, ya daure ya fita. Yana isa ya hango matashin mai kudin nan na yola, cikin mamaki ya isa da sallama ya mika mishi hannu suka gaisa, daga nan suka fara tab'a hira yace.
"Mr Sadeeq Lamido Sadeeq, yau kai ne a gidana? Gashi gidan babu kowa sai ni bari na kawo maka ruwa, sannan Madam"

"Haba barshi kawai yanzun zamu koma, mun zo maka jajje ne, kuma toh bamu san yadda zaka dauki abin ba, duk da cewa.

Ba wani abu bane, amma mun kawo maka wata mata ce, ko itace wacce kake nima."

Fita Amrah tayi ta shigo da Yumnah, tana. Shigowa ya mike jikin shi na keerrma, yace.
"Don Allah, ki daina min gizo. Tunda baki kusada dani"

Bakinta na rawa, gashi dakyar take daya kafa, tace.
"Uncle! Nice Baby Yumnah."

A hankali ya karasa gareta, tare da bude mata hannu, ta shiga, duk da cikin ya tokare shi.
Juyawa yayi cikin juriya yace.
"Na gode kun dawo min da farin cikina, ban san me zan iya biyan ku dashi ba, amma ina muka fatan Alkhairi."

"Auuuwu dama kina magana kika mana shiru?!"
"A'a Ammih, ina ganin shi maganar yazo min"

Na karshe cikin Kuka, rike ni Uncle yayi sannan yace.
"Toh muje family house din mu, sai ku samu ganawa da iyaye na!"

Dukkan mu, muka nufi can gidan Hajiya, Ni da Uncle muka shiga gidan, duk wanda ya ganni sai ya shige gidan, kafin mu shiga kowa ya fito.

Ihu da murna kawai ake, sannan da aka nutsu, suka bada labarin abinda ya faru, sannan Ni kuma aka juya kaina.

Akan na basu labarin abinda ya faru, share kwalla nayi sannan na fara da cewa.
"Lokacin da na fita daga dakin Hajiya, ina kuka. Kamar zan dauki Annur sai na fasa, kawai na tafi Ni daya na, ina zuwa garden din sai naga zoben da Uncle ya hanani dauka, tunda na ganshi naji ina son zoben, Ina ganin shi kawai na dauka.

Tunda na saka a hannuna, naji kamar ana juya min duniyar baki daya, tare da kwala min kira .

Tunda na fadi a gurin ban kuma fahimtar inda nake ba, kawai na farka ne sakamakon tsawar da aka daka min, naji ana jan zoben da hannuna.

Tunda na fara tafiya bana cin kome sai ya'yan itace, shima wurgo min ake naci, sai ruwa shima kawai ina fara jin ƙishirwa, za akawo min shi bakina a zuba min sannan a ture ni!!!"

Shiru nayi,.kafin ma kuma fashewa da kuka, ina gaya musu irin wahalar da nasha, tare da tafiyar da nayi har yanzun kafafuna suna nan da ciwon da k'aya yaji min,"

Mik'ewa Uncle, ya fita can ya dawo, sannan yazo na cigaba da basu labarin irin bakar wahalar da nasha, da tafiyar da nake, ga laulayi, kuma kome dare kome rana haka zan ta tafiya,, bana barci bana ina kwanciya.

Har Addu'a nake Allah yasa na mutu da bakar fitina da nake fuskanta, babu ranan da baza a min tsawa ba, kuma bana ganin me min tsawa, Uncle! Uncle!!

Please Login or Register in order to submit comment