Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

*_SO DA ZUCIYA!!_*

*_NA_*

*_NANA HAFSAT_*
*_(MX)_*

*_ZAFAFA BIYAR 2022_*


*_SHAFI NA DAYA_*
*_FREE PG: 1_*

___________

*RIMIN KEB’E*
*GADA MAI ‘DOYI*

*GIDAN ARDO BORKINDO*
(AURE-AURE)

“Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!?

Almajirin nata rera baitin barar sa. Dadaa nata ce masa yayi hak’uri, yaki tafiya, Ya rike robar barar sa ahannun hagu, Dayan hannun kuma ya sakashi a hanci yana sakato daskararren tasono yana gogewa a kodaddiyar rigar shaddar jikin sa ruwan bula, Kayan sun fattatake.

**Fatimah-Zahrah (Zaarah) Yar bafulatanar budurwar na kwance akan shamilalliyar katifar kwanciyar ta irin ta boarding school dinnan. ‘Kulaficin nacacciyar baitin rera barar almajirin ce ta tashe ta daga baccin yunwar dole data dauke ta. Ta ja tsaki tana sosa manyan gashin idanun ta da suka jike da ruwan hawayen ta. Ta juya kanta gefe, Ta sauke idanunta akan mahaifiyar ta dake zaune tana yanke faratan hannun ta.

“Dadaa..?

Ta ‘karasa tana rufe bakin ta, Bayan bahaguwar hammar data taho mata.

“Kin tashi??

“Na tashi Dadaa! Bansan bacci ya dauke ni ba ma.?

“Ai wannan wanki da kika tula dole ki baccin gajiya, Allah ya yi albarka.?

“Aamin Dadaa?

“Ga abinci can cikin kwanon ki. Tun da zafin sa yanzu nasan ya huce.?

Da azama ta janyo kwanon ta bude shi, Dauke yake da danwake da man ‘k’uli da jan yaji.

“Wayyo Allah na! Danwaken Iya fatsuma. Dadaa ina su Hamma Modibbo Da Na'eelah da Raheelah??

“Su Raheelah sun tafi Islamiyya, Hamman ku kuma bai jima da barin nan dinba. Shi ya kawo danwaken nan ma.?

“Allah sarki Hamma, Allah ya kara budi.?

Cikin haka mahaifin su Malam Ardo borkindo ya shigo cikin gidan bakin sa dauke da sallama.

“Atuwaa,Dadaa ku fito”Ya zunduma musu kira yana daidaita zaman da yayi akan wata ‘ballalliyar kujera da ta gaji da lalacewa.

Mama Atuwa ta fito daga cikin d’akinta tana susar kunne da gashin kaza. Ta tsaya ‘kerere akan sa sanye cikin riga da zani kowanne kalar sa daban. Yaja tsaki yana girgiza kai.

Atare Dadaa da Zaraah suka fita tsakar gidan nasu,

“Bappah Barka da dawowa?

Zara ta tsugunna har kasa tana yiwa mahaifin nasu sannu da zuwa. Ya amsa fuskar sa a daure. A ‘darare ta koma cikin da’ki. Don inda sabo ta saba da tsangwama da kyarar mahaifin nasu.

“Sannu da zuwa...? Dadaa ta masa sannu ta rakube a gefe ta zauna.

“Ayau yau, Nakeso a share dakin abincin can. Jibi i war haka amarya zata tare.?

Gaba d’aya Dadaa da Mama Atuwa sai suka zube masa idanun su. Kowannen su kallan sa yake cikin tsantsar mamakin kalaman sa. Dai dai lokacin da almajirin nan ya sake dawowa zaure yana kurma barar da yake. Hade da bubbuga ‘kafar sa a kasan fashasshen dab’en da akayi wa zauren.

“Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!?

“Kundugurin uban ka, Nace kaci malafar kan uban ka. Zaka fita ko sai na kirb’a ka anan?? Cewar Mama Atuwa hade da daga hannu ta masa dak’uwa.

Almajirin ya tsaya sararo baisan abinda yasa take masa fada ba Kamar yayi wani lefin? Zara dake daki ta kirawosa ta bashi sauran danwaken da takasa ci. Saboda maganar auren da taji bappan su zai sake karowa a karo na ba adadi. Yayi ya sake su kamar hular sawa.

“Me muka rage ka da shi da zaka sake karo wani auren Ardo? Nace mai ka nema ka rasa agare mu. Allah ya tsinewa dubu goman da ka samu nasan da ita zaka sake karo auren nan.? Cewar Mama atuwa dake huci Kamar tsohuwar zakanya.

“Toh Malam Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lapia.? Dadaa tafad’a tana mikewa tsaye hade da komawa cikin daki.

Mama Atuwa ta buga tsallen albarka tana doddoka hannunta ajikin bango.

“Ardo! Tselen uban can, Abu ta kazar uban can kayya kai, Wabillahil gidan nan zai babbake akan amaryar nan da zakayo. Ke kuma tsohuwar munafuka kina wani dudduk’e kai, Kamar sabuwar amarya, Har da wani yi musu fatan alkhairi. Toh baki d’aya na hadaku nayi Allah ya isa..?

Malam Ardo yamike yana girgiza kai, Zai fuce ta jawo kasan rigar jikin sa yar shara,

‘Yar karamar ‘yarta da ta taso daga bacci alokacin ta tsaya a tsaye ta sau fitsari, Hancin ta dagaje dagaje da majina, Ta riko fatattakakken zanin Mama Atuwa tana cewa,

“Mama yunwa nake ji.?

Atuwa ta sake damk’o kasan rigar Malam Ardo bata ko bi takan Farillatu yar autarta ba, Cikin tsananin takaici hade da kwakwaso rantsuwa ta dire, Da d’oriyar nanawa cinyarta duka tacigaba da cewa,

“Ni da kai sai Allah ya mana hisabi Ardo. Lokacin da kazo neman aure na mekace shekarun baya? Ca kayi da gani babu kari, Matar ka ta farko ma had’aku akayi ba kai ka ganta kana so ba, Kace ni da kai, Bayan aure zamu gwangwaje mu gyagije, Muci duniyar mu da tsinke, Tarin alkawarurrukan da kayi mun sunada yawa Ardo. Harda cewa Kullum zamu dinga shan shayi da buredi mai yanka yanka Ardo, kace da lemon kwalba da shinkafa. Amma tun sati biyu da auren mu ka dena mun komai. Shekaru sha 15 kenan kadena duk wasu hakki na dana yara na dayake akan ka. Aure 8 kayi Ardo, kowacce da tazo tayi yan satinnai Sai ka rabu da ita, Saboda tsabar bakin hali Irin naka. Samun miji Irin ka nayi dana sani, Dana kori manema na a baya, Na bi kyau ba halin kwarai Irin ka, Allah sarki idi mai kifi. Kullum sai ya aika mani da sukunbiya jela...Rana?

Bata kasara ba Malam Ardo yaja dogon tsaki yana girgiza kai,

“K’ofa abude take, Duk sanda kika shirya fita... A shrye nake na baki takardar sallama.?

Mama Atuwa ta wulla masa harara tana tab’e baki,

“Saki? Hohoho ai naga gidan zama Ardo, Na tara yara har 5 kace na fita? Babu inda zani. Na zame maka kadangaren bakin tulu , Akashe ka a fasa tulu a barka ka ‘bata ruwa. Ahayye Atuwa maman sailuba da Sameerah, Uwar Hajaara da Farillatu...?

Malam Ardo yaja tsaki hade da bige hannun ta daga rikon rigar sa da tayi, Ya fice yana mita. Ita kuma Mama Atuwa ta figi hannun Farillatu ta goyata tana jera tsaki, Had’i da yadawa Dadaa maganganu. Ranar kaf dangin Malam Ardo na kusa dana nesa sai da Atuwa ta zage su tas kowanne ta kamo sunan sa, Sai ta aibata shi.............

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
1/2/22, 18:40 - Buhainat: *_SO DA ZUCIYA_*

*_FREE PAGE:2__*

*_ZAFAFA BIYAR PAID BOOKS_*

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .

***Ruwan sama tamkar da bakin kwarya. Unguwar rimin kebe ta wanku da ruwan sama. Ko’ina yayi shar. Bishiyu sun ‘kara rinewa sunyi koraye shar da su. Hamamin warin gada mai ‘doyi ya ragu ainun da falalar ruwan sama.

Tun daga nesa Zaarah ke tafe dawowar ta kenan daga makaranta. Yau din an taso su da wuri sakamakon ruwan da akeyi ba winduna a makarntar, Hakan yasanya ruwan zuba ta cikin kwanukan azuzuwan ciki harda na su Zaarah. Shiyasa malaman suka taso su kafin lokaci ya cika. Dubada ruwan ya kanyi gyara sosai duk sanda aka yi. Kwanukan kan rufto ko kuwa wani sashe na azuzuwan ya zaftaro ya fad’o a kasa. Domin makaranta ce ta gwamnati. Wanda duk wani dan adam ya kalla da idanun basira zai iya cewa makarantar gwamnati ta mance da ita. Domin daliban duk tsatson marasa galihu ne. Akan tabarma suke zama. Malaman kuma akan benchi. Sai madaidacin allo da malaman ke bayani ajikin sa. Da ya gaji da gajiya ya karye sai yan chalks (chak) gustsuraru da malaman kan yi musu rubutu.

Ita kadai take tafiya kan hanyar zuwa gidah daga makaranta. Sanye cikin uniform kalar sararin samaniya. Sai yellow (yalo) d’ankwali dake nuna alamar ita din perfect ce. Kayan makarantar sun zauna ‘das a jikin ta. Duk kuwa da sunji jiki ainun, Ga faci nan ajikin kayan an musu dinkin allura da zare, Ta musu ninkin guga kai kace gogewa tayi da dutsen guga. Saboda yadda suka sha kari. K’afafuwanta sun sha sandal takalmi wanda daga gefe gefen takalman an d’inke da zare irin na musu shoe shiner dinnan.

Ta cikin hijabin kana hango tudun yalwataccen gashinta ta d’aure shi da leda. Bayan ta saqale da jakar baya. Wadda aka rubuta da manyan bak’i na foundation/gidahniyar Unicef. Ita kadai ke tafiya tana tafe tana lazumi. Kamar yadda Dadaa ta umarta su dinga yi. Dandazon sauran dalibai na tafe a bayan ta suna shewa da ife-ife. Ita kuwa Zaarah tana tafe Ita kadai abunta. A haka ta karasa shiga tsukukan layin su. Wanda kwalbati ta ruguje gefe da gefenta nata amayar da hamamin kwatar dake zuba ta tsakiyar kwalbatin.

Sakamakon yalwataccen ruwan da akayi, Layin gaba daya ya damule da cakwalin tab’o mai tsananin dank’o. Ta ‘kusa kai tashiga layin nasu. Wanda baya bullewa. Gidan su ne na karshe a layin. Mai dauke da shago a kofar gidan inda Hammah Modibbo ke kwana. Zata shiga gida kenan ta hango su Raheelah da Na’eelah kowannensu dauke da bokiti da yafi karfin su. Zasu tafi ebo ruwa.

“Adda manga (babbar Yaya)Sannu da zuwa.?
Suka hada baki wajen gayshe da ita.

“Sannun ku, Ina zuwa haka? Wannan bokitan waye??

Ta tambaye su cikin tsananin mamaki , Sanin bata taba ganin bokitan ba agidan.

“Na Aunty amarya ne.?
Cewar Na’eelah.

“Bappah ne yasa mu, Yace mu zuba mata.? Raheelah ta fada tana sosa idon ta na hagu.

Zaarah ta girgiza kai kawai, Tayi Allah ya kyauta azuciar ta. Kafin ta dube su tace,

“Karku dinga ciko ruwan, ku debo iya karfin ku. Sannan banda biyawa wani wajen. Da kun eho ku dawo gidah kai tsaye. Duk wanda zai kiraku kar ku je ku dawo gidah da sauri.?

“Toh Adda Manga...?
Suka amsa baki d’aya.

Tukun sannan ta karasa shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama. Dadaa na tsakar gidan tana ebe yan kwanukanta da aka fur fito dasu daga dakin girkin da ya zama parlorn amarya a yanzu. Anata yab’e sashen amarya da fenti. Gidane madaidai ci mai dauke da dakuna uku matsakai ta da dakin girki. Sai band’aki daga can ‘kurya. Wanda katangar gefen sa ta zube. An kare da langa langa. Dakuna biyu na kallan gabas d’aya na kallon arewa.

Masu kawo jeran bazawar Malam Ardo tuni sun gama yi mata jere sun tafi. Dakin an saka gado da mudubi. Dakin girkin daya zama madadin parlorn ta sun saka wardrobe din gadon da kuma kujeru guda uku. Sai manya manyan bokiti a gefen dakin. An cire marafan su, Su Na’eelah Da Raheelah na zuba ruwa aciki.

A haka Zaarah ta karasa kalle kallen jeran amaryar mahaifin nasu. Ta shige cikin dan tsukukun dakin su bakin ta dauke da sallama. Dadaa ta amsa ta, Tana kokarin jere yan kwanukan ta da aka furfito musu dasu daga dakin girkin su daya zama mallakin parlorn amaryar malam ardo.

“Yar albarka an dawo??

“Na dawo Dadaa. Kinsan duk sanda akai ruwa mai nauyi da wuri ake taso mu.?

“Zahiri hakan take, Toh Allah ya temaka ya kuma baku sa’a.?

“Aamin Dadaa. Naga su Raheelah ai awaje.?

“Eh zasu ebo ruwa ba, Baffan kune ya sasu.?

“Amaryar ta taare ne??

“A’ah, Yan uwanta dai sun zo sun yi j...?

Bata karasa ba sakamon fad’owa dakin da Atuwa tayi cikin tsananin furgici da ‘dimuwa.

“Jammu...? Ta kira sunan Dadaa cikin rawar baki da dimuwa.

“Na’am Atuwa. Meya faru?? Cewar Dada da hankalin ta gaba d’aya itama ya tashi ganin yanayin na Mama Atuwa.

Atuwa ta yage jemammen hijabin jikin ta, Da yayi du’kun dukun dashi da datti. Ta shiga sosa duddugaggen gashin kanta tana in’ina.

“Kinsan wa Ardo ya auro mana??
Ta shiga tambayar Dadaa tana nuna yatsanta d’aya ga parlorn amaryar ta Malam Ardo.

Dadaa ta girgiza kai alamun a’ah. Zaraah dake gefe ta baje kunne don sauraron wa mahaifin nasu kuma ya rakito wannan karon.

“Jimmamman..Jimmamman dai matar tsayyabu da yai wa shika 3. Ashe itace bazawarar da Ardo ya rakito ya aura........Yanzun naji yan majalisar bakin gada na cewa Ardo aure aure an daura auren sa da jimmamman diyar ‘dan talle mai ‘data....?

Zaarah da Dadaa duk Sai suka kasa cewa komai, Jin wadda Malam Ardo ya rakito musu. Wai jimmamman matar tsayyabu na lado daya saka. Diyar’dan talle mai ‘data.

Dai dai lokacin da.......

#ZAFAFA (NAMU BA IRIN NASU BANE😍💯🙌🏽)

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
1/2/22, 18:40 - Buhainat: _*SO DA ZUCIYA_*

*_FREE PAGE:3_*

_*NANA HAFSATU_*

*_ZAFAFA BIYAR PAID BOOKS_*

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .

___________


****Dai-dai lokacin da su sameerah, Farillatu da kuma guggun yaran mak’ota suka fara ife-ifen yiwa su Sailuba da Hajara oyo-yo. Sai yauk’i suke suna baje hanci. Su ga yan hutu da sukaje garin Suleja wajen kanwar mahaifiyar su (Mama Atuwa). Su Sameerah sai gudu suke suna tsallen murnar dawowar yayyun nasu. Dandazon sauran yara na biye dasu. Kayan su duk’un duk’un. Wasu ma pant ne kawai ajikin su ba riga. Sai dai fatan Allah ya kare kawai.

Murnar ife-ifen shelar dawowar su Sailuba ne yasan ya Mama Atuwa tsaida maganar da take na Jimmamman (Jim-Mam-man) amarya kuma bazawara ga Malam Ardo mijin su. Ta kwasa aguje tana rangad’a gud’a, Kai kace sabuwar amaria aka kawo. Nan duk murnar dawowar ‘yammatan yayan nata ne. Sailuba da Hajara.

“Ahayye biyu kyautar Allah, An buga daku anbar ku ya zasuyi daku? Sai kallo. Kaf Rimin kebe baya ku ‘yayan Atuwa. Allah dai ya kawo muku mazaje masu motoci mai nishi su aure ku...?

Su kuma sai hura hanci suke, Suka ajiye jakar ghana must go din da sukayi kama kama da hannun ta.

Kamar su d’aya da Atuwa, Yanayin fad’adden bajajjen hancin ta daya kama gam a fuskar ta. Hakan suma suka dakko kamannin nata. Sai hasken mahaifin su da sukayi suka kuma ‘kara dana bleaching. Saboda tsananin yadda fatar su ke shekin kyallin yellow yellow, Da kuma bak’i bak’i a kafafuwan su da hannayen su.

Kana ganin su kallo d’aya zakayi musu kasan yan biyu ne. Suna kama da junan su ainun. Sai dai tsayi daya bambamta. Hajara tafi Sailuba tsayi. Suka zube akan tabarmar Atuwa dake shimfide a dan tsukukun kofar dakin ta. Duk ta huhhuje taji jiki ainun tabarmar. Sai ‘daga kai take tana leka jakar kayan su.

“Wai ba wuta ne har yanzu..?? Cewar Sailuba hade da tankwashe k’afafunta. Tana mai latsa lambobin jikin yar Nokia wayar hannun ta mai chocilan (3310).

“Babu Sailuba! Yo wa zai gyara aganin ku. Sati biyu cir kenan tun tafiyar ku har wa yau baa gyara ba. Malam ya ‘karo kud’i da dubu goman da Nomau kansila i bashi. Yau aka daura auren sa da Jim-mam-man dai ta karshen layin yan tumaki. Ko bai karo aure bama kunsan sarai Sai dai mu dawwama ba wutar. Modibbo kuwa ai sai Allah ya saka masa. Da uwar data haifeshi tana nan ai datayi kukan bakin cikin ‘danta da aka mayar Kamar tandan waina.?

Nan suka hau yada maganganu. Kafin Sailuba ta mike ta karasa kofar dakin Dada. Tamkar zata bige Dadaa dake sunkuye tana daure sililfas dinta daya tsinke da leda. Sai Dadaan ce ta matsa gefe. Ita kuma ta tsaya tserere a bakin kofar dakin. Tana jefawa Zaraah dake kulle yan kayayyakin su data nunnunke a dankwali harara.

“Zaman ki a gidan nan bayada wani amfani..?

Zaarah da batasan da wa Sailuba take ba. Tacigaba da tattare komai na dakin. Hade da mikewa tsaye ta soka dan turaren tsinken kamshi data siyo jia a jikin hudar bango. Batabi takan Sailuba ba.

“Magana nake miki, Kin bawa iska ajiyata. ‘Karamar gaja.?

Sai a sannan Zaarah ta juya kanta tana kallon Sailuba, cikin zazzakar muryarta ahankali a kuma nutse. Kamar ko yaushe da bata biye musu ajikan su. Ta dan ‘kakaro murmushi hade da dan matsawa gaba.

“Me kika cewa ne yar uwa??

“Uwar ubanki nake cewa.?

Maganar sai ta bama Zaarah daria ma, Tadan dara sosai har hak’oranta na bayyanawa farare tas dasu a jajjere da wushirya. Kyakkyawan dimple dinta dake k’arawa fuskar ta kyau suka lotsa. Cikin sakakkiyar fuska da tattausan lafazi tace da ita,

“Kaka fa kika zaga, Allah ya jikan su. Ko da yake abokiyar wasa ce ai ko.??

“Oho miki uwar annamiman ci, canta matse miki da Irin kalaman ki marasa Kan gado. Nace ke yanzu ba zakisan yadda zaki yan Nepa karsu yanke mana wuta ba??

“Mezan yi wanda ya wuce na basu hak’uri yar uwa? Nayi nayi sun ki ha’kura, Banida abinda zanyi bayan haka. Wutar da ita da babu yar uwa duk d’aya ne. Mu ba abun kallo ne damu ba. Ba fanka babu komai da zamu more. To Meye na damuwa ko kuwa??

“Yar ciki da bak’i kawai...! Sailu babe rabu da ita dan Allah. Banzan bakin jininta ma ai ba zai sa su ki yankewa ba. Kullum jiya i yau. Sai tara samari masu tafiya tamkar iska zata kwakushe su dan yunwa.? Hajara ta karasa fada tana mai zazzage kayan da sukazo dasu a jaka akan tabarmar dake shimfide a kofar tsukukun dakin su.

“Gaskia ne ‘dayar biyu. Sailuba dawo nan ku nuna mun abubuwan arziki da kuka sassamo. Wannan kuma menene?? Atuwa ta fada tana daga wata leda mai dauke da sausage aciki.

“Abunnan ne fa, Ke Mama an cigaba fa, Hajara yama sunan sa?? Cewar Sailuba dake daga kai tana tunani.

“Sawsaji.. Naman gwangwani ko leda ba.? Hajara ta karasa fada tana mai jefa soyayyen sausage din a bakinta.

“Yauwa sawsaji (sausage) Soya shi ake Fa Mama. A mai Anti Hab’i ta soya mana da zamu taho. Sawsaji naman y’an gayu.? Sailuba ta ja kalmar sausage din kai kace dai dai take fa’da.

Haka dai Atuwa ta cigaba da tambayar su, Duk abunda tadakko sai ta tambayi menene shi? Su kuma suna amsata cikin zak’ewa da nuna su din yan gayu ne. Zaraah data karasa tattare dakin tsaf, Ta sauya kayanta zuwa daurin zani da hijabi. Ta sab’i sosan wankan su da sabulu ‘dan yanka ta nufi ban’dakin su na gidan dake can karshen kurya. Ta janyo langa langar da ake saya kofar bandakin ta rufe. Sannan ta koma ta dakko ruwanta dake rufe tun ebowar datayi da asubah ta shige bandaki bakinta dauke da adduar shiga bayi. Ta fyallo wankanta ta koma daki sam batabi takan su Atuwa dake yada magana ba suna tafa tafukan hannayen su.

“Wannan k’amshin fa daga ina??
Atuwa tafada tana kallon hannun Sailuba data jawo takardar da gasashen zabo ke ciki a jakarta.

“Nama ne Mama.?

“Iyye dakyau, Bara mu dandali abun arziki. Shima habin ce ta gasa muku??

“A’ah wannan tsayawa akayi a Kaduna yin Sallah, Shine mukayi wasu samari garori suka saya mana.?

“A hayye kun wanki garori.?

“Mun wanka Mama... Ke dai zakiji labari Idan muka shige ‘kurya. Nan akwai mahassada”Hajara tafada. Suka kashe hannuwa da Atuwa.

Ita dai Dadaa data karasa kauda komai nata, Ta shige cikin daki. Dai dai lokacin da su Na’eelah suka karasa sawun k’arshe na ruwan da Malam Ardo yasa su zubawa amaryar sa. Suna ajiye bokitan suka shige dakin su da sauri. Har cikin dakin Dadaa kana jiyo k’amshin gasashen zabon daya sha kayan hadi sai tashin kamshin tafarnuwa yake da kayan kamshi.

A dole Dadaa ta d’auke hankulan su Raheelah Da Na’eelah ta hanyar fara yi musu tatsuniya. Zaraah na daga can gefe tana yin aikin gidah (assignmnt) da aka basu a makarnta.....

••?. ••?. ••?.

Ana karasa kiraye kirayen sallar ishai sai ga Malam Ardo ya shigo gidan sanye cikin sabon yadi ruwan zuma. Ya dora hula kai kace yaron saurayi ne. Hannun sa rike da ledoji biyu farare na awara guda shida-shida an bad’e kowacce da yaji.

Dakin Mama Atuwa ya fara shiga ya ajiye mata awarar akan ‘ballallen benchin da suke daura jakar kayan su akai.

Atuwa dake kwance ta daga kai tana kallon sa shak’ek’e.

“Meye wannan Ardo...? Hum namiji hankaka. Wane salon munafuncin ne wannan harda leda. Ko mance dakin amaryar taka kayi ne. Jim’mam’man.??

Malam Ardo ya yamutsa fuska ya sake dakko ledar ya dire mata agabanta.

“Gashi nan awara ce.?

“Me hakan ke nufi? Ko awarar ce kayan fadar kishiya da kayo mana a karo na 9? Iyye??

“Idan ba zaki ci ba bani abuna.?

Ta wulkita idanu hade da galla masa wata uwar harara. Ta tattake ta dau ledar ji kake ‘kwas a k’irjin Malam Ardo.

“Allah ya kwashewa awarar albarka. Don bakin munafurci me zamuyi da awara guda 6? Ko ta uban uban mecece oho, Ba Za’a ci ba. Kai awara ta dama. Don kuwa mu yanzu muka sakushe hakoran mu da zabi.?

Sai a sannan Ardo ya juya ya Kalli ‘yayan nasa. Shi yama manta dasu. Dake gaba d’aya yaran sa matan ba’a gaban sa suke ba.

“Ai dole ka kalle su, kanada Iyali tamkar baka da su.

Please Login or Register in order to submit comment