Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.
Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad'an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba

"Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki."

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana,

" Lafiya Mama? Me tayi?"

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.
Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.



***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k'asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope, sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai sauran lokaci.
Tunawa da tayi da envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud'e, murmushi tayi ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart a k'asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai.
Cigaba da rikewa tayi a hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana jin wani irin feeling, she's nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba. Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.

"Mun sauka." Taji yace sai kuma yave

"Owk tura min number shi."

Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message ya ciro ta ya kira ya fad'a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa

"Ummi muje gashi chan ma."

Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda yake nufo su.

"Welcome Sir."

Yace cikin girmamawa, ba bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a daidai aljihun.

"Thank you."

Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban motar ya zauna ita kuma Iman ya bud'e mata baya sannan ya jasu suka fita daga airport din. A daidai wani hotel suka tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace

"Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina bukatar wani abu ki kirani."

"In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe."

"Allah ya kaimu." Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga gefe yana kallo suka bar wajen.

Ta cikin dark tinted glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.
A wani babban gida cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.
1/31/22, 18:49 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ofn1zci8smgg&utm_content=6k8ur6p

*21*


***Ya tsaya gaba dโ€™aya ya mayar da hankalin sa da nutsuwar sa kan Zaraah da kallon sa ya isheta ta sunkuyar da nata kan tana dan jan kasan leben ta tacikin niqabi.

โ€œMeyasa kik...Ki..kazo latti? Uhm....?โ€?

Ya tambayeta cikin lankwasar da murya hadi da tsare ta da idanun sa masu kama dana jin bacci. Zaraah gaba dโ€™aya yanayin kallon sa ya ishe ta. Hakan daya ke mata baisan bakinta ma takasa bude shi tabashi amsa ba.

Ya danyi murmushi yana shafa kwantaccen sajen sa, Shi kansa ya kan rasa meyasa ZUCIYAr sa ke kasa sukuni ba a duk sanda ya dora idanun sa ga Zaraah

โ€œSa...Sajeedah! Magana nake miki fa.. Ko dai har yanzu ana jin haushin muโ€™allim dinne? Uhm?โ€?

Tayi saurin girgiza kai tana jefa idanunta dayan gefen.

โ€œKin haku..rah?โ€? Ya sake tambayarta ya mai sauke ajiyar zucia.

Zaraah da batasan akan me yake bata haโ€™kurin ba ta dai san can cikin zuciar ta haka kawai dazu taji ya bata haushi, Da ita Kanta ta rasa dalilin yin hakan, Domin ita batasan meye SO ba ballanta ZUCIYAr ta ta hasaso mata musabbabin haushin sa da take ji.

โ€œFadโ€™imaa!! Ko sai na zube gw..Gwiwo yi na a kasa na baki hakโ€™uri? Ki temaka ki amsa kinji?โ€? Ya karasa yana mai hade hannuwan sa biyu alamun ban hakuri.

โ€œMalam! Bafa abunda ka mun. Allah ni.. Ni bansan hakurin me kake ta bani baโ€? Ta karasa tana mai zumburar bakinta gaba, Dake niqab din bawani bakโ€™i ba sosai.

Kwarai matuka yanayin shagwabar Zaraah na ninkawa sudeis SOnta a ZUCIYAr sa. Shi kansa ya rasa meyasa kaunar ta ke ninkuwa acikin zuciar sa dik sanda aka ambaci sunan ta, Ko idanun sa suka gamo ta. Ahankali cikin sanyayyar murya da wani salo mai tafiyar da mai saurara yace da ita,

โ€œNi nasan meyasa, Ko kinason sani, Uhm? Batulaaa, Suna mai girma ne dake fa..โ€?

โ€œAโ€™ah! Banaso.โ€?

Ya bude baki zai bata amsa kenan, Shugaban daliban ajin ya taho wajen su. Tun daga nesa ya shiga yiwa Zaraah magana,

โ€œAmeera! Kinga Malam Sudeis, Shi ne zai mana Hadith.โ€? Ya fada yana mai cigaba da takowa inda take, Hadi da kallon โ€˜kasa ta โ€˜karfunan barandar saman. Ko zai hango shi.

Dake zaraahn na tsaye a saman bene. Shi kuma sudeis yana matattakalar bene ta uku, Ya jingina da bangon hadi da yin wata tsayuwa mai cike da kamala sa tsantsar kyautata wa ga abinda ake SO. Saboda yadda idanuwan sa ke aika mata da sakโ€™on SO DA ZUCIYAr sa.

Kafin Zaraah ta bawa Ibrahim amsa, Sudeis ya yi hanzarin hayewa saman yana mai duba agogon dake wutsiyar hannun sa.

โ€œGa ni, Ustaz Naseem har ya fita ?โ€?

โ€œEh Malam! Tun dazu.โ€?

โ€œToh muje ko, Fadโ€™ima ke koma aji, Kai kuma Ibrahim zo ka tayani da daukar kayan.โ€?

Hakan kuwa akayi, Zaraah tayi gaba abunta, Tana mai jujjuya hakuri da yake bata. Akan abunda gaba dโ€™aya tarasa musabbabin kiran ta da yayi.


**FASLUN SALMANUL PARISA**

**Yana shiga cikin ajikin, Suka hada baki wajen sake gayshe shi. Tamkar yadda suke yi wa kowanne Malami Idan ya shigo. Ya amsa masu, Hadi da satar kallon Zaraah dake janye fuskar ta daga kallon sa. Ai kuwa caraf idanun su suka sarqe. Wannan karon shi yai hanzarin dauke idanun sa daga gareta. Saboda tsananin yadda bugun ZUCIYArsa ya tsananta. Da kuma cikar idanu na kwarjini daya ga ta masa.

Cikin kwarewa da sanin ya kamata hadi da sake yin sallama da basmala, Tukun sannan ya fara karanto hadisin na arbaโ€™una Hadith. Yana yi yana satar kalkon Zaraah ta gefen idanu.

ุนูŽู†ู’ ุนูู…ูŽุฑูŽ ุฑูŽุถููŠูŽ ุงู„ู„ู‡ู ุนูŽู†ู’ู‡ู ุฃูŽูŠู’ุถู‹ุง ู‚ูŽุงู„ูŽ: โ€? ุจูŽูŠู’ู†ูŽู…ูŽุง ู†ูŽุญู’ู†ู ุฌูู„ููˆุณูŒ ุนูู†ู’ุฏูŽ ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆ ุณู„ู… ุฐูŽุงุชูŽ ูŠูŽูˆู’ู…ูุŒ ุฅุฐู’ ุทูŽู„ูŽุนูŽ ุนูŽู„ูŽูŠู’ู†ูŽุง ุฑูŽุฌูู„ูŒ ุดูŽุฏููŠุฏู ุจูŽูŠูŽุงุถู ุงู„ุซูู‘ูŠูŽุงุจูุŒ ุดูŽุฏููŠุฏู ุณูŽูˆูŽุงุฏู ุงู„ุดูŽู‘ุนู’ุฑูุŒ ู„ูŽุง ูŠูุฑูŽู‰ ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ุฃูŽุซูŽุฑู ุงู„ุณูŽู‘ููŽุฑูุŒ ูˆูŽู„ูŽุง ูŠูŽุนู’ุฑูููู‡ู ู…ูู†ูŽู‘ุง ุฃูŽุญูŽุฏูŒ. ุญูŽุชูŽู‘ู‰ ุฌูŽู„ูŽุณูŽ ุฅู„ูŽู‰ ุงู„ู†ูŽู‘ุจููŠูู‘ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆ ุณู„ู… . ููŽุฃูŽุณู’ู†ูŽุฏูŽ ุฑููƒู’ุจูŽุชูŽูŠู’ู‡ู ุฅู„ูŽู‰ ุฑููƒู’ุจูŽุชูŽูŠู’ู‡ูุŒ ูˆูŽูˆูŽุถูŽุนูŽ ูƒูŽููŽู‘ูŠู’ู‡ู ุนูŽู„ูŽู‰ ููŽุฎูุฐูŽูŠู’ู‡ูุŒ

ูˆูŽู‚ูŽุงู„ูŽ: ูŠูŽุง ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู ุฃูŽุฎู’ุจูุฑู’ู†ููŠ ุนูŽู†ู’ ุงู„ู’ุฅูุณู’ู„ูŽุงู…ู.

ููŽู‚ูŽุงู„ูŽ ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆ ุณู„ู… ุงู„ู’ุฅูุณู’ู„ูŽุงู…ู ุฃูŽู†ู’ ุชูŽุดู’ู‡ูŽุฏูŽ ุฃูŽู†ู’ ู„ูŽุง ุฅู„ูŽู‡ูŽ ุฅู„ูŽู‘ุง ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ูˆูŽุฃูŽู†ูŽู‘ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู‹ุง ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูุŒ ูˆูŽุชูู‚ููŠู…ูŽ ุงู„ุตูŽู‘ู„ูŽุงุฉูŽุŒ ูˆูŽุชูุคู’ุชููŠูŽ ุงู„ุฒูŽู‘ูƒูŽุงุฉูŽุŒ ูˆูŽุชูŽุตููˆู…ูŽ ุฑูŽู…ูŽุถูŽุงู†ูŽุŒ ูˆูŽุชูŽุญูุฌูŽู‘ ุงู„ู’ุจูŽูŠู’ุชูŽ ุฅู†ู’ ุงุณู’ุชูŽุทูŽุนู’ุช ุฅู„ูŽูŠู’ู‡ู ุณูŽุจููŠู„ู‹ุง.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุตูŽุฏูŽู‚ู’ุช . ููŽุนูŽุฌูุจู’ู†ูŽุง ู„ูŽู‡ู ูŠูŽุณู’ุฃูŽู„ูู‡ู ูˆูŽูŠูุตูŽุฏูู‘ู‚ูู‡ู!โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ููŽุฃูŽุฎู’ุจูุฑู’ู†ููŠ ุนูŽู†ู’ ุงู„ู’ุฅููŠู…ูŽุงู†ู.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุฃูŽู†ู’ ุชูุคู’ู…ูู†ูŽ ุจูุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ู ูˆูŽู…ูŽู„ูŽุงุฆููƒูŽุชูู‡ู ูˆูŽูƒูุชูุจูู‡ู ูˆูŽุฑูุณูู„ูู‡ู ูˆูŽุงู„ู’ูŠูŽูˆู’ู…ู ุงู„ู’ุขุฎูุฑูุŒ ูˆูŽุชูุคู’ู…ูู†ูŽ ุจูุงู„ู’ู‚ูŽุฏูŽุฑู ุฎูŽูŠู’ุฑูู‡ู ูˆูŽุดูŽุฑูู‘ู‡ู.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุตูŽุฏูŽู‚ู’ุช. ู‚ูŽุงู„ูŽ: ููŽุฃูŽุฎู’ุจูุฑู’ู†ููŠ ุนูŽู†ู’ ุงู„ู’ุฅูุญู’ุณูŽุงู†ู.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุฃูŽู†ู’ ุชูŽุนู’ุจูุฏูŽ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูŽ ูƒูŽุฃูŽู†ูŽู‘ูƒ ุชูŽุฑูŽุงู‡ูุŒ ููŽุฅูู†ู’ ู„ูŽู…ู’ ุชูŽูƒูู†ู’ ุชูŽุฑูŽุงู‡ู ููŽุฅูู†ูŽู‘ู‡ู ูŠูŽุฑูŽุงูƒ.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ููŽุฃูŽุฎู’ุจูุฑู’ู†ููŠ ุนูŽู†ู’ ุงู„ุณูŽู‘ุงุนูŽุฉู. ู‚ูŽุงู„ูŽ: ู…ูŽุง ุงู„ู’ู…ูŽุณู’ุฆููˆู„ู ุนูŽู†ู’ู‡ูŽุง ุจูุฃูŽุนู’ู„ูŽู…ูŽ ู…ูู†ู’ ุงู„ุณูŽู‘ุงุฆูู„ู.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ููŽุฃูŽุฎู’ุจูุฑู’ู†ููŠ ุนูŽู†ู’ ุฃูŽู…ูŽุงุฑูŽุงุชูู‡ูŽุงุŸ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุฃูŽู†ู’ ุชูŽู„ูุฏูŽ ุงู„ู’ุฃูŽู…ูŽุฉู ุฑูŽุจูŽู‘ุชูŽู‡ูŽุงุŒ ูˆูŽุฃูŽู†ู’ ุชูŽุฑูŽู‰ ุงู„ู’ุญูููŽุงุฉูŽ ุงู„ู’ุนูุฑูŽุงุฉูŽ ุงู„ู’ุนูŽุงู„ูŽุฉูŽ ุฑูุนูŽุงุกูŽ ุงู„ุดูŽู‘ุงุกู ูŠูŽุชูŽุทูŽุงูˆูŽู„ููˆู†ูŽ ูููŠ ุงู„ู’ุจูู†ู’ูŠูŽุงู†ู. ุซูู…ูŽู‘ ุงู†ู’ุทูŽู„ูŽู‚ูŽุŒ ููŽู„ูŽุจูุซู’ุชู ู…ูŽู„ููŠู‹ู‘ุงุŒโ€?
ุซูู…ูŽู‘ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ูŠูŽุง ุนูู…ูŽุฑู ุฃูŽุชูŽุฏู’ุฑููŠ ู…ูŽู†ู’ ุงู„ุณูŽู‘ุงุฆูู„ูุŸ.โ€?
โ€ซโ€ฌู‚ูู„ู’ุชู?: ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ูˆูŽุฑูŽุณููˆู„ูู‡ู ุฃูŽุนู’ู„ูŽู…ู.โ€?
ู‚ูŽุงู„ูŽ: ููŽุฅูู†ูŽู‘ู‡ู ุฌูุจู’ุฑููŠู„ู ุฃูŽุชูŽุงูƒูู…ู’ ูŠูุนูŽู„ูู‘ู…ููƒูู…ู’ ุฏููŠู†ูŽูƒูู…ู’ โ€?. [ุฑูŽูˆูŽุงู‡ู ู…ูุณู’ู„ูู…ูŒ]โ€?


ALHADITHUT THANI (2)

An rawaito daga Sayyadina Umar (RA) kuma, ya ce: tsakananinmu muna zaune a wajen Manzon Allah (SAW) wata rana sai wani mutum ya bullo a gare mu, wani mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baKin gashi, babu wanda yake ganin gurbin tafiyar sa, kuma babu wanda ya san shi daga cikinmu har ya zo ya zauna kusa da Manzon Allah (SAW), sai ya jingina gwiwowinsa izuwa gwiwowin Manzon Allah, kuma ya dora tafukansa a bisa tafukan Manzon Allah (SAW),
Sannan sai ya ce: (Ya Muhammadu ba ni labari a bisa Musulunci, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: โ€œMusulunci shi ne ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi (SAW) Manzon sa ne. ka tsai da sallah, kuma ka ba da Zakka. Ka yi azumin watan Ramadana. Ka ziyarci dakin Allah Mai Girma idan ka sami ikon zuwa gare shi).
Sai ya ce: ka yi gaskiya, sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gasgata shi.
Sannan sai ya ce: To, ba ni labari a bisa Imani. โ€œSai Annabi ya ce: โ€œKa yi imani da Allah, da Malaโ€™ikunsa, da littattafansa da Manzanninsa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da Kaddara, (wato alkhairinsa da kuma kishiyar sa).
Sai ya ce: To, ba ni labari a kan kyautatawa: sai Manzon Allah (SAW) ya ce: โ€œShi dai ihsani (Kyautarawa) shi ne ka bautawa Allah kai ka ce kana ganinSa, idan ka kasance ba ka ganinSa to shi yana ganinkaโ€?.
Sai ya ce: Ba ni labari a kan tashin alKiyama! Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Wanda ake tambayar baifi wanda yake tambayar sani ba.
Sai ya ce: ba ni labarin alamominta (tashin Alkiyama). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: (Alamominta) idan baiwa ta haifi uwangijiyarta. Kuma zakaga masu tafiya ba takalmi matsiraita talakawa masu kiwon dabbobi, suna tsawaitawa cikin gine-gine.
Sai mai tambayar ya tafi Muka zauna zamani mai tsawo.
Sannan sai ya ce: Ya Umaru ko ka san wannan mai tambayar?
Sai na ce: Allah da Manzonsa ne suka sani, sai ya ce: to, wannan dai Jibrilu ne ya zo muku domin sanar da ku addininku. Muslimu ne ya rawaito shi...

A hankali ya karasa yana mai furzar da iskar bakin sa mai tsananin zafi hadi da kamshin mint flavored.. Ya sake mai da idanun sa ga Zaraah da itama tsautsayi yasata dora idanun ta akan sa.

โ€œAmira.....โ€?

Shiru tayi bata amsa ba, Ya sake nanatawa yana nuna ta da yatsa. Ita kam badan ya nuna ta ba, Sam takasa gane wa. Yau yacemata fadima gobe ya kirata da wani. Gashi batada karfin ZUCIYAr da zata tambayeshi meyasa? Gaba dโ€™aya ZUCIYAr ta nata kissima mata abubuwa data kasa ganewa. Domin kalmar SO ma Zaraah ba zata iya fayyace taba, bare kuma SO DA ZUCIYA da ke ninkuwa koda yaushe.

Cikin sanyin jiki ta mike tama kauda kanta gefe,

โ€œKarba aikin gidan dana baku ki kawomin office, Sannan week dinnan gaba dโ€™aya Insha Allah bazan samu damar zuwa ba, Ustaz Naseem zai dora daga inda na tsaya. Amira karbo ki kawo mun. Kai kuma Ameer je ka kirawo ustaza Heekma don itace da ku.โ€?

Gaba yayi, Zaraah na biye dashi a baya. Ahankali yake tafiya cikin takunsa na kasaita da dattako mai hade da karamci. Doguwar corridor din nan gaba dโ€™aya kamshin turaren sa ya badโ€™adeta lamarin sai sam barka.

Zai shiga ofishin kenan sai ga ustaza heekma tafuto daga ciki, Tana ganin sa ta dan yi Murmushi,

โ€œNagode da shanya har na bushe Ustaz sudeis.โ€?

Dan murmushi shima yayi, Gaba dโ€™aya ya mance da ita a ofishin nasa ashe ya barta. Ya sosa keyar sa yana mai cigaba da murmushin da kyakkyawan hakoran sa suka bayyana. Ta wutsiyar idanu kuma yana hango Zaraahn sa a gefe daga dan nesa,

โ€œAfuwan Ustaza, Tuba..Nak..nake.โ€?

โ€œBa komai Ustaz, Bari naje ajikin naka zamuyi sirah dasu.โ€?

โ€œMasha Allah dama Ameer yanzu zai taho kiran ki, Kilan ma yaj..Yaje ajin..na..ki bakya nan.โ€?

โ€œEh wallahi. Bari na je.โ€?
Ta karsa hade da wucewa,

Yayi sallama ya shiga office din. Hadi da janyo deodorizer na yerwa incense and more ya shiga faffesawa yana lumshe idanu. Zaraah na daga waje ta tsaya. Ya leka da kansa .

โ€œBa...Toul..โ€? Ya kira sunan nata hadi da murya mai dadin sauraro.

โ€œShigo ki karba...โ€?

Shjga cikin ofishin tayi da sallama tana dan sake sunkuyar da kanta kasa.

โ€œZauna akan kujeran mana.โ€?

Dan zama tayi akan kujerar dake kallon tasa. Teburi ya raba tsakanin su. Lumshe idanu yayi ya sake budewa,

โ€œInteesarrr!โ€?

Zaraah ta daga kai tana kallon sa, Sunyi wani kallon kallon wanda ZUCIYoyin su suka harba a tare. Sinadarin SO yayi gaggawar maye guraben kashi kashin zuciyoyin su. Sun dau tsawon lokaci a haka. Kafin Zaraah tajanye nata tana โ€˜dan matsa yatsunta saboda tsananin yadda kallon sa ke zagaye jikin ta. Hakan take awurin sa, Gaba dโ€™aya SO DA ZUCIYA dโ€™aya ne ke kwarara a magudanar zuciar sa. Na mace dโ€™aya tak daya fara mallakawa SO DA ZUCIYAr sa kacokom.

โ€œDuk sunan ki ne fa....Zaraah, Binta, Batoul, Sajeedah, Zakiyya, Inteesar, Kauthar da yawa dai. So zakiga inata canza miki sunaye. Ko na dena? Uhm? Zaraaateey. Na dena? Bakya...so?โ€? Ya karasa yana mai rankwafar da kansa izuwa fuskar ta, Idanuwan ta manya da sukaji ishashhen kwalli sai sheki sukeyi, Su Zaraah ta saukar da kallon sa ga nashi manyan idanun masu kama da na jin bacci da suka wadatu da zara zaran gashin idanu.

โ€œZarateeey! Na dena fada? Uhum? Dan Allah ki amsa ni? Ko so kike na durkโ€™usa? Zaraah? Kome kikace zan ajiye girma na agefe nayi inde bai sabawa addini ba. Zaraateey. Kinji? Ki tallafawa..Dan Muโ€™allim dinki ko ya samu sassauci acikin ZUCIYAr sa.. Kinji? Ko dai sai na zube gwiwoyi na a kasa?โ€?

Yanayin kalaman sa gaba dโ€™aya sun dโ€™auki Zaraah sun dulmiya acikin wata duniya da batasan taba. Ba kowace duniya bace fyace ta nazarin menene ma SO? Da har Zaโ€™a saka shi cikin ZUCIYA? Sai kawai ta fashe da kuka, Gaba dโ€™aya tarikicen mazan rimin kebe dake zuwa take fita a dole kenan duk ba SO bane? Kalaman sa, yanayin zazzakar muryar sa, dattakon sa, Dimbin ilimin sa, Uwa uba shidโ€™in gwarzone acikin gwarzaye kuma maโ€™abocin tsafta da karamci. Kan kace me? Zaraah ta fashe da kuka...

โ€œSubhanโ€™Allah.!!! Zaraah! Ku...ka? Ni ne? Uhm? Kiyi mana hayateey!โ€? Ahankali ya zaro hankici fari tas ya ajiye agabanta dake tashin kamshin black oud.

โ€œDan Allah ki dena Kuka? Ni ne ko? Shhhh! Na dena, Rikโ€™e ki goge hawayen naki..Kinji?โ€?

Karba tayi tashiga goge hawayen. Tarasa hawayen farin ciki take ko na bakโ€™i. Take zuciar ta ta bata amshin kukan dadโ€™i ne. (Ni ma hansatu na kara da haka malamai suke Zaraah. Soyayyar ustazai ai nagartacciya ce๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜‚๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ?)

Kafin ta gama goge hawayen, Ya zagaya ta bangarenta da ruwan roba a hannun sa.

โ€œSha ki tausasa zuciar ki zaraah na... Kinji? I wonโ€™t hurt your feelings.... Za..ra..teey!โ€? Ya karasa hade da tsugunnawa ya mika mata robar ruwan nestle din daya ciro acikin mini fridge din dake ofishin.

Sai daya tabbatar ta karba zata sha tukun sannan ya mike ya koma kujerar sa ya zauna. Hade da jan littafan yan ajikin ya shiga bubbudewa yana saka hannu.

โ€œShekarun ki nawa?โ€?

Tambayar sa ta daki dodon kunnen Zaraah.

โ€œSha biyar...โ€?

Girgiza kai yayi yana murmushi,

โ€œAjikin ki nawa?โ€?

โ€œSs1...โ€?

โ€œMasha Allah! Zaraah!โ€? Dan rubutu yayi a notepad ya mika mata.

โ€œKarki karanta sai kinbar school dinnan. Zanyi tafiya abuja wani islamic conference. Na je ko?โ€? Ya tambayeta da gasken gaske.

Da sauri ta daga kai tana kallon sa. Ya dage girar sa alamar Eh.

โ€œIdan...kika ce na bar shi. Wallah bazan je ba.โ€?

Tayi saurin girgiza kai,

โ€œKaje Malam!โ€?

โ€œToh shikenan tunda kin amince. Ya..yadda kikace ai haka zaโ€™ai.โ€?

Ita dai shiru tayi bata sake ce masa komai ba. Ya karasa marking books din ya mika mata.

โ€œGasu nan. Sai dai baki mun addua ba.โ€?

โ€œAllah ya dawo da kai lapia.โ€?

Ya dโ€™anyi murmushi yana lumshe mata idanun sa. Wani salo na sako ya shiga aikawa zuciyar ta, Ta idanun ta.

โ€œIna handkerchief dina?โ€?

โ€œGashi zan wanko sai na dawo dashiโ€?

โ€œTsadadden hawayen naki zaki wanko mun? Uhm banaso, Nafuson kayana a haka Zaraah.โ€? Ya karasa Hadi da mika mata hannun sa. Ta dora masa ya karba ya masa kyakkyawan masauki a aljihun sa.

Ficewa tayi da sauri. Fuskar ta kumshe da murmushi. Shima a nasa bangaren murmushin yayi. Ya jinginar da kansa a kujera yana lumshe idanun sa. Wai yau shine ya dulmiya acikin kogin soyayya..

Ko da aka tashi driver ne yazo daukar Zaraah. Ta shige mota tana saurin nannade takardar daya bata. Ta shiga karantawa,


โ€œDear second love of my life after my late mother...

โ€œZaraah People told me that love would find me when I least expect it. You entered my life out of the blue, but I feel Iโ€™ll never be the same. Sajjeddah I used to think that โ€œlove at first sightโ€? was some kind of urban myth โ€? then you smiled at me. Zaraah na kuma da SO DA ZUCIYAR ki......... Inteesar We met so briefly but, since that day, I havenโ€™t been able to concentrate on anything else. Letโ€™s meet again before I lose my job๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜๐Ÿ˜โ€?

ZUCIYAr ta ce ta Tsananta da bugu. Mai tsananin duka lokacin data karasa karantawa. Kifa kanta tayi acinya tana kunshe murmushin ta.

**GIDAN MALAM ARDO***

Tsaye suke cirko curko suna layin bandโ€™aki, Yayin da idrisu ke sakin kashin sa abandakin. Ardo tamkar yayi kuka saboda tsananin yadda cikin sa ke murdawar gudawa. Ba shiri tusa ta kufce masa.
Ji kake โ€˜siiiit!!!!


โ€ขโ€ขโ€?

YAU DAI NAYI ISHASHSHEN TYPING๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜ญ
IDAN KUNGA NAYI KADAN IDANUNA SUN MATSA NE๐Ÿ˜žALLAH YA BAMU LAPIA BAKI DAYA. KAUNAR KAUNA๐Ÿ’ฏโค๏ธ






MISS XO WRITES๐Ÿฅฐ
1/31/22, 18:49 - Buhainat: * I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ofn1zci8smgg&utm_content=6k8ur6p

*22*

***Jimmamman tayi hanzarin rufe hancin ta da wandon Zainab dake hannunta. Akan layin shiga bandakin itama take. Da โ€˜dan ruwanta a wata roba da alama itama bayan gidan zatayi.

โ€œHaba Ardo...Haba Ardo meye haka?โ€? Cewar jimmamman takarasa tana mai dankara masa harara.

โ€œGaskia dai anci baya wallahi. Fisabilillahi ya zaka saki duwaiwai ka banka mana tusa? Da girman ka? Da ace ka aurar da yaran ka billahil lazi da kanada jikoki. Aikin kawai.โ€? Cewar Atuwa dake tana daga gefen sa ta tsugunna. Kuma sanda Ardo ya banko tusar hancin Atuwan na tabo bayan sa. Don haka a hancinta ya saki bomb din.

Ta karasa magana hade da zuba ruwa a bakinta ta kurkuro, Hade da zuwa yatsanta ta kwakwalo hancinta. Tana mai rufe hancin da tafin hannun ta.

โ€œDan wulakanci a salansar hancin nawa zaka baje duwaiwuka ka banko iska. Aikin kawai.โ€? Atuwa ta shige daka tanata mita.

Ita kuwa Rumalle dake bacci sai alokacin tatashi tana matse idanu. Ta futa tsakar gidan tana kiran Ardo.

โ€œArdon Rumalle! Kana Ina ne angona?โ€?

Jimmamman dake tsaye ta yamutsa fuska tana mai karkade kafafun ta.

Ardo ya matse ciki da hannun sa yana nunawa Rumalle bandakin da Idrisu ke ciki. Idrisun kuwa sai wake waken sa yake,

โ€œKiriku yarone.. Am..โ€?

โ€œAmma me? Dan tselan kan uban ka dake Fanda. Ba zaka fito ba ka dena wakar nan kana ganin baban ku Ardo yama kan layi sai wake wake kake. Fito dan kar uban ka.โ€? Rumalle tafada tana kamo hannun Ardo.

โ€œYi hakโ€™uri mijin Rumalle, Shi dama Idrisu yadda kasan fara, Haka yake da tsinannen kashi.โ€?

โ€œYasin sai yayi bayan gidah sau uku a rana.โ€? Usmanu dake zaune akan bokiti ya fada.

Ardo dai bai ce komai ba. Yanata sauke zuciya, Sai gumi ne yake sharara a fuskar sa.

โ€œMijin Rumalle kai ne kake wani kamshi?โ€?

โ€œTusa ya saki Mama, Warinta har cikin dakin mu.โ€? Haladu ya fada yana mai gyara silifas dinsa daya tsinke da wutar da suka dora ruwan wanka.

Rankwashi Rumalle ta sakarwa kwanyar kan Haladu ya sosa wajen yana dariya.

โ€œNi banda kamshin turaren dan duwala ba abunda naji, Kuma Idan ma iskar yafitar dan uban ka shine mahaifin ka a yanzu. Yo ba abun ayi masa barka bane ya fitar da cuta. Uwar uban kowa yana yi. Harda mace dake daga hanci.โ€?

Jimmamman sarai tasan da ita take, Don haka bata tanka taba. Idrisu ya fito daga bandakin yana mai gyara tazugen wandon sa. Ai Ardo baisan sanda ya yakice hannun Rumalle ba, Ya shige cikin bandโ€™akin. Na kusa duk suna jiyo zubar bayan gidan sa. Ba shiri suka dare saboda yadda iskar wajen ta maye gurbin bayan gidan sa.

Ardo ya kusa awa dโ€™aya a banโ€™daki, Tamkar yana zubar da kayan cikin sa. Ya dadโ€™e sannan ya fito yana tale kafafu tamkar dan kaciya.

โ€œAngon Rumalle...โ€? Ta kura shi cikin rage sautin muryar ta.

Bai ce mata โ€˜kala ba. Ya hararo โ€˜dakin Dadaa wanda ya zama madadin su idrisu a yanzu. Gaba dโ€™aya sun cika gidan da hirar su, Sai kace yan gidan. Sunata hayaniya da guje guje. Ardo yaja siririn tsaki a kasan makโ€™oshi Kafin ya wuce zaure ya tsugunna. Ya rasa yadda zai yi yaji dadi. Ga wata gudawar na neman zubowa, Ga katsawar ciki ga hayaniyar su Idrisu da suka karadโ€™e gidan baki dโ€™aya.

Atuwa dake cikin daki tafito tana leken bandakin,

โ€œWaye a bayi?โ€?

Jimmamman dake kan shadda tayi shiru.

โ€œWane bankadadden ko bankadaddiyar ce aciki. Anti Amarya kina bayi ne?โ€? Cewar Atuwa.

Rumalle dake tsaye kan Ardo tace,

โ€œAโ€™ah uwargidah. Ga ni nan. Inaga mokadaddiyar can ce.โ€?

Atuwa ta sheke da dariya tana sosa idanunta. Domin sun dinke da Rumalle. Takance ita ba zata ji zafin kishi ba. Jimmamman din ce mai ji. Itace saniyar ware. Gwanin ban tausayi Idan suka sata a baya.

โ€œA hayye landandandan tsann! Ardo...Ardo!โ€?

โ€œMenene?โ€? Cewar Ardo daya zabga uban tagumi yana kallon bango.

โ€œMaganar tambayar su Hajara ne da zaโ€™a zo. Na gayamka su a shirye suke mazajen nasu.โ€?

Ardo yaja tsaki yana girgiza kai,

โ€œMe zanyi aciki?โ€?

โ€œWane irin me zakayi bayan kai ne uban su, Na gayawa su Kawu Tanimu ma su zama a shirye a koda yaushe zasu iya zuwa.โ€?

โ€œBa sai sun zo ba, An basu. Sati na sama Zaโ€™a dโ€™aura auren.โ€?

โ€œHaba Angon Rumalle, maganar uwargidah fa abun dubawa ce. Dole sai kana nan zaa yi tambayar tunda kai ne mahaifin su, Ba Zaโ€™a kawo wani ace shi bane.โ€?

Ardo ya mike ya karkade rigar sa ya fice yana watsa hannu sama.

Yana fita yayi hanyar gada yana mita shi dโ€™aya, Modibbo dake gyaran Inji shida sauran masu gyara suka gayar da Ardon.

โ€œBappah Ina zaka ne? Meya faru kake magana kai dโ€™aya?โ€?

โ€œBari Modibbo, Atuwa ce ke neman chazamun kai, Sai kuma โ€˜yayan Rumallen can masu runtuma runtuman kai, Sai bige bige da tsalle tsalle suke. Sun cika gidah da makota da hayaniya. Duka na hade su na kwashe musu albarka.โ€?

Modibbo ya sassauta muryar sa don saura kada su jiyo su.

โ€œHaba Bappah! Ka dubi girman Allah ka dena kwashewa mutane albarka. Ka kyโ€™ale su da halin su sai Allah ya maka maganin su.โ€?

โ€œHakane Modibbo hakane.โ€? Cewar Ardo, Tare da saka hannunsa ya shiga shafa goshin sa. Da alama dai duniya tafara yiwa Ardo zafi.

Modibbo ya zaro dari biyu duk ta damalmale da bakin man inji ya mikawa Ardo.

โ€œBappah ka sayi wani abun ka ci dan Allah.โ€?

โ€œTohm Modibbo! Allah ya maka albarka, Allah ya daukaka ka. Kaji?โ€?

โ€œAamin Bappah! Amma kayi wa Allah ka dena samun albarka ni dโ€™aya Bappah, Sauran ma duk yayan ka ne Bappah....โ€?

Yana magana Ardo na daga kai Kamar gaske, Modibbo ya cigaba da cewa,

โ€œDukkan mu

Please Login or Register in order to submit comment