Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batamana lokaci.. Ya dube ni kafin ya saki murmushi mai taushi. Yace SO kadai ya isa. Idan ya rike SO to tabbas ya gama da ZUCIYAr Zaraah na. Domin SO DA ZUCIYA abune guda daya Addayo. Daga ZUCIYA aka samo SO. Daga SO ake mallakar ZUCIYA baki daya. Da yardar Allah Addayo SO DA ZUCIYAr Zaraah da Maheer zai bada kala. A turance zan iya kiransa da... Bazan iya fadan kalamen da yake yawan fada ba don da turanci ne. Amman har agaban Na Ikko ma ya ambata da yawan gaske."

"A LOVE SOO BEAUTIFUL!!! " Maheer ya fada ahankali yana goge hawayen dake zuba a fuskar. Wanda gaba daya Yan parlorn shi suke yi

"Zahiri haka yake cewa. Daga karshe yace Addayo inaji ajiki na Zaraah kamar mallakin babban Yaya zata zama. Nace masa ni rabu da ni ba wanda yasan gaibu. Yace nima ba wai na sani bane. Kawai dai sunfi dacewa da juna Allah kuwa. Ni zan samu wata kyakkyawa awani wurin. Ina fatan aljanna ce ma da yardar Allah. Na Zama daya daga cikin samarin aljannah. Yana kai karshe nasa yatsa na dungure masa kai. Hade da rufe murfin motar mukayi gaba. Sai bayan rasuwar sa kalaman sa suka shigaa zagayemun kwakwalwata. Shysa ko da wannan yaron yayi mun magana ya nemi shawarata nace na amince. Domin wasiyyar sudeis ce. Ya kamata acika masa ita

"Amman babu dole Zaraah. Bazamu sbiga hakkin ki ba. A yau dinnan. Kai a yanzu ma da yardar Allah Zan sa na Ikko ya rubuta miki takarda ya sawwake miki.. Allah Kuma ya dubi maraicin sudeis da mukayi baki daya ya baki wanj mijin Wanda zai kaunace ki har karshen rayuwar sa. Kai na Ikko dakko takarda da biro. "

"Wayyo Allah na. Dadaa, Addayo, Bappah ku gafarce ni. Wallahi na amince. Na yadda na Kuma hakura zan zauna da igiyar auren Ya Maheer. Saboda na cikawa Yaya sudeis burin sa. Na kuma bi umarnin da kuka Yi akai na. Allah ya yafe mana baki daya Amman na yadda na kuma amince zan cika burin Yaya sudies na SO DA ZUCIYAr da yake muradin son haduwar wajen zama abu daya. Dan Allah ku gafarce ni. Allah na yarda zan zauna da Ya Maheer din......."

Albarka! Albagka! Godia! Nasiha! Kyauta! Addu'oi babu wanda Zaraah da Maheer basu shaba a ranar daga bakunan Dadaa, Addayo da captain Muhammad Muhammad ..

Duk kuwa da zuciyoyin su Zaraah da Maheer basu aminta da juna ba. Haka aka karashe zaman ranar cikin farin ciki da zuba ruwan addu'oi ga marigayi sudeis ibn Harith . 'Da na biyu ga captain Muhammad muhammad . Kuma 'kani ga Doctor Maheer Muhammad Muhammad.


××××××


A watan da aka saka tariyar Zaraah da Maheer a watanne Maheer tafiyar gaggawa ta same shi zuwa ga kasar saudiyyah. Sai halacci wani taro amadadin marigayi sudeis.

Zaraah amarya an kare makarantar sakanni in dire😂 tayi jamb taci postutme. Kai har ta samu gurbin karatu a jami'ar bayero university dake Kano. Inda zata karanci fannin common and Islamic law,,

Duk wani gyara da akewa amarya Kama daga magungunan sanyi zuwa na jiki da sauran su anyiwa Zaraah shi. Kai harda Maheer dinma Addayo ta kasa ta tsare Yana shan maganin sanyin shima .

sauketa a islamiyya da dakkota ..Kai harda zuwa unguwa. Duk Maheer ya daukewa Zaraah . Baya gajia da yi. Zasu gaysa a mutince. Idan zata unguwa dole saita tambaye shi. Wata rana ya amince. Wataran ya dage gira wajen cewa: Ba inda zaki je😍😂.

Toh a haka dai. Har Allah ya kawo ranar dasu Zaraah suka fara lectures. Mudikalle shi ne direban dake kai Zaraah makaranta ya dakkota. Domin Maheer yayi tafiya. Gyaran gidan da zasu tare ma yanata tafiya.


××FACULTY OF LAW××
(BAYERO UNIVERSITY KANO)


Sati uku kenan da fara lectures din su Zaraah. Malam M2 (M sqaure) Da yan facultyn ke dokin ganin sa tun day 1. Ba shi ba alamar sa .Har anci sati 3.


Zaraah suna class itada su Najwa suna jiran gawon Shanu. Saboda har yau ba alamar zuwan sabon malamin Mai suna M sqaure (M2) har a time table ga sunan sa nan. Bai taba attending lectures


Kwatsam Yan ajin na zaune wasu na tsaye anata hira. Malamin ya shigaa sanye cikin blazer baka. Da pcap. So enticing 😍

"Settle down pls . Head of the class close the doors pls. Silence. Everyone Tear a sheet of paper. Write your reg number and today's date. Then pass the paperz accordingly to the person sitting next to you ... "





XOXOWRITES💯🥰
2/12/22, 11:37 - Buhainat: SDZ❣️

NANA HAFSATU 🧕😍

33

Cikin daddad’ar muryar sa mai kwantar da hankula da nutsuwa . Wanda ya shaki ilimin arabi ya surka da boko. Gwanin ban sha'awa a duk sanda ya bude baki yayi magana. A hankali kuma a nutse cikin lankwasar da muryar sa. Ya sake maimata musu cikin harshen hausa.

‘Ku zazzauna dan Allah, Shugaban aji tashi ka rufe kofofin ajin nan. Ayi shiru dan Allah. Kowa ya yago paper ya rubuta lambar rijistarsa da kwanan watan yau. Sai Kowanne bayan ya rubuta a jere ka mikawa wanda yake kusa da kai..?

“استق? من فضلك. رئيس الفصل يغلق الأبواب من فضلك. الصمت. الجميع يمزق ورقة. اكتب رقم التسجيل الخاص بك وتاريخ اليوم. ثم مرر الورقة وفقًا للشخص الجالس بجانبك ...? ya fada Cikin harshen larabc".

Rassurez-vous svp. Chef de classe fermez les portes svp. Silence. Tout le monde Déchirez une feuille de papier. Écrivez votre numéro d'enregistrement et la date d'aujourd'hui. Passez ensuite le papier en conséquence à la personne assise à côté de vous.. Ya sake fada cikin harshen faransan ci.

Zaraah dake zaune kan kujera. Gefenta kuma Adamancy ce course mate dinta. Dukkanin yan ajin sunyi tsit suna sauraron sa. Yan matan ajin gaba daya hankulan su kacokam sun daura akan malam M2.

Ya yinda Zaraah ke mamakin yanayin muryar sa data ke da tabbacin tayi kama daya data Maheer. Bataji ko taga labarin zai koyar a jami'a . Dan zahiri datace Maheer dinne. Sai kalle shi take daga kafa zuwa wajen fuskar sa.

"Kawata ba dai kin fola ba?" Zaraah tajiyo muryar Adamancy na tsokanar kawar su Zubee.

"Yo ba dole na fola ba. Dan gayu mai zazzakar murya mai kwantar da hankali. " Zubee ta fada.

Zaraah ta girgiza musu kai kawai tana dariya.

Sai da Maheer ya kammala karbar attendance din da class captain ya bashi. Tukun sannan ya daga kansa sama hade da gyara mic din dake maqale a aljihun sa.

Ya fara basu hakuri abisa rashin zuwan sa lectures . Sai Kuma ya shiga bayyana musu sunan sa . Da course din da zai koyar da su.

"Suna na Dr. Maheer Muhammad Muhammad. Wanda a makaranta kuma nan dama sauran wajajen karatu da nayi. Amfi mun laqabin kira da. M2 wato M square . Square din na nufin surname dina Muhammad, other name kuma Muhammad. Sai first M din ta name na nufin Maheer. So zaku iya ko cigaba da kirana M square din,


"Ina da rules and regulations. Doka da ka'idodi. Idan na shigo class ba wanda zai shigo. Bawanda zai fita sai da uzuri. Attendance is compulsory. Kuma individual attendance ne ba general ba. Attendance dinmu 30 marks ne. Open test 10 marks . Sai exams. Oh yes. Presentations zai zama in groups . 5 marks. Then sauran marks din sune na exams. Banda intention din fadar da kowa a exams. Fyace wanda ya karya wannan dokokin.


"Maza zasu koma zama a left row, Mata a right. Banda surutu. Abide my rules . Khalas mafi mushkila. Duk wanda yabi dokokin dana fada. In shaa Allah da A zai fita a exams. As for weeks din da banzo ba. Na bawa kowa 10 marks. Insha Allah briefly yanzu zan fara muku bayanun course outlines din. Zamuyi discussing 3 topics yanzu..duk wanda bai gane ba. Zai iya tambayar inda yake son karin haske. Ni kai na zan iya nuna mutum ince ya tashi ya ban amsan kasa. An gane?"

"Yes sir! " Yan ajin su ka kurma murya wajen amsa shi. Banda Zaraah da ke mamakin ganin sa. Ashe dai shidinne? Kuma a matsayin malamin su na boko? Bayan shugabantar da su da yake a islamiyya. ?

Wani hawayen takaici ya zuraro mata. Don tasan ba makawa sai ya sake takura mata. Don ta lura da gayya yake abubuwan sa yanzu.

Wayar tace tayi 'karar shigowar sak'o. Number kuma bakuwar number ce.

"Dago ki kalle ni. KO na shelanta musu ke matata ce. Wanda aka hadamu aure bama son juna. Idan har baki tsayar da idanun ki akai na ba. Zakisha mamakin abunda zai faru."

Tana karasa karantawa . Ta dubi Maheer da ke podium a tsaye. Yana danna abu wadda take da tabbacin wayar sace daya turo mata sak'o. Ashe har ya gano ta?

A hankali ya zare face mask din fuskar sa. Ya saki tattausan murmushi daya haskaka kyakkyawar fuskar sa. Ba karya ya kara kyau. Gawani gemu da gashin baki da saje daya tara. Sun matukar kara masa kyawu. Cikin daddadar muryar sa. Mai sanyaya zuciya. Ya cigaba da musu magana cikin harshen turanci.

"Zamu fara da topic din rayuwar 'Dan Adam a musulunce. " Bayani ya shigaa yi musu a nutse. Har ya 'karkare ya kamo wani. Da Zaraah ta juyar da kai zai yi tari a yangance. Alamun ta juyo ko ya shelanta.

"Musulunci ya yi matuqar girmama ‘ya mace, ta hanyar ‘yanta da daga zama baiwar da namiji. Haka nan kuma ya ‘yanta ta daga zama ‘yar tsana, wadda ba ta da 'kima ko mutinci . Daga cikin hukunce-hukuncen da suka qunshi mutanta ‘ya mace a Musulunci, akwai:

Yancin Gado: Musulunci ne addinin da ya ba wa mace cikakkiyar dama da yancin cin gado, ta hanyar tsaga mata wani rabo bisa adalci da karramawa.
Yancin Zaven Miji: Haka kuma Musulunci ya ba ‘ya mace cikakken,

" ‘yancin zaben mijin da za ta aure. Ya kuma hannunta mata wani yanki mai girma a fagen tarbiyyar yara. Ga abin da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake cewa a kan haka: “Haka nan mace makiyayiya ce a cikin gidan mijinta. Za a kuma tambaye ta a kan abin da aka ba ta kiyo.? [Buhari: 853/ Muslimu:1829].

"Adireshi:، Musulunci ya tabbatar wa mace cikakken haqqi na cigaba da amfani da sunan mahaifinta a matsayin adireshi, wanda za riqa kiranta da shi. Ma’ana, aure ba zai sa a wayi gari ana kiran tada wani suna wanda ba na mahaifinta ba ko zuri’arta.


"Ciyarwa da daukar Nauyi: Musulunci ya wajabta wa namiji kula tare da daukar nauyin ‘ya mace ta hanyar ciyarwa da biyan dukan bukatunta na yau da kullum, ba tare da gori ba. Matuqar ‘ya mace tana cikin wadanda ciyarwa da daukar nauyinsu suka rataya a kan mutum, kamar matarsa, ko mahaifiyarsa, ko ‘yarsa. To, wannan nauyi ya hau kansa bisa wajabci.


"Taimakon Mace Mai rauni:Taimakon Mace Mai rauni: Haka kuma Musulunci ya qarfafa tare da kwadaitarwa a kan falalar da take akwai a cikin taimakon mace mai rauni, wadda ba ta da kowa sai Allah. Yin haka a Musulunci abune mai kyau, ko da kuwa babu wani zumunci a tsakanin mutum da ita. Tattare da haka addinin ya kwadaitar iyakar zafari a kan yi wa irin wannan mace hidima da dawainiya. Ya kuma bayyana cewa, hakan yana daga cikin manya-manyan ayyuka masu lada a wurin Allah Madaukakin Sarki. Tabbacin hakan kuwa shi ne fadar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: “Mai dawainiya da matar da mijinta ya rasu, da miskiniya, daidai yake da mai jihadi saboda Allah, da mai tsayuwar dare ba tare da ya gajiya ba, da mai Azumin dab da shan ruwa.? [Buhari:5661/ Muslim:2982]..

"Sai matan da Musulunci ya Qarfafa Kula da su,
? ?

"Mahaifiya: An samo daga Abu Hurairata radiyallahu anhu, ya ce:“Wani mutum ya taho wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: Ya Manzon Allah wane ne daga cikin mutane ya fi kowa cancantar in kula da lamarinsa? Sai ya karba masa da cewa: Mahaifiyarka. Ya ce masa: Sai wa kuma? Ya kara masa da cewa: Mahaifiyarka. Ya sake ce masa: Sai wa kuma? ya sake amsa masa da cewa: mahaifiyarka. Ya kuma sake cewa: Sai wa kuma? Sai ya ce masa: sa’annan mahaifinka.? [Buhari: 5626 / Muslim: 2548].

"Haka Kuma an samo daga Uqbata dan Ámirin radiyallahu anhu, ya ce: “Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: Duk wanda yake da ‘ya’ya mata guda uku, ya kuma yi haquri da dawainiyarsu; ya ciyar, ya shayar, ya tufatar da su daga cikin dukiyarsa. To, za su zama hijabi tsakaninsa da Wuta a ranar Qiyama.[Ibn Maja:2669].

Haka dai Maheer ya cigaba da koyar dasu abubuwa da dama. Ya koma kan bangaren maza a musulunci. Ya kare da matakai na mazhabobi da dama. Kafin ya karkare. Ya a'amsa tambayoyin su. yanayi yana satar kallon Zaraah dake kallon sa itama.


××××. ××××. ××××.

Bayan an tashi daga lectures baki daya. Su Zubee sun tafi saboda su a hostel suke, Zaraah ta zauna akan stairs tana jiran zuwan Mudikalle direba. Shiru shiru. Ba shi ba alamar sa. Tagaji ta kira shi. Wayar kare a kunnenta ta nufi titi

"Mudikalle . Na ce yau ba zaka zo bane ko ya ya? Wa? Toh fah. Naji naji. Shikenan. " Ta katse kiran tamkar ta runtuma ihu jin wai Maheer ya bashi umarnin dai na dakkota tunda ya dawo.

Cigaba da tafiya tayi. Tana tafiya tana kalle kallen inda zata samu adaidaira. Sai jiyo karar kutsewar mota da taji.
Ashe Maheer ne. Cikin wata sabuwar anaconda royal blue color.

"Shigo mu tafi," Ya ce da ita bayan yayi kasa da mudubin.

Ta bude motar ta sbiga. Tana turbune fuska. Sam bataji dadin hakan ba . Tana shiga ya ja motar suka tafi. Wayar sace ta fara 'kara. Ya dauka ya kara a kunne.

"Hello.... Gimbiyaa tahh! Me kikace? Lapia kalau . Ya komai? Oh eh eh. Kakki damu kin gama kin samu insha Allah . Yauwa. Ni ne da godia sai na kira. "

Yana katse kiran ya dan kara volume din wakar Baby Riddim. Yana bi ahankali .

Steady your face jor for me
I wanna take a picture
So this could last longer for me (longer for me)
Yeah, take my secrets
Guard them like precious money (precious money)
I never want to hear you quiet
So I write songs for you (write songs for you)
So I write songs for you (so I write songs for you)
And I believe
Yes, I believe
I'm falling for you like a thief
Weak in the knees
'Cause when I see you
I fit to steal the keys to your heart again (your heart again)
Yeah, yes, I believe
Yes, I believe
I'm falling for you like a thief
Weak in the knees
'Cause when I see you
I fit to steal the keys to your heart again (your heart again)
My baby bad
My baby good
My baby all the things I need
My baby buss up the silence o (buss it up, buss it up)
My baby buss up the silence o (buss it up, buss it up)
My baby bad
My baby good
My baby all the things I need
My baby buss up the silence o (buss it up, buss it up)
Buss up the silence o
Steady your face jor for me
I wanna take a picture
So this could last longer for me (longer for me)
Take my secrets
Guard them like precious money (precious money)
I never want to hear you quiet
So I write songs for you (write songs for you)
So I write songs for you (so I write songs for you)
Oppositions they come left and right
But I don't care (I don't care)
Popo fit dey our front, say leave you
But I die there
No more milk or malt
'Cause you are my only strength (my only strength)
Whether rich or poor
I know that you are my best, best, best, best
And I believe
Yes, I believe
I'm falling for you like a thief
Weak in the knees
'Cause when I see you
I fit to steal the keys to your heart again (your heart again)

Yana bi a hankali yana lumshe idanu. Kai daga kallon sa kasan har cikin qalbinsa wakar na tafiya dashi. Zaraah kuwa haka kawai ta tsinci kanta cikin haushin wayar daya amsa. Da kuma wakar da take kyauta ta zaton ta wayar yake rerawa baitin a zahiri. Taja tsakin dabatasan dalilin yin sa ba. Ko kadan bai tanka taba. Sai ma kumshe dariyar da ke son kufce masa.

×××

Har sashen Dadaa ya kai da hancin motar sa. Zaraah ta sauka bayan ta buga murfin motar jikake.. Gwaaaam. Maheer ya saki dariya yana dora kansa kan sitiyarin motar. Ya jima a haka. Kafin ya wuce da motar sashen Addayo . Bangaren su kuma an kammala gyare shi har an masa gate.

Ranar asabar aka saka a matsayin ranar da su Zaraah da Maheer zasu tare agidan su. Anyi furnishing gidan da furnitures masu matukar kyau da tsada. Dakuna 3 parlor biyu. Kowanne da bandaki, Sai dinning area da kitchen da store da balcony (baranda)


×××RIMIN KEBE×××
(GIDAN MALLAM ARDO BORKINDO)

Ta wutsiyar idanu . Ardo ke kallon kwanan abincin dasu Usmanu suke cin shinkafa da wake. Kamshin man kuli sai tashi yake.

Rumalle ta shiga gidan tana kkrga chanjin hannunta.

"Kunga kuwa har ansaye zobon nan. Yauma dire musu nayi na koma gefe suka siye duka."

Ardo caraf ya fito yana yamutsa fuska.

"Rumalle menace miki akan zuwa bakin gada sayar da zobo?"

"Yo Ardo kai ma kasan bazan fasa zuwa ba. Domin kuwa ba zamu ci babu ba. Banda tarin tsiya me ka sani? Sai kallon matan mutane da zuwa tadi wajen kawayen yayan ka."

"Zaki dena fita ko kuwa?"

"Wabillahil lazi bazan Dena ba "

"Toh kije na shika ki. Ki tattara komatsan ki da yaran ki, ki barmun gidah "

"Gi me?"

"Gidah na. Ki fice kafin na dawo. Kin ji na gaya miki."

Rumalle ta yage mayafin dake jikinta ta daura shi a kugu.

"Lalle Ardo. Wohoho. Yaro besan wuta ba sai ya taka. Rumalle nake kaf fanda babu wanda nake shakka. Wannan gidah kamar yadda ka alkanwarta ka bani shi kyauta . Don haka wabillahil kai da matan ka ne zaku bar gidan nan ba ni ba. Idan har kaga an fitar da Rumalle daga nan gidan to la shakka mutuwa nayi aka futar da gawata."

Wuf sai ga Atuwa a tsakiyar su. Don sauri zaninta na kuncewa tana daurewa. Ta kece da dariya tana nanawa cinyar ta duka.

"A hayye landantsan. Allah me alheri. Ai kuwa dai gidab ha badu. A hayye landantsan tsan. "

Ardo ya sharce gumi yana dalawa Atuwa harara,

"Matsiyaciya. Idan ubanki ne ya sai gidan sai ki sani na fita. Allah ya kwashe miki"

"Ya kwashe maka albarka dai. Ba kai aure aure ba. Ana zugaka kana dashare fuska. To ka aurowa kanka. Gida ya badu. Sai a rankaya a koma kauye. Don kuwa ni gaba nayi. Jammu Allah ya dasa mata kwandon arziki tayi aurenta na arziki . Shar da su itada yaranta. "

"Banason wasa Rumalle. Na shika ki sau daya. Kar ki tunzuro na Kara wani shikan akan wani."

"Kara 100 ma. Gida ya zama nawa. Daren farkon mu ka gayamun naje dakin Modibbo na dakko acikin jaka."

"Banda haukan ki a ina ake kyautar gidah sukutum?"

Kafin Rumalle tayi magana. Atuwa ta dire tsallen albarka hade da daga hannu sama ta kwakwaso rantsuwa kai kace ita aka bawa gidan. Ta nanawa cinyar ta duka. Hadi da rangada guda. Ta sauke aiyiriri a kunnen Ardo. Hade da cewa

" A hayye landantsan tsan. Allah mai alheri. Wabillahil Rumalle taci gidah. Kyauta ta badu. Ba Kai zamudin.aure ba. Daren farko ka yiwa amaryar ma kyautar gidan ka jallin jal da Allah ya baka. Hau ta hau Arddo. Mijin Atuwa sahibin jimmamman. Ubansu Zaraah angon Rumalle mai gidah. Kayya kaiiiiiiiiiii"



Masu tambaya. Duk books Dina Banda paid suna wattpad: missxoxo00

Instagram: @yerwaincense_and_more


XOXOWRITES 💯❣️
2/12/22, 11:37 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SO DA ZUCIYA*

*NANA HAFSATU*


*34*


Ardo takaicin Atuwa da ke zakalkalewa yasa shi jan dogon tsaki. Hade da kutuntumo ashariya ya 'dure akan Atuwa.

"Bak'ar munafuka. Allah ya kwashe miki albarka Atuwa."

Atuwa ta sheke da dariya. Kafin ta rangada guda ta saki. Jimmamman na daga tagar wundo tana leken su.

"Ba kai uban aure ba. Kana yiwa Allah shisshigi kan haihuwa. Bakayi maraba da yara matan da kake dasu ba. Ka dau kaunar son yaya maza tamkar su din martabar su daban ce. 'Dayan da Allah ya albarkance ka dashi ka dau son duniya ka dora masa. Ka tsani sauran yaranka mata. Har fada kake a baya kan cewar idan Modibbo ya tashi aure zaka dau gidan nan ka bashi. Mu kuma mu koma kauye ko ka shika mu. Toh gashi nan yanzu hau ta hau kan k..."

"Idan kika kuskura kika karasa magana. Wabillahil sai na hau kan ki da bugu. Munafuka. Yauwa ke kuma Rumalle tsaf zan kai karar ki kotu akan wannan iskar zancen. Mahaukacin ina ne ni da zan dauki kadarata daya a duniya na baki? Ni ba sakarai bane."

Rumalle ta tabe baki. Hade da zaro rake cikin kullin gyalenta tashiga gabtara kada kai.

"Ni ba irin ka ba ce Ardo. Zan iya maka afuwar shikan da ka mun na kyaleka ka cigaba da zaman matan ka har nan da sati biyu kafin ka nemi wani muhallin ku kara gaba."

Ardo cikeda takaicin yadda Rumalle ke magana cikin gadara da isa. Ya zare raken hannunta ya take shi a kasan takalmin sa yana huci. Hade da kokawar zare rigar yar sharar dake jikin sa.

Jimmamman ta sheko a guje ganin zai yi tabargaza agaban yaran sa.

"Cika ni jimmamman. Kyale ni na chasa tah. Har ni zata kawo wa zancen banza. Agidan uwar ubanta na bata gidah?".Ardo ya shiga kokarin zare hannuwan jimmamman dake rike hannayansa. Bayan a zahiri idan an barshi da Rumalle kadai sai ta hallaka shi.

"Cika shi . Kafin na hade da ke na zaune. Agidan uwar ubanka borkindo dake Fanda ka ke. Banda tarin tsiya da abun kunya me ahalin ku ke da shi? Kaf banda ciki da waje dangin ku ne matsiyata. Wanda shanu hudu gare ku duk yawan ku. Wallahi banda kaddara meyasa zan aure ka Ardo?.wallahi ni ba sa'ar auren ka bace. Gidah Kuma ko ana ha maza ha mata sittin ta ubangiji ya zama nawa."

"Jar uban can kai. A hayye landantsan. Allah mai alheri. Yau ana wata ga wata. J"

Kasan gwiwar hannun sa Ardo ya sa kai wa Atuwa bugu a makoshi. Ta rike wuyanta tana kurma ihun zafi.

"Wato ga mareniyar wayon ka ko? Shine daga magana saboda ita tafi karfin ka daketa. Sai ni mareniyar wayon ka. Burbudin kashin duwaiwukan ka ko! Toh wallahi ban yafewa. Kuma Allah ya kwashe maka albarka. " Atuwa ta karasa fada tana mulma wuyan ta da Ardo ya kai mata bugu.

Rumalle ta mike daga zaman da tayi. Ta dau buta tayi hanyar bandaki tana yan wak'e wak'e. Tashige bandaki ba addua ba komai. Ta kwaye mazaunai tashiga kasayarwa tana waka.

" A hayye sama ruwa kasa kudi. A hayye sama kudi kasa ruwa. Wahabu wahidin lillahi. Sama ruwa kasa kudi. Katsina ta dikko ma ana maka ruwa. Sama kudi kasa ruwa. Kaduna ma ana maka r......"

Bata karasa wake waken data ke aciki ba. Ardo ya shigaa cikin bandakin ya janyota ..ko tsarki batayi ba... Domin wakar da take raira baitin ta ta karasa harzuka shi.

"Ba sama ruwa kasa kudi ba. Wallahi yau zakisan ainihin sama ruwa kasa kudi. Baki isa ba kinyi kadan ki cinye mun dukiya dan malafar kan na tsoho me allura na gangaren litiya fanda. Uban kakanki kenan. "

"Cika ni nayi tsarki kai dai kamar sabon tab'i."

"Kin gama kasayarwa acikin gidan nan tunda ba naki bane. Almura da idanu yan kanana a ciki."

Atuwa dake mulmula wuya ta kece da dariya. Kafin ta janyo gallan da Farillatu ta tsinto a shara. Ta shiga kidi tana rausaya kai.

"A hayye landantsan tsan tsan. Durama a gidan Ardo. Akan me? Akan gidan Ardo. Meya faru. Ardodo. Daren farkon su yayi kyauta. A hayye landantsan. Allah me alheri. Ku chasu bamban ku chasu. Ku chasu bame rabaku. "

Rumalle duk Ardo ya gama tukwikwiye ta yana neman bugata da kasa. Rashin wanke duwaiwukan ta da

Please Login or Register in order to submit comment