Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai ma cigaba da rera karatun sa da yayi.

Ko da ya karasa karatun sa. Sam yaki bari su had'a idanu. Saboda tun a baya sun riga sun tsara yadda zasu gudanar da soyayyar su. Akwai ta gidah akwai kuma ta idan suna su daya. Dake kowa na gidah yasan da abunda ke tsakanin su. Hakan yasa sudeis yin takatsantsan idan suna bainar jamaa. A islamiyyar ma suna matukar kokarin 'kin bayyana tsakanin su. Sai dai suyi sak'on rantsattsun aikawa juna sak'o ta idanun su.

Toh yau ma hakan take. Ta kwayar idanun ta ya gano akwai abunda ke damun ta. Don haka ya mata wani kallo mai tattare da ban hakuri da nuna tsantsar kaunar sa gareta.

Ya dan shafa keyar sa yana mata kallon 'kasan idanu.

"Ina matemakiyar Ameerah?"

"Ga Ni ya mu'allim" Asiya ta amsa shi hade da mikewa tsaye.

"Zo ki karbo muku littafan ku"

"Toh ya mu'allim."

Ya fuce yana waiwayon fuskar Zaraah. Data kauda kanta gefe . Ofishin sa ya wuce kai tsaye ya bawa Asiya littafan su. Ya dan zauna a kujera yana mai tunanin daya baro Zaraah acikin sa.

Ganin shima zai shiga damuwar da bai san dalilin ta ba, Hakan ya san yashi janyo littafin fiqhu ya shigaa karantawa. Dai dai lokacin da Maheer ya shigaa cikin ofishin bakin sa dauke da sallama.

"Wa'alaykm salam babban Yaya"

Zama Maheer din yayi a kujera dake kallon ta sudeis.

"Ya nagan ka kai ma yau haka haka?"

"Kai na,, Na ne yake dan ciwo babban Yaya "

"Ko kuma dai dan an daki zaraahn ka dukan latti?"

Tanan sudies ya gano dukan lattin da akayi mata ne ya haddasa mata canzawar yanayi.

"Ko daya. Ita wayace tayi lattin? ai dole a hukunta ta" Ya fada cikin karshen gaskiyar sa. Fuskar sa ta fad'ad'a da murmushin jin ba wani abun bane na daban.

"Ai na yarda da maganar ka lalle tanada zuciya. Dukan sauran yaran ma sawa tayi a mata du baki daya . Nace lalle anyi gwarzuwa." Maheer ya karasa fada yana tabe fuska.

Shi dai sudies ya sake sakin tattausan murmushi kafin yace,

"Ai nagaya maka tanada zuciya. Kawai kokari zakayi ka zare kiyayyarta a ranka. Ka maye masa gurbi da zallar so."

"Zan futa a harkar ka gaskia. Inde muna maganar arziki ka shiga ratattaka maganar halayen ta. Tanada zuciya batada zuciya ba abunda ya shalle ni. Manyan mata ma basu isheni kallo ba bare yar jaririyar ka. Wannan sai kai." Ya karasa yana yamutsa fuska.

"Kayi shiru dai babban Yaya. Sai kag,..ga reshe ya juye da mujiya. Idan Allah yayi Zaraah ce matar ka bay..."

Bai karasa Maheer ya mike da sauri ya fita hade da dankarawa sudies kyakkyawar harara da guzurin dogon tsaki. Sudeis yayi dariya kawai yana girgiza kai.


××××. ××××. ××××. ××××.

Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u.

Cikin lokuta dake ta ja da yardar Allah. Zaraah sun shiga aji uku na karshen sakandire. Biyu ya kamata tashiga. Amma dake tanada saurin girma tuni ta kere yan ajin su a komai

Ta zama cikakkiyar budurwa mai tashen yammatanci. Hakan yasa capt. da kansa yayi shawara da mai makarantar aka sauyawa Zaraah aji zuwa na uku maimakon na 2 . Tuni suka fara shirye shryen zana jarabawar 'kare sakandire.

Zaraah ta kara wani irin madaukakin kyau mai dauke da haske, sheki da Kuma walwalin fata. Tanada kerarren shape mai daukar hankulan jama'a..hakan yasa ko da yaushe cikin hijabi take.

Wata iriyar soyayya suke da Sudeis Wadda ta kai ga har an kai kudin aurenta wajen Ardo. Wanda Rumalle ta cinye rabi da kwatan su.

'ya'yan Atuwa ma an aurar dasu. Cokali Ardo bai saya musu ba. Gidah ya zama sai Atuwa da farillatu da. Jimmamman da yan biyunta. Sai Rumalle dasu usmanu. Rumalle tayi 'barin ciki har sau biyu. Hakan ya sanya Ardo fara cireta a ransa .


°°°°°

Har mota ta rakashi tana cuno baki gaba. Maheer dake gefe yaja tsaki yana maka Mata harara. Itama ta rama hade da murguda masa baki.

"Dalla Malam zo ka ja mota mu tafi. Idan ka dawo kwa cigaba."

Sudeis dake soyewa da Zaraah ya dan daga masa hannu alamar minti daya.

"Me zaki tanadar mun idan zan dawo! Uhm,,, Baby luv? "

Zaraah ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta da suka sha jan lalle.

"Sai ka dawo din dai. Allah ya dawo mun da Kai lapia. Allahumma Aamin"

"Aamin hayateey. Babban Yaya ga amanar Zaraah na nan. Dan Allah ka rike mun ita da hannu biyu. Gatanan amana dan Allah. Zuciyatah da kai daya ta aminta. Kai kadai ne zaka rikemun ita fiye da ni kankin kai na. Kema Zaraah na ga amanar babban Yaya nan. Duk abunda yakeso idan har bai sab'a shari'ah ba ki masa."

Maheer yaja dogon tsaki ya koma mota. Yayinda wasu hawaye suka shigaa reto a fuskar Zaraah. Ta rike murfin motar tana kokarin sanya idanunta cikin nasa. ko kadan bai bari sun hada idanu ba.

"Haba habibi. .. Ni dai gaskia ka daina mun irin wannan maganganu kamar Wanda zai dad'e? Kuma ma karasa wanda zaka bawa ajiyata sai shi?"

Ya girgiza Kai kafin yace,

"Saboda ko nan gaba zaki tabbatar da maganganu na. Ya Maheer bani da na biyun sa wajen kulamin da Ke, Dan Allah ki sassauta kiyayyar da kike masa.. Nan gaba komai zai warware."
Ya karasa fada hade da saurin janye idanun sa daga kanta ya shige motar suka tafi yana daga mata hannu.

Har suka fice daga gidan sannan ta sauke nata hannun da sauri ta koma cikin sashen su da sauri don tenakawa Dadaa su tafi asibiti. Haihuwa tazo gab. Zuciyarta cike da kewar sudeis ta shige dakin Dadaa.

A tare suka shirya Dadaa da taimakon Mai aikin Dadaan. Direba ya jasu sai asibiti. Capt muhd ma hankali arashe ya tafi asibitin.

Dai dai lokacin da Maheer ya dauki hanyar gidah bayan sauke sudeis da yayi a airport. Kai tsaye ya wuce asibitin da Dadaa zata haihu saboda kiran da Capt ya doka masa na yazo yanzu ya ajiye dik abunda yake.

Dadaa tadau tsawon lokaci tana labour. Yayinda likitoci masu karbar haihuwa suka tsaya akanta suna bata temako.

Awajen awanni 3 ta dauka kafin cikin ikon Allah ta sauka lapia. Dai dai lokacin da gidajen talabijin dana rediyo suka shigaa yad'a labarin hatsarin jirgi da akayi. Jirgin emirate daya lula a sama ya fado ya kone. Gaba daya fasinjoji da kowa da kuma komai ya 'kone.

Jirgin kuwa bakowane bane fyace wanda sudeis ya shigaa . Jirgin zai tashi ne zuwa daular Dubai. Inda zasuyi wani taro na musabakar Al'Qur'ani da za'ayi.

Gaba daya Maheer da Capt dake waiting area sai suka rasa tacewa. Maheer ya shigaa laluban number sudeism hankulan su baki daya basa jikin su.

Dai dai lokacin da Zaraah ta isa wajen su dauke da jaririn a hannunta, kyakkyawa kamar sa daya da Capt tamkar yayi kaki ya tofar.

"Bappah ga jaririn"

Hannun sa na rawa. Jikin sa na kakkarwa ya karbu jaririn. Yayinda Maheer ya fucea da sauri. Ambaliyar hawaye sun wanke fuskar Capt. Zuciar sa taki yadda da labarin hatsarin daya faru. Zaraah kuwa ta dauka kukan farin ciki yake.

Ya Kara sa masa hudubar ya mika mara shi dakyar saura kadan ya jefar dashi ahankali yace da ita..

"Rike sudeis yaci. Sudeis ya tafi, sudeis ya dawo. Allah yabamu hakurin rashi" Ya karasa fada hade da fucewa da sauri . Bai jira wani abu ba ya tsare adaidaira sahu yace ta Mika shi airport

Yayinda Zaraah ta koma ciki tana mai sanarwa Dadaa sunan yaro

"Sudeis Muhammad Muhammad"



#A LOVE SOO BEAUTIFUL!!🤗😍
#MAHEER & ZARAAH LOVE STORY
#JOURNEY OF LOVE
#AL HUB HAYATT💯🤗😍
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
2/3/22, 08:32 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SO DA ZUCIYA*

*NANA HAFSATU*


_28_


Dadaa ta 'dan kalli jaririn tana mai datse labbanta saboda tsananin yadda take jin ciwo kadan kadan.

"Ina bappan su Sudeis?" Dadaa ta tambaya sanin baya minti kalilan nesa da ita.

"Yafi ta da sauri bayan ya rad'a wa jaririn suna."

"Okay Allah ya dawo dashi lapia."

"Aamin Dadar mu. Dadaa yaron nan fa da bappan su Sudeis yake kama. Amma idanun ki ya dakko ."

Dadaa ta dan kallo gefen zaraahn tana mai saukar da idanunta akan jaririn kafin ta janye da sauri. Saboda gaba daya samun cikin jinsa take tamkar wasa. Sai bayan yafito ta tabbatar da gaskene. Domin gaba daya aranta tacire zancen kara haihuwa. Shekaru goma da yan kai kenan bata sake haihuwa ba sai yanzu. Ta Kuma samu albarkacin samun 'da namiji.

"Dadaa yunwa fa yake ji. Kinga Yana faman tsotsar hannun sa."

Dakyar da sudin keya. Dadaa ta karbu yaron. Ji take tamkar ruk'o aka bata. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskarta.

Dai dai lokacin da wayar Dadaan dake hannun Zaraah tashiga 'kara.

"Bappah ne."

"Toh kawo'' Dadaa ta karba cikin sanyin jiki, Domin gaba daya tasan tabbas ba lapia ba. Abunda zai sa Capt yayi nesa da ita. Arana mafi farin ciki agare su, Lalle koma menene abu ne babba wanda ba yadda za a iya tsallake shi.


Cikin sanyin jiki da murya ta daga kiran sa. Tamkar Koda yaushe tashiga gayshe shi cikeda girmamawa da kuma madaukakiyar kulawa agare shi.

Shidin ma capt a nasa bangaren yana zaune shida Maheer ne a airport inda ake kokarin gano gawawwakin don mika kowanne zuwa ahalin sa. Hawaye ne ke kwarara a idanun na captain yayinda wani daga cikin ma'aikatan ya dakko burbushin wani sashe daga hannun rigar da Sudeis ya saka. Sai agogon sa da kyallen ya tukwikwiye shi. Tanan suka gano tabbas sudeis kwanan sa ya kare. Babu sauran wata sheda data nuna shidin ne. Ba yaga wannan sashi na hannun rigar sa izuwa agogon sa.

"Jon wuro (Mai gida) Kayi shiru, Meya faru?" Dadaa ta tambaye shi cikin tausasshiyar muryarta mai dauke da damuwar da zuciyar ta tashiga. Na halin da yake ciki.

"Zaraah na kusa da ke?" Ya tanbayeta a sanyaye yana kokarin daidaita muryar sa dake sarkewa saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.

Tuni Dadaan ta hasko akwai matsala don haka bata nuna yadda zaraahn zata gane ba tace dashi.

"Eh! Alhamdulillah"

"To kisa tatafi wani wajen ba tare da kin nuna mata wani abu ya faru ba. Sudeis ne... Allah ya masa rasuwa." Yana karasa fada ya katse wayar..

Tuni jikin Dadaa ya fara kyarma. Ta ajiye wayar a hankali tana kokarin saisaita kanta ta yadda Zaraahn ba zata 'dago wani abun ba.

"Yan biyu suna makaranta ne?"

"Eh kin manta da safe muka Kai su ni da Ya sudeis?"

"Oh eh! Toh kinaji komawa gida zaki ki dakko musu kayan gidah ki wuce makarantar tasu. Sai ku shirya ku tafi can rimin kebe. Kya gayawa Haj Mari ma."

"Yanzu Kuma Dadaa? Wani abun ya faru ne?" Ta tambayi Dadaan tana mai kokarin gano wani abu.

"Mezai faru? Nan dinne cika zeyi. Kuma kinga ace su Atuwa ba suji ba ai ba dadi ko?"

"Dadaa a kirawo su mana ta waya."

Wani kallo Dadaan ta watsa mata na ta shigaa taita yin ta. Ai kuwa Zaraah ba tasake cewa komi ba. Ta shiga harhada yan kayanta a jaka.

"Kwana zamuyi acan din?"

"Ko zuwa dare ko yamma haka. Kwa gayda mutan gidan."

"Zasuji insha Allah."

Saurin fucewa tayi daga dakin. Yayin da Dadaa ta rufe fuskarta da tafukan hannayen ta . Wasu zafafan hawaye masu dumi suka shigaa yar tsere a fuskarta.

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. Ya Allah kafimu kaunar Sudies. Yaa Allah ka jikan sudeis ka gafarta masa kurakuren sa. Allah kasa yana aljannar ka mai girma firdausi. Yaa Allah ka bamu hakurin rashin sa. SubhanAllah!!"

Daada ta karasa tana mai sharce hawayen dake diga daga idanunta. Wanda har sai da suka shigaa sauka akan fuskar baby sudies da take shayar da shi.

"Hajia akwai abunda za'ayi?"
Harira mai aiki ta tambayi Dadaa.

"Babu komai harira."


××Koda Zaraah ta futa wucewa gida tayi kai tsaye kamar yadda Daada ta umarceta. Jikinta gaba daya yayi sanyi. Jinta take tamkar mara lapia. Saboda tsananin yadda gabanta suka Yi lakwas. Bugun zuciyarta ya tsananta.

Hailala tashiga Yi ahankali har takarasa shiga gidah . Kai tsaye ta wuce sashen da yake matsayin nasu. Ta duba dakin Yan biyu ta dakko musu kaya kala 'dad'dai.

Sam bata 'bata lokaci ba ta kullo sashen nasu ta tafi titi kai tsaye. Motar da take amatsayin ta sudies ce ta yanko kwanar titin da zai sadaka da gidan Capt muhd. Wanda Zaraah ke a tsaye a bakinsa tana jiran wucewar dan sahu.

Sai da gabanta ya fadi lokacin da motar ta tsaya a daidai saitinta. Maheer ne ya tsaida motar hango ta da yayi. Daga makabarta yake ta airport road. An rigada an hade mamatan waje daya an sallace su an kuma binne su. Sakamakon babbakewa da sukayi. Ba ta yadda zaa gane wannan shine wa ne.

Kifa kansa yayi akan sitiyarin motar, sautin muryar sudeis na masa gezo a kwakwalwar kansa . Ya matse hawayen dake sharara a idanun sa. Ya sake daga kansa ya sauke a fuskar Zaraah dake tsaye a gaban motar tana danna yar wayarta Nokia mai fitila.

Sake gaba yayi da motar daidai saitin ta ya tsaya yana mai zuge glass dinta. Ta daga kai ta dora akan motar. Caraf idanun su suka hadu. Sunyi wani kallo na yan wasu dak'ik'ai kafin zaraahn tayi azamar dauke nata tana jan siririn tsaki.

Maheer ya samu kansa da jin haushin tsakin data yi masa. Wani 'kasan na zuciyar sa ya saisaita masa ita. Kafin ya dan mayar da kansa gefe. Ya zaro gilashin sa dake cikin aljihu ya zura a fuskar sa. Saboda wani kuka dayaso kufce masa. A duk sanda ya daga idanu ya dora akanta. Sudies kawai yake hangowa da kalaman sa na karshe akan amanar Zaraah .

Fucewa yayi bayan ya bude murfin motar. Ya zagaya ya bude mata kofar baya.

"Shiga na kai ki inda zaki je." Ya fada muryarsa na rawa. Saboda ya baro Dadaa da Capt a asibiti Kuma Dadaan ce ta sheda masa yadda sukayi da zaraahn.

"Bazan shiga ba.."

Ransa matuka gaya ya sosu amman saboda amanar ta da Sudeis ya bashi hakan yasa ya sake daurewa ya rike murfin motar,

"Dan Allah kiyi hakuri ki shiga... Zaraah" Ya karasa hadi da jan sunan nata cikin wani salo mai taken rarrashi.

Girman Allah daya ambata. Hakan yasa Zaraah shigewa cikin motar bayan ta aika masa da sak'on murguda baki.

Ya shige motar ya tada ita. Sai da yahau kan titi tukun sannan ya dan rage sautin karatun dake tashi acikin motar .

"Ina zan Kai ki?"

"Makarantar su yan biyu "

Bai ce komai ba ya wuce kansa tsaye. Dakyar yake ta kokarin danne damuwar dake cikin zuciyar sa na rashin dan uwan sa sudeis .

Yana karasa tsayawa a kofar makarantar Zaraah ta bude ta fita. Shiga ciki tayi tadan jima saboda sai data tsaya suka sauya kayan su zuwa na gidah.

Suna fitowa taga Yana nan inda ya faka bai tafi ba.

"Sanabe" Ta furta tana yamutsa fuska.

"Adda manga ba motar zamu shiga ba?" Suka hada baki wajen tambayar ta. Sanin motar ta sudeis ce.

Bata amsa su ba. Illa rike hannun su da tayi. Raheelah a hagu Na'eelah a dama. Ita Kuma tana tsakiyar su. Suka cigaba da tafiya zuwa titi. Yayi reverse da motar ya shiga binsu a baya. Ya Sha gaban su ya tsaya.

"Ku shigo na ajiye ku"

Zatayi magana kenan yai saurin katseta,

"Dan Allah ku shiga."

Sarai ya gano lagwanta. Don haka bata sake musu ba. Suka shiga cikin motar. Su a baya, Na'eelah a gaba.

"Ina zamu je?"

"Rimin kebe."

Danna map yayi dake jikin screen din motar ya rubuta address din. Take map tashiga nuna masa hanya har suka karasa rimin keben.

"Karfe nawa Zan dawo daukar ku?" Ya tanbayeta a hankali Yana sauke zuciya.

"Dare."

Ya juya kan motar ya dauki hanyar asibitin da Dadaa take. Ya dako su Dadaan suka koma gidah. Nan gidah ya shiga tunbatsa da mutane yan zaman makokin sudeis da kuma barkar baby sudeis da aka haifa.


********.

Suna karasa shjga layin su da yayi gaje gaje da kwata. Suka fara jiyo ihun sautin Ardoo. Yanata magiya.

"Wayyo Allah na. Dan girman Allah Rumalle kiyi hakuri. Ki yafemun. Qur'anin ubangiji mak'oshi na zai dagargaje. Da kwankwaso na. Na tuba Rumalle."

Wannan Ife ifen Ardoo ketayi tundaga farkon layin ake jiyo shi. Suka karasa shiga ciki yayinda jimmamman ke kofar dakinta tanawa Asabebiya kktso. Atuwa kuwa na tsaye tanata dadarawa bakinta jambakin gyatuma radau. Sai kallon fuskarta take a mudubin dake hannunta na fashashshiyar hoda .

Ashe Ardo lefi yayiwa Rumalle. Dan kwua ya kirb'a Usmanu da duka akan ya siyar masa rediyon sa. Ashe Rumalle na rike da abun a zuciyarta .shine ta zaune Ardo akan gado tahau ruwan jikinsa. Hadi da shake masa wuyan sa.

"Ah wargajalle mutanen gayu. Yau June agarin?" Cewar Atuwa dake kokarin yafa mayafinta.

Gayshe su duka suka yi. Yayinda Atuwa ta sake 'daga katuwar muryarta ta saki gud'a tare da cewa,

" A hayye landantsan. Allah mai alheri. Ku samu waje ku zauna. Bana bappan naku ya dakko ruwan dafa kansa. Iya karbar fanushiman (purnishment) wajen Rumallen sa."

Ta karasa hade da yaye labulan dakin Rumalle. Sai ga Ardo ya hada gumi sharkaf Yana kakarin mutuwa. Ganin su ne yasa Rumalle sauka daga Kansa.

"Tashi ka tafi. Sun fanshe Ka. Gobe ka 'kara maimaitawa. "

Atuwa tasheke da dariya tana duban Ardo daya di'iba aguje yayi waje. Dariya ta shiga yi sai datayi mai isarta kafin tace,

"Jammu wannan karon bata baku'dan kayan dadin nan ba?"

"Nama manta, Dadaa ta haihu dazu ba jimawa. An samu namiji."

Jimmamman ta saki kifiya tana mikewa tsaye. Suka hada baki wajen tambayar su,

"Namiji?"

Ai atuwa bata samu bakin magana ba, Sai guda data sake saki tayi waje tana nanata,

"Dole ne Ardo yaji Wannan dadd'adan zance. "Dan qundun uba, Kai Kai a hayye landantsan, shagali budiri wan dinner. Wabillahil lazi har gada zanje na sanar masa. "

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
2/4/22, 07:42 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SO DA ZUCIYA*

*NANA HAFSATU*


*29*


***Atuwa na ta zambad'a sauri a hanya tana kalle kallen lungu da sak'o wajen nemo Ardo. Don shelanta masa haihuwar Jammu .


Can gefen gada ta hango shi. Ya tsayar da zabbau me awara suna tad'i. Ta sauke bokitin awarar a tsakiyar su. Shi kuma Ardoo ya choge daga gefe yana zuba mata zance. Yayin da zabbau ke rike da gammon dora awarar a hannu tana jujjuya shi. Sun lula sosai a fagen zancen da suke. Sai ga Atuwa ta isa wajen su. Ta duk'a ta dau awara guda da daya ta cusa a baka.

"Ina kudin awarar da kikaci?" Cewar zabbau. Hade da mikawa Atuwa hannunta alamar ta chanke mata kudinta.

"Zabbau kenan. Ko Adaman shehulle (mahaifiyar zabbaun) na goya ta a baya bake ba."

"To ni meye ruwana aciki? Kawai kiban goma ta. Gaskia."

"Uban iyali. Malam Ardoo saurayin kawayen 'yayan sa. An gayda Ardo uban iyali. Nazo maka da daddadan labari. Amman kafin sannan biya mun goman awara dana ci ."

Harara Ardo ya dankara mata kafin ya zaro nera goma daga cikin nera 80 din dake aljihun sa ya mikawa Zabbau me awara. Atuwa taja guda tasaki hade da shewa.

" 'karuwa muka samu Ardodo."

"Ta mai fa? " Ardo ya tambayi Atuwa cikin kade kunnuwansa don jin daddadan labarin karuwar da suka samu.

"Jammu ce ta haihu."

"Jammu kuma? To meye garin gami na da ita?"

"Kayya bakacin ribar zance Ardo. Sai gani nayi abun atayaka murna ne tunda anyi zaman mutinci da kuma yalwar arzikin 'ya'ya a tsakanin ku. Gashi kuma garin ku 'daya"

"Ina sauraron ki. Wannan rawar kan da kike. Ko sunan ki aka sawa jaririyar ne?"

"Ka ji ka da wata magana. Na gayan ka abunda ta haife ne?"

"Yo ai nasan ba zai wuce hakan ba "

"Toh sanin ka bai fadi daidai ba "

"Toh uwar yan kanzagi. Ya akai?"

"Kai dai bari Ardodo. Sa goshinka bisa kasa ka fara yiwa Allah godia."

Ardo ya washe baki. Take zuciar sa ta hasaso masa kilan auren Dadaa ne ya mutu takeson jimmamman din ta roka mata shi. Ya mayar da ita dakinta.

Take ya goho ya duka yayi sujjada bayan ya dubi gabas. Wandonsa har sab'ulewa yayi. Ya janyo shi ya mayar come da jin dadi . Ya girgiza kai cike da jin dadi yace da Atuwa.

"Ai shika da nayi ba uku na shika ba. Idan ma ukun nayi ai tayi auren kisan wuta ko?Yo dama su Usmanu ne a dakin, Sai su futa daga ciki. Kice mata tadawo dakinta da zarar tagama id.."

Bai karasa fada ba. Jimmamman tasaki katuwar dariya tana jujjuya kai.

"Angon Rumalle mijin jimmamman. Na Atuwa bada kanka asare. Kaga uban iyali baban su Usmanu. Nifa du zancen nan ca zan maka Jammu ta haife 'da namiji charan chas Ardodo"

Ardo ya ware idanu. Cikin rawar jiki da baki yace da ita.

"Sharota kikayi ko Atuwa?"

"Wane irin sharota Ardo? Ba karya nake ba. Yanzun zuwan su Zaraah ai zancen haihuwar suka taho dashi. Kazo muje ku gaysa kaji da kunnen ka."

Ardo dake tsaye yana fuskantar Atuwa. Cikin manyan kaya, 'kirar riga Yar shara shudi'ya da wando . Duk kayan sun cukwikwiye saboda azabad chasar da Rumalle tayi akansa. Duk ya kara figewa ya jeme. Ya koma tamkar tsoho. Yace da ita,

"Allah dai ya kwashe miki albarka Atuwa. La'an"

"Karka soma la'ance mun. Da yardar Allah sai dai kaga kwashewar albarka akan ka. Aikin kawai." Ta karasa fada, Hadi da buga tsakiyar zaninta ta watsa hannu sama tana mai surfawa Ardo bak'ar magana.

Ardo ji yake tamkar ya fad'i kasa yayita birgima saboda tsananin yadda zuciar sa ke masa rad'adi. Wai Jammu ce ta be haife namiji?

Yaje ya dawo haka ya dinga safa da marwa akan gadar rimin kebe . Can ya samu gefen wani dakali ya zauna bayan ya zabga uban tagumi. Duk wanda ya wuce sai ya kalle shi. Ganin bayan tagumin daya zabga harda 'karin magana shi kadai. Yana nuna sama ya nuna kasa. Tamkar mai kirgen bulan gini.

Liman zai wuce yaga Ardo a zaune yana magana shi daya tamkar zaucacce.  Fasa tafiyar yayi ya dawo gefen Ardo ya taba kafadun sa.

"Malam Ardo lapia kuwa?"

"Na'am jammu!"

"Jammu kuma? Malam Ardo."

Sai a sannan Ardo ya dawo hayyacin sa ya dubi liman dake mika masa hannu suka gaysa.

"Ya mutan gidan kowa kalau?"

Ardo ya

Please Login or Register in order to submit comment