Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ma ya bayar da tasa gudunmawar wajen taimakon wadansu. Shi bayar da dan kadan saboda Allah, idan mutum ya gan shi a Ranar Lahira zai yi ta mamakin yadda ya kai haka don girma, saboda Allah Yana kiwata masa shi ne a wajenSa, matukar dai abin da ya bayar din ya same shi ne ta hanyar halal.

"Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya bayar da wata sadaka (ko kyauta) daidai da dabino daya na halal ? domin Allah ba Ya karbar komai, sai mai tsarki (halal) ? Allah Zai karba da hannunSa na dama, kuma Ya kiwata (Ya tattale) shi, kamar yadda dayanku yake kiwon maraki har ya zama bajimi ? to Allah zai tattale shi har ya zama kamar girman tsauni a Ranar Lahira.? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

"Don ya kare mutane daga juya baya da kuma runtse idanunsu wajen bayarwa saboda Allah, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci su bayar da sadaka komai kankantarta. In sun yi haka, za a samu kyautatawa da tausayi da rangwame da shaukin juna a cikin zukatansu da kuma tsakaninsu. Ya gargade su da su guje wa rowa da kankame dukiya, a hana ta zagayawa tsakanin jama’a mabambanta, lamarin da yake haifar da jafa’i da bala’i a tsakaninsu, a yayin da ya ce, “Ku kange kawunanku daga Wutar Jahannama ko da da bayar da kyautar (ko sadakar) rabin dabino ne.? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

"Allah Yana son Musulmi ya zama na kirki, mai amfani ga al’ummarsa, wanda kuma yake taimakawa a samar da kyakkyawa kuma kwakkwarar al’umma, wadda kodayaushe tana cikin alheri, ko Musulmin nan yana da wadata ko talaka ne shi. Wannan dalili ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya karsasa Musulmi ya kasance mai kyauta cikin kyauta-yi, gwargwadon iyawarsa da karfinsa, domin kowane irin aikin kwarai sadaka ne, inda ya ce,

“Kowane Musulmi lallai ne ya bayar da sadaka.? Sai sahabbai suka ce, “Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), to in mutum ba zai iya haka ba fa?? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi aiki da hannunsa ya samu abin da zai biya wa kansa bukata kuma ya bayar da sadakar!? Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi kokarin taimaka wa wanda yake cikin halin kaka-nika-yi (wato yake cikin tsananin matsi)!? Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?? Sai ya ce, “Sai ya yi wani abin kirki, ya nisanci mummuna, wannan zai kasance masa a matsayin sadaka.? Buhari ne ya fitar da Hadisin. Musulunci ya yalwata da’irar kyauta-yi ta yadda ta hade kowane gefe na rayuwar Musulmi! Wato in ka rasa wannan abu, to da wuya ka rasa wancan! Wanda yake cikin talauci, ko kadan kada ya karaya ya ce ba shi da abin da zai bayar ko ya yi, wanda zai samu martabar mai kyauta ko sadaka. Matukar dai ya mayar da hankali wajen yin abin da za a kalla a ce madalla, to yana matsayin kyauta ko sadaka, wadda za a ba shi gwaggwabar lada a Lahira, saboda maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada, wadda Imamul Buhari ya fitar cewa, “Kowane irin aikin kirki, sadaka ne.?

"Musulunci ya bayar da tabbaci ga kowa cewa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa wajen gina al’umma, ya karfafe ta, ya ciyar da ita gaba a harkokin yau da kullum ta yadda za ta kasance natsattsiya kuma tabbatacciya, wadda kowa zai yi alfahari da ita, alhali a karshe zai zama ya ci kyakkyawar riba. Allah Ya sa mu dace!

"Musulunci adalin addini ne mai rangwame ga matsayin kowane Musulmi. Bai dora wa kowa, sai abin da zai iya dauka. Bai cewa mutum ya bayar da dukiyarsa ma, sai dai daga abin da ya ci ya rage. Ba ya zargin mai kadan. Ya ma fi son kowa ya samu damar biya wa kansa bukatarsa, domin hannun sama ya fi hannun kasa (wato mai bayarwa ya fi mai karba matsayi)! Amma dai duk abin da ya yi saura, to (Musulunci) yana kwadaitarwar a yi kyauta da shi cikin kyauta-yi, saboda shi Musulmin kirki ba ya kankamewar abin hannunsa, ya yi rowa, domin ya koya daga addininsa na Musulunci cewa bayar da sadaka (da kyauta), abu ne mai kyau, alhali kankamewa da rowa, abu ne mummuna, kamar yadda Hadisin da Imam Muslim ya ruwaito ya fada cewa:

“Ya kai dan Adam, idan ka bayar da abin da ya yi saura na dukiyarka, abu ne mai kyau gare ka; idan kuma ka ki bayarwa, ka rike abinka, to abu ne mara kyau gare ka. Babu zargi a kanka don ka rike abin da kake da bukatarsa. Ka fara bayar da kyautar ga wadanda suke makusantan bukata gare ka. Ka sani, hannun da ke sama ya fi hannun da ke kasa (wato ya fi kyau ka bayar da ka karba)!?

"Musulmin kirki ba ya mantuwa wajen yin kyauta cikin kyauta-yi, musamman wajen bayarwa daga cikin abin da yake saura a hannunsa, bayan ya fitar da bukatun kansa da na iyalansa, ko da cikin irin ajiyar nan ta shirin ko-ta-kwana, ko kuma ajiyar da za a ce an kirga shi cikin mawadatan al’ummarsa.

"Toh wanan duk romon fashin baki ne kan kyauta da kuma kyaauta yi a musulunce. Saboda shari'ah da zamu yanke tagaba akan haka taken ta yake. Sai mu dawo Kan shari'ar ku. Na gidah da malam Ardo miji ga Rumalle. Yayi kyautar gidan sa kacokam ga Rumalle. Inda Malam Ardon ya musanta zahiri lallen gaskia bai bata kyautar gidansa ba. Hasalima shi bayada masaniyar sanda yayi kyautar bare tabbacinta. Duk kunyi alwalar ai ko?"

"Allah me alheri. Yau ana kwal landantsan. Kan balastin kayya kai. " Cewar Atuwa dake zaro idanunta kur akan mai shari'ah.

"Duk wanda ya sake magana cikin ku zai yi waje. Ku kamar kananun yara." Cewar masu tsaron kotun.

"Yauwa. Bazan iya yanke hukunci kai tsaye ba. Saboda nan kotu ce ta musulunci. Don haka kowanne cikin ku Ina nufin Ardo da Rumalle. Zakuyi rantsuwa kan tabbacin bayarwar ko akasin haka. Daga nan sai mu yanke hukunci. Domin zama daya za'ayi wa shari'ar ku. Tunda abune na cikin gidah. Sai ku sasanta sauran a tsakanin ku. Basu qurani Anas."

Anas ya dakko da hannu biyu ya fara mikawa Rumalle. Ta rike gam. Ta kwarara magana da karfi .

"Ni Rumalle. Na rantse da Quran mai girma da ke hannu na. Ardo mai gidah na . Yabani kyautar gidan Sa da muke ciki da bakin sa ya fada. Yace takardar mallakar gidan na dakin Modibbo a cikin jakarsa. Ai kuwa kwan biyu da takardar a hannu na kaiwa mai unguwa ya ajiye Mun. Saboda gudun rana irinta yau. Wabillahil kaf dangin su Ardo ya Mai shari'ah makaryata ne. Kakansu har yabar duniya shata ake Kiran sa saboda sharara karyar sa. "

"Amma Rumalle Allah ya kwashe miki albarka. Ke bama ke kadai ba. Tun daga kan iyannani mai fura gyatumar uban ki. Na hadaku duka na kwashe muku albarka. Matsiyaciya yar matsiyata. Wabillahil lazi na 'kara Miki wani shikan akan 'dayan. "

"Kottttt (court) Ya isa. Kada Wanda ya sake magana acikin ku. Ke tunda kin gama jeki. Kawo qur'anin. Kai Kuma zo ka karba."

Ardo ya karasa da sauri har Yana tuntube ya fadi. Wandon ya Yi kasa zai Fadi. Atuwa dake bayansa tayi saurin mikewa ta gyara masa..

"Cikani dalla. " Ya buge hannunta. Ya karasa ya karbu qur'anin da hannu biyu . Gumi ya shjga kwararo masa duk kuwa da yadda ake sanyi. Saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki .

"Na rantse da qur'anin da ke hannuna ya mai shari'ah. Ni Ardo borkindo . Ban bawa Rumalle gidah na ba. Kaji Allah. Banda masaniya ko sa'ilin da akai haka yallabai. Wabillahil lazi karya take. "

"Da tarnatsa shi ke karyar. Makaryaci ne. Jak"

"Kotttttt! "

"Anas karbi qur'anin ka mayar inda yake. Ku kuma ku zazzauna. Hukunci biyu ne zuwa 3. Domin wata shari'ar sai a lahira. A dan ilimin da ke cikin kai na . Hukunci na farko shine gidah bai kyautu ba. Domin wanda keda mallakin abunda aka kyautar yace bayda masaniyar sanda akayi. Na biyu dole ne malam Ardo ya bawa Rumalle wani dan kaso na cikin dukiyar sa. Ba wai ina nufin ya bata wani sashe a gidan ba. Kudi daga dubu 5 zuwa 7 . Banda kasa da haka. Zai bata ne a matsayin lasa mata zumar da yayi na kyautar gida dayace ya bata acewarta kenan. Iyakacin abinda zan iya yankowa kenan a matsayin hukunci daya zuwa na 2. Sai hukunci na uku. Dole ne Ardo ya fara bawa Rumalle hakuri abisa kyauta da yayi ya kwace acewarta.

"Haka Kuma dole Rumalle tabawa Ardo hakuri abisa kagen kyauta da yace ta masa. Cikin lafuza masu dadi da girmamawa kasancewar shi din miji ne agare ta. Toh duka duka anan zan tsaya . Allah yasa hukuncin da muka zartar ya zama shine mafi adalci da Kuma kyautawa. Abunda muka yanke ba daidai ba. Muna neman yafiyar ubangiji. Allah ya yafe mana baki daya... Ayi hakuri dika dan Allah. Duk Wanda akawa ba daidai ba. Sai aje gida a sasata. Akuma cigaba da zaman hakuri da juna"

"Kotttttt!!!"

Suka hada baki wajen fada. Banda Rumalle dake hawayen takaici. Ardo kuwa dadi ne ya mamaye shi ya dubi Rumalle ya gasa mata harara.

Alkali ya koma ciki. Yayinda Anas da saura suka tsaya kallon ban hakuri tsakanin Ardo da Rumalle.

Ardo ya bawa Rumalle hakuri . Yayinda Rumallen sai da aka kada aka raya sannan ta bashi hakuri a gatsine. Ta kuma dire tsallen albarka kan lalle ya bata kudin da alkali yace a bata.

Ardo ya fuce da sauri bayan an samu me tsaro dake biye dashi karya gudu. Wajen Manumi me wanki ya wuce ya ranto dubu biyar ya koma kotu ya bawa Rumalle .

Anan mai unguwa ya samu waje ya zaunar dasu duka ya ja musu kunne Kan zamantakewar aure. Hakkoki da sauran su. Ya Kuma jawa Ardo kunne Kan karya kuskura ya sake shikan wata daga cikin matan sa uku.. jimmamman nada igiya daya. Yayinda Rumalle keda daya itama.sai Atuwa dake da igiya biyu.

Ya sake jan kunnen Ardon kan lalle dole ya tashi ya nemi sanaa. Ko da kuwa ta karfi da karfe ce.

Ranar dai a kotu har kusan yamma suka kai. Rabiu miji ga Hajara dake aikin majistra a kotun shine yazo shi wajen su ya kwashi gaisuwa..Atuwa nata saye fuska wai ita kunyar siriki.

Ya sassayo musu lemon kwalba kowa daya da cincin din Muhsina me cincin din yan gayu dake rimin kebe. Daurin murtala kowa. Ya kuma sake bawa Ardo gudar dubu kyauta wai a sayawa iyali kayan Miya. Ya wuce da sauri Ardon nata doka masa godia yana dashare baki

"Allah me alheri. A hayye landantsan. An gayda Ardo do mijin Atuwa. Mai dakin jimmamman angon Rumalle..ubansu Zaraah . Nace yau ga ranar 'yaya mata ka fara gani. Sirikin 'yarka ya saya mana lemon kwalba da cincin din Muhsina. Ga dubu ya baka. Wabillahil lazi sai ka sayawa Farillatu biredi me yamka yanka...."

Ta karasa fada hade da wafce dubun tayi hanyar shago kai tsaye ..

"Wata da kwanaki 3. Rabo na da mai yanka yasin sai na ci "cewar Atuwa tana tafe tana jan Farillatu da hannu. Yayinda Ardo ke biye da ita yana zunduma mata Kira

"Kede Atuwa ko bankadaddiya. Idan Kika duaki abunda yafi nera 100 sai kin biyani. "

Jimmamman na bayansa tafe da yan biyunta. Yayinda Rumalle ke mita ita kadai tana saukewa alkali kwandon Allah ya isa na.gidan dayace bai kyautu ba.


××BAYERO UNI. KANO××
(FACULTY OF LAW).

Dr. Msquare na.........










XOXOWRITES 😍
2/17/22, 11:27 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p

PLS FOLLOW US ON IG🥰🙏JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO



SO DA ZUCIYA!!

ZAFAFA 5 PAID BOOKS❣️

PG: 37


××Yana karasa parking ya bude ya fita. Zagayawa yayi da sauri ya budewa Zaraah kofa. Ta fito tana yan waige waige karta hango wani daga yan ajinsu.

Maheer na sane ya shigaa matsawa gabanta. Tana baya harta kai jikin kofar motar.hade da sa hannuwanta biyu ta kudundune jikinta.

Ta kuma dartse idanunta gam. Maheer yayi dariya. Hade da saka yatsan sa daya ya lakuce kumatunta. Bayan ya hura mata iskar bakin sa ahankali akan gashin idanun ta. Wadda ta haddasawa Zaraah bude idanun nata tana kallon sa cike da mamaki.

Ya maze fuska kai kace bashi yayi hakan ba.

"Matsiyaciya. Wuce ki shige sarkin tsoro. Calm down nan entrance din malamai ne banda student yar kanwata ."

Ai Zaraah bata bari ya sake cewa komi ba. Tayi gaba da sauri tana cin tuntube. Gabanta na tsananta bugu. Saboda tsananin yadda ya sauya lokaci daya tamkar marigayi sudeis ..

Tana zuwa tawuce wajen zama ta zauna. Ba jimawa sai ga kawayen ta sun zo suma suka zazzauna. Theory and practice in Islam course suka fara yi. Wanda barrister koguna ya dauke su. Sai lectures din karshe ta 2-4 itace ta Maheer.

Ya shiga ajin a nutse cikin takunsa na takama da kasaita, Ya danyi addua kafin ya tsaya akan podium din. Idanunsa na kan Zaraah dake kokarin avoiding kallon sa .

Ya dan sauke atishawa ta yadda zata gano yana nufin ta fuskance shi. Tukun sannan ya fara koyar dasu kai tsaye..

"Sharia, Musulunci doka ko shari'a doka mai addini dokar kafa bangare na Musulunci al'ada. Ya samo asali daga hukunce-hukuncen addinin Musulunci, musamman Alkurani da hadisi . A cikin Larabci, kalmar shar'ah tana nufin "dokar" Allah madawwamiyar ikon Allah kuma ya bambanta da fiqh, wanda ke nufin fassarar ilimin dan adam. Yadda ake amfani da shi a wannan zamani ya kasance batun jayayya tsakanin masu tsattsauran ra'ayi na musulmai da masu ra'ayin zamani.

"Shari'a :Legal order (en) Fassara da academic discipline (en) Fassara
Bayanai, karamin bangare na
religious law (en) Fassara da law (en) Fassara, Gudanarwan qadi. en) Fassara da Islamic jurist (en) . So Karatun gargajiyance na fikihun musulunci yasan hanyoyin sharia guda hudu: Alqur’ani, sunnah (ingantaccen hadisi), kimanta (dalilai na misali), bayanin kula 1 da ijma (juridical yarjejeniya). Makarantu daban-daban na shari'a - wadanda suka fi shahara sune Hanafi, Maliki, Shafi'i, Hanbali da Jafari - hanyoyin dabarun samar da,

" hukunce-hukuncen sharia daga hanyoyin karatun ta hanyar amfani da tsarin da aka sani da ijtihad. Hukuncin gargajiya (fiqh) ya bambanta manyan hukunce hukuncen shari'a guda biyu, ʿibādāt (al'adun gargajiya) da muʿāmalāt (alaƙar zamantakewa), waɗanda tare ke tattare da batutuwa da yawa. Hukunce-hukuncensa suna da alaƙa da matsayin dabi'a gwargwadon ka'idodi na doka, [8] [9] sanya ayyukan zuwa ɗayan rukuni biyar: na wajibi, shawarar, tsaka tsaki, ƙiyayya, da haramun. Don haka, wasu wuraren sharia sun hade da masaniyar Yammacin Turai yayin da wasu suka fi dacewa da rayuwar rayuwa daidai da nufin Allah...."

Bayani ya shigaa yi musu sosai. Bayan ya kammala ya shiga amsa tambayoyin su kafin ya karkare ajin da basu aikin group assignmt . Ya fuce bayan ya turawa Zaraah sak'on.

"Ki fito mu wuce."

Sai da yadan jima da futa tukun sannan Zaraah ta fita a sace. Wuf ta shige mota suka dau hanya.

Wayar sa ya janyo. Ya danna Kira,

"Hello!! Gimbiyar mu. Ya kike? Alhamdulillah wallahi. Kina gidah? Okay toh bara na karaso. " Yana katse kiran ya juya kan motar zuwa hanyar masarautar basannabas.

"Ina zamuje Kuma?" Zaraah ta tambaye shi . Ranta a bace tarasa meyasa takejin haushin wayar da yayi da gimbiya don renin hankali .

"Rakiya zaki mun. Kinji? Wajen g..."

"Na sani naji ai. Gimbiya" ta karasa hadi da juyar da kanta gefe.

Maheer ya danne dariyar dake son kufce masa. Ya sanya hannun sa kan faifan sidin wakar larabawa da ake fasaarawa da yaren turanci. Yana bi ahankali yana girgiza kai cikin nutsuwar da wakar ke sanya shi. Ga wani sanyi dake ratsa shi na musanman.

"حبيبى وانا جنبك
7bebe oo ana jnbk
my lover when you are near me

تعرف بحس بايه
t3rf b7s b2eeh
do you know what i feel

وانا فى حضن قلبك
oo ana fee 7'9n 8lbk
and when i'm between your arms

ببقى عايز اقولك ايه
bb8a 3ayz 28ool eeh
do you know what i want to tell you

يا محلى الدنيا وانا جنبك
ya m7la l.donya oo ana jnbk
the world became really beautiful when i am next to you

يا كل منايا محتاجلك
ya kol monaya m7tajlk
you are all my wishs i really need you

حبيبى يا عمري متسبنيشش
7bebe ya 3omre ma tsmnesh
my love , my life don't leave me alone

وحيات اغلى حاجه عندك
oo 7yat a'3la 7a8h 3ndk
for the sake of the most precious thing you have

حبيبى النهارده لازم تعرف
7bebe l.nhrda lazm t3rf
my lover today you have to knew

حبك عملى جنان
3obk 3mlee jnan
that your love makes me crazy


انا بحبك بحبك .. حب محبوش انسان
ana b7bk b7bk .. 7ob ma 7bosh ensan
i love you i love you .. love that no one before felt it


اه يا حبيبى
ah ya 7bebe
my lover

وما يحرمنيش منك
oo ma y7rmnesh mnk
and you always stay with me ( the closest translate (

وما يبعدنيش عنك
oo ma yb3dnesh 3nk
and i never be separated from you


يا محلى الدنيا وانا جنبك
ya m7la l.donya oo ana jnbk
the world became really beautiful when i am next to you

يا كل منايا محتاجلك
ya kol monaya m7tajlk
you are all my wishs i really need you

حبيبى يا عمري متسبنيشش
7bebe ya 3omre ma tsmnesh
my love , my life don't leave me alone

وحيات اغلى حاجه عندك
oo 7yat a'3la 7a8h 3ndk
for the sake of the most precious thing you have...."

Kofar katafaran gate din aka bude musu. Ya shige da kan motar ciki.

"Ina ne nan?"

"Masarautar basannabas. Zamuje sashen gimbiya... Khadija matar amini na. Sarki Aliyu salmanu . Mudikalle direba ai yayane awajenta. Mahaifiyar Sa tana auren mahaifin gimbiya kafin rasuwar sa....."

Haka kawai zaraah ta samu kanta da daga kai alamun okay. Ta fito daga motar suka wuce Kai tsaye. Waya ya Kira khadijan. Take aka budemusu sashen suka shigaa.

"Ranki ya dade gimbiyar mu. Yau dai ga Zaraah nace bari na kawo Miki ita?" Cewar Maheer daya Kare Zaraah Yana gayawa gimbiya Khadija dake sakkowa daga bene.

Ta kasa boye farin cikinta. Da Sauri ta zagaya ta rungume Zaraah ajikinta..

"Yau an kawomin ke Yar kanwata. Da har nayi fushi. Mai martaba baya kasar shysa banzo ba. Zo ki zauna."

Taja hannun zaraahn suka zauna. Yayinda Balkin haladu ta kakkawo musu kayan Dadi ta jere agaban su.

"Zaraah ko?"

"Eh" Zaraah ta daga kai ahankali.

"Masha Allah ! Sunana Dijama. Oganniya yar baffanta. Ko ince Miki dijangala Yar baffanta ta gajiyalle Mai Yar hakiya...................
2/17/22, 11:27 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p

PLS FOLLOW US ON IG🥰🙏JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO



SO DA ZUCIYA!!

ZAFAFA 5 PAID BOOKS❣️

PG: 38

××38×××

×××Zaraah tayi dan murmushi kawai hade da daga kai alamun toh. Maheer dake gefan su sai kallonta take tamkar zai hadiyeta. Jin 'kaunar Zaraah yake na suka masa magudanar jiki da bargo.

"Zaraah ko baki dauke ni a matsayin Yaya bane?" Dije ta tambayi Zaraah. Hannunta kan na zaraahn.

"Na dauka mana."

"Toh ki saki jikin ki. Ki dauke ni tamkar yayar ki. Duk abunda ya shige miki duhu da yardar Allah idan har befi karfin ilimina ba zanyi kokarin na yaye miki shi. Ko da kuwa oga Maheer ne da laifi zamu seta shi. "

"Ko dai take bani tough time ba. " Maheer ya samu kansa da gayawa dije haka.

"Aa. Gaskia ban yadda ba. Ana kallon Zaraah ansan saliha ce. Kai da aminin naka ai halin ku daya. Hakuri zamu yi tayi da ku. "

"Haka zaki cema?"

"Yo ai gaskia ne. "

"Toh shikenan. Allah ya saka mana" ya karasa fada yana daria.

"Kanwata zo mu koma dayan parlorn muna bukatar privacy gashi wa'e ya zuba mana idanu. "

"Wa'e ma tashi zai yi ya baku waje. " Ya mike tsaye yana kallon Zaraah.

"Tashi ki masa rakiya kanwata. Da safe zakazo ka dauketa amma ko?"

"Idan ta jima awa biyu."

"Wallahi baka isa ba." Cewar dije. Tana daria.

Kamar gaske Zaraah ta mike tabi bayansa. Dai dai fita kofar waje ta choge.

"Menace miki acikin mutane uhm? Zaraah. Kiyi magana ," Yana magana yana jagaba kusa da ita.

Zaraah ta kasa cewa komai saboda yadda kwarjinin sa ya dabaibaye ta baki daya.

"Matsoraciya" ya fada Yana lakuce mata hanci.

Shigewa mota yayi . Yayinda Zaraah ta koma ciki wajen dije. Data bararraje tana dama kwalba a kofi.

"Har kin dawo?"

"Eh... Ranki ya.."

"Amin amma karki karasa dan Allah. Naface ki dauke ni amatsayin yayarki. Kuma aminiya tunda mazanmu ma aminai ne. Kinganni nan ni bakina baya shiru, kiyi hakuri "

"Haba sis ki dena cewa haka" cewar Zaraah a kunyace.

"Wallahi kuwa. Ci abincin dan Allah. Ni kwalba zan sha. Ku yan gayu bakwa sha."

"Nima ba yar gayu bace sis."

"Ah yar gayu ce . Ni kuwa cikakkiyar yar kauye nake. Kauyen durbun . Haihuwa da tashin kauye. "

"Nima haka."

"Aa wallahi. Kede CI abincin dan Allah. Alhamdulillah yara basanan bare su hanaki ci da hira. "

"Inason yara wallahi. Suna ina?"

"Sunje gidan kawu na. Gaba daya na tattara na kai su . Dama babansu bayanan . So nake na wargaje na huta ni daya"

Zaraah me zatayi ba daria ba. Tashiga dariya sosai

"Yauwa ko kefa? Saki jikin ki sosai agida kike. "

Haka dai Zaraah da Dije sukayi ta yar hirarsu. Bayan Zaraah tagama cin abincin. Dije ta rakata dakinta tayi alwala sukayi sallah. Sannan suka haye kan kujerun dakin suna cigaba da hira.

"Maheer yace kina bashi tough time. Yar kanwata meyasa? KO har yanzu marigayi sudeis yana cikin ranki. Nasan yana nan. Hakuri zakiyi Zaraah ki cigaba da masa addua. Kisa aranki taki kaddarar kenan. Kuma kin karba da hannu biyu.

"Meye laifin Maheer? Hes nice, attentive , and most caring. What more could you want in a man than Maheer ? Allah ne ya kaddara Maheer shine mijin ki ba sudeis ba. Sudeis dai yayi sharar fagene kawai. Allah yayi ba mai zama bane a duniyar . Da Maheer da Sudeis duk abu daya ne Zaraah. Shin Zaraah gaba daya meye ma auren uhm? Barin gaya miki ko ni maimartaba bashi nakeso yake so na ba. Ke nida saurayi na na baya har yaran da zamu haife mun samu suna Zaraah ahaukanmu. Nan duniya a lokacin bakiga yadda muke kaunar juna ba. Bantaba kawo wa a duniya bashi zan aura ba.."

"Shima rasuwa yayi?"

"A'ah! Ai da rasuwar yayi ma da dan sassauci. Yana raye ingaya Miki. Tawa kaddarar kenan daga zuwa taron sauka kinsan ni yar jarida ce abaya. To anan dai Allah ya kaddara mai martaba zai ganni. Haka banda masaniya aka daura mun aure dashi Ashe wai shine. Ke ko fuskar sa bantaba gani ba. Nasha gwagwarmaya acikin gidan nan na sarauta Zaraah. Idan nace zan fayyace miki komi sai kinyi kuka Zaraah. Nasha wahala ba kadan ba. Allah ya rubuta ni ce zan zamo tamkar KIBIYAR AJALI (littafina na baya) da zata tarwatsa duk wani tuggu na masarautar basannabas Zaraah .

"Gaskia sis kinsha wahala Ashe?"

"Tab Zaraah ai wasu abun ba zasu fadu ba. Da sannu Zan sanar miki komi iNsha Allah . Amman yanzh dai Zaraah inason ki rungumi kaddarar auren ki da Maheer. Tabbas auren ku da shi alkhairi ne Zaraah . Barikiji zaraah, Aure yana daga cikin manya-manyar huldodi wadanda Musulunci ya qarfafa tare da kwadaitarwa a kan yin su. Ya kuma gaya wa duniya cewa, sunna ce ta Manzanninsa.,

" Zaraah! Musulunci ya kula matuqa tare da mayar da hankali a kan wannan ibada ta aure. Inda ya fitar tare da shimfida hukunce-hukunce da ladubbanta. A hannu daya kuma ya tsara haqqoqk kowane dya daga cikin ma’aura a kan dan’uwansa, domin hakan ta ba wa wannan alaqa damar ci gaba da tabbata da dorewa. A haka har yanayin tsarin zaman gida ya zama mai nagarta, ta yadda zai iya samar da ‘ya’ya masu natsuwa da kwanciyar hankali, da rayuwa a kan addini. A hannu daya kuma su zama zarata a gaba dayan fannonan rayuwar al’umma na yau da kullum. Zaraah . Kina ji kuwa ?"

"Ina ji sis ..."

"To ki temaka ki ajiye marigayi sudeis a gefe addua ce mafi kusanci yanzu tsakanin ki da shi. Sai Kuma ki juyo ki fuskanci mijin ki da Allah

Please Login or Register in order to submit comment