Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauke zuciya yana girgiza kai

"Ina cikin makauniyar kaddara liman "

"Toh pah! Ta mecece malam Ardo?"

"Mata ta dana shika a baya ce tayi aure wai harta haife da namiji yau."

"Shine kake zaune kana bayani Kai daya kamar sabon tab'i? Iyye?" Liman ya karasa fada tare da zama kusa da Ardo.

"Wacce matar taka. Ai wanda ka shika sunada yawa. Wacce daga ciki?"

Ardo ya daga kai zai yi magana sai ga Asabebiya kawar jimmamman data mata kitso. Ya zuba mata idanu yana binta da kallo harda lek'ar da kansa . Zai mike liman ya zaunar dashi cikin takaici.

"Meye haka?"

"Liman Asabebiya naga ta kara murjewa. Carkwadi. Yar na'innatuwa ce ko?"

Liman yaja dogon tsaki. Yasa hannun sa ya bige yatsun Ardo dake nuna Asabebiya .

"Mahaifinta aminin ka ne ko liman?"

"Buhun uban ka Ardon nace buhun uban ka. Asabebiya shekaran jia waccen aka daura mata aure da Ansari me kyamis a farin masallacin unguwar yan doya "

Ardo ya rafka uban salati yana jimami.

"Amma Allah ya kwashewa An.."

"Karka karasa. Kowa ma kwashe masa albarka. Dama inason zuwa wajenka zuwa na musanman. Amma tinda yauma mun hadu ai shikenan. Ina fatan kana saurarata!"

Ardo ya kada kai yana mai duban liman sosai

"Ina jinka yallabai."

"Yauwa dattawan rimin kebe na gada mai doyi dana yan farin masallacin unguwar doya. Da hayin yin bola dana yan dusar hayi. Sunyi zama sosai akan ka."

Ardo sanin ansaba hada masa kudi yasa ya mike ya zube akan gwiwoyinsa yana barbadawa liman godia.

"Godia nake liman. Karamcin ku yayiwa kalamai kadan wajen zayyano godia ta agareku. Ka ciri dubu aciki a siyawa iyali kukar miya. Akuma mikawa dattawan mu godia kafin nazo da kai na."

Liman ya yi murmushi yana kambama karfin hali da nakasar zuciya irinta Ardo.

"Ba kudi bane Ardo . Atakaice dai dattawan sunce ba Kai babu Karin aure ba bu Kuma shika. Domin ka yiyyi na farko ka Kuma yi na karshe. Sannan dole ne ka tashi ka nemi Sanaa ardo. 'dan ka namiji daka laru akansa. Allah yafika kaunar sa ya karbu abinsa. Don haka dole ma tashi tsaye akan iyalin ka. Ka cire zancen aure ko shikar sa. Domin an shatale maka layi akansa ba zaka ketare ba. Kuma sunce idan kak'i aminta da dokokin su to ka tattara kabar unguwar rimin kebe.

"Sai a biyu na biyu. Wannan magana ce zan maka jan kunne akanta Ardo. Ka cire mayatar son haihuwar 'yaya maza a ranka. Kai lalle a dole Sai ka samu namiji ? Wacce iriyar rayuwa ce haka? Kai bakasan yawan haihuwar 'yaya mata bama alkhairi ce sannan Kuma arziki ne. Banda kai da gaulancin ka ai 'ya'ya mata sunfi jin'kai. Mazan me sukeyi ? Inada su har 5, Amma kafin su kyauta ta mun. 'ya 'ya matan dake gabana sun temakamu. Hakama wadanda ke gidajen auren su duk suna kyauta ta mun fiye da 'kartin mazan da nake dasu guda biyar . Saboda haka kayiwa kanka fad'a,

"Ka rungumi yaranka da iyalinka a matsayin taka kaddarar kenan. Sai kaga Allah ya yaye maka ya Kuma buda maka lamuranka Ardo. Yanzu kamar ayace kagani akanka. Ka shikata tayo wani auren ta haifi namiji. Don haka Wannan ya zama izina agare ka malam Ardo. Allah ya jikan Modibbo ya raya wanda suke raye da albarka. Allah Kuma ya buda musu su temake ka da al'umma baki daya. Aamin,"

"A,,,min" Ardo ya amsa a rarrabe. Zuciyar sa na matukar masa zugin hukuncin da aka yanke masa.

"Da kun kyale na shika rumale. Liman a ruwan ciki na ta zauna tana mun shakar mutuwa. Ga gand'ama gand'aman yara har 3 da ta dawo dasu. "

Liman ya hankalci dimuwae da Ardo ya shigaa , don haka ya shigaa tausasar zuciyar Ardo. Har sai da ya tabbatar damuwar Ardon ta ragu sannan ya zaro nera dari biyar ya mika masa

"A kula da iyali a sayo musu kad'in miya ko dan nama ne a watsa musu . Nima albarkacin 'yaya na mata naci. Zannirah ce ta aikomin da dubu biyar dazu."

"Masha allah! Allah ya saka da khairan."

"Amin Ardo. Tashi ka tafi gida dan Allah Kuma ka rika Jan girman ka kana kokawa da matan ka ko cacar baki shysa suka renaka. Ka ja girman ka don Allah Ardo."

Ardo dai tinda ya dafe kudin sa a aljihu ya mike. Ya dauki hudubar liman wata Kuma ya zubar da ita awajen. Kai tsaye ya wuce layin yan dusa wajen gaddafi me gurasa da nama. Yasa aka yanka masa gurasa da naman sa na dari hudu ya sayo leman roba na dari ya shigaa dannawa a baka yana korawa da lemon sa.


×××××××.

Zaman makoki sosai akeyi a gidan na Capt muhd. Anata kawo abinci daga makota da yan uwa hadi da abokan arziki. Ataya Capt jimamin rashin sudeis dansa a Kuma yi masa barka da samun baby sudeis.

Kusan duk wani makusanci ga ahalin capt muhd. Sai daya shigaa cikin rudanin babban rashin sudeis da akayi. Yaron kirki mai tarbiya da dimbin ilimi. Mutuwar lokaci daya.

Maheer ya shigaa matsanancin rudanin rashin sudeis. Tunda ya zauna akan runfar da ake makokin baya tashi sai dai idan zaayi sallah ya mike yabi jam'i ya koma ya zauna. Maganganun sudeis da suka zama tamkar wasiyya kwakwalwar sa ke tariyo masa duk sakanni.

"Babban Yaya na baka amanar Zaraah na. Kai kadai na aminta da kai wanda zai rike mun Zaraah tsakani da Allah . Ka cire kiyayyar zaarah a zuciyar ka. Ka tarairayeta babban Yaya. Zaraah batada matsala saita zuciya. Dan Allah idan tahau kai ka sakko. Ka koya mata so da abunda ya 'kunsa."

Yana tunanawa Yana hawaye. Ashe wasiyya sudeis ya bar masa? Hawaye nata kwarara a fuskar sa. Dakyar ya mike cikin sanyin jiki ganin takwas harta wuce da rabi. Kai tsaye ya dau mota ya dauki hanyar rimin kebe. Wannan zuwan ma da temakon map ya karasa unguwar.

Almajiri ya tura gidan yace akirawo su Zaraah su tafi. Yaran ya shiga ya fito,

"Wai suna gidan gate. Gidan Haj Mari ."

"Kasan gidan ?"

"Eh"

"Muje ka rakani."

Almajirin ya shigaa gaban motar suka tafi har gidan Haj Mari. Yaci saa kuwa har sun fito zasu tafi.

"Zaraah...ku shigo mu tafi"
Ya fada Yana mai zuge glass din motar .

Gaban Zaraah ya fad'i don dadi, saboda da farko sai taga kaman sudeis ne. Don tanata jiran kjransa taji shiru. Ganin Maheer ne yasa tadan yamutsa fuska tamkar tamai shegen duka.

"Zaraah! Shigo mu tafi don Allah."

Ta bude gidan baya ta zauna. Yayinda raheelah tashiga gaba. Na'eelah kuma tazauna kusa da Zaraah. Ya hau titi yanata tafiya ahankali. Yanata sak'a yadda zaa sanar mata rasuwar sudeis. A haka suka karasa gidan .

An share makoki ganin dare yayi kowa ya tafi. Na gidah na gidah Kuma sun koma ciki. Yana gama parking suka fice ko kallo bai isheta ba.

Yanayin yadda ake shara adaren ne ga plates ma'aikata anata wanke wanke yasa Zaraah jin jikinta na bata wani abu. Suka shige sashen na Dadaa Kai tsaye. Yan biyu suka sheka wajen baby sunata kallon sa.

Dadaan dai tana zaune tayi jigum. Kallo daya zaka mata kasan ba lapia ba.

"Dadaa meya faru?"

Dadaa tayi shiru tana auna yadda zata sanarwa Zaraah. Harira dake gefe tayi caraf cikin azarbabi tace,

"Wannan ne ya rasu a jirgi sudens (sudeis )"

Zaraah ta saki wata gigitacciyar kara tafadi a kasa sumammiya.

"Gaskia harira an gayshe ki. Sam baki iya fadar mutuwa ba. "

Da sauri aka kwashi Zaraah sai asibiti. Likitoci suka shiga bata temakon gaggawa.. Ta farfado amma bata magana. Sai ambaliyar hawaye dake sharara a fuskarta.

Hakika zukatan mutane da yawa sun shiga rudani na halin da Zaraah tasamu kanta aciki. Ba cin abinci ba magana sai kuka kawai. Drip aketa durka mata sai allurori. Abinci ko ambata sai ta amayo dashi.


°°°°°. °°°°°. °°°°°.

Ranar suna ba'ai shagalin suna ba. Illa dai rad'in sunan da akayi a masallaci. An Kuma yi yanka. Kowa yabi jariri da addu'oin alkhairi. Allah kuma yasa ya gaji mai sunan sa.

An sallamo su Zaraah daga asibiti. Amman tamkar an sauya zaraahn baya zuwa ta yanzu. Duk wata walwala da take tadena. Kullum cikin kuka take. Da sallolin nafilfilim har abada hannunta rike da charbi tana adduoin saman aljanna ga sudeis mai kaunarta.

Kullum tana zaune a 'daki. Ba ruwanta da kowa da kuma komi. Dama sauran yan gidan sun debu Karan tsana sun dorawa Dadaa da iyalinta. Musanman yanzu data samu albarkacin haihuwa.

×××

Dadaa na zaune tana kallon baby sudeis dake saka hannun sa a baki. Yara duk sun tafi makaranta. Capt muhd ya shigaa parlorn bakinsa dauke da sallama.

Dadaa ta gayshe shi cikeda girmamawa. Ya amsa Yana mai daukar baby sudeis a hannun da.

"Su Maijidda sun shigo kuwa?"

"A'ah! Amman inajin basa nan don na je dazu kofofinsu a rufe."

Capt muhd ya girgiza kai kawai yanawa baby sudeis wasa. Kafin yace,

"Ki rabu dasu. Dama zaman TAKUN SAAKA nake dasu ai. Kema Kuma ba zasu so ki ba saboda kina kaunar su Maheer da marigayi sudeis . Kinsan meyasa?"

"A'ah"

"Saboda basa kaunar ci gabana. Sun so su halaka matata wadda tarasu. Wato mahaifiyar sudeis . Yayar babar Maheer me rasuwa. Sun so su halaka ta saboda tasamu albarkacin 'da namiji. Suna cewa wai nafuson ta. Da Kuma abunda ta haife. A shekarun baya suka shirya wani tsari da zai zama anyi hatsari gaba daya daga Jamila da Maheer da Sudeis din duk su mutu.

"Dake Allah adali ne. Sai gashi naje fandan. Ta roke ni Kan zasu kara kwana. Ashe direba an kunce notocin cikin motar anan fandan suka aika wani ya tsara komai. Washegari muka shirya Ni da ita da yaran biyu wato sudeis da Maheer. Muka dakko hanyar gidah. Wanda nayi waya dashi a karshe kawu na ne Harith. Lokacin da hatsarin ya taho mana muna waya dashi. Ya jiyo sanda motar ta kwace muka fada wani kurgurmin rami. Kai na ya bugu. Airbag takare su Maheer Allah yayi sunada kwana a gaba. Ta murfin mota ashe ya bude Jamila ta fada ramin ta rasu. Ni daganan bansake sanin inda kai na yake ba. Ashe take na shigaa coma aka kaini asibiti a Qatar. Da taimakon kawu na da muke waya shi ya gano komai.

"Maijidda da Iklima ba matan kwarai bane Jammu. Ba wai Ina gaya miki bane don kitsane su. No ki barsu da halin su kamar yadda Addayo ke fada. Badan Addayo ba wabillahil lazi dana sakesu duka. Tunda har sun san su had'a Kai suyi kokarin kashe mun mata da yara. Wadda sukazo suka same Ni da ita. Yar uwace agare Ni. Gari daya da komai. Akan kaunarta gare ni da yadda na dora raina akan Maheer saboda rashin mahaifiya da yayi. Ashe zagwan kasa suke su kashe su. Yaran su su gaji gado ko? Saboda yaransu su girma su rike companies dina ko? Saboda haka daga yau Ni da Addayo da yaran mu zaki aminta dasu. Babu ruwan ki da sabgar wa'incan. Inaso a karshe ki bani dama na aurar da Zaraah ga Maheer domin zumuncin mu ya sake kulluwa Jameelah. Banason Zaraah ta sani Kuma Kinji? Kin amince?" Ya karasa Yana mai fashewa da kuka.

Dadaa ta mike ta koma kusa dashi tana hawayen itama,

"Insha Allah bappan su . Da yardar Allah komai yazo karshe. Allah Kuma ya cigaba da kareku baki daya. Allah Kuma ya jikan su da rahama baki daya. Bappan su Zaraah ai 'yace awajen Ka. Don haka kanada dama da Kuma girman iko ga duk abunda ka zartar akanta ya halasta...."

Ya Kai mata runguma mai ratsa jiki. Dadaa na kashe shi da salo kala kala. Sai dayaji zuciyar sa ta Sarara tukun sannan ya mike ya nufi sashen maheer. Ya same shi da maganar zaraahn. Maheer bai turje ba. Don shi kansa so yake ya cika amanar sudies duk kuwa da bayason zaraahn

×××

Cikin sati na gaba, capt muhd ya tashi da kansa bisaga jagorancin Maheer suka nufi rimin kebe da Alhaji dangoje. Suka zanta da Ardo dake dama an karbi kudin sudeis don haka atake awajen bayan anyi sallar la'asar. Aka daura auren'

Maheer muhammad muhammad da amaryar sa Zaraah Ardo borkindo, akan sadaki mafi daraja💯❣️


#unedited 💯
2/7/22, 09:08 - Buhainat: _SO DA ZUCIYA!!_

_30_

_ZFF2022__
_(PAID NOVELS)_

_NANA HAFSATOU❣️_

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________

×××Ana daura auren Maheer ya samu gabansa da matsananciyar bugawa. Ya saka hannun sa a hankali yana mai dafe saitin zuciar sa. Take wasu zafafan hawaye suka shigaa reto a fuskar sa. Alhaji Dangoje da Ardo sun fita izuwa farfajiyar masallaci suna mai rarrabawa mutane goro da alawa da dabino.

Capt muhd ya sake matsawa kusa da Maheer. Domin gaba daya tausayin 'dan na sa ya sake dabaibaye shi. Ya rasa mahaifiya tun yana jariri. Kanwar mahaifiyar sa da rikon sa ya koma hannunta itama tarasu abisa tuggun da kishiyoyi suka yi. 'kani kuma 'dan uwa mafi kusanci agare shi shima Allah ya karbu abun sa.

Maheer bayada kowa yanzu. Sai Capt muhd da kuma Addayo. Kasancewar kakanninsa na bangaran uwa dik sun rasu, Yan uwa ma fulanin tashi ne. Ba wanda keda masaniyar inda suka nausa.

Ya dafa kafadar sa yana mai mika masa hankicin dake hannun sa.

"Kayi hakuri Maheer. Ka yafe mun na yi saurin zartar da umarni akan ka batare da na baka lokaci kayi shawara ba. "

Maheer ya goge hawayen dake tsiyaya a idanun sa sannan yace,

"Bappah bakamun komai ba. Ai ko da ace bansan Zaraah ba. Bantaba ganin taba. Kuma ka auramun ita. Dole ne zan zauna da ita har karshen rayuwata bappah insha Allah. Dan Allah ka dena bani hakuri. Hawaye kuma da nake bappah ba akan auren nan bane. Su Inna natuno da sudies. Na tuno da yana raye da dashi zaa daura . " Ya karasa fada yana mai fashewa da kuka gwanin tausayi.

Capt ya shigaa bubbuga bayan sa yana bashi hakuri. Shima hawayen ne ya shigaa zurara a nasa idanun. Yai saurin kauda kai don ma kada Maheer din ya gano shi.

"Allah ya fi mu kaunar su Maheer. Addu'oi zamu cigaba da musu. Allah ya gafarta musu. Ya bamu hakurin rashin su. Hakika munyi babban rashi amma babu yadda zamuyi Maheer. Kayi hakuri kaji. Duk da bana shakku akanka nasan zaka rike Zaraah amana. Don Allah Maheer kada ka bari shedan ya shigaa tsakanin ku. Kuma kaga sai a hankali sabon ta da kai. Wannan daurin aurenma batada masaniya. Idan lokaci yayi za'a sanar da ita. Amman dai kayi kokari ku saba da juna tamkar yadda suka shak'u da marigayi..," Capt ya karasa hade da saurin goge hawayena dake neman fashewa ya koma kuka .

"In shaa Allah bappah."

"Yauwa to share hawayen naka ka tashi mu tafi."

×××Ardo dake leken su Capt daga waje ganin suna shirin futowa hakan yasa shi saurin yafito su garzali abokan sa.

"Ku zo ku gaggaysa da surikin nawa."

Ya janyo hannun Maheer da fitowar sa kenan daga cikin masallacin.

"Zo ku gaysa da abokai na." Ya fada yana mai nunnunawa Maheer su da yatsa.

"Wannan garzali ne uban Adama kawar Zaraah, Wannan shine Mati jatau me kayan gwari, Wannan kuma akilu ne uban su Hannafi abokin Modibbo. Wannan kuma sabitu ne me gidan wamka da bahaya. Wannan kuma inusa ne dan uwawwu me kosai. Can wa'incan dake tsaye ajikin bishiya kana ganin su?"

Maheer ya kada kai alamun eh

"Toh ubale ne me gurasa, Sai liman, da kuma 'Dan tani me ice."

"Masha Allah" cewar Maheer da ke kakaro murmushi.

"Yauwa shine mijin zaraahn yar awaje na. Sunan sa Masheer "

"Maheer ne bappah "

"Yauwa Masher. Mahaifin sa matukin jirgin sama ne a baya. Gashi nan shima. Sai aminin mahaifin nasa gashi can shi Kuma attajirine . Usulin sa dan kauyen Dangoje ne dake fandar mu. Yo duka ma dai yan fandan ne. Yauwa."

Abokanan Ardo suka shigaa leka kayuwa suna ganin Maheer da Capt . Alhaji Dangoje yana daga can gefe yana murmishi. Domin gaba daya zubin Ardo da yanayin maganar sa dik dariya take bashi.

Wani me balangu dake tsallaken titin masallaci Capt yasa ya yankowa kowa a takarda. Gefe daya kuma ga lemuka da suka furfito dashi daga cikin mota. Mutanen wajen suka shigaa wanke bakin su da nama suna kurkurawa da lemo. Lamarin sai sam barka.




×××. ×××. ×××.

Ta cikin barandar parlorn ta suka hango wucewar Dadaa. Dauke da wata yar jaka a hannunta.

Haj Jidda taja tsaki ta saki labulen da suka dage.

"Wannan mata ko bak'ar munasira."

"Ai bantaba ganin makirar mace ba irinta wallahi." Cewar Haj Iklima.

"Allah kuwa yadda kikasan mijin nata ne ita daya. Nacacciya."

"Ai ko kadam jinina bai hadu da ita ba. Rannan ina hango dosowarta na sawa kofar lock taita bugawa naki budewa. Shine ta koma."

"Mun biyu kenan. Don ina jiyo sallamar me aikinta na rufe cikin dakin. Ta karaci shawaginta ta tafi ."

"Kingan shi. Gotogoto jeme jeme zakiga ya sab'a yaron a kafada yana zagaye gidan nan dashi." Haj Iklima ta rike throwpillow tana gwadawa dashi.

"ke kuwa yana rawar takashi yayi amaria. Ko nace bz mai tarin agola. Yadda kikasan akan sa aka fara haihuwa. Kamar du namu yaran ajiya aka bashi ba mallakin sa ba ne."

"Hmm! Allah dai ya kyauta."

"Aamin"

"Ga shegun agolan yaran nan nata sai kace shi ya haife su . Dan gaba da renin hankali."

"Ke kuwa an jika an bashi ya sha."

Suka shigaa yi da Dadaa da captain tamkar zasu yayyanki naman jikin su suji dadi.

×××Dadaa ta karasa yar barandar dake sashen Capt. Jikinta sai tashin kamshi yake yi.

Yana ganinta ya mike ya taro abarsa yana murmishi.

Dadaa ta gayar dashi cikin girmamawa. Ya amsa da faraa.

"Sai kamshi kike Jammu naa! Yau ma dai turaren kayan kika yi?" Ya karasa fada yana sinsinar kasan mayafinta daya kai kofar hancin sa.

"Eh mana turaren yerwaincenseandmore dinnan dai dana gaya maka na saya."

"Habawa wani irin kamshi kike so heavenly exotic. " Ya fada yana mai jinginar da kan dada a kafadar sa.

"Kaga bansan mekace a karshe ba. Anya bazan koma boko ba na faro daga farko. Ka amince mun kaji?"

Ya girgiza kai yana murmishi .

"Ke nakeso na ke kuma kauna ba karatun boko ba. Nama fi kaunar ki a haka, Ga ki a hakan kika zarta wasu matan da suka kurbi romon boko suka koshi. Ina kaunar ki sosai Jammu nah. Shi yasa banason ko yaya kiyi nesa da ni. Ni kuwa ya maganar business din da nace me zaki fara na baki kudin?"

"Godia nake bappan sudies . Ai ni gani nake da kabar zancen kasuwancin nan. Ni da yara ba abunda muka nema muka rasa. Komai ka dauke mana shi bappan sudies. "

"Karki kara fadar haka. Ni dai kiyiwa wa kikace ma magana? Cikin sati mai kamawa nakeson jin sunan kasuwancin da zaki kinji ko?"

"Na ji bappan su. Kawo hannu a yanke qumba naga tafito da yawa." Dadaa ta karasa tana mai zaro yar jakar hannun ta dake dauke da kayan yanke farce.

"Godia nake uwar alkhairi. Baki na ba zai iya nuna tsantsar farin cikin da ke nunkuwa ta sanadiyyar ki ba. Allah ya saka miki da alkhairi. Kece gugar kafata. Gyara mun farata na. Yimin tausa da sauran su. Jammu nah kin gama sace zuciyar captain baki daya."

Daria suka saki baki daya. Dadaa ta rike hannunsa cikin hankali da nutsuwa tashiga yanke masa faratan da gyare masa su tas...

××××

HAKA kawai ya tsinci kansa da tsara sabuwar doka ga dalibai mata. Na sanya safar hannu data 'kafa. Duk dalibar datazo babu su to zata karbu hukunci na kawo tsintsiya ko tabarma da doriyar bulala 3 zazzafa.

Yana daga zaune tun dazu yake jiran fitowar ta daga cikin gidah . Yan biyu ne suka fara fitowa daga cikin gidah suka bude bayan motar suka shigaa bayan sun gaishe shi.

Sai data mula tasha iska tareda doriyar adduar Allah yasa yayi zuciya yatafi. Don sam bata kaunar sabuwar tsurfar daya dauka ta shi zai dinga kai su inda zasuje ya kuma dakko su. Ciki harda makarantar boko da islamiyya.

Ranta a matukar turnike tafito. Saboda tsananin yadda take jin takaicin yadda Maheer yake neman mulkar dukkaninta batare da saura ba.

Ta bude murfin motar da karfin gaske tana yatsina fuska. Nan duniya bawanda ta tsana sama da Maheer .

"Zaraah"
Ya fada ahankali yana tada motar.

"Na'am" Ta amsa cikeda takaici.

"Barka da rana"

Tayi biris bata amsa ba. Ya saki tattausan murmushi. Saboda Yana son ya zolayeta. Sam taki sakin jiki dashi. Gashi batasan 'baranbaramar da akai da ita ba.

Kai tsaye ya wuce islamiyyr . Ya karasa parking Yan biyu na Shirin fita ya hango hannunta ba safar hannu. Gashi tayu lalle. Yatsunta da kafafun sun dau lallen takara haskawa.

"Zaraah! Meyasa baki saka safa ba? Uhmm? Zaraah?" Ya karasa Yana kwantar da kujerar dayake kai ya maida dubansa gaba daya kanta.

"Bani da su."

"Ni inada su" Ya fada ahankali hade da zaro murfin gaban motar ya ciro sabuwar safar hannu data kafa,

"Gashi sa"

Wafcewa tayi tafice daga cikin motar. Maheer ya girgiza kai yana murmishi. Ya haye ofishin sa.

Minti kadan sai ya leka ajin su Zaraah ya tabbatar babu namijin dake magana da ita cikin dalibai.

Haka kawai Maheer ya samu kansa cikin kishin zaraahn. Wani irin kishi da bai taba kawowa ba kuwa.

Ko da aka tashi daga makarantar', Shopping mall ya wuce dasu kai tsaye. Ya shige ciki wajen kayan mata. Ya shigaa lafto hijabai kala kala. Masu mugun tsawo da kauri. Da sabuwar waya fil a kwali.

Ya wuce mota bayan ya biya kudin Zaraah nata latsa baby nokia dinta.
Sai da suka isa gidah zata fita ya dakatar da ita,

"Dauki naki ne....?"

"Wait... What? Why? "

"Cuz you are my property!" Ya Bata amsa kasan makoshi.

"Banji ba"

"Saboda ke mallaki na ce!!!!"

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
2/7/22, 09:08 - Buhainat: _SO DA ZUCIYA!!_

_30_

_ZFF2022__
_(PAID NOVELS)_

_NANA HAFSATOU❣️_

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN

Please Login or Register in order to submit comment