Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rainan su da kulawa dasu a karshe wani katon yazo ya aure su shikenan bashi zai more su ba. A cewar sa mace wahalace shi kuma ba zai wahalar da kansa ba wajan kiwata su a karshe su tafi gidan wasu babu ko na buhun shinkafa bare kudin cefane.

Fitilar da ta kashe shigowar kawo amarya, ita ta kunna. Abin da ya bata mamaki shine ganin Zaraah a zaune ta zabga uban tagumi ga alama kuma tunani ta fada dan ko motsawa ba ta yi daga inda take.

“Zaraah! Zaraah!! Ke Zaraah...!!!”Cikin firgita da zabura Zaraah ta dago tare da cewa.

“Na'am Dadaa?

“Haba tunanin me kike yi haka??

Babu zato bare tsammani wasu hawaye Dadaa taga Zaraah na fitarwa, kuma cikin sanyin muryarta mai dadi da babu hayaniya tace.

“Dadaa ina jin tsoran lokacin da zai zo a yi mana wulakanci akan irin wannan abun da Bappah yake yi. Ance duk abinda mutum ya yi sai an yiwa nasa. Yanzu Bappah baya gudun muma muyi aure miji ya dinga wulakanta mu??

Wani irin zafi ya daki zuciyar Dadaa, kuka take son yi amman tana gudun kar Zaraah ta kuma karaya da samun rahamar duniya. Ta dade cikin shiru bata samu amsar da zata bata ba, wanda hakan yasa Zaraah ta kuma tsorata, zuciyarta ta kuma shiga cikin tashin hankali, tasan shirun da Dadaa tayi tabbaci ne na cewa suma idan suka yi aure mijin su zai mai da su banzaye...

Dak’yar Dadaan ta iya saita kanta, Cikin ikon Allah da buwayar sa kuwa ta shiga magana da Zaraah cikin nutsuwa hadi da kwantar mata da hankali, Ta yadda ta goge bak’in Ardo dake zuciar ta Zaarah. Domin uba ne agurin su. Don haka duk abunda yayi idan har ba sab’awa mahalicci yayi ba. Dadaan na k’ok’arin wanke Ardon agurin yaran nasa. Sam bataso su tashi da jin haushin sa da kuma ‘kullatar sa a zukatan su. .

Tas Dadaa ta wanke Ardo kamar ko yaushe tasamu suka shiga wata y’ar hirar daban. Kafin Dadaan ta juya tayi addduar bacci ta tofe yan biyu da addu’oi don tuni bacci yai awun gaba dasu. Ta tofe lungu da sako na dakin da addu’oin kariya. Kana ta umarci Zaraah data matse hasken fitila idan zata kwanta.

Zaraah ta rage sautin rediyon da Hamma Modibbo ya saya mata kwanaki. Tashiga neman tashar da bata wuce ta duk daren Allah. Sannu ahankali ta nemo tashar. Kamar ko da yaushe gidan rediyon sun saka sautin qira’ar bakin bahaushen balaraben mai tattare da nutsuwa, ‘kima da kuma kaifin tunani, Dimbin Ilimi da kuma sautin qira’a ba kowa bane fyace matashi kuma mahaddacin AlQur’an dake k’asar ta Mecca, inda yake karo karatun sa akan fannin islama. Matashin malamin dan kano ne wanda makarantu dama manyan manyan kasashe ke san kasancewar sa a tattare dasu. Sai dai shid’in na dabanne, Baya shiga harkar kowa da komai idan har bai shafi bangaren sa ba. Karatu ne kawai agaban sa. Indai ba yan uwa na kusa da kuma wanda suka san shi tun yana karami ba. Ba wanda zai iya ce maka ga yadda fasalin sa yake, Sai dai sautin ‘kira’ar sa.

Sannu ahankali haka Zaraah tak’arasa jin sautin kira’ar matashin saurayin. Ta lumshe idanu bayan ta kashe rediyon. Ta jero adduoi ta tofe jikin ta. Ta matse hasken fitilar sannan ta kwanta da dama. Kunnuwanta ba abunda suke tariyo mata sai sautin daddad’an karatun, Sudeis Ibn Harith.. A haka bacci ya dauke ta. Dake bata sallah bata, futsari ne kawai ya tasheta da asuba takoma ta cigaba da baccin ta. Ihun shekowar kururuwar Atuwa ce tasa Zaraah ta tashi daga daddadan mafarkin muryar, Sudeis Ibn Harith. Da sauri Zaraah ta mike ganin Atuwa na shirin fad’owa kanta.

“Ke Atuwa lapia?? Cewar Dada dake tsaye tana gyara dan yargalallen labulan su da Atuwan ta yago shi daga jikin ‘kusa da k’afarta.

“Ina fa lapia Jammu, Ardo nagani da fulas na shayi dayan hannun kuma da lafceciyar leda dauke da soyayyen kwai, Sai kamshi yake. Gefe d’aya kuma biredi mai yanka yanka Jammu. Mai yanka yanka biredin....Da tuntub’e yai saurin shigewa cikin dakin bankadaddiyar. Lalle Ardo, Biredi mai yanka yanka. Murtala 10 ne fa..?

Atuwa ta karasa fada tana kambama shayi da kwai da kuma biredi mai yanka yankan da Malam Ardo ya sayowa Jimmamman amaryar sa. ...


#pls follow/like and refer my scented product to your beloved ones🥰🔥💯🍓

Instagram:yerwaincense_and_more
Muna sales. Tun daga 4 ga December zuwa 10 ga watan sabuwar shekarar 2022 watan janairu/January Insha Allahu. Mun cire kaso 30 na kudin kayayyakin mu. Akwai kuma kyauta ta musanman ga wanda suka saya kaya daga dubu 7 zuwa sama.

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
1/31/22, 18:28 - Buhainat: *_SO DA ZUCIYA._*
_(A LOVE SO BEAUTIFUL)_

*_NA_*

*_NANA HAFSATU_*

*_ZAFAFA 5 2022_*
_(PAID NOVELS/LITTATTAFAN KUDI NE)_

*_FREE PAGE:5_*
_(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA)_

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

<><>••?

Dadaa ta girgiza kai kawai jin abunda Atuwa tace. Ta gyara labulen ta hanyar bubbuga ‘kusar da hannunta tashige cikin hudar data wawake, ‘kasar ta dan zubo mata a idanunta. tasa kasan hijabin jikin ta tana gogewa,

“Sannu Dadaa! Da kin bari na gyara.? Cewar Zaraah dake bin Dadaan da kallo cike da tausayin mahaifiyar tasu, Mace mai kamar maza kenan. Dadaa uwa ta gari ce.

Atuwa dake leken dakin jimmamman ta tagar dakin Dadaa taja tsaki tana gartsa yatsa.

“Jammu baki ce komai ba.?

“Mezan ce Atuwa? Ai ba yau farau ba ko? Inda sab...?

Ai Dadaa bata karasa ba, Atuwa ta wafce zancen,

“Na almurannan yafi kai ya ninka na baya, Wancen dake wucewa da ‘kullin shayin a leda? Ko mancewa kikai? Wannan kuwa fulas na shayi ici ko musu shayin dashi, Ga narkeken biredi mai yanka yanka na murtala 10. Kina jiyo kamshin soyayyen kwai. Lafceciya dake ledar fara ce. Ana hango komai.? Ta karasa fada had’e da nanawa cinyarta duka.

Dadaa ta girgiza kai kawai, Hade da jan wata yarkacacciyar kujerar katako ta zauna akai tana gyara zaman carbin hannunta.

“Aure auren Ardo naga baya damun ki, Yanzu uban kayan dadin daya wuce dasu bakiji kirjin ki na miki zafi ba??

“Akan me Atuwa? Bayan muma Allah yana hore mana muna samun abunda zamusa acikin mu. Kullum Modibbo yana ko’karin kawo abunda zamu ci Atuwa, Na menene zaki dinga damuwa akan lamarin Malam??

Atuwa ta yamutsa fuska hade da dankarawa Dadaa harara, Cikeda takaici tace,

“Shi yasa kowacce bola ya kwaso akanki yake zubata. Sannu tattabara uwar soyayyah. Kullum ne sai kin gogewa Ardo bak’i. Kamar kece matar sa ta fari. Jammu kinada kininibi.?

Zaraah dake gefe a tsakure itadai binsu kawai take da kallo. Raheelah da Na’eelah na gefe suma sun tashi sunata mutsuttsuka idanu.

“Ba haka bane Atuwa, Tun ina sawa har na dai na, Ga ni nayi wannan auren shine karo na ba adadi kenan. Kinga kuwa inda sabo ai mun saba, Dubada kowacce tazo da yadda yake tarairayarta daban.?

Atuwa ta ja tsaki hade da kwakwulo cikin kunnenta da yatsa, Yatsan ya ciro dankareren datti ta goge a zaninta na atamfa. Kafin ta sake gasawa Dadaa harara ta hura katon hancinta kafin tace,

“Mu da yaran nan duk d’aya muke awajen sa, Ya tsame mu a matsayin matan sa ya ajiye a gefe. Sai kace fankunan da basuda amfani haka Ardo ya mayar damu. Gaba d’aya ba aurat...?

Ganin Zata ‘baro ta gaban yara, Hakan yasa Dadaa mikewa ta rik’o hannun Atuwa suka fita waje. Ba jimawa tadawo cikin dakin tana girgiza kai.

“Atuwa kenan...?

“Dadaa barka da safiya, Dadaa barka da safiya.? Cewar Zaraah da su Raheelah da suka gaishe da Dadaan suma.

“Adda Manga! Barka da safiya?

“Barkan mu yan albarka. A tashi a wanko baki..? Dadaa ta amsa su duka.

“Barkan mu dai yan biyun Dadaa.?

Zaraah ta fad’a hade da mikewa tsaye, Ta janyo wata yar farar leda mai dauke da daddakakken gawayi da gishiri.

“Abun goge bakin ya ‘kare ne?? Cewar Dadaa. Ta tanbayi Zaraah.

“Ya k’are Dadaa..?

Sassan musu tayi kowa a hannun hagu. Hannun su na dama dauke da burushi na goge baki. Suka dauki babbar buta suka je can tsakar gidah suka fara wanke bakunan nasu.

Dai dai lokacin da Malam Ardo ya fito daga dakin jimmamman yana sakin wata katuwar bahaguwar hamma mai tattare da mik’a.

“Bappah! Barka da safiya.?

“Barka! Ku matsa can haka, Ya zaku zo daf da dakinta kuna wanke bakunan ku?? Ya karasa yana nuna musu yatsantsa can karshe Kusa da ban’daki.

Basuyi musu ba, Suka matsa daga can karshen suna wanke bakunan su. Atuwa dake kallon su ‘kar ta rafka dariya tana girgiza kai.

“Ardo aure aure kenan. Wannan hular kuma ko yaushe zaka canza ta oho??

Sarai Ardo yasan dashi take, Don haka bai kulataba ya murtuke fuska yana zabga mata harara.

“Nace abani na karin kumallo mijin jimmamman. Tana ina ne tsaleliyar amar au bazawarar taka??

Ardo dai bai kula Atuwa ba, Sai ma shigewar sa ciki da yayi kawai hade da jan labulen ya rufe ruf.

“Na jimmamman...? cewar jimmamman

“Na’am amaryar Ardo...?

Jimmamman ta sake murmushi hade da shigewa jikin sa tana shafa gemunsa daya koma fari.

“Yau shinkafa da waken fatsuma nake so. Da hakarkarin kaza. Sai zobon ta mai gardin dadi.?

Ardo ya dan zame jikinta daga nasa jin wata tsurfa tata ta daban.

“Haba amarsu. Jia kikaci dabgen kaza kika karashe ta da safe, Ki ka kora da lemon kwalba mai sanyi, Da safe kuma kika ce kinason shayi da biredi mai yanka yanka na sayo harda ‘koyi. Jimmamman tawa ni d’aya ki sarara wa Ardon naki mana.?

Jimmamman ta yamutsa fuska, Hadi da kwararrabe ta tamkar zatayi kuka tashiga bubbuga kafafunta a kasan dakin. Wanda takunsa yasa Atuwa zura kanta ta taga tana leko dakin tamkar Zata hango su.

“Yan iska...? Atuwa tafada tana gartsawa dan yatsanta cizo.

“Yau ba zaku makaranta bane??

“Kayya Mama satin banza ake, Idan munjema shara ce zakayi. Sai wani satin.?

“Toh su Bukari (samarin su)ya za’ai su san Kun dawo tunda acan hanyar makarantar suke.?

“Karki damu Mama. Sailu tasanar musu a wayar ta.?

“Dama wai dan ku samo na abincin rana..?

“Za’a san yadda zaai Kamar ko yaushe.? Sailuba tafada hade da kudundune jikinta da zani tacigaba da bacci.

**Su kuwa su Zaraah suna gama wanke bakunan su suka koma daki. Dadaa ta had’a musu shayi ta gutsutstsura musu biredin da Hamma Modibbo ya kawo.

A gurguje suka cinye suka shirya cikin kayan makaranta. Hamma Modibbo ya shiga dakin ya gayar da Dadaa suma suka gayshe shi. Ya zaro nera sittin ya dankawa Zaraah.

“Ku raba 20 20?

“Har yau dai dan albarka? To angode Allah ya saka da alkhairi ya kara maka budi.. Miyetti Miyetti, Allah hukkumo sa’a.?

“Aamin Aamin Dadaa.?

“Mungode Hamma.? Su zaraa suka masa godia. A tare suka fito ya shige dakin Atuwa su kuma suka tafi makaranta.

Ya gaishe da Atuwa ya mikawa Hajara nera 60 yace su dauki 20 kowa. Farillatu bata fara zuwa makaranta ba. Ba godi bare na gode. Haka ya karaci tsugunon sa ya fice. Atuwa ta bi bayan sa da tsaki tana tabe baki.

••?

Can sai ga Ardo ya fito daga dakin jimmamman da kwanon abinci zai sayo mata abincin na gidan fatsuma. Atuwa dake goge k’afarta da k’asa taja tsaki tana girgiza kai.

“Allah wadaran wahalalle. A haka zaka kare.?

Ardo dai bai tanka ba, Don yadda ransa ke abace na abincin da jimmamman tasa ya siyo sam bai bi takan zancen da Atuwa ke yada masa ba. Haka ya fice yana hade rai. A hanya Sai Allah ya sanya alkhairi ake masa na auren daya kara.

Haka ya ciyo bashin kb mai shago ya sayowa jimmamman shinkafa da wake da hakarkarin kaza a gidan fatsuma mai abinci. Tun a hanya ya gwaigwayi kazar ya ci. Ya dan tsakuri loma d’aya ya afa a bakin sa. Don yasan ba Zata bashi ba horan yunwa take masa jimmamman. Gaba d’aya tundaga Kan kaza kawowar biredi mai yanka yanka da kwai bata bashi ko kadan ba. Ya wanke hannun sa a bakin rijiyar hanya. A haka ya karasa gida Ya shige cikin dakin yana dashe baki.

“Gashi tawan..?

Jimmamman na yauk’i ta karba tana kurawa abincin kallo,

“Ya naga an gutsiri nan an kuma debi abincin??

Ardo ya wulkita idanu cikeda in’ina yace,

“Almajiri na bawa.?

“Allah ya tsine uban mai k’arya??

“Fisabilillahi meye na tsinuwa kuma amarsu? Daga debawa almajirin??

“Karya ne! Ga bakin kanan yana kamshin miyar. Karka sake min haka kaji masoyi na? A matsayi na ta gaban goshin ka ai ba haka ya kamata ka dingayi ba.?

Ardo ya kad’a kai kawai, Yana kallo tayi zaman durshan ta cinye abincin nan tas, Ta cinye naman ta tsotse kashin har sai da ya zama gari. Tukun sannan ta saki katuwar gyatsa hadi da dora hannunta akan cikinta tana shafawa.

“Allah ya bar mun Kai mai gida na.?

Ardo da hawayen takaici suka ciko masa a idanu ya Kada kai kawai yana kwakwalo dariar dole. Yana mamakin yadda ta cinye uban abincin nan ba tayi. Mikewa yai yana gyara zaman rigar jikin sa.

“Toh ni na fita..?

“Toh nawan, Allah ya dawo mun da kai lapia.?

Kai tsaye ya fice, Atuwa nata doka masa harara bai bi takanta ba. Jimmamman na kallon ta ta taga. Tafuto da sauri da kibiyar kitso a hannu. Kanta mai dauke da kalba guda uku daya gefen kuma ba’a kitsa ba. Hakan ya faru ne sakamon an fara mata kalabar kafin a kawo ta gidan Ardo, Lokaci ya kure ba'a karasa kalabe mata ba aka kawota gidan Ardo.

“Suwiyti dalin (sweetie-darling) wash, Ina yayi ne??

Ta dubi Atuwa tana tambayar ta. Atuwa ta kalleta shakeke tana tab’e baki. Jimmamman tasake cewa,

“Ko a hankali ya fice? Don karya tasheni a bacci?Kinga ya kawo mun shinkafa da wake da hakarkarin kaza. Bayan na ci. Na dan kwanta a cinyar sa. Na sashi susar kai. Ashe ya iya kitso? Kinga Sai ya kalabe mun uku, Na fara bacci ashe ya fita.. Dan Allah ina yayi??

Tinda tafara magana harta karasa Atuwa salati take rafkawa, gefe D’aya kuma uban takaicin kalaman jimmamman take ji, Hadi da mamakin annamimanci Irin na Ardo, Ashe har ya iya kalaba? Shekara da Shekaru bai taba gwada musu ba.

“Kinji Yaya?? Jimmamman ta sake tambayar Atuwa tana lumshe idanu.

“Na hadaku ke da shi na kwashe muku albarka.? Ta karashe hade da jan dogon tsaki ta shige dakin ta tana nanawa bayanta duka. Jimmamman tajima a tsaye tana daria Kafin ta shige nata dakin tana rausaya. Dadaaa na kallon komai ta tagar dakin ta. Itanma murmushin tayi tana kambama makirci Irin na Jimmamman.

Atuwa kuwa, Tunda ta koma daki take jera tsaki tana girgiza kai. Jira take kawai Ardo ya dawo ayi mai yiwuwa akan abicnin daya sayowa Jimmamman dama kalabe mata kai da yayi...

•?
Ai kuwa Ardo na dawowa da rana, A kofar gidah ya ci karo dasu Sailuba sun yab’e baki da jan jambaki dan fenti Kamar amaren akuyoyi. Ya dubesu yaja tsaki Saboda takaicin kasancewar su ‘yaya mata kuma Wai duk na sane, Yadda ya debesu ya zubar haka suka kalleshi shak’ek’e suma Sukai tafiyar su.

Ya shige cikin gidan bakin sa na doka tsaki. Hular sa wata koriya ya manta a dakin Atuwa tun kwanakin baya. Don haka Kai tsaye ya shige dakin na Atuwa. Ya nashiga ta mika masa kibiya. Hade da jan rigar sa tai masa zaman dab’ar akan bencin dake dakin.

Kafin ma yace komai ta wage gwaigwan kanta dake hamamin doyin rashin wanki. Ta zauna agaban sa tana mika masa kibiya da hannunta na dama.

“Menene haka? Lapiar ki kuwa?? Ardo ya tanbayeta cikin tsantsar sanin meke damunta ko hauka take ne?

Atuwa ta janyo hannun sa hadi da sake dora masa kibiyar daya jefar ta kuma juya tana murza fuska,

“Zauna ka kalabe mun shi tas, Ni ba sai ina bacci ba ma.?

Ardo zai yi magana Atuwa ta d’aga katuwar muryar ta yadda na cikin gidan da makota kowa zai jiyo,

“Kalabe shi gidah 6 charanchas Ardodo....?

Mamaki da takaici ne suka cika Ardo ya tattaro kasan rigar yar sharar jikin sa ya toshe hancin sa, Saboda yadda tsamin jikin Atuwa da kuma doyin kanta ya dabaibaye shi.

“Idan ba zeyi 6 ba kalabe gida 4 kawai.? Tak’arasa fada tana sakarwa kanta kwanyar rankwashin kai’kayi da yake mata.


**TUKUR RD***
(NASARAWA GRA)

*CAPTAIN MUHD MUHD AVENUE*












MISS XOXO writes💯🙌🏽
1/31/22, 18:28 - Buhainat: Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*SDZ*
_(A LOVE SO BEAUTIFUL!!)_

_MX_

_6_

**TUKUR ROAD**
(NASSARAWA GRA)

**CAPTAIN MUHD MUHD AVENUE**

Dank’areran gidah ne daya lamushe jerun gidajen bungalow (wato gidan ‘kasa marar bene) A jere reras guda hudu. Sai islamiyya a gefe da kuma computer room, Can gaba da jerin gidajen kuma daga baya wurin swimming pool ne da lilika a gefe gwanin sha’awa. Sai wani wajen na gymnasium (wajen motsa jiki) da kana iya hango cikin wajen saboda gilashi ne kofofin garai garai, Daga karshen bangaren kuma garden ne. Sai wajen kiwo daga b’angaren hagu, Shak’e da kaji, Zabbi, Zomaye da sauran su. Ga kuma wajen kifaye catfish suma acikin wani tsaftataccen ruwa anyi wajen kamar rijiya mai tsananin zurfi kifayen sai wutsul wutsul suke. Kiwo dai gasunan kala kala. Gidah kuma sai hamdala domin dik wani abun more rayuwa gidan ya kunsa idan ka zare babu.

**Zaune Haj Jiddah take akan doguwar kujera kirar Turkish royal. Komai na parlorn royal design ne na kalar light golden da dark golden. Had’adden parlor ne da ya amsa sunan sa. Ya cika da kayan more rayuwa irin ta sahun masu farcinan susa. Babu dogon jawabi domin babu ce kawai babu a gidan.

Ta cikin yar talabijin din dake nuna hotunan bidiyon harabar cikin gidan da sansanin waje ta kalla, Ganin Amadi driver ya danno da kan hancin motar gidan, Da sauri ta mike jikin ta na ‘bari ta shiga gyaggyara doguwar rigar lesin da ke jikin ta. Tana sauraron shigowar su.

Ahankali Addayo ta sakko daga motar bayan driver ya bude mata murfin motar. Sanye take cikin riga da zani na atamfa ta yi lullub’i da atamfar ta mai dashii matsayin mayafi. Ta cikin dan d’ankwalin ta daya zame kana hango kanannadadden bakin gashin ta na fulani. Kyakkyawar tsohuwa ce mai dauke da fuskar kamala. Tink’is tinkis tashiga dogara sandar hannun ta. Masu aiki na biye da akwatunanta a baya. A haka ta shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama.

“Wa’alaykm Salam! Sannu da zuwa Addayo.”Cewar Haj. Jiddah ta sunkuya har kasa. Cikin ladabi.

Addayo ta ansa ta, Hade da zama akan doguwar kujera tana mai sake ‘bantarar goran hannun ta.

“Ina kuma yaran?? Ta tambaya bayan ta mai da goran cikin dan tofin dake jikin ta.

“Isma’el da sameer suna office, Sai Bee dake school, Safwan kuma dazu ya fita..? Cewar Haj. Jiddah ta amsa Addayo cikin ladabi, Tana dan murza tafukan hannuwanta data hada, sakamakon Addayon bata daukan raini.

“Wacece kuma Bee, Ba dai Bintu ba ko?? Cewar Addayo.

Haj jiddah tashiga sosa saman girarta tana in’ina,

“Wai saboda a saka..?

“Me za’a sakaya Hauwa? Sunan nawa ne bai muku ba har yanzu kenan? Na dauka abaya dana tsawatar an dena ashe baku dena din ba.?

“Ayi haku’ri Addayo, Insha Allahu za’a dena.? Tak’arasa tana mai nunawa masu aiki gefen da zasu ajiyewa Addayo kulolin abinci.

Addayo bata sake ce mata komai ba, Hannun ta rike da carbi tana ja. Masu dauke da yatsunta da suka rine da jan kunshi. Cikin haka Haj. Ikram abokiyar zaman Haj. Jiddah ta shigo cikin parlorn itama.

“Addayo barka da zuwa, Anzo kalau? Ina wanka kuka karaso shi yasa banzo da wuri ba. Ya jiki jiki da sanyin nan? Allah ya bamu ikon wucewar sa lapia.?

“Alhamdulillah! Aamin Aamin.?

Haj Ikram ta juya suka gaysa da Haj Jiddah. Sannan kowacce ta rakube sukayi zaman kurame. Sai da Addayo ta mula ta sha iska. Tukun sannan ta nemi shiga bandaki. Ta rage cikinta. Tukun sannan ta zauna tafara cin abincin da tasa Haj. Ikram ta zuba mata.

Tana karasa ci ta mikawa Haj. Jidda wayarta data ciro a dan tofi.

“Addayo me za’ayi??

“Kirawo mun lambar Utai mai kifi. Zaki ga an rubuta masa sunan akai.?

“Toh Addayo.?

Kiran Utai mai kifi Haj. Jiddah tayi sannan ta mikawa Addayo da hannu biyu cikin girmamawa.

“Salama Alaikum! Utai kana jina? Lapia kalau, Yauwa dan Allah da maraice yar ‘kulle (magana) na ke komawa gidah. Ka dauketa ka kaita gidan ka ajiya. A rika bata kifi na wazobiya. Zan aiko a tawomun da ita. Idan anzo daukar Na’ima. Yauwa. Kashe! Kashe wayar.?

Tana karasawa ta zare wayar daga kunnenta. Ruwan dake cikin yar bowl da aka kawo mata da liquid soap ta wanke hannun ta kana ta koma kan kujera ta zauna tana mai cigaba da jan carbin ta.

Sannu ahankali d’aya bayan d’aya haka yaran gidan suka daddawo daga inda suka jajje. Kowannen su Sai da ya zo ya kwashi gaisuwa wajen Addayo. Da dare kuma Haj. Ikram itace ta kawo wa Addayo abinci.

Suka cigaba da zaman jingum jingum. Sai da Addayo ta musu sai da safe, Ta shige masaukin ta. Sannan sukayiwa juna sallama kowacce ta koma sashen ta. ..

Addayo ta jima hannunta a hade tana addu’oin samun lapiar ‘danta tilo d’aya daya hadu da tsautsayi na hatsari a shekarun baya. Wanda ke ‘kasar Qatar raina hannun Allah. Domin ya shiga coma. Sai fatan Allah ya bashi lapia kawai....
#Capt. Muhd Muhd Ave...!!

••?._____________••?.

Ardo ya mike yayi wuf zai fice, Atuwa ta jawo rigar sa ta baya tana cika tana batsewa.

“Nace ka kalaben kan nawa shine zaka fice? Ai babu inda zaka sai ka kitse mun kayi na.?

Ardo takaici ya ishe shi. Ya shiga zame hannayen Atuwa daga rikon data masa.

“Cika ni Malama. Cika ni nace miki.?

“A hayye sabada. Mun san shafe shafe munsan hoda. Ni zakayiwa kanon ci? Billahil lazi baka isa ba. Kai kuwa tamkar ka kitse shi ka gama.?

“Hauka kike ne? Zaki cika ni ko sai na sa bugu??

“Saka bugun uban yan aure. Nace bugar ni. Yadda kake a ‘kar mashe a kuma bushe ko’ina sai kashi, Har Kai ne zaka dake ni??

Kan kace me? Atuwa da Ardo sun kacame da kokawa. Atuwa saura kadan ta dake ta kuma kirb’e Ardo, Allah ya temaka Dadaa ta shiga rabiyar fad’an. Da sauri Jimmamman dake labe itama ta shiga dakin tana janye Ardo.

“Haba Suwitidalin, Haba Nawan, Haba Annurin rai na. Meya faru? Zo muje ‘daka mucigaba da bude sabbin shafin soyayyar mu...? Haka Jimmamman tayita maimaitawa tana janye Ardo.

Atuwa kuwa wani sabon takaici ni ya turnik’e ta. Ta rarumo zanin Jimmamman dake shirin fita da Ardo. Sai ga cikon da Jimmamman tayi a ‘duwawu ya fad’o. Dankwalaye ne har biyu na atamfa jimmamman din tayi cikon duwawu dasu. Kowane ‘barin ‘duwawu d’aya tasa dankwali d’aya.

Atuwa me zatayi ba dariya ba. Tashiga babbaka dariya tana gud’a,

“A hayye an dai ji kunya Ardo. Ashe bana mai cikon ‘duwaiwai ka dakko mana? A hayye sabada. Allah mai abin mamaki. Yau fa ake yinta karuwa da wa’azi. Kan

Please Login or Register in order to submit comment