Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

color ta zuba adon gwal na sarka da dankunne da zobuna da awarwaraye. Ta yafa mayafin kayan akan ta. Tayi kyau ba kadan ba.


"Sannu kinji?"


"Na wartsake fa yaya yusra"


"Allah ya kara afuwa... Amin"


"An daura ko? Iyye congratulations... Yaya yusra ta zama matar aure"


Yusran tayi murmushi ta dube ta tache,


"Godiya nake baby sis... " So take ta fada mata amman kuma ta rasa yadda zata ce mata ai tare da nasu aka daura auren.


Cikin haka sai ga shigar hajiya Jamila dakin tayi sallama. Suka amsa,


Ta janyo stool ta zauna akai ta dubi yusra tace da ita,


"Bata shirya ba?"


"Ai ban gaya mata ba Aunty"


Hajiya jamila ta kada kanta, ta hada hannuwan ta tana lankwasa su tace,


"Amaal..."


"Na'am Hayateey..."


"Ki tashi ga kaya nan acikin drawer irin na yayarki yusra kalar naki ne dabqn ki saka zaa dauke ku hoto da su Hajiya.... "


Gabanta ne ya tsananta bugawa jin abunda mahaifiyar tata tace,


"Hayateey... Bangane ba?"


"Amaal Allah yayi miki albarka... Ki sani mahaifin ki bai yi miki zaben tumin dare ba. Kamar yadda a fari ma biyayya kikayi kika amince da auren Hisham wannan karon ma biyayyar ce zakiyi ta, ki amshi kaddarar ki da hannu biyu... Dan uwan ki ne... Kuma me kaunar ki ne tun kina zanin goyo kinji da kunnuwan ki. Yau tare da yar uwar ki ysura an daura miki aure da Al-mustapha yayan ki.",


Dummmmmm taji kofofin kunnuwan ta sun toshe.. ganin ta ya fara dishi dishi..take jikin ta ya soma mata kakkarwa. Hawaye masu dumi suka fara zuba daga idanun ta..


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta furta a sanyaye cikin lafazi me ban tausayi. Duk azaton ta dai wallahi ba za'a bata Al-mustapha a matsayin mijin da zata aura ba. Al-mustapha fa? Wanda duk duniya ita ya tsana? Maganganun daya gaggasa mata suka dinga mata yawo akai..


Yusra ta janyo ta jikin ta rungumo ta sosai.. hannunta daya ta saka akan fuskar amaal din tana share mata hawayen da ke zurara,


"Bar kuka dan Allah. I assure you auren ki da hamma alkhairi ne. Nan gaba zaki farin ciki da hakan. Wallahi duk inda masoyi na hakika ya kai to hamma ya zarce gaban haka... Yana kaunar ki sosai. Ni bansan dalilan sa na rashin bayyana miki ba..."


Girgiza kai kawai tayi. Can sai hawaye sharrr. Ta shiga shessheka. Jijiyoyin kanta suka tattashi. Idanunta suka sake kadawa sukai jazir. Saboda Allah ashe sai da aka daura mata aure da Al-mustapha. Duk ga maza nan a dangi


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta fada cikin kuka da muryar ban tausayi..


"Amaal...." Yusra ta kira sunan ta ranta duk baby dadi itama.


"Dakko kayan nata a drawer kina budewa zaki gansu daga sama." Hajiya jamila tace da yusra.


Yusran ta mike ta bude drawer ta dakko mata kayan ta ajiye agaban ta.


"Gashi .. Dan Allah tashi ki saka"


"Amaal karki bari na maimaita zancen saka kayan nan...idan kuma kinfi karfin mu to ki bar su."


Hajiya jamila ta yunkura zata mike kenan Amaal tayi saurin taddo ta ta rungumeta tsam a jikin ta tana kuka sosai.. cikin rawar jiki da murya tace,


"Hayateey kiyi hakuri ki gafarce ni.. "


Hajia Jamila ta saka hannu ta goge mata hawayen da ke zuba a fuskar ta tace,


"Allah ya miki albarka Amaal... Allah ya sanya alkhairi da dimbin albarka a rayuwar auren ku gaba daya. Allah ya kauda duk wata fitna yasa gidajen zaman kune. Yadda kuka yiwa iyayen ku biyayya kukw amince Allah ubangiji ya shi muku albarka ya biya muku dukkanin bukatun ku"


"Aameen Hayateey"


"Aameen Aunty"


Hajia Jamila ta fuce da sauri bayan ta dafa kafadar yusra. Ko da ta fita jingina tayi a bakin kofa hawaye na fita daga idanun ta irama... Hakika tasan ba a yiwa Amaal zabon tumin dare ba. Sannan tasan Al-mustapha zai riketa da alkhairi da yardar Allah. Kawai dai tana tausayin tilon yar tata ne. Batada taba bijirewa na daga abunda su iyayen ta suka zartar akanta ba.. kowane irin hukunci ne haka ta ke karba tun tana karama... Duba da cewa ita kadai ce awajen mahaifiyar ta ta bata sangarta ta ba. Tanada tsananin biyayyar da kauda kai a abu sosai tamkar wata mai manyan shekaru.


"Ki tashi ki wanka ki saka kayan muje ko?"


"Tohm"


Mikewa tayi ta shjge bandaki bayan tayi addu'a. Wanka tayo hadi da dauro alwala. Ta saka kayan nata. Kalar ja ba kadan ba tayi kyau .


"Bari a kira me makeup din ko?"


"Da an barta banaso"


"Banda musu"


"Tohm"


Yusra ta kira me makeup din a waya nan da nan tazo tayi mata makeup din wmma light. Ta daura mata dankwali ba kadan ba Amaal tayi kyau.


Itama ta zuba uban su gold daya gaji da haduwa ya kuma sha kudi masu tarin yawa .


Yusra ta dakko wayarta ta dunga daukar hotunan amaal din saboda tayi kyau sosai,


"Mashaa Allah... A beaute..."


"Nagode Yaya yusra"


"Muje ko?"


"Tohm"


Sauka sukayi suka nufi mota suka shiga direba ya jaa su sashen Hajiya Maryam dake cike da Yan uwa. Nan da nan aka fara daukar su hotuna kala kala .


Kafin daga bisani aka nufi wajen walima akayi wa'azi akaci aka aha aka kuma dauki hotuna hadi da raba gudunmuwa.


Hisham yazo akaita daukar hotuna da shi da amayar sa.


"Ina wuni Yaya Hisham" Amaal ta gayshe shi


"Lafiya lau kanwar mu. Ko ince yayar mu " ya fada yana kallon yusra. Sukayi daria baki daya harda Amaal din..


Yusra ta dauke su hotuna duka su ukun ta kuma dauke su su biyu itada Hisham sannan ta dauki Hisham da Amaal.


Data tashi saka hotunan a status sai wanda Amaal take da Hisham taje ta saka only view by Al-mustapha wato iya shi kadai ze ganshi. So take ya kulu sosai saboda bashida masaniyar daurin auren Amaal da shi kansa, ance kar a gaya masa tukun.


Haka dai aka karasa shagulgulan biki...aka Kai amarya yusra gidan ta.. Amaal kuma tana sashen Hayateey dinta tukunna.


Yan uwa da abokan arzuka duk suka tattafi. Kandem estate ta zama sai wadanda ke cikin ta kawai..




*ENGLAND*
(MANCHESTER)




Yana daga kwance akan gadon sa.... Ya juya ya hararo wayar sa daya kashe ta gaba daya ..


Ya sauke ajiyar zuciya ya kunna yana dan bubbuga kasanta. Tana karasa kunnuwa ya budata da face id ya shiga ciki bayan ya kunna wifi


Sakonni ne sukai ta shigowa wayar sa... Na sauran kafafen social media dana text messages. Messages dinsa ya shiga rututu gasunan na su Habibi Talba, Aayan, Yusra, da Bappah Nuraddeen har sau uku ma ya turo masa.


Na Bappan ya shiga jikin sa na bari. Inda bappan ke sheda masa da lallai lallai ya tatttaro kayan sa ya dawo gidah ba tare da ya dau lokaci ba.


Kuma ya karbi kaddarar sa da hannu biyu, sakamakon lefin da yayi an hukunta shi ta hanyar aura masa wata yarinya tare da sauran yan uwan sa da aka daurawa aure a ranar wato su Amaal.


Yana karasa karantawa ya bude baki cike da mamaki. Messages din Aaayan ya shiga yanata ce masa ango kasha kamshi.


Mutane anata masa maraba. Gashi baisan ma wacce yarinyar aka aura masa ba.


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun..." Ya fada da karfi yana bude idanu sosai tabbatarwa da wallahi an daura amsa aure dagaske..


Wata zuciyar ta tabbatar tare da hasaso masa tabbas da labiba aka daura masa aure yar kanwar mahaifiyar su. Saboda yarinyar na tsananin kaunar sa. Kusan kowa ya sani.


WhatsApp ya shiga da sauri. Status din yusra kanwar sa ya fara cin karo ta saka na Hisham da Amaal da ta dauke su..


Ya saka hannu yana zooming fuskar amaal din tayi murmushi tamkar ya zura hannu ya wayar ya sace ta.


"Tayi aure fa Al-mustapha dan Allah ka hakura matar wani ce" wata zuciyar ta tunasar da shi


Yayi saurin futa daga WhatsApp din gaba daya ya ajiye wayar bayan ya kashe wifi dinma.


Hakan bai masa ba ya sake dakko wayar ya goge WhatsApp application din gaba daya yana sakin siririn tsaki.


Wayar sa ce tayi kara alamar kira na shigowa. Dauka yayi da sauri ganin mahafin sa ne,


"Assalamu alaikum Bappah"


"Waalaykm Salam... Barkan ka dai ranka ya dade uban masu gidah" Alhaji jalaludden ya kira shi cike da bacin rai


Tamkar yana gaban mahaifin nasa ya tsugunna yana shafo keyar sa,


"Tuba nake Bappah... Barka da yam.. safe.. au Rana"


"Barka ishasshe.. Ranka ya dade yayi karqo"


"Tuba nake Bappah"


"Wato ka sallamamu kayi gamon kan ka ko?"


"Bappah! Dan Allah ku gafarce ni"


"Ache wai kai zakayi tafiya wata kasar ba Wanda ka fadawa ko mahaifiyar ka sai ji mukayi wai baka kasar ka tafi."


"Bappah ku yafemun doron zuciya ce ta debe ni"


"Rufamin baki mutumin banza.. Na baka nan da sati daya ka tattaro ko aina kake ka waiwayo gidah kaji na gaya maka"


"Inshaa Allahu Bappah.. ayi hakuri"


"Ni da na sallama ka ma bappanin ku ne sika rika a kyale ka. Kai ma Allah ya temaka maka anhada da Kai acikin Yan uwan ka an daura muku aure."


Al-mustapha ji yayi tamkar ya fashe da kuka. Wai kamar shi ace an daura masa auren dole. Be San wacece amayar ba, haka kawai sama ta ka sai ji yayi an masa aure kamar wasan yara,


"Ina magana kayi shiru"


"Tuba nake Bappah.. labiba ce ko?"


"Koma wacece Ina ruwan ka? Ko kuwa hakan be maka ba ne ?"


"A'a bappah ayi hakuri nagode"


"Yauwa ka waiwayo ka dawo. Karka bar yar mutane da igiyar auren ka akanta"


"Tohm... A huta lafiya"


Yana katse kiran ya dauki pillow ya danne kansa dashi. Wani tuququn bakin ciki yaji yana masa yawo tin daga tafun kafar sa.....


Wasu hawaye daya tabbatar na bakin ciki ne sika shiga kwarara a idanun sa. Wayar sa ya janyo ya shiga processing komawar sa gidah Nigeria. Har ga Allah bai so hakan ba. Yaso ya dade sosai kafin ya waiwaya gidah. Har sai tunanin Amaal da kaunar ta sun gudu daga cikin zuciyar sa.


Hotan fuskar ta ta sake zuwar masa a zuciyar sa.. ya ja tsaki a zahiri yace,


"Al-mustapha matar wani ce ta. Dan Allah ka dena tunanin ta....




_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/25, 6:15 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 42_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


Lefe na gani na fada yan gaske eanda suka girgiza dangi cikin sa da kewayan sa Bappah Jalaludden yasa aka yiwa amarya Amaal.


Sannan nan da nan ya cigaba da karasa ginin da Al-mustapha ya zanawa kansa yana yi na kansa wanda zai zauna idan yayi aure ..


Gata ne Amaal take samu ta ko'ina... Domin mota sabuwa dal Alhaji Muhammad yasa aka bata ta kaita makaranta saboda biyayyar da tayi na auren Al-mustapha.


Ga kudin pocket money da ake bata na kashewa kullum ne ba fashi. Hajia Jidda mahaifiyar Al-mustapha safe da dare take aikawa Amaal hadaddeen abinci. Haka kuma kullum sai taje ta ganta a asashen hajjya Jamila mahaifiyar amaal din.


Wani lokacin harda Bappah Jalaludden suke zuwa wajen nata. Ga yusra da ke kiranta ta video call suna gaisawa. Wata iriyar shakuwa da so suke nuna mata da ita kanta lamarin har tsoro yake bata..


Kowa haba haba yake yi da ita a zuriyar ardo kandemi. Tsananin hankalin ta da dimbin biyayyar da take da ita yasa kowa yake dada kaunar ta domin Amaal batada abokin fada ko gaba... Kowa nata ne.


Ko yan uwan ta su Hindu dake takalar ta da fada tuni ta dena shiga shirgin su ta baiwa bola ajiyar su. Ta tataro kayanta ma ta bar musu sashen su kadai suke dabdalar su tana wajen mahaifiyar ta a zaune


Gashi duk bayan kwana biyu sai anyi mata gyaran jiki... Tamkar wadda zataje gasar sarauniyar kyau..




*ARDO KANDEMI INT. AIRPORT NUKAA*




Karfe sha bjyu na rana jirgin su ya sauka a filin sauka da tashi na farfajiyar filin iyapot na Ardo kandemi dake birnin Nukaa.


Aaayan ne yaje daukar sa tun wajen sha daya yake jiran sa a mota... Suna sauka kuwa yana fitowa ya hango motar Aayan din ya nufi motar da sauri dauke da akwatin sa.


Aayan din ya futo yana dashare masa hakora,


"Ango.... Ga ango... Ango ..."


"Dan wahala kawai. Dalla dena kira na da wani ango. "


"Yo karya akayi maka? Wallahi an daura maka aure"


Al-mustapha ya tabe baki ya saka hannuwan sa ya dafa kan mota yana duban Aaayan yace,


"Labiba ce ko? Yarinyae nan ko mayya ce sai haka wallahi"


Aaayan ya tuntsire da daria. Al-mustapha ya zabga masa harara ya bude gaban mota ya shoga bayan ya zura akwatin sa a baya. Aayan ma ya shjga ya tashi motar yanata daria. Al-mustapha ya dube shi cike da takaici yace,


"Wai aka tsallake ka ba'ayi hadin auren nan da kai ba. Wallahi baa kyauta ba"


Aaayan ya dube shi yana grigiza kai yace,


"Wallahi baa kyauta mun ba. Narantse da Allah ban so zan sake wani azumin a kandemi estate ba. Agidah na nake so naci girkin matata. Mu rangwaje soyayya nake gaya maka. Amma wai aka ki ayimin auren nan such is life"


Al-mustapha ya dube shi ya tabe baki hadi da sakin tsaki yace,


"Kai fa ka dauka auren abunda ya kunsa komai kenan? "


"Abunda yake damuna kenan ni .. komai yabiyo baya"


"Ina tanbayar ka labiba ce ko?"


"To kai azaton ka wa za a baka Hindu?"


"Hindu? Amma Allah ya isa"


Aaayan tsabar daria sai da ya nemi gefen titi yayi parking ya shiga dariya harda rike ciki sosai yace,


"Hindun bata isa bane ko bata kai ba?"


"Dan wahala. Kai a aura maka ita mana"


Aaayan yayi murmushi yace


"Hindu kan akwai kaya ba lefi zan iya maneji yasin"


Al-mustapha ya sake jan wani tsakin yace,


"Kai fa gaba daya banza ne. Kai kssai structure din mace shine agaban ka?"


"To meye auren?"


"Uban ka ne."


"Dan wahala na labiba"


Al-mustapha ya dube shi yaja tsaki yace


"Duk Ina direbobin gidan ne za a turo ka dauke ni?"


"Yo da ka samu ma nazo na dauke ka. An gaya maka yanzu kanada sauran muhummanci ne a idon mu? Kai din daka tattara komai naka ka bar kasaar ba tare da masaniyar kowa ba. Dan wahala yasin da sede kayi bolt koka hau dan sahu ya dawo da kai gidah. "


Al-mustapha ya sake duban sa yaja dogon tsaki yana grigiza Kai yace,


"Dalla rufemun baki..."


"Kaga hotunan bikin kuwa?"


"Naga na Amaal da mijin ta"


"Perfect couples nake gaya maka...duk Nigeria ba wadan da suka dace da juna irin su.."


"Dan Allah kayi shiru. "


"Yo sai nayi shiru naki fadan gaskia? Baka ga na yusra ba da .......


"Wace yusran?"


"Yusra dai Fatima"


"Auren tayi itama.. Bangane ba meya faru ne haka aurar da kowa akayi ne?"


Aaayan yayi dariya yana grigiza Kai yace,


"Kai,yusra, amaal ku kenan kadai"


"Waya auri yusra to? I can recall yusra batada saurayi tun ex dinta da suka bata baata sake saurayi ba fa wata aura?"


"Itama hada ta akayi da da wani"


"Kan balai.. auren meye haka aka yiyyi ne? Auren dole fa kenan"


"Kusan haka. Amman dai ba wani dole dan ana cewa zaa hada ita a auren dana amaal atare ta amince dawanda aka bata caraf tace eh"


"Woah.. agaban kowa kenan akayi?"


"Kowa yana nan".


Al-mustapha ya sake zare idanu daya tuno batula me aikin su da mahaifiyar su ta mayar kamar yan gidan abu kadan tace tana tausaya mata Kuma itace zata aurar da ita inshaa Allah,


"Ko Batula aka aura nun please?"


Aayan ya sake fashewa da dariya yana girgiza kai yace,


"Watace daban fa. Kuma wallahi mekyau ce. Ni fa da har zance dan Allah aha dani da ita sai kuma nayi shiru kawai. Amma wallahi zaka ji dadin zamantowar ta matar ka yarinyar batada hayanjya ga nutsuwa."


Mtscew.. Al-mustapha yaja tsaki cike da takaicin maganar aaayan yace,


"Kai na cuwo yake. Danyi shiru please."


"Nayi shiru fa kace? Ni da baki na, motata ta, har zaka dinga yanka mun dokoki. Bazan ba"


Bai sake tanka shi ba. Ya sa hannu ya kwantar da kujerar da yake kai ya lumshe idanun sa,


"Ka zauna muyi magana mana"


Al-mustapha ya girgiza masa Kai alamun a'ah. Yaja pcao din kansa ma ya rufe fuskar sa da ita,


"Wato ga mahaukaci ko? Ka bawa banza ajiyata ba"


Kanzil Al-mustapha bai ce masa ba... Aayaan ya cjgaba da Jan motar sa kawai har suka karasa gidah.



*KaNdEm EsTaTe*



Aaayan ya shige da motar sa cikin gidan har farfajiyar parking space din sashen Hajiya Maryam.


Masu kula da sashen suka taso da sauri sunayi musu sannu da zuwa.


"Ranka ya dade Ina kayan?"


"Ai ba wasu kaya bane Alhasan...."


"Zan dauka a haka ranka ya dade"


Alhasan ya bude gidan baya ya curo akwati da hand luggage din Al-mustapha ya shigar masa da ita sashen Hajiya Maryam


Bakunan su dauke da sallama suka shiga ciki.. kan Al-mustapha a kasa cike da kunya ya karasa ciki ya zauna agefen hajiyan daga kasa


Suka gayshe su cikin girmamawa. Hajiyan da Alhaji Muhammmad da sauran bappanin su suka amsa fuskokin su a sake idan aka tsame bappah jalaludden aka ajiye a gefe.


Al-mustapha ya basu hakuri abisa tafiyar da yayi bai fada musu ba.


Hajia tasa aka kawo abinci aka jere. ya bubbude ya zuba kadan a plate ya fara ci,


"Har yanzuu danyaye baka son abinci dai?"


Murmushi kawai yayi yace


"Ina ci Hajiya"


"Ba wani baka ci, wannan abincin kamar Wanda zaa bawa husna?"


Yan parlorn suka saka dariya. Shima Al-mustapha murmushi kawai yayi.


Bayan ya karasa cin abincin ya shiga bandaki yayi awala ya fita masallacin cikin gidan yayi sallah sannan ya sake komawa sashen Hajiyan


Su Bappah Nuraddeen ne suka fara maganar auren da akayi masa. Kan ya rike wadda aka hadasu auren da daraja yayi biyayya sai Allah ya saka musu albarka. Kansa akasa yace,


"In shaa Allahu"


"Allah ya maka albarka kaji?"


"Aamin Bappah..."


"Akwai ginin da kake yi wanda ka zana mahaifin ka ya cigaba da karasa maka shi. Ya kumayi maka lefe an Kai gidan su matar ta ka. Kafin akarasaa ginin, Wannan sashen bayan na hajia da bakowa sai ku fara zama anan din. Can din kuma ya kusa kammalluwa sai ka dauki matar ka ku koma idan an karasa"


Ji yake tamkar ya bude baki ya zunduma ihu. Shikenan wai shi dinnan da yake a zaune a haka mijin aure ne? Au yanzu nan shidin yanada mata ? Allah me iko a a duk sanda ya so ..


"Ko bakaji ba?"


"Naji Bappah. In shaa Allah..." Bayan ya bawa bappah Nuraddeen amsa, ya amsa ya sake juyawa saitin mahaifin sa yace,


"Bappah nagode Allah yakara arziki ya saka da alkhairi "


"Aameen" kawai Bappah Jalaludden ya fada.


Dik suka mike suka firfita. Bai wani jima ba shima ya nufi sashen su ya gayshe da mahaifiyar sa. Ya Kuma bata hakuri a bisa laifin da yayi..


Aayan ya kira yusra ya sheda mata Al-mustapha ya dawo.. Nan da nan ta kira su hajiya Maryam tace dan Allah kar akai masa Amaal abari zatazo da kanta tukun sai ta tsokane shi.


Ta Kuma kira Hajiya jamila ta ce mata Al-mustapha ya dawo ta turo me gyaran jiki ta sake yiwa Amaal na kwana daya. Amaal kamar tayi kuka saboda gyaran jikin nan har ta gaji da shi. Saboda ko'ina na jikin ta yayi kyau ta kuma sake cikowa sosai komai ya zauna... gyara yayi gyara.


Har ga Allah bataji dadin dawowaar da akace yayi ba.... Al-mustapha yana zaune a sashen mahaifiyar tasa ya saka hannu ya sosa keyar sa yace,


"Ina bintu?"


"Wani abun kake bukata?"


Ya girgiza kai yana lankwasa hannuwa. Ta dube shi ta tabe baki tace,


"Fadi abunda yake ran ka"


"Mami ita aka aura mun ko?"


Ta dau ruwa kenan zata sha ta ajiye tana kallon sa tayi murmushi kawai kafin tace,


"Ba ita bace... Mijin da bintu zata aura ma jiya yazo zance ya shigo ya gayshe ni"


Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tunowa da labiba kuma sai yace,


"Ko labiba ce Mami?"


Hajia Jidda ta mike tabar masa wajen tana cewa,


"Idan ka fita ka rufemun kofar parlorn kasa"


Ya sake sauke wata ajiyar zuciyar ya kwantar da kansa akan kujera kawai yana tunane tunane. Gashi kowanne tunanin yake sai Amaal ta shigo ciki. Yaja tsaki yana dukan goshin sa cikin takaici..


Dakyar ya mike ya nufi dakin sa ya kwanta bayan yayi sallar nafila. Yanata rokon Allah ya sanya albarka a rayuwar auren dole da akayi masa...Allah kuma ya sanya masa hakuri da dangana da zama da matar da aka aura masa...




_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/25, 6:47 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 43_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___




*WASHE--GARI*




*Yusra* da kanta ta kira Al-mustapha tace za'ayowa amarya rakiya yaje yasiyo dukkanin abun bukata. Bai amsa taba ya kashe wayar saboda tsabar takaici...


Yana fita parking space yaci karo da Aaayan zai shiga mota. Yayi sauri ya bude gidan gaba ya zauna


Aayan ya dube shi yana kallon sa shakeke yace,


"Malam meye haka?"


"Yi hakuri.. me da me ake kai wa amarya ne?"


Aaayan ya tuntsire da dariya ya dube shi yace,


"Ni magidanci ne?"


"Be serious please.."


"Kaji, drinks, snacks, fruits, da sauran su"


"Muje ka raka ni please"


Aayan ya tabe baki yaja motar suka fita daga gidan. Suka biya tukubar kaji suka siyo gasassu sannan suka siyo sauran abubuwan da zasu saya suka koma gidah lokacin dama an idar da sallar ishai...


Aaayan da Al-mustapha na zaune a sashen Al-mustapha da aka bashi da amaryar sa kafin a karasa nasa gini. Muryoyin su suka daki kofofin kunnen sa.


Kamar ya tashi ya gudu yake jin sa shi wallahi bai shiryawa auren nan ba. Aaayan ya daga murya ya amsa musu. Al-mustapha ma ya amsa kasa kasa.


Yusra ce ta fara shigowa suka gaysa. Sai kuma Amaal da Hisham daga baya. Al-mustapha ya dube su da mamaki ko meye abun zuwa wajen sa oho.


Hisham ya bashi hannu suka gaysa. Amaal ma ta gayshe su . Aaayan ne

Please Login or Register in order to submit comment