Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka amsa...


"Ahh uwata..." Alhaji Abubakhar ya fadaa


Karasawa kusa da su tayi tana murmushi duk kuwa da kakaro shi take zuciyar ta ba dadi


Hajia Aisha ta rungume Amaal tana murmushi ..


Hisham yana taso ta kalle shi suyi magana ta dauke kanta kamar bata san yana wajen ba ..


"Da hajiyar mu da baba.... Da Amaal zakuje Umrah nan da yan kwanaki in shaa Allahu... Muna fatan Allah ya karawa baba lafiya Amin.."


"Ahh ma shaa Allahu .. Allah ya saka da alkhairi, Muna godia kwarai da gaske da karamci... Me sunan Hajiya da hajiya da baba na godiya kwarai da gaske... Allah yabar zumunci" Kawu Adamu ta fada fuskar sa kumshe da faraa


Haka dai akayita Allah ya sanya alkhairi.... Al-mustapha na gefe ya saita bangaren su kawai yana bin su da kallo,.. Musanman moves din Hisham da idanun sa ke kan Amaal tun da tazo..


Kasan makoshi takaicin hakan ya kama shi dik ya sururuce akan mache yace,


"Solob'iyo..."


"Magana make Musty fresh?" Aaayan ya tanbaye shi


"No.."


Haka dai suka yita hira a parlorn . Kawu Adamu ya dubi Alhaji Abubakhar yache


"Yanzu ka dawo Nukaa gaba daya kanen?"


"Eh Kawu na waiwayo gidah"


"Ma shaa Allahu.. Allah ya sanya alkhairi ya sa kun dawo a sa'a"


"Allahumma Aameen Kawu... Allah ya saka da alkhairi... Har da kai a umarar nan"


Suka saka dariya baki daya... Alhaji Abubakhar yayi gyaran murya ya cigaba da cewa,


"Sai magana ta gaba kusan inche itache muhimmiya maa.... Ni da iyalina munason sake karfafa zumunta a tsakanin mu.."


"Ma shaa Allahu... " Alhaji Nuraddeen ya fada..


"Dan ku Hisham yana son 'ya daya daga wajen amini na... Yana son ta da aure nan ba da wani lokaci ba... Ya jima yana bibiyata da zancen ni da mahaifiyar sa . Nache masa ya bari sanda muka waiwayo gidah sai ayi zancen ido da ido.."


"Ma shaa Allahu abu yayi.."


"Alhamdulillah.."


Tuni yan parlorn suka fara tofa albarkacin bakin su,.. Hisham ya kasa hakuri yache da Amaal,


"Amaal..."


"Yaya Hisham...,"Ta amsa shi kanta a gefe.


"To wacece kenan daga cikin yaran?"


"Mai sunan Hajiya., Amaal"


Amaal baki bude ta juya tana duban hjsham ya lumshe mata idanu alamun eh... Sam ko a mafarki bata taba kawo haka ba


Bappanin sunyi murna kwarai matuka idan aka tsame jalaludden da dama a sashen Hajiyan suka same shi kuma duk maganar da suke baya tofa komai..


"Indai sun sulhunta a tsakanin su ai Alhamdulillah komai yayi"


Alhaji Abubakhar yayi murmushi yana kallon amaal yace,


"Yache kuna waya da chatting ma ko?"


Munayi mana Amma ai ba soyayya mike baa. Ta fada cikin zuciyar ta .. Ta samu kanta da daga masa kai ahankali kuma tache,


"Eh.."


"Ma shaa Allahu... Abu yayi yan auuta kuma yan fari " Kawu Adamu ya fada yana murmushi


"Daya sanar mana munyi matukar farin ciki.... Saboda naji dadin wannan alaka da zaa hada.. zumunci zai kara karfafa... "


Haka dai aketa tofa albarkacin bakuna.. Amaal tamkar ta fashe da kuka tabbas tana kaunar Hisham don bashi da halayen da zaace zaa tsane shi sai dai ba kaunar zaman takewar aure take masa ba... Tana kallon sane amatsayin dan uwan ta na jini tamkar yayan ta kuma malaminta dake koya mata darussa....


Ta sauke kallon ta akan Aayan da yanayin sa ya sauya lokaci daya .. kallon ta yake ki ko kiftawa bayayi kuma irin kallon nanne me tarin ma'anoni mai tattare da sakon 'baki kyauta mun ba....'


"Me babban suna......" Alhaji Abubakhar ya kira sunan ta.


"Na'am babaa"


"Kin amince zaki auri Hisham a matsayin mijin ki? Kada kiji kunya ko ki kawaici idan ba kaunar hakan a ranki.. duka nan iyayen ki ne mu da kakannin ki kuma ba zamuyi muku tulashe ba... Shin zaki auri Hisham nan da dan wani lokaci ba mai dadewa ba?"


Gabanta ne ya tsananta bugawa... Ta daga kai ta sauke akan Hayateey da ta kauda kanta da sauri taki bari su hada idanu.. ta dubi abbiey da yayi mata murmushi kawai.. ta samu kanta da dan taune kasan lebenta tana jansa ahankali..


"Kibi zuciyar ki kinji.... Karki takura.." ya sake ce mata yana karfafa mata gwiwa...


Al-mustapha ya mike daga zaunen da yake yayi hanyar fita... Ta kakaro murmushi tache,


"Na amince....."


Gabansa sa ne ya buga alokacin daya jiyo amsar data bayar.... Wani abu ya taso ya tokare masa a wuya... Take ya fara jin kamar garin yana masa yawo ya kamo bango yana dafe da shi ya nufi sashen su ya shige daki ya murza masa mukulli ya kwanta..wayar sa ya janyo ya dan dudduba sai kuma ya ajiye kawai yana jin zuciyar sa na masa zugi..


"Tun baaje ko'ina ba na mallaka maki Hisham plaza.... Allah ya muku albarka."


Hajiya Ruwaida ji take tamkar ta fashe.... Alhaji jalaludden ya daga ya dube su yana tabe baki..sauran suka fara yi masa godiya suna mai taya amaal murnar gagarumar kyautar da aka mata..


Sun raba dare tare sunata hira kafin Kuma kowanne ya nufi sashen sa.. Suma su Hisham aka musu rakiya masaukin da zasu kwana kafin su koma gidan su dake unguwar gaban kandem estate.....




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/13, 12:41 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 31_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


....




*Yana* daga zaune abubuwan nata cin sa musanman da yaga ga tafiyar data karaato ga kyautar da akayi mata... Junaidu ya sake kere shi a komai na rayuwa bayan gurbin sa daya handame..


Wayar sa ya janyo ya shiga sako ya rubuta wa wasu lambobi sako......Ya gama bai wa zuciyar sa go-ahead akan hukuncin da ya zartar.. Dama lokaci yaje jira kuma ya cika..


Jerin sakonnin ta suna ta shigowa na amincewar gurbantar da rayuwar Amaal da za'ayi itama tana goyon baya... Yayi murmushin gefen baki yana dartse harshen sa..


Gaba dayan su... Sun amince da hukuncin da ya zartar...Sai daya tabbatar komai daya kintsa ya gama shiryuwa . Tukun sannan yabu lafiyar gado ya kwanta baccin bakin ciki ya dauke shi..


Hajiya Ruwaida ta kasa sukuni bayan sun bar sashen Hajiya maryam.. zantuka na ta cin ta suna addabar ran ta. Sashen Hajiya Hadiza ta nufa tanata sauri ta samu Hajiya hadiza ta sanar mata dukkanin abunda ya faru a bangaren Hajiyan...


Hadiza ta shiga zagaye sashen ta tana kaikawon yadda zata bullowa lamarin dama tuni an mata sako an sanar mata yadda komai ya kasance ta kuma gama kudurtawa a ranta yadda zata salwantar da rayuwar Amaal...


Don haka batai bacci ba sai da ta tabbatar data shirya yadda komai zai lalace akan Amaal da mahaifiyar ta....




WASHE-GARI....


Daga sashen su ta futo sanye cikin dogon hijabin islamiya... Tasha mamaki dataga securities din dake kula da sashen ba ko daya bayan dazu ta wuce su... Sai kukan kanaru kawai dake tashi..


Sai take ganin tamkar ana biye da ita a baya saboda inuwar da take gani ta gefen ta... Da ta waiwaya kuma sai taga ba kowa..


Ta dakko wayar ta da niyar kiran Hayateey kuma unfortunately ba service..


Wani hayaki ta fara ganin yana dosar inda take marar dadin shaka... Yana kuma hawa mata kai don tuni idanuwan ta suka fara kawo ruwan hawaye..


Nan da nan jiri ya fara daukar ta.... Ta fara ganin dishi dishin inuwar wasu mata sun doso inda take ga kuma wata mota data taho wajen su


Kokarin komawa take amman ta kasa saboda jikin ta ba karfi..... Tana jiyo hannuwan su a jikin ta suka chusa ta acikin motar...


Daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba... Sai farkawa tayi ta ganta akan wata kujera an kulle mata hannuwan ta ta baya sai zugi sike.. kafafunta ma an harde su waje daya an kulle.. hakama bakin da aka nane mata shi da wani abu mai danko..


Kokarin kwance kanta take tana mutsu mutsu ta kasa...gashi duk maganar da take a banza a rufe bakin yake ruf.. ambaliyar hawaye suka fara kwarara daga idanun nata..




*KANDEM ESTATE.....*




Yana zaune a faada anata faadanci wayar sa dake gefen sa tayi haske... Tamkar ba zai dauka ba sai ganin duk yan uwan ne a dabaibaye ba bare hakan ya sa ya janyo wayar tasa kasa kasa... Yafara dubawa...sako ne ya shigo ciki na,


"Na hane ka da waiwayowa kasar gaba daya kaa ki.... Daka dawo ma nache kar ka zauna a kandemi nanma kaki amincewa ka zauna.... Ka kuma amince aka baka abu mafi soyuwa agareni na sarautar birnin Nukaa.. Daman na gaya maka a baya... Sai kayi dana sanin dawowa Nukaa... Tabbas a yau dinnan wani abu mafi soyuwa a gareka ya bar ka kenan har gaban abadan...... "


Yana karasa karantawa ya mike.... Fadawan sa sukabi bayan sa ana tambayar lafiya ya dakatar da su...har ya nufi sashen Hajiya sai kuma ya fasa zuciyar sa na tabbatar masa da ya duba inda yake waswasi akai..


Sashen Hajiya jamila yaje... Tana tsaye zata futo kenan suka hadu.. ta rissina ta gayshe shi cikin kulawa ya amsa,


"Ina zaki?"


"Zan dubo yarinyar nan ne da kai na na aika iya bata sashen su nasa anje islamiya nan ma bata nan..."


Hannun ta ya kama ya shigar da ita cikin parlorn ta....


"Sun dauke ta ko? Sun sache mun amaal ko? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"


"Ba wanda ya isa ya sache ta, bar kuka" ya fada yana kwantar mata da hankali,


Ta ture hannun sa tana kuka sosai tamkar karamar yarinya tache,


"Ka gaya mun abunda ka sani... Junaidu"


Yadda ta fado sunan sa gatsal ba wasali yasan tana cikin wani hali. Ya sake rarumo hannunta cikin kulawa yace,


"BAKON MUNAFIKI ne..... Tabbas BANA MUTUM DAYA BANE.... Bansan su wa da wa yake hulda ba... Kai bansan ma ko mace bache... Kowa suspect ne.. fatana Allah yasa tana cikin aminci... Ki share hawayen ki Amaal zata dawo lafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa..."


"Idan suka mata wani abun fa?.. Ina nufin idan aka b....


"Karki karasa m... In shaa Allahu rabbi Allah ba zai bada galaba ba... Kalau zata dawo cikin amincin sa da kulawar sa."


"Toh Allah ya amince..."


"Allahumma Aameen"




Tashi yayi Hajiya jamila itama ta mike tana cewa da shi,


"Zan bika.."


"Faadar zaki bini?"


Ta girgiza kanta tana lankwasa hannuwa.. ambaliyar hawaye na zuba tache,


"Ya maganar amaal to...?"


"Jamila ki kwantar da hankalin ki dan Allah... Zanyi duk mai yiwuwa ganin Amaal ta dawo gidah" ya karasa fada yana dafe da kafadar ta cikin kulawa da ban hakuri...


Fita yayi ya nufi sashen Hajiyan su... Daman jikin sa ya bashi ba Hajiya ko baba aka aiwatar da mugun nufi akan su ba.daman yafi tunanin ko amaal da Jamila matar ta sa..


Yana shiga ya tarar da hajiyan da baba suna zaune da alama sun gama karya karin kumallo ne.. ya durkusa ya gayshe su cikin girmamawa... Yayi matukar mamaki da ya jiyo mahaifin nasa yace da shi,


"Alhamdulillah junaidu...."


Da sauri ya daga kai ya dube shi...


"Baba bakin ka ya bude?"


"Dama baki na a bude yake.. amman ba wanda ya sani sai mahaifiyar ku... Da kuma Maryam yar wajen ka.. yarinyar da Allah ya temaka ta ceto ni daga miyayun da ke son halaka ni..."


Hawaye suka cika idanun sarki junaid ya tuno Amaal dai an saceta bai san sanda yace,


"Baba... Sun dauke Amaal.... Sun dauke mai sunan Hajiya..."


Alhaji Muhammad ya daga kai da sauri ya bude baki zaiyi magana Alhaji jalaludden ya shiga parlorn yana gayshe da su .. ya daga masa kai kawai hade da kakaro murmushi,


Sarki junaid yayi shiru... Abunda ya faru alokacin ya sake daure masa kai.. to meyasa baba bai bude bakinsa agaban yaya jalaludden ba?


Kenan mahaifin na su ma ya gano jalaludden shine bakin mugun BAKON MUNAFIKIn da BANA MUTUM DAYA BANE dake assassa tuggu da makirci da mugunta a zuriyar Ardo kandemi?


___






#Ya labarin Amaal?su waye suka sache Maryaam Amaal??? ...
# BAKON MUNAFIKI....
(BA NA MUTUM DAYA BANE)
#A love Soo pure 💞
Love conquers All❗




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/14, 9:03 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 32_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___






"Yaya! Barka da safiya ........" Sarki Junaid ya danne zuciyar sa ya gayshe da yayan nasa cikin ladabi duk kuwa da tsantsar bacin ran da ke lode a ransa..


Jalaludden ko kallo Junaid bai ishe shi ba... Ya cigaba da danna wayar da ke hannun sa kawai yana mai gyara zaman gilashin dake sakale a fuskar sa..


Hajiya Maryam ta juya ta kalli mai gidan nata Alhaji Muhammad da shi din ma ita yake kallo...


Gyaran murya tayi ta dan dagaata yadda kowannen su zai jiyo ta sosai tace,


"Bappana..... Bakaji yana gayshe ka ba ne?" Hajiya Maryam tache da Hon.. Jalaludden.


Ya dan juya ya fuskance ta yana gyada kai yace,


"Ya rike gaisuwar sa Hajiya...."


"Bangane ya rike gaisuwar sa ba? Wai kai dan Allah me yake damun ka ne? Menene hakan kake yi ne saboda Allah?"


"Hajiya duk abubuwan da yake har yanzu bakya ganin laifukan sa sai ni?"


"Ni kake gayawa haka? "


"Kiyi hakuri Allah ya huci zuciyar ki.. kawai dai ya kamata ache kowa ya gama sanin halin wannan MUNAFIKIn me fuskoki biyu..."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Yaya wai dan Allah me na tare maka a rayuwa?"


"Ya isa hakanan... Ya ishe ku.. Yanzu neman inda yarinyar nan take zaa saka a gaba..."


'wacce yarinya?" Jalaludden ya tanbaya yana duban mahaifiyar ta sa da kallon karin bayani..


"Maryaam yar wajen ku mana..."


"Wacce Maryam kenan?" Ya sake tanbaya don baki daya ta bache masa akan sa.


"Maryam 'yar junaidu ta karshe yar wajen Jamila matar sa"


"An dauke ta fa kuka ce... Ya zaai azo har cikin gidan nan a dauke mutum?"


"Kana nufin baka da masaniya?" Sarki junaidu ya samu kansa da tanbayar dan uwan na sa..


Wata harara mai cike da dimbin mamaki jalaludden yayiwa junaid,


"Lalle baka da hankali.."


Hajiya Maryam ta daga musu hannu...hadi da janyo wayar ta ta lalubo lambar kawun su Adamu ta kira shi bugu biyu ya dauka bayan sun gaysa ne ta gaya masa abun da ke faruwa ta karkare da,


"Kazo bangare na..."


Tana gama waya dashi ta kikkira sauran iyalan nata... Ba jimawa kuwa duk hallara a sashan nata, har surukanta matan da 'yayan su...


"Hajiya wani abun ne yake faruwa?"


'muna cikin tashin hankali... Mun wayi gari da rashin Amaal... Ma'ana an sache ta bata nan"


Kawu Adamu ya bude baki cike da kidimewa da tsantsar tashin hankali yace,


"An sace Amaal kuma? Yaushe? Ba nan jiya harda ita mukayi ta hira ba?"


"Yau aka dauke ta"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun " bappah Nuraddeen ya shiga maimaitawa


Baki daya parlorn suka dimauce.. Aka shiga sallallami anata jajanta lamarin. Cikin kankanin lokaci aka baza labarin batar ta cikin filin cigiya.,


Kafafen yaada labarai... Gidajan rediyo, gidajen talabijin, jaridu da sauran tashoshi na yanar gizo sai haska batan Amaal suke yi.. Wanda Allah yasa ya gano inda take zai samu rabo mai tsoka na kyauta... Sannan ana neman barar addu'oi daga bakunan mutane masu albarka kan Allah ya bayyanata cikin aminci.


Cikin kankaknn lokaci masarautar kandemi ta cika da yan uwa da abokan arziki da suka zo jajantawa... Gefe daya kuma an baza dakaru na farin kaya dana sojojin sama dana ruwa da masu kananan khaki na gidah anata bincikar gano inda take..


Alhaji Abubakhar ma da iyalin sa ana sanar musu suka zo sashen Hajiyan suma sunyi matukar mamaki musanman Hisham da sunyi chat da itama da asubah ta lambar tata a WhatsApp


Hajjya Jamila tana cikin madaukakin tashin hankali mai wahalar fasaltawa. Ko abinci ta kasa ci. Hamid sai baya hakuri yake yana kokarin karfafa mata gwiwa.. shima baki daya ransa babu dadi... Zuciyar sa na masa radadi...


Amma inaa... Ta kasa samun sukuni. Idanunta tamkar garwashin wuta saboda tsananin tashin hankali. Muryar ta har ta dashe.. yayarta hajja Fauziyya ma Hamid na gaya mata cikin tashin hankali ta zo kandemi. Baki daya dai dangi sun girgiza musanman da akaji cewar ai har cikin gidan akazo aka dauketa ba waje ta fita ba...


"Amma abunnan da mamaki...... To menene alfanun dauke ta da akayi..? Wannan karamar yarinyar ma? Yarinya mai hankali da nutsuwa... Ran sarki ya dade ko akwai wani da kuke takun saaka? Ko kuma daga wajen gari ne kidnappers dinnan sai ahankali.. sun kira waya kuwa? Ina nufin wadanda suka sache ta..."


Sarki junaidu yayi shiru kansa akasa... Can ya dago ya dubi aminin nasa Alhaji abubukahr yace da shi,


"A iya sani na sa ma da kowa wanda ke nan zai iya bayarda sheda.. yarinyar nan batada abokin fadaa.. ita ba me kwaramniya bache bama ballantana ache sunyi hsyaniya da wani ko wata an dau fansa akai... Sai dai Ina tabbatarwa da koma su wanene sika yanke wannan danyen hukuncin... Tabbas don ni akayi.."


"Subhanallahi.. junaidu kasan me kake cewa kuwa? To Kai din ai halin ka tayi.. dika Kai da mahaifiyar ta ba kuda abokin faada ba ajin kan ku da kowa... Ya zaka ce haka?" Kawu Adamu ya tsawatar masa..


"Kawu ku amince.... Wanda ko ince wadanda suka dauke Amaal ba yan waje bane... Daga zuriyar Ardo kandemi ne... A tsakanin mu ne... " Cewar sarki Junaid.. ransa ba dadi.. kana kallon sa kasan yana cikin damuwa marar misaltuwa


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Me kake nufi junaidu?" Gwaggon court ta tambaye shi fuskar ta dauke da damuwa.


"Ina nufin dan zuriyar nanne ya dauke ko ince suka sache ta.."


"Ranka ya dade yan zuriyar nan fa kache... Meyasa kake tunanin haka?"


"Ba tunani nake ba... Daman ansha tsoratar da ni da mugayen kalamai ta kafafen sadarwa ko ta text messages ta nambobi kala kala... Tun sakonnin basa gabana har lamarin ya fara bani shakku akai... Nagano tabbas akwai me bibiyata yana son yaga bayana... Kuma wadannan sakonni da ake turomun na tsoratarwa ba iyani kadai ba har wasu daga cikin iyalina ma anayi wa tun muna kasar waje kafin ma mu waiwayo gidah. Bayan mun dawo dinma baa dena turowar ba. Ko yau bayan an sache ta dinma sai da aka turomin sako... Ina faada kikavin kilama kafin a sace ta dinne..."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. " kawu Adamu yayita mainatawa cikin damuwa sosai.


“Abunda yasa aka dauke Amaal saboda ta ceto rayuwar Baba gashi a zaune dan dai ba zai iya magana bane bakinsa a rufe….”


“Me kake nufi kache junaidu” cewar prof Abdullah… shi dama dan boko ne babu ruwan shi da shiga sabgar su sosai. Kullum cikin karatu yake


“Ina zuwa… Bari kuji.” Wayar sa ya dakko ya sanya recordings din duka na binciken da akayi nasa akan allurori da karin ruwan da akewa mahaifin nasu don akashe shi.


“Innalillahi wa inna ilahi raji’un … Ke duniya Ina zaki damu? To akan duniya sai mutum ya nemi ya kashe rai? “Kawu Adamu ya fada yana jinjina lamarin.


“Amaal Itace wadda ta ceto rayuwar Baba………” ya fadi dukkanin abubuwan da Amaal ta fada musu tun ranar farkon data fara zuwa bangaren da alhaji Muhammad yake jinya. Ya k’ark’are da,


“Shine cikin dabara da hikima ta dakko allurorin da ruwan su da kuma karin ruwan da akeyi masa… kun dai ji da kunnuwan ku muggan tsibbun da akayi amfani da su ana masa karin ruwa. Haka kuma allurorin lalata masa gabbban jikin sa dama komai nasa ne baki d’aya allurar da akewa dokuna don rage musu kuzari a kasar waje... Texas precisely.. rabi fa kunji akeyi wa dokunan amman shi baba fin d’aya ake yi masa…..”


“Innalillah wa inna ilaihirrajiun duk a Yaushe akai haka?” Gwaggo aisha ta tambaye shi tana girgiza kai.


“Yaya nuraddeen, Yaya jalaludden, Almustapha da aaayan lokacin da kuka hadu da Amaal a bakin gate zaku shjga wajen baba kuna shiga kuka tarar da shi ya farfado ko?”


“Tabbas bima naje na same shi har yana ninke rigar sa,Bayan sun kira ni…” Kawu Adamu ya fada yana tsiyayar da hawaye..


“Me kake nufi junaidu? Me kake son cewa? Nufin ka acikin mu BAKON MUNAFIKIn yake?” Alhaji jalaludden ya tambaye shi idanu cikin idanu.


“Yanzu na gama maganar nan dai anan wajen…. Kamar yadda na fada zan sake maimaitawa… Ranar da Amaal ta jiyo kukan baba da numfarfashi da yake yi yana sauke ajiyar zuciyar wahala…. Wanda ya shiga sashen bayan likitocin sun kammala allurorin su kai ka shiga yaya..”


“Kana nufin kache ni ne zan kashe mahaifin mu kenan?”


“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Wannan Duk bata ta so ba… Kuyi hak’uri rashin fahimta ne.” Kawu ya shjga raba tsakanin su ganin sun hayayyakowa juna zasuyi fada


“Gashi kunaji yache ni na shiga.”


“Eh yaya kai ne ka shiga… kai ne wanda ka kira waya kace ‘Mungode sosai sun aiwatar da komai yadda akeso cikin kwarewa.’ Ka kuma bawa likitocin da suke masa allurorin kudin mota suka tafi…..”


“Innalilahi wa inna ilaihirrajiun….. kunajin abunda yake cewa?”


“Wanene mai turamun sakkonni a waya na barazanar Kar na waiwayo Nukaa? Kar mana dawo kasar gaba d’aya? Wanene wanda ya ke kullallaliya aka kafe ni awaje naki dawo wa gidah’ wanene baya son ganin Farin ciki na dana y’aya na? Ko gayshe ka sukayi baka amsawa musanman Amaal…. Me ta tsare maka? Ku kalli tarun sak’onnin baranazar da yake aiko mun kuma dama duk kuna wajen sanda aka ce ni Za’a bawa sarautar kandemi wane Furuci yayi? Karya nayi?”


“Dan Allah abar maganar nan…”


“Ba za abari ba Aisha… Rabu da shi ya cigaba…”


“Kache ka tsanani, ka tsani wanda yake kaunata ma ka tsani ka wayi idanu ka ganni a kandemi… Duk akan sarauta? Kasani dai dai da minti d’aya bantaba kaunar rawanin nan ba. Kuma a yau a dai dai yanzu ni junaidu na sauka daga karagar mulkin kandemi.. A dawomin da ‘ya ta… Zan tafi na bar maka kasar gaba d’aya, Ga rawanin ku nan...."


Alhaji jalaludden ya mike… Cikin fushi ya daga hannu ya shararawa junaidu mari, Sai da kowa ya girgiza yace


"Kache ni ne me?"


Sarki junaid ya mike tsaye ya saka hannu ya nuna shi da

Please Login or Register in order to submit comment