Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Al-mustapha yaja ya dankara masa lafiyayyar harara yace,


"Kaketa wannan dogon turancin da ko saninta bakai ba? That aside naga budurwar kache tazo kuna zance amma bata gaban ka kana planning auren wadda baka ma san sunan ta ba... Banza mahaukaci. Ka cika yaudara wallahi ", Ya karasa fada yana mai jan dogon tsaki..


"Look.... Naji kache sunan ta Maryam Amaal... A'ina ka santa?"


"Kai a'ina ka santa?"


"Student dina ce mana..."


"Ni kuma cousin dina ce... First cousin ma kuwa"


"Shikenan... Yaya Al-mustapha... In-law... Dan Allah kabani ita"


Al-mustapha ya daga kai ya sake hararar sa yana girgiza kai,


"Kacika kule kulen yammata"


"Wai waccen yarinyar nacacciya datayita kirana har yau na amince muka hadu? Maza wallahi bata gabana.. tun a Instagram take bibiyata kasan tsawon shekarun da take nace mun kuwa? Bamu taba haduwa ba sai yau shima gajiya nayi da nacaccen nacinta tacika stalking yau dai na ce sai dai tazo my hadu ni bazan samu zuwa ba.. tana ta roko na shine fa tazo..."


Al-mustapha ya taba baki yana yamutsa fuska,


"Ka yarda dani mana... Yauwa sannan tare suke ma da ita Maryam Amaal din"


"Kawarta ce ko?"


"No... Not really... Baby H din tace amaal kanwar kannenta ne da suke uba daya...yadda na lura kaman amaal din agidan su baby H din take a zaune ko? I dunno dai...cuz inata tanbayarta akan Amaal din taki bani amsa kaman basa good terms haka.. kasan mata one can't tell... "


Al-mustapha yayi shiru yana jujjuya sunan wai baby H...


"Wai Hindu?"


"Exactly... Amma dai da baby H na santa"


"Okay...."


"Kasanta?"


"Well... Yar uwata ce dai itama... Amma ba kaman yadda muke da amaal ba... Duka dai agidah daya ake under same roof.. Amma dai ita Hindu din itace ke agidan su Amaal din"


"Woah.... Amma ita meyasa take haka?


"Bangame take ba? Me kake nufi.. oho dai matsalar ku ce kai da ita... "


"Ni fa kade na hadani da ita wallahi bana son ta."


"Amma kai banza ne wallahi . Baka santafa kache.. akan wane dalilin tataso tazo har wajen ka?"


"Daya daga cikin abunda yasa bana son ta kenan ma... Batada kamun Kai... Kicewa saurayi ko'ina yake zaki zo ki same shi bakya jin fargaba? Na biyu kizo da wata iriyar shiga dake nuna tsiraicin ki awaje? Na uku tasaka wani seductive turare saura kadan nayi aika aika Allah yatemaka wallahi korarta fa nayi... Could you imagine.... Tana saka hannu tana wani tattaba ni... Tana macen? Ina martaba da kimar ta suke? Wai ahaka kake tunanin zan zabeta komai awaje ga Amaal dake killace jikinta da komai nata yarinya me nutsuwa da hankali? Kai nifa nayi mata wallahi.... Ka gayawa su Bappah zan aiko manya gaskia... Aurenta kawai nakeson yi ba sai an dau wani lokaci ba..


Al-mustapha ya mike bayan ya girgiza masa kai kawai,


"Meye haka muna magana?"


"Office zan tafi mana..."


"Magana mike fa akan Amaal kanwar ka . Da nake so da aure"


"An bada ita tuntuni...."


"Bangane ba...?"


"Ina nufin an bawa wani auren ta tun tuni..." Yana karasa bashi amsa yayi gaba abinsa


Habibi Talba yabi bayan sa yanata kiran sunan sa..


"Aboki na sai mun sake magana... " Al-mustapha ya fada yana mai bashi hannu sukayi musabaha


Wani malami da zai zarta su a shekaru yazo wucewa suka tsaya suna gaysawa...habjbi talba ya nuna Al-mustapha yana cewa da dayan malamin,


"Shine amini na da nake gaya maka fa... Architect Al-mustapha jalaludden........


...
_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/10, 10:09 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 29_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


---
Habibi Talba ya saka hannu ya dafa kafadar malamin ya cigaba da cewa,


"Al-mustapha wannan shine architect kuma Dr, Aliyu da nake gaya maka guru ne a faculty din nan... Shine overall best kaman kai.."


Al-mustapha yayi murmushi... Shima Dr. Aliyu murmushin yayi... Suka hada hannu suka sake gaisawa,


"To Dr.. Aliyu da Habibu sai na sake zagayowa in shaa Allah.."


"Zakaci uban ka idan ka sake cemun Habibu na gaya maka sunana Habibi banason wulakanci.. alright sai nazo sake ganin sabon office in shaa Allah..Allah yasa an bude a sa'a Allah kuma ya sanya alkhairi."


"Allahumma Aaameen.."


"Toh Arc.. Al-mustapha sai anjima.." Dr Aliyu yayi masa sallama.. ya bawa habibi Talba hannu suka sake gaysawa ya shige ciki...


Shi kuma Al-mustapha ya shiga cikin mota ya zauna zai bar wajen .. Habibi Talba ya sake zura kansa ta glass.. ya saka hannu ya tokare da hannuwan sa duka biyu,


"Meye ne?" Al-mustapha ya tambaye shi cike da kosawa,


"In-law please .."


"In-law din uban ka?"


"Aboki na please hear me out... Allah ba da wasa nake ba inason Maryam Amaal kaga yadda malamai ke admiring nata kuwa? Kasan beauty with brains ce wallahi.. komai ta hada .. "


"Okay bama kai kadai bane kenan kuna da yawa?"


"Kwarai haramun ne?"


"Amma anyi mutanen banza masu son daliban su"


"Lefi ne?"


"Dalla matsar da hannuwan ka zan tafi ni."


"To wai kai ba abun farin ciki bane ace kanason kanwar ka?"


"Matsa na wuce Malam..."


Habibi Talba ya bude baki can ya saka hannun sa ya rufe baki yana nuna Al-mustapha da yatsa..


"Menene?" Al-mustapha ya tambaye shi yana tada motar da key..


"Ko son ta kake ne? Saboda gaba daya mood dinka ya canza."


Al-mustapha yaja dogon tsaki yana buga siriuyari...


"Nake son waccen yarinyar? Allah ya kiyaye..."


"To ai yadda kakeyi ne kowa zai ce sonta kake ... Mood dinka fa gaba daya ya canza... On a serious note..jokes aside"


"A jerin matan da nake so bata ciki ..... Ai idan nace maka Ina son waccen yarinyar to ka kirani da garanbawul.... Wanda zai yi reno don kwa reno zaka yi... Yarinya ce fa danya sharaf. Yo waccen idan nace ina sonta ma ai sai reni ya shiga tsakanin mu .. batada qualities din da nake so ajikin mace gaba daya.... Ko abu daya bata dakko na."


Habibi Talba yaja tsaki yana masa wani kallo,


"Na yadda baka son ta . Amma karya kake kache yarinyar nan batada qualities din da zaa sota.... Kana ganin mache option komai yaji kache wani bata da.. Mtscew nama rasa me zance maka.. Kai ai inaga baa haifi yarinyar da yau zakace kana son ta ba... Shekarun ka dai kullum karuwa sike ka zauna kana ruwan ido.. idan ni da amaal mukayi sure muka haihu sai mu ..


Bai karasa ba Al-mustapha yasaka hannu ya cire hannuwan Habibi Talba yayi reverse yaja motar yafita daga faculty din gaba daya cikin kurewar gudu mai tattare da kwarewa.


Habibi Talba yayi murmushi kawai yana girgiza kai... Ba sabon abu bane halayen Al-mustapha kala kala na ban mamaki... Sai dai shi wani irin mutum ne mai madaukakin kirki marar misaltuwa... Duniya baki daya bata dame shi ba.. yanada Ibada sosai da sanin ya kamata bsshida wani hali na makuusa... Kuma dai akan mache bai taba ganin yayi haka na. Domin bashi da lokacin kula yammatan ma tun suna karatu awaje haka halayyar sa take...


Irin su night outinngs dinnan su clubbing da sauran su duk bayayi... Kullum yana gidah yana game ko yana karatu ko yana wani abun daban na debe kewa da zai kebance shi kadai


Amma yayi mamaki da attitudes din daya bashi na ranar... Amman ya dau hakan a matsayin tsananin kiyayyar da yakewa cousin din tasa kaman yadda ya gaya masa..


Haka habibi Talba ya koma motar sa ya bude ya curo ipad ya nufi wani aji da zai koyar da su ganin lokaci yayi... Gefe daya kuma yana mamakin tsanar da Al-mustapha yayiwa Amaal dinma domin shi a haduwar su ta farko daya fara shiga aji zai koyar dasu yaji ya kamu da kaunar ta... Dabi'un ta na yau da kullum kuma suka sake ingiza wutar kaunar ta a ran sa..



Al-mustapha yana tafiya a mota yana tunanin maganganun Habibi Talba... Wai yana kaunar amaal kuma so yake ya aureta batare da an dau lokaci ba..


Tsaki yaja... Hannunsa daya akan sitiyari dayan kuma ya dora shi akan glass ya dafe kansa...


Lokaci zuwa lokaci ya kan saka hannun nasa akan girar sa ya sosa a haka ya karasa sabon ofishin sa na...


'Architectural excellence..'


Direba na ganin motar ya tashi da sauri ya bude masa gate ya shiga ciki,


"Sannu da zuwa yallabai"


"Barkan mu dai.... Kana lafiya?"


"Alhamdulillah ranka ya dade..."


"Mashaa Allah.."


Rufe murfin motar yayi ya shige cikin office din...sectary dinsa na zaune akan kujera da computer agaban ta tana dannawa... Tana ganin sa ta yashare baki tana gayshe shi,


"Sannu da zuwa sir.."


"Sannu kina lafiya?"


"Alhamdulillah sir..."


Shigewa yayi cikin office dinsa bakinsa dauke da sallama... Ofishin ya hadu kwarai matuka.. dauke da kujeru set daya samfarin Italian...


Harda dinning area da bookshelf agefe shima... Ga fridge dinsa nan da closet daga gefe...sai dispenser da wani katon agogo mekyau shima... Can daga bakin kofa kuma hanger ce ta hanging kaya... Komai dai unique ne a ofishin na sa..


"Ya akai sadya?" Ya tambaye ta ganin ta biyo shi ciki..


"Sir... Dama wannan mutumin ne ya sake zuwa wai ga orin designs din da yake so nan.. yace ka temaka ka dauka kiran sa please cikin satin nan yake son zanen zaa fara masa ginin."


Al-mustapha ya dau takardar data ajiye yana karantawa.. ya yamutsa fuska bayan ya daga mata kansa,


"Ba damuwa..."


"Sir ba wani abu da kake so a kawo?"


"Babu... Nagode"


Har ta kai bakin kofa zata fita sai ta jiyo tanata mammatsa hannuwan ta,


"Ko a hado maka iced tea dinnan?"


"No thanks.... "


"Ko co",


"Banason komai..."


"Sir ko..."


"Check out... Haba!" Ya fada da karfi hadi da saka yatsa ya nuna mata kofa


Da sauri ta futa jikin ta har yana rawa saboda tsananin tsoro... Tana fita ya sauke zuciya ya zauna akan kujera yana girgiza kansa da hannun sa daya ya dora akai.. Hadi da furzar da zazzafar iska daga bakin sa.....


Bayason takura... Gashi ransa ba dadi daman a jagule yake . Ita kuma sadya ta cika cinkisa sai kwazazzafar maganar tsiya..


Duk sai yaji abunda ya mata bai kyauta ba duk kuwa da ba lefin sa bane amman bayason ganin bacin ran mace musanman idan ta zubar da hawayen ta,


Mikewa yayi daga zaunen da yake ya fita daga office din. Dama kana fita daga office dinsa sai dan bangaren da take ...zagaye yake da wani hadadden design da akayi mata..


Dauke da kujera mekyau da computer.sai yar dispense dinta itama awaje karama da mini fridge sai photocopying machine da typewritter..


Ya nufi inda take zaunen ta hada kanta da benchi tana rera sautin kukan ta a hankali... Kukan nata na dada sashi yana jin haushin kansa . Bayason yaji ko yaga kukan mace gaba daya a rayuwar sa..


Ya saka hannun sa ya dan daki benchin data kwanta ya kuma rankwafa cikin muryar rarrashi yace,..


"Sadya..... "


Kin dagowa tayi ta cigaba da kuka tana rerashi a hankali...


"Sadya.... Please... Ki dai na kukan nan... Ki yafe mun kuma kinji? Raina ne ba dadi .. Na kuma ce miki idan mutum yana cikin wani yanayi ki dena takura masa da magana.... Sadya... "


Dagowa tayi da kanta data ci kuka ta koshi... Ya janyo handkerchief dinsa ya ajiye agaban sa.. ta daga da sauri ta kalle shi yace


"Ki share hawayen ki... Ki dena kuka kinji? "


"Tohm sir..."


"Yauwa sadya.. To ni zan tafi sai gobe idan Allah ya kai mu"


"To shikenan sir... Allah ya tashemu lafiya"


Ya dan daki benchin gaban sa ya kara murmushi ya mata sallama sannan ya saka kai ya fita..


"Yallabai zaka dawo yanzu ne?"me gadin sa ya fada yana rissina masa


"Sai zuwa da safe in shaa Allah . godiyy nake.. Allah ya tashemu lafiya"


"Allahumma Aameen ranka ya dade.",


Al-mustapha ya shiga cikin motar sa ya key tayar da jta ya dauka hanyar gidah..


;;;;;;;;;;;===========


*KANDEM ESTATE*


Direba na ajiye su a gidah ta wuce sashen mahaifiyar ta.


"Kin dawo?" Hajiya jamila mahaifiyar ta ta tanbaye ta... Bayan Amaal din ta gayshe ta


"Na dawo Hayateey.... Washh! na gaji"


"Sannu... Ga abinci can an gama ai, Na zubo miki?"


"Dan kadan amma ba yunwa nake ji sosai ba munci gurasa."


"Tohm.."


"Yaya ya dawo?"


"Ya dawo..Amma ya sake fita"


"Oh okay...."


"Yi sauri ki gama zamuje kasuwa"


"Kasuwa?"


"Eh sayayyar abubuwan da zaa dafa wa baki... Da zan aika iya kuma kar na manta dawasu abubuwan"


"Baki kuma?"


"Oh eh... Aminin abbiey dinku ne zasu zo da matar sa inaga da hisham ma."


"Okay ALLAH sarki... Zuwan me kuma?"


"Ai wai Nukaa zasu dawo gaba daya... Kuma akwai maganar da zasuyi wai muhimmiya.... Abbiey din naku yace shima bai san maganar meye ba dai... It shall be well"


"Da zama gaba daya a Nukaa ?" Ta fada tana gwalalo idanu


"Eh......"


"Allah sarki..."


"Yi sauri ki ci abinci.... Ki gama dai komai kizo mutafi"


"Tohm..."


Haka dai ta karasa dukkanin abubuwan da zatayi... Suka tafi kasuwar.. Suna dawowa suka fara abubuwan dik da suka dache na daga girkuna, gyaran gidan da sauran su....


Yamma lis sai ga shigowar motocin su gidan cikin convoy....
___


_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/13, 11:37 AM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 30_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___




A jere motocin suka shiga cikin kandem estate... Kai tsaye suka nufi faada inda za'a sauke su... Ranar daman ba'ayi zaman faada ba saboda mai martaba na da manyan baki... Kwana biyu kuma baya jin dadi sai wazirin sa ne ke zama...


Suka bubbude motocin suka furfuto...Harda masu aiki da matemaka na farin kaya..


Suka furfuto daga shiga cikin motocin bakin su dauke da sallama... Aka shiga amsa musu ana musu lale marhaba


Sunyi kyau cikin kayan da su kayi matukar dacewa da su....


Mahaifiyar Hisham tayi shiga ta alfarma cikin wani dandatsetsen lace daya sha kudi ya koshi.. Ya sha uban su stones da suka kara masa kyau da kyalkyali...


Da ma'aikatan ta na biye da ita .. Sai Hisham dake sanye cikin manyan kaya da sukayi matukar karbar jikin sa..


Zatin haibar sa ya sake futowa. Tamkar an kara masa kyau saboda yadda ya sake wani irin kyau lokaci daya..


Alhaji Abubakhar yana gaba suna biye da shi da da sauran maaikata suka shjga cikin faadar da aka yo musu iso..


Cike da farin ciki marar misaltuwa sarki junaid ya fara murmushi zai mike daga zaunen da yake Alhaji Abubakhar ya tare shi yana rissina masa,


"Wane mutum.. ranka ya dade... Allah ya jya maka..." Ya durkusa yana sara masa..


Sarki Junaid ya dawo kusa da shi ya zauna yana mai bashi hannu suka gaysa,


"Godiya nake yallabai.. Allah yakara lafiya da nisan kwana... Mai Nukaa gaba dayan ta


Sarki Junaid yayi murmushin kalaman da Alhaji Abubakhar yake gaya masa yace,


"Tare da kai aminin kwarai... Alkhairin Allah ya bi maka a duk inda kake.."


"Allahumma Aameen..",


Nan take aka fara gayshe gayshe a fadaar cikin girmamawa da sanin ya kamata..


"Ah harda babban pilot...?" Sarki Junaid ya fada yana kallon Hisham,


Hisham din ya matsa kusa da shi yana murmushi hadi da sosa keyar sa yace


"Eh ranka ya dade. ... Ban koma hutu ba tukun"


"Ma shaa Allah... Allah ya bada sa'a ya kara tsarewa."


"Allahumma Aaameen.."


Nan da nan maaikatan suka fara cika gaban su da kayayyakin motsa baki kala kala da abun sha.. lamarin sai wanda yake wajen kawai..


Hisham sai dan waige waigen fadaar yake yi. An sake kawaata ta da kayan more rayuwa yan waje.


Hajia Aisha mai dakin Alhaji Abubakhar yana gefe tare da su Hajiya Ruwaida... An zuzzuba mata komai a plates a gabanta.


"Ina sauran yaran ne.... Wannan ne bansani ba?"Cewar Alhaji abubukahr hadi da nuna Al-mustapha daya shiga faadar ba dadewa.


"Barka da yammaci."


"Barka dai..."


"Al-mustapha ne... Babban 'dan mu .. shine na fari awajen Yaya jalaludden sai kanwar sa Fatima Yusra."


"Allah sarki... Ga kamar nan kuwa... Ai ku da yake ma shaa Allah ana debo kamanni."


Shi dai Al-mustapha yana gefe sai kakaro murmushi kawai yake.. Hajia maryam ce tasa shi agaba lalle ya tashi ya shiga cikin mutane yan uwa ya dena raraa gefe yana komawa baya.. don sam Al-mustapha bayason hayaniya. Dik inda aka cika waje to fa tashi yake yi ya bar wajen kome akeyi.


"Ai ma shaa Allahu kam... Ana debo kamanni." Jamila Ina yaran nan ne?"


"shiryawa suke... Zasu zo in shaa Allahu..",


Tana fada Hisham ya samu kansa da sauke katuwar ajiyar zuciya.. Daman so yake kawai yayi tozali da Amaal sahibar sa..


ร—ร—ร—ร—ร—.


Amaal na daga zaune akan gadon ta tana gyara zaman agogon ta data saka shi a wutsiyar hannun ta ..


Ta dan dauki wayar ta tana kallon fuskar ta ta camera.... Ta gama gyara komai ta dakko mild turaren ta (marasa karfi) ta faffesa..


Hindu dake tsaye awajen closet dinta tun dazu rike da wayar a hannun ta. Lokaci zuwa lokaci takan saki tsaki tana sake duba fuskar wayar da alama.. Sako take jira ya shigo. Domin tun jiya batada sukuni. Amaal na jiyo Hindun da daddare tana gayawa su ikhram saurayin ta Habibi Talba bai neme ta ba. Ta kira shi baya dauka ta kuma masa magana ta WhatsApp nanma beyi responding ba..


Ji kake taratststs... Wayar hannun Hindu ta fadi a kasa dai dai lokacin da amaal ta mike zata futa... Ita kuma Hajiya hadiza tayi sallama dakin nasu tana,


"Ku futo abbiyen ku yana tanbayar ku bakin sun zo...",


"Kan babban balain can....." Hindu tayi kukan kuraa ta cafki wuyan Amaal.


Amaal ta shiga neman kwacewa tana,


"Meye haka? Mena miki.."


"Menene Hindu .?" Hajjya hadiza ta tanbayeta tana kokarin raba su


Hindu ta fashe da kuka tana mai nuni da Amaal.


"Allah ya isa tsakani na da ke... Allah ya isar mun Allah ya miki abunda kika mun... Wayyo Allah na"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Yaya Hindu? Me zan miki? Wallahi ba abunda na miki.. Meya faru dan Allah?"


Hajiya hadiza ta buga mata harara ta karasa kusa da Hindu ta riko ta tana janyo ta jikin ta cikin muryar lallashi tache,


"Wani sharrin ta miki? Me ta hada miki? Halin uwar ta ta dakko ai... Mamugunta masu mugun baki."


"Ta rabani da shi Mama.. ta raba mu"


Amaal ta saka hannuwan ta dafe kirji don batada masaniyar lefin da take ikirarin tayi mata shi,


"Da wa ta raba ki Hindu? "


"Kinsan rannan tare mukaje school da ita ai... Malamin su ne... Muna fa wayar mu bakiga hirar da mukeyi da shi ba.... Mun fuskanci juna sosai ..Tunda muka rabu na dawo gidah naga be neme ni ba ba waya ba ba magana, Dana kira shi baya dauka.. beyi responding to messages din da na tuttura masa da su ba.... Shikenan innalillahi wa inna ilaihi rajiun.."


"Hindu ki nutsu ki gaya mun meya faru... Wani sharrin ta kulla miki haka?"


Hindu taja hanci tana cigaba da tsiyayar da hawayen fuskar ta tache,


"Yace mun shi Amaal dinnan yake kauna yake kuma burin ya aura... Wai shi da yan gidan su zasu zo wajen abbiey su nemi auren ta... Harda cemun dan Allah na fada agidah shi dagaske yake ba da wasa ba ya kamu da kaunar ta... Wannan wacce iriyar musiba ce? Wane irin bakin asiri ne sukayi haka suka raba mu farkon haduwar mu da shi?'


Amaal na tsaye sai ta zube akan gado tana dafe kirji.... Idanuwan ta sun fuffuto waje,


"Shegjya algunguma me raba soyayya..." Ikhram ta fada tana banka mata harara,


"Makira dangin asiri ba.." cewar Ikhlas tana tabe baki..


"Dama wallahi tun ba yau ba nasan farin jinin yarinyar nan bana Allah bane... Har muka gama school duk mazan ajin mu son ta suke.. kowa yace itace crush dinsa..." Najwa ta fada itama tana kallon amaal din hade da tabe baki..


"Har teachers kin manta? Abun da zai sake daure miki kai kowa fa? Duka mazan don balain bakin asiri..." Na'eelah dake gefen su ta fada itama..


Ita dai Amal hawaye ne take masu zafi suka fara zubowa daga idanun ta.. maganganun su na dada daga nata hankali.... Ita dai tasan tunda take bata taso taga Hayateey dinta na asiri ba.. kusan su aka tsana a dangin gaba daya ma sai yan shekarun da basu wuce biyar ba komai ya fara warwarewa akeyi da su..


Farin jinin kuma tun tana karama tasan haka kowa yake cewa yana sonta. har tayi ta kuka tana gayawa Hayateey ita ta gaji...


"Kina che me?" Hajiya hadiza ta tanbayi Hindu tana jujjigata idanunta tamkar zasu fadi kasa saboda tsabar tashin hankali sai zaro su take.


"Ita zai aura...ita yake so. Har da wani ce mun nayi hakuri Allah ya bani wani nagari kuma na temaka na dinga suturta jiki kome... Wayyo Allah na habibi Talba fa .. "


Hajiya hadiza ta nufi Amaal ta daga hannu ta wassaka mata maruka dika kuncinanta biyu. Amaal ta dafe wajen da sauri tana hawaye..


Ta kifa kanta akan cinyar ta tana shesshekar kuka.....


Alokacin kuma wayar Amaal ta fara kara. Hayateey ce ke kiran ta... Ta katse ta sake kira.


Hajiya hadiza ta dau wayar ta cullar gefe ashe ta danno amsawa,... Cikin fushi da hasalewa tache,


"Sai na salwantar da rayuwar ki...Amaaal sai kinyi dana sanin shiga hurumin da ba naki bane..."


Tana gama magana ta riko kafadar Hindu suka fita daga dakin... Su ikhram sika bi bayan su suna aibata Amaal..


Ita dai Amaal ta kife kanta tanata kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara...duk yadda taso ta danne bacin ran ta ta kasa ta cigaba da zubar da hawaye kawai ta na jinjina akan abunda bata aikata ba ba kuma tasan da shi din ba...


Alhaji Abubakhar ne ya sake tanbayar inda amaal take ganin yaran duk sunzo ba ita...


Hakan yasa hajia jamila take ta jujjuya abunda kunnuwanta suka fara jiyo mata awaya duk da bata jiyowa sosai... Amman tabbas muryoyin su ne da ta Hajiya hadiza..


Iya ta kira a waya tache taje ta dubo mata Amaal su kuma futo tare, Ta same su a bangaren Hajiya..


Alokacin kuma suka rankaya sashen Hajiya Maryam don duba jikin Alhaji Muhammad da kuma gaishe da su .


Amaal ta shigq bakinta dauke da sallama... Idanuwan Hisham akanta ta tsuguna ta gayshe da su cikin girmamawa

Please Login or Register in order to submit comment