Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba. Na san dai sunan sa"


"Allah ya rufa asiri... Ni dai na gaya miki a ko'ina kike ki tsare nutincin kan ki ... Baki da muharraami sai wanda kuka fito tsatso daya...Allah ya cigaba da kare ki ya tsare miki mutuncin ki har gaban abadan"


"Allahumma Aameen Hayateey.."


"Bari na duba Hajiya"


"To sai kin dawo. Ki gayshe ta"


"Tohm"


Fita tayi... Wata bakar mota ce ta fita daga sashen kakan su. Mutanen nan biyu na rannan wadanda take da tabbacin likitoci suka fita daga bangaren..


Gabanta ya tsananta bugawa. Ta waiwaya sashen hajiyan sai kuma ta mike wajen kakan na su tanata waiwaye waiwaye..


Shiru ba kowa kamar rannan... Ta karasa bude kofar dakin a hankali. Tayi mamakin data ganshi akwance idanun sa a abude.


"Kakaaaa..Assalamu alaikum..." Tayi har sau uku bai ce komai ba.


Ya kasaa magana yayinda yaketa Mata nuni da idanu ta Karin ruwan dake shiga hannun sa.


Da sauri ta karasa kusa da shi idanun ta taf da hawaye. Hanun ta na rawa ta bude drawer dataga rannan sun saka allurar nan. Ta dakko da sauri ta saka wata leda data gani a gefen gadon.


"Sannu kaka..."


Hawaye na zuba a idanun ta. Haka shima nasa idanun sunata kwaranya. Dik nunin da yake mata da idanu na karin ruwan ta kasa fahimta..


'idanun ka ne ke ciwo?" Ya lumshe idanun ya bude


Dakyar ya jya fitar da harshen sa dake masa zafi da radadi da nauyi ya karkata shi yana mata nuni da Karin ruwan.


Jikin ta na rawa ta daga Kai ta kallo ruwan. Wasu abubuwu ne acikin sa, Nan da nan ta zare masa ta cire ruwan ta saka a wannan ledar.


Da sauri ta bude kofar ta fice da ledar a hannun ta... A kofar gate din bangaren ta hadu da Bappah Nuraddeen da Bappah Jalaludden da Aayaan da kuma Al-mustapha zasu shiga ita Kuma zata fita...






_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/5, 9:49 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BM_




_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 25_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


Jaa tayi baya da sauri... Ta tsugunna akan ledar..


"Barkan ku da safiya...." Ta fada hannun ta a kasan ta tana mai chusa ledar...


"Barkan mu dai.... Mai sunan Hajiya" Bappah Nuraddeen ya fada fuskar sa kumshe da murmushi marar misaltuwa.


"Na'am Bappah..."


"Favorite cousin sissy.."


"Yaya Aayaan.."


Bappah Jalaludden yayi gaba abun sa Al-mustapha ma bai bi ta kan ta ba yabi bayan mahaifin sa.


"Babaa kika zo dubawa ne? Sannu da kokari."


"Eh....Amma ban ma ganshi ba"


"Sannu angode.... Allah yayi albarka"


"Aameen Bappah"


Sai data ga sun shige cikin gidan sannan ta mike ta dau ledar da sauri ta fiche.


Gabanta na tsananta bugawa ta wuce sashen mahaifiyar ta. Bakin ta dauke da sallama ta shiga...


"Hayateey...."


"Bata nan Amaal."


"Sannu da aiki iya..."


"Yauwa Amaal.. Ga abinci can kan dinning"


"Tohm iya.. Nagode"


Sama ta hau da sauri..... Dakin da yake a matsayin nata wanda ba kwana take ba ta shiga. Ta ajiye ledar ta bude da allurori a kwali da sirinji da wasu ruwan allurorin , Gefe daya kuma ruwan karin ruwan ne shima aciki bakikkirin da wasu abubuwa acikin sa da karare...


Tsayawa tayi tana bin su da kallo...Ta sauke nannauyar ajiyar tana cije kasan leban ta.


Drawer din jikin dressing mirror ta janyo ta zura ledar aciki, zuciyar ta na sak'a mata abubuwa da dama na yadda zatayi da kayan data dauke..



Karasa shiga sukayi. Bappah Jalaludden ne agaba Al-mustapha na biye masa a baya. Sai Alhaji Nuraddeen daga baya... Aayaan kuma ya tsaya yana duba wayar sa bakin gate kafin ya mayar da its aljihu ya bi bayan su..


Da sallama Alhaji jalaludden ya bude kofar dakin da mahaifin nasu yake ciki,


Gyaran murya yayi daga cikin dakin..


"Waye. Ko kawu ne?" Alhaji jalaludden ya lekar da kansa ciki azaton sa Kawu Adamu ne ya amsa da gyaran muryar...


Yana karasa shiga ya tarar da mahaifin su a tsaye yana linke rigar jikin sa daya cire,


"Babaaa???" Bakin sa a bude cike da mamaki.


Su Alhaji Nuraddeen suma suka shiga dakin.. dukkanin su suka tsaya chan suna mamaki marar misaltuwa


"Babaa.."


"Kakaaaa."


"Kakaaaa"


Suka shiga kiran sunan sa... Kowanne da mamaki dabaibaye a fuskar su..


Aayaan ya karasa da sauri ya rungume kakan nasa..


"Alhamdulillah! Alhamdulillah..."


"Babaaa" Alhaji Nuraddeen ya fada hade da kamo kafadar mahaifin na sa ya zaunar da shi akan kujera ya durkusa agaban sa yana kallon sa cike da kulawa yace,




"Babaaa.."


Alhaji Muhammd ya daga masa kai yana murmushin shima


Jalaludden ya karasa da sauri shima ya zauna a kusa da mahaifin na su,


"Baabaa... Ka gane mu?"


Alhaji Muhammd ya daga kansa kawai yana murmushi


"Kakaa baka iya magana?" Al-mustapha ya tanbaye shi. Ya yinda Aayan ya koma kusa da su shima yana bin kakan na su da kallo


"Ina ga fa kaman baya magana..." Aayaan ya fada cikin tabbatarwa,


"Ku kira bappanin ku... Jalaludden dan kira su Kawu Adamu kai ma . A kiraa kowa dai."


"Tohm"


"Tohm Bappah"


Shi dai Alhaji Muhammd sai bin su yake da kallo kawai...


Sukaa kikkira wayar cikin kankakin lokaci kuwa sashen ya cika taf. Kowa ya hallara. Amaal ma ta karasa tana kallon kakan na su. Itama ita yake kallo


"Ko da yake ke ai kin gan shi ko fave...." Aayaan ya jeho mata tanbayar yana nuna kakan na su.


"A...a" Ta amsa a ararrabe tana raba idanu.


Alhaji Muhammad ya girgiza kai alamun bata gan shi ba...


Haka dai yan uwan gaba daya akaita murna da farin ciki samuwar warakar jikin na Alhaji Muhammad.


Aka sake gyarr sashen Hajiya Maryam akai fleeting na maganin sauro ko'ina na cikin gidan. Bayan ya futa aka bulala turarukan wutan yerwa incense and more.


Sai bayan ishai tukun sannan aka rankaya sashen gaba daya. Nan ma wano sabon zaman akai. Shi dai Alhaji Muhammad ba bakin magana sai dai idan wani ya fadi wani abun ya juya ya kalle shi maana yana ji, Amma baya iya mayarwa...




_-_-_-_-_-_-




Amaal na zaune a parlorn hajiya jamila sai ga shigowar mahaifan nata. Hayateey ce agaba sai abbiey din nasu a baya.. yasha jallabiya da hula fara irin ta larabawa dinnan.


Amaal ta zube a kasa ta gayshe da su gaba daya cikin girmamawa sika amsa.


"Amaal...." Ta jiyo mahaifin nata ya kira sunan ta


"Na'am Abbiey"


"Dazu naji Aayan na cewa ke kika fara ganin fardowar baba... Ina son sanin gaskiyar lamarin duk kuwa da kince a'ah..."


Katiwar ajiyar zuciya ta sauke... Kafin tache,


"Abbiey kayi hakuri... Nayi maka babban lefi. "


"Na yafe miki... Da wanda na sani da wanda bansani bada Wanda zaki aikata Nan gaba.."


Murmushi tayi. Wanda kyakkywarn hakoranta a jajjere sika bayyana tache,


"Yau ma dai wajen Hajiya zani sai na fasa nayi bangaren kakaa saboda motar dana gani irin ta rannan da wadannan doctors din biyu... "


"Ina sauraron ki."


"Tohm... Danaga sun ja motar sun tafi sai naje ba kowa dai kaman ko da yaushe. Ina shiga sai na ganshi a kwance.m Amma idanun sa bude. Na kira sunan sa dai baya magana.Kawai sai na bude drawer dinnan na dakko allurai da sirinjin dana gani duka na zuba a wata bakar leda dana gani a gefen gadon... "


"Tohm... Ina jin ki uwata"


Shiru tayi kanta a kasa tace,


"Na dakko ledar?"


"Je ki dako"


Mikewa tayi ta hau sama.. sarki junaid da Hajiya jamila suka kalli juna. Fuskokin su na tu'ajjabin labarin da amaal ke gaya musu...


Can sai ga ta sakko da leda a hannun ta ta ajiye agaban mahaifin nata,


"Ga su"


"To cigaba Ina Jin ki"


"Tohm bayan na saka a ledar ne naje kusa da shi saboda yadda naga idanun sa na yi nake tanbayar sa da ko ciwo suke sai ya rufee idanun ya bude. Ni Bangane ba. Sai da ga baya naga ya zaro harshen sa dakyar yana mai mun nuni da Karin ruwan da ke shjga jikin sa... Dubawar da zanyi sai naga ruwan da yake shiga Kalar sa Baki da wasu abubuwa acikin harda karare. Nayi sauri na zare na cure gaba daya... Na saka ledar na fito bakin gate sai ga bappah jalaludden da ballah Nuraddeen da Yaya Aayaan da Yaya Al-mustapha.. sai kawai na durkusa akan ledar na gayshe su bayan sun shige ne sai na taho nan. Amma bappah jalaludden da Yaya Al-mustapha ma bssu amsa gaysuwata ba.."


"Amma meyasa baa ki gaya mun ba eh?"


"Hayateey da nazo bakya nan ki tanbayi iya."


Sarki Junaid ya sauke katuwar zuciya. Ya saka hannu yana daddaga allurorin....


"Toh Alhamdulillah....Allah yasa karshen wahalar kenan. Allah kuma ya kara masa lafiya mai dorewa ya Kuma bude masa bakin sa da baya magana.."


"Allahumma Aameen"


"Kinyi kokari... Kin Kuma kyauta da kika ceto rayuwar sa da ga fadawa kogin halaka. Sai dai ko nan gaba idan zaki abu ki dinga bi ta kan manya.. Yanzu da kin samu abun ki awajen da ya kenan? Irin wannan abun ba masu irin shekarun ki ne keyi ba amaal... Kinyi matukar kokari da hazaka.. Allah kuma ya Kare ki da kariyar Sa. Ko da wasa kada ki bari wannan zancen ya futa kina ji ko kin gayawa wasu bayan mu?"


"A'ah abbiey"


"Toh kada ki kuskura ki bari wannan zancen ya futa waje... Daga ni sai ke sai mahaifiyar ki sai mahaliccin mu gaba daya"


"In shaa Allah Abbiey"


"Allah ya miki albarka.. Allah ya miki albarka... Allah ya miki alnatka"


"Aameen Abbiey"


Wayar sa ya janyo a aljihun da ke gaban rjgar sa ya shiga wata number ya rubuta message can ya dauki hotan kayan cikin ledar ya cigaba da danna wayar tasa.


"Ki saka a akwatin nan ki nannade da sealtape ki bawa isa direba zan aika shi inda zai Kai .. zaayi bincike akannsu da duk ma abubuwan da suka dache"


"Inshaa Allah Abbieyn su.. Allah ya bada Iko"


"Allahumma Aameen."


HajiyaJamila ta mike ta dauki ledar da kayan ciki tayi karamin parlor ta hau sama ta dakko duk abjbuwan da zata bukata ta shiga shirya kayan tana nade su...


Sai wajen 12 saura kwata amaal tayi musu sallatama ta tafi sashen su. Zuciyar ta na mata dadi. Ranta fes tana jin ta cikin madaukakin farin cikin samuwar lafiyar kakan su Alhaji Muhammad....




/////////////////////////////////////////////




Tanata sauri ta shirya cikin wata riga kirar Caribbean kalar ja,. Saman rigar a dan tsuke kasan ta kuma ya bude..


Ta yane kanta da mayafin rigar ja shima. Batayi wata kwalliya ba ta dai shafa hoda ta goga kwalli.


Ta dan goga red lipstick kadan a bakin ta.. Ba kadan ba tayi kyau kamar wata balarabiya..


Ta janyo wayar ta.....Ta shiga daukan selfies tanata murmushi. Ta gama ta mayar da wayar ta cikin jaka,


"Jikin ki sai rawa yake kamar mazari zaaje gun maza ko?" Hindu ta ce da ita tana tabe naki..


Murmushi amaal tayi tana zura takalman ta tache,


"Wai su Yaya Aayan? Su ke bi na bani ke bin su ba.... Sai kun taho"


Ta fuce da sauri tana duba wayar ta dake ringing... Tabar Hindu da cizan yatsa


Wajen Hayateey taje suka gaysa...Daga nan ta wuce bangaren Hajiya . Ba kowa a parlorn sai kakan su Alhaji Muhammadu yana zaune da carbi a hannun sa tayi sallama ta shiga ta zauna,


"Kakaa Ina kwanaa? " Ta gayshe shi duk kuwa da tasan ba bakin magana


Dan juyawa yayi ya kakkali parlorn. Itada dai Amaal na bin sa da ido


"Kaka wani abun kake so ne?"


"A'ah..... Maryam! Nagode Allah yayi miki albarka."


Ta bude baki zatai magana ya saka yatsan sa akan nasa bakin yana mata alamar da tayi shiru...


Ta rufe bakinta da tafukan hannauen ta tana daga Kai... Mamaki ya cikata gefe daya kuma tausayin sa ya mamayeta.


"Salamu alaikum" aaayan da Al-mustapha suka shigo ciki..


Amaal ta amsa musu sallamar. Yayin da alhaji Muhamamd ya daga musu Kai. Labban sa suka motsa amsawar.


Gayshe da shi sukayi dik kuwa da da Kai yake daga musu yana murmushi...


Aayyan ya shiga cikin kananan kaya samfarin polo wear. Yayin da Al-mustapha ya ke shirue shirye cikin manyan kaya riga da wando na yadi me laushi ya saka hula data karbi aokin jikin kayan


"Kinga yadda kikai kyauu favorite. Wow wow wow...Dama ga ki me kyau.." Aaayan ya juya wajen Amaal yana yaba kyan da tayi.


"Thank you... Favorite Yayaa ayaan"


"Ina Hajiya?"


"Nima bangan taba inaga tana ciki.",


Cikin haka sai ga hajiyan ta futo daga daki tana dogara yar sandar ta ta karaso ta zauna suka shiga gayshe ta tana amsa musu daya bayan daya da faraa a fuskar ta


"To bari mu je"


"To Allah ya dawo ku lafiya. Allah yabar zumunci "


"Aamin Hajiya... Fave muje ko, Babaa Kai ma tashi muje" aayan yace da Al-mustapha.


Duk suka fita wajen harabar gidan bayan sun musu sallama.. Nukaa hills and garden zasu je gaba dayan su yaran zuriyar gidan.


Luxurious bus ce katuwa tazo daukar su wasunsu har sun fara shiga ciki. Al-mustapha na daga gefe yana jujjuya mukullin hannun sa.


Amaal na wajen wata bishiya tana amsa kiran Hisham daya kirata bayan yaga hotanta da ta saka a status na WhatsApp. Sai murmushi take tana amsa wayar. Hannunta daya na kan reshen bishiyar tana wasa da ganyen jiki...


Ya samu kansa da binta da kallo tun daga tafun kafarta zuwa fuskar ta. Ba karamin kyau tayi masa ba ..


"Fave muje ko?" Aayan. Ya fada yana nuna mata motar


"Ke ungo rike..." Al-mustapha ya kira ta yana mika mata mukulli


"Me zanyi da shi?"


"Ki share mun daki na kiyi mopping... Ki canza bedsheet din ma "yana magana yana takawa inda take a tsaye cikin isa da takun kasaita.....


_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/7, 5:10 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BM_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 26_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___




*Da* sauri ta fara ja baya, ganin yadda yake tunkarar ta. Hannuwan sa zube cikin aljihu. Ya narkar mata da manyan idanun sa yana mata wani irin kallo mai wuyar fassarawa... Amman fuskar nan tasa a hade take ba alamun wasa.


"Maza meye haka? Wacce irin shara bayan kasan fita za'ayi..? Beside ina masu taya aikin gidan nan fisabilillahi?" Cewar Aayaan


"Ita naga damar sawa to... Ina ruwan ka?"


Amaal idanun ta suka cika taf da hawaye. Su Hindu dake kallon su farin cikin hakan ya mamaye su baki daya.


"Ungo." Ya taka daf da ita har suna jiyo tururun numfashin juna. Ya yin da sanyin kamshin turarukan jikin su ya gauraye ya bada wani ni'imataccen kamshi mai kwantar da zuciya.


Ta daga manyan idanun ta da suka cika taf da hawaye ta dora akan sa.. Kallon sa take mai tattare da tsantsar tsana.


Ya samu kansa da kafa mata idanu yana nazartar ta... Zuciyar sa na zillo tamkar zata fadi kasa..


Ta karbi mukullin..Hannun ta daya kan idanun ta tana share hawayen da ke zurara daga idanun tah....


Aayaan ya bi bayan ta yana kiran ta...Yaja igiyar jakar ta yana kiran ta,


"Tsaya mana favorite..."


Tsayawa tayi saboda kukan daya ciyo ta ta saka hannun ta ta rufe fuskar ta tana shessheka.. Aayan ya juya ya gallawa Al-mustapha harara...


Cikin haka sai ga Fateemah-Yusra kanwar Al-mustapha... Daman su bjyu ne awajen iyayen su.


Ta girmi Amaal da shekaru ba masu yawa ba. Amma tana da manyance sosai. Don haka tana zuwa ta tsaya saitin su tana cewa,


"Kukan me take wannan?"


"Ita da mutumin ki ne mana..." Aaayan ya fada yana nuna mata Al-mustapha da yatsa..


"Hammaaa..." Ta karasa wajen sa


"Yusra.."


"Me ka.mata take kuka.... Kabar spare key din ka. Mami tasa an wanke maka toilet an gyara dakin anyi mopping. An ma canza bedsheet without your consent dai.."


Ta karasa fada tana mika masa mukullin... Sam bai ji dadin hakan ba. Ya juya ya hararo Amaal yana yamutsa fuska


"Karbo mun mukulli na awajen waccen yarinyar"


"Hamma me zata maka da ?"


"Jeki karbo dalla"


Yana karasa fada ya shige cikin motar. Ta tafi wajen Amaal tana yake.


"Amaal.." ta kira sunan ta tana daga ta


"Yaya yusra.."


"Na'am... Yaya Aayan wai me ya faru ne?"


"Gyaran dakin sa ya sata da sauran stuffs"


"Luckily enough kuma an gyara din.. Shima dai hamma. Kai Allah ya shrye shi. Ina key din kawo kinji?"


"Au an gyara? Dan wahala" Aayan ya fada yana hararo motar


"Muje dearest sis..." Ta riko hannunta suka shiga motar


Suna shiga cikin motar kamar fada Al-mustapha shi kuma ya futa daga ciki... Aaayan ya leka yana kiran sa


"Musty fresh meye haka? Zo mu tafu mana"


"Kuje ba zani ba sai dai idan yarinyar nan zaku fasa zuwa da ita... "


Aayaan yaja dogon tsaki yana girgiza kai,


"Wannan kuma baka isa ba kayi kadan... Katon banza katon wofi...."


Ya koma ya zauna yana cewa direban yaja motar su tafi. Su Hindu sai murmushi akeyi Al-mustapha yace yafasa zuwa saboda da amaal zaaje


"Kiyi hakuri kinji sis?"


"Da me fa yaya yusraa?"


" Da abubuwan da hamma Al-mustapha yake miki... "


"Oh.."


"Dan Allah kiyi hakuri kinji? "


"Bakomai..." Amaal ta amsa. Kasan zuciyar ta na mmamakin kiyayyar da yake nuna mata a fili.


Tayi hamdala hadi da sauke katuwar ajiyar zuciya. Don dama idan yaje ma she won't be comfortable...


Direba ya kai su har cikin Nukaa hills and garden.. Suka furfuto da kayayyakin kulolin abincin da suke j da shi da abun sha da sauran abubuwan bukata..


Grass carpet ne kawatacce da aka shimfidee shi awajen ya bada irin picnic site dinnan me maana.. amman duk da haka suka shimfida babbar tabarmar da sukaje da ita suka zazzauna..


Abun shaawa Aayan yasa sika fara addua... Daga bisani Kuma aka fara hira ana zuzzuba abinci da abin Sha.


Bayan sun gama, Yaran ciki sukai swimming wasu sika hau lilo wasu dokuna wasu suka hau pirate ships da motoci da sauran su.


Sai da sukayi sallar laasar suka wuni cur anan sannan sika dauki hanyar gidah nanma Aayan yasa suka tsaya wani joint na ice cream ya sissiyawaa kowa scoop uku da donut daya da shawarma. Sannan suka tafi gidah.



+++++




Har sai da motar su taja sannan ya samu kansa da dai na waiwayan motar ya nufi sashen Hajiya...


Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Hajiyan ce kawai a zaune tana jab carbi ta amsa sallamar da yayi. Ya nemi waje ya zauna,


"Ina kakaa?"


"Ya kwanta kansa ke cuwo"


"Allah sarki.... Allah ya bashi lafiya Amin"


"Amin Aameen..."


Hajjya nata jab carbi ta. Ya janyo wayar sa ya shiga WhatsApp. Yana cikin duba statuses. Ya gano na Aayan kaman ba zai dai duba ba sai kuma yayi viewing..


Hotunan su ne kala kala acan wajen. Harda videos.... Gefe daya Kuma hotunan amaal ne ya sassaka su tayi kyau tayi mirror selfie da Wanda tayi video din kanta tana murmushi..


Ya samu kansa da zooming hotunan yana kalla daya bayan daya ..


"Kun fasa zuwanne?" Muryar Hajiya ta doko dodon kunnen sa


"A'ah .... Su sun tafi"


"Kai meyasa bakaje ba?"


Jan kan leben sa yayi yayi yace,


"Banason rashin kunyar yarinyar nan amaal. Jini na be hadu da ita ba shiyasa"


Hajiya Maryam ta kalle shi tana girgiza kai,


"Meyasa kake haka ne Dan yaye? Saboda Allah me yarinyar nan ta maka? Yarinyar da batada kwaramniya ma? Bantaba Jin ko ganin Wanda ke ganin lefinta ba wallahi sai akan ka"


Ya smau kansa da yamutsa fuska... Dai dai lokacin da hannun sa ya danno kan selfie din aaayan da amaal din awajen Wani lilo sin tsattsaya,


Mtscew... Yajaa tsaki da baisan ma ya fito ba


"Tsakin me kake?"


"Bakomai hajiya... Kai na ne ke dam saramun"


"Bari a dakko maka Panadol to."


"A'a zai lafa Hajiya...nagode "


"A zubo abinci ko?"


"A'a Hajiya..


"Ba abunda kake bukata?"


"Babu Hajiya"


"Shikenan..."


Tashi tayi ta shiga daki. Can an dan jima Kuma ta dawo. Gogan naku na zaune akan kujerar lokacin zuwa lokaci kuma ya kan duba agogon dake wutsiyar hannun sa


"Wai tsakin me kake ta faman yi ne?" Hajiya ta tanbaye shi.


Da alama bai masan yanayin tsaki ba. Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana kakaro murmushi,


"Bakomai... Network wayata nake son ya dawo"


"Okay tohm"


Can sai suka fara kallo wani tsohon film din hausa da ake a Africa magic hausa. Hajiya ta bada hankalin ta sosai tana kallon. Yayinda Al-mustapha ke Jan kasan leben sa yana taunewa kamar wata alawa..


Ya mike ya daga labule ya koma ya zauna,


"Hajiya"


"Na'am danyaye"


"Ki kira aaayan ki ce su dawo haka?"


"Ah akan me zan kira su su dawo suna can suna kulla zumunci? "


"Hadari ne ke ta haduwa fa.."


"Yo ai ba yara bane dazasu bari ruwa ya dake su dan yaye... zasu samu mafika."


"Akwai....akwai tsare tsaren da muke da Aayan ne akan office dina... Shiysa nake son su dawo da wuri saboda mu samu mu karasa"


"To ka kirawo shi mana..."


"Ba..ban..Banda network a wayar"


"Zasu dawo ai komai dare inshaa Allah.. idan Kuma ka matsu yanzu kakeson kuyi abin to ga waya ta nan ka kira shi.," Ta karasa fada tana mai tura masa wayar gsban sa


Yayi haka zai dauka kenan yajiyo karar budewar gate din sashen... An shigo da zungureriyar motar da sika tafi da ita.


Ya samu kansa da sauke zuciya mai dauke da maduakakiyar farin ciki marar fisaltuwa.


Duk kowanne ya tafi hanyar sa. Aayaan, amaal da yusra Kuma sika tunkari sashen Hajiya


Al-mustapha ya nemi waje ya zauna yana mai sake hade fuskar sa tamau.


Suka shigs parlorn sunata sallama. Hajiys ta amsa musu. Al-mustapha ma ya amsa yana Wani danna wayar sa ya dora kafa daya kan daya


"To ga Aayanun nan ya dawo ai danyaye. Gwara ku karasa aikin da kuke ko?"


Aayaan ya kalli Al-mustapha kallon karin bayani,


"Wane aiki?"


"Babu..."


"Aikin me dalla..?"


Al-mustapha ya mike ya fuce da ga sashen yana eani kobarewa... Yana fita amaal ta sauke numfashi


Da tasan yana sashen Hajiyan kuwa da ba zata ma shigo ba....


Ta rasa wacce iriyar tsana yake mata.. Ta jujjuya kai kawai kasan makoshi ta furta


"Allah ya kyauta..."


A bangaren hajjya sukai magribaa har bayan ishai tukun sannan itaa da yusraa sukayiwa hajiyan sai da safe. Yusra ta nufi bangaren su. Ita Kuma amaal ta nufi sashen Hayateey tanata sake sake a zuciyar ta.....






_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA

Please Login or Register in order to submit comment