Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana tsokanar sa ya sake cewa


"Ka zauna mu cigaba ma na."


Wata harara Al-mustapha ya dankara masa ya fuce dai yabar parlorn. Yana fita amaal ta sauke zuciya... Don babu wata alaka ta yan uwantaka da ke shiga tsakanin su


"Danyaye an koma daki"


Yusra tayi murmushi tache,


"Hajiya ke kika sangarta shi ai...abu kadan zai ce shi waye waye"


Aayan charaf yace


"Ai musty fresh arrogant ne na karshe... Ku kalla fa kawai ya tashi yabarni da cards din whot a hannu..


Ita dai Amaal kawai jinsu take .. ta tabbatar Al-mustapha tsananin kiyayyar ta da yake mata ne ne yasa dazun tana shigowa ya fita...


Yana shiga cikin dakin nasa ya wuce gaban wata drawer ya janyo wasi takardu da hotuna aciki ya koma kan gado da su ya zazzage...


Hotunan ta ne tun tana jaririya da wanda tafara girma har ya zuwa lokacin da suka koma kasar waje da zama da wanda yayi saving idan an sassaka a kafafen sadarwa ya wanko su..


Ya kwantar da kansa akan pillow ya dauki hotunan yana duban su tamkar zai shiga ciki... Ya yinda hannun sa ke zagaye katin hotunan hannun nasa...


Ya kwantar da hotan akan kirjin sa yana lumshe idanun... Ya sake bude wayar sa ya shiga wata folder da yake saving duk wasu hotunan nata yana kala daya bayan daya.. irin kallon nan da matsananciyar kaunar da ake yiwa abunda ake wa kallon..


Cikin yanayin da yake ciki kanwar sa yusra ta tura kofar dakin ta same shi bakinta dauke da sallama...


Har ta shiga bai san an shigo ba. Yayi nisa ainun.... Ta lekar da kanta tana kallon hotunan Amaal da ke zube akan gadon. Ga kuma na cikin wayar sa daya tsurawa idanu yana kallo.


"hamma....." Ta kira shi tana girgiza kanta.


Sai asannan ya farga... Da sauri ya yi zunbur ya mike ya tattara hotunan ya mayar cikin drawer ya zura wayar a a aljihu ya dubeta yana yamutsa fuska,


"Meyasa zaki shigo mun daki ba tare da nabaki izini ba? Wato saboda kin renani ko?" Ya shiga fada yana mai nuna ta da yatsa...


"Hamma Al-mustapha kayi hakuri... Amma nayi sallama sau uku. Na kuma kwankwasa ma shiru. Na bude na shigo na ganka. Amma ba haka kawai na shigo maka daki ba... Mami ce ma tace na kira ka..."


Ya saka hannu a kasan keyar sa ya sosa yana furzar da iskar bakin sa.. ta dube shi kanta a kasa tace


"Meyasa ba zaka gaya mata ba?"


Wani kallo ya watsa mata yace


"Meyasa ba zan gaya wa wa ba? Me zan fada?"


"Hamaa.... Kana kaunar Amaal tun taleetale amman ka kasa fada. Tun tana zabin goyo kake kaunar ta hamma. Amma kana nunawa ko a gabanta ka tsaneta baka kaunar ta baka ma san ta ba. Meyasa kake illatar da kan ka? Meyasa ba zaka sanar mata abunda kake ji game da ita ba a zuciyar ka ba? Hammaa meyasa kake azabtar da kan ka?.."


Ya bude baki zai daka mata tsawa sai kuma ya fasa. Ya saka tafukan hannuwan sa duka biyu ya rufe fuskar sa,


"Hammaa.... " Ta kira shi muryar ta na rawa...


Hawayen da yake ta kokarin kar su zubo ne suka yaudare shi suka zuba a fuskar sa,


"Hamma kuka? No please.... Bari naje na gaya mata ni"


"Ki gaya mata me Yusra? Kyale ta.. Aure fa zatayi ma an kusa. Ita da shi suna kaunar juna tuntuni bazan yi silar batawar bappah Junaid da aminin sa ba. Ba kuma zan sa a daura mata sure dani ba na dole"


"Lalle Hamma ba sonta kake sosai ba."


Kallon ta yayi yana girgiza kai yache,


"Fita mun a daki... Kuma kar ki kuskure naji maganar nan awani waje wallahi sai ranki ya baci ko da wajen su Bappah ne da Mami...."


"Shikenan... Sai da safe" ta fada a sanyaye ta fita daga dakin


Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi ya ko koma kan gado ya zauna ya ciro wayar sa .. Yana shiga chat message dinta ya shigo...


"Hey... Na dawo"




"Barka da dawowa... Habibty! I think of you a thousand times a day. Believe me when I say your love is more than a world to me. .....Maryam! My heart recognized you as my wife the moment it heard you speak. Please tell me it was right and say yes...."


Amaal a nata bangaren tana zaune reply din Arc. N ya shigo wayar ta. Tayi murmushi ma kafin ya bude.. Tana karantawa tana murmushi tache da shi,


"I'm out of words.... I just wish I met you earlier.... Bazan iya cewa agidah ba zan aura Yaya Hisham ba... Nurayn"


"Maryaam! I know what I want out of life and it’s you. Nothing but you. please say you’ll marry me, beautiful girl. My heart can only love you, and my soul only recognizes your voice. Let me hold you close forever as my beautiful wife..."


Amaal da ke kwance ta saka hannu ta runtse idanun ta. Kalaman sa na mata yawo a magudanar jiki gashi bayason shirin sa yayi nasara akanta ta bijere alkawarin da tayi tache dashi,


"Mu dena maganar ma please .. Allah anbadani an kusa aure na. Thanks .. night night"


Yanada kwance akan gado sai birgina yake ya koma can ya juya can ya lula duniyar kauna... Ya samu kansa da kasa kyaleta duk da shi kansa yasan auren zatayi amman nutsuwar hakan taki samuwa agare shi.. Ya sake rubuta mata,


"Maryam soyayyar ki tazamo abu mai matukar muhimmanci a rayuwa ta kin zamanto wani bangare na jikina da idan bake rayuwata zata shiga mawuyacin hali, shigowarki a a rayuwata sun zamanta sanadiyar dawwamar murmushi a fuskata, Maryam so shine abu mafi tasirin warkar da kowane irin ciwo.ma kullum zuciyata kan samu nutsuwa idan ta tuna dake.. ina miki fatan alkhairi Ina kuma tabbatar miki da cewa kaunar ki daga Allah take a zuciya ta, rai na da kuma gangar jiki na baki daya... Ki huta lafiya♥️"


Yana karasa rubuta mata ya ajiye wayar ya mike kenan zai shiga bandaki wayar tasa ta fara kara ya dauka mahaifiyar sa ce,


"Al-mustapha tun dazu nasa yusra ta kirawo mun kai shiru ba kazo ba. Dan Allah zo sako zaka karbo mun agidan antyn ku. Ba direba a kusa. Yusra Kuma saboda idonta ba zaata iya driving ba"


"Okay Mami gani nan bari na dan watsa ruwa."


"Kai sauri to"


"Inshaa Allah."


Bandaki ya shiga bakinsa dauke da addua yayi wanka hadi da dauro alwala ya sauya kayan sa zuwa jallabiya ya faffesa turarukan ya zura wayar sa a aljihu ya fita....




Ko bayan data ajiye wayar bayan ta karanta sakon daya turo samun kanta tayi da juyar da kanta gefe..Hawaye suka shiga diga idanun ta. Tabbas itama tana kaunar Arc. N da suka hadu a manhajar Instagram..


Tun bata san neye so ba shi ne ya koya mata ya Kuma chusa mata kaunar sa a ranta. Duk kuwa da bata taba ganin sa ba.. Amman suna matukar son junan su. Gashi da maganar auren wani akanta.


Ta ja kasan leben ta tana taunawa... Ta daga Kai ta dubi gefe su Hindu kowacce tana harkar gabanta ba abunda ya dame su.Wani lottafi ta janyo ta shiga karantawa..


..
_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/20, 5:54 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 38_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___





Haka dai rayuwar ta cigaba da garawa. Kamar yadda Alhaji Abubakhar yayi allawari kuma ya cika donma ya daga a alokacin da aka sache Amaal sai data wartsake gaba daya tukun sannan aka gama musu komai na tafiyar. Suka tafi makka


Amaal, Hajia maryam, Alhaji Muhamamd sai bappah Nuraddeen dayaje amadadin kujerar Kawu Adamu da a baya Alhaji abubakhar ya aminta.


Satin su biyu a saudiya, daya a Dubai suka waiwayo gidah bayan an dudduba jikin Alhaji Muhammad komai lafiya kalau...


Bayan sati biyu da dawowar su ne kuma sarki Junaid ya dawo da Hajiya hadiza da Hajiya Ruwaida dakunan su tare da jan kunnuwan su sosai. Shima sai da Hajiya maryam ta masa Jan ido tukun sanan ya ce su dawo dakunan su..


An kawo kudi da kayan lefen Amaal. Tsayawa bayyana adadin yawa da tsaruwar kayan ma bata lokaci ne. Domun kunsan wanene mahaifin Hisham da irin tarun dukiyar sa. Kuma dan sa ne daya jal a duniya basu da wasu yaran bayan shi. Don haka kayan da akayi masa ko karamar kasuwa aka bude sai haka..


Dangi sun taru sunata kallon kayan anata Allah ya sanya alkhairi. Don tuni har an fidda anko ma na wani royal blue lace... Aka sanya biki nan da sati bjyu masu zuwa.... Tuni aka kirawo madame yerwa me kamfanin turaren wutar yerwa incense and more ta fara gyaran ciki da wajen amarya.. da hada mata turaruwa masu matukar kyaawun gaske .


Anyi furnishing gidan amarya ciki da wajen sa. Dangi sunyi zumunci kwarai matuka wajen bada gudunmuwar su... Shagalin hidimar biki ce kawai tayi ragowa..



:;::::::


Da saafe ya shirya ya tafi office .. Anan aminin sa yazo ya same shi suna hira.


"Dan Allah wai bikin amaal saura yan kwanaki ko?"


"Uhm...aina kaji?"


'ka manta student dina ce? Naga bata zuwa ne na tanbayi kawayenta da suke tare sukace an kusa bikinta ne. Lalle an kasa mu"


Al-mustapha ya tabe baki ... Paper ce agaban sa ya rike biro yanata zana shirme..


"An kasa ka kam tabbas"


"Ni da kai dai... Garanbawul..!!!"


Al-mustapha ya daga kai da sauri ya dube shi,


Habibi Talba yayi murmushi yana jan kasan leben sa yace


"A jerin matan da nake so bata ciki...Ai idan nace maka Ina son waccen yarinyar to ka kirani da garanbawul....
Wanda zai yi reno don kwa reno zaka yi... Yarinya ce fa danya sharaf. Yo waccen idan nace ina sonta ma ai sai reni ya shiga tsakanin mu .. batada qualities din da nake so ajikin mace gaba daya.... Ko abu daya bata dakko
na."


"Meya haka? Wa kake magana akai ne... Ni kanwata ce kawai nothing more" Al-mustapha ya fada ganin habibi Talba na neman kure shi..


Habibi ya sake duban Al-mustapha yace,


"Yarinyar da tun muna high school kake yawo da hotunan ta kala kala kana cemun kanwar ka ce.... Kai long story short.. Maza meyasa kayiwa kanka babbar illa haka? Kana kaunar ta amman ka bari wani yayi maka shigar sauri kana forming hard guy. Banza garanbawul.."


"Tashi ka futa mun a office"


"Naqi na fita"


Mikewa yayi shi ya harhada abubuwan sa ya mike zai bar masa office din habibi dake zaune har Al-mustapha ya kai bakin kofa yace,


"Matsoraci wanda ba zai iya fuskantar macen da yake kauna ba tun tana zanin gayo..Yace yana son ta.. Allah wadaran naka ya kasance sullutu..To Allah ya baka wata tagari,, Me sadaukar wa wani soyayyar da yake wa wacce yake kulafucin so"


Yana gama fada ya mike ya dafa kafadar Al-mustapha ya fuce daga ofishin......




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/21, 7:19 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 39_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


Al-mustapha ya jima a tsaye bayan da Habibi Talba ya fice ya barshi a tsaye... Mamaki yake Ashe habibin bai manta kalaman da yayi katobara ya faada ba akan inde yace yana son amaal to a kira shi da garanbawul wanda zaiyi reno tunda yarinya ce danya sharaf...


Ashe kuma kallon sullutu yake masa ya gano Amaal itace yarinyar da yake musu maganar ta tun suna high school..
Hannun sa ya sa ya dafe goshin sa yana dana sanin katobarar zancen da yayi musu a baya... Duk kuwa da cewa yake kanwar sa ce. Ko aina Habibi Talba ya gano da shegen binciken sa..?


Komawa yayi ya zauna akan kujerar sa ya bude wayar sa ya shiga WhatsApp yana kallon statuses... Saboda bayasan komawa gidah ma don ya tabbatar yan uwan sun sake cike gidan. Don tuni wasu daga garurwa har sun fara zuwa. Wanda ke awaje ma sunata tahowa..


Kasancewar wannan ne biki na farko da sarki Junaid zaiyi zai aurar da 'yar sa. Yar autar sa kuma autar gidan wadda Allah ya amince zata kere yayyunta ta fara yi.


Wani short clip ne ya shigo ta family group dinsu dake WhatsApp din. Tamkar bazai shiga ba saboda ta saman notification ya hango. Sai Kuma ya bude ya shiga group din yayi downloading bidiyon. Ashe katin daurin auren bikin amaal ne da Hisham..


Ya samu kansa ta tallabe haba da hannun sa daya.. dayan kuma ya dan rage sautin bidiyon da ke tashin wakar maheer zain ta aure. 'BarakAllah..."


"A madadin zuriyar Ardo kandemi... Mai martaba sarkin Nukaa, Amb. Junaidu Muhammad Mahmud Kandemi da na Dr. Abubakhar Mai dingishin kudi..Suna farin cikin gayyatar ku zuwa daurin auren 'ya'yan su...Maryam (Amaal)Junaid Muhamamd da angon ta Captain Hisham Abubakhar... Wanda zaa daura inshaa Allahu bayan sallar jumuah a masallacin masarautar kandemi.. Akwai shiryayyiyar walima bayan daurin aure. Wanda ba zai samu halarta ba dan Allah yayi addua.."


Bayan ya gama kalla.. daga kasa kuma an sake turo wasu bidiyoyin ya bude na biyu yana karantawa da ke rubuce da,


Together with their families[Maryaam-Amaaal] and [Captain. Hishaam] invite you to share in the joy and celebration of their wedding day. On Friday after jumu’ah prayer.. Venue: Kandemi central mosque.. grand reception follows immediately ....


Siririn tsaki ya sauke...Ya zura wayar a aljihun sa mikewa yayi ya fuce daga office kan sa na ta masa zugi da radadi


"Sir ka tafi kenan?" Sadya sectary dinsa ta tanbaye shi


"Na tafi... Sai da safe"
Kai ya saka ya fuce ya shige mota. Ko da ya shiga ya zauna kasa tashin motar yayi ya tafi


Ya kifa kansa akan sitiyari hannunsa dika akan satiyarin fuskar sa a kasa. Ji yake tamkar kirjin sa zai ballo kasa.


Ya zaro wayar sa ya shiga nan da nan ya cike e-ticket... Ya gama yanke hukunci a zuciyarsa tafiyar sa itace zata saka shi nutsuwa.


Ya murza key zai bar harabar ofishin nasa Habibi Talba ya bude gaban motar ya shiga. Abun ma ya bashi mamaki ya dube shi yace,


"Meye haka?"


"Lefi ne dan na shigo motar ka garanbawul?"


Al-mustapha yaja siririn tsaki yace da shi,


"Dan Allah karka karamun bacin rai akan wanda nake cikin sa.."


Habibi Talba ya kalle shi yace


"Musty fresh kenan.... Wannan abubuwan da kake idan baka sani ba sake illata kanka kake... Wallahi da ache na tabbatar Amaal itace yarinyar nan da kake dawainiya da kaunar ta a school kana gaya mana yadda kake sonta . Allah da tuni na samu manya na sanar musu dawowata da nayi. To Amma baka taba ce mana ai da aure a tsakanin ku ba nunawa kake kanwar kace ta jini"


"To ba kanwar ta bace ta jini?"


"Amma ai akwai aure a tsakanin ku... Saboda ita fa ka waiwayo Nigeria gaba daya... "


"Wai waye ya gaya maka?"


"Ya gaya mun kana son amaal? Ni makaho ne an gaya maka? Duk magangunan da kake ta fada kana baka son ta inata nazartar ka na gani kaunar ta kake fiye da kalamai. And again hotunan ta na wajen ka tun muna school plus sunan yazo mun na sake duba kamannin ma na tabbatar itace..."


Al-mustapha ya tabe baki...


"Sauka ni tafiya zanyi"


"Sai kayiwa wanda bashida mota gori. Sannan kuma ba inda zani muje gidan ku"


Al-mustapha ya dube shi ya zabga masa harara. Ya tashi motar suka bar ofishin sika dauki hanyar kandemi.


Habibi Talba sai zuba magana yake. Shi de Al-mustapha na kada kai kawai ko ya amsa masa da uhm ko uhm uhm..


Notification ne ya shigo ta wayar Al-mustapha da ke kusa da giyar motar a ajiye. Habibi Talba ya dan daga wayar ya dubu screen din.


'E-Visa notification ne' Har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalli Al-mustapha,


"E visa kuma? Wa zeyi tafiya?"


"Ni ne..."


"Kai Kuma? Ina zaka?"


"Ina ruwan ka?"


"Dan wahala kawai."


Al-mustapha ya tabe baki ya cigaba da tuki har suka karasa... Sun furfuto daga cikin motar sai ga yusra kanwar Al-mustapha da Amaal..


Tun daga nesa kake jiyo kamshin turaren gyaran jikin da akeyi mata.. Suna doso su kamshin ke dada mamaye ko'ina..wani irin sanyayyen musulmin kamshi mai dadi.


Gyaran jikin da ake mata ya karbe ta. Domin fatar nan tata ta sake haske tayi santsi da laushi.. Tamkar an sake kara mata kyau. Harta gashin girar ta sun sake cika da baki. Leben nan nata ta shafa man baki sai kyalli yake da laushi..


Sanye take cikin doguwar rigar hijab bubu..Ta yane kanta da mayafin daya shiiga da kalar sa ja da ratsin baki..


"Ina wunin ku?" Yusra ta gayshe su. Suka amsa...


Amaal ma ta dan sunkuya cike da ladabi tace,


"Barkan ku da yammaci..."


"Amaal... Amarya" Habibi Talba ya fada yana murmushi


"Malam" ta fada cike da kunya


"Allah ya sanya alkhairi. Yasa gidan zamanki ne"


"Aameen" Yusra ta amsa shi. Saboda amaal din jtada dai kanta a kasa tana lankwasa hannuwan ta cike da kunya...


Tunda suka zo wajen Al-mustapha ya kasa dauke kansa daga kallon amaal da yaketa yi tamkar zai mayar da ita cikin sa..


Tana dago Kai suka hada idanu ya bata rai ya bar wajen da sauri. Habibi Talba yabu bayan sa yana cewa da shi,


"Jirani mana garanbawul.. Kai fa dan wahala ne."


Sashen Hajiya Maryam ya nufa Habibi Talba na biye da shi a baya.. suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama.. sika gaysa da hajiyan.


"Wannan aboki ka ne?"


"Eh hajia kin manta shi ko?"


"Kaman dai nasan fuskar nan tabbas"


"Habibi Talba ne.. Tun Muna kanana muke tare. Mahaifin shi abokin su Bappah ne.. yanada sarautar Talban gabas na garin Yalwanje... "


"Haka .... Ma shaa Allahu. Ya mahaifan na ka kalau?"


"Alhamdulillah Hajiya".


"Safiya kawo musu abinci" Hajiya ta dan daga murya tana kiran me aikin ta


Nan da nan me aikin ta shiga kawo musu abincin da trays tana ajiyewa da ruwa da lemuka.


"Ku zuba kuci dan Allah"


"Tohm Hajiya. Allah ya saka da alkhairi "


"Aameen Aameen Habibi"


Cikin haka Aayaan ya shiga ya same su .. suka gaysa ya zauna ya debi abincin ya fara ci,


"Hajia wannan shine malamin su Amaal fa da hindu ke magana" aaayan ya fada yana sake zura lomar abinci a bakin sa..


"Au shine.... Allah sarki"


Habibi Talba yayi murmushi yace,


"Ni ne hajiya"


"An ka samu ni da kai" Aayaan ya fada yana dariya.


Shi dai Habibi Talba murmushi kawai yayi masa. Al-mustapha kuwa kanzil bai ce ba ya cigaba da cin abinci yana korawa da ruwa.


Sun dan jima bayan sun kammala cin abincin suna ta hira daga bisani Al-mustapha da Habibi Talba suka yiwa Hajiya sallama suka fita...


"Muje ka ajiye ni a site can nabar motar"


"Nagaji maza.."


"Haba mana"


"Muje"


Motar sika koma suka shiga.. Al-mustapha ya kai Habibi Talba har site..


"Dan Allah Ina zakaje? Yaushe zaka tafi? Kuma yaushe zaka dawo"


"Meye haka? Kaman wani wanda yaci bashin gidan rediyo?"


"Dagaske nake please"


"Manchester..... "


"England dai?"


"Yes..."


"Yaushe zaka tafi? "


"Soon inshaa Allah"


"Exact date nake son sani"


"Will let you know .."


"To yaushe zaka dawo?"


"Sai na huta"


"Sai kayi healing dai... "


"Whatever... "


"Later.. will holla you"


"Alright. ka gayda su mummy"


"In shaa Allah.",


Yaja motar sa ya koma gidah ransa duk babu dadi kwata kwata.. Kai tsaye ya shige daki bayan ya shiga bangaren su.


Ko da aka tambaye shi akace akawo masa abinci ma yace a'a yaci awajen hajia. Kwana yayi bayyi bacci ba yanata sake sake sai salllar nafila da yayi ya roki Allah yasanya hakan ya zamo shine alkhairi agare shi.


A daren ya hada kayan sa a akwati da hotunan Amaal gaba daya da niyyaar idan yabar kandemi sai ya samu waje ya kona su duka..


:::::::




Shirye shiryen biki aka fara yi. Kwanakin bikin suka karaso.. Da ke Amaal din batason taro hakan yasa ba wani events za'ai ba. Akwai gagarumun Grand kamu/ royal mother's eve dai daza ayi. Sai daurin aure da walima shikenan..


Ranar Thursday yammatan gidan cousins suka hada bridal tea party. Iya su kadai ne kawai da amarya Amaal da kawayen ta. ...


Tayi shiga cikin barbie gown pink color kaman wata princess. Ta nade kanta da mayafi shima pink. Sai takalman ta silver color. Ba kadan ba tayi kyau.


Sun ci sun sha sun gyagije. Sunata games, Ita dai tana zaune a kujera tana kallon su. Wayar ta a hannun ta notification ya shjgar mata ta Instagram, ta bude. Arc. Nurayn ne ya turo mata message da,


"Assalamu alaikum wa rahamatu Allah wa barakatuh! Hey! Maryaam, I know you are seeing this… I want to thank you for being in my life. Also, I want to wish you the best! You deserve the whole world! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nake bazan taba mantawa dake ba, Na kan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata... Daga karshe kuma Allah yayi ni da ke ba masu zama a karkashin inuwa daya ta maaurata bane. Na shigo rayuwar ki a BAKON masoyi wanda yazo a qure. Ban bayyana miki kaunar da nake miki ba har Allah ya yi hukuncin sa dai ke din ba tawa bace. Ki sani kaunar ki ta dade acikin rai na, Ina miki fatan alkhairi a sabuwar rayuwar da zaki shiga. Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa Amin... Na bar ki lafiya..
Arc... Nurayn!! Thou dai ki gafarce ni nurayn suna ne kawai na saka a social media. Amma usulin sunana na yanka ba haka bane.. Na bar ki lafiya. Allah ya yafe mana kurakuren mu Amin.."


Ta karasa karantawa hawaye 'daya ya zurara daga idanunta tayi sauri ta goge hawayen.. ta rubuta masa,


"Wa'alykm Salam... Nagode kwarai. Allah ya saka da alkhairi. Goodbye" Tana karasa tura masa tayi sauri ta shiga tayi blocking dinsa already shima har yayi unfollowing dinta.


Haka dai suka karasa event din ranar dakyar ta samu ta daidai ta kanta... Akayi hotuna sosai... Bridal tea party

Please Login or Register in order to submit comment