Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakawa Kawu Adamu tsawa


"Tana tsaunin zagayen makarantar mata dake karshen lungun wadawa na unguwar balbelu...."😭


"Kaji bakin mugun ko? Kunji unguwar da take ma? Kai Adamu bakada Imani. Wallahi wallahi baka da Imani. Makarangar matan da ke unguwar balbelu din tun yaushe gwamnati ma tache a dena amfani da makarantar saboda miyagun da ake tunanin suna bibiyar ta da yn shaye-shaye.... " Bappah maheer ya fada yana girgiza kai cike da takaicin Adamun


"Gaskia na kara tabbatarwa ba Allah a ranka... Allah ubangiji ya kyauta.. ka guji bakin duniya. Adduar Wanda aka zalunta wallahi batada hijabi da Allah . Yarinyar nan hakin ta na cutar da ita da kayi wallahi Allah ba zai taba barin kaba.." bappah usayni ya fada yana girgiza kai.


"Nima Kuna nuna mun kiyayya ai... Daman tinda nazo doron duniya nasan bakwa kaunata.. Don haka maganganun ku basa damuna... " Ya kasa kai zai fuce. Dss din sake tsaron kofar sika sake bude kafafun su.


Bappah maheer ya kira sunan sa da karfi,


"Ba magana ake maka ba ne... Wallahi Ina mai tabbatar maka idan aka dakko yarinyar nan akaga an mata wani abun na illa na rantse da kadaitar ubangiji Adamu sai kayi dana sanin samuwar kanka a zuriyar kandemi .."


Kawu Adamu yayi murmushi... Ya nemi gefen stand na tv ya zauna, Cikin muryar ko ajikina dinnan yache,


"Ko kanada masaniyar tsananin kiyayyar da kuke nuna mun che yasa dukkanin ku kuma nabi na toshe wasu ababen farin cikin ... ku kuka fara kamar yadda kuke da hannu a hanewar sarautar da nake da gadon ta .. Bappah maheer ko ka tuno wata kwangila ta mambila da zaka samu miliyoyi kanata murna daga baya aka hanaka aka bawa aminin ka? Ni ne silar hanaka.. Bappah usayni Ina gidajen da akace gwanmati ta bawa ku tsofaffin maaikata Kai da abokan aikin ka gidajen Ikeja da ke Lagos? Ai kaga daga baya aka cure sunan ka aka kore kama ma daga masu karban pension... Bakowa bane sila ni ne nan.. Bappah Hassan aikin da zakaje embassy na Ecuador bakowa bane ya hana asa maka hannu a takardar tafiyar fache ni... Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan danayi na ramako akan muguntar da kuma kuka mun kuke kan yi mun..."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Adamu! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Daman ance makashin ka na g* ka . Allah ubangiji ya kyauta.. "


"Kwarai kuwa... Rama cuta ce ga macuci... Kunmin na muku... Da da ran iyayen mu duk haka ba zata faru ba... ai kamar jalaludden ne... Dana dinga amfani da na'ura mai kimiyya Ina sanya nasa kiyayyar dan uwan sa a ransa.. Baya kaunar sarauta amman na dage na dinga tura masa sakonni masu jan raayi har ya amince.. da niyyar sanya zazzafar kiyayyar idan tayi tasiri ku kwamktin saka sarki zakuu tsaidani a sarautar kujerar Nukaa amman kuka ki.. Da hanyoyi na bi na saka aka saka hannu akayi stamp amatsayin junaidu ne yasa aka zartar aka hana jalaludden babban mukamin da yakeso na matemakin shugaban kasa... Tun daga nan na fara saka kiyayya a tsakanin su.. Na kuma koma kan junaidu shima, Na sanya aka kara masa wa'adi aka ki dawo da shi Nigeria, Ina kuma tura masa sakonni masu tsoratarwar amman shi ban gama nuna masa jalaludden bane sai dana bari ya dawo Nukaa gaba daya. alokacin dana saka aka dauke yaran sa acan kasar na awanni nayi hakane da...


"Dakata hakanan Adamu na tabbatar kai din BAKON MUNAFIKI ne Kai din Kuma BANA MUTUM DAYA BANE... Kana bin kowa na cikin mu kana cin dudduniyar sa kana kuma saka kiyayyar juna a tsakanin yan uwa.. Dan uwan ka ma baka barshi ba da kuka fito ciki daya ballantana mu da kuma yayan yan uwan ka.. "


"Kwarai.. ko matan gasunan ni ke raba kansu dik dan su bujire junaidu kar ya waiwayo kasar ma amman ya dawo. Ban kuma dena dinba na cigaba fiye da abaya ma.. " yakara sa fada yana nuni da su Hajiya Hadiza


"Musanman ke da ke bada gundunmuwa sosai... Duk da dai tun kafin na fara turo sakonni dama can bakya kaunar jamila..kuma kin amince a salwantar da rayuwar Amaal din.. junaidu ko ka tuno sanda kake gaya mana ka bawa Hamid gashinan ragamar asusun bankin kandemi? ... A ranar na kara tabbatarwa da sai na illata zuriyar ka da mafi soyuwar abunda ke ranka tunda naga alama ka bada himma sosai kana kuma kaunar abunda nake muradin son samu.."


"Ya isa dakata.... Illa ce kayiwa kowannen mu kai da Allah mahallicin ka. Yanzu dai muje a dakko yarinyar nan daga nan Kuma sai a yanke maka hukunci dai dai da Kai" bappah maheer ya fada hadi da saka hannu ya janyo Kawu Adamu da karfi ya tura shi awajen kofar fita, ya dubi yan parlorn yace,


"Ina masu motoci a kusa? Muje ko"


Al-mustapha ya tashi da sauri .... Hakama Aayan daya mike shima ya bi bayan Bappah maheer. Sai sauran bappanin na su suka dunguma sukai waje. Hamid da Hajiya jamila ma wajen sukai. Ta shiga gaban motar hamid da sauri..


Motoci suka shisshiga aka chusa keyar Kawu Adamu agaban mota. Suka tafu a jere kusan motoci bakwai suka dauki titi, A convoy zuwa inda amaal take a boye....


Parlor ya zama sai Hajiya Maryam da Alhaji Alkali Muhamamd da su Bappah Abdullahi, Haj Aisha matar Alhaji Abubakhar mahaifin Hisham, da Hisham din kansa, da su Hajiya hadiza daketa raba idanu musanman datasan ta bada gudunmuwa na kason lefi a dauke Amaal... Sai jimami suke... Tu'ajjabin maganganun da Kawu Adamu ya fayyace ya bayyana a fuskokin su cike da dimbin tarin mamaki marar misaltuwa..



============


Har bakin kofar makarantar suka faffaka motocin... Kallo daya zakai wa makarantar ka tabbatar ta zama fankoo (unwanted building) Ga juji nan a gefe an mayar da wajen reshen zuba shara...






_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/18, 5:43 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 36_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


Maryaam-Amaal na cikin ajin makarantar data zama kango kuma mafakar yan shaye shaye da zuba shara.


Wani aji ne aka kulle ta aciki akan wata yarkacacciyar kujera...Ba komai acikin sa sai kwalaban shaye-shaye da ledoji na datti da wani kare a yashe a gefe an daure shi da igiya. Kamar yunwa zata kashe shi saboda tsabar ramar sa..


Hawaye ne suke gangara ta kyakkyawar fuskar ta... Cikin zuciyar ta take nanata,


"La'ilaha Illa Anta Subahanaka Inniy Kuntu Minaz Zalimeen.."


Wasu murdaddun maza katti har biyu ne daga gefe can a zaune sun seta ta, Daya da kulqi a hannun sa dayan kuma wani abu ne a paper a nannade yanata busawa kana kallon sa kasan na bugarwa ne . Saboda yadda yake jin sa a duniyar sama ta mashaya yana ife-ife....


Dayan da ke busa sigari me kulqi a hannu ya mike daga zaunen da yake ya nufi inda Amaal take a 'daure a kujera...


Ya sanya hannun sa akan gefen fuskar ta yana tafiyar tsutsa da shi. ... Sai mutsu mutsu ta keyi tanason ta kwace kanta, hawaye na ambaliyar kwarara daga idanun ta . Ga hayakin tabar da ke dayan hannun sa na damun ta sai hawa mata kai yake yi.


Cikin muryar sa marar dadin sauraro mai tattare da doyin tabar da yake afawa yace,


"Bamu da damaar mallakar ire iren ku sai dai kallo daga nesa .. ko a talabijin amman yau ga aljannar duniya agaba na... Dole na fanshe tarin kwadayi na akan ki yammata...."


Ya saka hannun sa ya yage hijabin da ke jikin ta tun daga farkon sa har karshe ji kake kyet ya raba shi biyu... Ya tuge hular kanta ya wullar a gefe itama..


Ya rankwafa yana sunsunar gefen wuyan ta .. ya daga yaja numfashi yana lumshe idanun sa...


"Yammata.... Kin gama haduwa... Maza zo ka sunsuna daddadan kamshin dake tashi daga jikin ta." Ya sake saka kofofin hancin sa akan gashin ta yana sunsuna.. tare da saka hannun sa akan belt din jikin sa yana kuncewa ahankali..


Hawaye nata kwarara a idanun Amaal.. sai kokarin kwance wa take ta kasa. Dayan da ke zukar abun shaye shaye ya mike yana tangadi saura kadan ya faada kan Amaal.


Ya saka hancin sa yana sunsunar gefen kunnuwan ta da gashin nata... Ya saka hannun sa a tsakiyar wuyan ta yana wani tafiya dashi ahankali ya kusa kai tsakiyar kirjin ta kenan aka bugo kofar da karfi..


Al-mustapha ne ya fara shigowa sauran na biye da shi. Da alamar ma shi ya bugo kofar ta fado kasa.


Dai dai lokacin da idanun sa suka kai kan gardayen da ke tsaye kan Amaal din. Daya hannun sa kusa da kirjin ta. Dayan kuma ya saka hancin sa akan gashin ta.


Cikin zafin nama ya karasa ya saka hannu ya wanke fuskar wanda yasa hancin sa akan gashin Amaal da marika lafiyayyu guda biyu. Tare da saka kafa ya shure dayan da hannun sa ke wuyan ta.


Ya shiga dukan sa da iya karfin sa.. Aayan ma ya kamo dayan ya fara dukan sa.. Hajiya jamila ta fashe da kuka ta karasa kusa da Amaal din jikin ta nata rawa ta saka hannu ta yage abunda aka nane bakin ta da shi,


"Ha... Ya.. Teey" Ta fada a wahale a kuma rarrabe tare da fashewa cikin matsanancin kuka.


Al-mustapha ya zare suit din dake jikin sa ya runtse idanun sa ya sakata akan kirjin Amaal din dake daga ita sai doguwar riga mai gajeren hannu. Wuyan v style... Tunda dan shaye shayen ya yage mata hijabi ya wullar da hular kanta.


Ya fara kokarin kwance daurin da akayi mata Hamid na taya shi. Gwaggon court ta zare babban dankwalin ta ta yafawa Amaal din. Itama hawaye tuni suka fara zuba a fuskar ta,


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Wallahi Adamu sai Allah ya tambaye ka.... Amaal jika ce fa awajen ka. Wannan wane irin wulakanci ne? Ka kawo ta nan hakan bai isa ba. Kasa akayi mata wannan mugayen kullewar a hannuwa da kafa. Aka kuma rufe mata baki sai kace a film? Tsabar mugunta? Hakan bai isheka ba kuma ka hadaata da maza gardaye yan shaye shaye suka a tare da ita a daki daya. Kalli yadda muka shiga muka sameta a halin da suka sanya ta? Kaicon ka Adamu kaicon ka. Allah ubangiji yayi maka yadda ka mata." Bappah Usayn ya fada yana girgiza kai.


Bappah Maher ya kasa cewa komai saboda tsabar dimaucewa. Ya juya ya cukumi wuyan Kawu Adamu. Ya saka hannu ya zabga masa mari yana hawaye yace,


"Allah ya isa... Allah ya isar mata, Allah yabi mata hakkin ta akan ka. Ka nada jikoki ai ka sani zaa yiwa naka gwargwadon yadda kayiwa wannan yarinyar koma fiye da haka.. Ka sani wallahi sai Allah ya wulakanta ka."


Haka dai kowanne ya shiga aibata shi yana fadar albarkacin bakin sa. Sarki Junaid ya koma can gaban bango ya jingina. Ya kasa cewa komai.. sai hawaye da ke futa daga idanun sa.. ya saka kasan rigar sa ya goge.. Gaba daya yama kasa sanin abunda zai yi.


Aka kunce Amaal ta kasa takawa saboda rawar da jikin ta yake ba karfi kwata kwata a tattare da ita.. Gwaggo Aisha da gwaggon court ne sika rirriketa gefe da gefe..


A wahala tace,


"Ruwa..."


Aayan ya fita da sauri sai gashi ya dawo da robar ruwa guda daya ya bude ya mika mata, tanata kokarin zama Gwaggon court tace da ita,


"Sha mana amaal"


"Zama zan bakyau shan ruwa a tsaye"


"Allah sarki yairnya mai hankali.... Allah ya miki albarka. Tabbas annabi yace ko kasha ka amayar."


Dss Bappah Hassan ya bawa dama suka shiga ciki da handcuffs suka daddaure hannuwan gardawan,


"Har na wannan matsiyaciyan... Allah wadaran naka ya lalace. " Bappah Usayn ya fada yana mai nuni da Kawu Adamu


Aka garkame hannuwan sa shima aka tasa keyar su suka fita wajen gaba daya.. sarki junaid ya rungume Amaal tsaf ajikin sa yana hawaye itama tana.yi. hajia jamila na gefen su tana hawayen itama.


" A wuce asibiti da ita tukun" Bappah maheer ya fada yana shiga gaban mota


Duk suka shisshiga motocin su... Aayan sai hakuri da sannu yake bawa Amaal ya bude mata mota ta shiga. Al-mustapha nata kallon su ya kasa ce mata komai shi kansa bai san dalilin hakan da yayi ba..


Suka dunguma sukayi wani babban asibitin kudi da ake ji dashi a kandemi... Nan da nan likitoci suka karbeta, bappah maheer yace ayi mata general checkup. Aka fara yi hadi da saka mata karin ruwa saboda rashin kuzarin jikin ta.


Yayin da su kuma suka tsaya carko carko wasun su a zazzaune suna jiran agama yi mata dukkanin abubuwan da suka dache,


"Allah ubangiji ya tsine maka albarka Adamu. Allah ya la'ance ka ya 'dai'dai ta ka..." Bappah Maher ya fada yana mai nuni da Kawu Adamu da yatsa cikin dana sani da dimbin damuwa..


Yanata doka tsaki idanuwan sa na kan gardayen da Kawu Adamun ya sasu tsaron Amaal.


Kawu Adamu da alama zuciyar sa a kekashe take. Don chingam ma yake taunawa tamkar tsohuwar karuwa..


Dik wasu gwaje gwaje anyi mata su... Babban abunda suke fargaba bai faru ba. Martabar ta na nan kaman kowacce nutsattsiyar 'ya mace.


Sai dai hayakin da aka sa ta shaka a kandemi da za'a sace ta ya janyo mata severe allergy dinta ya tashi na sinuses sannan mura ta kamata da zazzafan zazzabi.


Gefe daya yunwar da ta sha na awayoyin da babu abinci chronic ulcer dinta ta tashi... Sannan daddauretan da akayi ya sanya mata samuwar muscles spasm.


Ta sha karin ruwa sosai na kwarin jiki dana antibiotics saboda infection na rashin tsaftar wajen da aka sanyata. Sai na abinci da ba zata iyaci ba. Gefe daya kuma allurori ta sha. Sannan aka sallame su bayan awowi da tulin magunguna dazata shassha da na shafawa a jiki.


Suka rankaya gaba daya suka nufi kandem estate bayan Bappah Nuraddeen ya kira yace a tanadar da abinci gasunan tare da Amaal..




**KANDEM ESTATE**



Masu gadi suka bude tangamemen babban gate din motocin suka shige ciki. Sashen Hajiya Maryam sika dunguma sika yi baki dayan su..


Amaal ta wartsake don da kafafin ta ma ta taka tun daga asibitin ta shiga mota haka da suka dawo kandemi ma sashen Hajiya Maryam. Sai dai kallo daya za kai mata ka dauka ta shekara a kwance ba lafiya ne. Saboda yadda ta tame lokaci daya. Fuskar ta tayi fayau. Manyan idanun ta suka sake fitowa furfutowa waje tubarkallah..


Abinci aka zuzzuba aka ajiye mata a gaban ta. Hayateey dinta na gefen ta ta sa Amaal din ta fara ci tana korawa da ruwa. Kadan ta ci saboda ba yunwa ajikinta sosai sakamakon karin ruwan da aka yiyyi mata.


Bappah maheer ya sanarwa su Alhaji Muhammd komai tun daga kan titin da suka dauka zuwa inda amaal din take. Har sanda sika shiga kangon makarantar. da dai duk abunda ya faru.


Bappah Abdullahi dayayi recording komai da ya faru ya mikawa su hajia Maryam ipad din nasa suka gani. Da sauran mutanen da ke parlorn.


Haka dai akayi ta mayar da zancen. Suka zuzzuba abinci suka ci.. Kawu Adamu da yaran sa Suma aka mika musu yache bazai ci ba. Su kuma yan shaye shayen kamar zasu hadiye plates din suka cinye abincin tas.


Daga nan tambayoyi suka fara biyo baya... Daya daga cikin masu shaye shayen yace,


"Wallahi mu kudi kawai yake bamu ko fuskar sa bamu taba sani ba sai yau. Ya saya mana wayoyi tanan yake kira ya gaya maana abunda zamu aiwatar. Yace ga sakon da zamu turawa lambobi kaza na tsoratarwa ko mu sauya murya mu kira wasu daga ciki. Komai dai shi yake shiryawa."


"Kuma ko da yasa aka kawo wannan bebyn🤣 wasu matane suka kawo ta su uku.... Ya kirawo mu a waya yache zamu ji shi ya sanya mana kudaden aikin mu. Da ke gasiya baya wasa da kudin aiki nan da nan ya sallame mu. Yana kuma saya mana eh yane muna korawa..." Ya karasa fada yana gwadawa da kwalbar shaye shaye


"Mata kuma.... ?" Bappah Usayn ya tambaye shi...


"Bappah...... Eh mata ne Bappah su suka kamani sika shigar da ni motar amman bangs fuskokin su ba saboda wani hayaki ne marar dadi ya kewaye wajen daga nan ban sake sanin inda kai na yake ba " Amaal ta fada muryarta a sanyaye..


"Saka cctv footage dinnan Nuraddeen."


Nan da nan bappah Nuraddeen ya saka suka fara ganun komai tiryan tiryan abun mamaki mata ma'aikatan cikin estate dinne Kawu Adamu yayi amfani da su.


Suma aka kirawo su aka fara interrogating dinsu. Daga karshe dai wancen fado sunan wannan, Kaza ya kamo sunan kaza haka aka tara dinbin mutane dake aiki a karkashin shu. Kusan dukkanin ma'aikatan sashen estate din suna masa aiki


Aka kwashe su duka bayan an gama komai aka hada da Kawu Adamun...Da sauran likitocin da duk ma wanda suka bada gudunmuwa. Don sake tsaurara bincike da rage iri. Daga nan kuma zaa yanke masa hukunci dede dashi da shari'a ta zartar.


Sarki junaid a wajen yace ya saki hajia hadiza da hajia Ruwaida. Zaman sa da su ya kare. Sai da Hajiya Maryam ta tausashe shi tukun sannan ya amince zai ci gaba da zama da su amman kowacce ta tafi gidan su har sai lokacin da zai neme su da kan sa..,


Yaran kuma ya tsawatar musu sosai yaja kunnen su da su hade kan su duk sanda ya sake jin wata baaraka ta taso daga garesu to su kuka da kansu kuma kowacce zata bi bayan mahaifiyar ta.


Sai da dare yaja sosai tukun sanan sika watse. Kowanne ya nufi sashen sa bayan an su Bappah maheer sun sake sulhunta/gargadi tsakanin zuriyar Alhaji Muhammad musanman bappah jalaludden da sarki Junaid. Aka yafu juna sannan sika yiwa juna sai da safe




======


Haka kwanaki sukai ta shudewa...... Amaal ta koma makaranta bayan hutun da tayi na wata daya bata zuwa.


Ta fara Instagram chat tana chatting da mutane na can sosai musanman Arc. Nurayn sabon abokin da ke bata kulawa kamar saurayin ta. Gashi soyayyar su tayi nisa dik kuwa da taki amincewa yazo su gaysa.


Gefe daya ga Hisham daya amince zata aure shi.,..... Yana son ta amman baya bata kulawar datake bukata. Don haka rannan yazo suna gaysawa yake ce mata,


"Idan mukayi aure zaki quitting chats gaba daya.. ki bar WhatsApp kadai....shima sai kin canza number din ki..."


"Saboda me fa?"


"Saboda nasan maza suna rushing dinki... And I won't allow that, Matata wani yana ganin ko da dp dinta ko da bake bache akai"


Amaal tayi murmushin yake ta dan dube shi tache


"Maganar ka kenan kullum yaya Hisham, To ya ya bazan chatting da wasu samarin ba bayan ba daurin aure akai na? Beside baka bani kulawa gaba daya... Ni bansan meyasa kake cewa zaka aureni bama kwata kwata baka nuna mun yadda zan gane kana so ma din....I want time, I want attention, I want connection, I want relationship..Yaya Hisham It feels like I’m dating my self like a sinking ship.. Gaskia I don't understand this relationship of ours...




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥


[9/20, 5:52 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 37_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___







*Hisham* yayi shiru yana duban ta sosai yache,


"Babe... Kinsan me kike faada kuwa?"


Ta dube shi tana mai jinjina kanta cikin tabbatarwa tace,


"Maganar gaskia kenan Yaya Hisham..."


"To zan gyara"


"Haka kake fada ko da yaushe kuma baka gyarawar..."


"Amman dai kinsan soyayya ba itace aure ba ko?"


"Yaya hisham idan ba soyayyar a tsakani taya zamu fuskanci juna?"


Hisham ya zare idanu yana duban ta yace,


"Haba babe... Ki ma dena wadannan maganganun please...kinji? I promise to be an excellent lover "


"Shikenan...."Ta amsa shi a sanyaye.


Ya sake daga wayar da ke hannun sa yana dannawa... ta dube shi ta girgiza kai kawai


"Kafi bawa wayarka muhummanci akai na...."


Yayi sauri ya jefa wayar a aljihun gaban rigar sa.


"I'm sorry...."


Murmushi tayi masa tana kada kai kawai,


"Kin hakura?"


"Uhm..."


"Baki hakura ba kenan"


"Meyasa kache haka?"


"Please na dena... Ki yafe mun"


"To kayi hakuri.. Nima ka yafe mun"


"Baki mun komai ba babe..."ya kalli agogon da ke hannun sa ya sake cewa,


"Zan tafi.... Bye"


"Tohm Yaya hisham... Ka gayda su baba "


Ya mike daga zuanen da yake...Daman a parlor suke zancen. Karamin parlorn sashen Hajiya jamila.


"Zasu ji inshaa Allahu"


Ya mike tsaye yana mai gyara zaman rigar jikin sa.. mikewa tayi ita ma tayi shiga cikin riga da mayafi wadatacce,


Har bakin motar sa ta raka shi... Ya sbiga ciki yana daga mata hannu tana daga masa . Ya futa daga estate din..


Sashen Hajiya Maryam ta tafi... Daman duk ranar bataje ta gayshe ta ba tamkar yadda suka saba a koda yaushe..



Tana shiga bakinta dauke da sallama. Idanuwan ta suka sauka akan su Aaayan da Al-mustapha da ke buga game din whot.


Sai Fatima Yusra da ke gaban hajia a tsugunne tana yanke mata farce.. Duka suka amsa sallamar da tayi din.


Ta shiga kanta a kasa. Ta dan matsa wajen Hajiyan ta gayshe ta. Sannan ta hada gaisuwar tayi musu su uku...


Aayan da Yusraa ne kawai suka amsa mata gaisuwar da tayi.... Al-mustapha ya dan saci kallon ta..


Hajia maryam dake kan kujera ana yanke mata farce tace,


"Takwara surukin nawa ne yazo?"


Amaal kanta a kasa ta kasa cewa komai saboda kunya tace,


"Eh..."


"Ko da naji.. to ya yake hashimun ?"


Namma ta kasa cewa komai tayi murmushi cike da kunya. Yusra nata tsokanar ta... Aayan ma haka yana cewa 'an kasa shi'


Al-mustapha ya mike tsaye ya fuce...


"Pickup 2... General market.. check" Aayaan ya fada

Please Login or Register in order to submit comment