Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din windon asalin main room
Ta soma kafa idon ta
Da shike a gefe daya a bude ne

tsaf ta kalle su sheme shema akan gado rungume da juna sai dariya suke

Kanta NE ya soma kuncewa Amma haka ta danne
Bata yi wani ganganci ba ta sauko a hankali ta koma mota
Dan murmushin hauka ta Daura a fuskan ta tace bani jakata

Shima wani mugun murmushim yayi sannan ya mika mata
Tau.... tau ....ta Daura masa harsahin bindiga a goshi ta koma ciki abun ta

Bata bi ta windown ba ta kama hanya ta asalin cikin gidan tayi kofar dakin Kamr Mai iska haka take tafiya

"Ba tan tama tana bude kofar ya budu

bata ko jira ko Mai ba idonta a rufe ta soma sauke wutar bullet akan gadon kota ena kawai
Sai da ta harba taji kyat.... bullet ya Kare sannan ta shiga hankalin ta

Jin shiru ba wani ihu ko kara ya sata haura kan gadon da Sauri ta duba da mamakin ta ta ga bakomai sai kayan pillow da suka tarwatse

'What" no.... no.... ta soma cewa tana komawa da baya ga wani azaban ciwon ciki da takeji alokacin

Wani ihu mai karfi ta tsala ta tsuguna kasa
kai taga ma hakan bai mata ba ta juya da Saurii zata bi wani boyayayen kofa da ta gani an wangale sa a baya

Chak ta tsaya dajin karar video call na wayar dake gefen gadon na ringing

"A daburce ta juya ta danna button ta tsaya chak ta kallo

Seif ta gani zaune cikin wata mota mai shegen kyw ga suhaimah agefen sa tasha wanka sai kwar kwasa take fuskan ta dauke da murmushi

" dan dariya yayi ganin yadda take hauhawan numfashi ita kadai kamar zata fadi kasa

Sai da ya kammla sannan yace ' sabreenah my life"
Kar ki damu zan miki bayanin komai ko dan albarkacn baby na Dana bari a cikin ki
" u see rayuwa ba haka take ba
Kin aikata min komai kin yaudari mutane mafi kusan ci dake akaina right ?" Dan Tafa Mata Yayi yace
Wowww...nasani u do it for love ko?

Hawaye ne masu daci suka soma sauko mata bakin ta na bari ta kasa cewa komai

C'mon baby sabreen kiyi hakuri mana wannan irin Bacin rai haka
Dan daga kafadar sa yayi yace nima ba laifi na bane

" laifin matata ce suhaimah"don itace asalin rayuwa ta sabreen"sannan ya manna ma suhaimah hot kiss ya karashe maganan sa


Karyaa kake yi seif"" cikin murya mai razanrwa ta fada ta na nuna su da dan yatsan daya Kasa tsyawa Dan barin da yake

Kayi kadan ka yaudare ni Seif 'kayi kadannnnnn.......
Cikin tsawa ta karaashe
Ashe dai baka cika kwarzon wasan ba kayi sauri ma game din naka
tunda ga takardun companyn alfah nan a hannuna sai naga ta fadin

Wani mahaukacin dariya suka kawshe mata da shi dukan su su biyun suhaima kam harda hawaye a fuskan ta Tana Buga Kan sit

Wasu takardun Alfah?
Wayannan ? Cewar suhaimah tana dago mata takardun

Jakar ta ta sa hannu ta laluma taji shol sai ji tayi suhaimah tace
Yarinya kenan
Ai dagangan muka aiki mugu ya kawo ki nan duk shiri ne'
kina haurowa
Shi ya kawo mana takardun daya zare a jakar ki kafin ya mika miki
Sannan ya ajiye mana akan Windwn sama Inda kika gama leken mu duk
Muna sane dake

Dan shiru tayi Kafin Tace"
Uhmmm ena fatan dai kin kashe su mata da mijin na sanki baki sanya sabreen"


Dan daura Hannu tayi tagumin Mai kunshe da neman tsokana da son ta tunzira ta tace
oh" oh ""allah sarki ALFAH wat a sad lovee story...amma na tausaya musu

da Dan yatsa take nunata tace Kuma fa duk kece munafukar su ko sabreen"?

ba tare da sabreen din ta amsa ba suhaimah tace good job
Komai ya tafi dai dai

Sabreen kinsan me matsalarki kin cika daukar kanki kamar ba matsayin mai aiki keke awajen mu ba

Dan rufe bakin ta tayi cikin tsigar zolaya tace au na manta ashe kema dai kawai amfani dake mukayi bamu Fada miki ba Kamar dai yadda ki kama nauman/ kin fahimta?

Sorry ...tace tana Kyle
Kyle dariya ciki ciki


Nan seif yace
Ba lokacin bata lokaci kar ki damu in kin haihu na baki dama ki sayar da dan ki fanshi kudin aikin ki
Cikin wani dariyan mugun ta suka katse wayar Suna Mata bye bye suka barta tsaye durus kamar icce

Xuciyan ta na bugu diff diff kamr zai tashi da ita sama jikin ta na bari duk alokaci daya
Daura hannu tayi aka ta tsuguna ta sake wani razananen ihu wanda ya sata barkewan jini atake

duk da zafin data keji
Kamar mahaukaciya ta soma rolling awajen tana zage zage
Har ta sume tsaban azaban da cikin ta yake mata


Jim kadan da faruwar haka jamian tsaro suka ISO suka katattara ta su kayi asibiti da ita sarkafe da hankcouf hannu da kafa




*surriem*
[3/30, 19:47] Surayyah Ms: [18/03 4:11 am] SmsπŸ’•: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATIONπŸ–Š*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*ALFAH*

*(the story of a wicked betrayal)*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

ByπŸ’•

*SURAYYAHMS*πŸ”₯


*ALhamdullhi my first short story* *"ALFAH"bazan ce komai ba*
*Sabida gaskiya it's more than I expected DUK DA'the story is tiring and full of misery sum times da kyr nake typing"AMMA ALHAMDULLIH DUMBIN MUTANEN DA SUKE KARANTAWA SUKE KUMA JIN DADIN SA YA SA NASAN INSHA ALLAHU SAKO YA ISA...WANDA HAKAN SHINE CIKAN BURI NA*


*ENA MIKA GODIYA TA NA MUSAMMAN*
*MA ALFAH FANS GROUP ZANYI MUGUN MISSING DIN*
*COMMENTS DIN KU I REALLY APPRECIATE YOU GUYS#NAGODE*

*SANNAN MUTANE DA DABAN DABAN ""GROUPS DAYAWA WANDA BAZAN IYA KAYYADAWA BA/ #JUST KNOW THAT I HEART YOUR SUPPORT.. COMMENTS.. AND PRAYERS*
*JAZAKHUMULLAHU BIL JANNAH#NAGODE*



THIS PAGE IS *DEDICATED* SPECIALLY TO THOSE WHO BELIEVE IN ME "KAFIN MA NAFARA WANNAN NOVEL DIN

*MEELAT MUSA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
*MY UMMERHENY*
*AYEESAH*
*SIYAMAH IBRAHIM*
*FEENAH BAE*

*I HEAR YOUR SPIRITS*❀



β–Ά5⃣9⃣



[18/03 4:26 am] SmsπŸ’•:

Doctoci ne kusan uku akanta suna faman aiki amma ena ......

nan MA sai da aka mata cs aka Ciro dan Seif ba rai
Amma haryan zu sabreen bata ko motsi'komai Nata ya dakata

A gefen su Seif kuwa duk burgan sa akan cewa ya Tara kudin da sabreen take aiko masa inta karba wajen alfah tunda acct Dinsa duk an kulle gashi baida karfin karba"gudun Kar aka masa sa ace yayi defending din kudin

Niyyar said da su fara aikin cin hanci da documentation na karbe duk wani dukiyar alfah ciki da waje""

Sai dai wajen Ciro Kudin can hancin MA yakai awowi kusan uku a banki baiji wani kwakwaran vayani ba
Ga suhaima sai kiran sa ta ke ya fito tagaji da jira''

" manager yadai ko kudin sunyi yawa ne yafada yana dan washe baki

Dan kallon sa yayai yace ogah "Ka kara hakuri dai muna kan aikin kA ne netwk na bamu wahala sosai
Duk wannam matsalan da bazata samu ba da a salin branch na cikin gari ne

Uhm um bakomai kadai kokari ka hanzar ta cikin dan Burga yace kasan zan iya missing important meeting a Japan so hurry up

Shiko manager a tsora ce yake don gudun In jamai'an tsaro basu karaso akn lokaci ba Seif zai iya fahimtar wani abu ya gudu" ya barsa da bala'i

Wani karamin bankin ne na uba a dan wani LGA a kusa da cikin garin Abuja' da shike ba cika zuwa ta wajen bane seiif yayi kokari ya ajiye kudin da sabreen ke basa da su kusan shekara biyu kenan

shika dai ne Wanda alfah Bata sa aka kulle ba sabida Dama fixed ne

Aganin sa edan komai ya kammala Zai iya karbe acct Dinsa daga Hannun Koma waye ne"

Yana zaune yana buga game a sabon Samsung Galaxy note 8 dinsa yaga suhaimah ta shigo sum sum cikin bank din Kamr Mai Shirin fashewa

Da dan hanzari ya karaso fuskan sa a marairace yace my life kin gaji ko? Netwk NE fa
!
Kar karwa bakin ta soma yi
Wanda ya sa shi Shiga rudu
Yana dan juyawa Kuwa ya ga rundunar jamaian tsaro sun soma kewaye su da bindigogi

" a take wasu mahaukatan zufa suka soma keto masa suhaima sai ruwan hawaye take faman yi

gashi ba Hanyar tsira

Ko jiran minti guda ba'ayi ba ka dura su mota hannun su sarkafe da ankwa aka yi da su cid office


A gefen su alfah kuwa" tun daga ranar nauman ya koma shiru shiru gaba daya ya sauya daga yadda yake da Chan

Duk iya kokarin nanny Fatima da alfah s
don su tabbatar masa komai ya wuce amma Sam yaki sakan jikin sa
,,
Karshe ma gidan su ya koma wajen baba Yusuf ya cigaba da zama da shi
Duk da ba da son ran su ba
haka don' dole suka kyale sa

Kusan sati guys' komai ya tsaya ana jiran sabreen ta tashi

Tuni alfah ta cigaba da aikin ta da shike dama fake takardu ta ba ma sabreen din tun farko
Shyasa lokacin da take signing ba taji komai aranta ba

" Anty kubrah ce kullum jigila kofar office da kofar gidan su ALFAH rokon gafara amma Sam security basu bata dama tayi ido hudu da ita ba ma

A gefen alfah kuwa damuwan ta mijin tane kawai don' tarasa yadda zatayi ta dawo da shi kamar yadda suke ada chan baya

Ranar " daga office ta wuce gidan su baba yusf bayan gaisuwa ta shige kitchen da niyyar Daura abinci
',ko cokali bata gama ajiyewa ba taji ya cafko hannun ta
Yayi waje da ita"fuska ba alaman wasa yace' stop it ..Aleesha na ce bana son haka ko?

Dan yarfe hannun ta tayi kamr zatayi kuka tace akan me?
Bayan ka guje ni acahn nan din ma bazaka bari na yi aiki na a matsayi ma ma matar ka ba

Hannu yasa ya to she bakin ta daga furta wani kalma
" murya a sanyaye yace' bake kike da wannan hakkin ba
Ni ya kamata na zama bawar ki ..nine zan Sha wahala sosai akan ki bake ba"

Dan jawo ta yayi ya sauke mata narkakum idon sa cikin NATA yace"
Bazan iyaba ALFAH
I'm not ready yet na sake shiga rayuwar ki ",ki kyale ni kinji?....

Kallon sa ta cigaba dayi a raunane takai masa duka kan kirjin sa tan
soma kuka tana cewa
" baka so na ko nauman?

Kar kada mata kai yayi a sanyaye alamam a:ah

Bai hankara ba ya sake jin Saukar wani dukan Kan chest dinsa
Cikin kuka tace 'karya kake yi ba gashi kace na kyale ka ba" wato rabuwa dani kake so kayi ma kenan ko?

shiru baice uffan ba shikam

Dan goge hawayen ta tayi a zuciye tace shikenan"
To Kayi duk abunda kake so "

Hannu ya Kai zai kamata ta ture sa
da gudu ta fice ta bar sa tsaye awajen

Dan sirarran hawayen sa ya goge "yacee am sorry"
"Bazan iya sake cutar dake bane don' ni kaina yanzu ba adai dai nake ba

Kamar daga sama yaji muryan baba Yusuf kusa dashi" yace nauman?

Rusunawa yayi a gefe ya gaishe sa

sannan yasa kunne yana jin duk wani Fada da nasihan da baba yusuf ya Shiga masa masu ratsa zuciya

" indai har cutar da ita kake tsoron sake yi nauman to ka tashi yanzun nan ka koma wajen matar ka ku zauna"karshen maganan sa kenan ya mike Don ya
Bar wajen

A ladabce nauman ya dago jajayen idanun sa yace nagode baba

Bai wani bata lokaci ba ya Shiga ciki yayi wanka ya sanya golden brown shadda
na jumfa mai kywu da tsari komai yayi Ra's ya fito da jarumtan sa da kwarjinin sa sosai

shikan sa ya manta rabon sa da yin kwalliya haka
Haka Tunda ya dawo sai Yau ya hau asalin motar sa da aka sace sa aciki
Sannan Ya nufi gidan alhaj fadoul

",kusan mintuna talatin suna dan tadi da nanny Fatima a falour alfahn Sam taki fitowa

dan dolen sa ya cire kunya yace
Nanny alfah fa?

Dan murmushi kawai tayi don dama ta fahimci abun tace" ta na ciki
A kunyace ya mike yacee toh bari na dubata

Itama nannny site dinta kawai ta koma abunta zuciyan ta fal

" kwance tayi da hijabi ta juya kanta gefe kamar mai tunanin wani Abu

Daga kofa Sai da ya kammala kare mata kallo sannan ya karaso daf da ita
Ko da jin qamshin turaren sa ta soma yunkurin juyowa shikam hannu kawai yasa ya soma cire hijabin nata jin haka yasa ta
Kota kula sa har ya kammla sannan ya kunna ac low

" daf da fuskan ta ya sa nashi yace' haba madame zaki kashe min ku ne azafin nan kin sa hijabi ga blanket sannan kIn kashe ac?
A dinga min adalci mana


Cikin dan shgwaban da bata San tana dashi ba ta soma matso idonta tana Neman hawaye su sauko
Dan murguda baki tayi tace eh din ena ruwan ka toh
Ba kace baka so nah ba sannan ta karashe kamar za tayi kuka......
Cikin idon sa itama ta kalla tace kaje din nima bana son...charaf taji ya cafke lips dinta ya soma tsosar su ahankali kamar wanda yake shan Zuma

Kusan mintuna talatin ahakan sun gama cukuikuye junan su
Murya chan kasa yace" na tuba gimbiya ta .Allah ya huci zuciyar ki ..ni na isa nace bana son ki rayuwata? nidin banza"

Kau da kanta tayi cikin Jan aji murya kasa kasa tace bn amince ba

"Kunnuwan sa duka biyu ya kama ya lanwngame yana rokon ta amma Sam take ta juyo ta kalle shi kamr da wasa alfah ta daure fuskan ta sosai

Har ya kaiga ya cire hular sa ya zuba gwiwa akasa a marairece ya soma cewa "wifey na kiyi hakuri dan Allah
Bana kara cewa ki kyale ni

ko a mafarki ne kika ji nafada kimin irin dukan dazun nan kinji". Sosaii abun yaso ya bata dariya musamman ma da taga ba alaman wasa shima a fuskan sa duk ya susuce fuskan kalar tausayi kansa akasa kamar maroki

Mikewa tayi ta zauna ta dube sa da kywu tace' promise?

Dan gyda kansa yayi yace " an oath baby na'

Daf dashi ta karaso ta rungume sa tana cewa I love you

Shima hakan yafada tare da kara haurowa da ita saman gadon
Kafin kace wani Abu salon wasa ya canza

Dan saida alfah tayi dan zazzabi da safe tsaban rikon da ya mata a daren


Ranar suna gida throut ko office ba taje ba tana nanike ajikin sa har tayi bacci

Bude ido tayi taji mummnan labarin cewa nauman da nanny fatima na chan asibiti wajen sabreen

Akan cewa aunty kubra ta ma sabreen alluran mutuwa har ta mutu
Ita kuma tana chan hannun yan sanda
A kan washe gari za Shiga kotu enda zA'a yanke ma Seif
Suhaimah da ita din hukunci


Duk da yanzun bata ko son jin sunar sabreen amma sosai taji mutuwar ta aranta haka kawai ta tsinci kanta da yin hawaye lokaci guda

Kusan karfe Tara saura suka shigo gidan suka tarda ita
Da dan gudnta ta zo ta rungume sa ta soma kuka a hankali

Hakuri duka suka soma bata da kyar ta sasaauta tace meya faru ne .meyasa aunty kubra har zata kashe sabreen

" calm down ALFAH..nauman yace

muma nan bamu san komai ba tuknna
Amma naji tana cewa sabreen ne tabata oder ta kashe ta
Ganin reactions dinta nanny tace
Jeki kwanta alfah" ka kaita ciki nauman fuskn ta dauke da damuwa

Ba musu ya jata su kayi ciki sannan itama ta nufi site dinta Tana jimamin abun



*surriem*
[3/30, 19:47] Surayyah Ms: [18/03 4:11 am] SmsπŸ’•: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATIONπŸ–Š*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*ALFAH*

*(the story of a wicked betrayal)*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

ByπŸ’•

*SURAYYAHMS*πŸ”₯


_Tsokaci_ βœπŸΎπŸ‘‡πŸΏ..........

*A rage dogon buri da son Kai Kai enda Allah bai Kai ka ba*
*Bature yace wai"" envy shot at others and wound itself"""*
*trust no one cos Even your shadow leaves you in Dark*

*Hattara da kawayen zamani πŸ™ŒπŸ½*

*dedicated to*πŸ’‹β€πŸ‘‡πŸΏ

*swty umerhny*
*besty asmeenat*
*my meelat*
*my real maman πŸ™Š*
*Cwt leemah*
*My lovely ummu farhana*
*My cwt auta raheemah*
*Meemah ta*
*Cwt bilkis*
*My maman areef oganniyya*
*aunty haleema20*
*Saleehat*
*ummu affan*
*Umman saed*


Fin πŸ˜πŸ™ŒπŸ½



β–Ά ~6⃣0⃣Finale~




πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š



[18/03 4:26 am] SmsπŸ’•:

ranar shiga kotu Duk iya kokarin sa kan alfah ta zauna a gida haka taki fir
Saida akaje kotun tare da ita da safe

Ba tare da bata lokaci ba a yanke ma Seif hukunci daurin rai da rai tare da horo mai tsanani
sanadin kamashi da laifuka daban daban ciki harda harkan cocaine

Don' haka aka kaishi babban prison na gombe wato kiriri prison

"ita kuma suhaima daurin shekara
89 aka mata tare da taran kudin alfah data debe kusan million hamsin da shida itama da horo mai tsanani

Duk iya bayanin aunty kubrah akan cewa sabreen ita da bakin ta ta bada dama ta mata allura yaci tura

dan shaidu da yawa sun shaida cewa aunty kubra Zara iya ta kashe sabreen don son ranta

Don' dolen ta ta amshi laifin da ba Nata ba
cikin ranta tana cewa alhakin ki ne ya kamani sabreenah
Ni na soma daura ki akan wannan mummunan hanya "


A hanyar ta na fita zuwa motar da za,akai ta prison itama daurin rai da rai
Ta dakatar da jamain tsaro sannan ta ma lauyanta magana akan ya tabbata ya mika ma alfah da nauman letter sabreen


Tsaban abun ya basu tausayi da sanyin jiki kwana biyu
suka yi Suna jimami kafin suka yanke hukuncin Bude letter" _kamr haka
"
_ASSALM_ _MY_ _TWO_ BEST _FRIENDS_
_DUK_ DA _NAJI_ _KUNYAR_ _FADAN_ _SUNAN_ NAN _AMMA_ BANA _NADAMAN_ _KASAN CEWA_ DA KU A _RAYUWATA_ " _URE_ D _BEST_ AND _MOST_ _BEAUTIFUL_ PART OF MY _LIFE_

NA _CUCI_ KAI _NA_ ..NA _ZALUNCI_ KAI NA"
A LOKACIN DA KA _NUNA_ MIN _KAUNA_ DA _KO WATA_ _MACE_ _ZATA_ SO A _RAYUWAR TA_
_HAKA_ MA _MATAR_ KA _ALFAH_ TA NUNA _MIN_ SO DA _YARDA_ FIYE DA _KOWA_ _A RAYUWAN_ TA
AMMA _MENAYI_ ? NA _HA'INCE_ KU .. _NA_ _HA_ _INCI_ KAINA"

_DUK_ DA NASAN _BANCANCAN CI_ _KOMAI_ DAGA _WAJEN_ KU BA _AYANZU_ ENA _NEMAN_ KU _GAFARA_ KO _BA ZAKU_ YAFE MIN BA....ENA _MATUKAR_ _KAUNAR_ KU _DUKA_
_SAI_ DAI _BAN_ NUNA _MUKU_ BA SABIDA _SHAIDAN_ YA _RIGA_ YA _RUDANI_ "

_ALFAH_ KI KULA DA _NAUMAN_ KINJI ? _DA_ KO DA _GASKE_ NE _BAZAN_ _TABA_ SAMA MIKI _MIJI_ _WANDA_ YAFI SA BA"

_HAKA_ KAIMA _NAUMAN_ KA _KULAMIN_ DA YAR UWATA _JININ_ _JIKI_ NA _ALEESHA_ ....
_ALFARMA KO INCE ALKWARI_ NA _KARSHE_DA ZAKU MIN "ENA _ROKON_ KU DA SHAFE _TARIHI_ NA A _RAYUWAR_ KU _DANA_ _YAYAN_ KU

NA _YAFE_ MUKU WANI _ADDUA_ _A GARENI_ DON KO _KADAN_ BAN _CANCANCI_ _KOMAI___ _DAGA_ _WAJEN_ _KU_ _BA_ .......


_BYE__ _FOREVER_ _SABREEN_ "


Sauke ajiyan zuciya yayi tare da Jan alfahn kusa dashi yana rarashin ta
"Allahu Akbar duniya kenan Allah ya dada kare mu da ga sharrin zuciyan mu

Ameen tace itama ta soma cewa a ranta
I wish baki yanke makan ki wannan mummnan hukunci ba sabreen" Allah mai son yafiya ne da zai yafe miki
Allah ya yafe mana baki daya"/


*AFTER 5yrs*

_Instabul_ .. _turkey_ 9.50am


"wani tikeken gida ne wanda aka yisa shape din butterfly
iya Karshen tsaruwa ya tsaru

A gefe Chan wani garden ne wanda kasan sa koriya ce sharr sai ganyen bishiya mai dauke da jajayenn flower da suke faffadi kasa Wanda suka Dada kawata wajen sosai

Wani kykkwar yaro ne fari sol da shi wanda atata bazai wuce 4yrs ba
mai bakin suma wuluk sanye da sky blue armless shirt da farin wando ya riko hannun wata karaman yarinya wacce kallo daya ya isar maka kasan yan biyu ne

Itama Sanye da short pink gown dinta

tsaban kyun su iri daya da dan uwanta sai dai ita idanun ta brown ne

sannan ga suman ta zirrr har gadon baya suna faman wasa kan steps din dake tskiyar garden din

Daga gefe Chan alfah ce akan cinyar sa da katon ciki kimanin wata biyar tana faman kiriniya ya bata camera ta dauke hoto itama...

*ALHMDULLIH NAUMAN YA DAWO BABBAN DESIGENR A KARKASHIN* *COMPANYN SA MAI SUNA ZAFREEN*
*WATO SUNAN* *YAYAN SU NA FARI* *ZAFAR DA ZAFREEN*

*KO DA ALFAH TA* *SAMU LAMBAR YABO DAGA KASAR DUBAI DA ITALY* *BUSINESS DIN TA YA DADA KARFAFA A* *DUNIYA BAKI DAYA*

*DAGA NAN SUKA TAHO HUTU NAN* *GIDAN KAKAN ALFAH A TURKEY*.
*CIKIN NISHADI DA KWANCIYAR"* *HANKALI HAKA RAYUWAR SU TA CIGABA*






πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€


*"Alhamdullihi sai kun jini a Sabon littafi na*

_Mai suna πŸ˜œπŸ€’

✍🏾........



*πŸ’…πŸ»YAR MAGAJIYAπŸ’…πŸ»*


*massalam*πŸ’‹πŸƒπŸ½β€β™€πŸ™ŒπŸ½
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment