Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ka dawo photographer shikenan kawai

Perfect sabreen tace tare da dan tafa hannu
Gaskiya da abun zai kayatar ..mata model miji photographer


Dan dariya dukan su sukayi sannan
Nauman yace toh yanzu kan muje gida tunda an solving wannan isssure din

Dan daiya tayi tace ka amince?

Da murmushi yace" uhm Amma sai na gwada nagani in suka karbi first shoot din mu sai mu cigaba ko ya?

Umm yayi muje koh?

Itadai sabreen shiru tayi atsakiyan su
Cikin ranta tace iskanci ko godewa ma baza sumin ba"

Damuwar sa kawai suje gida ya latsa ta
Munafuki kawai

A haka Dukkan su uku suka jera suka koma gida ana tafiya jefa jefa har suka isa
Jim kadan kowa ya kimtsa da kyar ya sa ALFAH ta ci abinci don' kusan kowani rana sai yayi da gaske take karba

Bayan sun kammala kowa ya watse sabreen ma da soyayyar su ya isheta daki ta koma
nauman na rungume da ALFAH ajikin sa da tuni tayi barci akan doguwar kujera na cikin dakin

" a hankali ya sauke ta kan gado yana kure ta ido da mamakin yadda yanzu ta sauya ...son bacci ga laulayi da rashin cin abinci"kiss ya manna mata a goshi sannan ya fito waje da niyyar dauko flash dinsa a dayan dakin su

Yana murda kofa da niyyar fita da abun a hannun sa yaji sanyin hannun ta anasa

Cikin dan zafin nama ta turo sa ciki
Tana binsa da wasu shu'umin kallo
Sabreen bana so....ki bani hanya kawai yace fuskn sa a daure

"Dan langwame fuska tayi ta kankame sa ta baya tana sauke numfashi
" nauman jiya baka ga kira na bane"?
Kasan na Riga na saba dakai kwana biyun nan da kyar nayi bacci jiya sabida rashin ka
Meyasa...


Stop ya Fada yana cillata chan gefe sanda tayi tangal tangal kamr zata Fada kasa

Na Fada miki baa son wannan abun da mu keyi anan
Meyasa bazaki koma gida ba ai nace zan dinga zuwa ko?
Haba sabreen in mistakley ALFAH ta kama mu fa
Me zance mata

Sai kace mata ni matar ka ce" cikin masifa ta fada muryan ta na rawa

Ohh ko? Ni
Kuma nace mata burin ki nake cikawa a gidan nan kenan ko
Mtsww kinyi kadan da zaki min barazAnr haka sabreen
Yadda kike ganin kinada shaida akaina nima enada shi akan ki
Silly girl"

A firgice ta ke kallon sa tace "What ?me kake nufi nauman
Wani shaida kake dashi akaina
Cikin dan tashin hankali take maganan

Bai karasa budr Baki ba yaji kamar wani irin yanayin motsi kamar sautin gudu a daki
Zuciyan sa ne ta Shiga bugu a razane yace ALFAH sannan
Da Sauri ya juya ya fice ya barta. A wajen a tsaye




*surriem*
[3/30, 19:47] Surayyah Ms: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATIONπŸ–Š*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*ALFAH*

*(the story of a wicked betrayal)*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

ByπŸ’•


*SURAYYAHMS*πŸ”₯


*Dedicated to all my fans..I love you..I love you....I love you...kai na baku❀gaba dayaπŸ˜œπŸ’‹*
*Allah ya barmu tare*




β–Ά4⃣5⃣



"Yana shiga dakin ya hango gadon empty ba kowa
Sai kakarin Amai da yake tashi daga bathrumm

Cikin tashin hankali da damuwa ya bankado kofar
A zube akan gwiuiwarta take sai amai take gwazawa kamr ranta zai fice"

Sabreen ne ta karaso wajen itama da dan Sauri tana so taga meke faruwa
Dai dai lokacin da shima ya zube gaban ta yana jera mata sannu

Amai kawai take yaki tsayawaa
Hankalin sa ya mugun tashi yana kallon ta
hannun sa bibbiyu rike da ita sai sannu yake jera mata
Cikin mamaki da daurewar kai sabreen ta soma zancen zuciya a tsaye akan su

Kar dai ciki ne da ALFAH?ennalillhi wa inna ilaihi rajiun na Shiga uku tafada cikin wani bugun zuciya'
Ana wata ga wata" ...
Kukan da ALFAH ta fashe da shi ya sata dawowa da hankalin ta akansu
Shima idon sa taf taf ya ciko ya riko ta yan dan bubbuga mata baya yana cewa sorry wifey"sannu
"Gwanin tausayi da kyar amai ya lafa mata

Bai ko kula ba ya shiga rage mata kayan jikin ta
Sabreen na tsaye tana binsa da wani irin kallo
Ko ajikin sa har ya sauya mata da towel ya fito da ita

Lumui tayi a jikin sa tana maida numfashi sai rarrashin ta yake kamar jaririya "

Itakam sabreen ma da abun ya isheta sulalewa tayi
Ta barsu ta koma daki tana kan jimamin abunda take hasashe akai

Kusan bayan ishai ta sake fitowa
Da niyyar sake duba su amma taji gam ko ena a kulle"

Harde hannu tayi kan kujera gashi tasha uban make up tace
"Hmmm nauman kenan.....ko ena sukaje oho
'ji yadda ya wani susucee ya haukace akan yarinyar nan sai kace ba shiri bane'
Na Dade da Fada ma suhaimah nauman soyyaya yake da ALFAH na gaskiya tace Sam ba haka bane
Amma Yau sai na gano gaskiya...ena nan a gidan nan

Anan ta zauna har suka shigo ya riko hannun ta tana biye da shi
Kamar da gaske ta mike tsaye ta sauya fuska kalar damuwa ta iso gefen alfahn tana jera mata sannu
Gyada kai kawai tayi alamn ta gode

Shi kuwa Sam yaki sake ta da kansa ya zaunar da ita kamar wata sabuwar sarauniya

Bari na kawo ruwa ko wifey
Ko wani abun kike so na daban cewar sa cikin dan damuwa

Kar kada kanta tayi alamn a'ah
Sannan tace ruwa zan Sha amma ba mai sanyi ba

Ok yace ya mike yayi hanyar kitchen da Sauri

Dan karamin tsuka sabreen tayi a ranta tana Allah wdar da rawar jikin da yake yi

Yana mulewa ta tsuguna tace'
Yadai ALFAH wai meke damun ki haka
Naga mijin ki duk ya kasa samun sukuni?
Ko wani serious Abu ne tel me

"Dan murmushi tayi bata ce komai ba sai ga shi ya fito da ruwan a cup

Da dan Sauri sabreen ta matsa gefe
Sannan ya tsuggunna gaban alfah nan ma ya nace shi zai bata ruwan ta sha

" hubby na ka huta haka kaga sabreen ma ta ce ka fini damuwa ko? Tace adan shagwabe

Dan murmushi yayi kawai yace yana kallon cikin nata
Ai dole na wifey na
Maman baby"
Yanzu fa sunan da zan na kiran ki da shi kenan
Ya fada yana dan dariya ciki ciki

Baki a wangale sabreen ta ke binsu da kallo don kuwa jin maganan na su ya sata Shiga wani mummunan shock
A zaune

Murya na dan rawa tace
Ciki kike da shi ALFAH?

Atake Dukkan su suka juya tare da amsa mata cewa ehhh
Sabreen'

Naumam har da karawa da cewa "
My lady is now a woman ....kwanan nan zanga super beautiful king ko queen dina

Wani takaitaccen murmushi tayi mai dauke da boma boman tashin hankali
A daburce kamar marar gaskiya
Tace Alha..mdul..hi

Allah ya sanya alkhairi friend congrats

Nagode sabreen ...ke kam yanzu ai kinyi nisa

Uhmm ...kawai tace da dan murmushin yake ta mike cikin daki tare da cewa excuse me

Koya kula ya dubi enda sabreen tayi Gefen ta ya koma ya zauna yana murmushi mai kayatrwa
" I'm so happy Aleesha...bazan iya misalta miki farin ciki na Yau ba
I wish zan iya kwana ena nuna godiya ta wa Allah
Sadaqan da mukayi dazo gani nake kamar ya kasa min compare to wannan babban kywta da Allah ya bamu"

Hannun ta ya kai baki ya kissing
Yace I love you alot baby na.... soooo much ya hada da lumshe ido

Murmushi kawai take yi batace uffan ba ta kwantar da kanta akan kirjin sa tana wasa da yatsun hannun sa a hankali tace I love you more hubby na" Kaine rayuwa ta

Kusan mintna suna zaune a haka kowa da nashi tunanin a ransa
Murya chan ciki tace"
Gobe zamu fara shoot ko?

Dan maida kansa yayi saitin fuskan ta yace no"

Meyasa ta fada tana dan sulalewa a jikin sa

" ba abunda zaki sake yi ALFAH
Komai zanyi I promise
Bana son wani abun ya taba min ke da baby'

Dan gwalo ido waje tayi tace "'Uhm.unmm nikam gaskiya ban yarda ba
Ai lpyata lau.nikam babyn mu ma haka

So kake nata lalaci ko
Thnk God doc janet
Ta gaya maka inbana motsa jiki zan Sha wahala wajen haihuwa
A shagwabe take maganr tana wani narkewa kamar yarinya

Dan shiru yayi yana kallom ta sannan yace Ok toh naji maman baby amma dai baza muyi dayawa ba ya fada cikin sigar tsokana

Trow pillow ta dauka ta jefa masa tana dan bubbuga kafa akasa shikuwa sai dariya yake mata yana nanatawa
A haka suka shige daki

A gefen sabreen kuwa bayan ta sha kukan ta har ta gaji waya ta dauka ta Shiga tura ma Seif sako amma Sam bai tafi ba
Hakan ya sa tayi wurgi da wayan kasa
Ta sake rushewa da wani kukan
Wayyo Allah na na Shiga uku" ALFAH tana da ciki? yanzu vasectomyn da nauman yai ya warwarwa kenan

"Toh Wallhi sai na kwabar da cikin nan
Wannan cikin babban barazana ne ma rayuwa ta what in nauman ya juya min baya?

Chab Dole ma ya kwabe
Nan ta dialling number Suhaimah su kayi wata magana sannaan taji dan dama dama

Mikewa tayi ta Shiga wanka da kyar ranan bacci ya dauke ta





*surriem*
[3/30, 19:47] Surayyah Ms: [18/03 3:20 am] SmsπŸ’•: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATIONπŸ–Š*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*ALFAH*

*(the story of a wicked betrayal)*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

ByπŸ’•

*SURAYYAHMS*πŸ”₯

*Yar hijirah* by
*My kakus Ummu farhana*
ENA tayaki farincikin kammalawa "

Allahu ya sada mu dake a next book dinki mai suna ...uhmm uhmmm πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸ˜œ



*DEDICATED TO MY BEST FRIEND ASMEENAT ZEEYAN*




β–Ά4⃣7⃣




[18/03 3:35 am] SmsπŸ’•: Tun asubahi yake faman nutsar da kansa don' wani zazzabin dake kokarin Shiga masa jiki"
Bai bata lokaci ba daga masaallaci ya sake ficewa Neman ta ...
A hanyar zuwa gidan su da sabreen
' tun daga gate yayi parking ya Shiga da gudu kamar ana bin sa
Amma gam yaji kofar alaman itama bata nan"

Dafe kansa yace ennalillhi .a rude yace ...kar dai sabreen ma tana tare da Alfahn ne"
Amma ai wayar ta yana shiga kusan karfe 1 saura

Ena zata je da sassafe haka?
Dan lekewa ya cigaba dayi kafin ya hakura ya fice ya bar anguwan

" sai wajen misalin karfe 9 aka turo kofar da ALFAH ke ciki"
Basu ce mata uffan ba suka zagaye ta
Cikin ta sai hargowa da gululu yake don' tsoro"

Ba abunda takeyi ranta sai addua ..hawaye kuma sun kasa dena zuba mata"

A gefen nauman kuma Yanke hukunci yayi zai kai case ma yan sanda a hanyar sa na tafiya yaga kiran sabreen din"

Wani wawan burki ya taka ya sauka kan hanya da Sauri ya daga yace"alhmdullhi sabreen
Ena ta neman ki tun jiya bakiga misdcol dina ba ne?
Banga ALFAH ba ko kinsan enda take.?..ko
Da zu Dana j gidan ki da safe baki nan pls talk to me ya karashe cikin damuwa da hargitsi...don' shikansa bazai iya maimaita abubuwan daya Fada ba

Wani wawan dariya mai ban haushi ta sake masa a kunne "kusan minti biyar
Saida tai mai isarta kafin tace"
"Wawa..mahaukaci..ma cuci ..azzalumi..mugu..dan isk...

Ya isa haka sabreen cewar sa cikin wata mugun tsawa"
Tsaban bacin rai Muryan sa na karkawa yace Ena ALFAH kawai na tambye ki?

Itama cikin tsawan ta mayar masa da cewa"
Na dauke ta. ..zan kashe ta na kashe dan dake cikin ta case close

Wani gum gum yaji a kunne sa da zuciyar sa A daburce har wayan na Neman fadawa daga kunnen sa yace" kin dauke ta fa kika ce' akan me ?
Kina da hankali kuwa sabreen?
Kidnapping ALFAH kikayi ko me?
Answer me ...

Cikin dan takaitaccen dariya tace hankali na daya kaine dai nake ganin ka soma samun tabuwar hankali don' kawai ALFAH tana dauke da cikin ka

A sanyaye cikin rashin son ya amince da zancen yace "Sabreen pls ...dan Allah kibar wannan wasan ..kifada min ena ALFAH take?

Dan tabe baki tayi tace ohhh baka yadda ba ko? Toh Kasa kunne kaji wannan

Karar number yaji alaman tana dialing wani call a wani wayan"
Yana ji yayi ringing da shike speaker ta sa tace bata wayar mijin ta yaji muryan ta'

"Kamar zuciyan sa zata fita a kirjin sa haka yake ji a lokacin

Take daya daga cikin su ya sa mata waya a kunne cikin tsawa yace yi magana "
Ita dai tasan kiran sa kawai akayi amma ta kasa gane waye ne''

Murya na bari tace hello"
Lumshe idon sa yayi yanajin saukar wutar takaici a jijiyoyin sa take idonsa suka kada suka sauya kamannin su
jiki a mace
Yace" wifey are you ok"?

Wani kukan ta fashe masa da shi wanda ya sashi zubda tsiririn hawaye shima: murya na rawa ya shiga cewa me suka miki? Sun taba min ke ko"

Itadai gyada kanta kawai take tana kuka amma sam bakin ta ya kasa cewa wani Abu sai
"Bansan su ba hubby..pls come am scared"
"Ki kwantar da hankalin ki zanzo kinji" I promise..zan...
Kyat suka kashe wayar su suka daga akunnen ta

Saida ya dan saitakan sa sannan ya sake danna ma sabreen"
Bugu daya ta dauka
Cikin dan dariyan tace',yanzu fa?
Ka yarda ko sai na hada da video

"Cikin bacin rai yace"Allah ya tsine miki sabreen ...I hate you,

Ohhh really'
Ai na Dade da sanin haka nauman...amma kasani ni ba abun wasar ka ba ce"u can't dumped me
Akan wata mace kayi karya wallhy

Kuma as for ALFAH da babyn naka kashe su zanyi naga yadda zakayi
Fool"

"Dan shiru yayi cikin sanyin murya yace toh naji ..fine'
Na rokeki kimin duk abunda zAki min ki bar ALFAH
Pls sabreen badan ni ba dan Allah'
Na yadda zanyi duk wani abun da kika ce but pls don't hurt her

dan shiru tayi dan harga Allah tausayin sa ne ya soma rabar zuciyan ta

" fine. tace a takaice..
....zan baka dama nauman
Amma kasani no backing out
Or else wallhy kaji rantse maka duk randa kamin kuskure sai dai tsinci gawar ta bazan sake baka dama irin wannan ba

Nasan zakayi tunanin zaka kai cune na ko?
Toh albishirin ka ...yanzu haka ALFAH ta dauka tare aka kidnapping din mu ..don kuwa tare na shirya mana komai
And quest what? Ya rana sunyi aikin su sosai"

Neva joke with me nauman "

Shi dai shiru yayi baice uffan ba"
Idon sa a lumshe
Jikin sa sai rawa yake shi kadai azaune

A hankali ya soma bude bakin sa murya ciki ciki yace" deal"
Sabreen na amince just let her go now"

Dan murmushin takaici tayi tace 'good
Anjima zan dawo maka da ita

Ah'a kifada min enda kuke kawai zan dawo da ita da kaina

No way" ka jira kawai nace maka in bahaka nafasa
Bana son rawan kai fa

Shikenan sabreen ...sannan ya katse wayar
Bayan kamar awa hudu ta goga ga abubuwa ajikin ta alaman ta jikita har wani dingisawa take yi

Sannan ta bada yaran ta oda suka watse a wajen gaba daya

Alfahn tana kwance taji an taba ta a firgice ta mike idanta har sun kumbara
Rungumar juna su kayi suka fashe da kuka kamr dagaske

Sabreen are you ok?
Cewar ALFAH cikin shashekar kuka

Itama kamar da gaakee ta dada kankame ta tace taso
ALFAH bamu da lokaci
Mu gudu kafin su dawo ni zan tsiratar da mu

Dan ware ido ALFAH tayi cikin mamaki tace"
Tsira anan? Kar fa aka mamu su kashe mu

Uhm uhm ...ALFAH wallhy bakowa trust me naga wani window a chn baya mu gudu kafin su dawo

Batare da bata lokaci ba suka tashi ta ja hannun ALFAH suka fice

Ta wani dan window ta turo ta suka kama hanya sai gudu su keyi
Cikin rantaa tana faman murmushin mugunta ganin yadda alfahn ke wahalar gudu a jejin ga danyen ciki


"A dabaran ce ta sake wani mugun murmushi "ta sake kallon ta cikin ranta tace
Allah ya sa cikin ma ya bare da kansa wawiya kawai"




*surriem*
[3/30, 19:47] Surayyah Ms: [18/03 3:20 am] SmsπŸ’•: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATIONπŸ–Š*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*ALFAH*

*(the story of a wicked betrayal)*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

ByπŸ’•

*SURAYYAHMS*πŸ”₯



β–Ά4⃣6⃣








[18/03 3:35 am] SmsπŸ’•: *Bayan kwana hudu* nauman
Kaffa kaffa yake yi da ita kamr kwai alfah harta mance randa ta ma kanta wani Abu cikin kwanakin komai ya dauke mata kamr bawa haka ya kasance mata

abun tun yana ba sabreen haushi a boye har ta soma korafi akan yawan kulawa da nauman ke ba ALFAH

Sam baya bari wani ya bata wani abun daban in bashi ba
Musamman a gida ko office

Hakan ya sa suka dinga asarar magani da suka yi akan zasu sa ma ALFAH din cikin ya zube ita da suhaimah

Ranr Monday "Da murnan sa ya shigo office din tana zaune shiru tana duba wani site na pre natal"
Bin cike sosai takeyi akn yadda zata tafiyar da diet da wasu abubuwan muhimmai na mata masu sabon shigar ciki wato first trimester'

Kiss ya dan manna mata a goshi sannan ya dago ta sama daga kujeran ya rungume ta sosai a jikin sa

Baby na we did it....sun yi accepting shoots din mu cewar sa cikin murna da annuri cike da fuskan sa

Cikin murna ta ce dan Allah ?

Gyada mata kai kawai yayi alman eh
Nan suka dada rungumar juna suna hamdala
Ba tare da bata lokaci ba suka koma kan aiki

Kusan sati biyu kenan nauman ya toshe duk wata hanya
Da zai sa ALFAH ta jikita kota rabi wani aiki ko surutu bai son ana sata yi sosai

Sabreen abubuwa sun cunkushe mata don last time na magana tsakanin ta da shi tun ranar da suka ajiyeta a gida ne yace mata Allah ya kara sauki zaizo amma shiru

Har yanzu bai sake waiwayan ta ba ya sadaukar da lokacin sa da hankalin sa akan ALFAH da aikin da suke yi


Ranar laraba ta zo office din wanda yayi dai dai da ranar da zasu shiga hutun break na kwana biyu a aikin su na contract din

"Dan hira suka yi sosai da sabreen din a dabaran ce tace" ALFAH gobe ai ba zaku fito bako?

A'ah nikam zan fito gaskiya

Kin san nauman Yau zai tafi Lagos bana son na zauna full day nikadai gwara dai Nazo na kammala wasu abubuwan "

Gyda kanta tayi cikin ranta tace suhaimah tayi gaskiya " gobe zan wulakan ta ki kuwa
Zanga uban da zai hana ni kwabar da cikin nan

A haka suka rabo zUciyan sabreen fal da tunanin gobe ba nauman sai yadda sukayi da ALFAH da cikin ta

A gefen nauman kuwa cikin kwanaki yA gama sa ranar da zai Fada ma ALFAH gaskiyan lamarin sa da sabreen
Koda kuwa zata rabu da shi ne
Tafiyan ne ya daga masa hankali don' yagama shiryawa akan gobe zAi warwaree mata komai

Kamar da wasa da safe aka kira sa aka cancelling din tafiyar nasa ....
Sai dai koda ya shigo duba ta a dakin bai ganta ba note kawai tabar mai akan mirror

"Baban baby na..I'm sorry ban tsaya na sanar maka ba dad ne ya kirani forest resort wani karamin meeting I will be back"
Much love hubby"

Sauke ajiyan zuciya yayi yace perfect"
Na sami daman shirya komai yadda ya kamata kenan "

Mikewa tsaye yayi ya shiga ya hada mata duk abubuwan data ke so a rayuwa wanda yake gidan

Ya Sha kwalliyar sa ya zauna jiran ta zuciyar sa cike da fargaba da tashin hankali ya abun zai kasance


A hanya ita kadai take tafiya har ta isa kofar resort...
Iya kallon ta Bata ga kowa ba
Har ta soma daga waya zata kira taji ance ALFAH

Da mamakin ta ta juyo tace sabreen?
Dama kina nan kema ?
Nazo meeting ne da dad dazu naga sakon sa na e-mail

Sabreen bata gama bude baki ba su kaji bindiga akan su

Wasu maza ne sanye da mask bakake suka rife su su hudu

Cikin tsawa yace "
Duk wacce tayi motsi sai na harbe ta
Ku wuce cikin mota"

A wani katon bakar jeep aka jefa ALFAH da sabreen sunyi zuru zuru kowa hankalin sa a tashe

Tafiyar kusan awa da rabi kafin motar ya tsaya aka watsa musu wani Abu a fuska
Dukkan su suka sume sannan aka shigar da su wani gida


A wani kaskantaccen daki a ka dire su duka
Sannan aka ja kofar aka rufe gam

[18/03 3:35 am] SmsπŸ’•: Har wajen la:asar nauman bai ganta ba yasa shi soma Neman Layin ta ji akashe ya dada firgita shi

Ko ena ya shiga dubawa
Yana tambaya amma shiru"

Har ya kama ya nufi Office din alhj fadou
A yayinda sectery ya sanar masa da cewa ai
Alhaji fadoul baya nan dazun nan da safe ya tafi kasar China

What? Kace karfe 6 flight dinsa ya tashi
To wa ya tura ma ALFAH TeX karfe 8 saura akan sunada meeting da shi?

Cikin wani matsanan cin bugun zuciya yake nanata ennalillhi wa enna ilahi rajiun
ENA kika shiga ALFAH?

Hakan ya fuce kamar mahaukaci ya soma duba ta ko ena lungu da sako
Kusan isha'i baigan ta ba kuma wayar ta baya shiga

A mota ya kife kansa yana tsoron halinda zuciyar sa zata iya Shiga ciki Yau inbai same ta

Achn gidan kuwa A rakube da juna suka zauna
Alfah na faman share hawayen ta
Cikin kuka sabreen tace me muka muku?
Kubar mu mu tafi gida"

Nan alfah ma ta sa ki tana cewa" "''Emm dan Allah ku kyale mu "mu tafi duk abunda kuke so zamu Baku ku bar mu dan Allah na roke ku

Dariya suka fashe dashi wanda sai da duka gida ya dauka da sautin sa

"Cikin mugun tsawatar wa yace kashe ku kawai zan yi" bana bukatar kudi ko wani abu
Kar wata ta sake magana anan kuna jina da ..cewar sa cikin tsawa mai tsoratr wa

A tsorace suka gyada Kansu alaman sunyi shiru

Dan shiru wajen ya dauka kafin yace" Wace ce ALFAH acikin ku ? yana zare musu mugayen idanun sa

Murrya na bari tace nine?
Batare da bata lokaci ba
Kamo ta yayi da karfi ya Ce zo nan muje
Dake ZAmu fara

A xabure sabreen ta danko ta acikin wani irnin kuka

" dan Allah kar ka kashe ta ..ALFAH kar ki tafi ki barni pls tafada a rude suka rungumi juna suna kuka
Ko ajikin sa ya Shiga banbare su sai kuka suke musamman ma sabreen dan ALFAH ta kasa cewa komai sai addu:a take aranta tana kuka'

Haka ya janye ta da karfi yayi waje da ita"
Gidan duhu bata ganin gaban ta

Jim kadan taji ta awani daki da baida haske sosai

Nan ya jefa sai bari take yi bakin ta ya kasa buduwa don' tsaban firgici da tsoro
Shakuru wuyan ta yayi ya kure mata ido
Sannan yace inkina son kanki da lpya ki nutsu anan karki motsa ko ena"
Edan naji wani motsin ki anan
Bazan daga miki kafa ba sai dai kiji ki a lahira

Da Saurii ta gyda kanta tunanin ta tausayin ta yaji Yau bai kashe tan ba"

GAM ya kulle kofar ya fice
Kasa ta sulale tana faman kuka ..cikin ranta tace murad kazo ka taimake ni ..za su kashe ni" i don't want to die
Cikin kukan mai hade da razana har tayi bacci

Zazzabi ne mai zafi ya ke Neman shigar sa ....amma haka ya cigaba da tuki yana dada zagawa ko ena ko zai ganta
Ranan shikan sa bazai iya kirga kafar sa nawa yayi a forest resort ba'

A gefen sabreen kuwa
Dakin ta ta shige ta dauro wanka zuciyan ta fall da farin cikin game din
Sautin kukan ALFAH take tunawa sai ta fashe da wani shu'umin dariya "
"Dan tabe baki tayi tace hmmm" gaskiya shawaran suhaima tayi"ba yanzu Zamu kwabr da cikin nan ba"

Hahaha Kadan ma kagani
Bazan kira ka yanzu ba
Sai na dan dana maka azaba zuwa gobe mugani" bakai son haihuwa ba" da shi zan kara daure ka akan game dina har buri na ya cika

Daga Yau bazaka sake ke tare doka na ba ..ta karashe da wani mugun dariya

"A kasa ya zauna gefen cushion yana danne danne idon sa har ya soma haurawa kamar wanda ya bugu sosai

Muryan a dishe ya sake kallon pics din ta dake manne a gefe yace" wifey kar ki min haka pls come home to me"


Please Login or Register in order to submit comment