Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata tsananin ciwo, ta zauna tana ajiyar zuciya.

A sashin Amina kuwa, ta saka 'yan aiki sai sauke musu kaɓakin alkhairi ake yi na Abinci, aka yi ta kiran 'yan uwa da dangi ana sanar musu da haihuwa.
Fadila dai duk jikinta babu daɗi, saboda rashin samun karɓuwa a wurin mahaifiyarta.
Su Khalil ma suka ƙaraso gidan, suka tare a sashen Amina, sai hada-hada ake.
Yazid da Hajiya suka yi musu sallama a kan zasu je su dawo.
Fadila sai kallon Amina take, sai ƙoƙarin kyautatawa kowa take yi, yanda ta ke karrama Hajiyar Yazid kamar mahaifiyarta.
Hajara ma sai ɗorawa take tana saukewa, ana bawa wanda suka zo barka Abinci.
Da yawa maƙota sai a yanzu suka san an yiwa Fadila aure, su dai sun daina ganinta kawai.
Amina ta yi ta aikawa ana sanar da mutane haihuwar Fadila.

Da magariba sai ga Yusra a gidan, da Hajara ta haɗu a hanyar shiga main falon, ta kalli Hajara ta ce "Wai da gaske Fadila ta haihu Hajara?".

Hajara ta ce "Eh, tana sashin Amina".
Yusra ta ce "Amina kuma?" Da sauri ta shiga cikin gidan.

Saboda rabonta da Fadila watanni tara kenan ko a waya.

Fadila na ganin Yusra, suka saka ihu suka rungume juna, har da hawayensu na farinciki.

Yusra ta ce "Girl, dama da gaske auren aka yi miki? Mummy ta gaya mini amma na yi mamaki".

Fadila ta ce "Ke dai bari, nan da mutane sosai, zo mu je ɗakina"

Yusra ta ce "Ina abin da kika haifa ɗin?"

Fadila ta ce "Zo muje, kya dawo ki ganta daga baya".

Suka wuce ɗakin Fadila, suka nemi wuri suka zauna.

Yusra ta ce "Girl auren nan ya karɓeki, kinga yadda ki ka yi ƙiba kuwa? Amma ban so aurenki ya zo mana a haka ba, bani labari ya aka yi abubuwa suka zo a haka?"

Hawaye ne ya gangaro da ga idon Fadila, ta gyara zamanta da ƙyar, ta bawa Yusra labarin komai har zuwa yanzu.

Yusra ta waro ido ta ce "You mean Yazid Daddy ya aura miki? Ya aka yi ya san shi?".

"Amina ce ta saka ya aura mini shi, Yusra ina son Yazid sosai, faɗar irin alkhairinsa gareni ba zai faɗu ba, haihuwar nan tawa fa, leshin suna kawai na dubu Ashirin ya saya mini, 'yar nan da na haifa, baki ga kayan da ya saya mata ba, Yazid yana wahalta mini duk da ba shi da shi"

Yusra cikin mamaki ta gyara zama ta ce 'You mean Yazid dai shi ne mijinki Fadila?"

Fadila ta jinjina mata kai ta ce "Yazid ne mijina".

"Amma Fadila mun sha haɗuwa da Yazid, amma bai taɓa gaya mini kuna tare ba".

Fadila ta yi murmushi ta ce 'Ni na hana shi ya gaya miki, saboda Daddy ya ce kar mu sake wani ya san shi ne mijina, saboda kar Mummy ta sani, Yusra ina son mijina, amna Mummy ta ƙi karɓata ya juya mini baya".

Sosai Fadila ta ke kuka, Yusra tayi ta rarrashinta, Yusra ta dubi Fadila ta ce "Fadila na yi miki murnar auren Yazid, mutum ne nagartacce, mai kirki, Allah dai ya ƙaddara sai kun yi aure".

"Haka ne, ina laulayin cikin nan har wurinki na aiko shi, ya sai mini cake kika bamu kyauta"

Yusra ta ce "Allah sarki, ya ƙi gaya mini kuna tare, na sha kuka sosai rashinki bestyna".

Fadila ta dafata ta ce "Matar Abdul, yaushe ne bikin?"

Jiki a ɗan sanyaye Yusra ta ce "Wallahi tun muna tare nake jin nauyin sanar miki Abdul zan aura Fadila, saura sati biyu bikinmu".

Fadila ta ce "Kar ki damu Yusra, ai kin san ni ba son Abdul nake ba, amma na tayaki murna, dan halayensu na yanayi da na Yazid, Allah ya kaimu lokacin".

"Amin Fadila, wai abin har ya kai sai dai kiyi jegon a sashin Amina?"

Fadila ta rausayar da kai ta ce "Gashi kina gani, ko abin da na haifa ba ta gani ba, Yusra na yadda da zancen Amina, wallahi su Hajiya Turai suna ziga Mummy ne kawai suna cutarta"

Yusra ta ce "Kin san na daɗe da fuskantar hakan, magana me kawai ban yi ba dan kar ki ji haushi, wallahi Fadila yakamata ki ajiye duk wani kishi da tashin hankali, ki saka a ranki auren Daddy da Amina ta yi, Allah ya riga ya rubuta hakan, amma wallahi mai ƙaunarku ce, kuma abubuwanta ba ganin ido bane ba, kalli halin da take ciki, amma sai ɗawainiya ta ke yi da ke, dan Allah ki daina gaba da ita"

Fadila ta ɗan murza zoben hannunta ta ce "Nima na yi wannan tunanin, ba dan su Hajiya Turai ba da wasu abubuwan basu faru ba. Yusra a baya Jahilci ne yayi mini katutu na ƙarancim ilimin addini, zamana da Yazid ya sanya na gano abubuwa da yawa. Yusra baki ji labarin Yazid ba abin tausayi, amma nima na zo na dinga muzguna masa a makaranta, ba tare da tunanin ya zai ji a ransa ba.
Matar Yaya Khalil, ita ma baki ji nata labarin ba, amma ita ma muka sakata a gaba da wulaƙanci ina dana sani sosai a kan wasu abubuwan"

Yusra ta sharewa Fadila hawaye ta ce "Kiyi haƙuri, ai Allah mai afuwa ne, mu cigaba da yi wa Mummy Addu'a kawai"

Haka suka yi ta hira, sannan suka koma sashin Amina, Yusra ta ga jaririyar su Fadila.
Sai dai Fadila ta roƙi Yusra a kan kar ta gaya wa kowa a makarantar cewar ta auri Yazid.



Sosai mutane suka cika gidan Alhaji Ahmad, mutanen Dutse 'yan garin su Amina, duk suka cika gidan.
Sai dai duk wannan budurin, Hajiya Zainab bata ko fitowa, balle ta ga me Fadila ta haifa, hakan ya sake jefa Fadila cikin tsananin damuwa, tana farinciki idan ta ga mutanen da suka taru dominta, amma ta rasa kulawar mahaifiya, a kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Hajiya Zainab, bayan damuwar da take ciki, ciwo sai gaba yake yi, da ƙyar take iya fitsari, ga ciwon ciki da na baya.


Tun da Inno ta zo, ita ke yiwa jaririyar nan wanka, ta haɗa wa Fadila ruwan wankan jego, tamkar jikarta haka take kula da ita, hakan ya sanya jikin Fadila ya yi sanyi, da irin rashin mutuncin da ta ke yiwa Amina, duba da yadda mahaifiyar Amina ke ta mutunta ta da son 'yar ta.

Ga shi Hajiyar Yazid kullum idan zata zo, sai ta zo da Abinci fal nama, ta kawo wa Fadila, duk da ta san gidansu akwai.
Idan Amina ta yi magana, sai Hajiya ta ce "Ƙyaleta kuɗin mijinta ne".

Ranar suna ana ta shiri, Daddy ya kama musu babban hall da za ayi taron suna.
Kuma Yazid daidai gwargwado yayi ƙoƙari, iya ƙarfinsa.

Amina ce ta ga Fadila ta ɓuya tana kuka, babu komai a ran Amina ta dafa Fadila ta ce "Fadila kukan me kike yi?"

Fadila ta girgiza kai ta ce "Ba komai".

Amina ta ce "Na san ba zai wuce a kan abin da yake tsakaninki da mahaifiyarki ba, amma kiyi haƙuri mai wucewa ne, duk tsananin fushin da ta yi zata huce. Ki cigaba da yi mata Addu'a"

Cikin kuka Fadila ta ce "Cewa fa ta yi babu ni babu ita".

"Faɗa kawai take yi, amma zata sakko, ai tsakanin ɗa da uwa sai Allah"

Khalil ma yayi yinƙurin zuwa ya samu Mummy, a kan ta yi haƙuri ta sassauta fushin da take yi da su.
Amma ta ci mutuncinsa ta koreshi.

Ranar suna an ci an sha, aka sakawa yarinyar suna Khadija ana kiranta Hidaya, sai dai zancen duniya ba ya ɓuya, da yawa mutane sun samu labarin rashin saurarar 'ya'yanta da Hajiya Zainab ta yi saboda sun auri talaka, hakan ya sanya fa yawa mutane suka dinga Allah wadai da halinta ciki har da 'yan uwanta da suka zo suna.


Bayan suna jama'a suka watse, sai Fadila da Amina, da Dattijuwar da take yi mata wanka.
Amina tana daga zaune, har wanka take yiwa Hidaya.


Hajiya Zainab na zaune, a babban falo, jikinta babu daɗi su Hajiya Turai sun zo dubata, sai ga Fadila ta fito ita da Yazid, sai Khalil da Hafsa.

Fadila na ganin Mummy, jikinta yayi sanyi, ta nufi in da Mummy take hannunta riƙe da jaririyarta. Sai dai tana ƙarasawa ta yi wata uwar ƙara ta saki Yarinyar a ƙasa, ita ma ta faɗi ganin Hajiya Salma ta rikiɗe ta zama wata ƙatuwar mage.

Ƙarar da tayi sai da Daddy ya fito shi da Amina, saboda iya ƙarfinta ta yi, jarirriyar ta fashe da kuka.
Khalil ne ya ɗauki Hidaya, yana faɗin Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Hatta su Hajara sai da suka fito a gigice.

Yazid ne ya ƙaraso gareta cikin damuwa, ya ɗagota yana kiran sunanta.

Ruƙunƙume Yazid ta yi, tana wani irin kuka, sai karta masa farce take a wuyansa ta ce "Zid ka yi mini Addu'a zan mutu, Wata ƙatuwar mage nake gani fa".

A gigice Daddy ya yo kan su yana faɗin, Me ya sameta?"

Hajiya Zainab kanta saukowa ta yi daga kan kujera ta yo kan Fadila.

Yazid ya ɗaga kai ya ƙurawa su Hajiya Turai ido, sai jikin Turai ya fara rawa, ya kalli Hajiya Salma ya ce "Hajiya Salma ko?"

Da mamaki ta kalli Yazid ta ce "Lafiya, a ina ka sanni?"

Yazid ya ce "Ban sanki ba, amma kamar yadda na bada saƙo a gaya miki, kika yi burus yau Allah ya kawo ƙarshen ku, da abin da kuke yi"

Daddy ya ce "Yazid menene? Kayi mana bayani" Fadila dai sai tura kanta take a ƙirjin Yazid, jikinta na rawa.

Yazid ya ɗan zame rigarsa, ya nunawa Daddy wuyansa zuwa kafaɗarsa, wurin tamkar an tsatsaga masa da reza.
Ya ce "Daddy, tun bayan aurena da Fadila, baifi da watanni uku ba, kusan bama bacci da daddare, kwana nake yi mata Addu'a, wannan raunin na jikina duk ita take yi mini.
Duk da zancen aljani mafi yawa ƙarya ne, amma sun tabattar da Hajiya Salma ce ta turo mata su".

Salati suka ɗauka, Hajiya Salma ta fara kumfar bakin za ayi mata sharri.

Yazid ya kalli Hajiya Turai ya ce "Ƙarya na yi?" Ta sunkuyar da kai ta ce "A'a, tabbas muna yiwa Hajiya Zainab asiri. Tun bayan haɗuwarmu da ita, duk mijinta yafi namu kuɗi, muka fara koya mata bin bokaye, dan ta mallake shi.
Sai dai tana da rowar tsiya, dan haka ita ma muka fara kai sunanta wurin malamai, aka bamu wata laya aka jefa a tsohuwar rijiya, ya zamana ba ta jin maganar kowa sai ta mu, kuma duk abin da muke so ta bamu zata nemo ta bamu.
Ana haka aurena ya mutu, na yi ta ƙoƙarin na samu na auri mijinta, amma ya ƙi, ba asirin da ban yi masa ba, amma abu bai yiwu ba, na koma zaman Saudiyya.
Hajiya Salma ma ba yadda ba tayi ba, a kan ta samu ya auri ƙnawarta ba nan ma ba nasara.
Sai daga baya na haƙura mijina ya mayar da ni.
Bayan Alhaji Ahmad yayi aure, muka yi amfani da wannan damar, muna kaita karɓo asiri, ana kuma asirce mana ita. Aka karɓo maganin da za a zubar da cikin abokiyar zamanta Amina, amma mu idan cikin ya zube, za a sadaukar wa da wani aljani jinin yayi mana namu aikin.
Sau biyu muka yi nasara kawai, bokan ya sanar mana, Amina ba zata taɓu ba sai dai ayi ta amfani da makirci a kanta.
Muka ɓullo da batun haɗa Khalil aure da 'yar ƙanwar Hajiya Salma, da nufin idan suka haihu, sai a kashe Khalil, amma Abin bai yiwu ba.

Muka bijiro da zancen, auren Fadila da ɗan Hajiya Salma, shima duk dan muyi yadda zamu yi mu tatsi kuɗi sosai a hannunku, muka dinga zuwa muna yin asiri a kan ta so Salim, amma abu ya ƙi ci, ƙarshe muna tsaka da wani aikin a kanta, sai ji muka yi an aurar da ita.

Muka dinga yi mata turen aljanu a kan duk in da take ta dawo, ta bijire akan lallai sai ta auri Salim, amma abu ya gagara.
Bokaye suka ce babu aure a tsakanin ta da Salim.
Kasancewar Hajiya Zainab, bata da abin so kamar Fadila, sai muka zaɓi haukata Fadila, saboda mu ƙuntata mata, dan har ga Allah muna hassada da ni'imar da ta fi mu.
Shine muke ta tura mata aljanu, idan aka ce an ƙona wasu sai mu sake biya a tura wasu, kuma galibin kuɗin da muke bayarwar, a hannun Hajiya Zainab muke karɓarsu. Dan Allah ku yafe mana, yanzu haka wani irin zugi nake ji a jikina, kamar zan haukace, ku yafe mana dan Allah".

Amina fashewa ta yi da kuka, jikinta ya ɗau wata irin rawa.

Fadila cikin kuka ta ce"Mummy, ashe Zaki iya zuwa wurin bokaye a cutar da wani, gashi nan abin ya ƙare a kanmu, har da wanda bai ji ba bai gani ba, Yazid yafi ƙarfin wattanni baya rintsawa, tamkar zan haukace, haka na dinga faɗuwa da tsohon ciki Mummy Why?"

Khalil kansa jikinsa rawa yake yi, sosai hawaye ke zuba daga idon Daddy.

Ya ce "Ku je dan kanku, Allah ne kawai zai saka mini cutarwar da kuka yi mini, na barku da Allah.

Sosai Amina jikinta ya cigaba da rawa, Daddy ya ɗagata ya ce maza Khalil ya je ya fito da mota.

Hajiya Zainab kuwa ɗora hannu ta yi a ka, ta fashe da kuka tana nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un, kun cuceni Allah ya isa ban yafe ba".

Ganin ba abin da aka yi musu, ya sanya sum-sum, Hajiya Turai da Salma suka fice daga gidan.

Hafsa kuwa zuruuu ta yi, abin yana ɗaure mata kai.

Kuka Mummy take tana wani irin gunji, ba ta taɓa zaton su Turai za su yi mata haka ba.

Fadila da ta ɗan farfaɗo tashi ta yi ta ce wa Yazid ya bar falon da ita.

Hafsa ta ɗau jariran, ta bi bayansu.

Tare da Hajara aka tafi kai Amina Asibiti, Daddy ba magana sai kuka kawai.

Suna zuwa Asibiti, aka ce cs za a shiga da Amina da gaggawa, dan jininta ya hau ba za a bari ta yi naƙuda ba.

Nan da nan Khalil ya ɗau Hajara suka dawo gida, ya sanar da su Fadila abin da ake ciki, aka kwashi kayan Amina na haihuwa suka nufi Asibiti.
Daddy ya ce ba za a kira su Inno ba, sai an gama aikin.
Awa ɗaya da rabi, aka fito da jarirai maza biyu, an yi mata aikin.

Daddy sai ya rasa me zai yi, Amina firgici ne ya sanya jininta hawa, ga baƙin ciki ga farinciki.

Ba wanda ya kuma bi ta kan Hajiya Zainab, sai magariba, ya zo ya tarar da ita a sume a sashinta.
Hankali a tashe ya ɗauketa zuwa Asibitin da Amina take, sai dai babu wanda ya san musababbin suman nata.


Hajiya Turai da Salma kuwa, suna tafe a motar Hajiya Salma, suna faɗa, tana yiwa Turai masifar dan me zata tona musu Asiri.
Aikuwa Turai ta hauta da bala'i, tana cewa bata san me take ji a jikinta bane, ji ta yi idan ba ta faɗa ba zata mutu.
Suna wannan masifar, Tirela ta taho, garin su kauce mata motar ta kifa, Hajiya Turai ko shurawa ba ta yi ba.

Ahalin Daddy da basu san wainar da aka toya ba, sai labarin haihuwa da suka ji, suka yi ta murna suna cewa arziƙi ya sauka a gidan Alhaji Ahmad.

Khalil ne yake zuwa duba Mummy, Sai Yazid.
Yazid ya yi ta yiwa Fadila faɗa a kan lallai kar ta ce zata ƙullaci Mummy, dan ba wanda baya kuskure a rayuwa.

Da Hajiya Zainab ta sake farkawa, ta ga Fadila da Yazid, ga Hafsa ga Khalil a tsaye a kanta, sai ta fashe da kuka tana faɗin "Dan girman Allah ku yafe mini, kuma ku rufa mini asiri, ina miji na in nemi yafiyarsa ina Amina, ashe abin da take gaya mini gaskiya ne, Fadila ku yafe mini".

Yazid ya ce "Mummy duk sun yafe miki, Daddy ma zai zo wurinki in sha Allah, Amina an mata aiki ta haifi yara maza biyu"

Ta kalli Yazid ta ce " Ɗan nan dan Allah ku yafe mini, na san ba zan tsawon rai ba, likita ya tabattar mininda shaye-shayen magungunan hausa barkatai da na dinga yi, wanda ban san da me aka haɗasu ba ya sanya ƙodata ɗaya ta gaza, dan Allah ku yafe mini, kar na mutu da hakkinku".

Fadila ta fashe da kuka, ta rungume Mummy, tana Cewa "Mun yafe miki Mummy, ba zaki mutu yanzu ba, dan Allah ki daina faɗar haka".

Fadila ta tashi da sauri, ta koma ɗakin da Amina take kwance, Daddy na zaune a gefe, da jarirai a hannunsa. Fadila ta zube a gaban gadon Amina ta riƙe hannun Amina ta ce "Dan Allah Amina ki yafe wa Mummy, kin san wani abun ba laifinta bane ba, Daddy dan Allah ku yafe mata, likitoci sun tabattar da Mummy ta gamu da renal failure".

Waro ido suka yi gaba ɗaya, Amina duk da halin da take ciki sai da ta tsure ta ce 'Ciwon ƙoda kuma?"

Fadila ta jinjina kai tana kuka. Tashi Daddy ya yi ya fita, dan tun da aka kawo Hajiya Zainab bai leƙa ya ganta ba, saboda ya sha mamakin abin da ya ji ta aikata ba tare da ta musa ba.

Yana zuwa ya tarar da ita, ta rirriƙe Khalil tana kuka.

Tana ganin Daddy ta saki Khalil, tana miƙawa Daddy hannu tana kuka.

Daddy ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, ya kalleta ya ce "Wane likitan ne ya ce kina da wannan ciwon?"

Cikin kuka ta ce "Likita ba zai yi ƙarya ba, ƙodata ɗaya ta samu matsala, Ahmad na san na cutar da kai, dan Allah kayi haƙuri na san ba zan yi tsawon rai ba, na yi dana sanin abubuwan da na aikata, dan Allah ka yi haƙuri Ahmad ka yafe mini".

Daddy ya dubi Khalil ya ce "Ka je ka zo mini da likitan da yake dubata".

Jiki a sanyaye Khalil ya fita daga ɗakin, kasancewar Amina ta fara takawa, dan kwanaki uku kenan da yi mata Cs, hankali a tashe ta shigo ɗakin da Mummy ke kwance ta riƙa hannun Daddy tana kuka, amma ya ƙi magana sai Hafsa da Yazid da kuma Fadila.

Amina ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin "Sannu Hajiya, wai ciwon ƙoda ni ai ban san a nan Asibitin kike ba".
Duk da wani irin kishi da yake tasowa Hajiya Zainab, a kan Amina, amma ta ga ƙoƙarin Amina da ta zo dubata.

Likita ne ya shigo, suka gaisa da Daddy, Daddy ya tambayeshi meke damun matarsa.
Nan likita yayi masa bayanin cewar, magunguna da take sha ba bisa ƙa'ida ba, ya sanya ƙodarta ɗaya ta taɓu.
Amma idan aka bi ƙa'idojin da zasu saka, zata iya rayuwa da guda ɗaya.

Hajiya Zainab ta riƙo hannun Amina ta ce "Ba wani tsawon rai da zan, ni na san mutuwa zan yi, dan Allah ki yafe mini, na san kema na cutar da ke, ki kuma saka baki ya yafe mini dan Allah".

Amina ta kalli Daddy ta ce "Daddy, dan Allah do something, dan Allah ka yafe mata.
Fadila ma kuka take yi sosai da sosai.

Daddy ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, Allah ya bata lafiya, ni yanzu fatana ta samu lafiya Allah ya yafe mana baki ɗaya".

Yazid ne da suka bashi tausayi, ya ce "Allah ya saka da alheri Daddy, Allah ya ƙara girma.

Fadila ta rungume Daddy tana yi masa godiya.

Ita ma Hajiya Zainab godiyar ta dinga yi, ta ce "A bani jariran na gansu, Hafsa ku yafe mini dan Allah"

Hafsa ta ce "Bakomai Mummy" cikin murmushi ta sauko da jaririyar ta miƙawa Mama, Fadila ma ta ce Mummy bari na karɓo miki Hidaya ma.

Ta fita da sauri, ta koma ɗakin da aka kwantar da Amina, Inno tana goye da Hidaya, Hajara kuma na bawa jariran madara.

Fadila ta ce "Inno, Mummy ce zata ɗau Hidaya"

Inno ta yi murmushi ta ce "To muje in sake duba jikin nata".


Fadila ta ce "Yauwa Hajara taho da 'yan biyu ma".

Haka suka ɗunguma zuwa ɗakin da Mummy take.

Duk suka jere mata yaran, tana kuka ta dinga shafa kan yaran tana kuka tana su yafe mata.

Amina ta ce "Hajiya dan Allah ki daina kuka, komai ya wuce tun da dai kin fuskanci gaskiya, Allah ya yafe mana baki ɗaya ya baki lafiya".


Gaba ɗaya jikin Hajiya Zainab yayi sanyi, duk motsi ta dinga neman afuwa kenan.

Mutanen da suka sake dawowa sunan Amina, sun yi mamakin ganin Hajiya Zainab duk ta rame tayi sanyi.
Ammi su Hajiya Maryam, da Azima da 'yan makarantar su Amina duk sun zo suna, kuma sun yi wa Amina alkhairi.



Hajiya Salma dai, ba ta mutu ba, sai dai lakarta ta taɓu, ba zata iya yiwa kanta komai ba, sai dai a kwantar a tayar.

Bayan sunan jariran Amina, Fadila ta ce zata koma gida, dan jikin Mummy ma da sauƙi sosai da sosai.

Amina ta cigaba da lallaɓa Daddy, tana nuna masa Cewar Hajiya Zainab ta saduda, dan haka yayi haƙuri komai ya wuce.
Allah ya sa Amina ta shawo kan Daddy, ya biya kuɗi aka fita da Hajiya Zainab Indiya, domin cigaba da kula da lafiyar ta.

Daddy ya bawa Yazid aiki a kamfaninsa da zai buɗe na kwangila a Kano.
Yazid dai ya karɓa ne kawai, amma ya barwa kansa cewa zai cigaba da lalaubawa idan ya samu wani aikin zai tafi, baya son ace Daddy ya dinga yi masa komai, dan yana auren 'yar sa.
Still Daddy ya kuma bawa Abdul aiki a kamfanin, dam ba zai manta alkhairin sa ba shima, a lokacin ya auri Yusra ma.

Babban muƙami Daddy ya bawa Yazid, ga zuwa makaranta, Yazid ya zama busy sosai, ya nemawa Fadila School of Nursing, cikin ikon Allah kuma ta warke daga ciwon iskokai.

Baba Uwani kuwa, matar Baban Yazid ita ma ta rasu tuni, amma Yazid bai yadda ya yanke alaƙa da 'yan uwansa gaba ɗaya ba.


Bayan Hajiya Zainab ta dawo daga indiya, jikinta yayi kyau sosai da sosai.
Daddy ya sakata a gaba, zuwa Dutse ta dinga bawa mutanen da ta ɓatawa haƙuri ciki har da danginta.

Ta yi nadama sosai da sosai, tayi mamakin zaluncin da su Hajiya Turai suka yi mata.

Tana ji tana gani dai, Amina ta ƙwace mata gida, sai abin da Amina ta ce shi ake yi, sai dai Aminan na iya ƙoƙarin ta wurin yi mata adalci.
Abubuwa suka ƙara yiwa Amina yawa, ga 'yan biyu watanninsu takwas ta kuma samun ciki, an sha daru sosai dan cewa ta yi zubarwa za tayi, ita ga karatu, ga kula da yara ga kuma ciki.
Sai da Daddy aya zazzare mata ido sannan ta haƙura, ga laulayi ga makaranta, dan ma Kusan kodayaushe twins suna wurin Hajara ko Hajiya Zainab.
Ganin yaran na ɗebe mata kewa, Fadila ma ta zo ta dire mata Hidaya ta tafi makaranta, suka mayar da ita tamkar Nanny.



Mijin Hajiya Salma ya tsallake ya je yayi wani auren ya barta, ɗanta Salim ya tattara ɗan abin da take da shi, ya dinga facakarsa, suka barta a wahala ga jinya.



Bayan Yazid ya kammala makaranta, ya samu scholarship a Saudiyya, a lokacin Fadila ta gama school of Nursing ita ma, ya tattara ta da 'yarsa suka bar ƙasar. Cikin ikon Allah yana karatu a ƙasar ya samu aiki, ya sake mayar da Fadila makaranta, ya buɗe wa Hajiyarsa wurin sana'a a Nigeria.


Sai da suka shekara Bakwai a Saudiyya, sannan suka dawo Nigeria, Fadila ta kuma haihuwar ɗa namiji, Amina kuma ta kuma haifar maza biyu da mace ɗaya.

Yazid ya samu alkhairi sosai zamansu a Saudiyya, ya dawo ya samu aikin yi a Nigeria, ga gefe guda Daddy na ta sake janyo shi cikin harkokinsa, dan so yake ya sakar musu shi da Khalil shi kuma ya huta.


Kwatsam an gayyaci su Yazid za su yiwa wasu malaman jami'o'i wurin screening, waɗanda za a tura su wani course ƙasar waje.
Babu tsammani har da Kankiya a cikin waɗanda Yazid zai tantance, Kankiya ya rikice, ya ƙadarra Yazid ba zai bari yayi nasara ba, amma ya ga Yazid ya girmama shi, yana nuna wa abokan aikinsa ai wannan malaminsa ne.
Kankiya duk kunya ta kama shi, ya dinga neman yafiyar Yazid, a nan Yazid ya sanar masa ya auri Fadila har da yara.
Kankiya ya taya shi murna sosai, Yazid ya yi masa tantancewar sa cikin mutunci da girmamawa.


Haka rayuwa ta cigaba da gudana, dukkanin ahalin suka cigaba da rayuwa cikin farinciki, sai dai Hajiya Zainab ta ƙarasa rayuwarta tamkar mujiya, dan Mutane ba su daina zunɗenta da bada labarin mugun halinta ba.



TAMMAT BIHAMDILLAH, ALHAMDILILLAH, ALHAMDILILLAH, ALHAMDILILLAH.

A NAN NA KAWO MUKU ƘARSHEN WANNAN LITTAFI, NA GABA DA GABANTA.
INA JINJINA TARE DA MIƘA SAƘON GODIYA TA GA MASOYAN ALƘALAMIN AYSHERCOOL BARKA DA JUMURIN BIBIYAR LITTAFINA.
JAMA'ATA NA WHAT'S APP, MUTANEN AREWABOOKS, WANDA SUKA BANI KYAUTAR DATA DA SAURANSU

Please Login or Register in order to submit comment