Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cirr, shi Yazid ji yake kamar a kan ƙaya yake, duk a takure yake, amma ita yadda suke nuna mata soyayya da karamci ya sanya ta ji bata son rabuwa da su.

Da suka tashi tafiya kuwa, Fadila ta samu alkairi sosai da sosai, kakar Yazid har da kukanta wai yaushe za a dawo mata da Fadila, ita dai tana son Fadila.
Yazid ya ce mata zasu sake dawowa in sha Allah.

Ita kanta Hajiya, ta ji daɗin Yadda Fadilan ta dinga nuna wa mahaifiyarsu kulawa, dan duk wanda ka nuna kana son mahaifinsa ka gama masa komai.

Suka shiryo suka nufo Kano. A sati biyun nan kuwa, Mummy ba ta fita ko ina, tana zuba idon ta ina za a kawo mata Fadila, amma ta ji shiru, haka ta cigaba da mita tana matsawa Daddy a kan ya cika alƙawari.

Su Fadila suka dawo gida lafiya, tana ta jin daɗin karamcin da dangin Yazid suka nuna mata.

Sai dai gidan su duk yayi ƙura, Yazid ya zage ya gyara gidan, dan Fadila kwanciya tayi ta ce ita a gajiye ta ke.

Ta huta ta dinga firfito da kayan tsarabar da aka bata, tana ta murna amma taga Yazid yana hararata.

Ɗan tsuke fuska ta yi ta ce "Me na yi maka?"

Ya ce "Ban sani ba, ƙememe ki ka yi zamanki wai ke ba zamu dawo gida ba a kan lokaci, ki ka sa sai da muka yi sati biyu, ke ko tunanin kina da miji ba kya yi ko?"

Tura baki ta yi ta ce "To me zan maka?"

"Au haka ma zaki ce ko?"

Ɗaga masa gira ta yi, tana saka mazarƙwaila a bakinta.

Yazid ya ce "Allah ya shiryeki, kuma gobe in Allah ya kaimu da safe zamu je Asibiti ki fara antenatal"

Ta ce "To ɗan ustazuna, na ga dai haushina ka ke ji, kayi haƙuri ka ji masoyin"

"Ba wani masoyi, kawai daga zuwa ziyara kika shantake"

"To idan muka dawo kai zaka dinga samo mini madara da zuma ne? Ko zaka dinga ba ni naman nan me daɗi"

"Kwaɗayayyiya dama kwaɗayi ne ya zaunar da ke, salon ace bana ba ki Abinci, a nan komai na sayo miki ko na dafa miki, sai ki ce ke ba kya so".

"Eh naji kwaɗayayyiyar, ni dama ka mayar da ni"

Yazid ya ce "Tashi ki koma sai kin dawo".

Washegari Monday, Yazid yana ta so Fadila tayi ta shirya su tafi, amma ta tsaya a gaban mudubi, tana ƙarewa kanta kallo.

"Zid da na yi ƙiba nafi kyau ko?"

Yazid ya ce "Eh, ta yi miki kyau sosai"

"Kenan dama baka san siriryar mace?"

Tasowa Yazid yayi, ya karɓi kayan ya fara saka mata, dan idan ya biye mata yau ma ba za a fara zuwa awon ba.
Amma a hakan mita ta cigaba da yi, ashe dama kallonta kawai yake baya sonta saboda ba ta da ƙiba.

Ya rakata Asibiti, aka yi mata duk abinda yakamata, sannan suka taho gida, sai dai duk ta ga jikinsa a sanyaye.
"Ɗan ustazuna, meke damunka, na ga kayi wani iri, ko ni ce na ɓata maka rai?"

Ya ce "A'a, baki yi mini Komai ba, Daddy ya ce zai turo a ɗauke ki"

"A ɗaukeni a kaini ina?" Ta yi maganar tana kallonsa.

"Gida za a kai ki, fatana Allah ya sa ki dawo"

Haka nan ita ma sai ta ji tana fargaba. Rungumo shi ta yi a jikinta ta ce "Babu abin da zai faru in sha Allah, ina sonka Zid sosai babu abin da zai rabani da kai da yardar Allah, muje ka rakani ma sai mu dawo tare".

Yazid ya ce "A'a, Daddy ya ce ba tare zamu je ba, yanzu idan mun ƙarasa masu ɗaukarki suna titi suna jiranmu"

Shafa kansa ta dinga yi a hankali ta ce "Ka kwantar da hankalinka, ba wata damuwa in Allah yarda"

Haka suka ƙarasa titin unguwar su, unguwar da har yau Fadila ko sunanta ba ta sani ba, suka tarar da zuƙeƙiyar mota mai tint.

'yan sanda ne guda biyu a motar, suka ƙarasa gaban motar, suka gaisa da Yazid, ta buɗe motar ta shiga, gaba ɗaya sai tausayin Yazid ya kamata, ta dinga ɗaga masa hannu, shima jiki a sanyayen yake ɗaga mata hannu".
Bai san dalilin ɗaukar Fadilan da Daddy ya turo ayi ba, dan bai yi masa cikakken bayani ba.

"Allah ka sa su dawo mini da matata". Ya tafi gida yana ta Addu'a cike da fargaba!




Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA DOMIN YA SAYA.
08081012143

84



Gaba ɗaya jikin Yazid yayi sanyi sosai da sosai, ya kasa sakewa yayi ta tunani daban daban a ransa, ya fara addu'a Allah ya taimake shi ya sanya Fadila ta dawo gareshi.

Sun ɗan yi tafiya mai nisa, sam Fadila bata gane kan hanyar da ake bi, sai dai ganinsu ta yi a gidan Daddy.
A ƙofar gidan suka tarar da Daddy, zaune a cikin mota shi da Amina, ɗan sandan ya kalli Fadila ya ce "Ranki ya daɗe ga Alhajin can"

Fadila ta buɗe motar ta fita, ta nufi wadda su Daddy ke ciki, Amina ta ɗan ƙura mata ido, Fadila sai cukuikuye hannu take a cikin hijjabinta tana ɓoye cikin.

Duk da ta yi farinciki da ganin Daddy, amma tana ganin sa tare da Amina, ranta ya ɓaci, ta tuna irin auren wulaƙancin da aka yi mata. A hankali ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga ta zauna, sannan ta ce "Daddy ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ya mai gidan na ki?"

Fadila ta ce "Yana nan lafiya"

Shi kansa Daddy yayi mamakin yadda Fadila tayi ƙiba, dan a yadda take ba zaka taɓa cewa zata yi ƙiba ba.

Ba wanda ya kuma kulata a tsakanin shi da Amina, dama Fadilan ma ba ta kulata ba.

Daddy cikin tsuke fuska ya ce "Zan kai ki gida kiga mahaifiyarki, amma muddin kika kuskura ki ka yi wani misbehaving, matakin da zan ɗauka ba zai miki daɗi ba, kuma ban yarda ki gaya mata waye mijin da na aura miki ba" bai jira mai Fadila za ga ce ba ya ba motar suka bar wurin.

Suna tafe suna hirarsu shi da Amina, Amina na ta cin dubulan, duk da yadda Fadila ke jin kamar ta jefa Amina waje dan haushinta take ji, amma zuciyarta ta dinga raya mata ta roƙi Amina ta sanmata dubulan ɗin nan saboda ranta ya biya. Amma ta dake ta daure ta kawar da kanta gefe.

Daddy ya na son yayi wa Fadila hira, ya yi mata tambayoyi saboda ba ƙaramin kewarta ya yi ba, amma yana gudun aikata hakan, azo a samu matsala daga baya.

Ko da suka shigo layinsu, gani take tamkar ta yi shekaru masu yawa rabonta da layin, hatta gidan ma duk yayi mata wani iri.

Daddy na yin parking ta a fito jiki na rawa, ta nufi cikin gidan da sauri, har da tuntuɓe, tausayinta ya kama Amina.

Ta kalli Daddy ta ce "Allah sarki, Allah ne kaɗai ya san yadda ta rayu tsawon wannan lokacin ba tare da gani ko kiran mahaifiyarta ba, gaskiya ta cancanci yabo, ta yi haƙuri kuma ta yi biyayya"

Daddy ya yi murmushi ya ce "To lawyer, amma koma dai meye ai ba a wahala take ba, kalli yadda ta koma fa"

Amina ta ce "Haka ne, amma duk da haka gurbin uwa daban yake".

Ita kuwa Fadila da gudu ta ƙarasa sashin Mummy, ko nauyin cikin bata ji, a falon Mummy suka haɗu, Fadila ta faɗa jikinta tana kuka.
Rungumeta sosai Hajiya Zainab ta yi, ita ma ta fashe da kukan.

"Fadila, ina ya kai mini ke tsawon wannan lokacin, da kika kasa ɓallowa ki dawo gida, hankalina duk a tashe ban san in da kike ba, na shiga damuwa sosai"

Fadila ta ɗago tana faɗin "Mummy, babu yadda za ayi na iya zuwa, ya ce idan na zo bai nemeni ba bai yafe ba, ni kaina na yi kewarki Mummy".

Gani ta yi Mummy tana ƙare mata kallo, daga sama har ƙasa, ta miƙa hannu ta janye hijjabin Fadila, sai ga ciki ya fara tasawa"

Waro ido Hajiya Zainab ta yi ta ce "Fadila da gaske aure yayi miki? Shi ne har kika yadda ki ka yi ciki, a garin yaya ki ka samu Ciki Fadila?"
Fadila ta yi shiru tare da sunkuyar da kai ƙasa.

"Sannin yadda aka yi ta samu ciki ba huruminki bane ba, tun da dai aurar da ita na yi, ba wai sakinta na yi a duniya haka ba" suka jiyo muryar Daddy, Hajiya Zainab ta kalli in da Daddy ke tsaye, Fadila kuma ta sunkuyar da kai kamar mara gaskiya.

Cikin takaici Hajiya Zainab ta ce "Amma ta yaya mutane zasu yadda aure ta yi, bayan babu wanda ya san da hakan?"

Daddy ya ce "Ai ba dole ne sai kowa da kowa ya sani ba, tun da mun cika sharaɗin abin da Addini ya tanada, gata nan zuwa yamma zan mayar da ita"

Jin Daddy kawai Hajiya Zainab ta yi, dan ba ta ga abin da zai sa ta bari ya sake ɗauke Fadila daga gabanta ba.

Ya juya ya fita ya bar ɗakin, jan Fadila ta yi zuwa ɗakinta, ta rufe bedroom sannan ta kalli Fadila ta ce "Fadila, wai ɗan gidan wa ma ya aura miki ne?"

Jiki a sanyaye Fadila ta girgiza kai ta ce "Mummy ba ɗan kowa bane ba, ba shi da komai sai Allah, amma ban rasa ci ba ban rasa sha ba da abin da zan saka jikina"

Mummy ta ce "Ke! Wai yana ga kina acting kamar kina son auren, bayan auren dole yayi miki, a ina mijin yake kuma waye shi?"

Fadila ta ce "Mummy ko na gaya miki ba zaki gane shi ba".

A hasale ta ce 'Ke dalla ki mini bayani a ina yake, mara tunani da ga zuwa kin ƙunso ciki kamar abin da kike jira kenan, ke ko kishin kanki ba kya ji kuma ba kya tausayina, maimakon ki ɓallo ki gudo amma kika miƙe ƙafa, har da ɗaukar ciki, to bari ki ji na gaya miki, ba in da zaki koma daga nan, kuma wannan banzan cikin sai an zubar da shi. Wato saboda dai ya nuna mini ban isa ba, shi ne ya aurawa Khalil 'yar talakawa ya rabani da shi, kema ya samo wani wahalallen ya aura miki, dan cin zarafi, to bai isa ba yayi kaɗan ba in da zaki koma".

Fadila ji ta yi tamkar ta cewa Mummy, dan Allah ta ƙyaleta tana son aurenta, amma ta yi shiru, dan kar su ɓata.

Hira suka dinga yi, Mummy na cigaba da alwashin sai ta wulaƙanta Amina kamar yadda ta kassara mata iyali, kuma ko ta tsiya sai ta kashe auren da aka yiwa Fadila.
Ita Fadila hankalinta yana can kan Yazid, ba ta san a wani hali yake ba, ta san shi da saurin rikicewa, ta kasa manta yadda ta ga fuskarsa ta sauya da zata tafi.

Ta tafi ɗakinta, ta je ta yi wanka, ta saka wasu kayan, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta, ita kanta ta san ta yi ƙiba sosai ta yi murmushi ta ce 'Su ɗan ustazuna an iya raino, duk na yi ƙiba" sai kuma ta shafi cikin jikinta ta ce "Allah ya kawo mini abin da ke cikin nawa lafiya, ina son na ganka amma Mummy ta fara iƙrarin rabani da kai"

Duk da yadda ta so ta zauna su yi hira sosai da Mummy, amma ta kasa saboda baccin da take ji, ga sauran gajiyar hanya na tafiya Jalingo da suka yi.

Hajiya Zainab kuwa ta kasa ta tsare, tana tunanin yadda za ta yi da cikin Fadila, da kuma shirin ko ta kwana a kan sai dai su yi wadda za su yi ita da Alhaji Ahmad, amma ba zata taɓa bari ya kuma ɗauke mata Fadila ba.

Sai la'asar Fadila ta tashi, Hajiya Zainab ta shirya mata Abinci, Fadila ta kalli Mummy ta ce "Mummy ni bana son wannan Abincin, idan na koma gida na san Hajiyarsa ta aiko mini da tuwo, ni yanzu da zan samu ƙosai ne ma dai da sauƙi"

"Ke dalla can rufe mini baki, sai ka ce wani cikin arziƙi to bari ki ji na gaya miki, sai kin rabu da cikin nan, maza ɗau Abinci ki ci".

Fadila ta ce "To bari na yi salla"

Bayan ta yi salla kuwa, ficewa ta yi ta tafi Kitchen, ta tarar Hajara na ta aiki, Hajara ta gaisheta cikin girmamawa, ta amsa mata ba yabo ba fallasa, ta nufi Fridge.
Hamdala ta yi da taga manyan mangwaro a ciki, ta zauna ta dinga sha kamar mayuwanciya, sannan ta baro Kitchen ɗin.

Sashinta ta koma, ta sake tattaro abin za take buƙata na kayan ta, ta haɗe wuri guda ta kai su falo ta ajiye.
Sannan ta koma wurin Mummy, ɗan kaɗan ta ci Abincin, Fadila na son yin hira da Mummy, amma Mummy ban da zancen kashe mata aure da zubar da ciki babu abin da take yi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Wani hali Yazid zai shiga idan aka kashe auren nan, aka kuma zubar masa da ciki, za a sake jefa shi cikin damuwa.

Fadila ta ce "Mummy, mijina maraya ne rayuwarsa akwai abin ban tausayi....

Kan ta ƙarasa Hajiya Zainab ta ce "Eh, kema na ki uban na ƙoƙarin mayar da ke marainiya ba, kuma mara amfani da ba ta san ciwon kanta ba, ni gani nake ke murna ma kike yi da auren da aka yi miki ko?" Fadila ta yi shiru ta sunkuyar da kai.

Biyar da rabi, sai ga Daddy a sashin Mummy, yana kiran Fadila, Fadila ta amsa ya ce "Maza ta so muje na mayar da ke"

Miƙewa Hajiya Zainab tayi ta ce "Babu wannan maganar, ai kuma ta zo kenan, ba ka isa ba fa"

Daddy ya kalleta ya ce 'Haka muka yi da ke?"

"Da ka tashi aurar da ita, ni wace yarjejeniyar muka yi? Babu in da zata, ta zo kenan ba zan yadda ka sake rabani da ita ba, ban san in da zaka kai ta ba"

Daddy ya ce "Babu in zan kai ta sai ɗakin mijinta, kuma da gani kema kin san ba a wahala take ba, dan haka kar mu zo muna jayayya da ke, har ta kaimu ga ɓacin rai".

Cikin rashin girmamwa ta ce "Ta daɗe ba ta kaimu ga ɓacin ran ba, wallahi babu in da zata je".

Daddy ya kalli Fadila ya ce "Ke kin san yadda muka yi, dan haka ta so mu tafi"

Aikuwa Fadila ta miƙe, ta yafa mayafin jallabiyarta ta nufi in da Daddy yake, dan yanzu haka tana son sanin halin da Yazid yake ciki.

Cikin mamaki ta ce "Fadila, au watsa mini ƙasa zaki yi a ido? Kin zaɓi ki koma cikin tsiya da wahalar da ya zaɓa miki?"

Fadila ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy, amma na riga na yiwa Daddy alƙawarin ba zan yi gardama ba, ina son gobe ma ya sake bani dama na zo na ganku, bana son irin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ku, kuma in da nice ki kwantar da hankalinki, mijina talaka ne amma yana kula dani, babu abin da zai sameni akasin alkhairi, adduraki nake buƙata a duk in da nake Mummy, kiyi haƙuri ki Kwantar da hankalinki"

Daddy ya ce "Alhamdilillah, 'yar ta ki ma har ta fiki tunani da hankali, wuce muje kar muyi yamma".
Fadila ta yi gaba tana goge hawaye, tana yi tana waiwayen Mummy, yayin da Mummy ta yi turus tana bin Fadila da kallo, Fadila ta ɗau sauran kayanta da ta tattara tai waje.

Abin ba ƙaramin ɗaure wa Mummy kai ya yi ba, anya ba asiri ya yi wa Fadila ba? Gaba ɗaya kamar an canza mata Fadilan baki ɗaya.

Babban abin da ya ƙular da Fadila bai wuce yadda yanzu ma tare da Amina za aje mayar da ita ba, ko meye dalilin hakan oho.
Ta buɗe mota ta shiga tana kuka, Daddy ya ƙaraso ya buɗe motar shi ma ya shiga, shi kansa Fadila ta bashi makaki ba kaɗan ba.

Sannu a hankali ya fara jan motar, Fadila sai waiwaya wa take ko Mummy za ta fito, sai ta ji duk babu daɗi na watsa wa Mummy ƙasa a ido da tayi.

Daddy ya numfasa ya ce "Fadila"
"Na'am ta amsa idonta fal hawaye".

"Kiyi haƙuri, mahaifiyarki za ta sakko ita ma, kamar yadda na fuskanci sauyi a tare da halayenki, ita ma ki dinga yi mata addu'a, daga cikin dalilan da ya sanya na aurar da ke ga mutum mai ilimin addini shi ne fatan samun sauya halayen da kika ta so a kai. Alhamdilillah an samu sauyi, kuma kin yi dauriya da biyayya ƙara haƙuri Allah ya yi miki albarka.
Fadila babu lallai ki samu mijin da zai so ki ya tattalaki kamar yadda mijinki yake miki, na ce a sama masa aiki ya ke ta bani haƙuri a kan kar in damu yana kula da ke. Har CID ne da ni a nan unguwar ta ku da suke kula da motsinku, kuma yaba da jajircewar mijinki bashi da shi amma yana ƙoƙari.
Idan kika yadda mahaifiyarki ta kashe miki aure, na farko dai ba zata iya samo miki miji mai nagartar naki ba, dan kuɗi ba sune kwanciyar hankali ba.
Sannan hakkinsa sai ya kamaku, ga kuma rabo ana sa ran samu a tsakaninku, dan haka ki ƙara haƙuri kin ji autana"

Cikin kuka ta ce "To Daddy"

Amina ta yi shiru, amma duk jikinta yayi sanyi Fadila ta bata tausayi sosai da sosai, ba kowane ɗa ne zai iya jure irin wannan punishment ɗin ba.

Shi kansa Daddyn dauriya kawai yake yi, ya ce "Ai dai kina son sa ko? Zid ake ce masa ko menene?" Yayi Maganar cikin sigar wasa.
Murmushi ta yi duk da hawayen da ke fuskarta.

Ya ce "Ai yana gabana lokacin da ake yi masa kashedin idan wurin budurwa ya je za a gane. Dan Allah Fadila kar ki yi kishi irin na mahaifiyarki, kishi halak ne amma kiyi mai tsafta, mu maza sai haƙuri zaki tara da yawa da ƙyar ki samu wanda baya son samun ƙari, komai kyautatawa da halaccin matarsa, sai dai masu hankalin cikinmu ko mata nawa zasu aura, ba sa manta halarcin matar fari, kuma ba sa wulaƙanta ta, sai dai ya danganta da halin matar. Nan gaba ko Allah ya hore masa ya ce zai ƙara aure, kalleshi kawai kiyi kamar baki damu ba, wannan abu ya fi komai ɓata mana rai, gashi nan ina ta baki satar amsa, kuma banda tarkacen ƙawaye mu mun fi so muga a kodayaushe mune abu na farko a gareku, ku fifita mu fiye da kowa, ku bamu muhimmanci kar ku saka wani abu a gabanmu sai a zauna lafiya, banda kishi na rashin ji Fadila"

Fadila ta ce "Ai ni ya ce ba zai yi mini kishiya ba"

Murmushi Daddy ya yi ya ce "Eh lallai soyayya ta yi daɗi, to Allah ya sa".

Duk da duhun magariba ya rufa, dan sai da suka tsaya Daddy yayi salla, sannan suka ƙarasa unguwar su Yazid, a titi Fadila ta sauke glass tana faɗin "Daddy gashi can" ta ƙarasa maganar tana ɗagawa Yazid hannu.

Slow Daddy ya yi da motar ya tsaya, Yazid ya ta so da sauri, hannunsa riƙe da leda, a kan dakalin wani masallaci yana ta rarraba ido a titi.

Cikin fara'a ya ƙaraso, ya risuna yana gaida Daddy.

Daddy ya ce "Afuwan, na ɗauke maka mata wuni guda ko? Tuba nake" Yazid ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.

Fadila ta buɗe motar zata sauka, Daddy ya ce "To Hajiya, ai kya bari na ƙarasa da ku ko?" Sai kuma kunya ta kamata.

Daddy ya ce Yazid ya shiga ya ƙarasa da su gidan, aikuwa ya shiga, nan suka gaisa da Amina ma.

Fadila ta yi ƙasa da murya tana taɓa ledar hannunsa ta ce "Me ka sayo mana?"

"Kununki ne da nake sayo miki da kuma kifi"

A hankali take faɗin zan ci daɗi.

Sai kuma ta matsa jikinsa take raɗa masa "Kayi missing ɗi na ko?" Yazid ya yi murmushi ya girgiza mata kai.

"To me ka zauna yi a titi kana jira?"

A hankali ya ce "hutawa kawai nake yi"

Hannu ta kai ta matse masa hanci a hankali ta ce "Ba wani nan" Daddy yana kallonsu ta mudubi, kawai ya ɗan yi murmushi, kamar ba yanzu ta gama koke-koke a mota ba.

Har ƙofar gidansu Yazid suka isa, Amina ta jinjina wa Fadila haƙurin da ta yi na zama a gidan nan, saboda yadda take ji da kanta a baya.

Yazid ya ce "Amma dai Daddy ai zaku shigo ko?"

Daddy ya kalli Amina ya ce "Mu shiga?"

Amina ta ce 'Ai ko ba zaka shiga ba, ni zan shiga na yi salla".

Yazid ya ƙarasa yana buɗe gidan, Daddy ya buɗe boot ɗin mota, ya kalli Fadila ya ce "Zo ki taya antynki ɗaukar kayan nan"

Ba ƙaramin ƙulewa Fadila ta yi ba, amma ba yadda ta iya, ta zo ta taya Amina ɗaukar fulasan abinci.
Ganin bayan motar ta yi shaƙe da kayan Abinci ɗanye, Daddy ya yiwa Yazid alama da ya zo.
Yazid ya ƙaraso yana risunawa, Daddy ya ce "Yazid ka samo yara su shigar muku da kayan nan, sai a biya su".

Yazid ya ɗan yi turus yana kallon kayan, Daddy  ya ce "ya na ga kayi shiru?"

Yazid cikin sanyin jiki ya ce "Daddy muna da abinci, ina ƙoƙarin ajiyewa idan mun shiga ma zaka ganix

Daddy ya dafa kafaɗar Yazid ya ce "Yazid ba gazawarka na gani ba, kawai na baku ne dan na tallafa maka".

Yazid ya ce "Daddy kar zuciyata ta mutu ne"

Daddy ya yi murmushi ya ce "Ai kai jarumi ne, kuma na yaba da ƙoƙarinka kar ka damu" Ba dan Yazid ya so ba, haka ya yarda ya karɓi kayan nan aka shiga da su cikin gidan.

Amina ta yi alwala, Fadila ba tare da ta kulata ba ta bata darduma domin ta yi salla.
Sai dai Fadila sai kallon cikin Amina take yi, ya yi girma sosai kamar ta kusa haihuwa, da ƙyar take sallar ma.

Daddy har cikin gidan ya shiga, shi kansa Daddy ya ga gidan yayi ƙanƙanta, amma farincikin da ke kan fuskar Fadila ya tabbatar masa da tana cikin farinciki.

Daddy ya shiga falon ya zauna, aka yi sa'a aka kawo wuta.

Yazid ya ce yana zuwa, ya fita Fadila suka yi ta hira da Daddy. Ba a jima ba sai ga Yazid ya dawo hannunsa da leda ya sayo manyan lemuka, ya shiga Kitchen ya haɗo kwanukan Abinci, da flask na girkin da yayi da rana ya zo ya jera.

Daddy ya ce "Ohh, Yazid sannu da aiki, ke Madam meye aikin ki ne na ga shi yake yin komai".

Fadila ta ce "Daddy bani da lafiya fa"

Daddy kawai ya girgiza kai, shinkafa da miya ga kayan ganye da kifi, Yazid ya ajiye musu.

Amina ta sake ta ci Abincin, dan ba ta iya cin Abincin da ta girka.

Har ku san tara na dare, Daddy ya ce Yakamata su je su gaisa da Hajiya.

Amina ta ce "Yakamata a ɗebarwa Hajiyan Abincin nan a kai mata ita ma".

Daddy ya ce "Haka ne, Fadila ɗauko kwano ki zuba mata".

Sai a yanzu Fadila ta san meye a cikin fulasan, wainar masa cikin fulas, ga uwar miya mai rai da lafiya ta sha nama, gefe kuma ga fulas ɗin dubulan.
Fadila ta ɗaga kai ta kalli Amina, a rant ta ce "Wai ita a dole ga me kirki, to in dai ni ce kin yi a banza"

Hajiya kuwa ta yi murnar ganin Alhaji Ahmad, suma ta karrama su, sai wajen goma na dare su Daddy suka tafi.



Mummy kuwa ta sha mamakin abin da Fadila ta yi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi sai dai ta fara tunanin ko Asiri aka yi mata idan ba haka ba yadda za ayi Fadila ta yi haka.

Hajiya Turai ta kira a waya, gaba ɗaya jikin Mummy a sanyaye yake.

Hajiya Turai ta ɗaga wayar tare da yin sallama.

Mummy ta amsa jiki a sanyaye.

Hajiya Turai ta ce "Yaya, ya dawo miki da ita ɗin ne?"

Mummy ta ce "Hajiya Turai, akwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin, Turai ya dawo mini da Fadila da ciki, kuma ta zaɓi babanta a kaina, dan ta zaɓi komawa in da ya aurar da ita, duk da ƙoƙarin da nayi a kan na riƙeta kar ta koma amma yarinyar nan ta watsa mini ƙasa a ido, kuma wallahi da alama wani talakan ya aura mata".

Turai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, wallahi Zainab wannan yarinyar da mijinki ya aura ita ta rusa miki gida"

"Turai ni yanzu ba ta wannan nake yi ba, ta yadda 'ya ta zata dawo gareni nake, idan Fadila ta haife cikin nan shikenan"

Turai

Please Login or Register in order to submit comment