Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Fadila take, amma ta ce rabonta da Fadila tun shekaranjiya a online.
Hajiya Zainab fa ta diririce, ta shiga kiran Alhaji Ahmad, amma shima baya ɗaga wayar.

Wajen ƙarfe tara na dare da rabi na dare, sai ga Daddy ya dawo. Sai dai Hajiya Zainab bata san ya dawo ɗin ba.

Amina na ganin Daddy tayi murmushi sannan ta ce "Yallaɓai, ya aka yi ne? Sannu da zuwa".

Daddy ya ce "Alhamdilillah, na kaita sai dai tana ta  bori".

Amina ta ce "Bakomai, zata saba ne, ni nayi imani da Allah tana son sa, komai zai zama tarihi in sha Allah, ka kwantar da hankalinka"

Daddy yayi murmushi ya ce "Dama ban ɗaga hankalina ba, na yarda da nagartar yaron".

Hajiya Zainab ce ta banko musu cikin bedroom tana zare ido.

Ya kalleta ya ce "Lafiya?"

"Ai dole ka tambayeni lafiya mana? Tun da baka damu da idan ka dawo ka neme ni ko 'yar ka ba?"

"Meyafaru?"

"Fadila. Bata dawo ba na kira wayarta tana ringing bata ɗagawa, na kiraka a waya amma ka share baka ɗaga ba".

Daddy ya ce "Wayarce a cikin mota, batun Fadila kuma kar ki damu, ki kwantar da hankalinki".

Cikin rashin Fahimta ta ce 'Kamar yaya in kwantar da hankalina ban san in da 'ya ta take ba?"

"Ai na ce ki kwantar da hankalinki, ni na san in da take kar ki damu"

"To ka gaya mini tana ina?"

"Tana nan lafiya" yayi maganar yana cire babbar rigarsa.

"Wai ban gane tana lafiya ba, ina ka kai mini 'ya ta?"

"In da ya dace, kuma bani wuri ina son na huta" ya bata amsa.

"Wallahi ba in da zani, sai ka gaya mini in da ka kaita".

Ya ce "Aikuwa sai ki ta tsayuwa"

Ya rage kayan jikinsa ya shige banɗaki ya barta.

Amina ta kalleta ta ce 'Dan Allah ki ɗan bani wuri, zan cire kaya ina son na kwanta".

A fusace ta ce 'Idan a kan ki nake sai ki sauke ni, tun da wurinki na zo"

Amina tayi mata shiru, ta wuce ta ɗaura towel ta cire kayan jikinta, daga ita sai towel tabi bayan Daddy zuwa toilet.

Buɗe baki Hajiya Zainab tayi, tana ganin salon barikanci da iskanci a wurin Amina, sun ma mayar da ita wata mara amfani a wurin.
Zuciya ce ta kwasheta ta je ƙofar banɗakin tana duka kamar zata ɓalla ƙofar.
"Ka fito ka gaya mini in da 'ya ta take, macuci wanda bai san darajar kansa ba" ta dinga dukan ƙofar iya ƙarfinta.

Banza suka yi mata, har ta gaji da bugun, ta koma gefe ta tsaya tana huci.

Sun ɗauka ta fita suka fito tare shi da Amina, suka tarar da ita a tsaya tana ta kumbura wuya.

Tana ganin sun fito, ta kuma kallon Alhaji Ahmad ta ce "Nace ka gaya mini in da ka kai mini 'ya ta"

Daddy ya ce "Zainab, nace kiyi haƙuri ki Kwantar da hankalinki, amma ki sani Fadla tana cikin kwanciyar hankali, da sannu zaki san in da take"
Amina kuwa wucewa tayi gaban mudubi tayi zamanta, ta fara shafa manta.

Tana jin yadda suka cigaba da fafatawa, tayi kamar ba ta san suna wurin ba, suka gama tashin hankalin su, Hajiya Zainab ta fice daga ɗakin.

Daddy ya tako ya dawo kan gadon da Amina ke kwance, shi ma ya hau ya ce "Am sorry Meenalina, duk an ɓata miki rai ko?"

Ta ce "A'a"

Ya ce "Yauwa, ya maganarmu?"

Amina ta ce "Wace maganar?".

"Maganar zuwa umara, ina son mu kuma komawa duba matar Khalil, ina son mu koma Lagos a gobe in Allah ya kaimu, idan ba haka ba zata sakani a gaba a kan lallai sai ta san in da Fadila take, idan kuwa ta sani ba zata bari ta zauna ba, sai ta san yadda zata kashe mata auren".

Amina ta ce "Amma akwai buƙatar ta san inda take, ka san uwa ce hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba".

Daddy ya ce "A'a, nima na san zata shiga damuwa, amma ba zan bari ta sani yanzu ba, tayar mana da hankali zata cigaba da yi, ki ƙyaleta kawai".

Amina ta ce "Shikenan"

"Yanzu dai gaya mini, suwa kika yanke a biyawa"

Amina tayi murmushi sannan ta ce "Da farko ina son a biyawa Babana, sai Zakiru sai kuma ƙanin mahaifin Hajiya Zainab sai kuma mai gadin Family house ɗin ku, sai kuma ina neman alfarmar ka biyawa mutum uku da suke da buƙata a family ɗinku, ko da maƙotanku ne, tun da na san a familynku babu wani mai ƙaramin ƙarfi da za a biyawa".
Murmushi Daddy yayi, ya ce "Allahu Akbar, abin da yake ƙara mini ƙaunarki rashin son zuciyarki, yanzu har da ƙanin mahaifin Hajiya Zainab a wanda kike so a biyawa, ita da ko da wasa bata taɓa sawa ko biyar na bawa wani nata ba sai dai ƙawaye"

Amina ta ce "To Daddy meye a ciki? Allah dai ya ƙara maka arziƙi da kwanciyar hankali mu ci mu bayar"

"Amin Babyna, ina alfahari da ke masoyiyata ina ƙaunarki sosai da sosai" yayi maganar yana janyota jikinsa.

Ita ma murmushi tayi, ta ce "Nima ina sonka sosai Sweetheart".

Washegari da safe, Amina tare da Hajara, suka shiga Kitchen yin girki, sam Amina bata nunawa Hajara ƙyama saboda tana matar gidan, sai ma kyautatawa da take nuna musu, domin bayan aurenta da Daddy yayi, har ƙarin albashi ta sanya yayi musu.

Ta dafa abin da zasu karya, da kuma abin da zasu kai wa su Hafsa Asibiti.

A dining Amina taje ta shirya abinci, ta koma sashinta da nufin tayi wanka ta tashi Daddy, su karya su tafi dubiyar, saboda da Yamma zasu bar gari.
Sai dai me tana zuwa bedroom ɗin nata ta tarar da Hajiya Zainab tana ta zazzagawa Daddy masifa.

A fusace Amina ta ce "Nifa gaskiya na gaji da shigo mini ɗaki da kike yi kai tsaye, ki tafi can ki dinga jiransa idan ya zo wurinki kuyi wadda zaku yi, ni ba zan iya jure in kallonki kina cin mutuncin mijina a gabana ba"

Hajiya Zainab ta kalleta ta ce 'Ki ka ce mijinki?".

Amina ta murguɗa baki ta ce "Eh mana, ko baki ji bane ba, mijinmu ko ma in ce mijina, tun da dai ke kin sallama mini shi".

Kallon banza Hajiya Zainab tayi mata ta ce 'Eh kece mayyar namiji, in dai shi ne kije kiyi tayi, a fito mini da 'ya ta kawai, yauwa".

Daddy ya ce "Zainab na gaji da wannan rashin mutuncin naki da wulaƙanci".

Mummy ta ce "Ai rashin mutunci da wulaƙanci, da kanka kayi cinikinsa ka saya, dan haka dole ka jure shi, ka gaya mini in da 'ya ta take".


Daddy ya ce "Ki je, zan yi wanka na karya, Dutse na kaita zanje na ɗaukota idan na gama shirina"

Wata masifar ta dira da bala'i, a kan me za a kai mata 'ya Dutse. Saboda ta ƙyaleshi, ya lallaɓata ya ce yanzu zaije ya taho da ita.

Amina ta daɗe ba taga azababbiyar mata kamar Hajiya Zainab ba.

Bayan yayi wanka ya karya, ya shirya shi da Amina, suka fice.

Asibiti suka fara zuwa wurin Hafsa, Khalil ne ya kwana tare da ita, yana jiran Maman Hafsa ta zo, shi kuma ya koma gida. Yana ta kula da ita kamar ya mayar da ita ciki.
Yanzun ma yana zaune a gefen gadonta, yana rungume da ita, yana shafa gashin kanta yana mata hira, hannunta kuma ɗauke da drip.

Su Daddy na shigowa Hafsa tayi sauri ta rabu da jikin Khalil.
Murmushi Daddy yayi ya zauna, suka gaisa yana mata sannu.
Amina ma sannun ta shiga yi mata tana yi mata ya jiki.

Hafsa ta amsa mata da sauƙi, so take ma a sallame su.

Khalil ya ce 'Babu mai sallamarki, sai kin warke".

Amina ta miƙo musu fulas, ta ce xGa abinci nan na kawo muku".

Khalil yayi murmushi ya ce "Mun gode sosai Anty Amina".

A nan Daddy yake gaya masa batun tafiya umara, da kuma waɗanda ya biyawa.
Khalil ya ce "Gaskiya Daddy kayi dabara, mussaman biyawa ƙanin babnsu Mummy shi ma, zai ji daɗi wallahi".

Daddy ya ce "Ai Antynku ce tayi wannan tunanin, har da Zakiru duk zamu tafi, albarkacin haka har ita Hajara zamu tafi, sun daɗe suna maana aiki a gidan nan, yakamata a mutuntadu, kai kuma idan kuka gama jinyar ka nutsu ka biya muku kai da matarka. sai dai Lagos zamu tafi mu anjima, kai zan bawa gabarar sanar da wanda za a biyawa, da kuma biya musu saboda wani dalili nawa".

Amina ta ce "To waye ya ce kace nina ce a biya musu"

Daddy ya ce 'Ai yabon gwani ya zama dole Aminatu'.


Khalil ya ce "Daddy godiya suke, Anty Amina Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana"

Amina tayi murmushi ta ce "Amin"

Daddy ya ja Khalil suka fice daga ɗakin, Amina kuma ta zauna suka cigaba da hira da Hafsa.
A nan Amina ta bata labarin abin da yafaru na aurar da Fadila da Daddy yayi ba wanda ya sani, sannan ta ce wa Hafsa ko Khalil karta gayawa.


Daddy kuwa a waje ya sanar da Khalil cewa da zarar Hafsa ta warke, sannan ya gama abin da ya sa shi ɗauki Hafsa su koma Abuja tare, kar ya kuma barinta ita kaɗai, idan ya so su zane a gidansa na Abuja zuwa ya kammala nasa.

Khalil ya amince, suna nan Maman Hafsa ta zo, suka gaisa tayi musu godiya sannan suka yi musu sallama suka tafi.






Yazid kuwa tun Asuba ya tashi Fadila, amma tayi mursisi taƙi tashi, ba ita ta tashi ba sai shida saura, lokacin ma Yazid bai dawo daga masallaci ba, ga wata irin yunwa da take tatalar cikinta, dan rabonta da Abinci, tun Fruit ɗin da ta ci jiya. Tashi tayi a hankali, ta nufi hanyar fita daga gidan, sai dai ta tarar da ƙofar a rufe.
Ta koma falon ta zauna ta takure jikinta, cikinta na cigaba da ƙugi.

Bakwai saura Yazid ya shigo gidan da sallama. Banza tayi masa bata amsa ba, ya shigo falon ya zauna a kusa da ita ya kalleta ya ce "Ina kwana?"

Tsaki tayi ta kawar da kanta gefe.

"Hmm, me kike so ki ci?"

A fusace ta ce "Ban sani ba, kaga malam ka tashi ka mayar da ni gidanmu"

Yazid ya ce "Meyasa?"

"Ban gane meyasa ba? Saboda ba zan zauna da kai ba, nafi ƙarfinka nafi ƙarfin na zauna da kai, ni ba matarka bace, ka tashi ka mayar da ni gidamu, ko ni na tafi".

Yazid ya kwantar da muryarsa ya ce "Kiyi haƙuri Fadila, yanzu idan kika fita zaki iya ɓata a unguwar nan, kuma ga furucin da mahaifinki yayi a kan barinki gidan nan ki koma gidanku, kiyi haƙuri ki zauna in cigaba da bashi haƙuri idan ya huce sai muje gidan naku"

Cikin kuka Fadila ta ce "Ni ba zan zauna da kai ba, ba ruwanka da furicin da yayi, kasai ka sakeni, ba zan zauna ba".


Ya ce "To shikenan, ki bari ki karya tukuna, sai muyi magana"

"Babu wata magana da zan yi da kai, kawai k mayar da ni gidanmu, wallahi baka yi mini adalci ba, dan meyasa zaka aureni, ni bana ƙaunarka ban taɓa sonka ba, kuma ban yake maka ba"
Shiru Yazid yayi ya dafe kansa, dan ya san an rina an saci zanin mahaukaciya.

Suna cikin wannan mujadalar ne, aka yi sallama da ji ka san muryar babbar mace ce.
Yazid ya miƙe yana faɗin Hajiya sannu da zuwa shigo.

Matar ta sake yin sallama sannan ta shigo falon, da fulas ɗin shayi a hannunta da wani ƙaramin foodflask, ta ajiye tana cewa "Amarya sannu ko, ga kayan kari na kawo muku".

Yazid ya ce "Fadila ga Hajiyata, ita ce mariƙiyata uwa ce a wurina" ko kallon in da matar take ba tayi ba, balle ta gaisheta ta kawar da kanta gefe.
Yazid bai ji daɗin abin da Fadilan tayi ba, Hajiya ta tashi ta ce 'In dai kuwa wannan ce matar, to Allah ya sauwaƙe ya tayaka riƙo, shiyasa ni sam ban murna da wannan auren ba, yaran masu kuɗi zama da su sai dole".
Miƙewa Yazid yayi yana lallaɓa Hajiya dan tayi shiru amma ta ƙi.
Fadila kuwa bayan matar ta bi da harara.

Haka dai Yazid yayi ta bawa Hajiya haƙuri, ta gama mitarta ta tafi.
Ya koma ya cigaba da rarrashin Fadila ta ci Abinci.

Hajiya Zainab gajiya tayi da zaman jiran Alhaji Ahmad ya dawo mata da Fadila, ta kira wayar Fadila tun tana shiga har ta daina.
Gajiya tayi ta kira Alhaji Ahmad, yana ɗagawa cikin fushi ta fara tambayarsa ya taji haryanzu shiru.

Daddy ya ce "Ai nace ki kwantar da hankalinki, tana hannu na gari, Fadila bata Dutse, babu wani abin ƙi da zai sameta kiyi haƙuri ni Yanzu haka ina Lagos ma!!!




Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YA TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA.



75

Wani uban zagi Hajiya Zainab ta maka, amma Daddy ya katse kiran ya ƙyaleta.
"Ni zaka ciwa mutunci, wallahi baka isa ba, wato ka ajiyeni ka mayar da ni hoto banza, ina jiran ka kawo mini 'ya ta, amma ka zaunar da ni ka ɗau wannan yarinyar mai kama da karuwai ka tafi da ita, to wallahi baka isa ba". Haka ta cigaba da masifa ita kaɗai tana bambami.


Yazid kuwa da ƙyar ya lallaɓa Fadila ta ci abinci.
Yazid ya kalleta cikin kulawa ya ce "Fadila yakamata na dafa miki ruwa kiyi wanka, mu kuma zaga ki ga gidan naki".

Fadila ta yamutsa fuska ta ce "Ina ne gidan, wannan ne gidan? Wannan ai bai yi kama da gida ba".

Yazid ya ce "Na ji, amma ki daure ki shiga kiyi wanka ki sauya kayan jikinki" sake takurewa tayi a wuri ɗaya taƙi kallon Yazid.

Tana kallonsa ya kwashi akwatunanta, ya kai cikin bedroom ɗin, ya shirya mata kayanta a sip guda ɗaya, ɗaya kuma nasa ne.

Ya dawo falon ya wuceta, ya shiga ɗan ƙaramin Kitchen da yake tsakar gidan, ya kunna risho ya ɗora ruwan zafi.

Mintuna kaɗan, ruwan yayi zafi, ya juye a bokiti ya sirka, ya dawo ya ce "Dan Allah ki zo ki watsa ruwan kya ji daɗin jikinki" gaskiyar Yazid, tana buƙatar ta watsa ruwa dan gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, dan ko a gida Fadila gwanar wanka ce.

Banɗakin da ke tsakar gidan ya kai mata ruwan, ta tarar da banɗakin wani ɗan tsukakke da shi, a ƙuntace ga kan fanfo sai masai pit latrine.
Wasu hawayen takaici ne suka zubowa Fadila, ta kalli in da sabon kwandon wanka yake, da soso da kuma sabulu.
Haka ta durƙusa tayi wanka, ta zuro kayanta ta fito.
Ko da ta fito, Yazid baya nan ya fita, ta shiga bedroom ɗin, ta ƙarewa ɗakin kallo, ƙatuwar katifa ce a ɗakin, sai sip da mudubi, sai wata cupboard ɗauke da uban litattafai na addini da na zamani kamar Library a ɗakin.

Taɓe baki tayi, ta buɗe akwatinta, bata ɗauko mayukanta na shafawa ba a ciki. Tsaki tayi, ta tashi ta duba kan madubin ta ga Vaseline, gaba ɗaya warin vaseline ɗin bai yi mata ba, haka ta daure ta shafa.

Ta duba ta ɗauki wata 'yar riga me sauƙin nauyi, ta saka ta koma ta nemi wuri ta yi shiru tana tunanin yadda aka yi Yazid ya aureta, da yadda Daddy yayi mata wannan irin maƙasƙancin auren haka.
Ta saka hijjabi, tayi sallar azahar, ta idar ta cire hijjabin ta zauna, ta tsunduma duniyar tunani.
Sallamar da Yazid yake yi ne ta dawo da ita hayyacinta, ya shigo falon riƙe da ledoji a hannunsa.
Kallo ɗaya tayi masa, ta ɗauke kanta zuwa wani wurin daban.

Ya shiga Kitchen ya ɗauko plate, ya zazzage mata wata lafiyayyiyar shinkafa da naman kaza. Ya saka mata cokali ya ce "Ga Abinci"

"Ni fa ba abincinka nake buƙata ba, ka mayar da ni gidanmu na gaya maka".

"Fadila, furucin mahaifinki abu ne mai girma, wanda zai iya yin tasiri a rayuwarki, kiyi haƙuri idan komai ya lafa zan mayar da ke gida da kaina kin ji ki ci Abincinki"

"To yaushe zaka mayar da ni?"

Yazid ya ce "Da zarar komai ya lafa zan mayar da ke in Sha Allah, amma ranar Monday zamu koma school ko?"

Ta kalleshi ta ce "Ni da makarantar nan har abada"

"Saboda me?"

"Ba zan sake zuwa ba, na gama makaranta"

Ya kuma kwantar da murya ya ce "Haba Fadila kin zaɓi kiyi asarar shekarunki da kika fara na karatu?"

"To ina ruwanka? Kai kayi asarar su ko ni?"

Yayi murmushi ya ce "A'a, ga Abincin".

Ba kunya ta karɓe masa Abinci ta fara ci, gefe ya koma shi ma ya fito da ɗan ƙaramin fulask, ya zuba kunu a kofi yayi Bismillah ya fara sha.

Bata ci da yawa ba ta ajiye, ta ɗan tsurawa Yazid ido sannan ta ce "Dan Allah meyasa ka aureni, bayan ka son bana sonka?"

Murmushi yayi ya ce "Ikon Allah mana, kina mamaki ko? Nima haka nayi mamakin yadda abin ya kasance, amma ki Kwantar da hankalinki dan Allah".

"Ba zan kwantar ba" tayi maganar tana hararsa.

Haka suka wuni kamar kurame, Babban abin da ya bashi mamaki yadda bata cigaba da yi masa tijara ba, sai tsiwa da hararsa da take ta yi, haka kurum yake yi mata kwarjini, ta kasa cigaba da yi masa rashin mutuncikHausawa suka ce, ba faɗa da malam ba daren) ko da yake ba abin mamaki bane ba, dan Yazid sosai ya duƙufa yake addu'a a kan zaman nasu tare da fatan Allah ya sa ta dangana ta zauna dashi. idan ta ɓangare guda Fadila ta tuna maganar Daddy sai gabanta ya faɗi. Tunani ta shiga yi ko a wane hali Mummy ke ciki yanzu oho.
Jikinta yayi sanyi, hawaye ya shiga zubo mata.
Cikin kulawa Yazid ya ce "Dan Allah ki daina wannan kukan zuciyata bata so?"
Da ɗan ƙarfi ta ce "Kar ta so ɗin, da baka son kukana ai da baka aureni ba".
Bai kuma tanka mata ba har zuwa dare, ya kawo mata abinci daga gidan Hajiyarsa. Nan ma ta ci abin ta, tayi sallar isha'i ta nemi wuri a falo ta kwanta.

Yazid ya shigo ya kalleta ya ce "Ki shiga ki kwanta, nan akwai sauro sosai" bata ce masa uffan ba, ta tashi ta shiga bedroom ɗin. Kasancewar tana jin bacci sosai, ta kwanta a kan katifar.
Can cikin bacci ta waiwaya, taga Yazid yana rage kayan jikinsa, rintse idanunta tayi tana tunanin ko mafarki take yi.
Amma ta sake buɗe idonta, taga ya hau kan katifar. Zumbur ta tashi zaune ta ce 'Meye haka?" Yazid ya kalleta ya ce "A ina?".

"A ina zaka kwanta?"

Yazid ya ce "A kan katifa mana"

"Gaskiya ba zan kwana wuri ɗaya da kai ba, ni ban taɓa kwana da wani ƙato a kan shimfiɗa ɗaya ba, kawai ka tashi"

Yayi murmushi ya ce "To a ina zan kwanta?".

"Ka koma ƙasa ka kwanta"

Ba musu ya tashi ya ɗau pillow ya kwanta a ƙasa.
Hakan ya sa ta ɗan sake, ta kwanta bacci mai nauyi ya ɗauketa.

Idon Yazid biyu, yaji saukar numfashin Fadila alamun tayi bacci, ya tashi tsam ya koma kan katifar ya kwanta a bayanta, ya janyota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, ya saka hanunsa a saitin zuciyarta, ya dinga karanto Alqur'ani yana addu'ar ubangiji Allah ya bata juriya da dangana, dan shi kansa ya san wannan auren na su jarabta ce a gareta, dan bashi da ƙarfin iya aurenta.
Ita kuwa jinta a jikin mutum ta zata mafarki take, ta ƙara sakankancewa.




Khalil ya shirya, ya zo gida domin gaida Mummy, dan ko ba komai mahaifiyarsa ce.
Sai dai ko da yaje, ya tarar da ita bata duk tayi wani iri.
Bai samu wata kyakkyawar tarba ba, amma duk da haka bai hana shi cewa "Mummy lafiya kuwa? Meke damunki ne na ganki wani iri?"

Mummy duk da a ƙule take da shi, amma ta ce "Ba dole ka ganni a haka ba, kai da ubanka kun haɗa kai kuna yinƙurin ku kasheni, ya ɗauke Fadila ya kaita wani wurin daban sani ba, ya gaya mini Dutse ya kai ta zai ɗaukota, amma tsabar wulaƙanci wai na kira shi a waya, yace mini wai yana Lagos" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.
Cikin damuwa Khalil ya ce "Mummy dan Allah kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ki bi komai a sannu ki daina ɗaga hankalinki, Fadila Daddy ne ya haifeta ba zai cutar da ita ba".

Cikin fushi ta dakatar da shi ta hanyar cewa "Kai dalla can rufe mini baki, dama ai kai goyon bayansa dama kake yi, domin kai ma ya tsaya maka ka auri 'yar matsiyata, dole ka goyi bayansa a kan dukkan abin da yake aikatawa, ka kyauta tashi ka bani wuri" Haka Khalil ya tashi ya fita.


Zakiru da Hajara kuwa, jin ance za a biya musu umara da Khalil ya sanar musu a zuwansa gidan, suka dinga murna suna jin daɗi, Khalil ya gaya musu Amina ce ta saka a biya musu.
Suka dinga murna suna saka wa Amina da iyayenta albarka.
Khalil tare da Hafsa suka je Jigawa, suma suka je suka sanar musu yadda aka biya wa wasu umara, har da ƙanin mahaifin Hajiya Zainab.
Nan da nan labari ya karaɗe dangi, dan Alhaji Ahmad bai taɓa yi musu alkhairi makamancin haka a rayuwarsu ba.


Yazid dai kusan kwanaki biyu suna fafatawa da Fadila, kan ya samu ta ɗan kwantar da hankalinta, dan har hirar arziƙi ta kan shiga tsakanin su, ko da kuwa ba zata amsa masa ba.

Yau da safe ya dafa musu tea, ya zo da kayan tea, har da ƙwai.
Ya zuzzuba musu ya miƙa mata nata, ta saka hannu ta ɗauka ta karya.
Fadila bata aikin komai a gidan nan, Yazid ne yake zagewa yayi komai, daga shara wanke wanke gyaran toilet duk shi ne yake yi, hatta kayan jikinta idan ta cire shi ne yake haɗawa ya wanke, ba abinda ta sani sai dai ta ci ta ƙoshi ta saka shi a gaba tana koke-koke.

Ga Yazid yana ta ƙoƙarin sayen duk abincin da ya san zata iya ci.
Yanzu ma kukan take yi, tana zaune a kan kujera sai aikin kuka take yi.
Yazid ya ƙarasa kan kujerar da take zaue ya zauna a kusa da ita. Tun da Daddy ya kawota gidan nan, wannan ne karon farko da Yazid ya zauna a kusa da ita a ido biyu.
Jikinta ne ya ɗau rawa, kamar yadda take yi a baya, idan ya zauna a kusa da ita a school.

Haɗe rai tayi ta ce "Dan Allah ka tashi daga kusa da ni"

Yazid ya ce "Meyasa? Ya naga jikinki yana rawa?"

A fusace ta ce "Idan ba zaka tashi ba, matsa ni na tashi".

Yazid ya sake matsawa kusa da ita ya ce "Jikinki da nawa ne, tamkar ƙarfe ne da kuma mayen ƙarfe, jikinki tamkar mayen ƙarfe yake, a duk lokacin da na kasance a kusa da ke, sai jikinki ya fara rawa, kina buƙatar nawa jikin a matsayin ƙarfe, kamar dai haka" ya janyota jikinsa. Aikuwa take jikinta ya daina rawar, sai dai kuma bugun zuciyarta da ya ƙaru, har numfashinta ya fara yin sama.
Kasa motsawa tayi, sai shiru da tayi tana kokawa da numfashi.
A hankali ya kama gashin kanta da tayi parking ɗin sa.
Jin Yazid na neman wuce makaɗi da rawa, kuma gashi ta kasa hana shi, kamar yadda ta taɓa gani a mafarki yau a zahiri hake faruwa, bakin Yazid ne a cikin nata. lokaci ɗaya tayi wata irin zabura ta rabu da jikinsa, ta haɗe rai ta fice tsakar gida ta tafi bakin rariya, tana zubar da miyan bakinta tana tsaki. Ɗan kashingiɗa yayi yana murmushi. Yayi shiru yana tuna farkon ganinsa da ita, zuwa yau da Allah ya sanya cikin ikonsa ta zama matarsa.


Ranar da ya fara shiga ajinsu a jami'a, kansa a ƙasa, ya shawo uwar tafiya mai nisa da ƙafarsa, saboda rashin wadataccen kuɗin mota a hannunsa. Yana shiga aji mutum na farko da ya fara sanya idonsa a cikin nasa ita ce Fadila.
Ras! Gabansa ya faɗi, ta ƙare masa kallo ta fashe da dariya, amma hakan bai hana shi ganinta ɗauke da wani kyawu na musamman ba, da tun da yake bai taɓa kallon wata mace har ta burgsehi ba, sabgogin gabansa ne suka dame shi.
A haka yayi ta'awizzi ya nemi tsari daga sheɗan, amma kamar wasa ƙaramar magana ta nemi komawa Babba, har Alla-Alla yake garin Allah ya waye ya je makaranta dan ya ga Fadila.
Komai nata burgsehi yake yi, duk da kasancewarta 'yar wulaƙanci ga izza da girman kai, amma zuciyarsa bata fasa begen Fadila ba. A haka har yayi ta maza ya fara kulata. Duk da da fari bata saurarsa sai wulaƙanci, amma bai gaza ba har zuwa ranar da rashin lafiya ta same shi ta kai shi Asibiti, ji yayi tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan farinciki.
Daga lokacin da suka samu saɓani kuwa, ta ce

Please Login or Register in order to submit comment