Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Meenali kin tabatta?" Ta jinjina masa kai.

Ta ce "Sai kuma.."

"Sai kuma me?"

"Sai kuma nima gaskiya kayi mini walima, a san aure muka yi, tunda ba kowa ya san hakan ba, idan na gama Neco sai ayi walimar gama makarantata da tariya"

Daddy ya ce "Sai me kuma?"

Ta kai hannunta fuskarsa ta ce "Sai kuma a maye mini gurbin wannan damuwar da sakin fuska"

"Meenal, dole na shiga damuwa, ban so al'amarin nan ya zo a haka ba"

"Kayi haƙuri, ka kwantar da hankalinka komai na Allah ne, kuma daga gareni ba zaka samu wata matsala ba in Allah ya yarda. Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu, amma dan Allah ka daina wannan damuwar"

Ya ɗan numfasa ya ce "Haka ne, Amen zamu je in kai ki gidan su Aziman ne yanzu?"

"A'a na fasa, ka samu ka ci Abinci ka huta, kar jininka ya hau dan Allah"

"Shikenan, amma ya kike jin jikina naki ba wata matsala ko zamu koma?"

"A'a babu wata mata, naji sauƙi sosai"

"Shikenan bari in tashi, idan da wani abu sai ki kirani kawai a waya"

"To Babyna" ta amsa tana lumshe masa ido.

Murmushi yayi sannan ya tashi ya fita daga ɗakin.

Hajara sai sake jinjina lamarin take.


Fadila da ƙyar ta iya rarrashin Mummy, ta nemi wuri ta kwanta, ita kuma ta koma ɗakinta, tana cigaba da tunanin wace shawara zata bawa Mummy. Ita kanta ta dasa a wani muhallin da zata ajiye abin da Daddy ya aikata.
Wasu hawayen takaici suka shiga zubo mata, saboda ita kanta a ganinta wulaƙanci ne da cin zarafi ga mahaifiyarsu.

Wayarta ta ɗauko tana kuka ta kira Khalil a waya, tayi sa'a wayar na fara ringing ya ɗaga, yayi mata sallama.
Kasa Magana Fadila tayi sai uban kuka da ta fashe da shi.

A rikice Khalil ya ce "Fadila menene? Meyafaru?"

"Daddy ne Khalil"

"Me ya sami Daddyn?"

Ta share hawaywnta ta ce "Khalil Daddy ne yayi aure"

Khalil yayi tsaki ya ce "Shine zaki ɗaga mini hankali, wallahi na zata wani abin ne ya same shi"

"Khalil, baka yi tunanin wani hali Mummy zata shiga ba? Ka san wa ya aura ne? 'yar aikin nan Amina 'yar gidan mai gadi fa, could you imagine?"

Khalil ya ce "To kuma shine kike wannan kukan kamar ance Daddy ya mutu? Ni duk kin tayar mini da hankali"

Fadila ta ce "Khalil, baka damu da halin da Mummy zata shiga ba ne? 'yar aikinta fa ya aura?"

"Fadila aure fa kika ce, Aure yayi ba wani abu ba dan Allah karki tayar mata da hankali da wannan kukan da kike yi"

"Amma Khalil ka bani mamaki fa, ka manta yadda Mummy bata son kishiya? Wato ko a jikinka ko?"

"Ba haka bane ba Fadila, yanzu ace mahaifinmu ya nemi 'yar wani a waje fa? Na san zuciyar Mummy babu daɗi, na san ba a kyauta mata ba, amma kamata yayi ki kwantar mata da hankali, ba ki zauna kina kuka ba, ta sake shiga cikin damuwa ba. In Allah ya yarda zan shigo a satin nan, amma karki bari Mummy ta ce zata yi wani abu da zai janyo mata dana sani a nan gaba"

Gaba ɗaya haushi ne ya kama Fadila, saboda gaba ɗaya ji tayi kamar Khalil bai damu ba sam.

Kashe wayar tayi, ta ajiye, ta fito domin ta koma wurin Mummy.

Tana fitowa falo ta ga Amina ma ta fito, tana ta share share, tana gyara falo.

"Ke!" Fadila ta dakawa Amina tsawa.

Amina ta ɗago kai ta kalli Fadila.

"Baƙar munafuka algunguma, saboda munafurci shine ki auri mahaifina kinga kuɗi jiki na rawa kika shiga kika fita kika aureshi, to wallahi kin kawo kanki kabarinki, sai kin bar gidan nan da ƙafarki, baƙauyiya dabba kawai mayyar abin duniya".

"Fadila kenan, duk abin da zaki gaya mini, ma riga na gama da ke, tun da na haɗa shimfiɗa da babanki. Daga ke har mahaifiyar ki zan baku shawara, ba ruwanku da ni, kuyi rayuwarku nayi tawa mu zauna lafiya, idan ba haka ba yanzu na fara baku mamaki, a cikin gidan nan ku kiyayeni!!!




AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL



62


Murus bakin Fadila ya mutu, ba abin da take sai bin Amin da kallo, ga kalaman na Amina ba ƙaramin baƙantawa Fadila rai suka yi ba, wai har ita Daddy zai ce a yiwa warning a kan wannan Yarinyar da take yiwa kallon ƙasƙanci. Amina ta bata mamaki ƙwarai da gaske.
Amina kuwa ta cigaba da aikinta, ta share Fadila da ke tsaye tana binta da ido.

Kasa jurewa Hajiya Zainab tayi, ta ɗau wayarta ta kira Hajiya Salma, har ta kusa katsewa Hajiya Salma ta ɗaga, suka gaisa Hajiya Salma ta ce "Ya naji muryar taki ƙasa-ƙasa ko baki da lafiya ne?"

"Hajiya Salma ba gara ace kwance nake ba lafiya ba, idan likita ya dubani wataƙila na warke ba, a kan masifar da nake ciki a yanzu"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyafaru ne?"

"Hajiya Salma na ƙara yadda, namiji ƙanin ajali ne, tsawon shekarun da muka yi tare, a wannan karon ya gwada mini halin nasu"

"Zainab, dan Allah ki warware mini ki daina yi mini magana kwan gaba kwan baya, me yayi miki?"

Ta  ɗan numfasa sannan ta ce "Aure yayi"

"Shi wa?"

"Ahmad mana Salma, aure yayi ban sani ba yau watanni kusan uku da ɗaura masa aure, sai jiya Allah ya toni asirinsa, kin san abin baƙin ciki kin san wa ya aura?"

"Bala'i, wace 'yar hau ɗin mai tsautsayin masifar ya aura?"

"Salma 'yar aikina, 'yar wurin maigadi"

"Laila ha illalahu Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam, dan Allah Zainab kice mini da wasa kike yi mana"

Cikin karaya Hajiya Zainab ta ce "Na taɓa yi miki irin wannan wasan ne?"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma Ahmad ya cika mara mutunci, shi duk matan duniya ya rasa wadda zai aura sai wannan? Amma Zainab kina me har alaƙa ta shiga tsakaninsu suka yi aure baki sani ba"

"Hmm, Salma munafuncin ɗa namiji ya wuce lissafinki da tunaninki, ko da wasa bai taɓa nuna wata alama na yana son Yarinyar nan ba, Rashin kunya tayi mini, Fadila ta tureta ta faɗi sai jini ya ɓalle, na kira Doctor Aliyu aka dubata sai ga ciki, na kira shi nace zan koreta ya ce in jira ya dawo, ashe wai ya aureta wata Uku kenan, wai idan ta gama jarrabawa zata tare, sannan ya gaya mini, Ashe abin competition da ta tafi Abuja suna tare, Salma na rasa yadda zan yi da raina, ji nake tamkar na balbala fetur na ƙonemu duka a gidan, kaina ya toshe na rasa mafita".

Hajiya Salma ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai ba zamu so kiyi abin da za ayi mutuwar kasko ba, ubansu zamu ci sai ta fita ta bar gidan nan ko tsirara ne, shi kuma zai gane bashi da wayo, zan yiwa Turai magana zamu zo"

"To shikenan Salma, sai anjima"

"Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar kiyi musu wani abu da zaki illatasu, abu ya kwaɓe miki, ki bari dai mu zo"

"In Sha Allah, ba abin da zan yi sai kun zo ɗin" suka yi sallama ta kashe wayar.

Amina jin ta ɗan ji sauƙi ya sanya, ta ware ta cigaba da aikinta, amma hankalinta na kan Daddy, tunda ya fita bai dawo ba, ta san yana tsoron dawowa saboda Hajiya Zainab zata rikita masa lissafi. 'Aikuwa ba zan abri hakan ta faru ba, idan ita bata son sa ni ina so, ba zata katse mini walwalarsa ba, wadda ita ce tsanin farinciki na ba'

Kitchen ta shiga tana gaganiyar ɗora Abinci, Hajara ta shigo Kitchen ɗin tana ganin Amina, da sauri ta ce "Amina ai kinfi ƙarfin wannan aikin yanzu, ga baki da lafiya ga shi kin zama matar gida, ai wannan aikin sa mu".

Amina tayi murmushi ta ce "Ni ɗin wace da ba zan aiki ba, in naɗe sai dai ayi mini komai, ladan da zan samu fa. Manta kawai zan yi aikina, kya tayani da abin da ba a rasa ba".

Hajara ta ce "A'a Amina, idan Allah ya ce ka huta ai sai ka huta, ke ina ke ina wannan aikin yanzu, yanzu fa daidai kike da masu gida, ke ma matar gidan ce, dan kije ki huta nayi aikina"

"Hmm, lallai Hajara gani kike da wasa nake" Amina ta cigaba da ayyukanta.

Sai da ta kammala, Hajara na tayata suna hira, amma Amina ba ta bari Hajara tayi mata tambayar rainin hankali ba, ko bin diddigin taji yadda abubuwa suka gudana ba.

Ƙarfe takwas na dare, Amina ta gama komai ta cewa Hajara, ta je ta sanarwa da su Hajiha Zainab, an gama girki su fito suyi dinner.
Ita kuma ta wuce ɗakinta, ta ɗau waya ta kira Daddy.

Yanayin yadda ya amsa wayar kawai, ya isa ya nuna maka yana cikin damuwa.

"Hello My dear kana ina ne?"

A ɗan rikice ya ce "Lafiya, wani abin ne yafaru? Ko wani abun tayi miki?"

"A'a ni ba abin da tayi mini"

"To jikin ne?"

"A'a fa duk ka kwantar da hankalinka, naga haryanzu baka dawo bane ba, nayi maka girki ka dawo kaci Abinci ka kwanta ka huta mana"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Zan dawo in sha Allah"

"Yauwa dan Allah ka dawo yanzu kaji My"

"Shikenan Meenali, gani nan" ta katse kiran, ta ajiye wayar ta shiga wanka.

Hajara kuwa koda taje ta sanar da Fadila an gama girki, wata irin tsawa ta daka mata, ta koreta daga ɗakinta, saboda shirme kuma, sai ta tafi ɗakin Hajiya Zainab, wai ko ita zata ci.

Wata ashariya da Hajiya Zainab ta bankawa Hajara, bayan ta gama sanar mata da batun an gama abinci, sai da Hajara ta rikice.
"Munafuka kema kin san komai, dake aka haɗa kai, ki ƙulle kayanki sai kin bar mini gida kema, gayyar tsiya gayya jaraba matsiyatan banza da na wofi, zaki fita ki bar mini ɗaki ko saina taka wuyanki, algungumai zuriyar tsiya" sum sum Hajara ta baro ɗakin Hajiya Zainab, ta tafi wurin Amina.
Ta tarar da Amina a zaune, tana ta shafa turare.
Amina ta kalli Hajara da take kamar a razanae ta ce 'Lafiya kuwa?"

"Sunce ba sa ci, ni wata uwar ashar da aka yi mini, tunda nake ban taɓa jin irinta ba, dama ace mini matsiyaciya na saba, amma wannan ashar tayi mini zafi, wai kuma nima ta koreni barin gidan nan zan yi" Hajara ta ƙarasa maganar kamar tayi kuka.

Amina ta ɗan jinjina kai ta ce "Kiyi haƙuri, ba in da zaki in sha Allah"


Da ta gama shirinta ta windown kitchen taje ta leƙa, taga Alhaji Ahmad ya dawo.

Ta shirya ta tafi sashinsa, da kayan Abincinsa na dare.

Da sallama ta shiga, ya amsa mata yana zaune yayi shiru, alama yana cikin damuwa.
Ta zauna a kusa da shi ta ce "Sannu da zuwa"

"Yauwa Meenal, ya jikin?"

"Jiki Alhamdilillah na warware, ga abinci nayi ta so ka ci"

Daddy ya kalleta ya ce "Baki da lafiya kika yi girki?"

"Idan ban yi ba kai me zaka ci, me mutanen gidan za su ci? Naji sauƙin jikina ne, ta so ka ci"

"Meenal bar abincin nan kawai"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka ci, ga yunwa ga damuwa da wanne zaka ji"
Ganin duk ta damu ya sanya shi haƙura, ya ci Abincin da kanta ta dinga ba shi tana yi masa hira, har ya ɗan saki ransa.

"Daddy, nayi girki naga mutan gidan sun ƙi ci, duk da na san haushina suke ji, amma ni ba zan daina ayyukan da nake na gidan nan ba, daga girki gyaran part ɗinka kan na tare, gyaran ko ina ma, sashensu ne kawai Hajara ta dinga gyara musu, kuma ni zan zauna da su tsakani da Allah babu ruwana da su, ni dai fatana kawai Allah ya baka ikon yi mana adalci"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Meenal kenan, naji daɗin maganarki Allah ya dafa mana"

Ta amsa da "Amin" sai da ya gama ci, ta tashi tana masa sallama ya ce "Ba zaki kwana a nan ba?"

"Saboda me zan kwana a nan?"

"Ba zaki buƙaci wani abun ba? kije ki kwana ke kaɗai keda baki da lafiya"

"Ba abin da zai faru da ni in sha Allah, good night" tayi kissing ɗin lips ɗinsa.

Bayan tafiyar Amina, ya sake komawa wurin Hajiya Zainab, saboda yana matuƙar jin tausayinta, ya san kishi shi ne weak point ɗinta, bata ƙaunar taga wata ta raɓe shi, amma lokaci guda ya shammaceta haka.


Ko da ya tura ƙofar ɗakin, a zaune ya tarar da ita a kan gado, tayi uban tagumi.

A hankali ya ƙarasa in da take, ya zauna a kusa da ita, ya janyota jikinsa amma kamar ya haɗata da wuta, a fusace ta fizge ta ja gefe.

"Wallahi Ahmad ka kuma gangancin taɓani, sai na illataka kai saboda tsabar rashin mutunci da rashin kunya har kana da ƙwarin gwiwar tunkarar in da nake ka haɗa jikinka da nawa, kaje ka ƙarata a wurin waccan 'yar matsiyatar"

Daddy ya ce "Calm down please, Zainab duk abu kece matata ta fari, kuma ba zan so duk wani abu da zai tarwatsa kan iyalina ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki fuskance ni. Rana ɗaya gaba ɗaya kin fita hayyacinki ki rame lokaci guda"

"Kaga bana son wannan soki burutusn naka, ji nake kamar zuciyata ta fashe, na tsaneka Ahmad bana ƙaunarka ko son ganinka bana yi, na tsani mai sonka ma dalla tashi ka fita ka bar mini ɗaki".

"Na ji ba kya sona, ba komai ni ina sonki, amma kiyi haƙuri ba zan fasa baki haƙuri ba, naji na yi miki laifi na karɓa amma ina neman Afuwa, dan Allah kiyi haƙuri ki samu ko Abinci kici"

"Wallahi Ahmad kai ba ƙaramin munafuki bane ba, da can da in ci Abinci da na mutu ba ruwanka, sai yanzu zaka wani lallaɓani wai naci Abinci, ni zaka yiwa fuska biyu saboda rashin tsoron Allah?"

Munanan kalaman da Zainab ke amfani da su a kansa, ba ƙaramin ciwo suke masa ba, yana ta dannewa yana cigaba da rarrashinta amma sai cigaba take da gasa masa su yadda take so. Bai sake ce mata komai ba, ya tashi ya bar mata ɗakin.

Wayewar garin Allah, Amina ta saka a ka fitar da Abincin daren jiya da basu ji ba, aka bayar, tayi girkin safe ta ajiye musu, sannan ta je ta kaiwa Daddy nasa.
Ganinta da uniform ya sa Daddy ya ce "Baby har zaki iya zuwa makaranta?"

"Eh mana, yau zamu fara exams fa, ga Abinci nan ka karya, idan an tashi ina gidan su Azima, da magariba sai ka ɗaukeni"

"Ok shikenan, hakan ma yayi, a dawo lafiya, Allah ya bada sa'a, in sha Allah yau zan cika miki alƙawarin abin da kika yi ta nacin nan a kansa"

Waro idanuwanta tayi waje ta ce "Da gaske Daddy?"

Ya jinjina mata kai.

Jikinsa ta faɗa tana murna ta ce "Allah ya biyaka da Aljanna my love, kai mutum nagari Allah ya ƙara wadata da arziƙi Hubby"

Murmushi yayi ya rungumeta Sosai ya ce "Amin Meenalina, kema Allah ya saka miki da alkhairi da ankarar da ni abubuwa masu muhimmanci. Allah ya kawo mana wasu twins ɗin da kin gama exams Baby"

Rufe fuska ta shiga yi, saboda kunya da ta kamata.

"Ba zaki ce Amin ba"

Ɓoye fuskarta tayi a ƙirjinsa ta ce "Ni kunya nake ji"

Dariya ta bashi ya ce "Kunya kuma, madam kice Amin kawai".

"Na faɗa a zuciyata ai"

Yayi murmushi ya ce "Zo ki tafi kar ki makara, ba dan wancan uzurin ba, da ni zan kai ki, ki tafi da magungunan ki ki samu ki sha. Allah ya kiyaye hanya"

"Amin Dear na" ta tashi daga jikinsa ta fice tana ɗaga masa hannu.




A yadda Fadila take jinta, da halin da Mummy take ciki, bata ji zata iya zuwa makaranta ba.

Kafin Daddy ya fita, sai da ya kuma leƙawa wurin Hajiya Zainab, ta sake ƙare masa zagi da cin mutunci, ya fita ransa babu daɗi sam.


Ƙarfe tara, Fadila yunwa ta gallabeta taje dining ta tarar da Abinci, ta karya, ta kuma komawa wurin Mummy tana cigaba da bata haƙuri. Da ƙyar ta ɗan ci Abinci kaɗan, Fadila ta koma nata ɗakin.

Ƙarfe goma na safiya, su Hajiya Turai suka iso gidan, gaba ɗaya yadda suka zo gidan kamar masu shirin zuwa ya ƙi.
Har bedroom suka iske Hajiya Zainab, duk tayi wani iri.
Hajiya Turai ta ce "Zainab, gaskiya kinyi sake, ke kuwa kina me wannan ɗanyen aikin ya faru a gidanki? Idan ban manta ba kwanaki na ja miki kunne a kan wannan Yarinyar, amna ki ka yi biris da ni, kika nuna mini ba abinda zai iya, ga shi kwaikwaya miki rashin mutunci da rashin daraja, amma Allah wadaran halin Alhaji Ahmad, wannan ai ba budurwar zuciya bace sai dai ace bunsurar zuciya ce da shi.
Wato a baya ya buga ya buga, kin toshe bai samu kafa ba, shi ne ya ɓullo miki ta bayan gida, kai maza sai Allah"

Hajiya Salmanta ce "Uhumm ai ni gaba ɗaya kaina yama kulle, na rasa abin yi, namiji ƙanin ajali, buhun ƙaya kenan, mugu ɗan masara ana kayanka kana kayan gemu"

Hajiya Zainab ta rausayar da kai ta ce "Ban taɓa zaton Ahmad zai yi mini haka ba, na rasa mema zan sam na huce, tun jiya nake zaginsa amma zuciyata ta ƙi samun salama"

Turai ta ce "Ina ita munafukar Yarinyar take?"

"Ina na san musu, ni tun jiya ban kuma fita ko falo ba"

"Au barinta kika yi ta kwanar miki a gida? Baki ci ubanta kin korata ba"

"Hajiya Salma, al'amarin nan ya zo mini a bazata, Yarinyar nan fa a tsaye take, bata da mutunci ko kaɗan ban gane hakan ba, sai da wannan abun ya faru. Kin san mutumin nan har warning yake mini, wai in gayawa Fadila ni da ita ba ruwanmu da matarsa, Yarinyar nan idan ban bi a sannu ba ƙarshe ni ta koreni daga gidan, dan da biyu ta aure shi, dan ta rama abin da nake wa ubanta"

Turai ta ce "Ke Auzibillahi wane irin ta koreki daga gidan, ai sai dai ita ta fita ta bar shi, nijar zamu tafi wurin malamai dan ubanta sai bi daji tsirara tana hauka"

Hajiya Zainab ta ce "Hauka kuma, ni ba ruwana, kawai ta bar mini gida, yayi mata korar wulaƙanci"

Hajiya Salma ta ce "Ke dalla can banza kawai, idan ya saketa daga baya suka kuma jonewa fa, ta haukace ta bi bola kawai. Kuma ki buɗe masa wuta da rashin mutunci da tashin hankali, ki hana shi kwanciyar hankalin da zai zauna ya ji daɗin Auren, ki buɗe masa wuta ba sani ba sabo"

Haka suka cigaba da hure mata kunne, da ɗorata akan keken ɓera.



Amina kuwa tana gidan su Azima, suna falo sun ci Abinci suna hira, Daddy ya kirata yake tambayarta, ta sha maganinta kuwa?
Ta ce masa yanzu zata sha, bayan ta ajiye wayar, ta duba jakarta ta ɗauko ledar maganin.

Ammi ta ce "Baki da lafiya ne?"

"Eh amma na warke?"

"Mhmm meya sameki haka ne?"

Shiru Amina tayi ta fara kame-kame, ɗaya bayan ɗaya Ammi tabi magaungunan da kallo, ta kalli Amina ta ce "Idan kin sha maganin ki sameni a ɗakina" Amina ta amsa da to.


Kamar yadda Ammi ta umarceta, haka taje ta sameta a bedroom ɗinta.
Ammi ta kalli Amina sannan ta ce "Amina, maganin meye wannan, ki gaya mini gaskiya meye ya faru?"

Amina ta ce "Bakomai, ai na warke zazzaɓi nake yi"

Ammi ta ce "Amina, 'ya na ɗaukeki, garin yaya haka ta faru bayan baki tare ba"

Amina a ranta ta ce "Na shiga uku da wannan tereren bankaɗar, kowa sai ya san halin da nake ciki, ya aka yi Ammi ta gane wani abu?'

"magana fa nake Amina"

"Ammi ai ban gane a kan me kike magana ba"

"Laaa kun ga 'ya zata raina mini hankali? Meya haɗaki da maganin ƙarin jini na masu ciki"

A zuciyarta ta sake cewa "Wayyo Allah na shiga uku ni Amina'

A fili kuma cikin jin kunya ta ce "Ammi ai ya zube'

"Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru Amina? Ke ba kya gudun ayi miki mummunar fahimta tunda ba kowa ya san kun yi aure ba, kuma uwargidanki ta sani ki shiga uku? Tun da ba kirki ne da ita ba".

"Ai yanzu ta sani"

"Kamar yaya?"

Nan Amina ta gaya wa Ammi komai, Ammi tayi salati tana mamakin yadda abubuwa suka gudana.

Ammi ta numfasa ta yi ta yiwa Amina faɗa a kan gangancin da tayi, saboda ba kowa ya san sun yi aure ba.
Ita dai Amina tayi shiru ba ta kuma tofawa ba.


Kamar yadda su Hajiya Turai suka ɗora Hajiya Zainab a kan keke ɓera, ta cigaba da zuba wa Alhaji Ahmad rashin mutunci daban-daban.


Amina dai ta mayar da hankali, a kan jarrabawar ta, tana cigaba da kula Alhaji Ahmad.
Tun yana lallaɓa Hajiya Zainab yana bi ta kanta, har ya watsar da ita, ya cigaba da sabgoginsa.

Yayi mata maganar tariyar Amina, ya tambayeta a wani ɓangaren take son zama a gidan, amma tayi masa banza sai cin mutuncinsa da tayi ma.

Amina kuwa tana tuntuɓar Ammi, da Hajiya Maryam, a kan shirye-shiryen walimarta na tariya da kammala makarantarta.
Alhaji Ahmad ya tambayi Amina, furnitures ɗin da zai canza mata.

Amina ta ce "Ni ka bar mini na sashin naka sun isheni"

"A'a, sabuwar amarya a baki tsoffin furnitures"

"Ba wata sabuwar amarya'

"Sabuwace mana" yayi maganar yana murmushi.

"Daddy, ni dai ka bari ko babu yawa Baba ya sai mini ba sai ka saya ba"

"Saboda me ba zan saya miki ba? Duka furnitures ɗin gidan ma sauyawa zan yi, dan haka ba ruwanki, ba alhakin Baba bane ba, na bawa Hajiya Maryam kuɗin kayan lefenki"

"Wayyo daɗi, duka ni kaɗai, Kana ji da ni Daddy"

"Ba dole na ji da ke ba 'yar Babyna"

suka Cigaba da hirarsu, cikin soyayya da kulawa.


Hatta Fadila sai ta ga dama take gaida Daddy, saboda haushinsa take ji, ya jefa Mummy cikin halin damuwa.

Amina rayuwarta take yi a gidan hankali kwance, ko shiga sabgarsu bata yi, sai dai wasu lokutan Hajiya Zainab idan suka haɗu ta kan ci mata mutunci. Amina sai dai ta ce "Ni ba zan biye miki ayi ɓarin mutunci ba, ko bance miki komai na riga na gama da ke, zagi da cin mutuncin da zaki yi mini, ba zai canza komai ba. Dan haka ki cigaba kar ki fasa, kece a wahale bani ba. Kuma zan cigaba da baki mamaki a gidan nan ta in da baki zata ba, su kansu 'ya'yan da kike taƙama da su, idan har baki canza hali ba, suma sai na rabaki da su, saboda wautarki"

Hajiya Zainab ji take kamar ta kashe Amina ta huta da baƙin ciki.


Yazid ya lura da mood ɗin Fadila a 'yan kwanakin nan, bata walwala ku san kullum yanayinta babu daɗi, hakan ya sanya yake jin shima babu daɗi a ransa, sai dai ba ya jin zai iya zuwa ya tunkareta yaji damuwarta.


Hajiya Zainab na zaune a falo, tana shan shayi, gaba ɗaya bakinta babu daɗi, abu mai ruwa-ruwa kawai take iya sha, a cikin abin da bai fi sati biyu ba gaba ɗaya ta zabge, ta fita hayyacinta.

Alhaji Ahmad ya fito daga sashinsa, Amina na binsa a baya, kallo ɗaya tayi musu ta kawar da kanta taji kamar ta ɗora hannu a ka ta zabga ihu, Yarinyar da sai dai ta bata umarni a da, ta ci mutuncin ta son ranta, wai ita ce yau ta aure mata miji, da alama ma hankalinsa a kwance yake.

Suka ƙarasa falon, Daddy ya zauna, Amina ta zauna a kusa da shi.

Ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Hajiya ina kwana?"

"Ya kwana a ɗakin uwarki" ta bawa Amina amsa.

Amina murmushi tayi ta ce "Na gode"

"Zainab, ba zaki taɓa canzawa ba ko? Yarinyar nan na ƙoƙarin mutunta ki, amma sai zubar da mutuncinki kike yi, ai shikenan dama ina son sanar da ke, in Allah ya yarda jibi, za a fita da furnitures ɗin gidan nan gaba ɗaya. Zan zuba sababbi sannan akwai walima na tariya da kammala makarantar Amina. Zata zauna ne a part ɗina shine nata ɓangaren. Sannan sai kuma maganar raba kwana".

Tamkar saukar wuta haka ta dinga jin zubar maganganunsa a zuciyarta, ko kunya baya ji.

"Ban gane zata tare a ɓangaren ka ba, idan har kana son zaman lafiya, ka kaita duk in da kake so ka ajiyeta, amma banda gidana".

Daddy ya ce "Ba zan raba kan iyalina ba, a nan zata zauna, kuma kamar yadda na tambaye ki da farko, kina son part ɗinki ko in canza miki, baki zaɓa ba, dan haka Amina zata tare a sashena"

Miƙewa tayi a zafafe ta ce "Baka isa ba, kayi kaɗan wallahi sai ta bar gidan nan ka kaita koma ina ne, amma ba gidana ba"

"Ba shawararki nake nema ba, hukunci

Please Login or Register in order to submit comment