Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki a kan abin da ba kya so ba kinji sweetyna"

A ranta ta ce "Innalillahi, me Daddy ya zama ne?"

Haka yayi ta surutunsa, ita dai ba ta ce masa komai ba suka cigaba da tafiya.

A bakin layin ya ajiyeta, ya ce "Maza daga nan ki wuce gida, kije ki samu ki huta, sai mun yi waya" kai kawai ta ɗaga masa, ta fice daga motar da sauri, ta shiga layin.

Daga nan Kai tsaye wurin Alhaji Sambo ya wuce, ya gaya masa yadda suka yi Amina, Alhaji Sambo ya ce "Shawarar da zan baka ita ce, ka cigaba da lallaɓata sannu a hankali, tunda yarinya ce ƙarama, kar ka nuna zaka yi mata dole, komai zai zo da sauƙi in sha Allah".

Daddy ya ce "Allah ya amince, ina fatan ta amince ɗin, kamar tana sona shirirtarta ce ta dameta shiyasa ba ta gane hakan ba".

Alhaji Sambo yayi dariya ya ce "Ai shirirtar kake yiwa, kawai ka cigaba da wasanka, sai dai kayi taka tsantsan kar wannan masifaffiyar matar taka ta sani, dan wallahi ta sani yarinyar ta shiga uku ne".

"Ai ba zan bari ta sani ba, ina sane da duk abin da nake yi".

Alhaji Sambo ya cigaba da ba shi shawarwari, daga bisani suka yi sallama.

Ko da taje gida ɗakinta ta wuce, tana tunani tana jujjuya maganar da Daddy yayi mata, ita kaɗai ma a ɗakin sai kunya take ji, tana sake jin abun wani iri.

Da daddare ta gama shirinta, ta zauna ta ɗauko littafinta tana karatu, kawai sai taga wayarta tana ringing, ta duba taga Daddy ne, taƙi ɗagawa ta zubawa wayar ido.
Ya kirata ya kai sau uku, amma taƙi amsa wayar.

Saƙonsa ne ya shigo wayar "Meenali meyasa ba kya ɗaga wayata?"

"Bakomai" ta tura masa dan shirme.

"Wai duk a kan maganar nan ne, dan Allah ki saki ranki, ki ɗaga wayar muyi magana". Yana tura mata saƙon ya kuma kiranta a waya, jiki na rawa ta ɗaga, ji take kamar a gabansa take kunya na sake ratsata.

"Duk dan nace ina sonki shi ne kika ƙi amsa mini waya?" Tayi shiru.

"Meenal, ke ma'abociyar ilimin addini ce, abin da na nema a wurinki, bai saɓawa addini ba, ki kalleshi a ma'aunin Addini ba al'ada ba, kin ji, ni dai fatana ki saurari zuciyarki ki gani idan zaki iya aurena ki zauna da ni, amma idan da wanda kike so ba zan takura miki kinji"

"To"

"Yauwa, na san wataƙila yanzu kina karatu ne, ayi karatu lafiya" ko sallama ba ta yi masa ba ta kashe wayar gaba ɗaya.

Babu wanda ta gayawa abin da ya faru, da abin da Daddy ya ce mata. Sai dai duk abin da zai haɗa su kauce masa take yi, ta koma shiryawa da uwar safiya ta tafi makaranta, idan ta dawo kuwa ba zata bari su haɗu ba, ta wuni a ɗaki. Ta daina kunna wayarta gaba ɗaya, dan karma ya kirata ya sameta.

Ranar wata juma'a, bayan ta dawo daga makaranta, Hajiya Zainab ta tafi yawon bikinta, Fadila kuma na makaranta. zaton Amina Daddy ma baya gida, dan haka ta fito falo tana cin kantu a leda, tana goge goge, ba tsammani ta juya ta ganshi a tsaye yana kallonta. Gaba ɗaya ta rikice ta na neman wurin ɓuya, kamar wadda ta yada zani a gaban siriki.

Yayi murmushi yayi mata alamar ta zo. Ji tayi kamar kar taje, sai kuma taga idan tayi hakan baya kyauta ba, dan haka tabi bayansa.
Bai tsaya a ko ina ba sai a tsakiyar falonsa. Ya kalleta ya ce "''yar Babyna, laifin me nayi miki kuma kike guduna, kika dai na amsa wayata?"

Tayi shiru tana wasa da ledar hannunta.

Ya miƙa mata tafin hannunsa ya ce "Ɗan sanmini abin da kike cin"

Ba musu ta miƙa masa ledar kantun.

Ya ce "Zaki bani abin hannunki amma kina guduna ko, dan Allah ki bar wayarki a kunne muyi magana da daddare kinji?"

Ta amsa da to, ya ce "You can go, ko in zo in tayaki aikin ne"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Hmm to shikenan, sai munyi wayar, jeki ki cigaba da aikin ki" ita dai ba tace masa ƙala ba ta bar falon.

Da daddare da Daddyn ya kirata ma dai, shirun tayi masa yayita kiɗansa yana rawarsa, bata iya ce masa komai, sai ya gama wayar ta ajiye tana dariya.

Suna daf da fara jarrabawa, ta shirya zata tafi makaranta, ta fito falo ta tarar da Baba a durƙushe a gaban Hajiya Zainab, sai banbamin bala'i take yi masa. Cak Amina ta tsaya ta rasa abin da za tayi ko ta ce, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, tana ta ci masa mutunci, Amina ba ta san laifin da Baba yayi mata ba, sai da tayi ta gama ta sallmeshi, sannan Amina tabi bayan Baba.

Cikin sauri ta ƙarasa ta cimmasa "Baba" ya tsaya ya waiwayo ya kalli Amina.

Ƙwalla ta gani kwance a idon Baba, ya dake ya ce "Makarantar zaki ne?"

"Baba me kayi mata take maka wannan rashin mutunci da sassafe"

Baba ya ce "Kar ki damu, Kina da kuɗin makaranta ko na baki?"

Hawaye Amina ta fara yi, wani irin tausayin Baba ya sake kamata.

Saura ƙiris hawayen idonsa ya zubo, amma ya dake ya ce "Yi maza ki tafi kar ki makara"

Haka Amina ta tafi makaranta tana kuka, gaba ɗaya haka taje makarantar bata walwala.

Azima tai ta tambayarta meke damunta, amma taƙi gayamata sai kukanta kawai take.

Da aka tashi daga makaranta, sun fito zasu tafi, Amina ta ce "Azima kinga sabon dabino, muje na sayawa Baba yana son sabon dabino sosai"

Azima ta raka Amina, suka sai dabino, Azima ba ƙaramin burgeta Amina take ba, saboda alaƙarta da Babanta, dan ita nata mahaifin ya daɗe da rasuwa.

Amina ta kalli Azima ta ce "Azima wannan dabinon sai dai kiyi haƙuri, na Baba ne, dan haka ni da ke ba mai ci"

Azima tayi murmushi, ta ce "Ai nima mai saya ce in baki ki kai wa Baba. Amina ina fatan ubangiji Allah ya baki miji nagari a garin nan, wanda zai riƙeki amana ya raba Baba da wannan aiki a ƙarƙashin mutanen gidan nan naku marasa mutunci"

Shiru Amina tayi tana nazartar maganganun Azima, kamar ta tunatar da ita wani abu mai matuƙar muhimmanci, da sauri Amina ta ce "Azima na gode, sai Allah ya kaimu gobe" ta nufi titi tana cigaba da juya maganar Azima a ranta.

Baba yayi murna da dabinon da Amina ta kawo masa, Yayi ta yi mata addu'a.

Amina da taje ɗakinta, tayi salla ta dinga tunanin maganar Azima, Allah ya bata miji nagari wanda zai raba Baba da aikin gadi.

"What if na Auri Alhaji Ahmad, kenan Allah ma ya riga ya bani ban ankare ba" tayi maganar tana murmushi.

Amina ta wuni ta na nazarin maganar Azima.

Kamar kullum da daddare, Amina na tsaka da karatu, Daddy ya kirata, yau ba jan aji ta ɗaga wayar.

"Hello 'yar Babyna"

"Daddyna" ita kanta da ta faɗi hakan sai da kunya ta kama ta.

"Wow, amma naji daɗi sosai, ya school ɗin 'yar Babyna?"

"Alhamdilillah, ya aiki?"

"Aiki kam akwai shi, kin bani aikin tunaninki Sweetheart, ina cikin damuwa, duk na rame".

Cikin kulawa ta ce "Daddy damuwar me kuma?"

"Kin ƙi bani amsa zaki aureni, kince ba kya sona"

Amina ta ce "Ka tambayi Baba duk abin da yace maka shikenan"

"Kina nufin idan Baba ya amince zaki aureni?"

A kunyace ta ce "Mmm, amma kar kace masa ni nace ka tambayeshi"

Wani lumshe ido yayi yana murmushi ya ce "Thank you Meenalina, idan har Baba ya amince na aureki, zan baki farinciki da kulawa iya yina"

"Hmm sai anjima"

"Au ba zaki tsaya muyi hirar ba, a haka za mu yi auren Babyn, Ahmad yana sonki sosai fa"

Kashe wayar Amina tayi, ta dafe ƙirji tana murmushi ta ce "Daddy dama haka kake? Sai kunya yake bani, innalillahi wa yaga na auri Daddy".

Ta shiga what's app ɗinta, ta duba hotunansa da yake turo mata.

"Wayyo Allah na, masha Allah Daddy fa yana da kyau, ga shi da gemu ga gayu. Yana aura ta zan saka Baba ya bar aikin gadi a gidan nan, kuma duk wani mai rabo sai yaci arziƙin da ake wulaƙanta mu a kansa, wayyo zuciyata". Tayi maganar tana tsalle a kan katifarta

Daddy kuwa jinsa yake tamkar ya taka rawa, saboda tsabar farinciki da jin daɗi, washegari da safe Alhaji Ahmad ya koma wurin Alhaji Sambo, ya sanar masa.

Alhaji Sambo ya ce "Alhamdilillah, yanzu abin da ya rage kan ka tambayi mahaifin nata aurenta, zan fara zuwa garinsu, nayi maka bincike a kansu tukuna dan ko ba komai yakamta ka san wa zaka aura, Daddy ya ce hakane.

Alhaji Sambo da kansa ya je Shanono, yin bincike a kan dangin su Amina, ya samu kyawawan bayanai a kan mahaifinta, sai dai sai da aka gaya masa batun guduwa da Amina tayi daga garin za ayi mata aure.

Da Alhaji Sambo ya dawo wa da Alhaji Ahmad da sakamakon binciken sa, Alhaji Ahmad ya ce Bakomai, da ta gudun ai wurin Baba ta taho nan gidansa, hakan ya ƙara bawa Alhaji Ahmad ƙwarin gwiwar zuwa ya tunkari Baba Hassan.

Malam Hassan yayi mamakin ganin Alhaji Ahmad a ɗakinsa na gadi.

Suka gaisa da Baba, gaba ɗaya jikin Baba yayi sanyi, saboda tsananin mamaki har tsoro yake kar wani laifin yayi.

Alhaji Ahmad ya duni Baba cikin nutsuwa ya ce "Malam Hassan, na san zaka yi mamakin ganina a daidai wannan lokaci, sai dai na zo ne domin wata muhimmiyar magana sosai da sosai, amma ina son ka kalli maganata a mahangar  addini, wata alfarma na zo nema a wurinka, ban sani ba ko zaka iya yi mini"

Baba ya ɗan yi shiru yana tunanin wace irin alfarma ce haka, ya numfasa ya ce "In dai bata fi ƙarfina ba, kuma bai saɓawa addini ba in Allah ya yarda zan maka"

Alhaji Ahmad ya ce "Masha Allah, abu ne na alkhairi, da nake saka ran ya zame mana alkhairi a tsakaninmu. Malam Hassan ba wata alfarma ba ce ba, Auren Amina nake son ka bani, ina son zan aureta idan ka amince"

Jimmm Baba yayi, yaji maganar daga sama, wani banbarakwai.

"Malam Hassan, ba takura maka zan yi kayi mini abin da baka yi niyya ba, ba takura muku zanyi ba, idan kana ganin babau damuwa ina son ka bani aurenta, ta zama a ƙarƙashin kulawata"

Baba yayi shiru sannan ya ce "Amma Yallaɓai, wannan lamari da ka zo da shi yayi girma da yawa, al'umma za suyi mana kallon butulallu, daga zuwa cin arziƙi, shikenan kuma sai ka auri 'ya ta"

"Malam Hassan kar ka damu da wannan, ai addininmu bai hana ba, idan kana ganin babu damuwa ina neman wannan alfarmar, amma zan baka dama kayi shawara tukuna"

Malam Hassan ya ce "To shikenan, Allah ya wuce mana gaba".

Bayan kwana da biyu da yin maganar, Baba ya dage yana Addu'a a kan lamarin, baya son yayi jayayya a kan lamarin, saboda ya lura da tun kan Alhaji Ahmad ya gaya masa, Ya lura da yadda kusancin Alhaji Ahmad da Amina yayi yawa.
Dan gaba ɗaya ta daina jin nauyinsa,  ƙarewa ita ma Daddy take ce masa, baya son ya zaƙe ya zo yaji kunya daga baya.

Amina ta kai masa Abincin dare, ya tsayar da ita, ya ce "Uwata magana za muyi"

Ta ce "To Baba".

"Maigidan nan ya zo mini da wani zance na cewar wai yana sonki, zai aureki, duk da dai alamu sun nuna kun gama fahimtar juna kan maganar ta iso gareni"
Nan Amina ta tubure a kan cewar ita bata san zancen ba.

Baba yayi murmushi ya ce "Hmm koma dai mene, ki je kiyi ta addu'a, sannan idan kina son mutumin nan zaki aureshi, ki aure shi saboda Allah ba wani abu ba, kuma abu na gaba ina jinjina yadda zaki da iyalansa, sannan kuma ga batun karatunki bana son karatunki ya tsaya".

"Ai ya ce saina gama karatu x

Baba ya ce "Kuma ki ka ce baki san zancen ba" da sauri Amina ta shiga taitayinta, ta tuno katoɓarar da tayi.

Baba ya ce "Tashi kije, ki cigaba da Addu'ax

Amina ta tashi ta tafi.

Baba ya duƙufa yana ta Addu'a a kan lamarin, saboda ya lura da yadda ita kanta Amina ke da rawar kai, kuma ya fuskanci tana son Alhaji Ahmad ɗin.

Alhaji Ahmad kuwa ya cigaba da lallaɓa Amina, yana kyautata mata tare da yi mata alwashin bata kulawa idan sun yi aure.

Baba ya bawa Alhaji Ahmad damar ya je garinsu ya nemi auren Amina a wurin su Kawu Bala.
Ahmad ya je ya sami 'yan uwan mahaifinsa, ya sanar musu da yana son suje Kano Shanono su nema masa aure.
Familyn Alhaji Ahmad sun yi farinciki da jin cewa zai yi aure, dan kusan duk a ciki suke da Hajiya Zainab, da yadda ta kainanaye Musu ɗan uwa, ta hana shi sakat ta rabasu da shi.

Be gaya musu wa zai aura ba, kawai ya ce su je su nema masa Aure. Za'a ɗaura masa aure yanzu, amma tariya sai bayan shekara ɗaya zata tare.




AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


59

Ba tare da Amina ta sani ba, Baba ya bawa Alhaji damar zuwa ya nemi auren Amina a wurin yayyensa su Kawu Bala.

Dangin Alhaji Ahmad da suka ji batun zai yi aure, amma tariya sai bayan shekara guda, suka dinga murna kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha, a dangin nasa ba kowane ya san zai yi auren bama, sannan bai yadda sun san wa zai aura ba, kawai ya ce wa 'yan uwansa za aje nema masa Aure a Shanono.
Lokacin da suka je wa su Kawu Bala da maganar, suka dinga kushe Amina, da faɗar miyagun maganganu a kanta, 'yan uwan Alhaji Ahmad suka ce babu ruwansu shi ya ce yaji ya gani. Baƙin ciki da hassada kamar Ya kashe su Baffa Lawan, saboda su so su kayi Amina ta dawo a ƙasƙance cikin tozarci.

Suka bada maƙudan kuɗi, a matsayin kuɗin Auren Amina, aka sanya sati biyu kacal zasu dawo a ɗaura Aure.
Amina bata san budurin da ake yi ba, tana can tana jarrabawa.

Ranar wata juma'a, Daddy da jama'arsa suka tafi Shanono, Baba ya ce wa Amina zai je ƙauye, bata san me zai je yi ba, tayi masa Allah ya tsare, lokacin suna jarrabawa kuma sun daf da yin wannan tafiyar.

Har aka je Shanono aka ɗauro mata aure, bata san an yi ba.
Tun da aka ɗaura auren nan Alhaji Ahmad yake jinsa kamar a wata sabuwar duniyar yake jinsa, sai dai da yaga Hajiya Zainab sai gabansa ya faɗi.
Da ya dawo daga ɗaurin Aure ya tarar da ita tana mopping, ji yayi kamar ya karɓa yayi mata.

"Amaryata" ya faɗa lokacin da ya zo kusa da ita.

Waige waige ta shiga yi, dan kar ta je wani yaji me ya ce.

Ta ce "Ni dai kar ka janyo mini tashin hankali, a falo fa muke"

Murmushi yayi, ya wuce yana jin nishadi na ratsa shi.

Baba bayan ya dawo, ya kira Amina a waya, ta zo ta same shi, ta kasa gane me take gani a fuskar Baba, farinciki ko kuma damuwa.

"Uwata" ya kira sunanta.

"Na'am Baba"

"Kowane abin halitta da kika gani a doron duniya, tun kan Allah ya samar da shi ya tsara masa abin da zai same shi, me kyau da akasin haka.
Ranar juma'a, an ɗaura miki aure ke da Alhaji Ahmad".

Waro ido tayi ta dafe ƙirji ta ce "Baba aure kuma? Dama yanzu za ayi auren?"

"Eh, shi ya buƙaci hakan, idan kin gama jarrabawa, zaki je ƙauye za kuyi wuninku na mata, amma ya tabattar mini da ba zaki tare ba sai Allah ya sa kin gama karatunki"

Ai sai Amina ta fashe da kuka.

"Kefa kika nuna mini kina so, meye na kuka kuma? Ni dai fatana ki tsare mutuncinki yanzu da da akwai banbanci, yanzu kina da Aure saɓanin da. Sanan ki rage wannan rawar kan naki, kuma ki kula da kanki, kinga dai baki tare ba sai Allah ya sa kin kammala karatunki, to ki kula ki jira ki tare, kin san dai me nake nufi. Sannan ki duƙufa da Addu'a, dan na san wannan auren naki ko a yanzu ko a gaba, zai zo da tangarɗa".

Ai gaba ɗaya daina gane Abin da Baba yake faɗa tayi, ya gama gaya mata abin da zai gaya mata, ita babban abin da take hangowa idan an tashi graduation shagalin da za ayi ba zata sake ba sosai saboda tana da Aure.

Jiki a sanyaye kamar wadda aka bawa saƙon mutuwa, haka ta tafi ɗakinta, ta rufe ƙofa ga zauna ta dinga kuka, sai da tayi mai isarta, sannan ta tashi saboda kiran salla tayi alwala.

A Kitchen haka Hajara ta addaba mata a kan meya sameta a fuska, fuskar ta kumbura, amma tace mata bakomai.
Da suka gama girki ma, ɗakin ta koma tayi zuguum, ko Abinci ta kasa ci.

Wayarta ce ta fara ringing a kusa da ita, cikin ƙwarin gwiwa ta ɗaga wayar, za ta yiwa Daddy tsiwa, saboda ya sa an ɗaura mata aure ba da saninta ba, amma ajiyar zuciya da yayi ta wayar, kawai taji bakinta ya mutu.

"Sweetheart ba magana?" Tayi shiru taƙi cewa uffan.

"Magana fa nake yi, ko mulkin ne ya motsa?"

Kawai ta fashe da kuka iya ƙarfinta.

A rikice ya ce "Subhanallah, Amina menene?" Ta katse wayar ta ajiye, ta cigaba da kuka.
Tana kallo ya cigaba da kiran wayar, amma ta share shi.
Washegari tana shirin makaranta, yana cigaba da rangaɗa mata waya, amma taƙi ɗagawa.

"Idan ba zaki ɗaga wayar ba, idan an tasheku daga school, ki jirani zan zo na ɗaukeki, sai muyi magana amma kin tayar mini da hankali Meenali" tana gama karanta saƙon ta murguɗa baki, ta ajiye wayar tayi ficewarta.

A makaranta ma gaba ɗaya ranar bata walwala, ana tashi daga makaranta ta cewa Azimi gidansu zata bita.
Azima bata takurata sai taji meke damunta ba, suka tafi gidansu Azima tare.

Kamar kullum, Ammi na ganinsu tare, kamar ta goya Amina. Ta karɓi Amina cikin sakin fuska, amma taga fuskar Amina a haɗe.
cikin damuwa Ammi ta ce "Aminatu, mene? Na ganki duk wani iri". Ai kamar jira take yi, ta fashe wa Ammi da kuka.

Ammi ta rungumeta tana rarrasinta, sai da ta samu ta tsagaita da kukan, sannan ta kalleta ta ce "Gaya mini, menene?"

"Ammi Aure aka yi mini" ta faɗa tana fashewa da wani kukan.

Azima ta ce "Aure kuma?"

Ammi ma abin ya ɗaure mata kai, ta ce "Yi mini bayani Amina, shi Baban ne ya yi miki auren ko kuwa kamr yaya an miki aure?"

Amina ta zauna ta warwarewa Ammi komai, har zuwa ɗaura mata aure da aka yi.

Maimakon Ammi ta ɗaga hankalinta ita ma, sai kawai tayi murmushi.

Azima ta ce "Taɓɗijan, dama duk wannan Daddy da Meenal ɗin da ake sonki yake, amma dai anji kunya raƙumi ya shanye ruwan 'yan tsaki"

Ammi ta ce "Ubanki ke dai raƙumin fitsararriya, ni kaina da zan samu wani dattijon arziƙin kamarsa dana aura masa ke. Tashi ki bani wuri ma zan yi Magana"

"Ammi kiyi haƙuri" Azima tayi maganar cikin shagwaɓa.

"Zaki tashi ko sai ni na tashi" Azima ta tashi sum sum ta bar wurin, tana ta mamakin yadda wannan lamarin ya kasance.

Ammi ta sake matsawa kusa da Amina ta ce "Kina jina ko Amina? Ita rayuwar duniya a duk lokacin da kace wani bai isa ba, sai Allah ya nuna maka kaine baka isa ba, ki duba wulaƙanci da cin zarafin da matar gidan ke yi miki ke da mahaifinki, amma da yake Allah sannu a hankali yake hukunta bayinsa sai ya ƙaddara aure a tsakaninki da mijinta.
Da farko abin da zan gaya miki shi ne kiji tsoron Allah, ki saka a ranki kema wata dama ce Allah ya ara miki, idan kin yi amfani da ita yadda ta dace, ki rabauta, akasin haka kema zaki ga abin da ba kya so.
Meye a ciki Allah ne ya kashe ya baki, meye aibunsa, Allah ne ya kawo lokacin da zaku huta, dan haka karki damu, kiyi ta addu'a sannan zan yi iya ƙoƙarina in ga kin yi abin da ya dace a gidan mijinki. Yanzu ta san an yi auren?"

Amina ta ce "A'a, wai sai mun gama makaranta zai gaya mata sai na tare"

"Ahh to babu laifi, babban abin da nake so da ke shine, ki kula da kanki kinga yanzu kina da aure, banda biyewa su Azmia saboda yanzu ke da su ba ɗaya bane ba" Ammi ta zage sosai ta dinga yi mata nasihohi.
Amina dai jin Ammi kawai take yi, amma gaba ɗaya ta rasa in da zata saka kanta, a kan Aurenta da Daddy yayi da gaggawa haka.

Ammai ta ce "Idan kun kammala jarrabawar, kan ki tafi ki zo nan, a gyara miki kai, a yi lalle"
Amina ta jinajina mata kai, sai Yamm sannan Ammi ta saka direba ya kai Amina gida.

Gaba ɗaya jinta take kamar ba ita ba, wai an ɗaura mata aure, ta zama matar Daddy, gani take tamkar mafarki.

Gaba ɗaya ta nemi kuzarinta ta rasa, da daddare ta fita kaiwa Baba Abinci, ta hangi Daddy a dining, suna cin Abincin dare, ya ƙura mata ido ba tare da kowa ya lura ita yake kallo ba.

Zumɓura masa baki tayi ta wuce, da ta lura iya yake kallo, murmushi kawai yayi mata, ita kuma ta fice daga falon.

Da ta kaiwa Baba Abincin ma, nasihohi ya cigaba da yi mata, a kan ta kula da kanta, tun da yanzu tana da aure, kuma ta tsare mutuncinta sannan ta cigaba da Addu'a, Allah ya sassauta abin da ka iya biyo baya, idan har iyalansa suka san meyafaru.

Bayan Amina ta dawo daga wurin Baba, ta tarar da dining kaca kaca, ko arziƙin haɗe kwanukan da suka ci Abinci ba suyi ba.
Tsaki tayi, ta wuce dining ɗin, ta tattare kwanukan, ta gyara wurin tsaf.

Ta wuce sashinsu, ta tattara kwanukan da aka ci Abincin faren tana wankewa, sai ga Hajara ta shigo Kitchen ɗin.
"Yauwa Amina, ance ki kaiwa maigidan nan shayin dare, da kayan marmari" shiru Amina tayi mata ta cigaba da aikinta.

"Amina magana fa nake miki"

'Ai naji ko" Amina ta faɗa a hasale.

Ta gama abin da take sannan ta dafa shayin da Fruit ta kai masa, tun da tayi sallama yake binta da ido, a ƙasan maƙoshinsa ya amsa mata.

Ba ta ce masa uffan ba, ta ƙarasa ta ajiye masa, ta juya zata tafi.

"Amina" ya kira sunanta kai tsaye yau ba karantawa, sai taji wani dammm babu daɗi, ta juyo ta dawo tana tura baki, ta tsaya masa a ka.

"Sai kaina yayi ciwo, kika tsaya mini a ka?"

Neman wuri tayi ta zauna a ƙasa, saukowa ya yi ya zauna a kusa da ita ya ce " 'yar Babyna me nayi miki ne? Na ce miki zanje school ɗauko ki, kika yi tafiyarki, kin daina mini magana me yayi zafi?"

"Daddy shi ne kuka haɗa kai da Baba ka aureni, ba cewa aka yi sai na gama makaranta ba, amma Baba ya ce wai an ɗaura mana aure" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Murmushi yayi, bai zaci Baba ya gaya mata ba, ya so sai taje ƙauye ta ji.

"To meye a ciki? Shine dalilin fushin dama? Bana son in zauna zaman jira wani ya zo ya canza miki ra'ayi, kiyi haƙuri ki daina kuka. Zan saka Zakiru ya kai ki. Ai ba abin damuwa bane ba, kema sai hankalinki yafi kwanciya kina ganin mijinki ko sweetyna?" Tura baki tayi alamar baya gamsu da maganganunsa ba.

"Ki kwnatar da hankalinki, ba wani abu ai, na ƙara miki kuɗi a account ɗin ki idan da akwai abin da kike buƙata"

Yayi ta janta da hira, har ta ɗan sake, sukayi sallama ta tafi.

Kamar yadda Ammin Azima ta umarceta, ta je aka yi mata gyaran kai, aka yi mata lalle tayi kyau tayi shar da ita.
A tsakanin kwanaki ukun nan, Ammi ta sanya aka yiwa Amina ɗinkuna masu kyan gaske, tayi mata sayayyar kaya masu kyau, Azima sai tsokanarta take yi, ita kuma da tuna Azima ita free take amma ita an yi mata aure, sai ta hau kuka.

Zakiru ne ya kai Amina ƙauye, tare da wannan uban kayan Abinci da bata san da su ba, mutane suka dinga zuwa ganinta, saboda yadda tayi kyau ana ta mamakin yadda ko ranar ɗaurin Aure babu wanda ya ga angon nata.

Ranar wunin biki kuwa, sai ga Maman Azima tare da Azimar sun zo, Amina bata taɓa zaton zasu zo mata b, tayi ta murna tana jin daɗi.

Tun da ake biki a ƙauyen, ba a taɓa yin bikin da aka ci

Please Login or Register in order to submit comment