Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gata kuma da barkwanci.

Mutumin ya ce "Na ji daɗin wannan karamci na Hausa Fulani, kuma ina fatan zan kawo ziyara garin Kano domin tabattar da abin da kuka yi mana presenting game da ƙabilarku, sai dak kafin in zo Kano a bani mata da saniya, na bawa wannan yaran da suka yi presenting ethnic groups ɗinsu naira dubu ɗari biyar kowannen su, ita kuma wadda ta ce zasu bani kyautar mata da saniya, na ƙara mata naira dubu ɗari biyu a kai, sannan akwai kyautuka na musamman ga makarantar da tayi nasara, zan bada kuɗin a ranar da za a rufe ceremony.

Nan aka yi ta tafi ana shewa, aka shiga kaɗe kaɗe da raye-raye a hall ɗin, kamar yadda aka saba a duk lokacin da aka kammala presentations ɗin ranar.

Wannan mutumin na ɗazu ne da ya basu kuɗi, ya sa aka kira masa Amina ya tsareta da surutai.

Suna cikin magana ne taga Joseph ya nufo su, Amina ta kalli mutumin ta ce "An zo ɗaukata, zan tafi"

Ya ce "Shikenan sai mun haɗu gobe"

Ta jinjina masa kai, ta cewa Joseph tana zuwa, taje ta ɗauko jakarta, ta ɗora after dress a kan kayan, tabi Joseph suka fice daga hall ɗin. Ta tambayi Joseph yaushe suka zo?.

"Ai tun kan ku gama Quiz muka zo tare da Oga".

"Amina ta ce Amma ya aka yi ban ganku ba?"

"Eh ai yau ba a wurin baƙi na musamman ya zauna ba" ta gyaɗa kai, suka ƙaraso wurin mota.

Ko da ta buɗe bayan motar ta shiga, fuskar Daddy sam babua annuri, ya haɗe rai tamau bata taɓa ganin ya ɓata fuska haka ba sai yau.

"Daddy lafiya kuwa?" Tayi maganar cikin fargaba. Banza yayi mata ya kawar da kansa.

Ba ta haƙura ba ta kuma cewa "Ko wani abu ne ya samu Khalil?"

Still ya kuma yi mata shiru, Amina tayi shiru da bakinta, har suka ke gida bai ce mata komai ba, bayan sun shiga cikin gidan kasa jurewa tayi, tabi bayansa tana masa Magana.

"Daddy dan Allah idan laifi nayi maka ka gaya mini mana, ko wani abin ne ya faru?"
Tsayawa yayi cak ya kalleta, sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta tsaya tana kallonsa. Duk da tazarar da ke tsakaninsu, haka ya sanya hannu ya janyota, ya fara ƙoƙarin cire after dress ɗin da ke jikinta.

Kwanakin nan ta kasa gane kan Daddy gaba ɗaya, yana tsiro mata da wasu ɗabi u da bata san shi da su ba, a baya ba ruwansa da ko kai hannu kusa da ita, amma yanzu ta kasa gane kansa.

Riƙe rigar tayi tana faɗin "Daddy meye haka?"

Idonsa jawur, ya cigaba da ƙoƙarin cire rigar jikinta.

Riƙe rigar tayi tana ihu, amma yafi ƙarfinta, sai da ya cire after dress ɗin kan kayanta, ya rage sai kayan saƙin fulanin da tayi presentation da su a jikinta.

"Daddy meye haka ne?"

"Shut up!" Ya daka mata tsawa, sai da ta razana.

"Ke baki ji kunyar kanki ba? Kalli kayan da suke jikinki, da su kika fita gaban mutane kina rawa kina da hankali kuwa?"

"Amma Daddy ai kayan basu matsani ba"

"Basu matse ki ba ko? That's good for you"

Ya juya yana huci, ya bar ta a tsaye a falon.

Amina sai murna ta koma ciki, tana murna ta samu kuɗi masu yawa, tana son ta gayawa Daddy ya tayata murna, amma yayi fushi bata taɓa zaton ya iya fushi haka ba sai yau.

Ɗakinta ta wuce, tayi wanka ta canza kaya, yunwa take ji sosai, ta fito falon ta tarar da Daddy a zaune, ya lumshe idonsa yayi shiru.

"Daddy me zan girka maka?"

"Na ƙoshi" ya bata amsa a taƙaice.

"Dan Allah Daddy kayi haƙuri, na san nayi kuskure, ba zan sake ba in Sha Allah"

Tashi yayi ya barta a wurin ba tare da yace mata komai ba.

Jiki a sanyaye ta tafi Kitchen, ta tarar da kayan Abinci an sayo an ajiye, ta dafa indomie, amma ta kasa ci jinta take kamar ba ita ba komai ma baya mata daɗi, ta ɗau wayarta ta kira Daddy, amma ya ƙi ɗagawa, ta tura masa saƙonni na ban haƙuri, amma yaƙi tankawa.

"Daddy am sorry, kayi haƙuri mana" ta furta maganar lokacin da take sake tura masa wani saƙon.

Bata gaza ba, ta kuma fita falon, ta hango ƙofar ɗakinsa a buɗe. Cike da fargaba ta nufi ƙofar ɗakin, ta leƙa amma ba ya ciki.

Dawowa tayi falo ta zauna tayi tagumi, abin duniya ya isheta, shi haka yake idan yayi fushi, abin nasa babu sauƙi sam, bata taɓa zaton ya iya fushi haka ba.


Kamar yadda Alhaji Ahmad ya yiwa Hajiya Zainab alƙawari, ya tura mata kuɗin da ta nema a wurinsa, kuma ya bata, da taga alert jiki na rawa ta kira Hajiya Salma a waya ga sanar nata kuɗin nan sun samu, suka yi ta murna tare, Hajiya Salma ta tura mata account number ta tura mata kuɗin nan. Ta kira Mummy a waya tana cigaba yi mata godiya, daga nan kuma suka faɗa hirar batun Khalil.

Hajiya Zainab ta ce "Ai karki damu, na yiwa babansa magana muna dawowa daga umara, babansa zai je nema masa auren Kursum, ai yarinyar tayi na yaba da ita"

Hajiya Salma ta ce "Alhamdilillah, kuma a lokacin ma na san Bashir zai dawo, sai su haɗu da Fadila ma"

"Aikuwa da faɗuwa ta zo daidai da zama, duk sai a haɗa ayi maganar a wuce wurin, kin san halin Fadilan ma ita idan na biye mata yin auren a yanzu ma baya gabanta, gara tun wuri kan tayi mini irin ta ɗan uwanta, ta kwaso mini gayyar tsiya ko da ba halinsu ɗaya ba ita da Khalil, in nema mata miji da kaina, na san ba zata ƙi ba ita 'yar I don't care ce"

"To shikenan, Allah ya daidaita mana kansu, kawai da kun dawo a fara magana, sai mu ɗaufa azamar biki"

Suka yi dariya, Hajiya Salma ta ƙara yiwa Hajiya Zainab godiya, sannan suka yi sallama.


Duk wani abu da Amina za tayi ta bawa Alhaji Ahmad haƙuri, ya shareta ya ƙi kulata, har girki tayi masa amma ya ƙi ci, ya cigaba da sabgoginsa. Kasancewar washegari lahadi ace, babu wani event da za suyi ranar, aka ce kowa ya huta ranar. Abu kamar wasa Amina ko Abinci ba ta iya ci, sai aikin kuka, gaba ɗaya taji haushin kanta take ji, duk abin da tayi masa na rashin kunya da cizo bai fushi da ita haka ba sai a kan tayi rawa a gaban mutane, ita na ta wanni fannin taga rashin dacewar hakan, amma rawar ba ta rashin kunya ba ce, kuma ko ina na jikinta a rufe yake, amma ya ɗau wannan fushi haka.

Wunin ranar lahadin nan, bai wuni a gidan nan ba, sai dare bayan ƙarfe tara ya daw gida. Amina ta riga tayi wani irin mugun sabo da shi, hakan ne ya sanya ta ƙara shiga damuwar rashin kulata da yake yi.

A falo ya tarar da ita taci kukanta ta godewa Allah, yana shigowa ta miƙe tana masa sannu da zuwa. Da kai kawai ya amsa mata ya wuce ɗakinsa.
Binsa tayi ɗakin tana kiran sunansa.

Sai da ya shiga ɗakin sannan ya tsaya ya kalleta ya ce "Lafiya?"

"Daddy dan Allah kayi haƙuri, ka daina fushi da ni"

Maimakon ya bata amsa sai ya ce "Bani wuri zan cire kaya"

Ta ce "To ka haƙura?" Bai kulata ba ya fara cire kayan jikinsa.

Juyawa tayi ta bar masa ɗakin tana share hawaye, tana fita ya bi ƙofar da ido, ya shafa ƙirjinsa a hankali ya ce "Am sorry meenalina, ba yadda na iya dole in hukunta ki, yadda gobe ba zaki sake ba, am not punishing only you, but together with my soul am missing you" ya ƙarasa maganar kamar tana gabansa.

Wankansa yayi ya fito, ya koma falo ya tarar da ba ta gaza ba ta kuma yi masa wani girkin.
Ya zauna ya kwashi girkinsa tukuna, sannan ya nufi ɗakinta, har ta kashe fitila, ya sa hannu ya kunna fitilar. Tana zaune a kan gado tayi shiruu alamar tayi kuka ta gaji.

Ya nufi in da take zaune a kan gado, yana zuwa ta juya masa baya tana haɗe rai.

"Dan kin samu na biyoki zan rarrashi shi ne zaki ja mini aji?" Sai ta fashe masa da kuka.

"Shikenan ya isa, is ok let's talk juyo kiji?" Noƙe kafaɗa tayi ta ƙi kallonsa.

"Ni zaki jawa aji dan kin samu na sauko?"

"Amma ba nayi ta baka haƙuri ba ka ƙi haƙura, kayi ta sakani kuka ko Abinci bana iya ci" tayi maganar wasu hawayen na zuba daga idonta.

"Inyee Meenalin ba, tana son Daddy ashe, har kin yi missing ɗina haka?"

Murguɗa masa baki tayi tana goge hawaye.

Dariya yayi yana girgiza kai ya ce "Meenal, dole in yi fushi da ke, kin je kin yi rawa a gaban mutane a haka, kuma wani ƙaton banza ya keɓe da kw kuna hira, naji babu daɗi saura ƙiris na zane ki ma, kuma kuɗin da ya baki ba zaki karɓa ba"

Ta kalleshi ta ce "Meyasa?"

"Saboda haka nace" tayi shiru tare da sunkuyar da kai.

Ya ce "Tashi muje in baki Abinci"

Ta ce "Ni na ƙoshi"

"Kika ƙoshi da me? Oya tashi muje"

Ta noƙe kafaɗa ta ce "Ni sai dai ka kawo mini nan in ci"

"Ni zaki aika, kuma ki sa aiki?"

"Eh ramawa zan yi, ka dinga sani kuka duk haƙurin da na baka"

"Ai shikenan ya wuce, muje in nuna miki wani abu"

Ta kalleshi ta ce "A ina?"

Ya ce "Muje ki gani"

Ta sauko daga kan gadon, shima ya miƙe suka fice daga ɗakin.






Yau Litinin a yau su Amina zasu yi karawar kusa da ta ƙarshe a gasar Quiz, wadda kusan ita ke jan ragamar makarantarsu gaba ɗaya.
Ko da Alhaji Ahmad ya fito falo, kallo ɗaya ya yi mata jikinsa yayi sanyi, saboda yadda fuskarta da idanunta suka kumbura, alamar ta daɗe tana kuka sosai.
Ya dafe goshinsa yana sake ɗora zargin komai a kansa, ya tunkari in da take, ya zauna kusa da ita, ya sauke mata tagumin da tayi, ta ɗago jajayen idanuwanta ta kalleshi.

"Dan Allah Amina, ki sassauta wannan kukan haka kin ga cikin mutane zamu shiga, kar ki wani abu da zai janyo hankalin mutane har a fuskanci abin da ya faru, kar mutuncina ya zube a idon mutane".

Wasu irin hawaye ne masu ƙona zuciya, suka zubo daga idonta, ta kalleshi da kumburarrun idanunta ta ce  "Kai mutuncinka ne ya dameka ko? Nawa kuma ko oho, na gode sosai"



😳🙄JAMA'A MEKE GOING NE, NIFA BAN GANE BA"

AYSHERCOOL
08081012143

VIP GROUP, KAR KUGA KUN BIYA KUƊI, NA CIGABA DA GANIN POSTING ƊIN VIP A GROUPS ZAN DAINA MUKU POSTING KULLUM, AND I MEAN IT🤨GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL



51

Sosai daa gaske Amina ta sake fashewa da kuka, jikinta har rawa yake yi, saboda yadda take kukan.

Cikin kwantar da murya Daddy ya ce "Amina, i feel your pain, na fiki shiga damuwa da tashin hankali a kan abin da ya faru, amma dan Allah ki tsaya ki fahimceni, wannan abu ne da ya faru tsakanin ni da ke, babu wanda ya sani, ba wanda ya san muna tare ma, dan Allah ki rufa mana wannan Asirin, ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai gane"

Cikin kuka ta ce "Ni dai ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni, duk da irin tarin nasihar da Baba yayi mini kan nayi tafiyar nan, Wannan shi ne sakamakon da zan masa?" Tayi maganar tana shesheƙar kuka.

Miƙa hannu ya yi yana ƙoƙarin janyota jikinsa, amma ta ja da baya.

"Shikenan, dan Allah kiyi haƙuri ai na baki haƙuri, kuskure ne ya riga ya faru, kiyi haƙuri ki daina wannan kukan, ki zo mu tafi lokaci yana ƙurewa"

"Ni ba in da zani, ba zani makarantar ba, na fasa duk competitions ɗin tun da a kansu koma menene ha faru da ni, ni gidan zan koma ba zan sake kwana a garin nan ba"

Gaba ɗaya Daddy ya rasa abin da yake masa daɗi, gaba ɗaya Amina ta birkice masa ta caza masa kai.

"Amina so kike kiga ina kuka nima? Wa zai rarrashi wani kenan? Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki zo muje ko quiz ɗin ku gama sai na san abin yi"

"Ni ba in da zani na gaya maka, na riga na haɗa kayana kawai ka sakani a mota mu tafi"

"Meenal ko durƙusa miki zan yi a kan gwiwata ne? Dan Allah ki mini Wannan alfarnar, ko ita kaɗaice alfarmar da ta rage zaki iya yi mini a rayuwata"

Da ƙyar da siɗin goshi, da rarrashi da kwantar da murya, Daddy ya sanyata ta shirya, suka tafi wurin competition.

Sai dai abin yayi affecting ɗin ta, gaba ɗaya bata da karsashi a wannan karon, babu ƙwarin gwiwa, sai shirme take yi, lokaci lokaci hawaye na cika idanunta.
Gaba ɗaya ta kasa mayar da hankali, har ɗaya makarantar na neman yin galaba a kansu.
Gaba ɗaya Daddy ya rasa ina za zai saka ransa, wannan babar dama ce ga Amina da zata taimaki karatunta, ta samu damarmaki, amma tana neman tayi wasa da damar. Aka tafi hutun mintuna goma sha biyar, hakan ya bawa Daddy damar janta gefe, ya cigaba da aikin rarrashi, kamar wanda aka tafi aka bar shi da 'yar yaye.

Mutumin nan ne da yayi musu alƙawarin kuɗi, ya nufo su yana kallon Amina da take zubar da hawaye Daddy na mata Magana ƙasa ƙasa.

"Yarinyar fulani, meke damunki ne? Haba our champion of the year, ya kike nema ki bamu kunya ne?"

Wani irin haushin mutumin ne ya kama Daddy, yaji tamkar ya tashi ya make shi ya huta.

Amina dai kallo ɗaya ta yiwa mutumin ta sunkuyar da kai tayi shiru.

Ganin ba su kula shi ba ya sanya ya kalli Daddy ya ce "Ko kaine babanta?"

Ya amsa masa da "Eh ni ne"

"Amma ya aka yi ba kwa kama sam? Yarinyarka ta burgeni sosai da ina da ɗa da na nema masa aurenta" yayi maganar cikin sigar wasa. Daddy bai tanka masa ba, ya ja hannun Amina zuwa wani wurin daban.

Ya dinga share mata hawaye, yana cigaba da kwantar da hankali, tare da yi mata alƙawarurruka daban daban, Allah ya ɗora shi a kanta, da ta koma tayi abin arziki, makarantarsu tayi nasara zuwa zagaye na ƙarshe wanda a nan za a fitar da gwani.

Su kansu malaman makarantar su Amina, da sauran ɗaliban wasu makarantun ma da suka saba da juna a wurin, suka dinga tambayar ta meke damunta, amma ta ce musu babu komai, sai haƙura suka yi suka ƙyaleta.

Da aka zo tafiya ma, ta tuburewa Daddy cewar ita ya barta cikin 'yan makarantarsu, ya kawo mata kayanta ba zata sake kwana da shi a gida ɗaya ba, nan ma sun shafe tsawon lokaci suna fafatawa sannan ta amince ta bi shi gida.

Hatta girki da take musu ta daina, sai dai yayi order Abinci, ya zo ya zauna ya yi ta aikin rarrashi yana bata, gaba ɗaya damuwar da Amina take ciki ya fara shafarsa.




Khalil ya warke, har ya ce zai zo ya kaiwa Daddyn ziyara, Daddy ya ce masa ba sai ya zo ba, shima barin Abuja zai yi, ya wuce Lagos.

Tun Amina na share Daddy, tana ta yi masa wulaƙanci, shi kuma yana binta yana lallaɓata, har ya fara bata tausayi, kullum cikin bata haƙuri yake, yana kuma ƙoƙarin kwantar mata da hankali, da ta motsa cikin rawar jiki zai fara tambayarta me take buƙata me zai yi mata, gashi ba kowane Abinci yake iya ci ba, dan haka ta lura galibi Fruit kawai yake ci.





Fadila ce zaune, a ɗakin Yusra tana ta jujjuya yadda za ta yiwa Yusra bayani ba tare da ta yi mata wata fassara ta daban ba.

"Girl, ya ne? Kin zo kin sani a gaba kina kallona, kin ƙi magana"

Fadila ta ce "Girl ba zaki gane ba"

"Zan gane, yi mini bayani mana"

"Kin san abin da ya faru kuwa ranar da muka yi exams ɗin Kankiya kuwa?"

Yusra ta ce "A'a baki gaya mini ba"

Nan Fadila ta bata labarin abin da ya faru, da duk yadda suka yi.

Yusra ta ce "Ikon Allah, ai tun farko yakamata ki ɗau wannan matakin, ba sai da lamarin yayi tsami haka ba"

"Bari kawai, bana son in yi wani abu ne da zai sa Kankiya ya rasa aikinsa, yanzun ma dan ta ƙure ne, bana son wani abu ya sami Yazid saboda ni, ƙiri ƙiri suka haɗa kai da abokinsa Tj suka nemi su ci zarafinsa fa"

"To Allah ya kyauta"

Fadila ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kin san wani abu Yusra?"

"A'a sai kin faɗa"

"Yazid ya yi fushi, ya daina shiga harkata baya son duk wani abu da zai sake haɗani da shi"

Yusra ta gyara zamanta sannan ta ce "Ai dama abin da kika yi masa baki kyauta ba, na gaya miki kika ƙi yarda"

Fadila ta ce "Kinga ni fa ba wannan ne ya dameni ba, Yusra ni ba son Yazid nake ba so nake na taimaka masa"

"Ki taimaka masa kamar yaya kenan?"

"Yusra, Yazid ya faɗi wasu abubuwa da na fuskanci yana buƙatar taimako, tun a farko na fuskanci ba shi da shi, kuma ya gaya wa Kankiya cewa, ni ina da komai shi ba shi da komai sai Allah da karatunsa. Ina son sanin idan da abin da zai taimake shi da shi in taimaka masa"

Yusra tayi murmushi ta ce "To yanzu ke Fadila ai kin riga kin ɓata lamarin, maganganun da kika gaya masa dole ya ji babu daɗi ga wulaƙanta shi da aka nemi ayi duk dan saboda ke, dole yayi ƙoƙarin nesanta kansa da ke."

"Girl, Yazid he is simple minded, kawai ina son in taimakawa rayuwarsa, amma zai yi wahala ya yadda he is avoiding me, ko lokacin da muke shiri da ƙyar yake karɓar abu a hannuna"

"Girl, yanzu duk wani abu dole ki bari a koma school, idan aka koma sai mu san ta yaya zamu ɓullowa lamarin, muyi bincike a kan sa, sai kiga ta ina zaki ɓullo masa"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah yasa ya amince da taimakon, dan Yazid da alama yana da taurin gaske sosai"

Yusra tayi murmushi daidai lokacin da take miƙa hannu kan wayarta da ke vibrating. Ta ɗaga wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama.

"Salamu Alaikum, Yaya Abdul brk da rana"

"Barka dai, kin tashi ko kuma ni na tasheki?"

Murmushi ta yi ta ce "Haba dai, rana fa tayi na tashi tun ɗazu"


Ya ce "Hmm ai ke 'yar hutu ce, yaya zan samu Cake ɗin anjima?"

"Eh zaka samu in Sha Allah, guda ɗari ko?"

"Eh ɗari, gudunmawa zan bawa abokina za mu yi reception gobe in Allah ya kaimu, zai yi Aure"

Yusra ta ce "Ma sha Allah, Allah Ya sanya alkhairi, saura naku kai da Yaya Khalil Allah ya nuna mana"

Abdul ya yi murmushi ya ce "Sai dai Khalil, tun da yana da budurwa ni ko budurwar bani da ita, yanzu reception ɗin nan kowa zai je da budurwarsa ni sai dai in je ni kaɗai, ki samo mini hayar budurwar da zata rakani in biya" yayi maganar cikin zolaya.

Sosai Yusra take dariya, ta ce "Hayar budurwa kuma?"

"Eh mana Kodayake ba sai naje da nisa ba, ai gaki sai ki rakani kawai, gani ga ki ga cake ɗinmu"

"Yaya Abdul kana da abin dariya, sai muyi ciniki ka biyani in raka ka ai, bari in je in fara aikin dan in gama da wuri"

"To shikenan, ki sako mini account number in tura kuɗin"

"Yaya Abdul ai kai ne, ka saka kuɗin 50, kawai"

Abdul ya ce "No, Ana Yaya sama Yaya ƙasa zan karya jari, no sako account kawai"

"Ko ka saka na 100 kana da gyara guda 50"

Sai da ta lura Fadila ta fara ƙosawa da wayar, sannan ta yi masa sallama.


Fadila ta ce "Wai da wa kike waya haka ne?"

Yusra ta ce "Yaya Abdul ne, yayi mini magana ta IG jiya, wai yana son cake"

Fadila ta yamutsa fuska ta ce "Shi ne kuke ta wannan surutun, ni surutun gayen nan ba ƙaramin haushi yake bani ba, yai ta surutu ba wani class"

"Shi Yazid baya surutu kike saurarsa"

"Amma ai Yazid gently yake surutu, kuma ba ko yaushe yake yi ba"

Yusra ta ce "Allah Fadila, kice he is so classic?"

Fadila ta haɗe rai ta ce "Yusra ba wannan maganar muke ba fa, alaƙata da Yazid daban"

"Shikenan naji, yi haƙuri zo muje ki tayani muyi cake ɗin tare?"

Fadila ta miƙe ta ce "Allah ya kiyaye" ta ɗau jakarta ta fice.







Ranar da su Amina za suyi zagayen ƙarshe na completions, ta shirya ta fito falo, amma taga Daddy bai fito ba, gashi lokaci na nema ya ƙure.
Cike da tsoro ta tunkari ƙofar ɗakinsa ta tsaya tana knocking.

"Come in" shi ne abin da taji ya faɗa. Kamar kar ta shiga, sai kuma ta murɗa ƙofar ta shiga da sallama.
Yana zaune a bakin gado, idanunsa sun ɗan yi ja, ta dube shi ta ce "Naga haryanzu baka fito ba, kuma lokaci yana ƙurewa".

Ya ce "Bana jin daɗi ne, kije Joseph zai kai ki, sai dai dan Allah Amina ki kula sosai, dan Allah kar ki je kiyi wani abu da bai dace ba, ko ki tsaya kula wannan mutumin".
Ba ta ce masa komai ba, ta rufe masa ƙofarsa ta tafi.


Duk abin da bawa ya sanya a gaba, cikin ikon Allah idan har yana miƙa lamuransa ga Allah, idan har da rabo sai ya yi nasara.
Abu kamar wasa Amina ta ɗaukarwa makarantarsu gwarzuwar shekara, da maki mai tazara a tsakaninta da abokan karawarta, a cikin ƙwarin yaran da sai da aka tace sannan aka ɗebo su.
Yayin da makarantar ta su ta zo ta biyu, a debate da suka yi.

Makarantarsu sun yi murna nara misaltuwa, aka sanar da cewa jibi za ayi ceremony na karrama waɗanda suka yi nasara, ayi walima washegari kuma kowa ya tafi.

Tun a mota Amina taji tana missing ɗin Daddy, da yanzu yana nan ya biye mata suna murna tare a mota.
Suna zuwa gida tayi clashing da wani mutum sanye da lapcort, da box a hannunsa ya fita.
Tana shiga falon taga Daddy a zaune, gefensa da magunguna, murmushi yayi mata yana faɗin "Congratulations Meenalina, am proud of you"

Fuskarta Babu yabo babu fallasa ta ce "Thank you, amma yaa aka yi ka sani? Naga baka je ba"

"Na kalla live, ai ana haskawa a wata tasha" yayi maganar yana nuna TV

Ta ɗan jinjina kai ta wuce shi, dan haryanzu tana jin haushinsa.


Babban abin da ya sanya ta ɗan damu shi ne yadda ko salla baya fita Masallaci.
Ko falo bata sake ganin ya fito ba tun da ta dawo, basarwa tayi ta fara haɗa kayanta, saboda sun kusa komawa gida, amma ta kasa basarwa tayi ta tunanin halin da yake ciki.



Khalil jikinsa yayi sauƙi sosai, sai rama da yayi, har ya koma ya cigaba da zuwa wurin aikinsa, sai dai ya kasa fidda rai a kan samun Hafsa.
Yana son zuwa gida, amma ya san yana zuwa Mummy babu abin da zata yi masa sai wancan zancen da baya so, na batun yi masa aure da wata daban.
Haka nan ya daure yake kiran Mummy a waya gaisheta, amma wani lokacin sai ta ƙi ɗaga wayar, wani lokacin kuma ta ɗaga ta amsa masa ciki ciki.



Ƙarfe huɗu, Abdul ya isa gidan su Yusra, a lokacin ta gama yi masa aikinsa na cake gaba ɗaya.
Ya kirata a waya, ya sanar da ita yana waje yana jiranta.
Maimakon ya ga ta fito da kayan Cake ɗin sai ya ganta ita kaɗai.
Ta ƙaraso suka gaisa, ya ce "Chef ina kayan?"

Yusra ta ce "Baka taɓa zuwa gidanmu ba, sai yau da taka ta kawoka, dan haka ka shigo ka ci Abinci"

Abdul ya yi murmushi ya ce "Banda abinki Abinci da la'asar ɗin nan, a ƙoshe nake ai"

Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Aikuwa na ajiye maka Abinci, idan baka ci ba ba zan baka cake ɗin ba"

"Ayi haƙuri next time idan na zo zan ci"

"Naƙi wayon, Abincin fa da daɗi dan Allah ka shigo Yaya Abdul" tayi maganar cikin magiya.

Yadda ta kwantar da kaine ya ga babu daɗi ya ce mata a a.

Tayi masa jagora zuwa cikin gidansu, babu laifi gidansu me kyau ne sosai, suma suna da rufin Asiri sosai.

Ta gabatar masa da Abinci da abin sha, da fari niyyarsa ya ɗan sa albarka ya tashi ya tafi, amma yaji Abincin ya ratsa shi sosai yayi daɗi.

"Yaya Abdul da ɗazu ka zo da kun haɗu da Fadila, muna tare ɗazu"

Jiki a sanyaye Abdul ya ce "Ai ko mun haɗu babu lallai ta

Please Login or Register in order to submit comment