Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?" tace "ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma......" "For Heaven's sake Ramlah!!" na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, "this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!" cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, "am sorry babe, I shouldn't have said what I said earlier.... M sorry, really" ta kauce daga gabana, "me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!" nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, "look Ramlah! Wallahi I really didn't meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I'm trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah...." zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, "m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it's hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn't know, ki yafe min" rungumeta nayi ina tapping bayanta, "I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you" ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa "m sorry Nafeesah" nace "what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan" ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taron mu da Ramlah kenan.
[09:16, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*22*

_'Some nights I can hear you., Screaming on the phone over something that he did....., And I wonder what can I do to make you throw him out so you can let me in.....!'_
A song by *Shayne Ward* Titled *'Melt the Snow'*. I hope you will enjoy listening to it.

Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it's not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn't. God Forgive him but he's enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss.....! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, "Muneer you evil bastard!" yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!...." da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne.....!.

☆☆☆☆☆☆☆☆

A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar "Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?" sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata "idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne" ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da 'harara a duhu' saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, "Are you ok Nafeesah???!"

*♡Jeedderh♡*
[09:16, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, "yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?" na zaro ido ina kallonta, "Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai" ta turo baki, "to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?" nace "dat's a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?" tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace "haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?" da sauri ta dago kanta ta kalleni, "da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai'i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da 'ya'yansu, Anty tace "Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?" nayi murmushi tare da gyada kai, tace "eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki" Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace "Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?" nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace "anan ma zata dinga mana weekend koh?" na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace "ehh" a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, "pretty ina zuwa?" ta juya tace "ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau" yace "a'ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata" aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, "babu komi Abbu, taho muje kinji?" ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace "Nafeesah!" na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, "are you sure Pretty ba zata takura miki ba?" na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace "umh.... Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?" nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace "good! I'm happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe" da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu'ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that was the worst moment I've regretted the most in my life!!!.

*♡Jeedderh♡*
[09:16, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*23*

Kalmar 'Are You Ok' kalma ce da nake matukar tsoro idan ina cikin halin damuwa. I am a very emotional person, shi yasa idan ina cikin halin damuwa bana son mutane a kusa dani saboda gudun su tambaye ni lafiya? Don zan iya fashewa da kuka, ni a gare ni tambayar are you ok kamar fama min gyambo ne. Yanzu ma sai da nayi iyaka kokarin da zanyi na danne kukan da yake kokarin barke min nace "m fine Abbu, kawai bana jin dadin jikina ne" ya kalleni kawai nasan bai yarda da abinda nace ba, ban ga laifin shi ba don yadda nake a hargitsen nan babu wanda zai yarda wai gajiya ce ta maida ni haka. Ya kalleni sosai kamar wanda yake so yayi magana sai kuma kawai ya maida kallonshi ga titi, a raina naji dadin hakan nasan tambaya daya zai kara jefo min zan fashe da kuka, kuka kuma ba abinda nayi niyar in ci gaba dayi bane saboda Muneer. Har yayi parking a parking lot din dept din Microbiology, na yunkura zan bude motar ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana, na Juya a hankali na kalleshi. Idanuwan shi fes a kaina suke, naji wani slight rawar jiki kafin in sadda kaina kasa, muryar shi a sanyaye yace "akwai abinda yake damunki Nafeesah wanda kika ki gaya min and I wouldn't force you to tell me, kawai ina so in gaya miki cewa komi na rayuwa sai da hakuri, koma menene yake damun ki kiyi hakuri ki dauke shi a ba komi. Idan ma wani abu ne kika rasa kike ganin kamar ba zaki iya hakuri da rashin ba kada ki manta Allah yana tare da Ke. Shi ya mana alkawarin canza mana abinda yake sharri ne a gare mu zuwa ga mafi alkhairin shi don haka ki roke shi game da abinda yafi alkhairi a gare ki ba kiyi holding into something wanda yake ba alkhairin ki bane kin gane?" na gyada kaina a hankali maganganun shi sun shige ni. Abinda ya kamata in tuna kenan a lokacin da naga hoton Muneer da amaryar shi jiya, abinda ya kamata inyi kenan ba wai in kira shi ba ina kara fallasa kaina da disappointing kaina, sai yanzu naga cewar hakika abinda nayi jiya ban kyauta ba, naji kunyar kaina ta kama ni har ma data Muneer din, ko da wane ido zan sake kallonshi kuma yanzu??. Nace "na gane Abbu nagode sosai, In shaa Allahu zan yi amfani da shawarar ka" yace "good" shiru ya biyo baya a cikin motar, can naji ya sake magana cikin whisper, kamar kuma wanda yake tsoron yin maganar, "anjima kuma sai gida koh?" na gyada kaina a sanyaye, barin rayuwar Abbu da iyalan shi!! Tunani ne mara dadi dake fadar min da gaba a duk lokacin da ya fado min a cikin raina don haka nake iyaka kokarina wajen ganin na kauda tunanin daga cikin raina. Na sake tsintar muryar shi yana tambayana, "da gaske zaki dinga zuwa kina mana weekend?" nace ehh, a cikin raina nasan fada kawai nake yi ba don zan dinga zuwa ba sai don kawai kada su dameni da tambaya. Kamar yasan abinda nake tunani, yace "da gaske kike ko kuma kina fada ne kawai?" shiru nayi wannan karon, yayi murmushi tare da kallona kawai yace na gane. Dash board ya bude ya ciro wata karamar jaka fara mai hannu ya miko min, na amsa fuskana dauke da alamun tambaya, yace "it's a small thank u gift, thank u for staying with us Nafeesah, we enjoyed having u in our life and we wish you will come back to us forever!" na dan rausayar da kaina cikin alamun rashin gane inda maganar tashi ta saka gaba, me yake nufi ne? Murmushi yayi ganin ya saka kwalwa na cikin rudani. Yayi murmushi yace "oya! Up you go! Naga abokan ki suna jiran ki tun dazu" sai lokacin idanuna suka koma ga inda muke zaune, su Ni'ima na hango tsaye a kofar shiga lab dinmu suna hirarsu da Ramlah, cikin sauri na jefa jakar daya bani cikin handbag dita na mishi godiya tare da bude murfin motar na fita. Gabadaya kallo suke bina dashi cike da alamun tambaya nasan bai wuce na mamakin abinda muka tsaya hirantawa da Abbu bane tun

Please Login or Register in order to submit comment