Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta, don haka ban tarki kiranta ba sai dai na tura mata text message which of course bata yi replying ba.
Ina fitowa daga class na koma daki, su Ni'ima suka kira ni suka ce suna dakina. Ina shiga suka tare ni da shewa ni har suka sa gabana ya fadi ina tunanin ko zancen mu da Abbu ya kai kunnensu ne, sai da muka gaisa har muka fara hira naga basu yi maganar ba sannan na dan saki jikina. Na kunna stove ina kallonsu, "me zan dora muku?" Ni'ima tace Indomie noodles, Sadiya kuma tace Spaghetti, na kallesu "guys, idan zaku daidaita akan abu daya ku daidaita don kun san bani da lokacin yin girki biyu" suka kwashe da dariya, Sadiya tace "dora mana noodles, wannan maman Babyn ba zata barmu mu shaki iska mai dadi ba idan ba a dafa noodles dinnan ba" nace "kema ai Maman Babyn ce" ta wani zare ido, wa?? Muka kwashe mata da dariya ni da Ni'ima. Nan da nan na dora Indomie na ta dahu na juye mana a tray muka fara ci. Muna cikin ci kiran Abbu ya shigo wayata, na kalli wayar tare da kallon su Ni'ima dake kallona suma, na ci mur tare da janye wayar na kife ta akan gado, suka yi sharing glancing a tsakaninsu. Sadiya ce tace "wai ni me ke tsakanin mutanen nan biyu ne? I've started putting a big question mark a tsakanin su" Ni'imah tace "kamar kin shiga zuciyata wallahi... Ni kaina na kasa fahimta" na kara hade fuska ina cusa indomie bakina ba tare da nayi magana ba, sam bana so maganar mu da Abbu ta fita ta shiga cikin dangin sa don tsakanina da Allah ban san da wani ido zan kallesu ba, ban shirya ba. Ni'imah tace "idan tayi wari dai mun ji" ni dai na kyale su ban tankasu ba. Muka gama na wanke kwanuka na kai mana soft drinks muka sha, daga nan na koma class bayan nayi sallah na bar su a dakin, dana dawo ban same su ba sun bar mun sako dai kan cewa sun tafi. Da dare Abbu ya sake kirana, na daga wayar da sallamata ya amsa ya dora da cewa "me bawan Allah yayi aka ki daga kiran shi dazu" nace "bana kusa da wayar ne Abbu.... Ina yini?" ya amsa, anan yake fada min wae washegari zai tafi Ilorin zai yi sati daya a can. Yace "me zai hana idan na dawo kawai a daura mana aure Nafeesah?" nace "Abbu baka tunanin it's too sudden?" yayi sighing, "Nafeesah, y do u always keep saying yayi sudden? Kina tunanin haka zan ci gaba da kallonki Ina kauda kai har zuwa yaushe? Har ki gama makaranta ko me?" nayi kasa da murya nace "at least in dan yi nisa a karatu na mana!" yace "really? Kin san? Ko session dinnan ba zan bari ya kare ba ba tare dana aure ki ba Nafeesah, idan kuma ba so kike yi in..... God! Nafeesah wae me kike nufi da rayuwata ne??" muryar shi ta dan fara yin sama alamun ranshi ya fara baci, nayi shiru ban bashi amsa ba. Lokacin dana gama yanke shawarar yarda da Abba, kamuwa da son shi da amincewa akan cewa zan aure shi, ban yi tunanin zancen aure ba, ban yi tunanin cewa zai taso zancen aure nan kusa ba, ban yi tunanin zai so ya aure ni ina cikin karatu na ba, nayi tunanin zai bar ni in karasa karatuna ko kuma at the very least ya bari sai na kusa kammala karatuna sai kuma gashi yana zancen aure in the next two weeks when I'm not even ready for it, hell ban ma san meye ma'anar auren ba, me zan yi kenan?? Ga zancen mu da Mommy ga.... Ya katse ni ta hanyar cewa "just forget about it Nafeesah, bana son tursasaki yin abinda baki yi niyar yi ba. Na hakura da zancen auren, idan muka ci gaba da zama a haka ma ya ishe ni, I want your happiness" naji kwallah ta tsattsafo min a idanu, nace "Abbu kayi hakuri" yace "don't mind Amour, na fahimce ki" nayi murmushi mai sauti wanda na tabbata ya jiyo sautin shi, ya maido min da martanin wani wanda yasa naji gwiwoyin kafana sun yi wani sanyi, yace "Pretty na tana ta cigiyar ki, yaushe zaki zo ki ganta?" na zaro ido kamar yana gabana, har sai da naji gabana ya fadi nace "ni?? A'ah gaskiya" ya danyi er dariya, "tsoron me kike ji ne? Na manta ma dazu in fada musu you are now my wife to be" nayi saurin cewa "pls Abbu no! Don Allah ba yanzu ba!" yace y? Na dan turo baki, "ni dai don Allah a'ah" yace "naki, sai na fada musu" na kula tsokana ta kawai yake yi don haka na kyale shi yayi ya gaji sannan muka danyi hira kafin muka yi sallama na mishi Allah ya kiyaye hanya muka ajiye wayar. Abin mamaki sai ga kiran Mommy ya shigo wayana, nayi tsuru Ina kallon wayar kamar ba zan daga ba, Ina tsoron abinda zai faru idan na daga kiran. Sai daya kusa tsinkewa sannan na daga, a hankali kamar mai tsoronta nayi sallama tare da gaida ta, cikin usual tone dinta ta amsa yadda take min, ta tambayeni karatu da sauran abubuwa duk na amsa mata da lafiya lau, tace "naji abinda kika yi Nafeesah, kina ganin daidai ne hakan?" nace "Mommy kiyi hakuri don Allah" tayi shiru kafin tayi ajiyar numfashi, "to tell you the truth naji haushin Abin daga farko, daga baya sai naga cewa abinda kike so kenan and I don't have the right da zan hana ki yin auren da kike so ba Ummiey. I really hope decision din da kika yanke shine daidai kuma zai kawo miki farinciki mai dorewa a cikin rayuwar auren ki" naji zuciyata tayi wani irin sanyi, na saki sansanyar ajiyar zuciya Ina jan hamdala a cikin raina, nace "Mommy nagode sosai" tace "Ni me ma zaki ce mun ne? Kwana biyu baki kira ni ba saboda kina gudun kar in hana ki yin soyayya ko?" nace "mommy ba haka bane" tace "idan haka ne ma ya zanyi? Tunda daddyn ki ya kitsa miki kin hau kai kin zauna, ina jinshi ai yana baki shawarar kar ki kira ni shine ke kuma kika ki kirana" na sake cewa "kiyi hakuri" ina danne dariyar data taso min, ta kuta, "he was even threatening me wai zai iya karo aure, bai san cewa abinda matar shi Ibrahim din zata yi da halin da zata shiga idan taji zancen auren bane nake gujewa ba, yayi zaton son raina ne nake shirin shiga tsakaninki da abinda kike so ba. Ummiey mata da kike gani baki san irin tashin hankali da fargaba da suke shiga idan suka ji zancen kishiya ba balle ita data zauna dake a gida daya ta rike ki cikin amana, dare daya ace zaki aure mata miji kin san ba zata ji dadi ba dai koh?" jikina yayi sanyi na sadda kaina kasa, wannan yana daya daga cikin abinda ya saka ni hesitating at first amma ya zamu yi? Ba zamu danne farinciki cikinmu don faranta ran wadda bata san namu farin cikin ba. Mommy tace "kada ki damu fa, kuma kada ki saka maganar a cikin zuciyar ki babu abinda zai faru da yardar Allah. Amma ya miki zancen aure? Yaushe yace za ayi?" nayi wuri-wuri da ido, tace "baki sani bane? Zan yiwa Daddyn ki magana, ya kamata ace anyi auren nan kawai" nayi saurin cewa, "Mom, ba zaku bari in gama karatu bane?" shiru ya biyo baya kafin tayi magana, "kina da hankali kuwa Ummiey? Shekaru nawa suka rage miki kafin ki gama karatunki, kina tunanin zamu zuba miki ido ko kuma shi Ibrahim din ne yace sai kin gama karatu?" nace A'ah, tace "to ai ko shine Ummiey ba zamu zuba miki ido ba, zan yiwa Daddynki magana a zauna ayi maganar auren ku don gaskiya hankalina ba zai kwanta ba kina karatu a Kano shima wanda ke son naki yana Kano mu muna nan Kaduna bamu san abinda ke faruwa ba a yadda duniyar nan ta baci" nace "Mommy baki yarda dani bane?" tace na yarda dake Ummiey, nasan irin tarbiyar dana baki, but still, hankalina ba zai kwanta ba gaskiya" nayi rolling eyes, "ai shikenan Mom" tace "zan dai tuntubi Daddynki inji, goodnight baby" na mata sai da safe tare da kashe wayar.

Babu ranar da bamu yi waya da Abbu ba tunda ya tafi, idan ma bamu yi wayar ba muna tare ta hanyar text message yana kashe ni da dadadan kalamai da suke kara narka zuciyata zuwa gare shi. Sai a dan tsakanin na fahimci ainihin ma'anar Soyayya, ashe da shirme nayi, ashe ba son Muneer nake yi ba tunda ko a lokacin dana yi tashen son shi ban taba kawowa raina bazan iya rayuwa idan babu Muneer ba, amma a yanzu, na tabbata cewa muddin babu Abbu a cikin rayuwata to tabbas rayuwa ba zata yiwu a gare ni ba, ko zan yi ta to mara gardi da dandano ce. A yanzu bana taba iya tunanin runtsa idanu matukar ban ji muryar Abbu a yini ba saboda nasan cewa ba zan iya barci ba, nayi wani irin sabo da muryar Abbu wanda sau tari hakan yake bani mamaki. A kowace rana kuma a kowane lokaci wata kofa a cikin zuciyata sai ta bude da sunan Abbu rubuce a jikinta Ina da tabbacin nan da dan lokaci kankani kila numfashina ma idan aka kula sunan Abbu ne zai dinga fita daga cikin shi. Duk da dai ance wai sanin gaibu sai Allah amma zan iya cewa ta bangaren Abbun ma hakan take koma fiye da haka. A yadda na fahimce shi cikin dan lokacin, yana daga cikin mutanen da baiyana halin da zuciyoyin su ke ciki abu ne mai matukar wahala da wuya a gare su, sai dai su baiyana shi through their actions kawai. Baya zama yana wani tsara min kalamai na soyayya kamar yadda yace bai iya irin wannan Abun ba but I am comfortable da yanayin yadda yake tafiyar dani, yadda yake tattalina da yadda yake nuna kamar duk duniyar nan babu wata 'ya mace mai gashi a cikin idanun shi sai ni, wannan kadai ya ishe ni numfashi mai dadi a rayuwa sanin cewa abinda nake matukar so da qauna shima yana sona da kaunata equally. Shi yasa ko a lokacin da Mommy ta sake tuntuba na da zancen aure a karo na biyu, tace "bikin Hansa'u yana matsowa, me zai hana a hada auren ku gabadaya kawai a daura a can Malumfashi? Bai fi watanni biyu ba za a daura in yaso ko bayan kun karar da session dinnan ko semester din sai ayi biki da tarewa ko?" nace "Mommy sai wani saurin ku aurar dani kuke yi kamar wadda kuka gaji dani? Wane irin aure ne kuke shirin yi mun haka daura aure kafin tarewa?" tace "to ai gani nayi hakan zai fi mana sauki da mutanen da zasu zo daurin auren, ace anyi aure da wata daya wasu ko gama kafe gajiya basu yi ba a sake juyowa yin wani auren kin ga ai akwai takura, ba gwara ayi a wuce wajen ba?" nace "Mommy ni bani da zabi, kuyi duk abinda kuke ganin daidai ne" tace "to Allah ya miki albarka, Yasa hakan shi yafi alkhairi.... Oh su Ummiey za a zama matar aure!" da sauri na kife wayar a kan gado na fara juyi akan gadon idanuna akan fuskata kamar Ina gaban ta. Abbu ya kira ni a daren ranar cikin tsananin farin ciki da murna, yace "kin gama yi mun komi Nafeesah, kin saka zuciyata cikin farincikin da bata taba shiga ba, Allah ya miki albarka Nafeesah! I'll definitely compensate you Amour, yau zan ma iya barci kuwa saboda murna?" da wadannan kalamai nashi na kwanta suna min amsa kuwwa a cikin kaina, tabbas I'll be the luckiest bastard on earth matukar na auri Abbu, Abbu!! Allah ya nuna min ranar da zan zama matar shi lalle zan kere sa'ah.

Bayan kwanaki biyu Abbu ya dawo daga Ilorin, da yake dawowar safe yayi gida ya wuce ya dan huta ya shirya kafin ya shigo cikin makaranta, lokacin muna cikin lab muna practical don haka yace in same shi a office dinshi idan mun gama. Sai karfe biyar muka fito, ban tsaya yin komi ba na tunkari ofishin Abbu cikin wani irin doki, ji nake kamar in yi fuffuke ko in bude idanuna in ganni a gaban shi, in dora idanuna akan kamilalliyar fuskar shi mai saka ni cikin nishadi, nayi kewar shi, ban taba kewar abu a rayuwata har nake ji numfashina yana daukewa saboda rashin wani abu kamar yadda nayi kewar shi ba, how I can survive without Abbu a rayuwata yanzu, only Allah knows. Jikina har rawa yake lokacin dana hau corridor da jerin offices yake ba, naja nayi burki a kofar ofishin shi Ina kokarin saita kaina kila idan na shiga kai tsaye a yadda nake zai iya zaton ko gudu nayi naxo gare shi. Na daga hannu da niyar yin knocking na jiyo wata murya tana magana, cikin Jan hankali, cikin kissa da kisisina, cikin wata murya dake baiyana tsananin bukatuwa da roko..... Zuciyata ce ta bada wani irin sauti da naji shi tamkar saukar aradu......
~Me kuke tunani game da chapter din Yau?
~Mommy fa? Ya kuka gani? Ta burge ku??
~Keep voting, sharing and commenting word by word dearies,
#TeamAbbu
#OneLove





*♡Jeedderh♡*
hh[12:19PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*



*42*


"Dr. Ibrahim baka tunanin lokaci yayi da xaka yi recognising din soyayya ta zuwa gare ka? Kana sane da halin da ruhina yake ciki saboda kai, soyayyar ka na azabtar da zuciyata a kowace rana amma kayi kunnen uwar shegu dani kana nuna kamar baka san komi ba, haba Ibrahim, ka tausaya min mana please!!" kafafuna suka shiga rawa na kasa yin knocking din da nayi niyar yi, a hankali na matsa ta jikin tagar office din da yake a bude take. Abbu yana tsaye ya juyawa tagar baya, ya rungume hannayen shi a kirji yana fuskantar ta yayin da ita kuma take fuskantar tagar duk da cewa dai bana iya hango fuskar ta amma yanayin shigar da tayi m not satisfied with it. Ko dai tayi kwalliya ne don tayi seducing din Abbu na ko kuma ta saba yin tambadaddiyar shiga ta marasa mutunci kamar yadda tayi yanzu. Abbu yace "Dr. Luba Ina ga wannan abu ai yana gare ki ne, ba tun yau ba na riga da na fada miki cewa Ina da aure har da 'ya'ya...." ta katse shi, "nima ai nace maka zan iya aurenka a hakan, meye hadina da matar ka ni? Kai zan aura ba ita ba!" yace "am getting married, in the next two months in shaa Allah!" ta laulayo wani ashar ta maka, "says who? Karya ne Dr Ibrahim, wallahi Karya ne! Babu 'ya macen data isa ta aureka Ina tsaye Ina kallo, idan ma wasa kake yi tunda wuri ka fadi kafin in aikata abinda ran mu ba zai mana dadi ba" yace "me yasa zan miki wasa? Ba tsoron ki nake ji ba kuma ba shakkar ki nake yi ba, ban san ko sau dubu nawa kike so in fada miki cewa bana son auren ki ba, you are not my type Ramlah" tace "but you are my type, and there's no way da zan zauna ina kallo a gaban idona wata ta dauke abinda nake so ba, Karya ne wallahi...." ta kara taku zuwa gaban shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi, ban san me ta rada mishi ba, naga dai taja da baya yayin da Abbu yayi shiru kawai, can kuma naji yace a hankali, "get out please Dr Luba" tace "ba kai kace in zo ofishinka ba ra'ayin kaina ne, don haka idan zan fita ma yanzu sai nayi ra'ayi, gashi kuma ban gaji da ganin fuskar ka ba, ya za ayi kenan?" na hangame baki cike da tsananin mamaki, lallai duniyar Allah mai fadi, xaka ga mutane daban-daban masu hali iri-iri, ita kuma wannan wacece? Zuciyata ta hau wani suya kamar zata fito daga kirjina, ji nayi kamar in banka kofar ofishin in shiga in jawo ta by her hair in fada mata Abbu nawa ne, in ma ta kai ga tofa mata yawu a fuska duk zan yi matukar zata fita daga cikin rayuwar Abin sona. Na koma ga kofar na fara knocking da karfina kamar zan balla ta, Abbu ne ya min izinin shiga. Na tura kofar na shiga with full of attitude and Charisma, so that wadda take ikirarin mallakar Abbu na ta karfi da yaji taga cewa am not the type of people da ake musu kwacen abinda suke so, abinda suke Jin cewa ba zasu rayu ba tare dashi ba right in front of their eyes ba tare da sun yi abu ba. Abbu ya juyo yana kallona, murmushin daya saki kadai yasa naji wani irin kwarin gwiwa ya mamaye ni, naji duk wata fargabar kada fa matar dake gabanshi ta kwace min shi ta tafi ta barni a take, tabbas Abbu shine mahadin rayuwata. Nima na mayar mishi da martanin murmushin wanda yake kunshe da zallar so da nuna tsananin kewar shi da nayi kafin idanuna suka sauka akan matar dake ikirarin claiming din abinda yake nawa. Ta sha uwar kwalliya a fuska saboda tsabar kwalliya ba zaka tantance ainihin kala ko kamanninta ba, tasha adon izgar doki wanda ya sauko a kafada da gadon bayanta, wani material ne a jikinta an mishi wani irin watsattsen dinki na Allah wadai wanda ya fito da shafaffen kirjinta kamar shafaffen silifas, dinkin ya matse ta tun daga kirjinta har cinyoyinta, ta wani kalleni tun daga sama har kasa yayin da nake kallonta disgustingly cikin nuna kyama kamar wadda taga abin kyankyami wanda na tabbatar da cewa sai ya kada mata 'ya'yan hanji. Abbu ya katse mana kallo-kallon da muke wa juna ta hanyar cewa "Dr Luba meet my dearing wife, Nafeesah. Nafeesah she's my co worker" nace "sannu, ya kike?" ta tabe baki tana wani yamutse fuska, "wannan abar ce dama kake wani tada jijiyoyin wuya kana cewa wai zaka aura? Me ta fini dashi?" Abbu yace "ko zaki iya bamu waje, Ina son sirri" ta buda kofofin hanci har suna naso, "ko baka ce ba yanzu zan bar maka ofishin ka kafin ka wulakantani a gaban wannan er yarinyar, sai dai kada kayi tunanin na hakura ne, ko ta halin yaya sai na mallake ka Ibrahim saboda kai nawa ne!" ta warci jakar hannunta ta fita tana murguda kugu kamar wani shafaffen plate saboda rashin cikowar shi, na bita da kallo Ina murmushin mugunta, matar nan ta rainawa kanta hankali da yawa, ni ta kira da yarinya koh? Allah ya kara hada ni da ita wani lokacin, ni kuma nayi alkawarin nuna mata aikin yarinta. Na maida kallona ga Abbu lokacin data fita daga office din ta maida kofar tayi banging kamar tashin duniya. Murmushi na sakar mishi softly, duk da cewa har zuwa lokacin zuciyana tana itching game da Luba ce ko Bana yace sunanta? Bana so in sani. Yaja kujera ya zauna a kusa dani tare da nuna min wata kujerar nima na zauna, yace "kiyi hakuri da abinda ya faru, kada kuma ki sa maganar ta a cikin ranki, ta saba irin wadannan maganganun duk burga ce da tauna tsakuwa don aya taji tsoro" nace "wai wace? Ni ban ma fahimci abinda take fada ba balle in saka shi a cikin raina...," ya kura min idanu yana murmushi, "kin san abinda yasa nake kara jin ki a cikin raina kenan? Nafeesah my other being" na sadda kaina kasa Ina dan murmushi, Abbu with his flirtations, a hankali nace "sannu da dawowa, ya hanya?" yace "it was tiresome, amma yanzu na dawo normal dana gan ki, my wife!" wayyo kunya! Na rufe fuska ta da hannuwana ina er dariya, shi kuwa dariya ya saki sosai, a tausashe. Nayi shiru Ina jin dariyar da yake yi, he sound so relieved and happy, and I feel proud knowing that ni ce sanadin farincikin da yake ciki.

Cikin barci na kai hannu kasan filona na lalubo wayata dake vibrating, duka-duka karfe goma ne da rabi na safiyar ranar Assabar, da yake ranar hutu ce kuma ban samu nayi barci da wuri a daren jiya ba shi yasa na ke jina kamar wadda ta kwanta a lokacin saboda tsabar barci. Ban ko tsaya duba caller ID ba na dauka, muryar Sadiya ce ta doki kunnena, "Asslm, Nafeesah hope ban katse miki barci ba?" cikin muryar barci nace "kin katse min mana" tace "sorry, dama muna nan AKTH ne shine zan fada miki" na tashi zaune a sukwane nace "Teaching Hospital kuma? Waye babu lafiya?" tace "Ni'imah ce wallahi, ta samu miscarriage yau da safen nan" jikina yayi sanyi sosai, Allah sarki Ni'imah. Nace "ki turo min da number din dakin da kuke, gani nan zuwa" na ajiye wayar tare da dirowa daga kan gado. Wanka nayi na fito na Karya, ban wani tsaya yin kwalliya ba na saka kayana kawai na fita, sai a cikin mota ne na kira Ramlah Ina fada mata, tayi jimamin abin sosai tace zata kira ta mata jaje. Ban samu Sadiya ba a dakin da aka ajiye su lokacin da naje, Anty Ameenah da Anty Rayyah suna nan a dakin tare da wata dattijuwa sai kannen Bashir mata su biyu, Ni'imahr na kwance tana barci an sa mata drip, ta wani dashe tayi fari tas kamar wadda babu jini a tattare da ita. Muka gaisa dasu Anty Ameenah cikin mutunci har tana bani hakuri akan wai an taso ni daga makaranta, nace a kunyace haba Anty, Ni'imah tafi karfin haka a wajena ai.... Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, suka amsa da ameen. Sadiya ta shigo dakin hannunta rike da na Jameel dan Anty Jameelah wanda yake tafiyar ta-ta-ta, muka gaisa da ita itama na musu jaje, naja Jameel a jikina ina tambayar shi inda yaje yana ta min gwaranci ina murmushi. Ni'imahr bata farka ba sai bayan azuhur, su Anty Ameenah suna waje suna sallah da yake ni fashin ta nake yi, na matsa gefen gadonta Ina mata sannu tare da tambayar ta abinda take bukata? Kuka kawai ta saka tana shafa cikinta, na rungumo ta a jikina ina dan jijjigata kamar nima in rushe da kukan nake ji, it's not easy ka dauki cikin abu ka raine shi, bayan ka gama kwallafa ranka a kanshi kuma sai Allah ya jarabce ka da rashin sa, hakika Allah kadai yasan irin sakayyar daya tanadarwa irin wadannan matan. Nace "kiyi hakuri Ni'imah, haka Allah yaso. In shaa Allahu zai kawo miki mafi alkhairin sa, stop crying please kinji?" ta jijjiga kanta. Naje na xubo mata ruwa a cikin cup ta kurba, lekawa nayi na gaya musu ta farka sai gasu sun duro cikin dakin, kowa sannu yake jera mata tare da nasihar fawwalawa Allah lamuranta, nan aka zuba mata abinci muma muka zuba namu muka ci. Da yamma sai ga Bashir din yazo ashe ma baya gari saukar shi kenan daga Abuja, bawan Allahn nan har da hawayen shi abin gwanin ban tausayi wallahi. Bayan Magriba su Anty suka yi haramar tafiya gida, Anty Rahina tace in zo ta sauke ni a makaranta mana nace mata ai ni anan zan kwana, tace inah! ga

Please Login or Register in order to submit comment