Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da safiyar ranar a falo sanye da wasu Pakistan riga da wandon su, na gyara gashina ya kwanto har gadon bayana yana ta sheki da kamshi. Gate naji an bude, nayi murmushi nasan Abbu ne ya dawo daga fitar da yayi. Na kara gyara zamana ina fuskantar mota, yana shigowa na tare shi da murmushi. A bakin kofar ya tsaya shima yana murmushin, hannu ya mika min alamun inje, babu musu na tashi na fara tafiya cikin jan hankali ina jujjuya jikina kamar wadda take rawa, kasa daurewa yayi in karasa ya taka da sauri ya taro ni tare da rungume ni. Sai daya gama welcome kiss dinshi and stuffs sannan ya umarce ni da in dauko hijabi zai nuna min abu a waje, na shiga daki na saka na fita na same shi yana jirana, hannuna yaja muka fita compound din gidan, dalla-dallan motoci biyu Land Rover Discovery fara da Vibe ja daga ganin su sabbi ne saboda yadda suke ta sheki a cikin soft hasken ranar ta alhamis. Ya miko min keys guda biyu, cike da tsananin mamaki nake kallon su kafin na maida kallona ga motocin, da kyar na iya kakaro “wadannan keys din fa Abbu?" yayi murmushi much like a grinning, “for you baby!" na zaro idanu na cikin mamaki, “duka?" ya zagaya ta bayana tare da rungume ni, “wannan..." ya nuna min jar vibe din, “is from me.... Wannan kuma..." ya nuna farar Discovery din, “is from your Daddy" nace “Dad kuma?" ya daga kafadar shi, “yanzu aka kawo ta daga can Kaduna, sai dana fada mishi cewa na sai miki amma yace shima tunda ya siya sai ki hada duka biyun kiyi amfani dasu" Daddy, my Dad! He's really the best. Ban fada mishi ba amma already ya riga yasan da irin motar da nake muradi, nayi tsalle na juya tare da rataye hannayena a wuyan Abbu ina dariyar dake nuna tsananin murna da godiyar da nake mishi duk da bakina bai furta ba. Ya miko min kumatun shi ba bata lokaci na bashi peck a kunatun, peck din daya koma deep mouth to mouth French kiss in a wink, in another wink na tsinci kaina a tsakiyar gadon Abbu, kayan sawa suna yin koina a cikin dakin....

Later da yamma na kira Daddy na mishi godiyar Mota, “Haba Uwata bari mana kar ki bata min rai? Meye abin godiya dan uba yayi wa diyar sa abinda yake responsibility dinshi ne? Beside saboda wa nake neman kudin idan ba ke ba uwata? All I wish for you is to be happy kin gane? Sannan zan tura miki da kudin sadakin ki ta account gobe in shaa Allah" nayi saurin cewa “Daddy ka bar su a wajenka pls" yace “aah, ai hakkin ki ne Nafeesah kuma ma ni bana son kudin ki" nace “to a ba Mommy" yace “itama bata so" ba shiri na saki dariya, nan muka yi sallama dashi.
Washegari kuwa ya turo min da kudin, dubu dari biyu bayan dubu dari ne sadakin, na kira ina tambayar shi dalili sai cewa yayi ai sabida in dinga ba baki da kuma sauran kashe-kashe saboda baya son in cika tambayar mijina, sai kawai nayi murmushi tare da mishi godiya.
Ina zaune Abbu ya fito daga dakinshi yana gyara karin hularshi cikin shirin tafiya masallacin juma'ah. Na tashi na taya shi kafa hular tare da raka shi har bakin kofa, yace “In kawo miki su Hafsy ne su miki yini?" da sauri kuma cike da doki nace “ehh, please Abbu" yayi dan murmushi tare da juyawa ya tafi ina mishi Allah ya kiyaye hanya. Yana tafiya na fada kicin na hau shirya musu cookies da kayan motsa baki ga kuma abinci, ina kicin din ma suka shigo gidan su da Abbu da ihun su suna kiran sunana, da sauri na fita waje nan suka kwashi ihu suka rugo suka rungume ni, nima na rungume su ina murnar ganinsu, sai da muka nutsa sannan na dago kai ina kallon Abdullahi dake gefen Abbu a tsaye, na mishi dan murmushi ba tare dana damu da yadda bai yi joining dinsu ba. Daga baya dai muka tashi muka koma cikin falo, na dauko musu duk abubuwan dana shirya musu nan fa hira ta barke, bayan mun ci abinci Abbu ya tafi daki ya dan kwanta kafin a kira la'asar ya barmu muna ta hirarrakin mu, har baya muka fita muka danyi wasanni kafin muka dawo falon. Yini guda suka mana sai bayan magriba Abbu ya maida su gida, don Hafsy ma da kafewa tayi anan zata kwana sai da kyar Abbu ya lallasota ta hakura suka tafi. Na hada su da tarkacen sweets, chocolates da tarkace dai iri-iri suka tafi.
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare





*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋



*52*


Ban sani ba shagala ce ko kuwa mantuwa? Zancen cewa angwaye kwanaki bakwai suke yi a dakin amaren su su koma na uwargida, kai in fact na manta cewa ma ina da abokiyar zama kwata-kwata a lokacin, na manta cewa bani kadai bace wadda take da Abbu, na manta cewa Abbu yana da wasu iyalan daya kamata ya kula dasu. Muna cikin cin abinci yake fada min cewa washegari idan zai je gidan Mubeenah zai dauko cousin dinsu Zaynab diyar wata kanwar mahaifiyar su zata dinga zuwa tana taya ni kwana. Na maida spoon cikin plate dina na ajiye ina kallonshi cikin alamun tambaya, and that was when it downed on me, ranar na cika sati daya cif da tarewa which means washegari zai fita daga dakina. Jikina yayi wani irin sanyi har yana hadawa da rawa na dai daure na cije na gyada mishi kai naci gaba da tura abincin da taste dinshi ya bace a bakina.
Duk yadda naso na daure in nuna mishi hakan bai dame ni ba kasawa nayi, sai daya fahimci sanyin da jikina yayi. Ya riko hannuna ya zaunar dani akan cinyar shi tare da dago fuskata, na daga idanuna da suka fara cika da ruwa na kalleshi, yace “come on mana baby kar ki bayar dani, meye kwanaki biyu kadai? Besides, zan dinga zuwa kullum ina ganinki kinji? Kuma zamu kasance a waya a koda yaushe don haka ki daina bata ranki, ni naki ne ok? Oya, give me that gorgeous smile of yours baby" na kuwa saki murmushin tare da dora kaina akan kirjin shi.

Washegari da safe ya tattara ya tafi bayan ya jira Zainab tazo, yarinyar tana da kirki ga fara'ah, na dan girme mata da shekaru tunda shekarunta ashirin. Na raka Abbu har bakin mota duk da sallamar da muka gama yi a daki, yaso ya kaini gado a lokacin nace a'ah, ba zan shiga hakkin abokiyar zamana ba don nima bana so a shiga nawa hakkin. Haka ya tafi ina daga mishi hannu har sai daya fita daga gidan maigadi ya maida gate ya rufe kafin na juya cikin gida cike da kewar Abbu, zama nayi muka dan yi hira da Zaynab kafin na shige dakina na kwanta don jiya Abbu bai barmu mun yi barcin kirki ba.

☆☆☆☆☆

“Wannan yace a cikin abinci kamar miya ko fate zaki zuba mishi yaci, manta kowa kenan. Ina mai tabbatar miki da cewa idan har yaci wannan maganin to wallahi sai dai uwarshi ta sake haihuwar wani, kin dai ga yadda mijin Umaimah (er autar su) yake mata, uwar shi ma yanzu sai Umaimah taso yake ganinta balantana wata banzar bazara wai ita kishiya, kema to haka zaki mallakeshi..., wannan kuma...." Saddiqa ta fito da wani ruwa a cikin kwalba tana nunawa Mubeenah, “...a cikin ruwan wankan shi zaki zuba mishi, shi kuma zai sanya mishi matsanancin son ki ne, ya zama babu wata ‘ya mace a cikin idanuwan shi sai ke ina fada miki, boka Saddar ya bani tabbacin a ranar zai dankarawa ita waccar banzar kishiyar taki saki uku, shi da kara aure kuma sai a lahira. Don haka ki kula sosai, ki bi komi a hankali yadda ya dace don hakan mu ya cimma ruwa kin gane?" kamar wata kadangaruwa ta gyada kai, “yauwa, ina turaren dana kawo miki last week nace kiyi tsuguno dashi?" Mubeenah ta gyada kafada, “turare? Na ma manta inda na jefa shi" Saddiqa ta maka mata harara, “wai ke banzar wani gari ce? Duk inda yake ki lalubo shi kiyi tsuguno dashi yau ba gobe ba, yaushe girkin ki zai fita?" tace “gobe da safe" tace “bamu da lokacin batawa kenan, yau yakamata yaci maganin, yayi wanka kuma ya kusance ki kina jina? Abubuwan nan da muke yi is all for u Mubeenah, kin dai san kaf danginmu babu mai kishiya sai waccan banzar yarinyar (Shakira) don kishiyar Umaimah hoto ce, don haka kema ba zaki biyo sahu ba kin gane??" Mubeenah tace “ehh".
Tayi murmushi, “yauwa., kudin aiki dubu dari da hamsin tashi maza ki dauko min" Mubeenah ta zaro ido, “dari da hamsin?" ta harareta, “to meye dari da hamsin matukar an samu biyan bukata?" Mubeenah ta gyada kai, “hakane kam. Sai dae babu kudi a hannuna sai dai idan Ibrahim ya dawo sai in amsa a wajen shi" Saddiqa ta yago hakura, “to babu damuwa, amma to dari biyu zaki tura min tunda dai nasan kema in kika tashi ba a dari biyun zaki tsaya ba" suka kwashe da dariya.
Nan taci gaba da kitsawa Mubeenah abubuwa har yamma ta gabato sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta kwashi manyan atamfofi biyu da lesuna cikin kayan da aka kaiwa Mubeenah na fadar kishiya bayan ta gama kwashe musu albarka, ji fa!. Mubeenah ta dawo daga rakiyar ta ta tsaya ta leka dakin Abbu, tun jiya daya dawo daga gidan Nafeesah ya leka ya gaya mata ya dawo tare da fada mata ya raba musu girki kwanaki bibbiyu bata sake ganin shi ba. Yanzu ma baya nan gashi akwai maganganu da take so suyi.

Dakinta ta koma, magungunan da Saddiqa ta kai mata suna zube akan gado, ta zauna a gefen gado tare da kura musu idanu kamar wadda take muhawara, ta saki ajiyar numfashi tare da tashi tsam ta dauki magungunan. Toilet ta shiga ta zazzage su a cikin masai tare da yin flushing, dama turaren data kai mata Harira ta ba ta jefa shi cikin kwatami. Daya daga cikin manyan abubuwa da Mubeenah bata so kuma bata ma yarda dasu ba shine bin malamai da bokaye, tana mamakin yadda mata suke yarda da karerayi da soki-burutsun bokaye da malamai, a ganinta in kura na maganin zawo to tayi wa kanta mana?? Shi yasa tasu ta matukar zuwa daya da Shakira kanwar su, sam bata cikin harkar bin malaman da sauran en uwansu suke yi, ta kan ce ita tafi ganewa tayi yaki akan abu ta yadda idan ta mallakeshi zata yi alfahari da cewa saida ta share zufa ta sha wahala kafin ta same shi ba wai a ruwan sanyi ta hanyar bokaye da yan tsibbu ba, kuma gaskiyarta.

Tunda gari ya waye take leke-leke da zarya daga falo zuwa dakinta. Ta kula kwata-kwata ya daina zama a cikin gidan, tana mamakin inda yake zuwa cikin kwanaki biyun daya mata. Tana nan zaune a daki taji tashin muryoyin su dasu Qaseem wadanda suke hutun makaranta ranar, Sai data ji shiru alamun ya shiga dakinshi sannan ta tashi tsam!.
“ok baby sai na iso, kar ki manta anjima da yamma dai zamu fita in fara koya miki tuki" na danyi tsalle daga zaune din da nake, “yeyh! Abbu na, sai kazo. Please ka taho da wuri fa!" yayi er dariya, “missing me that much??" dariya kawai nayi na kashe wayar. Shima dan murmushi yayi ya ajiye wayar yaci gaba da shirya takardu a cikin brief case din shi.
‘Baram!! Karan sautin turo kofar dakin nashi kenan kamar tashin duniya. Tun kafin ya juya yasan ko waye ya shigo, haka take shigowa dakin babu knocking balle sallama, kofar dakin ma haka take turo ta, duk ranar data shigo a hankali to ranar nema take a wajen shi.
Bata yi magana ba ta coge a bakin kofa, shi kuwa yaki daga kai ya kalleta yaci gaba da abinda yake yi har ya gama ya rufe brief case din. Wardrobe ya bude ya fara ciro kaya, ta kankance idanu cike da masifa ganin yadda yake abubuwan shi kamar bai san da Allah yayi ruwan tsirarta a cikin dakin ba.
“Ibrahim! Ina so muyi magana da kai!" ta fadi kanta tsaye cikin izza, ya juya a hankali tare da kallonta. Wani malulun bakin ciki da bacin rai suka kawo mishi wuya, wasu pyjamas ne a jikinta daga ganinsu sun dauki lokuta ba a wanke ba, ta kawo wata hular beanie ta maka a kanta fara ce amma tayi bakikkirin ta dafe alamun ta kwana biyu, gashin kanta da yayi cukus-cukus a cikin hular ya maida ta kamar irin sababbin kamun nan. Ya hade fuska sosai wadda tasa ta shiga hankalinta ba shiri amma hakan bai hanata yin dibar albarkar data kawo ta ba. “Ibrahim mai kake nufi da nine, an kawo amarya ban ga kalarta ba, ka kama ka killace ta a waje guda saboda ita er goal ce, er nasiha ta hadin kai da naji mazaje na hada matansu waje guda su musu kai baka yi hakan ba, ka dawo daga gidanta kaxo nawa amma har ka gama kwanakin ka amma sau daya na saka ka a cikin idanuna, anya Ibrahim baka dauko hanyar da amaryar ka zata raina ni ba kuwa??" ya jingina da jikin wardrobe din yana watsa mata kallon uku-taro, sai data dire aya sannan ya ajiye numfashi, “killace amarya kamar yadda kika ce nayi sabida ta kai matsayin a killace ta dinne, Nafeesah ba er gwal bace er diamond ce Mubeenah. Kawo amarya gidanki damka amana ni na hana saboda ban ga dalili ba, ke kanki ya kike kula da taki rayuwar balle har ki kula da rayuwar er wasu? Maganar rashin gani na da baki yi ina ji kin manta ne, dama can muna daukar satika ma bamu ga juna ba alhalin muna gida daya yanzun ma ina ga ai bata canza zane ba koh?" tayi tsuru tana zare idanu, maganar daya fada haka take, ita kanta bata san dalilin sako maganar ba, kawai maganar has been eating her brain ne dole ta fade ta ko ta samu sawaba.
Tayi gyaran murya tare da cewa “whatever! Amma kasan dai saboda Allah baka kyauta ba, kuma naji ance ka sai mata manyan motoci har guda biyu bayan ni ka bar ni da tsohuwa ina fama, tun kafin tafiya tayi nisa zaka fara shimfida rashin adalcin da ake cewa dama a jinin ku maza yake?" yayi murmushi cike da takaici, dama yasan duk inda zata je ta dawo dai maganar kenan. Ya daga kafada, “mota yeah, ni na sai mata daya Daddyn ta ya sai mata daya, ina ce kema lokacin da aka kawo ki an sai miki mota?" “karya ne!" ta fadi cikin hargowa, “karya kake yi kai ka sai mata, motar da kake fada ai Mahaifinka ne ya sai min da kudinshi ba naka ba mai ya hana kai ka saya min da kudin ka ko kuma yanzu daka sai mata nima ka sai min idan ba rashin adalci ba??"
Ranshi ya baci sosai, ya sha daukar fiye da haka daga wajen Mubeenah, ya sha jin munanan kalmomi daga gareta duk yana shanyewa amma yau baya jin zai iya shanyewa. Yana da hakuri sosai, sai dai duk ranar da aka kai shi bango akwai matsala. Tun daga tsawar daya daka mata Mubeenah tasan cewa ranar ta tsallake layin hakurin Abbu. Idanunshi sun juye saboda bacin rai, “enough Mubeenah! Ya ishe ki, ya ishe ni haka nan. Mota bani na sai mata duka biyu ba amma da ace idan nayi hakan Nafeesah zata karba happily da wallahi sai na sai mata fiye da mota biyu. Kin san saboda me? Saboda Ina Son Ta!! Saboda tana kula da farin cikina, saboda ita kadai nake kallo in san cewa yes! Ina da mata, in san cewa akwai wani da zan ba umarni kai tsaye yayi, akwai wadda bata zartar da komi sai da yawuna, akwai wadda zan bugi kirji ince Matata ce in kuma nuna ta a koina cikin duniyar nan ba tare da fargabar zata muzanta ni ba. Saboda ita kadai ce take bani hakkina ba tare da na biya ta ko sisi ba, saboda itace matar da nake sa ran zata haifa min yara ta kuma shayar dasu ba tare dana biya ta kudin shayarwa ba!! Saboda... Nafeesah itace komi nawa!! Zaki ga laifina idan na sayi jirgin sama na damkawa wannan matar kuwa?".

Mubeenah tayi shiru kanta a kasa, tunda take dashi bai taba mata ihu irin na ranar ba, bai taba daga murya kamar haka ba, duk abubuwan daya fada ta aikata har da ma wadanda bai fada ba duk tayi kuma sun faru, kalma daya data doke ta... “Kana Son ta?? Ni fa?! That means baka so na kenan?" without second thought ya gyada mata kai, “kwarai Mubeenah! Ni dake duk mun san cewa zaman hakuri da zaman ‘ya‘yanmu muke yi, amma zancen ‘so' kin san cewa babu shi a tsakaninmu" ta fara girgiza kai, bai jira mai zata sake ce mishi ba ya warci brief case dinshi a fusace ya ratsa ta gefenta zai fita, kofar dakin ma ko albarkacin ta rufe ta bata samu ba, tsoron shi daya Allah yasa cikin yaran babu wanda yayi over hearing din conversation dinsu yasan may be ya saka confusion a cikin kansu. Ranshi ya kara baci da wannan tunanin, daga bayan shi ya juyo muryarta a kausashe “Nafeesah!...." tun ma kafin ta gama fadin abinda tayi niyya ya juyo a fusace, “don't you ever dare drag her into this, ba irinki bace ita saboda haka ke kici gaba da laluben duniya ki barta taci gaba da laluben lahirar ta!" ya juya a fusace ya bar gidan zuciyar shi na azalzalarshi cike da bacin rai ko sallama bai wa yaran nashi ba da suke dakinsu suna kallo.
Mubeenah ta bishi da kallo cikin bacin rai na maganganun daya yaba mata yanxu, fargaba da tsoron anya bata bari kwabarta tayi ruwa ba kuwa? Dana sanin ina ma tayi amfani da magungunan da Saddiqa ta kawo mata???

******
Muna gama waya dashi falo na koma ina jiran karasowar shi. Ina cikin zaman jiran ne Zaynab ta fito daga dakin dana ware mata a sukwane tana ihu, “Anti Nafeesah.... Anty Sadiya ta haihu yanzu!!" nayi ihun nima tare da direwa cikin murna, sai da muka gama iface-ifacen na tambayeta abinda ta haifa tace Mace. Ba bata lokaci ta shirya ta tafi ganin baby. Na zauna ina jiran dawowar Abbu impatiently ina jin kamar inyi fuffuke inje inda suke. Ina dakina ina canza kaya daga shigar da nayi ta wani mini daya tsaya min a gwiwa da half vest mai hannu daya ta taryar Abbu zuwa riga da zani na atamfa, ban san ya dawo gidan ba sai dana leka waje naga motar shi a fake sannan. Abin ya bani mamaki, nayi tunanin zai shigo dakina direct idan bana falon kamar yadda yake yi, ban kawo komi a raina ba na nufin dakin da saurina cike da doki. Na tura kofar ko sallama doki bai bani damar yi ba na fara zuba mishi bayanai, “Abbu yanxu Sadiya ta haihu, kazo ka kaini in ga baby ka ji??" kwance yake yayi rub da ciki ya tura kan shi cikin filo, na zauna a gefen gadon ina dan jijjiga shi alamun ya tashi, “Abbu.... Abbu kaji?" nan ma shiru babu magana, ban sani ba common sense ne ya dauke min ko kuwa? Ban yi tunanin ina takura mishi ba ko barci yake yi naci gaba da jijjiga shi, “Abbu kazo ka kaini in ga baby kaji? Abbu??"
Juyowa yayi a fusace, cikin muryar dake hauhawa da bacin rai yace “Oh God Nafeesah!! Will you please just shut up and leave me alone??" jikina yayi sanyi ganin yadda fuskar shi take cike da bacin rai, “amma Abbu.." na fara magana in protest, “leave me alone!!" ya fada cikin karaji, sai kuma naga ya dafe kanshi da sauri, ya lumshe idanunshi na en sakanni kafin ya bude su, “please!!" ya fadi cikin sanyin murya wannan karon. Jiki na rawa na tashi na fita daga dakin ina tambayar kaina me ya hau kan shi??
Kujera na laluba na zauna cikin tsananin sanyin jiki, ban iya daurewa kwallar data taran min ba sai data gangaro kan kumatuna, gabadaya sai na dora laifin fushin Abbu a kaina. Watakila ni na dame shi da hayaniya har ranshi ya baci, kila barci yake yi na tashe shi da hayaniya kun san yadda mutane kan zama moody idan sun tashi daga barci balle shi da naje ina jijjigawa abinda Anty Shafa tace mata basa tashin mazajen su daga barci ta wannan hanyar. Ko kuma yana bukatar kadaici ne ni kuma ban kula da hakan ba? Idan haka ne kuwa ai laifi na ne. Tashi na sake yi na koma dakin, lekawa nayi kamar munafuka wannan karon yayi rigingine, na shiga dakin a hankali tare da maida kofar na rufe, barci yake yi. A hankali na dauki bargo na rufa mishi, na juya kenan naji an riko hannuna na juya da sauri. Ya bude idanunshi da suka shige ciki har sun canza kala ya kalleni dasu, take naji wani irin bacin rai na shige ni. Na samu kaina da tuhumar kaina da responsibility na bacin rai da yake ciki, a hankali nace mishi “kayi hakuri Abbu!" janyo ni yayi na fada kan gadon tare da jana jikinshi ya rungume ni, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri, yace “noo, am sorry! I shouted at you bayan baki yi mun laifin komi ba" na kwantar da kaina akan kirjinshi ina shafa saitin zuciyar shi da hannuna, “Allah ya huci zuciyar ka Abbu na. Wanda ya bata maka rai bai kyauta min ba ni kam tunda nima yasa nawa ran ya baci" kuma gaskiya na fada, raina ya baci kwarai daga ganin bacin ran dake dankare akan fuskar shi. Yayi dan murmushi tare da jan bargo ya rufe mu dashi muka shiga barci.

Koda muka tashi

Please Login or Register in order to submit comment