Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wadannan abubuwan ba Nafeesah.... Wannan din ma ya zamar min dole ne, naso ganin wani very badly kuma babu hanyar ganin nashi sai ta nan shi yasa" na gyada kai kamar na fahimce shi, sai dai maganar gaskiya na kasa processing maganganun shi a cikin kaina, babu abinda nake fahimta a lokacin irin daddadan kamshin turaren shi dake tashi da yadda zuciyata take bugu. Ya zura hannu a cikin aljihu ya ciro rafar kudi sababbi kar dasu ya miko min, naki saka hannu in karba har sai da yayi magana, "kudin liki ne ba wani abu ba, karbi" da sauri na hau girgiza kaina, "ina dasu nima Abbu ka bar kudin ka" ya hade fuska "akwai abinda na taba baki a duniyar nan ba tare da kin min gardama ba kuwa?" nace "Abbu Allah ba gardama bace, kawai akwai kudin likin a wajena ne nima" yace "to tunda na baki ai sai ki amsa koh?" na bude baki zan yi magana ya sake hade muryar shi, "Nafeesah karbi kudin nan kafin raina ya baci fa" yana iya? Sai kawai na saka hannu biyu na karba har da dan dukawa nace "Nagode sosai Abbu Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen.... Go back" ba musu na mishi sai da safe na wuce, ina jin idanun shi a kaina har na shige cikin hall din. Na koma wajen su Ramlah na zauna, lokacin da aka kira amaren suka fita wajen rawa muma muka tashi muka je muka fara liki. Sai sha biyu saura aka tashi daga wajen dinner dinnan, an daiyi komi lafiya an gama. Kafin mu isa masauki sai wajen karfe daya aikuwa mun sha fada sosai wajen Anty Ameenah kamar me! Washegari aka kai Amaren gidajen su na aure, ita Sa'adiya tana Lamido Crescent Ni'ima kuma suna Zoo road. A gidan Sa'adiya ne muka hadu da Ikram, mun gaisa da ita sama-sama tana ta wani shan kamshi ni kuwa ina mata dariya a ciki don nasan dalilin hade fuskar, sai a lokacin naji ashe cousin din mijin Sa'adiya ce. A washegari naso komawa gida Anty Ameenah tace ina! Ai sai na cinye sati daya din da aka bani daga gida, ban yarda da gaske take ba sai data dauke min jakar kaya ta kulle a bedroom dinta, ni wallahi dariya ma ta bani. Dole haka nan na zauna, dama kwana biyu suka rage min. Naje gidan Anty Haleemah da Anty Raliya, washegari kuma direban gidan Anty Ameenah ya kaini gidan Abbu. Da yake ranar Lahadi ce na samu Abbu a gida, na ga tarbar data bani mamaki kam. Tun daga bakin gate su Hafsy suka taro ni suna ihun murna har cikin falo. Gidan yana nan kamar yadda na tafi na barshi, matar gidan tana uwar daka. Na shiga har ciki muka gaisa na koma falo wajen su Hafsy, nan suka fara ajiye min tarkacen kayan makulashe muka shiririce anan muna hirar mu har aka kira sallar Axuhur, Abbu ya fito daga dakinshi sanye da jallabiya ruwan toka da alamun masallaci zai je, na zamo daga kan kujerar da nake zaune na gaida shi, ya amsa tare da wuce mu su Abdullahi suka tashi suka bi bayan shi ni da Hafsy kuma muka shiga dakinta muka yi tamu sallahr.

Abbu ya mana odar abinci daga restaurant muka ci namu ni da Hafsy a daki. Ina nan a gidan har yamma tayi, direban Anty Ameenah ya dawo daukata, na je nawa Anty Mubeenah sallama muka fita zuwa inda direban yake jirana cikin rakiyar su Hafsy. Abbu yana zaune akan kujera da laptop a gabanshi akan dan karamin table yana ta danne-danne a ciki. Na fasa shiga motar da nayi niyar yi na taka zuwa gaban shi, ya dago ya kalleni yana murmushi. Na sadda kaina kasa cike da kunya, "Abbu zan wuce" ya gyada kai, "gobe zaki koma koh?" na gyada kaina, yace "nima ina so zan shiga Kadunar gobe in shaa Allah. I'll drop you off goben, that is idan tafiyar tana nan" na kalleshi fuskana dauke da alamun tambaya sai dai na basar, ai yace akwai abinda zai kaishi kuma ma cewa yayi sai idan tafiyar tana nan ne sannan zai ajiye ni. Nayi murmushi nace "to Abbu, na tafi" ya gyada kai yana jifana da murmushin nan nashi, "ok Nafeesah! Mun gode da dariya" na danyi murmushi tare da juyawa na tafi. Muka sake yin sallama dasu Hafsy na shiga mota muka tafi, daidai saitin Abbu na dan saci kallonshi, idanunshi suna kaina yana kallona da wani irin yanayi da kallo with so much affection, nayi saurin sadda kaina kasa ban dago ba har sai da muka bar layin.

*******

Na fito jaye da trolley dina, Anty Ameenah tana zaune akan kujera a falonta ta kalleni tana murmushi, "tun kafin yamma tayi har kin gaji damu koh Nafeesah?" na girgiza kai ina murmushi nima "haba Anty ba haka bane, karfe hudu fa tayi already kuma kinsan akwai tafiya a gaban mu" tace "haka dai kika ce. Mun gode sosai duk da haka" na fara tafiya yayin data tashi ta biyo bayana. Abbu yana tsaye a jikin motar shi Toyota yana jiran fitowar mu. Hasken ranar dake haska shi ya kara haskaka shi cikin shigar Dogon wandon jeans baki da bakar shirt, hakan ya haskaka shi ba kadan ba. Kyawun shi da cikar kamalar shi suka kara fitowa sosai, ban san cewa na shagala a kallon shi ba sai da naji Anty Ameenah ta dan zungure ni, a matukar kunyace na sadda kaina kasa. Ya Allah! Abinda Bawan nan naka yake saka ni yi!! Ya bude booth muka saka akwatina a ciki. Na bude gefen mai zaman Banza na shiga na zauna, Anty Ameenah ta leko tana min addu'ar a sauka lafiya har Abbu ya shiga shima ya tashi motar muka tafi. Tuki yake yi a nutse kuma cike da kwarewa, baka jin motsin komi a cikin motar kamar babu abu mai numfashi a ciki. Ya kunna kira'ar Sudeis cikin Suratul Maryam, na dan kwantar da kaina a jikin kujerar. A matukar takure nake ji na, it felt so awkward for me, to be hooked up with someone you so much cherish, wanda nake hangowa a matsayin mijin da zan aura, wanda da kyar nake hana kaina throwing my self to him a duk lokacin dana ganshi, yanzu da muke tafiyar nan sai nake jin wani iri a jikina, gashi duk yadda naso koda barci ne inyi abun yaci tura. Muna barin cikin gari Abbu ya ware injin mota, lokaci zuwa lokaci za a kira shi a waya ya daga da wannan damar nake samu in kare mishi kallo. Abbu is really good looking and handsome man. Wajen karfe shida muka fara shiga Kaduna, na dan sauke ajiyar zuciya a hankali ina jin kamar in bude idona in ganni a tsakiyar gidanmu. Well, it has really been a hell of a ride (-Justin Bieber). Can u believe that tunda muka shiga mota kalma daya bata hada mu dashi ba?? Suddenly naga yayi parking din motar a gefen hanya, wani dan karamin daji ne gab da za a shiga Kaduna. Inda yayi parking din motar gaban wata korama, reflection din rana da take kokarin faduwa ya fita zane a Vikings, the view was wow! Gashi wajen babu hayaniya sai ta ababen hawa dake ta wucewa a guje. Na daga idona na kalleshi cike da mamakin dalilin da yasa muka tsaya anan, idanun shi suna ga koramar dake gaban mu, he seems out of the world, ya shige duniyar tunani. Na dan yi gyaran murya tare da cewa "Abbu.., laa.... fiya muka.... tsaya??" a hankali, bai kalleni ba, haka bai yi magana ba. Sai na tsaya kawai ina son in ga abinda xai faru. Lokaci mai tsayi muna a yanayin da muke har hasken rana ya fara daukewa duhu ya fara shigowa, tsoro ya fara shiga ta. Abbu ya kira sunana a hankali kamar mai rada, "Nafeesah!!" na kalli sashen da yake tare da amsawa, shiru ya sake biyo baya na kimanin minti guda. Kamar daga sama, kamar a duniyar mafarki naji saukar maganar, "Nafeesah! Zaki Aure ni??!". Tsabar firgita da mamaki sai da kaina ya buge da glass din motar, ban damu da zafin da naji ba Abbu kawai nake kallo kamar wata sabuwar mahaukaciya ko kuma shine nake wa kallon sabon mahaukaci?? Ganin expression din dana nuna yasa ya dan kauda fuskar shi daga kallona, "Nasan baki taba tsammanin faruwar hakan ba Nafeesah, na sani. Ni kaina nayi hesitating fada miki maganar nan yafi sau dari, sai dai I couldn't anymore. Auren ki nake son yi Nafeesah da gaske, ina kuma fatan cewa zaki aminta da hakan?" ya juyo ya kalleni. Allah ne kadai yasan yanayin da nake ciki a lokacin, baki nake so in daga a lokacin in amsa mishi da YES! Da duk karfin da Allah ya bani, in gaya mishi nima burina kenan sai dai ina! Na ma manta yadda ake yin magana a dan lokacin. Wasu kyawawan mintuna biyu suka wuce a haka, wasu masallatan har an fara kiran sallar magriba. Abbu yace "look Nafeesah! M not forcing you into this kin gane? Zan baki lokaci kiyi tunani da kanki don bana so in tauye miki hakkin ki Nafeesah, idan nayi haka na cuce ki. I just..... M just tired Nafeesah. I want us to get married ASAP. Hell, idan kika amsa min yanzu m ready to marry you tomorrow Nafeesah.... Na baki lokaci ki samu time ki yanke shawara akan abinda kike gani sai dai kada ya dauki lokaci pls, sannan ina so kiyi duba da Allah da soyayyar da Iyalina suke nuna miki Nafeesah, we really need u in our lives". Da wannan ya tashi motar muka kara gaba, duk yadda naso in dawo cikin natsuwata abin yaci tura, yes! I was shocked beyond my imagination. Har yayi parking a kofar gidanmu, ina jin yana gayawa Mai gadi da yake kokarin buddy kofa ba shiga ciki zai yi ba, Mai gadin yazo ya bude saitin kofar da nake yana jera min sannu da hanya. Kamar wadda aka daddaba daga barci, sai lokacin duniyata taci gaba da juyawa da dai tsayawa tayi cak. Na zura kafana daya waje da niyar fita, Abbu ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana. Na dakata ba tare dana juya na kalleshi ba, bani da kuzarin kallon shi, ina tsoron abinda kallon fuskar shi zai haddasa min. Nasan zan iya amsa mishi da yes a take a lokacin. Yace "please think about US carefully Nafeesah, ina fatan jin daddadan labari daga gare ki" na karasa cira daya kafar na fita daga motar. Mai gadi ya maida mishi murfin motar ya rufe, ya sungumo trolley dina ya biyo ni dashi. Da kyar nake daga kafa ta. Taimakon Allah ne kadai ya kaini cikin gida, Mommy ta fito da saurinta tana min oyoyo, gani na a haka sai data yi turus. Ta matso tana tambaya na lafiya na lau kuwa? Da kyar na iya daga baki nace mata "gajiya" tace "shine kuma kika yi zuru-xuru haka? Wuce kije kiyi sallah kici abinci sai ki kwanta" babu musu na shige dakina. Na dauro alwala nayi sallah, yadda nake jin cikina a cike nasan babu abinda zan iya ci a lokacin. Ko kayan jikina ban cire ba na haye gado tare da lashes wutar dakin. Ina jin lokacin da Mom ta leko dakin ta maida min kofar dakin ta rufe. A gajiye nake, barci nake ji, sai dai awa daya kenan da kwanciyata babu alamun barci a tattare dani. Maganganun Abbu suke replaying a cikin kwalwa ta over and over, for once in my life da naji farin ciki yana so ya saka ni kuka, sai dai shima kukan yaki zuwa. Ya Allah!! What in the world am I suppose to do??! Ranar nasan dama babu barci, ina zan iya barci dama idan har na cigaba da hango ni zaune akan gado a cikin gidan Abbu lullube da gyale???





*♡Jeedderh♡

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*34*


Da murmushi na tashi akan fuskata, rabon da inyi barci mai dadin na yau har na manta. Naje nayi brush na fito falo, babu kowa a falon dama nasan ba lallai in ga kowa ba saboda karfe goma sha daya na safe ne lokacin. Break fast na fara yi kafin na shiga dakin Mommy na gaida ta. Tace inje in shirya zata aikeni gidan Aunty Uwani, da saurina naje na watsa ruwa na shirya na fito. Turaren wuta ne da kayan labule da bed sheets ban san dai kona waye ba sai da naje can take ce min na diyar kanwar mijinta ne. Can kuryar dakinta na shige na nade akan gado ina kara tunanin makomar zancen Abbu a cikin raina, wani bangare yana shawarta ta da in kira shi a yanzu in fada mishi na amince, wani kuma yana gaya min hakan bai dace ba, wani kuma yana ce min in dan bashi lokaci dai gabadaya na rasa wanda zan dauka, a haka barci ya dauke ni saboda rashin barcin da ban samu a daren jiya ba, sai wajen karfe uku Anty Uwani ta tashe ni nayi sallah, bayan la'asar na musu sallama na wuce gida. Ina zuwa na ba mommy sakon data bani in kawo mata na wuce daki, ba a jima ba na fito muka shiga kicin da ita muka fara girki.

Kamar yadda yake Al'adar gidan mu, bayan an gama muna haduwa a dakin Daddy a yawancin darare, wani lokaci muyi kallo wani lokacin hira, sometimes ma musamman idan daddy yana ayyuka zaku ga kowa abinda ke gaban shi kawai yake yi. Ina zaune a kasan kujera ina browsing Mummy kuma tana kan kujera a xaune, Daddy ya fito daga bedroom din shi ya zauna a kusa da Mommy. Daddy ya kira sunana in a serious tone, "Uwata" na amsa a nutse tare da kallon shi, yace "last two weeks da suka wuce Ibrahim ya same ni da wata magana mai Muhimmanci" yayi shiru yana kallona yayin da zuciyata ta hau duka kamar zata fado kasa, ya cigaba da magana "Yace wai Yana So Ya Aure Ki! Ni kuma nace mishi sai naji daga bakin ki don bana son tursasa ki akan abinda baki da niyar yi, me kika ce? Zaki Auri Ibrahim?" Na sadda kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna, ban san abinda yakamata in ce ba, ina son Abbu kuma Ina son Auren shi? Ina son Abbu amma ina tunanin auren shi is not a good idea? Ko kuwa me zan ce?? Mommy tayi saurin riga ni magana, "Haba Abban Ummiey, kaima kasan cewa wannan ba abu bane mai yiwuwa. Shi bai yi tunanin abinda zai zo ya dawo bane ya kirkiro wannan magana? Wannan abu ba zai yiwu ba sam!" duka ni da Daddy muka kalleta, fuska a hade sosai take yin maganar, daga ganin yanayin idanunta nasan cewa she is strongly against it, sai jikina ya kara yin sanyi akan na da. Daddy yace "me kike cewa ne haka Habibty?" tace "Abinda ya kamata mana, Idan shi idanun shi sun makance da cin Amana bai kamata naka su rufe ba Abban Ummiey. Haba! Ace daga tura yarinya yin IT na wata shida kawai sai aji wai ta buge da aure mai gida? Kaima kasan cewa wannan ba abu bane da zai yiwu ba, sai dai idan so kake ka saka mu a bakin duniya kuma" Daddy ya danyi murmushi, "sai dai idan basa son junan su Habibty, amma idan suna so then who cares about what people will say? Su mutane ai aikin su kenan ina tabbatar miki idan kika ce zaki biye ta mutane to numfashi ma sai sun miki izinin kiyi kenan?" Mommy ta hade fuska "na kula ga gaskiya nan kana gani kuru-kuru amma kana takewa, son Kai ne ko me? Aure dai Nafeesah da Ibrahim babu shi!! Ba zan taba bada hadin kaina ga cin amanar wannan da kuke shirin yi ba" Daddy yace "ke kuma kin ki fahimtar abinda soyayya zata yi da wannan ba zata iya ba, baki tsaya kinji ta bakin yarinya ba kin zauna kina ta tada jijiyoyin wuya, be it zaman aure ko cin amana kamar yadda kika ce don ni dai ban ga komi ba a ciki, ina ga ai ya rage ga yarinyar koh?" Mommy tace "ni nasan Ummiey ba zata taba aminta da hakan ba, ga samari nan bila adadin suna karakaina a kanta sai ta buge da wani can, ga mata ga 'ya'ya, abokinka kuma for that matter, anya Abban Ummiey ka duba maganar nan sosai?" Daddy ya kalleni yace "Uwata!" na daga kai na kalleshi, yace "kada ki damu da abinda take fada kin ji? Just tell me idan kina son Ibrahim kuma zaki iya auren shi" na kalli Daddy na kalli Mommy, toh fa! Ga sanyin Idaniyata guda biyu a gabana, ko wanne ya zuba min ido yana jiran amsa ta wanda nasan cewa amsar da zan ba daya daidai take da bacin ran daya, abinda na tsani gani da ji kenan a duniyata ace daya daga cikin Iyayena yana cikin bacin rai sabida ni. Abinda Mommy take fada gaskiya ne, shima Daddy akan gaskiyar shi yake, to me zan yi kenan? M I going to disappoint one of them? Ya Allah!! M extremely confused! Na samu kaina da girgiza kai wanda ni a karan kaina ban san dalilin yin hakan ba, Daddy yace "me kike nufi da girgiza kai, eh ko aah??" na sake girgiza kaina, "ban sani ba Daddy!" Daddy ya kura min ido na tsawon lokaci, yace "tashi ki tafi kawai Uwata, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" ba musu kuma ba tare dana kara uffan ba na musu sai da safe na wuce dakina. Hannu dafe da kai na fada kan gadona na kwanta, na gaji! Na gaji haka nan. Haba! Kwana biyun nan kaina har ciwo yake yi tsabar tunanika da suka hana ni sukuni, abin ya ishe ni haka nan. Tashi nayi na fada toilet na dauro alwala na fito na haye kan Abin sallah, sallah na fara jerowa, dana gama na roki Allah akan yayi mun zabin abu da yafi alkhairi a cikin rayuwata, na gama nayi shirin kwanciya barci na kwanta zuciyata cike da sake-sake.


*****
Tsawon sati guda Daddy bai sake min zancen Abbu ba Mommy ma haka, haka a tsayin lokacin nan ban sake ji daga Abbu ba. Mun koma makaranta don dama ba wani hutu aka bamu mai tsayi ba. Ranar Asabar ina kwance a dakina da hantsi, mun gama waya da Harith kenan yana gaya min yadda suke shan fada shi da Ikram akan wai ni budurwar shi ce ni kuma ina ta shan dariya, na ajiye wayar tare da kurawa ceiling ido ina kallo. Wani kiran wayar ne ya dawo dani cikin hankalina, na mika hannu a sanyaye na dauki wayar. Ban san lokacin dana zabura na tashi zaune dangargar ba, Abbu. Kallon wayar kawai na dinga yi har kiran ya kusa karewa, in daga in ce mishi me? Koda yake na riga na gama yanke shawarar abinda nake ganin daidai ne a rayuwata so let's just finish this once and for all kawai, na karfafawa kaina gwiwa. Nayi gyaran murya tare da daga kiran na kara wayar a kunnena......





(Sorry for the short Chapter, m kinda busy this days wallah..)
So Kafin in tafi let me ask you this:
~Me kuke tunani game da Littafin Ni Da Abokin Baba Na so far?
~Me kuke gani ya kamata Nafeesah tayi a wannan lokacin, Accept or Reject?
~Who's siding with Mom, Dad? Raise your 👐 so I can count you guys lol
~Stay blessed and cool, see yah
Lots of Hearts and Flowers #teamAbbu 💞💞💐💐




*♡Jeedderh♡*

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*35*



"Assalamu Alaikum" sansanyar muryar shi ta doki kunnena, duk wani karfin gwiwa dana tanada da kaudin da nake na cewa Abbu ya daina firgita ni ashe aikin banza nake yi, a take muryar shi tayi raga-raga da naman jikina, yayi gyaran murya tare da ambatar sunana, na amsa a nutse kuma a hankali cikin muryar rada, shiru ya biyo bayan hakan na lokaci mai tsayi, baka jin komi sai karan iska dake wucewa ta cikin wayar. Yace "Nafeesah! Ya muka kare da maganar mu ne?" nayi shiru ina zare idanu, da me na shirya zan ce ne? Gabadaya komi ya fita daga cikin kwakwalwata, yace "umh?! Ina sauraron ki" na bude baki zan yi magana sai dai sautin dake fita kawai shine "ermm.... ermmm" na kasa yin takamaimiyar magana. Abbu ya tausasa murya, "look Nafeesah. I don't have much time yanzu, mintuna kadan suka rage min in tashi zuwa Vancouver zan yi wani four months course acan so please do tell me, me kike tunani? Ina son ayi ayi auren mu dana dawo Nafeesah, da so samu ne a gare ni da tafiyar nan dake zan yi ta a matsayin mata ta Nafeesah don ba wani tsayawa zan yi bata lokaci wajen soyayya kamar yaro ba, kin san na tsufa da hakan koh?" wata hudu a Vancouver? A perfect timing!! Yace ina jin ki Nafeesah, an fara kiran fasinjoji, me kike tunani? Zaki iya aure na??" na lumshe ido a hankali zuciyata na suya a kirjina kamar an tsoma ta a ruwan zafi, "I Am Sorry Abbu...... I can't!" shiru ba magana daga bangaren shi yayin da kowace wucewar dakika zuciyata take nunka gudunta har na fara tunanin idan na kara minti daya a wannan lokacin zata iya bugawa gabadaya. Bayan kaman wucewar lokutan dana kasa lissafawa, yayi gyaran murya, muryar shi lullube da wani irin embarrassment da daci yace "zan kira ki idan muka sauka Nafeesah" a hankali hannuna da wayar suka sauka akan gadona kamar wadda aka zare mata numfashi. Nayi imanin da ace Duniya da lokaci suna tsayawa da sai ince nawa sun tsaya, komi nawa ya tsaya cak. Bana fahimtar komi sai daci da sanyin jiki dana ji suna fita daga bakin Abbu, ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ina bukatar sanyin rai dana zuciya. Ina bukatar farin cikin iyayena, nasan cewa definitely Mommy zata yi farin ciki da hakan Daddy ne dai ban sani ba, ni kuma I only need those four months, In shaa Allah kafin lokacin ya cika, "I'll over come it!" na fada a fili cikin karfafawa kaina gwiwa. Karan bude kofa yasa nayi firgigit na kalli kofar, Mommy ta shigo tana kare min kallo, tace "kin yi bakuwa Ummiey" na kalleta da sauri, "bakuwa, wacece?" ta dan maida kanta wajen kofa tare da furta "shigo" Ikram ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, da sauri na tashi tsaye ina amsawa, iso na mata zuwa gefen gadona ta zauna, Mommy ta juya ta fita ta barmu muna gaisawa, ruwa da lemu na dauko mata a fridge na dawo, muka zauna shiru a dakin saboda ba wani sabo muka yi da ita ba dama, can na katse awkward

Please Login or Register in order to submit comment