Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sadiya nan da Gwoggo Hinde sun isa in zo ta maida ni makaranta kawai, nace mata ni fa anan nayi niyar kwana. Tayi shiru tana kallona ganin na kafe kafin tace "kin fadawa iyayen ki?" nace "zan fada musu anjima dai" tace ai shikenan, Gwoggo Hinde zo mu wuce gida dake kawai. Da haka suka mana sai da safe suka tafi bayan sun ajiye mana duk abinda zamu bukata. Na shiga bandaki na gyara jikina, ban taho da panties bama sai dana fita waje na sayo wasu pad ce ma ban nema ba da yake ni ma'abociyar ajiyar su ce a cikin jakata saboda emergency. Na fito daga bandakin ina gyara zaman rigar jikina, daidai lokacin Abbu yayi sallama ya shigo cikin husky voice din nan nashi Hafsy na biye dashi a baya, zuciyata tayi wani irin fari da ganin shi kamar zata haske duniya da abinda ke cikinta, gabadaya ranar ban ji muryar shi ba mun dai yi exchange din messages a tsakaninmu da rana, fuskar shi ta nuna zallan mamaki da ganina kafin baiyanannen farin ciki daya kasa boyuwa ya nuna akan fuskar tashi, na ja kujerar kusa da gadon Ni'imah din na zauna. Na Kalli Hafsy dake tsaye a bakin gadon Ni'imah na mika mata hannu alamun tazo ina murmushi, ta makale kafada tare da kara lafewa a jikin Abbu alamun ba zata zo ba, na janyo ta jikina tana kokarin kwacewa amma na hana ta, nace "haba Hafsy na ni dake bata baci, Waye ya tabo min ke?" ta turo baki tana nuna ni da yatsan ta, nace "ni da kaina? Me na miki?" tace bake bace ba kike kin zuwa ki gaida ni, kullum sai nace kizo ki ganni amma baki taba zuwa ba! Na dan saci kallon Abbu dake gaisawa da kannen shi amma idanuwan shi suna kanmu yana mana dan murmushi, na janye tare da kallonta nace "kiyi hakuri kinji? In shaa Allahu zan dinga zuwa Ina ganinki, so stop frowning and smile kinji?" tace "promise?" na gyada mata kai. Aka kwala kiran sallahr Isha'i a daidai lokacin, Abbu ya zube min wayoyin hannunshi a gabana ya fita da niyar yin sallah.....
~Nasan zaku ce chapter din yau ma yayi kadan, amma ya zanyi? Wallah bani da lokacin yin typing da yawa Ne shi yasa
~Lots of love and Hearts Ni Da Abokin Baba Na Fans
#TeamAbbu
#OneLove❤❤
#AnaTare🤝🤝🤝





*♡Jeedderh♡*
[12:19PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*



*44*




Kwanci tashi asarar mai rai, biki yana ta kara matsowa yayin da muke ta shirye-shiryen rounding off din semester dinmu. Tuni Ni'imah ta warware har ta fara shigowa school abinta, cikin Sadiya yana ta kara fitowa ni kuwa gandoki har na fara tanadar kayan jarirai, lol.

☆☆☆☆☆

Cikin mamaki na daga wayata dake ringing bayan na duba sunan wanda yayi kiran, “Yau ko dai batan lamba waya kayi Harith?" tunda ya samu aiki a Ibadan ya tarkata ya tafi zumuncin dake tsakaninmu yayi kasa, shi aiki ni kuma karatu don haka we were not in contact recently, yace “haba Nafeesah, har ke kina da bakin magana? Sau tari zan tura miki sako ta whatsapp amma bana ganin reply dinki, anya idan da amana ruwa ya dafa kifi??" nayi dariya nace “kasan rayuwar dalibai sai a slow wallahi, shi yasa. Ka yini lafiya?" yace “yeah, Alhamdulillahi..." nan muka gaisa dashi da tambayar juna kwana biyu, yace “Sis take fada min ranar nan wai ai an saka miki ranar aure, shine nace bari in kira in tambaya inji laifin me nayi da ban samu labari ba?" nayi murmushi nace “to kuma kawai daga sa min aure sai in hau shela? Kaima ai naji ance ka kai kudin aure gidan su Ikram" yace “yeah... Amma ya aka yi kika sani? Ko abokaina basu san da labarin ba" nace “nima a gari naji, amma daga majiya mai tushe, Ikram din ce da kanta take fada min" yace “iye lallai naga nuna wariyar jinsi, so u guys have been in contact with each other amma shine kike fada min wai wani rayuwar dan makaranta and stuffs ko?" nayi dariya nace “ai kasan zumuncin mata ko ta yaya dai in a week ba su rasa yin waya shi yasa... So what's up?" yace “mun shigo workshop ne cikin Kano, shine nace bari in tambaye ki idan ziyara is allowed, zan leko mu gaisa" nace “why not? You are welcome!" yace “to ba laifi, goben idan zan shigo I'll inform you" daga nan muka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Firdausi ta dago kanta daga typing din da take yi a cikin laptop dinta ta kalleni, tace “ni yanzu meye makomar ki idan an miki aure? Zaki ci gaba da zama cikin hostel ne ko kuma zaki zauna tare da kishiyar ki ne tunda har yanxu ba a gama gyara inda zaki zauna ba?" na zauna a gefen gadona ina sighing, “ban sani ba nima wallahi, but kila, may be in ci gaba da zaman hostel" tace anya? I doubt idan mijin nan naki zai yarda, na harareta “me kuke nufi wai? Abinda Sadiya da Ramlah suka ce kenan dama" tayi dariya, “to ai yadda yake nunawa ne, he's barely holding it in, a dokance yake kuma a kagauce da auren nan, azo kuma ace an daura amma ya barki ki zauna a hostel? Ni dai a ganina da kyar ya bari" na dauki dan karamin filo na jefeta dashi, “ke fa m dinki karama ce wallahi, sam baki da kunya" ta fashe da dariya ni kuma na maida bayana kan gado na kwantar ina kara juya maganganunta a cikin raina, gaskiya a son samuna koda ace gyaran gidan da za a ajiye ni bai kammala ba to Abbu ya barni in ci gaba da zama a cikin hostel abina har sai an gama don ni fa har ga Allah ban shirya fuskantar Anty Mubeenah a matsayin kishiya ba balle har ta kaini ga zama a gida daya da ita a matsayin kishiyoyin juna, woah! Ko ya zaman zai kasance?? Na gyara juyawa a kan gadon tare da janyo face mask na rufe idanuna, a hankali barci ya dauke ni.

Washegari lecture din Abbu gare mu, da wuri na tashi na shirya cikin jallabiya brown mai kwalliyar light ash a jikinta, ban yi wata kwalliya ta sosai ba na yi rolling gyale ash mai dan fadi, na zura takalmin vincci flat na fita da dan saurina, takwas saura ina cikin hall din, nayi ajiyar numfashi lokacin da nake zama a kan seat, Abbu baya tolerating late coming ko da wasa, minti biyar ya kara akan karfe takwas to ka hakura da lecture dinshi na ranar kawai, na tuna lokacin dana taba yin nauyin barci ban tashi da wuri ba, na isa wajen six minutes past eight na tarar da kofa a rufe, kuma fa Abbun yana kallona a tsaye a kofar class din amma yayi biris dani tare da sauran dalibai abokan latti na, haka muka gaji da jira muka kama gaban mu.... Na ciza bakina cike da takaici, har yau idan na tuno abinda ya faru sai naji kamar inyi me, kuma fa sabida shi nayi makarar, shi ya kira ni a daren ranar ya tsare ni da hira har dare ya tsala., ai kuwa dai da kyar ya samu ya shawo kaina. Na saki dan murmushi a hankali dana tuno irin bidirin da muka sha a lokacin. Ajin yayi tsit lokacin da Abbu ya turo kanshi cikin ajin, yayi shigar wani danyen vowel ruwan hanta, bai saka hula ba sai dai ya taje sumar kanshi da yake shi ba ma'abocin saka hula bane. As always, yayi kyau kamar ka lashe shi. Ya fara searching din hall din da idanun shi a hankali har ya lalubo ni, ya sakar min murmushi very soft and lovely, ban bata lokaci ba wajen mayar mishi da martani, yayi gyaran murya amma fa jefi-jefi idanunshi kan kalloni kamar yadda koda wasa nawa basu bar shi ba.

Muna gama lectures muka fita, tun saura minti sha biyar mu gama dama Harith ya min text kan cewa ya shigo cikin makatantar ina zai sameni, na tura mishi text din inda muke yace xai zo, don haka muna fita na hange shi inda ake ajiye motoci. Murmushi nayi na karasa wajenshi, ya wani kara fari ya kara zama magidanci kamar ba Harith din dana sani ba watanni hudu da suka wuce, shima mamakin da yake yi kenan yace wai na kara yin kyau nayi fresh, nan muka tsaya muna gaisawa sosai mun fara hira sama-sama ya kalli agogon hannunshi yace “I gotta go, Abuja zan wuce daga nan" nace “za aje a ga Amarya kenan? A gaishe ta" kamar ance in waiga bayana, ina juyawa na hango Abbu yana nufo mu, na zaro ido tare da juyawa ina kallon Harith dake kallona shima, fuskar nan ta Abbu a hade take murtuk, lallai yau kishin maza ya motsa. Sam banyi zaton har lokacin yana cikin department dinmu ba saboda ban ga motar shi ba, ai da banyi gangancin tsayawa da Harith a wajen ba. Harith yace “da alamun wanda zaki aura ne ke tunkaro ku" nace “ya aka yi ka gane? Ka san shi ne dama?" yace “not at all, but hararar da yake jefo min kamar zai kawo min naushi irin wadda nake wa duk namijin dana gani tsaye da Ikram" nayi er dariya, “he's cute, isn't he?" daga bayana naji anyi magana, “well, look who's calling who cute" he sounds so close alamun yana bayana kenan, na ja gefe da dan saurina ina dariya cike da jin kunya, Abbu ya mikawa Hatith hannu fuskar shi babu yabo babu fallasa babu fara'ar nan dake tattare a fuskar shi, “Ibrahim Galadanchi" abinda yace mishi kenan coldly, ina ganin yadda yake glaring din Harith da hot gaze dinshi wanda zai iya grilling din kifi, da sauri Harith ya mika mishi nashi hannun suka yi musabiha yace “Harith, fiancé din Ikram cousin din Sulaiman mijin Sadiya" sai lokacin fuskar Abbu ta dan warware kadan daga hadeta din da yayi amma bata koma normal ba har lokacin, suka dan gaggaisa a tsaitsaye ya dawo da kallonshi gareni da tun da naja gefe ban yi magana ba, kallon daya jefe ni dashi sai da yasa naji alamun kadawar ‘ya‘yan hanjina, yace “ki same ni a mota" da kyar na samu na iya daga mishi kai, ya wa Harith sallama ya nufi wata bakar Land Rover dake kusa da inda Harith yayi parking din tashi motar, haba ba mamaki ashe ya canza mota ne? Na kalli Harith daya jefe ni da murmushin mugunta, na harare shi ya wani yi shrugging yana daga gira sai kawai na girgiza kai don bani da lokacin biyewa tsokanar Harith, godiya na mishi muka yi sallama na wuce inda Abbu yake jirana na bude motar na shiga. Ina shiga yaja motar muka fara tafiya ba tare da yace uffan ba, na kalli fuskar shi har lokacin babu fara'ah a tattare dashi, da alamun na bata mishi rai sosai. Jikina yayi sanyi, na maida kallona ga tagar motar ina jin kamar in fita ta ciki, da alamun yau Abbu na baya cikin walwala, duk saboda ni!!

#TeamAbbu
#One Love
#AnaTare





*♡Jeedderh♡*
[12:19PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*_Wannan shafi dungurungum na marubuciya RUFAIDA UMAR IBRAHIM ne. I was touched and impressed lokacin dana ji cewa cikin masoya kuma makaranta littafin Ni Da Abokin Baba Na kina ciki. Sauran Marubuta dake bibiyar littafin ina gaishe ku, wadanda suke kan posting nasu littafan ina musu fatan alkhairi. Masoyan Ni Da Abokin Baba Na ina gaishe ku a duk inda kuke. #OneLove_* ❤❤❤



*43*



Suka kalli juna kafin suka kalleni, Sadiya ta dage gira daya "me kenan?" "me fa??" na tambayeta ina wani fuskewa ni ala dole ban fahimceta ba. Tace “ki wani daina fuskewa malama, mun san abinda ke faruwa tsakanin ku biyun nan" na kada mata idanu innocently, “ni da wa??" ta kai min duka a kafada, “zaki sani ne maras M, ace kamar mu kuna cikin relationship da Yayan mu mu kasa sani?" na kallesu su duka biyun ina so in karanta yadda suka amshi zancen, ban karanci komi ba sai dai murmushin dana gani kwance akan fuskar su na farin ciki ne bana embarrassment kona takaici bane, naji sanyi ya lullube min zuciya, at least abotar mu dasu tana nan. Ni'imah tana murmushi tace “Sady ke kike wani tsayawa ma kina neman karin bayani, ni fa dama tun ba yau ba na harbo jirgin su ita dashi, they were making it obvious shi yasa ni ban tsaya jira a fada min ba nayi jumping into conclusion" na dan harareta cikin wasa nace “ni kar ki mun sharri wallahi" tace “ba wani sharri sai gaskiya. Irin kallon da kuke wa juna dama tun ba yau ba be it kuna cikin mutane ko ku kadai ne wallahi na soyayya ne, ai Anty Rahina tace an kusa yin auren" na dafe kirji ina zaro idanu, nace “su Anty har sun sani??" dariya suka saki suna kallona kamar wata kuntacciya dinnan, “Allah kina kwafsi matar Babban Yaya, tunda har muka sani ai dole su Anty su sani kuwa" na rufe fuskana ina diddira kafafuwa a kasa, “Ya Allah! Da wani idanu zan kallesu ni kam?" suka sake kwashewa da dariya har da tafawa, na hade fuska ina kallonsu, “this is not funny fa!" na fada in a serious tone don su san ba wasa nake yi ba, amma ko a jikinsu sai ma wata dariyar da suka kara sawa. Ganin zasu sa min ciwon kai naja Hafsy data fara gyangyadi a zaune muka koma kan spare gadon dake dakin na zauna ita kuma ta kwanta kanta a kan cinyoyina. Hira nake janta dashi duk don in janye hankalina daga shakiyancin dasu Sady suke min, cikin dan lokaci barci ya dauketa. Na maida hankalina wajen buga game bana ko kallon inda suke, har suka gama shiriritar su da tsara yadda bikin zai kasance suka yi shiru, dinner ma sai da aka tsara kala biyu, luncheon da parties kuwa wai har da Tea Party, fruits party, Arabian nights dasu Fulani day da tarkace, ina jinsu dai ban saka musu baki ba sai dariya da nake musu kasa-kasa, da alamu wani noti a kansu ya kunce kila saboda murnar auren Yayan su ne ko wani abu? Muna nan su Abbu suka dawo daga masallaci shi da Bashir, sallama ya musu ya matso inda muke ya dauki Hafsy a kafadanshi ni kuma na kara gyara zaman gyalena na kwashi wayoyin shi nabi bayan shi. Ya bude seat din baya ya kwantar da Hafsy, ya maida seat din ya rufe tare da jingina da motar yana kallona, na sadda kaina kasa ina dan tapping kafafuna a kasan, akwai wadataccen haske sosai a wajen shi yasa naji na kasa sakewa in kalleshi, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu na kasa sakewa in kalleshi sosai koda yake ko a da can dinma idan muka yi kallon ido da ido sai dai by mistake, balle yanzu. Yace “gobe in Allah ya kaimu zan samu Alhaji Babba yayan Alhajinmu da maganar zuwa a tambayo min auren ki, zasu kai kudin na gani ina so za kuma a saka ranar auren gabadaya” nayi shiru kaina a kasa, me zan ce mishi? Shi Abbu bai san irin matsananciyar kunyar shi da nake ji bane da zai dinga zama yana tattauna maganar aurena dani ba. Ya kara jingina da jikin motar yayi alamun tagumi, “ni ai shikenan tawa ta same ni kuma. Son maso wani nake yi ko kuma ba a shirya aurena har yanzu bane?" na saci kallonshi, ba karamar dauriya nayi wajen danne dariyar data taso min ba, ya wani yamutse fuska kamar yaron dake shirin fashewa da kuka, nace “me nayi ni kuma?" yace “baki son maganar auren mu mana. Da nayi sai ki wani hade fuska kamar wadda ake tursasawa, ji yanzu ma na gaya miki magana maimakon ko ameen ki ce shine kike wani sadda kai kasa" na girgiza kaina ina dan murmushi, Abbu da rigima yake wani lokacin kamar karamin yaro haka yake. Kwanan nan haka yake, gaba daya ya zama very open to me, baya shakkar fada min duk maganar data fito bakinshi, wata rana ta saka ni jin kunyar shi duk da cewa abin yana burge ni kuma na kula hakan yana kara ja na zuwa gare shi. Nace “to ameen Abbu" yayi murmushi, “datz you my Amour.... Amma tsaya...." na kalleshi, yayi frowning face “yaushe ne kika ce kin daina kiran sunana da wani Abbu? Na gaya miki Abbu na yara na ne ba naki ba" nace “ai nace zan daina fa! amma ba yanzu ba" ya wani langwabar da kai, “har sai yaushe?" nayi shiru, ya sake cewa “ko sai mun yi aure?" na gyada mishi kai, yace “ba laifi, ni ai bawan Allah ne I can wait" nayi dan murmushi, “datz you kaima.... Wai don Allah meye ma'anar Amour?" yace “Love in french" na sadda kaina kasa ina blushing, da gaske ni Love dinshi ce? Nace “amma sauran messages da kake tura min shima French ne? Me suke nufi?" ya girgiza kai, “naaa! Ba zan gaya miki yanxu ba, zan dai koya miki French din sai ki karanta da kanki. Idan muka yi aure ma a Kasar Faransa zamu yi honeymoon dinmu ai, kila kafin mu dawo sai kin koyi yaren sosai, sai mu dinga canza yare a gaban mutane abinmu koh?" na kai hannu ina rufe fuskata ina dariya, can kasan zuciyana kuwa fata nake ina ma zan bude ido in ga har watannin da suka rage in zama mallakin Abbu sun zagayo? Ya kara jingina da jikin motar yana murmushi “ke da kunyar nan taki kuna birge ni, sai dai it's way too much gaskiya, kiyi kokari ki rage ta ko kuma ni da kaina inyi wannan aikin...!" na kara dukunkune fuskana wannan karon a cikin gyale ma. Yayi dariya son ranshi kafin yace “ina tunanin raba muku gida ke da Mubeenah, me kike tunani?" nace “idan hakan yayi maka bani da damuwa da hakan nima" amma a can kasan raina ba karamin dadin hakan naji ba, har ga Allah dama can bani son zama gida daya da Anty Mubeenah har yanzu ina jin kaina guilty wani lokacin, har yanzu kuma ban san da wane ido zan kalleta ba balle har inyi tunanin zama a gida daya da ita, duk lokacin da nayi tunanin na kan ji hankalina bai kwanta da hakan ba. Yace “hakan ya min perfectly, zan samu inci amarcina cikin dadin rai da kwanciyar hankali abina. Amma na dan lokaci ne fa, don tuni an fara mana sabon gini" nace “sabon gini kuma?" yace “yeah, inda zamu koma da zama mu dukan mu har yaran da zamu haifa nan gaba. Da wancan gidan na gina shine a matsayin inda zan rayu da matar aurena ne, ban taba kawowa raina kara yin aure ba sai da kika shigo cikin rayuwata sannan na fara samun second thoughts. A yadda nake so kuma ki cika min gida da yara inda muke zaune yanzu ya mana kadan. Ina so iyalina su tashi da hadin kai ba tare da banbancin komi ba Nafeesah, ina fatan zaki bani goyon baya wajen ganin hakan ya tabbata?" muryar shi ta tabbatar min da cewa da gaske yake, tausayin shi ya kama ni Allah sarki Abbu na! Da haka yaso ya karasa rayuwar shi cikin takaici da rashin kulawar matar aure? Ta wani fannin sai na tsinci kaina da godewa Allah daya kawo ni cikin rayuwar su, ko babu komi nasan zan kawo haske cikin rayuwar Abbu kamar yadda name tabbata cewa shima zai kawo haske a tawa rayuwar. Nasan cewa shawarar daya yanke is not a bad idea, ni kaina nasan ba zan juri ganin rabuwar kan yayanmu ba kuma da yardar Allah ba zan bada gudunmawa wajen ganin rabuwar kansu ba kamar yadda wasu iyalan suke, na gyada kaina nace “In shaa Allah Abbu, zan yi iyaka bakin kokarina" yace “Nagode sosai Nafeesah. Allah ya bani ikon faranta miki rai kamar yadda kike iyaka bakin kokarinki wajen ganin cewa kin faranta nawa ran" na sadda kaina kasa ina murmushi, daya daga cikin halayen Abbu dake matukar burge ni kenan, saukin kai da saurin fahimta. A kasan raina kuma na amsa Addu’ar da yayi da “Ameen”.


Bamu ankara da lokaci ya ja ba sai da muka ga Basheer ya fito zai tafi sannan Abbu ya duba agogo yaga karfe goma ta wuce, Abbu ya kama baki cike da tu'ajjibi yace “haka lokaci yake gudu dama?" na sadda kaina kasa ina magana a hankali yadda ba zai ji ba “kaine dai baka kula da lokaci yana tafiya ba saboda love ya rufe maka ido" ya mikawa Basheer hannu suka yi musabiha na mishi sai da safe nima ya karasa wajen abin hawan shi ya tafi, Abbu ya bude motar ya shiga ya zauna, ya kalleni yana kokarin yiwa motar key, “naji abinda kika fada sarai, zaki zo hannu ne ai zaki yi bayani by then" na ja da baya ina er dariya, na maida mishi murfin motar na rufe, yace “any thing for me?" na girgiza mishi kai, “babu, sai da safe Abbu na!" na juya da sauri na fara tafiya ba tare dana jira abinda zai ce ba, ina jin shi yana en maganganu har na mishi nisa kafin naji alamun yaja motar, na saki dariya a hankali. Ina shiga daki suka min caaa da magana, ni dai er dariya kawai na dinga yi da kyar na samu na kashe musu baki, Sadiya ta miko min leda mai dauke da gasasshen kaji da yoghurt, na zauna ina ci muna hira dasu har wajen karfe goma sha biyu Ni'imah tayi barci, sannan ne muma muka kwanta don dama duk saboda ita ne muke yin hirar don kar muyi barci mu barta ita kadai kadaici ya dameta, muka gyara daya gadon muka kwanta mu ma. Washegari wajen karfe goma Basheer ya kawo mana abin kari da kayan da Ni'ima zata canza, bayan su Anty Rahina sun zo mun gaida su nabi Sadiya gidanta muka je muka yi wanka muka canza kaya, sai kayan Sadiya na saka saboda ban tafi da wanda zan canza ba. Muna komawa muka tarar an sallame su, nan muka hada kaya muka wuce gidan Ni'imah. Muka gyara mata gida da komi muka mata girki, su Anty Ameenah ana kiran sallahr la'asar suka wuce, ni dai daga nan na musu sallama don a ranar zan koma makaranta. Sai bayan tafiyar su ne sannan na kira Mommy na fada mata abinda ya faru, sai da nasha fadan wai ban gaya mata da wuri ba sannan tace in hada ta a waya ita da Ni'imah, no dai na bata hakuri kafin in ba Ni'imah wayar Mommy ta mata jaje tare da kara mata da nasihu daga nan ta maido min wayar, na amsa, anan take fada min cewa wakilan Abbu zasu je gida Malumfashi tambayar aurena, nayi shiru ina gyada kai kawai, ta mim addu'ar Allah ya sanya alkhairi muka yi sallama da ita. Nima ba a jima ba na musu sallama na koma makaranta. Bayan kwana biyu aka

Please Login or Register in order to submit comment