Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

silence din nace "so???" ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana, na dan yi murmushi nace "Kina son tambayar Abinda ke tsakani na da Harith koh?" ta kalleni cikin mamaki kafin ta gyada kai, nace "magana ta gaskiya Ikram babu abinda yake tsakani na dashi, duk abinda kika ga mun yi was just a plan, yana so ne yayi provoking dinki" ta nuna kanta da yatsa, "ni kuma? Why??" na zayyane mata labarin duk abinda kenan, Ikram tayi shiru kanta a kasa har na gama. Tace "yaki ya fahimce ni ne kawai, shekaru biyu kadai suka rage min a karatuna, menene a ciki idan ya hakura zuwa shekarun biyu?" nace "Ikram kina son Harith shima yana son ki saboda haka ni ban ga abin tada jijiyar wuya a wannan maganar ba. Shawarar da zan baki shine to just go for it, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu idan har kika maida hankalinki akan hakan" tayi shiru kamar mai tunani kafin ta kamo hannuwana ta rike, "nagode sosai Nafeesah. In shaa Allahu zan zauna in duba hakan, nagode" na danyi rubbing hannunta dake kan nawa ina murmushi. Mun dan kara hira da ita kafin ta min sallama ta tashi, na raka ta har bakin titi ta samu abun hawa ta tafi ni kuma na koma gida. Da dare Daddy yake gaya min an sai min DE form a BUK, na turo baki nace "Daddy ni fa ABU nace maka ina so" yace "sun riga sun rufe saida basically ne shi yasa nasa aka nema miki BUK din" nayi shiru ina tunani, wannan shine kaka-kara-kaka din fa, ina gudun Abbu shi kuma yana kara bibiyata, nace "ni dai kawai na hakura sai next year" daga Mommy har Daddyn kallona suka yi, Mommy tace "sai mu saka ki a gaba muna kallo har shekara koh?" Daddy yace "Duk maganar zama bata ma taso ba, tunda an samu admission din ki daure ki tafi can din kawai" nace "amma a cikin hostel zan zauna koh?" Mommy tace "to in ba can ba ina? Dole can zaki zauna" Daddy ya daga baki kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru kawai. Daga haka aka fara processing din nemar min admission a BUK. A gefe daya kuma naci gaba da karatu na.

Sati daya, biyu, uku suka shude babu alamun kiran Abbu a cikin wayata, ban kuma sake jin magana game dashi ba. Tunanika iri-iri game da hakan babu kalar Wanda ban yi ba da wasi-wasi, kila ya hakura ne, kila maganar da nayi ta bata mishi rai, kila dama ba sona yake yi ba.





*♡Jeedderh♡*
[14:40, 12/18/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*36*



"So sai kawai kika yi rejecting din golden opportunity like that?" cewar Ramlah. Zaune muke a lecture hall dinmu bayan mun gama lectures. Kwana biyu bana cikin natsuwata, walwala ta min kaura kamar yadda fara'a tayi kaura daga fuskata., a duk lokacin dana samu na kebance babu abinda nake yi sai tunani, Ramlah ta kula da yanayin da nake ciki yau dai ta rike ni sai dana fada mata abinda ke faruwa, ko babu komi naji dadin fada mata din da nayi. Tunda abin ya faru babu wanda yaji maganar, ni kadai nake juya abun a cikin raina. Fadar irin mamakin da Ramlah tayi ma bata baki ne, data hangame baki sai dana cika mata shi da popcorn sannan ta rufe. Na kai popcorn bakina tare da gyada kai, "babu wani zabi daya rage wannan Ramlah, kema kin sani" ta kura min ido, "akwai so many and n much more choices Babe, ke ce dai baki so zaba ba". Muka yi shiru na dan lokaci, ta sake cewa "wai ba kince kina son shi ba?" na gyada mata kai, "then why did you do it? Bayan kin san zaki kasance cikin damuwa?" na kalleta sosai, "Ramlah, ina cikin rudani wallahi" ta girgiza kai, "no! Ki kike confusing din kanki dai, wannan abu ne mai sauki da cikin kiftawar ido zaki magance shi. Kina son mutum, then marry him mana, meye matsalar ki wai? You once fall for the wrong person yanzu kuma right person din yana sonki kina gudu da kafafun ki? Me kike so ne?" nace "so, kulawa, zaman lafiya Ramlah" tace "A cikin abinda kika lissafo wanne ne ba zaki same shi ba wajen Abbu?" nace "duka..... Ban sani ba ko Abbu yana so na ko baya sona ba. Ban sani ko dangin shi zasu karbe ni ko ba zasu karbe ni ba, ban sani ko iyayena zasu yi farin ciki da haka ko ba zasu yi ba...." ta katse ni, "wait don Allah. Shi Abbu da bakin shi yace baya son ki?" na girgiza mata kai, "ko Kadan. Yanayin acting dinshi towards me ne yake nuni da hakan. Ki duba ki gani tunda muka yi maganar nan dashi yau an wuce wata biyu amma koda wasa bai kira ni, bai taba nuna yana sona ba, bai taba furta cewa yana so na ba, a haka zan aure shi kuma? To ince nayi auren me?? Bayan haka alakar shi da matar shi is not in a good condition wanda hakan ya saka ni zargin cewa saboda ita yake so ya aure ni...." na zayyane mata duk irin yanayin zaman su dana sani da challenge dinsu akan karo aure, tayi shiru tana saurare na har na dasa aya. "shine nake jin tsoron na amince dashi kuma daga baya in zo ina dana sani" Ramlah hararata take yi kamar wata wadda na kashe mata da, tace "kin san Allah? Da ba don ke bace? Da sai na dalla miki mari. Wai me yasa ke kullum tunanin ki daban yake dana normal mutane?" nima na harareta, "kin fara ko? Meye laifina anan to?" ta dafe kai, "saboda kin kasa fahimta. Sai me idan Abbu baya son ki? At least yana so ya aure ki which means ko yaya ne yana admiring dinki., kuma ko ba jima zai fada tarkon son ki girl balle ma na riga dana san tuni ya fada" nace "me yasa kika ce haka?" tace "yadda ya dinga kallonki with so much tenderness and affection in his eyes ranar dinner din su Ni'imah, ke ko ba wannan ba kallon da mutumin nan yake miki da gaske na so ne" na girgiza kaina, "I doubt it Ramlah" wayana tayi karan shigowar sako, na ciro ta daga cikin jakata tare da bude sakon bakuwar number ce kuma har da karin alamun + wanda yake nuni da cewa sakon daga wajen Nigeria ne, cewa aka yi., 'Let's have a talk later please, I'll call you nine pm on dot in shaa Allah. -Galadanchi' hannu yana rawa nayi niyar maida mishi amsa Ramlah tayi saurin rike min hannu, na kalleta "meye?" tayi rolling idanu, "haba babe! Bashi kamar minti goma mana zuwa ashirin kafin kiyi reply?" nace "ban gane ba? He sent me a message, let me reply please" ta kwace wayar daga hannuna, "kin ce kin fada mishi baki son shi, then me kike so yayi tunani yanzu? Ya turo miki text, within a second kin maida reply as in you care dinnan, kinsan Allah mazan yanzu ba a musu haka koda kuwa wanda yake son ka ne balle ke da kike ikirarin kina son shi" na sadda kaina kasa, "Ramlah kin san halina sarai. Ban iya boye so ba kamar yadda bana iya boye ki, bazan iya yiwa Abbu haka ba" tace "at least try mana. Be like the classy girl you are, wannan yana da banbanci da son da kike yiwa normal mutane, ina gaya miki ta haka ne kadai zaki gane yana son ki ko baya son ki" na gyada mata kai a hankali. Ta dafa kafadata tana dan bubbugawa, "ban san irin son da kike mishi ba Nafeesah, amma zan baki shawarar ki dinga Addu'ah. In shi alkhairi ne a gare ki Allah ya baki shi, idan kuma ba alkhairin ki bane Allah ya canza miki da mafi Alkhairi" nace ina yi wallahi Ramlah, tace sai kici gaba dayi. Na gyada kai, "in shaa Allah, nagode sosai. Baki ji dadin da naji ba dana gaya miki wallahi" tace "kar ki damu, what are friends for after all? Naji ance BUK zasu fara registration da lectures dinsu next month, haka ne?" hirar mu ta koma ta makaranta, da yake ita university of Abuja zata koma, mun dan kara mintuna kamar ashirin muna hira kafin muka mike, na mata sallama na wuce gida ita kuma ta wuce hostel.

Ban maidawa Abbu reply dinshi ba, amma tun kafin karfe tara ta cika na samu waje na zauna ina jiran shigowar kiran Abbu. Kamar yadda yace, karfe tara tana cika kiran shi ya shigo wayata. Na daga wayar tare da mishi sallama ya amsa, a nutse na gaida shi nan ma ya amsa tare da tambayar karatuna, ya dan ja ni da hira kadan kafin ya dulmiya cikin maganar data saka shi kira na. "Nafeesah ranar nan muna waya na katse sai kuma ban sake kira ba, na kara miki lokaci ne wanda zaki yi tunani a nutse don a tunani na a wancan lokacin baki zauna kinyi tunani bane shi yasa. Ina fata in ji different amsa daga gare ki wannan karon". Nayi shiru ina tunani, wata marubuciyata tace wai 'Opportunity comes once (Dama tana zuwa ne sau daya -Takori)' ni kam yau dai ina so inyi wasa da tawa damar. Masu karatu kar kuga laifina. I am a girl in her twenties, a irin wannan age din babban abinda 'ya Mace take bukata daga kowane namiji shine kalmar so, sai dai ni yana proposing din aurena ne kawai ba tare da nasan ainihin abinda yake cikin ran shi ba. In amince da auren shi ince nayi auren me? I can't risk my happiness akan son zuciya irin nawa. Nayi gyaran murya a nutse nace "kayi hakuri Abbu, ina kan bakana har yanzu" ina dire aya ya tare ni, "why?" nayi shiru, yace "me yasa baki son Aurena ne?" nace "it's obvious, saboda kai baban Hafsy dasu Abdullahi ne, kai Mijin Aunty Mubeenah ne, you are Niimah's brother, Abby you Are My Father's Friend.... How are you expecting me to accept your offer?" yace "just because of that?" na gyada kai kamar yana gani na, "yace but is it a sin? Abubuwan nan da kika lissafo dukan su ba wasu obstacles bane da zasu hana ni auren ki Nafeesah! Just tell me ba kya so na shi yasa ba zaki iya aure na ba" nayi shiru zuciyana tana bugawa, ina zan Iya furta wadannan maganganu? Yace "tell me Nafeesah!" cikin husky voice nashi wanda ya fara gauraya da bacin rai, nan ma shiru kawai nayi, zan iya karya akan komi amma banda karyar kin Abbu, ba zan iya ba. "Goddammit Nafeesah! Me kike son nayi for goodness sake?!" wannan Karon bacin ranshi ya fito baro-baro, ya cigaba "kina bukatar ki ganni akan gwiwa na ina rokon ki akan ki aure ni? Ko kuma so kike yi in dinga binki sahu-sahu kamar yaro ina shelantawa duniya ina son in aure ki sannan zaki yarda?" na danyi chuckling a hankali, that is so childish. Yayi shiru kafin inji ya fara magana wannan karon a hankali kuma very calm, "ok, ok. Maganar su Hafsy da kike yi Nafeesah ina tabbatar miki they will be more than happy idan suka ji cewa zaki auri baban su saboda suna Son ki Nafeesah, sun dauke ki da muhimmanci sosai fiye da tunaninki, haka ma su Ni'imah, Dad dinki kuwa has already given us his Blessings. M just trying to be a nice guy anan kin gane? Bana so ne a miki abinda ba kya so ne kawai shi yasa, Mubeenah kuma wannan ba damuwar ki bace, ba lallai sai da blessings dinta ne zamu yi aure ba, Are we good now?" nace "still Abbu....." ya katse ni, "kina da wanda kike so ne?" nayi shiru ban amsa ba, jin shirun da nayi yasa ya sha jinin jikin shi, "akwai kenan koh?" nan ma nayi shiru, yayi kwafa "just wait till I come back. I will not let you go that easily Nafeesah, Aure a tsakanin mu kamar an daura ne Nafeesah coz you are mine! Saboda ni aka halicce ki ba dan wani ba. Zan baki sauran watanni biyu da suka rage min anan don ki tsara yadda Rayuwar ki a gidana zata kasance. Ina dawowa daurin auren mu ba xai dauki lokaci ba Nafeesah in shaa Allah.... Bari in barki haka, sai da safe" da kyar na iya daga baki nace "A tashi lafiya" kusan a lokaci daya muka katse wayar dashi. Na kai hannuwana duka biyun na tallabo kumatuna dasu, Abbu da gaske yake. Wani bangare na zuciyata yana murna da hakan yayin da wani sashen yake jimami da tantama, tantama akan in amince ko inyi akasin haka? Jimami kuma na ya makomar rayuwata zata kasance idan na amince din???


Daga wannan ranar kusan kullum sai mun yi waya da Abbu, yawancin lokuta zai kira ya tambaye ni karatuna da sauran su, bai sake tada min zancen auren ba, hakan shi yake kara jefa zuciyata cikin wasi-wasi. I mean yadda nake ji ana fada ko kuwa dai mostly yadda ake yi a cikin film, a situation irin haka zaku ga Namiji ya shiririce a gefen mace going to the moon and black, proposing ta hanyoyi daban-daban, amma shi Abbu babu alamun haka a tattare dashi. Idan text ya turo min babu kalmar so ko daya da nake tsinta a ciki haka ma idan muka yi waya dashi, amma kulawa kam ina shan ta, kullum cikin tambayar lafiyata da Al'amuran rayuwata yake. Hakan shi yake kara jefa ni cikin tunani., Abbu Wane irin mutum ne shi kam??
#TeamAbbu





*♡Jeedderh♡*
[14:42, 12/18/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*37*

High waist blue jeans, shabby coffee color T-shirt, black veil rolled, black and white kimono, jakar poshter rataye a kafada, one last look a jikin mirror na tabbatar dana fita yadda nake so. Yau ne ranar da zan zana exam dina na karshe a Kasu, probably rana ta karshe da zan taka kafana zuwa cikin makarantar idan ba da wani dalili ba dai. Na saka sneakers a kafada baki tare da daukar wayar hannuna na fita, karfe tara lokacin dana fita bakin titi, kafin in isa Kasu tara da rabi tayi already don haka exam hall dinmu kawai na wuce. Kyawawan awanni biyu suka wuce kafin mu fito, daga nan bankwana muka yi da abokanan nan mu muka wuce gida, Ramlah tun a ranar ta wuce Kano zata je ta fara shirin wucewa Abuja. Nima nasan lokacin da nake dashi a Kaduna ba mai yawa bane kafin in wuce Kano saboda BUK tuni sun fara lectures dinsu tun kimanin satika biyu da suka wuce. Na koma gida na samu tarba ta musamman a wajen Iyayena, wata kwaryar liyafa suka hada min inda en uwa suka taru wajen taya ni murnar kammala karatuna, I didn't expect it but I was happy and touched. Soyayyar da Iyayena suke min abu ne mai matukar wahala in iya fayyacewa masu karatu irinta. Kwana biyu ina gida bana fita ko nan da can ina aikin barci da relieving din stress din exams. Bayan na huta completely na fara shirye-shiryen wucewa BUK tare da iyayena. Ranar Lahadi da misalin karfe hudu na yamma, tafe muke a kan titin daya dauki hanyar fita Kaduna zuwa Kano a cikin motar Daddy Hillux, tare da Mommy, Anty Uwani da Sultan. Duk wasu abubuwa da zan bukata suna bayan motar da muke ciki, komi game da karatuna ya riga ya hattama a waje guda, abinda ya rage kawai shine shiga dakin daukar lacca a gobe litinin. Anty Uwani da Mommy bakinsu yaki rufewa wajen bani lecture Akan zamantakewar cikin makaranta, rayuwa ce da zan hadu da mutanen da ban sani ba kuma inyi rayuwa dasu, nasihohi da shawarwari dai. Mun shiga cikin BUK da misalin karfe biyar da rabi. Mommy da Anty Uwani suka taya ni shirya dakin da aka kaini, mun samu occupant daya a dakin luckily musulma ce kuma bahaushiya da alamun kuma zata yi kirki. Su Mommy suka taya ni gyara kayana da hattama su waje guda. Sai bayan sallar Magriba sannan suka juya, ni da Firdausi roommate dina muka musu rakiya har parking lot. A gabanmu Daddy yaja motar suka tafi muna daga musu kallo, ina kallon su har Motar ta bace mana daga gani. Iyayena suka tafi suka barni a bakon gari, bakon waje, again, for the second time. Na kai yatsa na dauke siririyar kwallar data tarar min a ido, wannan yana daya daga cikin challenges da 'ya mace take fuskanta a rayuwarta, wannan temporary ne ma fa, zan iya zuwa in gansu a duk lokacin dana ga dama kuma na bushi iska, to ina ga nayi aure kuma? Muka juya muka koma cikin hostel Firdausi na min dariyar kukan da nake. Sallah muka yi naci abinci na jira aka kira isha'i nayi kafin nayi shirin kwanciya barci na kwanta. Sai dana janyo wayata kafin naga alamun shigowar sako, ban san yaushe ya shiga ba amma ina tunanin lokacin da nake sallah ne. Zuciyata ta shiga bugu da tsallen murna lokacin dana ga sakon daga Abbu yake, yaushe rabon da inji muryar shi? Tunda muka fara exams ya daina kirana sai dai yana turo min text akai-akai. Yau ma kamar koda yaushe ko ince ko wane lokaci, ya nake? Ya su Daddy na? Ya kara da min lale maraba da zuwa makarantar BUK sai abu d'aya daya kara, cewa yayi; "Kar in saba da zaman hostel dinsu da wuri, saboda soon.... Very soon zan bar hostel din, saboda yana dawowa zai dauke ni daga hostel din" na turo baki kamar yana ganina, "wai ya daukeni kamar wata er tsana" sai kuma na kwashe da dariya ina birgima akan gadona, Abbu bai san cewa nima jiran dawowar tashi nake yi ba ne kome? He kept bragging about it, koda yaushe cikin zancen in jira dawowar shi yake making me go curious akan me zai faru idan ya dawo din. Ina lissafe da kwanan wata, ya daura akan wata hudu din da yace zai yi. Mommy ta kira ni muka gaisa tare da tambayata yanayin wajen nace mata lafiya, bamu yi wani hira ba saboda yadda nake jera hamma tace inje in kwanta kawai, nan muka yi sallama tare da kashe wayar. Addu'ar kwanciya barci nayi tare da lumshe idona, a tunani na barci zai kwashe ni a take saboda yadda nake a gajiye amma ina! Rayuwata a gidan Abbu, iyalinshi dashi kanshi, tun daga ranar dana fara ganin su har zuwa yau ta fara min yawo a idanu, nayi juyi akan gadona a karo na barkatai ina tambayar kaina tambayoyin dana kasa samun amsar su suma a karo na barkatai, will it be okay? Zan iya kuwa?

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*



*Wannan shafi na Sadaukar dashi ga Marubuciya SADNAF da MAKAWA, I really appreciate you guys with your cheerful and concern, thanks. Sauran Marubuta ina gaishe ku sosai tare da duk wani Makamancin littafin Ni Da Abokin Babana!*

*39*



Muna fitowa daga lectures masallaci na shiga nayi sallar La'asar daga nan na wuce flower Garden. Anty Ameenah tana zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada, tana hangoni ta fara waving dina tana murmushi, nima murmushin nayi na karasa gareta, kujera naja na zauna ina fuskantar ta, na gaisheta ta amsa tana tambayata abinda nake so a kawo min nace a bani egg roll da lemu don tun safe da zan fita dana sha shayi ban kara komi a cikin cikina ba, aka kawo mana egg roll, meat pie burger da lemun peach. Anty ta kalleni tace "Allah yasa ban takura miki ba da nace ina son ganin ki?" nayi saurin girgiza mata kai, "haba ko kadan wallahi" tayi murmushi tare da gyara zamanta akan kujera, "da farko ban yi niyar sa baki ba akan maganar wannan sai dai ina ga lokaci yayi daya kamata in saka baki, ba shisshigi nake miki ba amma ina so inji inda maganar ku ta kwana?" na dubeta cikin mamaki, "Anty wace magana kenan?" tace "maganar ku da Ibrahim mana!" sai dana kusa zubdo da abinda nasa a bakina saboda maganar da naji cikin bazata. Ta miko min tissue na goge bakina tare da korawa da ruwa, Anty Ameenah tace "m sorry idan baki so hakan ba" kai kawai na girgiza mata, amma a kasan raina ina mitar me yasa don kawai Abbu yana son aurena sai kowa a cikin dangin sa ya sani? Kamar wadda take karanta mind dina, tace "kada fa kiyi zaton Ibrahim ne ya gaya min ko ya turo ni, bashi bane. Kwanakin baya dai ya taba neman shawarata akan cewa yana so ya aure ki, me nake gani? Naji dadin hakan sosai, wallahi abu ne wanda ya jima yana min amsa kuwwa a cikin kaina, tun ranar farko dana fara ganin ki Nafeesah na yiwa Ibrahim sha'awar kasancewar ki matar shi, sai dai sanin halin Ibrahim yasa na kame bakina nayi shiru. Ba tun yau ba nake mishi maganar kara aure amma sai ya wawantar da maganar, ba ni Kadai ba Hajiyar mu ma tayi nata kokarin ganin irin zaman da yake yi da matar shi but to no avail. Amma jin da kanshi yazo yana ce min yana sha'awar kara aure nasan cewa da gaske yake, Ibrahim baya nuna bukata akan abinda yasan baya so, musamman akan zancen nan Nafeesah, I've seen something different in him. To kuma tun daga lokacin har yanzu ban sake jin yayi magana game da hakan ba, last time dana mishi maganar ma sai ya sake wawantar da ita, ni kuma gaskiya na kasa mantawa da zancen shi yasa nace bari in tuntube ki da kaina inji" nayi shiru tare da sadda kaina kasa, ince me? Tunda ni a karan kaina ban san ya muke ciki ba. Anty Ameenah ta kamo hannuna ta rike cikin nata, "look Nafeesah! I am not trying to persuade you or something else.... I just.... I mean ina cikin eagerness nason ganin rayuwar kanina tayi haske, ya samu farin ciki da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren shi. It has been good thirteen years tun auren shi da Mubeenah, aure ne aka musu na zumunci, ita diyar wani abokin Alhajin mu ne. Tun daga auren su Ibrahim ya rasa farin cikin shi, he was young, amma bai dandani abinda matasa kamar shi suke dandana idan suka yi aure ba. Ya rasa jin dadin yarintar shi a wajen yarinyar da bata san darajar shi ba saboda

Please Login or Register in order to submit comment