Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai bata son shi. A matsayin Ibrahim na namiji ya hakura da auren dole din da aka mishi amma ita ta kasa hakura, a wajen Mubeenah ne kadai na karyata maganar bahaushe da yace duk kiyayyar da mace take wa namiji da sun fara haihuwa take dawowa so, a gareta kam sai kiyayyar ta koma har kan 'ya'yan shi. You wouldn't believe me Nafeesah, lokacin da ta samu cikin Abdullahi da kyar ta iya haifeshi, Allah ne kawai ya nufa zai zo duniya amma sai da tayi attempting din zubar da cikin sau biyu, haka aka zo aka sha dabi da cikin Qaseem, daga haihuwar Hafsat taje aka saka mata loop a cikinta ba tare da sani ko yardar Ibrahim ba. Bata dauke mu a tsiyar komi ba, sai mu hadu da Mubeenah a hanya idan ba dama ta gani ba ba zata mana magana ba, idan mu mun mata sai ta ga dama take amsawa. Babu yanda bamu yi da Ibrahim ba akan ya kara aure amma ya ki, yace baya so yaci amanar da marigayi mahaifin Mubeenah din ya bar mishi akan ya kula da ita da farin cikinta, shi a ganin shi cin amana ne idan ya kara aure. Haka Ibrahim ya rayu tsayin shekarun nan, ya danne farin cikin shi saboda matar da bata san yana yi ba, wadda bata appreciating dinshi da dangin sa har ma da 'ya'yan shi. Wallahi baki ji farin cikin da nayi ba lokacin da naji cewa ya shirya fitowa daga cikin ukubar daya sa kanshi a ciki ba, shi yasa kwata kwata naji na kasa yin hakuri in zuba ido ki kubuce masa Nafeesah" jikina gabadaya yayi sanyi, ban taba sanin cewa irin rayuwar da Abbu yayi ba kenan, koma yake kan yi. Anty Mubeenah kam wace irin mace ce? Anya akwai sauran mata irin ta a duniyar mu ta yanzu? Anty Ameenah ta shafa hannuna tace "kinyi shiru?? Baki son shi ne ko kuma ya miki tsufa??" na girgiza kaina ina dan murmushi, "ban taba mafarkin kasancewar wani mutum a matsayin mijina ba sai Abbu Anty" farin cikin dana hanga a cikin idanuwanta abun baya misaltuwa, na sadda kaina kasa cike da kunya ina jin kamar kasa ta tsage in shige. Tace "amma me yake hana ki cika burin ki?" nace "ina jin tsoron abinda zai je yazo ne, my mom seems to be strictly against it. Sannan ban san me zai je yazo ba a rayuwar auren Abbu da Anty ba, bana son abinda zai tarwatsa musu rayuwar auren su da kan iyalinshi" Anty tace "believe me Nafeesah! You are not. Allah kadai yasan iya ceton ran da zaki yi, wallahi babu abinda zai faru a rayuwar gidan Ibrahim sai ma farinciki dana san zai wanzu in shaa Allah, ke kadai ce wanda zaki iya yin wannan aikin saboda na tabbata Ibrahim yana son ki. This the first time in my life da naga Ibrahim wanting something very badly kamar ki, na tabbata idan ya rasa ki sauran rayuwar shi will be shattered to pieces. Naji dadin wannan lamarin sosai, ina tabbatar miki da cewa you are the perfect match for Ibrahim. You suits each other, na tabbatar da zai kula dake, zai so ki. Kada kiyi zaton saboda shi kanina ne wai nake koda shi, ba haka bane. Saboda na yarda da Ibrahim na kuma yarda da halayen shi. Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah babu abinda zai faru sai Alheri, in shaa Allah ba zaki taba yin nadamar Auren Ibrahim ba kamar yadda na tabbata zaki kasance a cikin farin ciki matukar kina amsa sunan Matar shi. So dear, stop holding yourself in and just go for it, kiyi abinda kike son yi kafin lokaci ya kure miki, Allah ya Albarkaci rayuwar ki" na sadda kaina kasa ina jin wani irin confidence da kwarin gwiwa yana shiga ta. In shaa Allah ba zan kara rike kaina ga yin abinda nake son yi ba, da yardar Allah zan zama mallakin Abbu tun kafin ya subuce daga hannuna ya sa in tagayyara. Anty Ameenah ta kara bani shawarwari kafin muka mike muka fita daga cikin garden din, har inda tayi parking din motar ta na raka ta. Ta bude motar ta shiga, ta mika hannunta baya ta dauko Leda mai dauke da tambarin kamfanin shop rite Ta miko min, naso nokewa in ki karba amma ya kamo hannuna ta dora min ledar a tafin hannu dole na karba tare da mata godiya, tace "babu komi Ameenah, and please make sure to make it very fast" na sunne kaina a kasa ita kuma ta tashi motar ta tafi.

Tarkacen kayan makulashe ne ta kawo min, dambun nama, cookies da tarkacen biscuits sai turare masu kamshi a cikin ledar. Na bude biscuit din short bread na kai bakina na cinye tare da korawa da lemu, kwana biyun nan abubuwan dana mayar abincin cina kenan. Bayan nayi sallahr Isha'i na gama shirin kwanciya, na kwanta akan gadona tare da janyo pillow na rungume a kirji na, Maganganun Anty Ameenah suka fara dawo min a cikin kaina. Na tsinci kaina cikin mutuwar jiki tare da jina ina narkewa akan katifar da nake kwance. Allah sarki Abbu! Ban taba zaton cewa rayuwar auren shi munin ta yayi yawa har haka ba, na kara juyawa a akan gadon. Poor Abbu! Da yardar Allah sai na zama dalilin sharewar hawayen shi da yayi ta zubarwa a shekarun baya, in Allah ya yarda sai na zama haske da fitila a cikin rayuwar Auren shi. Da haka na lumshe idanuna barci ya dauke ni, idanuwa brown masu sheki da kyalli suna gagari a cikin duhu.

*******

Da kuzari sosai na tashi a cikin jikina ranar, tunda nayi sallahr Asubahi ban koma barci ba saboda ina da laccar safe, nayi wanka na shirya abin karyawa kafin na shirya jikina cikin riga da siket na leshi ruwan ganye dinkin yayi min cif a jikina, shi bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba. Ina cikin karyawa dinne na kira gida muka gaisa dasu, anan ne Daddy yake fada min cewa result dinmu na KadPoly ya fita kuma yayi kyau sosai, nayi hamdala tare da godewa Allah. Yace ya riga daya turawa Abbu da result din don a kammala shigar da takarduna a cikin BUK tunda dama awaiting result ne, nace mishi babu damuwa, daga nan ya ba Mommy muka gaisa da ita har take fada min ansa auren Hansa'u diyar Kawun su Daddy nan da watanni hudu, na musu fatan alkhairi sannan muka yi sallama da ita. A gurguje na karya naja gyale yellow mai yalwar fadi da flat din takalmi shima yellow sai jakar littafai da wayar hannuna na tafi. Kimanin mintuna arba'in muna jiran zuwan Mrs Adayi matar da take daukar mu Intro. Physiology amma shiru bata zo ba har karfe tara tayi laccar daya kamata ace tun karfe takwas aka fara ta. Na kalli agogon hannuna tare da dan jan tsaki, bana son abinda zai bata min lokaci duk da cewa bani da wani class din sai two, amma ina son ganin Abbu kafin ya tafi gida wanda nasan cewa muddin ta shigo sai ta cinye lokacin data batar a waje. Wajen karfe tara da rabi class rep yayi announcing din isowar lecturer din, nan da nan ajin yayi shiru daga hayaniyar daya dauka. Kofar hall din ta bude aka shigo, cikin takun nan nashi mai cike da kasaita da natsuwa ya taka har zuwa gaban allo. Ina jin irin sautin woah! Daya dinga fita daga bakin mates dina mata da kuma kus-kus din da suke yi sai dai hankali na baya kansu, yana gaban allo ina kallon halittar dake tsaye, sanye cikin suits navy blue da farar shirt sai navy blue din neck tie kafar shi sanye da bakin cover shoe, fuskar shi mai cike da kwarjini da ilhama tana ta shinning a cikin hasken ranar daya shigo, nasan dole dama enmatan ajinmu su rikice da ganinshi a yadda yayi kyawun nan, looking soo take away. Daga sama na dinga jin muryar shi lokacin da yayi introducing kanshi as Doctor Ibrahim Galadanchi, zan koya mana course din a madadin Mrs Adayi wadda ta samu accident din mota a daren jiya, zai daukeni course dinne har zuwa lokacin da zata warke. Ya lalubo idanuna ya rike da nashi idanun na en sakanni kafin ya janye idanunshi zuwa ga sauran dalibai yana wani smirking, "alright, can we start now?" gabadaya ajin ya dauki sowar "yes" Ya Allah! Ni kam na kasa tantance a wata duniya nake, har ya gama gabatar da darasin ranar cikin kwarewa da tataccen turancin nan nashi babu abinda na iya tsinta sai idanunshi dake karakaina a jikina suna kara hana ni natsuwa, A Father's Friend! A Lecturer! Way to go Nafeesah!! Ta yaya zan iya dealing da responsibilities dinnan?? Ya rufe littafin hannunshi tare da maida marker dinshi cikin cover dinta yana kallon en ajin, "let's call it a day here" kowa ya fara maida littafin shi cikin jaka, ba bata lokaci ya dauki brief case dinshi ya tunkari kofa bayan ya haske ni da wani irin kallo wanda yasa naji gabban jikina sun koma kamar ruwa, Abbu will really be the death of me!! Dalibai suka fara fita daga cikin class din amma ni ina zaune kikam kamar gunki, sai da Jalila wadda muka zauna seat daya da ita ta dan daddabe ni sannan na dawo cikin natsuwata, tace "Nafeesah lafiya? Tun dazu na kula kamar baki cikin natsuwar ki" na girgiza mata kai, "lafiya ta lau, kawai na dan gaji ne" tace muje koh? Na jinjina kai tare da mikewa tsaye, ina tashi karan shigowar message a wayata ya tsaida ni; Abbu ne. Cikin rawar hannu na daga, "meet me at room 13, Dept of Physiology, lecturers lounge" abinda yace kenan, na kalli Jalila ina dan murmushi nace "sorry, ku tafi kawai, akwai inda zan biya yanzu" tace ok, tare da wucewa. Ni kuma na tafi zuwa kiran Abbu. Ofishin shi shine na karshe cikin jerin offices din lecturers din dake wajen, na tsaya a bakin kofar ina kara kallon name tag dinshi dake rataye a jikin kofar an rubuta 'Dr. Ibrahim Mas'ud Galadanchi' na shafi sunan da hannuna tare da lumshe idanuna ina dan murmushi, Abbu! What have you done to my innocent soul?? A hankali nayi knocking a bakin kofar, cikin husky voice dinshi yace "yes come in please" na tura kofar a hankali na shiga, kafafuna suka nutse a cikin wani tattausan zagayayyen carpet an rubuta welcome a jiki, tattausan kamshin air freshener da sanyin split suka doke ni har sai dana saki ajiyar zuciya saboda sanyin dadin daya ratsa ni. Yana zaune a gaban desk top yana aikin typing, ya cire suit din jikin shi sai shirt din kawai ya bari, you have no idea irin kyawun da yayi mun a lokacin. Ofishin nashi babba ne, shelves shelves ne na littafai tun daga na bokon har na Arabi a kowace kusurwa ta Ofishin, sai desk da dai duk wasu tarkace da zaka samu a cikin Ofishin manyan laccarori da boko ta gama ratsa su. Ya dago kyawawan idanunshi daga kan desk top din da yake aiki a kai ya kalleni, murmushi ya saki mai sanyi wanda ban san lokacin dana mayar mishi da martani ba. Ya nuna min kujera alamun in zauna, ba musu naje na dan dosana kamar wadda za ace mata ar! Ta karta a sukwane. Na nutse nake bin Ofishin nashi da kallo, baby wasu tarkace da zasu saka mutum ciwon kai, komi a shirye kuma cikin tsari. A hankali ya daga baki yace "plss make me a cup of tea" na daga kai na kalleshi a hankali, ya wani langwabar da kai gefe kamar wani karamin yaro saura kiris in kwashe mishi da dariya. Na ajiye jakar hannuna akan kujerar na mike na kunna electric kettle dana gani a jikin socket, ya nuna min inda cups da sauran kayan shayin suke ruwa yana tafasa na hada mishi na kai na ajiye mishi, ya kalleni "thanks.... Ke fa?" na girgiza mishi kai. Aikin shi ya komawa yana yi yana dan sipping din shayin nima na koma na zauna. Ban jima ba naji ya kashe computer din, karan matsawar kujera alamun ya tashi daga inda yake, ya zauna akan kujerar shi wadda take fuskantana. Shayin shi yaci gaba da kurba idanuwan shi suna kaina, kaina yana kasa ina wasa da yatsun hannuna, ji nake kamar wanda rami zai bule daga cikin fatar fuskana saboda zazzafan kallon Abbu a kaina. Ya ajiye cup din akan teburi tare da dan matsowa daga kan kujerar da yake, yace "toh Nafeesah, yau dai ina so inji abinda kika yanke game damu, ya ake ciki? Na fada miki na gaji da jiran ki haka nan, na gaji da yawo da hankalin da kike min. This is the last time da zan tambaye ki, bayan shi ba zan kara ba Nafeesah I promise you don ni dai ba karamin yaro bane, so m asking you, me kike yanke game damu??" Zuciyata was beating very fast and erratically kamar wadda tayi gudun marathon, kaina, yatsa, gangar jikina da komi ma na jikina sun yi mun wani irin nauyi marar misaltuwa amma duk da hakan ban fasa daga kaina na nake jin ya koma kamar wani gingimemen dutse ba na kalleshi, fuskar shi was mixed of emotions, fargaba, hope, plead, idanunshi da suke matukar burge ni sun shige ciki, nasan da ace idanu suna magana dasu ne zasu yi rokon da nake gani akan fuskarshi tunda bakin shi ya gaza furtawa. A lokacin na gama yin concluding cewa farin cikina koma ince namu a yadda na karanci fuskar Abbu a lokacin, yana tattare damu ne, yayin da makullin kofar take hannuna, that means ni kadai ce zan iya bamu farin cikin da muke bukata kenan??
A hankali na sadda idanuna kasa, na tattaro duk kwarin gwiwa na tare da gyada kaina a hankali.....
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare *Ni Da Abokin Babana!* Fans





*♡Jeedderh♡*

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*40*

Na kasa tantance abinda ke zane akan fuskar Abbu a lokacin, murmushi yake yi sosai, amma zan iya rantsewa akan cewa na hango alamun moistness a cikin idanunshi, ban san me zai faru ba nan gaba, ban san ya zamu kare da Mommy ba sai dai irin farincikin dana gani a tattare da Abbu yasa naji duk wata fargabata ta barni, idan dai har zan dinga ganin irin wannan kallo daga Abbu to ban damu da duk abinda zai faru ba, nasan cewa murmushin Abbu ya ishe ni. Ya dauki mintuna da dama bai yi magana ba ina jin yana containing farin cikin dake cin shi ne, yayi gyaran murya yace "nagode sosai Nafeesah, amincewar ki da yardar ki a gare ni sun dadada min sosai you have no idea, in shaa Allah na miki alkawarin ba zaki yi nadamar aurena ba, Mrs. Ibrahim Galadanchi!" na kai hannuna biyu na rufe fuskata dasu ina dan murmushi yayin da naji Abbu yana er dariya, yace "why? Baki son sunan ne ko me?" naki bude fuskata balle in kalleshi, yace "idan baki son sunan it's okay, but bude mun fuskar ki plss" na kara kankame fuskar tawa, ina zan iya fuskanta Abbu a yanzu? Ina jin lokacin daya tashi daga inda yake ya dawo gefena ya zauna kamshin turaren shi ya cika min hanci, yace "zaki bude da kanki ne ko sai na janye da kaina?" a hankali na janye hannuwan nawa sai dai fuskana tana kasa, a yadda nake jina a lokacin nasan ba zan taba iya hada ido dashi ba. Ya rankwafo da kanshi saitin fuskata, da sauri na daga kaina na kalleshi cikin sa'a muka hada idanu dashi, wayyo Allah! Kasa tsaye in shige. Ban taba ganin Kwarjinin da yayi mun a lokacin a tattare dashi ba, wani irin magnet naji ya fara fuzgata yana kokarin hada ni dashi, da sauri na mike tsaye ina lalubar jakata tun kafin in kai ga yin abinda zan zo ina dana sani gwara in bar office din. Abbu ya bini da ido yana frowning, na tsaya a gaban shi ina rataye jakata a kafada kaina a kasa, nace "umh.... Zan tafi... In... na da class anjima" ya kalli agogon hannunshi tare da dan jan siririn tsaki, "so nayi mu tattauna game da yadda zamu tsara rayuwar auren mu dake fa, amma ba komi there's always a second time. Amma zan sanar da Daddynki dai" na kalleshi da sauri ina zaro idanu, "tun yanzu?" yayi scrunching din brows dinshi, "tun yanzu? Me kike nufi?" nayi kasa da kaina "na ga kamar yayi kusa ne" ya girgiza kanshi "bai yi kusa ba Nafeesah, na gaya miki na kagauta ki zama mallakin, ni da so samu ne ma sai ince satin sama a daura mana aure in killace ki a gidana, Ya Allah! Na tabbata burina ya gama cika, I wouldn't ask for anything sai dawwama dake a gidan Aljannar Firdaus" sai kawai na daga kafa na fara tafiya, Anya Abbu ne? Ban san me ya shiga kan shi da kwalwar shi ba a Kwanakin nan sai ya dinga min wasu maganganu da suke saka ni cikin ramin matsananciyar kunyar shi. Ya mike tsaye, "tunda baki son yin hira dani bari in maida ki hostel to" na fita na tsaya a bakin kofar Ofishin ina jiran shi, ya fito daga ciki ya rufe office din yayi gaba na bishi a baya har inda yayi parking din motar shi. Muka shiga yaja motar, a hankali muke tafiya yana ja na da er hira. Duk yadda nake kauce-kauce da kare-karen fuska sai dana dawo ina dariya, kafin mu karasa hostel na sake daga awkwardness din daya dabaibaye ni, a cikin motar ma mun jima muna hira a gaban hostel dinmu har sai da aka fara kiran sallar azuhur sannan muka yi sallama. Na bude murfin motar ina ce mishi ya gaida su Hafsy, yace "me zaki ce musu bayan tunda kika zo baki ziyarce su ba? Fushi ma take yi dake don ki sani... Koda yake ai na kusa ciccibar ki in kai mata ke cikin gidan gabadaya, ki fara haifo mata kanne nasan zata yi farin ciki sosai, zan gaya mata ta daina fushi dake haka nan" ni dai na ida sa kafata waje na fita ina dan murmushi, da gaske Abbu ya canza daga cool and calm Abbun dana sani zuwa Romantic, wanda yake fadar duk maganganun da suka zo bakin shi ba tare da yayi la'akari da cewa sun girmi kunnuwana ba. Ya dan leko da kanshi ta cikin motar, "baki ce komi ba fa" na dan juyo na kalleshi tare da haske shi da murmushi na juya na shige cikin hostel, ina jin hot gaze dinshi a kaina har na yi nisa a cikin hostel din, na tura kofar dakin na shiga. Firdausi na zaune akan kujera da littafi a hannunta tana karatu, ta dago tana min sannu da zuwa na amsa, kallona ta cigaba dayi kamar wadda taga wani bakon abu a jikina, na rataye jakar hannuna a jikin hanga na kalleta, "wannan kallon naki lafiya dai koh?" tayi murmushi tace "you are blushing! Did someone propose to you??" na kalli kaina a cikin madubi, I couldn't help the chuckling daya fito min, na kalleta ina murmushi "Ina ga dan zafi zafin da ake yi ne kawai" ta kalleni tana murmushi tare da gyada kai ta maida Idanunta ga littafin hannunta. Nima nayi murmushin na fita naje nayi alwala na dawo nayi sallah, kafin in gama Firdausi ta dafa mana indomie ina gamawa muka ci na sake fita wajen lecture.

A daren ranar sai ga wayar Daddy ta shigo, na daga wayar cikin sanyin jiki da faduwar gaba. Ina gaida shi ya amsa ya dora da fadin, "Ibrahim ya kira ni yanzu yana fada min wani labari" na sadda kaina kasa kamar ina gaban shi, "kayi hakuri Daddy" ya danyi murmushi, "meye kike bani hakuri dear? I just call to know that you are okay with it. Are you sure zaki iya?" na gyada kaina amma ban yi magana ba, yace "naji dadin zabin da kika yanke sosai Uwata, naji dadin cewa mutumin da kika zaba ya zama abokin rayuwar ki Ibrahim ne, naji dadin cewa zan barki a hannu na gari kuma na kwarai, nasan ba zan taba yin fargaba game da yadda kike ba saboda na yarda da Ibrahim. Allah ya miki albarka Nafeesah" naji hawaye suna kokarin cika min ido, da ace ina kusa dashi da sai na rungume shi, nace "I love you Daddy, nagode" yace "You are all we have Uwata, dole mu so farincikin ki, ina Alfahari dake" nace "nima haka Daddy.... Amma Mommy fa?" yayi kasa da murya nasan sirri yake nufi, "Mommy dinnan taki fa sai a hankali, tun dazu take hawa tana kumbura kamar fulawa daga mata maganar wae ai ita bata yarda ba cin amana zata yi, shine nace mata idan haka ne itama za a turo mata yarinya kamar ki idan tayi watanni sai in aureta, don Allah ba anyi 1-1 ba?? Sai kawai ta hau kumbure-kumbure, yau ko magana bata min ba dana dawo daga aiki" duk da banji dadin abun ba sai dana yi er dariya nace kai Daddy! Yace "it will be better idan baki kira ta ba for two days, zan yi kokari in ga cewa na ganar da ita abinda take fahimta" nace toh Daddy. Yace good girl, kije kiyi alwala ki kwanta, nasan kina da darasi da safe nace "exactly Dad, goodnight" muka yi sallama na ajiye wayata jikina a sanyaye. Na jima a zaune ina tunanin yadda zan yi idan Mommy taki bamu albarkarta game da auren nan, ni dai nasan cewa ba zan iya auren Abbu ba tare da yardar Iyayena ba gaskiya. Na tashi naje na dauro alwala nayi shirin kwanciya barci. Dana daga wayata naga message din da Abbu ya turo min mintuna biyar da suka wuce, cewa yayi; "A lokacin da kowa yake neman makwanci da niyar warware gajiyar data addabe shi, a daidai lokacin bawan Allah Ibrahim yake karawa kan shi wani tarin gajiyar, why? Saboda bashi da makwanci kwanciya balle filon tada kai. Ina fata wadda take karanta sakon nan zata yi gaggawar kasancewa tashi ko zai samu sanyin rai dana zuciya a tare dashi. Sai da safe, lots of love and kisses" n zan iya rantsewa naji saukar lebba a kumatuna, na kai hannu na dafe wajen ina duba gefe na, dariya na saki tare da dan dukan goshi na, silly me! I am even expecting him to kiss me, woah!! 'Goodnight' kawai na tura mishi as a reply na kwanta tare da lumshe idanuna. Barci mai dadi cike da kyawawan mafarkai ya daukeni ni.
~So how are you doing outta there Abbu and Nafee's fan??
#TeamAbbu
#OneLove

*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*



*♡41♡*


Kwana biyu kuwa ban yarda na latsa sunan Mom a wayana da sunan kira ba sanin halinta na sauka daga fushi da kanta idan ta hau don sau tari idan tana fushi bata cika son ana bin kanta ana bata hakuri ba ma, she prefers a kyaleta har sai ta sauka don

Please Login or Register in order to submit comment