Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kira da karya? just wait, in har ina raye sai na mayar dake abin kwatance, sai na muzanta ki fiye da kare, I'm warning u, ki fita daga rayuwar Ibrahim kafin in mayar dake abin kwatance!!" na daga kafada, “I'm not stopping you from doing whatever you will do, kawai abinda nake so yanzu shine ki matsa ki bani hanya in wuce" ta hasala iya hasala, hannu ta daga kamar zata mare ni, kallonta nake yi kamar wata kayan kashi a yatsine, ita da kanta ta janye hannunta ta maida shi kasa, nayi murmushin mugunta nace “kece kike ta shirme kina bin namijin da yake kin ki, tunda yace baya yi let him be, ana so dole ne malama?" ta wani zare ido tare da buga tsawa “ke...!!" nayi saurin katseta kafin ma ta gama fadin abinda tayi niyar cewa ta hanyar zare ido nima, nace “malama kin ganni nan ban yi kama da matan da threats dinki zasu yi tasiri a kan su ba, kiyi duk abinda zaki yi wanda kike ikirarin mallaka ba zaki taba mallakar shi ba saboda ba don ke aka yi shi ba, a shawarce zan gaya miki ki fita daga rayuwar shi, Idan kuma kin ki ji sai dai kiyi mutuwar da kike ikirarin yi! Abbu ne kamar na aure shi na gama" naja tsaki tare da zagayawa ta gefenta ta wuce abuna ina muttering kalmomin dani kaina bansan me nake fada ba duk don in yi provoking dinta, na kuwa yi nasara. Ina bada baya naji sautin karan data saki cike da takaici, na kuwa saki murmushi kamar zan sheke da dariya.

Washegari da misalin karfe daya aka daura auren a babban masallacin juma'ah dake garin Malumfashi. Muna zaune a dakinmu Ni'imah ta kawo wata yarinya tana min kunshi wanda hakan umarnin Abbu ne, text dinshi ya shigo wayata. Na mika hannu na da nake jin shi kamar ba a jikina yake ba na dauki wayar, kai gabadaya ma sauran sassan jikina haka suke tunda garin ranar ya waye, ina ji Niimah da Firdausi suna ta hira amma na kasa saka musu baki duk da cewa rabin hirar a wajen tsokanata ne. Text din cewa yayi, “Alhamdulillah. Yanzun nan aka shafa fatiha, kin zamo tawa ta har abada. Ina taya junanmu murna da farin cikin mallakar junanmu, Allah ya bani ikon rike ki cikin amana da kulawa Nafeesah" sai kuma wani da yace, “Wannan ranar rana ce da ban taba tunanin zata Riske ni ba, ranar dana mallaki abinda ban taba kawowa raina zan mallake shi ba. Jina nake kamar wani sabon halitta saboda tsananin farin cikin da nake ciki wanda na kasa misalta shi, Nafeesah kina da gurbi mai matukar girma da fadi a cikin zuciyata, na roki Allah mai Girma akan ya bamu zaman lafiya mai dorewa. You've Completed My Puzzled and Shattered Life, I really Cherish You Nafeesah" naji hawaye sun cika min idanu, nayi saurin runtse idanun ina kokarin maida hawayen, Allah abin godiya da Girmamawa, wai ni ce yau na zama matar Abbu?? Naji ina narkewa kamar wata jelly akan kujerar da nake zaune, na tabbata da ace ina tsaye ne da sai na fadi. Rangadediyar gudar da Ni'imah ta rangada ce ta dawo dani cikin tunani na, guda take tun karfinta da waya a hannunta ta hau kiran waya tana bada albishir din an daura aure. Wayana ya shiga kara na daga, Daddy ne. Cikin rawar hannu na daga, “Uwata! Amarya!!" abinda na fara dokar kunnena kenan, na kasa magana sai kai dana jijjiga, yace “Nagode Allah da yasa naga wannan rana, ranar dana damka amanar ki a hannun wanda na tabbatar zai rike ki dari bisa dari, dama babu burin duk wani uba na kwarai daya wuce wannan. Yau dai kin zama matar Ibrahim, kin fita daga karkashin kulawar mu kin koma karkashin shi, yanzu shi zai yi sanadiyar ki zuwa gidan Aljannah wadda nasan babu haufi zaki sameta da yardar Allah uwata, Allah ya miki Albarka, Ya Albarkaci Rayuwar Auren ki, Allah ya baku zuriya Dayyiba!" muryar shi tayi kasa can kamar wanda yake so yayi kuka, ni kam kasa daurewa nayi kawai na fashe da kuka, gabadaya wani iri nake jina a tunanina idan nayi kukan zan samu sanyin zuciya. Ya shiga lallashina har na samu nayi shiru kafin ya min sallama. Yana kashe wayar kiran Mommy ya shigo, itama dai Addu'ah ta min kamar yadda Daddy yayi, zuciyar Mace mai rauni, sai tasa kuka, nima kukan nake yanzu sosai su Ni'imah na aikin bani hakuri, ina ji daga wayar Anty Uwani da muryar wasu mata suna ba Mommy hakuri, Anty Uwani cikin fada tace “sai kisa hankalinta ya tashi ai, gashi nan itama kin sata kuka, ina amfanin haka?" tace “kukan farin ciki ne" tace “ai godiyar Allah ya kamata kiyi ba wai kuka ba, shima Abban nata yanzu na baro shi a waje yana share kwallah Allah yasa ba ita ya kira yana kukan ba.... Wannan ai sai ku sanyayar mata da gwiwa...." daga haka dai suka kashe wayar. A hankali nima nawa kukan ya fara yin kasa har ya dawo shessheka kafin nayi shiru ina ajiyar rai. A ranar dai har ba zan iya lissafa iyaka mutanen da suka kira ni suna taya ni murnar yin aure ba, tun daga kan abokaina da yan uwa har wasu daga cikin abokan Mom. Da yamma sai ga Ramlah ta dira a Kanon kamar daga sama, muka yi tsalle muka rungume juna ni da ita muna ihun murna, watanni biyar ciff tunda muka rabu da ita bamu sake haduwa face to face ba sai dai a Video call. Muka zube akan gado muna maida numfashi daya bayan daya, kallona take tun daga sama har kasa ta kyalkyale da dariya, “kaga Amarya a gidan Ibrahim Galadanchi, kin ga wani kyau da kika yi kuwa??" na kai mata duka ina dariya, “meye haka zuwa babu sanarwa?" tace “surprise, dazu na dawo har mun yi hutu abinmu" nace “kun huta ku kam" nan muka shiga hirar yaushe gamo, tana nan tare dani har aka kira sallar magriba, ganinta ne yasa na warware har na samu naci abinci. Nan dai ta min sallama ta tafi akan cewa zata dawo Washegari, bayan na rakata zuwa bakin kofar hostel din na koma daki nayi sallar isha'i, bayan na gama na zauna nayi ta jero addu'o'i game da neman albarkar Allah da zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da nake tunkara a cikin rayuwata. Abbu ya kira ni yace yana jirana a parking lot inda muka saba tsayawa, na tsinci kaina cikin faduwar gaba da sanyin jiki, cikin sanyin jikin na tashi na gyara zaman hijabin jikina na sauka kasa. Jingine yake da motar shi yana danna wayar shi, sanye yake cikin shadda ruwan Makuba yau kam har da hula a kanshi, akwai wadataccen haske a wajen hakan ne ya bani damar ganin fuskar shi sosai kamar cikin rana. Tunda na hango shi naji kafafuna sun fara hardewa, ban taba tsintar kaina cikin fargaba da tsoron fuskantar Abbu ba tunda nake a rayuwata sai ranar, da kyar na iya karasawa gaban shi ina maida numfashi kamar wadda ta sha gudu, babu abinda yayi motsi a jikinshi sai idanun shi da suke kare min kallo tun daga sama har kasa, kafafuna ba zasu taba iya daukana a haka ba sai nima na jingina da jikin motar ina kallon zara-zaran yatsun kafar shi da suka fito ta cikin kyakkyawan bakin budadden takalmin kafar shi yana ta sheki.....
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!
~Me zaku ce game da Shafin yau??
~Lots Of Love and Hearts
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare...





*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®•°Fikrah Writers Association°•*🖋
_In Dedication to Aunty Zee_
_Tukuici zuwa ga Marubuciya SADNAF_
_Godiya Mara Adadi Masoya, Makaranta Littafin Ni Da Abokin Babana, yawan ku ya kai adadin da ba zan ma fara jero sunayenku ba, just know that where ever you are Jedderh really appreciate your love and kindness, #OneLove_


*47*


A hankali ya sauke ajiyar zuciya wadda take nuna tsananin farin cikin da yake ciki, “Hii there My Queen, My Happiness, My Amour, My Bride! Sunayen naki suna da yawa fa, amma kullum zan dinga kiran ki da guda daya wanda nasan sai mun dauki shekara basu kare ba, how are you?" kunya ta kama ni na sadda kaina kasa, yau ko sallama ban iya nayi ba balle in gaida shi, haka kawai naji wani nauyi da matsananciyar kunyar shi sun dabibaye ni.
A hankali kuma kamar wadda aka tursasa na bude baki nace “Ina yini Abbu?!" ni kaina sai da nayi mamakin muryata, it was very low kamar wadda take rada, ban yi tunanin yaji abinda nace ba sai da naji yaja wani sharp breath har yana hadawa da lumshe ido, “Masha Allah!" ya furta a hankali yana kallona da lumsassun idanuwan shi, ya Allah!! Da ace yasan yadda kallon yayi affecting dina da yayi gaggawar dauke idanunshi daga kaina saboda nasan ba zai so amaryar shi ta zube kasa kila hakan yayi sanadiyar karyewar kafarta ba, sai ya ci gaba da kallona kawai. Na samu nace “Ya hanya?" duk don in katse kallon da yake jifa na dashi da kuma hirar da zukatanmu suke yi, yace “Alhamdulillah, akwai gajiya kam amma tunda mun iso lafiya ai shikenan, besides ni tunda na ganki ma naji ni kamar an dauke min duk gajiyar dake tattare dani" nayi kasa da kaina, yace “Dad dinki ya bada sakon gaisuwa a kawo miki, ya damka min amanar ki har sai da sashen karbar sakonni a kwalwata ya cika, he even threatens me, heol!!" ya wani yi rolling idanu tare da dan chuckling, na kalle shi ya haske ni da murmushin nan nashi da yake sa ni yin abin da ban shirya ba, ba shiri na sakar mishi murmushin. Yayi cocking kanshi gefe guda, “ko ke fa! Keep smiling like that baby, yau fa rana ce ta musamman a gare mu bai kamata ace murmushi ya kau daga kan fuskar ki ba.... Hmm, how I wish gidana za a kaiki yau din nan, da sai na nuna miki kaunar da babu namijin daya taba nunawa wata ‘ya Mace a duniyar nan, na saka ki a cikin farin cikin da baki taba tsintar kanki a ciki ba, amma tunda hakan ba zai samu ba zan rike komi har sai an kaiki gidana baby, ranar...." sai kuma yayi shiru yana girgiza kai, “it will be a surprise, sai kin zo kawai zaki gani" ya duba agogon hannunshi, motar ya bude ya fito da leda ya miko min, tun kafin in amsa nasan ko menene a ciki, kaza ce gasasshiya sai tashin kamshi da tururi take yi, yace “bana son farin cikin ciyar da amaryata a daren aurenmu ya wuce ni duk da cewa ba ni da kaina zan ciyar dake ba" nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, yace “you must be tired, jeki ki kwanta, nima zuwa zan yi inyi barci don ji na nake yi very exhausted Allah ma dai yasa in iya yin barcin" ni dai ban tanka mishi ba na daga Baki da kafa a lokaci guda nace “sai da safe".
Suddenly naji an janyo hannuna an dawo baya dani, kafin inyi yunkurin kwace hannuna da kaina gabadaya ko kuma ma in tantance abinda ya faru na tsinci kaina akan faffadan kirjin Abbu, yasa hannu daya ya dago habata ya kalli tsakiyar idanu na, abubuwan dana karanta a idanunshi a lokacin suna da yawa, zallan so, tsabar kawa, raw lust Ya Allah I couldn't take it, idanuwana na kame don ba zan iya cigaba da karbar sakonnin dake fita daga cikin idanunshi ba, naji hucin numfashin shi akan fuskana ban taba kawo komi ba sai da naji bakin shi akan nawa, it was as if duniya ta tsaya cak da juyawa, ya dago ya kalli fuskana da idanuwan suke rufe yace “it's something that I've wanted to do decades ago but being the good man I am holding it in, I Love You Nafeesah!!" abubuwan sun yi wa kwalwa ta yawa a lokacin har na rasa da wanne iri ne zan ji, his sudden kiss ko kuma sudden kalmar yana so na daya furta?? Na daga idanuna da suka min nauyi na sauke su a fuskar shi, kallona yake fervently, sai naji ni kamar wata danyar nama a gaban zaki, da dan sauri na janye hannuna daga nashi hannun, cikin sauri na juya na fara tafiya ina jin kamar wadda ake turawa don har ga Allah ban san ina nake jefa kafa na ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya kaini daki, nayi jifa da ledar daya bani akan slab na zube akan gado kamar kayan wanki na rufe kaina rikib da bargo, Firdausi ta bini da kallo baki a bude naji dadi da bata yi magana ba. Allah kadai yasan lokacin dana share a kwance a cikin bargon nan, daga karshe dai na mike saboda ihun da cikina yake yi na yunwa, tun macaroni din da muka ci da Ramlah da rana ban kara cin komi ba, na sauka daga kan gadon na dauki plate na bude ledar har da yoghurt a ciki mai sanyi duk da zafin kazar ya rage mishi sanyi, na dora ta akan plate da fork da er wuka na kai kan dan karamin bench da muka mayar kamar dinning na dora, na dauko kofuna da yoghurt din suma na ajiye, da hannu na wa Firdausi nuni alamun ta taso don ba zan iya daga baki in mata magana ba ma. Ta taso ta zauna a gefena tana wabi smirking, “Anya zan iya cin kazar amarcin nan kuwa? Idan aka tashi tambayana ita ya zan yi kenan?" nayi banza da ita na fara cin kazar, itama ta fara ci. Tace “ni naga kin wani firgice ne ko dai anyi abin ne?" na harareta tayi dariya kasa-kasa tace “dama sai dana gaya miki ai, mu dai ki rufa mana asiri ki bari sai mun kaiki kafin ki samu ciki kinji??" nan ma ban tanka mata ba, to ai ko nayi niyar tanka mata ma bani da kuzarin yin hakan. Ita kanta kazar jin ta nake yi tayi wani iri na bakina bana jin dadinta, sai yoghurt nayi ta kwankwada don shine mai sauki tunda hadiya kawai zanyi, sauran kazar Firdausi ta nade a cikin takardar ta ta saka a cikin fridge dinta. Littafai na dauko na dare kan study table ni ala dole zan yi karatu, koda na zauna babu abinda yake yawo akan littafin sai fuskar Abbu da murmushin shi, duk yadda naso inyi karatu a daren ranar abin yaci tura dole na hakura na koma kan gado na kwanta hannuna dafe da lebena wanda har lokacin nake jin tausasan lebunan Abbu akan su, it felt so awkward yet so good my body was shaking with desire.

Sai bayan da nayi sallar asubahi sannan na samu na kara bitar karatu. Karfe tara muka fara exam dinmu muka fito kafin sha biyu, daga nan barci nayi don jiya kam ban samu nayi barcin kirki ba. Sai da su Ni'ima suka zo sannan na tashi daga barci lokacin wajen karfe biyu ne, sai da nayi sallah sannan muka shiga shirye-shiryen zuwa wajen Reception din. Suka wanke min kai suka kafar dashi kafin suka gyara min shi sai sheki yake yi da tashin kamshi, nayi wanka na fito nan ma aka shiga yin kwalliya kuma. Da aka kira la'asar muka yi saurara muka yi sallah sannan muka ci gaba, na zura doguwar rigar shaddar da Abbu ya kawo min, Ramlah ta daura min dankwalin rigar yayi kamar gwaggwaro, na saka dankunne, sarka da awarwaro masu ratsin brown a ciki, muna cikin yin shirin wanda aka turo ya dauke mu ya yi waya yace ya iso, da yake suma a shirye suke sai duk muka rankaya muka tafi. Wata er ubansun Range Rover ce baka tana ta sheki tazo daukar mu, aka bude mana muka shiga maza biyu ne a gaban motar don haka muka shiga baya muka tafi, daya daga cikinsu ya juyo muka gaisa har da yin shakiyancin su na abokanan ango, su Firdausi ne masu tare min ni kam kaina yana kasa, duk inda muka wuce sai an bimu da kallo wanda probably nasan cewa motar suke kallo don kuwa haduwarta ya wuce misali.
Tafiya muke yi a hankali har Hotoro, aka yi horn a kofar wani gida aka bude muka tura hancin motar muka shiga, anyi decorating din wajen da kayan ado da ake yi wajen bukukuwa ga kujeru an shirya, wajen cike yake da mutane ana ta hada-hada, aka yi parking sannan muka fita. Wasu mata gungu guda suka zo suka ja mu har wajen da na tabbatar saboda ango da Amarya aka yi shi saboda wajen ya fita daban, wasu royal kujeru guda biyu a kasan canopy an sa tuntu akai a kasa kuma an shimfida wani babban carpet me fadi da laushi. Mai gayya mai aiki Abbu yana zaune a kujera daya, munyi anko da kayan jikinshi shadda light brown mai surfanin zare dark brown, leather brown cover shoes da hular zanna bukar itama brown, kaina a kasa yake ban yi gigin daga ido na dubi Abbu ko tarin mutanen da hankulan su ya dawo gare mu har suka taimaka min na zauna a kujerar kusa da Abbu, in a wink sun bace daga wajen, photographer yazo ya fara haskemu da flashes ya dauki kamar guda goma kafin ya tafi. Abbu ya dan matso saitin kunnena ya rada min “kin yi kyau sosai amaryata" na danyi murmushi ina wasa da yatsun hannuna. Mutanen wajen basu da yawa duk da haka na hango wasu daga cikin dangina na Malumfashi mazan, Aminu, Haruna da Samir duk diyan kanne da Yayin Daddy ne, a matan wajen kuma na hangi Anty Amina da Anty Rahina, Sadiya, Saratu, Da Halima su kuma cousin din su Sadiya dinne, sauran matan kuwa da zasu kai guda goma ban san su ba na dai yi zaton kila matan abokan Abbu dinne. Ba wani bata lokaci aka fara gabatar da walimar, wani daga cikinsu ya bude taro da addu'ah, ya mana fatan alkhairi ana yi ana raha ana ta shan dariya saboda jokes din da mutumin ya dinga cracking, daga nan kuma aka yi en ciye-ciyen snacks da aka raba da kuma drinks, daya bayan daya suka dinga zuwa kowa da matar shi, mu gaisa dasu su mana fatan alkhairi su bamu kyauta, wani a cikin wrapping sheet wani kuma a envelope har su Anty Aminah dasu Ni'imah, daga nan kuma aka shiga daukar hotuna kamar me?! A haka har duhu ya fara shigowa, sannan ne fa aka kara rufe taro da addu'ah muka fara sallama dasu suna shiga motocin su suna tafiya, kafin dai a kira magriba an barmu daga mu sai mu, su Anty Ameenah ma suka mana sallama suka tafi, su Ni'imah sun bi mazajen su sun tafi sai Ramlah tabi bayan su Sadiya. Muka shiga falon matar gidan mai suna Farha ta mana jagora ni da Firdausi har cikin bedroom dinta muka yi sallah, matar tana da fara'ah ga kirki, muna gama sallah muka fara hira wadda yawancin ta akan rayuwar aure ne, challenges din dake cikin shi da shawarce-shawarce akan zamantakewa da kuma wasu shawarwarin da suka sa ni sunke kaina cikin gyale na, tace “kunya kike ji? Wallahi idan kika ce zaki saka kunya cikin rayuwar aurenki to zaki samu cikas kuwa more especially ke mai kishiya, ai wallahi dagewa zaki yi ki cire kunyar nan ki kama mijinki tsam kafin kishiya ko wata a waje ta miki kwacen shi" na gyada kaina cikin yarda da maganganunta. Su Abbu basu shigo gidan ba sai bayan sallar Isha, Farha tayi-tayi damu akan mu tsaya mu ci abinci muka ce a'ah, ta bude wani karamin Kit, tana bude shi wani kamshi mai dadi ya hade dakin, ta dauko kwalaben humra guda biyu ta bani ita kuma Firdausi ta bata turare, tace min “sai dai humra din nan ki bari sai kin tare kafin ki fara amfani da ita Zai fi" muka mata sallama muka fita waje inda Abbu yake jiranmu, muka sake sallama da Farha da maigidanta muka shiga mota muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikin motar har muka isa makaranta, Abbu yana yin parking Firdausi ta bude motar ta fita bayan ta wa Abbu sai da safe shi kuma ya mata Allah huta gajiya. Tana fita kamar wanda yake jira ya kamo hannuna, bai damu da yadda nayi gaggawar kwace hannuna ba ya sake janyo hannun nawa yana caressing da thumb dinshi, “kunshin nan yayi kyawu sosai, idan ya goge ki sake yin wani kinji? Shima idan ya goge ki sake wani, I'd like to be seeing it kinji??" na gyada mishi kai a hankali, yayi murmushi “good girl, amma ni sai wani noke-noke kike yi da wani kauda fuska, kin daina min magana, laifin me na miki iye?" ban yi magana ba sai kaina dana girgiza yace “ikon Allah! Aikuwa ba zamu yi haka dake ba, za kina bude baki ne kina min magana idan ba haka ba kuma raina zai baci fa, and u wouldn't like me idan hakan ya faru, ok?" na sake gyada kai, sai kuma nayi sauri nace “toh" yace “na fara nema mana visa fa, wani gari kike so kije for our honeymoon?" na dan zare ido, “honeymoon?" yace “ehh mana, da kin gama exams kin koma za a dawo min dake daga nan kuma zamu tafi honeymoon dinmu" nace “amma da aka ce sai session dinnan ya kare?" ya wani zaro ido kamar wadda ta fadi wani sabo, “ses... me? Ni dai nasan da bakina baki ji na fadi haka ba koh?" nace “ai nayi zaton haka ne" tun kafin in gama yake girgiza kai, “no! Ba haka bane. Gidan da zamu zauna is ready, komi ya riga ya kammala, kun gama jarabawar ku to me zan jira kuma? kin dai san ba zan barki kici gaba da zaman hostel ba kuma yanzun ma don we've already agreed on it ne shi yasa kika ga nayi shiru amma maganar gaskiya ban jin dadin zaman ki anan" na wani yi rau-rau da idanu, ya dage gira, “Allah baby kina jin dadin ki, kuka zaki yi kuma, me na miki?" ya kai hannunshi na dama ya tallabo kuncina dashi yana caressing din kuncina, hannunshi was very warm, na lumshe idanu na a hankali, na jiyo yatsar shi a saman idanu na yana shafawa, “zan ga yadda zamu kare da rigimar ki baby, dama ana haka ne? Daga magana sai ki kama kuka irin daddyn ki ya shagwaba ki koh?" na turo baki tare da janye fuskata daga hannunshi wadanda suka fara sanya min sayingsanyin jiki, murmushi kawai yayi. “Wadannan kyautukan da kika samu ban san ya zanyi dasu ba, do u have any idea ko wajen da zaki ajiye su?" nace “ka ajiye min su a wajenka" yace “to shikenan, zan kaisu gidanmu in ajiye, idan kin

Please Login or Register in order to submit comment