Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da spoon ina saka shi a cikin bakina, tunanina ya tafi ga yadda Mommy take acting weird tun zuwan Abbu, no tun zuwan Hafsy ma. Bayan su Abbu sun tafi jiya, mun gama dinner kenan na shiga daki Mommy ta biyo bayana, sam babu alamun wasa a fuskarta ta kalleni, "Ummiey me ke tsakanin ku da Baban Hafsat?" na kalleta da sauri kuma cike da mamaki, tambaya ce mai sauki, haka kuma amsar ta ba mai wahala bace, amma me yasa naji kamar ba'a taba tambayana tambaya mai wahala irin wannan ba? Saboda ni a karan kaina ban san me ke tsakanin mu ba. Kai na girgiza mata, "Mommy me kika gani ne?" ta Harare ni, "Ummiey ba cewa nayi ki tambaye ni ba, amsa nake bukatar ji; Me Ke Tsakanin Ku Ke Da Baban Hafsat?" na danyi shrugging kafadata ina kokarin nuna babu komi, "me ke tsakanin mu kuwa Mommy? He's just Daddy's Friend, and I stayed with them for a while I think that's all!" tace "That's all?!" na jinjina mata kai cikin tabbatarwa, "yes!" tayi shiru tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya, "ko ma dai Menene Ummiey, Ina fata zaki tsaya a iya inda Allah ya ajiye ki, and alakarku ta tsaya a haka Nafeesah, No more.... Bana son wani magana ya fita daga baya kina jina??" kallonta nake cike da mamaki, me ke damun Mom ne haka yau? Duk da hakan ban fasa daga mata kai ba, sai lokacin naga tayi murmushi. "good! Hurry up and go to bed then" nan ma Kai na sake gyada mata, "sure Mom, good night" tayi murmushi ta juya ta bar dakin tare da ja min kofa. Sosai maganganun Mom suka tsaya min a rai, ranar haka na kwanta ina nanata maganar ta, 'In tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ni?? Kada wata magana ta sake fita bayan alakar mu ta yanzu? Tana nufin kenan ba zata amshi Abbu a matsayin miji na ba? 'Miji??' naji na sake maimaita kalmar., wa yace Abbu zai zama mijina? Ni kadai nake imagining komi a cikin raina ba tare da tunanin shi Abbu din me yake tunani ba. Ni kadai nake tunanika na na manta da cin amanar da nake shirin yi, to cin amana mana! Na zauna lafiya qalau da iyalan Abbu cikin mutunci da girmamawa, daga karshe kuma kawai sai aji na aure mai gida? Anya na kyautawa kaina dasu kuwa? Me zan ce musu to? Me zasu daukeni, maciya Amana ko me? Su Qaseem.......... Shit!!! Me zasu dauke ni yanzu? Suddenly naji wata irin kunyar kaina ta kama ni, I wasn't thinking straight and smart. Ni da Abbu belongs to different worlds, I think it's time for me to let him go., let my dreams scattered just like how I did with my first love; Muneer!! Zuciyata tayi zafi sosai, m really an unlucky being!! Me yasa ban taba samun nasara akan soyayya ba a rayuwata? I mean me na rasa? I am a very beautiful and attractive young lady in my twenties, ina da kyau ina da diri ina da duk abinda namiji yake bukata a jikin mace but why?? Why???.......

Ramlah ta dawo da hankalina cikin restaurant din ta hanyar jijjiga ni, "hey babe!! Come back to your senses!!" na zabura ina kallonta a tsorace kafin in Harare ta, "What?!" na fada almost shouting, tace "Ke zan tambaya, you were deep in a thought and you suddenly became teary, me ke faruwa dake ne yau?" na kai yatsa na dan taba idanuna, da gaske kuwa I was about to cry ga ruwan hawaye nan ya fara taruwa a idanuna. Ta rungume hannayenta a kirji tana kallona cike da tuhuma, na sauke kaina kasa kawai ina wasa da cokalina a cikin plate, I wasn't ready to discuss the matter with anyone a lokacin, I wanted to dealt with anything on my own don haka na share Ramlah kamar ban san abinda take nufi da hakan ba har sai data kai ga yin magana, "ba zaki magantu bane har sai na matse bakin ki?" na kalleta, "Ramlah am sorry ok? When I'm really, zamu yi maganar please!!" na fada pleadingly don nasan halinta zata iya takura ni, hakan kuwa daidai yake da saka kuka na a cikin restaurant din makarantar mu. Tace "da gaske?" na gyada mata kai, tace "ok, kar ya dade fa kin san bana son jira koh?" na sake gyada mata kai. Na dauki lemun exotic na pineapple na kai bakina, kamar ruwa haka na dinga zugar shi sai kwalin kawai na ajiye kasa. A tare muka mike muka fita daga restaurant din, muna fita naji Ramlah tana xunguri na a bayana, na harareta, baki ta tabe cikin gulma ta rada min "mutumin ki is coming" na kalli inda ta nuna min da idanunta, Muneer ne tafe shi da abokanan shi suna tahowa inda muke da alamu restaurant din zasu zo. Naji ana zancen auren shi da aka daura last week, personally ya turo min Invitation Card na bikin nashi amma a take na aika aka maida mishi Ita don ban ga abinda zan je inyi a wajen bikin ba. Tsaki naja na fara tafiya abina, Ramlah ta biyo bayana, muka yi clashing dasu amma Muneer ko glancing at our side bai yi ba. Na kara jan tsaki a raina nace "banza dan akuya!" satika uku da suka wuce he was still following me around like crazy yana begging dina akan in bashi second chance shine yanzu daga yin aure Sati daya yana share ni irin yaji dadin Amarya dinnan, na kara jan tsaki. As if I give a damn! Kamata yayi inji da damuwata ba wai ta wani Muneer ba. Hostel muka wuce ni da Ramlah saboda bamu da lectures ranar, next week zamu fara exams already mun yi covering lectures dinmu. Muna kan gadonta muna solving din wata problem a Calculus wayar ta tayi kara ta daga, ta dauki wayar ta kalli caller ID din, "Ni'ima ce" ta daga kiran tare da sakata a hands-free, "Guess what guys??" muryar Ni'imah ta doki kunnenmu cikin farinciki, muka hada baki wajen cewa "ya ne? Bamu mu sha please!" tace "umh.... Dama......" ta fara kauce kauce, Ramlah taja tsaki, "malama aiki muke yi idan ba zaki fada ba ki kashe wayar kawai" sai data gama kauce-kaucenta sannan tace "aure aka sa mana.... Nan da one month!!" "WHAT??!" muka fada cikin karaji in Unison.

"What the f**k! Wannan ai rashin mutunci ne Ni'imah" inji Ramlah tana hararar wayar kamar Ni'imar tana gabanta ne, nima nace "Lallai mu da aka raina ne sai yanzu ake fada mana, ba zan zo ba don ma kiji" Ramlah ma ta cafe nan ma muka hau korafe-korafe har sai da muka rasa abin cewa sannan muka yi shiru, Ni'imah dai saurarenmu kawai take yi, ina jiyo dariyar Sa'adiya daga background din wayar. Tace "duka-duka jiya ne aka yi abin fa!" muka yi kus, ta cigaba, "muma bamu yi zaton abun will be so soon ba kawai jin su muka yi Kun gane? Now na isar da sakon da zan isar shikenan, Kun dai san you guys are needed one week before a fara bikin ko?" muka yi dariya ni da Ramlah, "yeah of course, ai dole ne. Thank God we're finishing our exams nan da sati biyu" muka yi sallama dasu, littafin da muke karantawa muka maida gefe muka fara hirar yadda zamu gudanar da bikin, wannan hirar ita ta dauke min tunanina gabadaya akan maganar Mom da sauran su.

*****

Daddy ya kalleni, "yanzu Har Sati daya kawai saboda biki Uwata?" na turo baki gaba, "haba Daddy, su Ni'imah ne fa, kuma lokacin muna free tunda mun gama exams dinmu fa!" ya rausayar da kai, "ai shikenan! Allah ya kaimu" nayi tsalle akan kujera daga zaunen da nake ina clapping hannu, "nagode Daddy! That's why you're always the best!" na mishi thumbs up da duka hannuwana, yayi dariya. Naci gaba da duba littafin hannuna shi kuma ya cigaba da kallon tashar Sports. Can na tambayeshi game da DE form din da yace zai sa a cika min, yace "ni na ma manta wallahi. Bari zan sake yiwa Ibrahim Magana inji yadda ake ciki" nace "Daddy Abbu kuma? Me yasa shi? Ni da ABU nake so in cike?" yace "ba kya son zuwa BUK din ne, me yasa?" na turo baki na, "ni nafi so ina kusa daku Daddy yadda kullum ba zan sha wahalar ganin ku ba!" yayi dariya yace "Uwata kenan! To in kika yi aure kuma fa? Kin san dai dole ki bar gidan nan koh?" na sake turo wani bakin, Mommy ta shigo dakin hannunta dauke da plate wanda aka yanka fruits a ciki. Ta kalleni kafin ta maida kallonta ga Daddy, "Habibty ina fata ba gulma ta kuke yi ba koh?" Daddy yace "mun isa! Diyar ki ce take zancen bata so ta rabu damu" Mommy ta ajiye plate din a tsakiyar dakin duk muka sauka kan carpet tace "Rabuwa kuwa ai ya zama dole tunda dai ke diya mace ce kuma Aure zaki yi" 'Ai fa an tabowa Mommy inda yake mata kaikayi' na fada a cikin raina, kwana biyun nan dama Mommy kamar mai jira, da an danyi magana zata hau zancen aure da waye da waye. Sai da muka cinye fruits din tas na dauke plate din tare da musu sai da safe, na kai plate din kicin kafin na wuce dakina nayi shirin kwanciya barci. Na budo hoton Abbu a cikin gallery dina ina kallo kamar yadda ya zama Al'adar rayuwata kowane dare, na janye idanuna daga kan hoton nashi na maida su kan frame din daya bani. Ban san meye dalilin da yasa ya bani frame din ba, ban san me yasa nake jin wani irin warmness da calmness a tare dani a duk lokacin dana kalli frame din ba. Koma dai menene na yanke shawarar janye Idanuna da Zuciyata daga kan Abbu. We didn't Deserve Each Other.





*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*32*



Harith yayi parking motar shi a kofar gidanmu, da yake ya dawo tun last week. Yau tsokana muka fita, gidan su Ikram budurwar shi muka je da yake itama tazo hutu. Har kofar gidansu muka je aka mata sallama ta fito da saurinta ita ala dole masoyinta yazo, yadda tayi turus ganina akan motar shi ina wasa da keys din motar shi sai daya kusa bata mana budget, kaina na kawar gefe ina boye dariyar data kama ni. Haka ta daure ta karaso wajenmu muka gaisa Harith ya gabatar dani a matsayin sister dinshi, suka dan fara hira da ita, mintuna biyar basu cika ba na kalli Harith ina hamma nace "Hari, mu tafi gida!" da sauri ya mata sallama muka shige mota muka tafi, tana tsaye a inda take har muka bar layin. Dariyar abun muke yi har muka shiga gida kamar wasu sabbin mahaukata. Idanuna suka tsaya cak akan Abbu dake zaune akan fararen kujeru inda Daddy ya saba zama yana shan iska ko karatun jarida mostly on weekends. Kamar koda yaushe, babu abinda ya canza daga bugun da zuciyata take a duk lokacin dana ganshi, rawar da kafafuna suke da wani irin doki daya mamaye ni, makaman yakin dana tanada domin yakar zuciyar dake kayata min Abbu naji sun min nauyin dauka. Idanunshi fes akan mu suke, na kalli Harith a nutse nace "ina xuwa" ya gyada min kai. A hankali na fara tafiya zuwa inda yake zaune, kafafuna rawa suke yi saboda yadda nake jin idanun shi masu kaifi a kaina, da taimakon Allah dai na karasa inda yake. Na dan duka a hankali nace "Abbu barka da yamma" ya gyada kai, "barka dai Nafeesah. Daga ina haka?" na rasa abinda zan ce mishi saboda ba makaranta naje ba saboda ranar bamu yi exams ba, nace "mun dan fita ne" ya kalli kofar da Harith ya bi ya shiga falo ya kara kallona fuskar shi dauke da wani irin kallo daya kada min sassan jiki, "and who is he??" nima na kalli kofar, nasan da Harith yake, nace "Harith...." na rasa abin cewa saboda yadda idanunshi suke zagaye fuskata gabadaya sun dauke min kuzari, ganin nayi shiru babu amsa ya gyada kai, "well dama naso ganin Daddyn ki ne shi yasa na zauna jiran shi nayi zaton zai dawo da wuri don na biya ta ofishin shi baya nan, but bana tunanin zan cigaba da jira kam. Zan kira shi kawai" ya tashi yana gyara wuyan rigar shaddar daya saka, ya kalleni har zuwa lokacin normal kallonshi bai dawo ba, yace "Kano na nufa yanxu in shaa Allah. Nan da sati daya zaki zo bikin su Ni'imah koh?" na gyada mishi kaina a hankali, yace "good! Sai mun hadu kenan" ya fara tattaki xuwa inda ya ajiye motar shi, na samu kaina da take mishi baya har gaban motar. Ya saka makulli ya bude motar ya shiga ya kunna, sai lokacin ya juyo ya kalleni yana dan murmushi, Ya Allah! Da ba dan motar shi dana rike da hannuna ba da babu abinda zai hana ni faduwa a lokacin, na rasa irin effect din da Abbu yake dashi a tare dani. Yace "so??" nayi saurin kallonshi saboda gabadaya hankalina ya dauke daga gare shi, nayi saurin daidaita natsuwata nace "Allah ya sauke ka lafiya Abbu, a gaida su Anty Mubeenah da Hafsy" yayi murmushi wannan karon genuinely wanda tunda yaxo sai lokacin naga murmushin shi irin haka, yace "Ameen Nafeesah, zasu ji in shaa Allah!" yaja motar shi ya tafi nima na wuce cikin gida, a bakin kofa muka ci karo da Harith zai fito, yana gani na yace "sai anjima koh babe?" na harare shi ya danyi dariya saboda yasan na tsani sunan, ya wuce abinshi ni kuma na shige gida. Sai dana biya ta dakin Mommy na gaya mata na dawo, ta kalleni fuskarta babu yabo babu fallasa, "kin ga Baban Hafsat a waje kuwa?" gabana ya dan fadi, Allah dai yasa ba wani fadan zan sha ba. Nace "ehh, ya ma tafi ai" Mommy ta kalleni cikin tuhuma, na sadda kaina kasa ina wasa da jakar hannuna, tace "na tambaye ki abinda ke tsakaninku kin ce babu komi, yanzu kuma me ya kawo shi wajen ki?" na kalleta da sauri, "ni fa ba wajena yazo ba wajen Daddy yazo, ya gaji da jiran dawowar shi ne shi yasa ya tafi" tace "haka ya gaya miki?" nace "ehhh, ba haka bane?" ta dan harare ni na kauda kaina, tace "shi kenan je ki" kamar jira nake yi dama, da sauri na bar mata dakin na wuce nawa ina ajiye numfashi a hankali. Duk yadda Tunanin Abinda Mommy take nufi da Tunanin makomar rayuwata da Abbu suka so dabaibaye ni haka naki basu dama, na dage da karatun exams sosai. Cikin ikon Allah cikin sati daya muka gama exams dinmu, cikin lokacin mun kara zuwa gidan su Ikram sau biyu. Wato idan na tuno diramar da muka buga a zuwanmu na karshe gidansu dariyar dake kama ni koh??

Sai ana washegari a fara harkokin bikin su Ni'imah sannan na tafi Kano. Gidan Anty Ameenah muka sauka directly saboda a can amaren suke zaman biki, su Hafsy suka fito suka min oyoyo yaran sun wani kara girma, ban taba sanin nayi kewar su sosai ba sai dana dora idanuna a kansu. Qaseem ne ya dauki jakar hannuna na kama hannun Hafsy Abdullahi ya biyo mu a baya muka shiga gidan. Tarbar dana samu daga Anty Ameenah ta bani mamaki, har uwar dakinta ta kaini inda na samu su Anty Raliya da wasu abokan su, na gaida su suka amsa Anty Raliya na min korafin na tafi babu sallama ni dai nawa bada hakuri ne kawai don nasan cewa m at fault. Na shiga bandakin ta na watsa ruwa na fito nayi sallar Laasar, kafin in gama har an shirya min abinci a tsakiyar dakin ina gamawa na zauna na fara ci. Sai dana gama sannan aka kaini inda amaren suke. Dakine guda aka ware musu inda ake musu gyaran jiki, ina shiga hayaniya ta barke kamar me. Sai a lokacin aka min kitso da kunshi Allah ma yasa na je wankin kai a Kaduna.
Washegari aka yi kamu a Triple Crown Reception Masha Allah wajen ya tsaru iya tsaruwa, mata ne zallah a wajen mun yi shiga ta gargajiya haka ma kide-kiden da aka sa na gargajiya ne zallah. A wajen kamun ne muka hadu da Anty Mubeenah, tana nan yadda take babu abinda ya ragu a yanda take. Kibar nan tata marar fasali ta karu, table daya suka ja ita da kanwar ta Anty Shakira, ta hakimce tana ta hure-huren hanci yayin da su Anty Ameenah suke ta kai kawo suna kokarin entertaining din baki. Na ja hannun Ramlah muka nufi teburin da suke zaune, tun kafin mu karasa nake yago hakora ina murmushi har muka gaban su na musu sallama tare da gaida su, I didn't expected her to look at me with a smile on her face, tace "Nafeesah sai a haka ake ganin ku ko?" ko babu komi naji dadin yadda tayi, nayi zaton wulakanci zan sha a wajenta kam. Nayi er dariya kawai na zauna a gefen Anty Shakira ina kara gaishe su, nan muka dan yi hirar yaushe gamo kafin na musu sallama na tashi muka cigaba da gudanar da sha'anin bikin mu. Bayan mun koma gida da dare na shiga dakin Anty Ameenah zan dauko kayan barcina da yake tunda naxo kayana suna dakinta, ina yin sallama muryar Abbu ta amsa min, sai dana yi kamar in koma da baya don dai kawai nasan yaji murya ta ne shi yasa. Na shiga cikin falon a hankali kaina a kasa kamar tsohuwar munafuka, daga can gefen shi na durkusa nace "Abbu sannu da zuwa!" muryar shi tayi kasa sosai akwai alamun gajiya sosai a tattare dashi, yace "yauwa Nafeesah, bani ruwa please!" nace toh. Na fita zuwa kicin naje na dauko mishi ruwa mai dan sanyi, har zan fito na kula da farfesun kayan cikin dake cikin warmer, na koma na dauko plate na zuba a ciki na cicciba. Na dire kayan a gaban shi, ya kalleni ya Kalli abincin, fuskar shi ta nuna alamun relaxing and amusement. Ya kalleni cikin lumsassun idanunshi, "Nafeesah!!" ya kira sunana cikin muryar rada, na kalleshi a hankali ba tare dana amsa ba, it's not that ban amsa ba, nayi niyar amsawa sai dai muryata bata fita ne balle har yaji, yace "Nafeesah!! Zaki iya....." maganar shi ta katse lokacin da Anty Ameenah ta shigo falon, na kalleshi da sauri cikin mamakin dalilin tsayawar maganar shi. Anty Ameenah ta zauna a gefen shi cike da tsokana tace "ya aka yi Ibu??" na sadda kaina kasa ina kokarin boye dariyar data taso min da jin sunan da Anty Ameenah ta kira shi dashi, ya dan ja tsaki kawai ya fara cin abinda na ajiye mishi. Ganin haka na tashi na shiga dakin na dauko kayana na fito na musu sai da safe na fita, idanun su suna kaina har na fita. Na kai gadon bayana akan katifar da aka shimfida mana a tsakiyar dakin na kwanta, tunanina a lokacin me Abbu yaso fada min dazu??

Washegari aka yi Walimah anan farfajiyar gidan Anty Ameenah. Washegari kuma aka daura aure da dare muka tafi wajen dinner. Kamar da wasa ina juyawa daga seat din da nake zaune na hango Harith da Ikram a zaune, na zaro idanuna ina kallonsu daidai lokacin da shima ya juyo, na mishi alama da hannuna alamun "ya aka yi haka?" ya danyi shrugging kafadar shi. Wayata tayi kara a daidai lokacin da sauri na daga naga Ramlah ce take kira, na daga da sauri, tace in same ta a parking lot Fiancé dinta zai tafi mu gaisa. Nayi excusing kaina wajen wasu daga cikin abokan su Niimah da muke zaune a seat daya dasu na fita. A can parking lot na same su, muka gaisa da Ayan saurayin Ramlah, (Ban fa ce na Ummu Maryam da Ihsan ba... Don kar kusa Husna tayi daidai da naman jikina, tamm). Anan na baro su su gama sallamar su. A hankali nake tafiya saboda heel din dake kafa ta, gashi dinkin skirt din dake jikina ya dan matse ni somehow don haka bana iya daga kafata sosai inyi tafiya. Kawai ji nayi an ja hannuna anyi gefe dani, na daga baki tun karfina zan kwala ihu, aka sa wani tattausan hannu akan bakin nawa ta yadda babu yadda za ayi ihun da nayi niyar yi ya fita......





[truncated by WhatsApp]
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*33*



"What the....... Harith meye haka?" na fada ina hararan shi, ya sake ni tare da jingina da mota. "ina so ne muyi magana in secret, can idanun mutane yayi yawa shi yasa" nace "shine kuma sai ka tsorata ni?" ya daga kafada, "sorry ok! Ikram tana hango mu fa, muje" muka fito daga wajen da yaja mu muna dan dariya muka tsaya a daidai inda zata dinga hango mu sosai, Harith ya kai hannun shi kamar zai yi cupping din fuskata., "Nafeesah?" Husky voice din Abbu ya sankame ni a wajen, bayan kamar sakan goma na juya a hankali kuma cike da tsoron irin fahimtar da zai mana. Tsaye yake a gefen mu sanye da shadda light brown da hula a kan shi, kallonmu yake daga ni har Harith din cikin alamun tambaya da kuma bacin rai. Take naji jikina yayi sanyi, na kalli Harith da a lokacin hankalinshi ya tafi da Ikram wadda ta juya zuwa cikin hall din kamar tana share hawaye daga karshe ma sai ya bi bayanta. Na kalli Abbu da har lokacin kallona yake yi, idanunshi suna fitar da wani irin tartsatsin abu cike da alamun bacin rai, ya dan matso kusa dani yace "me kike yi anan?" na dan ja baya kadan saboda kusancin dake tsakanin mu kafin in ce "umh, dama na fito ne zamu gaisa da saurayin......" wani irin kallo daya watso min ne yasa nayi shiru jikina ya dauki rawa, me ke damun Abbu ne yau? Na daure na karasa ".... Ramlah kawata" sai lokacin na ga ya dan sassauta muryar shi idan ban yi mistake bama har da sighing yayi softly wanda na lura dashi ta yanayin yadda kirjin shi ya sauka a hankali. Ya katse shirun da muka yi ta hanyar cewa "kin yi kyau sosai yau.... Kodayake kullum ma haka kike" nace "hmmm" kawai saboda gabadaya na rasa abin cewa it's really unlike him. Na sha jin kalmar yabo daga gareshi amma ban taba jin makamanciyar wannan ba don haka naji abun so strange. Yace "zaki koma cikin hall din ne??" na gyada kaina da sauri, yace "k, ni zan koma ne yanzu" na kalli agogon hannuna kafin in kalleshi, "karfe tara ne fa kawai Abbu zaka tafi tun yanzu" yayi er dariya data saka ni shagala da kallonshi, "ban cika halartar ire-iren

Please Login or Register in order to submit comment