Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune?" cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace "wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??" dariya na kwashe da ita nace "wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?" tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, "Ya Allah! He's cool babe, dan dai yana da mata wallahi....!" duka na kai mata ina dariya, "da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya" ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, "sai dai rigar tayi show me da yawa" na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, "to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?" na turo baki kafin na daga kafada sama.

Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai'i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace "amma kinyi kyau sosai Nafee" nayi murmushi sosai har da fari, I'm a sucker for compliments. Yace "naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?" nace "y not?" na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *"Where are you now?"* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace "Abbu..... Gida. Gida zan tafi yanxu" tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan" nace "noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi" ta kalle ni sosai, "to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba" na girgiza kai, "baki san Abbu bane Ramlah..... Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan" na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, "muje koh?" na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace "to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride" yace "Kar ki damu.... Me za a cewa mutumin ne?" na danyi murmushi nace "kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba" yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu'ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, "wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?" jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba" yace "sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?" na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace "waye ya kawo ki yanzun?" nace "Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne" yace "dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?" nayi saurin cewa "ai abokin....." sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, "it's okay!" naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, "goodnight!" ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta.

*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, "For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don't you think it's high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?" tsaki naji taja, "kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??" shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, "hakkina fa kuma Mubeenah?" "ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?" amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace "am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba....!" katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, ".... Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn't give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!" ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace "zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah" cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace "m looking forward to it" daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma'auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka??

Am sorry for the late update, jiya through out a kwance na yini ban jin dadin jikina ne sam. Yau din ma ta maza ce nayi shi yasa wallahi. Just kara hakuri dani pa!

*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*19*

Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.
[09:15, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa'adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace "yah? Baki zuwa ne ke?" na kalli su Ni'ima kafin na kara kallon shi, "can I?" ya tabe baki, "that is idan kina son zuwa fa" na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni'ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni'ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai'i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi "Plss dafa mun shayi mana" nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, "lafiya Nafeesah?" na sadda kaina kasa nace "Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!" shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, "ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??" na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace "kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba" yace "dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka" nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace "tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?" na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace "Abbu nagode sosai, Goodnight!" na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu'ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani.

*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*20*

*Sakon taya murna zuwa ga marubuciya MAIMUNA SANI BELI na lashe gasar HIKAYATA da BBC ta hada na gajerun labarai. Allah ya kara miki kaifin basira*

"I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?" cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace "yes ma'am" tace "bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?" nace "I'm not very sure ma, I'm thinking of filling D E form" tace "ina fata a nan BUK ne?" na girgiza kaina da sauri, "no ma'am, ABU Zaria ne" ta kalleni tana murmushi, "why?" na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace "maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida" ....ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace "am wishing you all the best Nafeesah" nace "thanks ma'am" na fita.
Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, "Soon.....!" na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, "ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?" na yamutsa fuska, "stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai

Please Login or Register in order to submit comment