Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Su Hafsy suna wucewa makaranta na koma dakina na zauna ina kallo.

Tara da rabi ta nuna lokacin dana kalli agogo, nayi mika ina hamma ina jin kasusuwan jikina na amsawa saboda gajiya, ban kai ga kwanciyar da nayi niyar yi ba na jiyo kamar muryar Abbu a falo yana kwala min kira. Na saurara sosai har zuwa lokacin dana sake jin wani kiran kafin na warci hijabi na zura na fita, yana kan dinning a zaune yana kokarin rufe daya daga cikin food flasks din da aka ajiye akai, ya kalleni fuskar shi dauke da wani irin expression dana rasa ko wani iri ne; na jin haushi ne, embarrassment ne ko fusata? Shi dai ya bar wa kanshi sani. Na dan duka a gefenshi nace Abbu gani a sanyaye. Sai da yayi gyaran murya sannan yace "Please samo min noodles ko simple abu da zan ci, am quite hungry" na danyi jim kamar ba zan tashi ba suna da er aiki, yana da matar shi, ba za a ga laifi na ba idan na tashi na fada kicin na dafa mishi abinci? Koda yake ban ga laifin shi ba, abincin da Hareera tayi yau yadda kasan faten shinkafa saboda yadda shinkafar ta cafke, ita kanta Anty Mubeenah sai data mata fada yau dai har da ce mata idan ba zata gyara ba to lallai tana gab da barin gidan don ita ta gaji haka nan.... Abbu ya dan sake gyara murya ya kalle ni, "well??" nayi saurin dawowa cikin hankali na, "umh.... Dama zan ce ne noodles din kadai ta isa?" ya gyada kai, da sauri na tashi na wuce kicin cikin hardewar kafafu, zuciyana na gaya min cewa idanunshi shi a kaina suke. Tukunya na dora akan gas na hada duk abubuwan da nake bukata, ruwan yana tafasa na zuba indomie a ciki na kara da sardines, na dora ruwa a cikin kettle na zuba danyar citta da kanumfari er garlic don naga alamun kamar mura tana dan damun shi. Ina sauke indomie din na soya kwai na dora a sama, na juye shayin a cikin flask na dora duka kayan akan tray mai fadi na fita. Yanzu ya dawo tsakiyar falon ya zauna hannunshi rike da waya yana karatun labarai, na ajiye su a gefenshi na tura indomie din gaban shi da fork a ciki, na dauki kofi na tsiyaya shayin na mika mishi, shayin ya fara kaiwa bakin shi, ya dan yamutse fuska yana kallon shayin jin kamshin tafarnuwa na tashi, da sauri nace "umh... Naga kamar kana mura ne shine....." na kasa karasawa saboda kalmomin sun kare min kuma sai ya girgiza kai kawai ya fara kurbar shayin a hankali. Naje na dauko mishi ruwa da lemu irin wanda naga yana sha masu rangwamen sanyi a cikin fridge na kai na ajiye a gefenshi, "Abbu kana bukatar wani abu kuma?" ya girgiza kanshi, "babu Nafeesah, nagode. Sai da safe koh?" na tashi da sauri na bace a wajen. Duk zaman da nayi jina na dinga yi kamar akan kaya, zuciyana wani irin duka take kamar zata tsaga kirjina ta fito, ban san me yasa Abbu yake da wani irin effect a kaina na saka ni cikin rashin natsuwa ba.

Washegari ba laifi anyi abinci mai sense don mun zauna mun ci sosai, Abbu ya kalle ni yana ajiye spoon din hannunshi, "Nafeesah ko zaki iya dora min shayi irin na jiya?" a hankali na saci kallon Inda Anty take zaune, abincin ta take ci Hankalinta kwance kamar bata san Allah yayi ruwan tsirar mu a wajen ba. Na dan jijjiga kai na tashi, cikin mintunan da basu gaza bakwai ba na gama na juye a cikin flask, na hada da cup na fito falon. A gaban shi na ajiye su, ya kalle ni yana furta thanks! Kafin ya kalli su Hafsy, "oya a tashi a tafi koh? Malam Bala yazo" duk suka mike kowa yana daukar school bag din shi, muka musu sallama muka tafi.

Muna zaune da Ramlah a lab muna hira na kalleta, "babe ya za ayi ne? Ina bukatar wankin kai da kitso fa kaina yayi datti wallahi" tace ba damuwa, idan mun tashi sai mu biya ta saloon din Anty Haleemah, nima ranar Saturday naje aka wanke min" nace "to shikenan". Muna tashi kuwa Allah yasa su Malam Bala sun zo kenan, nace su wuce gida kawai ni Akwai inda zani. Muka je saloon aka wanke min kaina aka min kitso, da yake ba laifi Masha Allah ina da gashi sosai, Mommy irin bakaken fulanin nan ne, na gado zubi da kira irin tasu da kuma yalwar gashi, kalar fatar jikina kuma ta daddy ce, haka dangin shi suke wankan tarwada duk da cewa Akwai farare, kyawawan dara-daran idanu farare tas da bakaken eyelids, dogon dan siririn hanci kamar an zana da biro, dan karamin zagayayyen baki da jerarrun hakora kanana kuma farare tas da er siririyar wushirya a tsakiyar su. Muna gamawa da saloon gidan Anty Haleemah muka wuce, gidan flat ne dan madaidaici mai kyau dakalin ganshi kaga gidan mutum daya. Mijinta navy ne don haka bai cika zama a gidan ba, tare suke zaune da kanwar mijinta Khaleesat, mun dan saba da ita saboda a cikin BUK take karatu, tana yawan zuwa wajen Anti Haleemah din. Danta daya Mahmoud, nan muka wuni a gidan sai bayan Magriba ta hada ni da direba ya maida ni gida, kafin mu isa tuni an kira sallar isha'i. A bakin gate ya ajiye ni, na gaida maigadin gidan na wuce ciki. A hankali na tura kofar falon na shiga baki na dauke sallama, babu kowa a cikin falon. Na maida kofar na rufe na fara tafiya zuwa dakina, kamar daga sama naji maganar, "Where the heck have you been???". A gigice na juya, Abbu ne zaune akan kujera yana kallona kamar a fusace? Cikina ya bada sautin kululu.... It seems like m in trouble.





*♡Jeedderh♡*
[09:11, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*12*


Ya Allah! Cheerful Abbu din dana sani ya tafi, wannan Abbu din ban taba ganin shi ba, a fusace yake sosai kamar wanda zai tashi daga zaunen da yake ya hau ni da bugu, gabadaya jikina ya dauki rawa hawaye suka ciko idanuna, bana son fada ko kadan a rayuwata. Cikin rawar murya irin ta wanda yake so ya fashe da kuka nace, "Naje saloon ne shine na biya gidan su kawata Ramlah" ya galla min harara, "da ixinin wa??" nace "umh, ai na fadawa su Malam Bala da suka zo dauka na dazu", yayi shiru kawai yana kallona. Malam Bala ya fada mishi tun dazun, that means he have no right to be angry at her, but still, he's just pissed up. Dan siririn tsaki yaja ganin har na fara shesshekar kuka, ya shafa tattausar sumar kanshi da a koda yaushe a gyare take tana sheki, "it's okay.... Bani ruwa a fridge" da sauri naje na dauko na kawo mishi, yasa hannu ya amsa fuskar shi har lokacin a murtuke, ganin nayi tsaye naki in tafi yasa ya juyo yana kallona, "what?" he sounds so pissed up at me, da sauri na hau share kwallar data fara xubo min again nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi ba zan kara ba don Allah" ya lumshe idanunshi a hankali, "it's okay Nafeesah, banji dadin abinda kika yi ba, a gidanku kina kai har Magriba a waje?" nayi saurin girgiza kai, "to me yasa a gida na? Saboda kin raina ni ne ko kuma don kin baro gidanku kina tunanin zaki yi duk abinda kike so anan ba tare da an miki fada ba?" nan ma kai na girgiza a hankali nace "tun dazu muka taho, gidan Akwai dan nisa ne daga yau" yace "bana tolerating abubuwan nan Nafeesah kin gane? Daga yau kada ki sake wuce bayan Magriba a waje...... No! Duk inda zaki fita you must tell me first indai kina cikin garin Kano, understand?" nayi saurin jijjiga kaina, yace "you can go now!" kamar wadda take akan kaya, da sauri na wuce dakina. Sallah na fara yi kafin na kira mommy muka gaisa, labarin abinda ya faru na shiga bata, budar bakinta cewa tayi "ai yayi min daidai wallahi, wato har kin fara yawo barkatai ko?" sai lokacin naga wautata dana fada mata, na batan fuska kamar ina gabanta tare da turo baki, "mommy! Saloon fa naje saboda Allah daga can na wuce gidan su Ramlah, Ramlah ce fa kawata ke kanki kin shaida sau nawa take zuwa gidan mu ta kwana?" tace "but still baby, bai kamata ki tafi ba tare da kin fada mishi ba, kin san dole ranshi ya baci dama" na shiga diddira kafata a kasa ina gunaguni, "ni dana sani dama ban fada miki ba tunda ba zaki goyi bayana ba" ta sassauta muryar ta, "Ohh Nafeesah baki fahimta koh? Ba goyon bayan shi nayi ba, it's just the fact. Ke yanzu amanar muce a hannunsu, kina ganin ya dace ya barki ki dinga fita kina dawowa duk lokacin da kika ga dama a garin da yake bakon ki iye? Ko kina ganin girmamawa ce ki kama hanya ki fita ba tare da kin sanar dashi ba? Wani Malam Bala is not an excuse tunda ba a karkashin kulawar shi kike ba kin gane?" na gyada kaina a hankali she's right. Muryar daddy na jiyo ta cikin wayar, "Habibty ke da waye kuke waya kika kyale ni ni kadai a falo?" da sauri na shiga mata magiya akan Kar ta fada mishi hirar da muke don nasan kadan daga cikin aikin Mommy ne, ta ba daddy din muka gaisa. Hira muka shiga yi yawanci ta wajen aikin shi ce, mun jima sosai kafin muka yi sallama dasu. Kayan barci na na zura na bi lafiyar gado ko abinci ban nema ba.

Ina kan sallaya ina lazumi bayan nayi sallar asubahi, ban cika komawa barci ba a irin wadannan lokutan, kofar dakin naji ana kwankwasawa, na tashi naje na bude, Harira ce. Muka gaisa da ita a mutunce tace "dan Allah Nafeesah ko zaki taimake ni da girkin yau? Bana jin dadi ne" nayi fuskar tausayi nace "Eyyah sorry pa! Meye za a dafa?" tace "ki dafa duk abinda kika ga ya dace nace "to shikenan" tace nagode ta wuce dakinta. Daki na koma na dauko karamar hijabi data tsaya a kuguna na saka na fita zuwa kicin, yam delight nayi, kafin dahu sai na dauko fresh kifi a cikin fridge na fara shirin yin farfesun kifi.


(Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe please, da kyar ma na samu na warci lokaci nayi typing dinshi wollah)




*♡Jeedderh♡*
[09:11, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*14*


Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya.


Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe ina kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.

Mijin Anty Ameenah yana dawowa falon ya mana sallama ya tafi, Anty Ameenah ta dan taka mishi kafin ta dawo suka hau hira da Abbu. Mu kam muna zaune muna kallon news don in Abbu yana falo bamu cika kallon tashoshi barkatai ba, motsi kadai zai yi in Allah ya yarda da sannu na yake motsawa, bana ji a rayuwata na taba jin irin wannan feeling na 'protecting' da 'caring' ga kowane Bil'adama irin Abbu ba. Aka kira sallar Azuhur, Anty Ameenah ta umarce mu da mu tashi muje mu yi sallah, duk muka mike, mazan har Abbu suka fita zuwa masallaci ni kuma na tashi zan wuce dakina, Hafsy tana kan kujera tana barci, har na kai tsakiyar falon sai na juya na kalleta, "Anty ko zaki shigo kiyi sallah a daki na?" ta kalleni tana dan murmushi, "Eyyah, hutu nake yi Nafeesah, je ki abinki" a dan kunyace da jin kalamanta na juya. Ina gama sallah na koma falon, ina zama suma su Abbu suka shigo, muka bi Abbu da sannu ni da Anty Ameenah har ya zauna akan kujerar daya tashi. 'yar aikin gidan ta fito da niyar dora abincin rana, bata san abinda yake faruwa a gidan ba, ita dai taga bakuwa ta gaishe ta sannan ta wuce kicin abinta. Muna nan zaune sai ga Anty Rahina ta shigo goye da danta a baya, na tashi da sauri ina mata sannu da zuwa, hannu na mika a bayanta ta sauko min da babyn, na rungume shi tsam a jikina, Ya Allahu!! Ina son yara kamar me!
Anty Rahina ta zauna a gefen Abbu, sannu take jera mishi kamar bakinta zai tsinke na kula suna matukar ji da kanin nan nasu, fuska cike da damuwa take kallonshi, "me ya faru Ibrahim? Garin Yaya??" yayi shiru kawai yana kallonta, to me zai ce??


*_Flashback_*
Yana tsaye a bakin titi a kokarinshi nason yayi crossing ya shiga wani babban shopping mall a garin Lagos kafin su taho ya tuno da ita, haka kawai ya tsinci kanshi da son yi mata tsaraba ko don shima ya faranta ranta yadda itama take faranta mishi ta hanyar yi mishi dadadan girke-girke masu kara lafiya. Don haka ne ya ciro wayar shi ya tura mata da text.
"......yes, In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya....". Reply din data dawo mishi dashi kenan, yayi murmushi sosai, har kullum kulawar yarinyar zuwa gare shi tana matukar burge shi ba kadan, tunanin amsar da zai tura mata yake yi lokacin da aka ba wadanda suke kasa hannu su wuce, taku daya biyu yayi, bai tantance mai ke faruwa ba sai jin shi yayi kwance a kasa rike da kafar shi ta dama, ashe yabi ta wrong way ne, daidai lokacin an ba ababen hawa dake wajen hannu, ba tare da su duka sun kula ba wani mai mashin yabi ta kan kafar shi ya wuce.....!

*********
Yaja numfashi a hankali bayan ya gama tunano abinda ya faru, kallonta yayi yana dan murmushi, "kawai ikon Allah da tsautsayi" ta girgiza kai, "to Allah ya kara kiyayewa" duk muka amsa da Ameeeen. Maigadi yayi sallama ya shigo dauke da manyan kuloli, Malam Bala ya biyo bayan shi rike da wasu, Anty Rahina ta umarce su dasu kai kan dinning su ajiye, suka ajiye suka juya. Ta kalli Abbu, "na dafo maka abinci daga gida, kana jin yunwa ne?" ya gyada kai, ta mike "bari in zubo maka toh" da sauri na mike ina kara rungume Baby Jameel a hannuna, "Anty bari in zubo mishi" tayi murmushi tace to shikenan. Ta koma ta zauna ni kuma na wuce kicin. Harira nata kokarin hada miya, nace "kiyi abincin kadan fa, Anty Rahina ta kawo abinci" tace to shikenan. Na kwashe plates da spoon da zasu isa na koma falo, na zubawa Abbu abincin na kai mishi kafin na koma na zubowa su Anty Ameenah, ni da yara kuma muka hau dinning. Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, na kalli agogo. No wonder! Lokacin cin abinci yayi ai! Ganin su Anty Ameenah a falon sai data danyi turus! Kafin ta karasa, ta zauna akan kujerar dake kusa data Anty Ameenah tana dan murmushin yake, wai "su Yaya Ameenah ne? Ai ban san kuna gidan ba, ina daki ina ta barci" Anty Ameenah ta danyi murmushi, "Allah sarki! Muma mun zo duba mai jiki ne ai" tayi shiru kanta a kasa, Anty Rahina kam bata tanka ba Hankalinta na ga shayar da dan jariri. Ta gama kame-kame dai ta tashi tazo ta zuba abinci ta fara ci, Kai kawai nake girgizawa, rayuwar Auren bayin Allahn nan tana da matukar daure kai. Ita ta fara tashi daga kan dinning din, sai dai wannan karon maimakon ta koma dakinta, kan daya daga cikin kujerun falon ta koma ta zauna. Muma muna gama cin abincin na kwashi kayan da muka bata na kai kicin na sake dawowa falon, Baby Jameel kamar yadda nake kiranshi tunda suka shigo na amsa daga hannun maman shi, yaron ya bude idanunshi farare tas Mashaa Allah dasu yana ta walainiya dasu a tsakiyar falon, Ji nake kamar in lashe shi saboda yadda yake burge ni. Na fara jujjuya shi ina jan kumatun shi ina mishi en wasanni kafin na fara manna mishi kisses a kumatu, Abbu ya maida kanshi jikin kujera ya kwantar idanunshi a lumshe; "What he'll pay to become that baby!!".





*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] ‪+233 50 348 1936‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*14*


Da gudu na karasa wajen shi

Please Login or Register in order to submit comment