Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma idan kina ganin babu damuwa kuma zaki iya, y can't u just tell me?? I'll be a good listener and a judger" tayi shiru tana kallona cikin nuna can I trust you? Na kai daya hannuna na shafa bayan hannunta ina mata murmushi reassuringly, nace “trust me, wallahi u r safe with me... Ki yarda dani".

Numfashi ta ajiye a hankali, “na yarda dake Nafeesah, ke mutum ce ta gari mai hankali da natsuwa. Ina tunanin kila ki tsane ni akan abubuwan da na aikata...!!" tayi shiru tana kallona nima na kalleta ban yi magana ba sai data yi radin kanta kafin taci gaba da magana.

“Kamar yadda nasan cewa kin kula da yanayin zamana da Ibrahim Zama ne kawai muke yi wanda babu armashi ko na kankani. Auran hadi aka mana da Ibrahim ba tare da son mu ba, lokacin ina da wanda nake so. Haka aka kaini gidan Ibrahim ba don naso ba tunda duk yadda naso inyi akan kada ayi auren abin ya faskara. Ibrahim yana kyautata min a matsayin shi na wanda baya so na ma, amma ni na kasa yakar zuciyata akan ta so shi. Ina can ina karewa Mahmud wanda nake so mutuncina wanda kullum sai mun yi waya dashi ya jaddada min in rike mishi amana dai. Duk batanci na duniya babu kalar da ban yiwa Ibrahim akan ya sake ni ba amma yayi biris dani hakan shi yake kara min jin kin shi a raina. It took us almost a year kafin mu kusanci juna, shima ni da kaina naji ina son yin hakan na kai kaina gare shi. Daga nan muka ci gaba da rayuwar ma'aurata amma fa idan naga dama don wani lokacin ko ya neme ni ma sai inyi refusing dinsa, idan kuma ya matsa to sai dai ya biya ni kudin sannan..." tayi shiru hawaye ya zubo mata, yayin da nake jijjiga kai cikin mamaki. Ban taba zaton cewa alakar Abbu da Anty Mubeenah tayi muni irin haka ba, Anty taci gaba...

“Cikin haka na samu cikin Abdullahi, yeah naji dadin samun cikin saboda a lokacin zugar en uwana tayi tasiri akaina da suka ce idan na fara haihuwa a gidan Ibrahim yayana zasu zama magada saboda duk da cewa a lokacin yana karatun masters, amma yana da kudi don bai dogara da kudin mahaifin shi ba, ya dogara da kanshi. Sai dai bayan haihuwar Abdullahi da wata takwas dana kara samun wani cikin mai dan banzan wahala sai naji ina dana sani akan amincewata akan haihuwa. Mun sha danbarwa da Ibrahim akan cikin nan, nayi yunkurin zubar dashi sau ba adadi Allah ya nufa sai da yazo duniya. Wallahi Nafeesah sai da muka tsadance da Ibrahim ya biyani sannan na shayar da jaririn. Watan shi bakwai na yaye shi, babu ruwana da harkar yaran su duka shi yasa zaki ga shakuwar mu dasu bata yi zurfi sosai ba kamar yadda suka shaku da Ibrahim.

Bayan shekaru biyu na sake haihuwar Hafsy, daga nan ne naje asibiti aka saka min loop a mahaifa ta saboda bana son haihuwa da Ibrahim...."

Na zaro idanu waje sosai cikin tsananin mamaki, “loop Anty?" ta gyada kai, “abin ya ba Ibrahim haushi sosai, ya jima yana fushi dani kafin ya sauko ya hau lallashina akan in je a cire min ni kuma nayi biris dani har ya gaji ya daina yace zai karo aure, at first na firgita da jin haka daga karshe da naji shiru sai nayi zaton cewa tsakuwa ce yake taunawa don aya taji tsoro sai kwatsam naji zancen auren shi da ke. In fada miki na firgita ma bata baki ne, na shiga shock bana kadan ba sai dai na cije saboda a gani na bana son Ibrahim meye nawa na jin haushi don zai kara aure? Sai daga baya na fahimci I was wrong! Ina son Ibrahim rashin kulawa irin nawa ne ya hana ni gane hakan, sai daga baya ne bayan ya daga min murya a karo na farko a tarihin rayuwar auren mu, sannan na fahimci halin da zuciyata take ciki game dashi amma ban san ko ta wace hanya zan sanar dashi ba Don haka naja bakina nayi shiru. Amma a en kwanakin nan gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shi kuma kamar ya sani, yanzu ko kiran shi nayi a waya baya dauka ma. Zuciyata tana azabtuwa da hakan ba zan iya cigaba da jurewa ba, amma da wani ido zan kalli Ubangijina bayan abubuwan dana aikatawa mijina? Tell me, bayan duk my man and abubuwan nan dana aikata, da wani ido kike so in kalli Ibrahim??".

Na kalleta tun daga sama har kasa, tabbas ta banbanta da Mubeenar dana sani a da. Wannan Mubeenar ba wadda take cike da self esteem bace, sai wata Mubeenah wadda nadama take nukurkusarta. Tausayinta ya mamaye ni matuka.

Nace “kada ki ce haka Anty, shi Allah Gafurur-Raheem ne, yana yafe kuskuran damu muka aikata a gare shi matukar tuban muke nema da gaske. Abbu ma haka ne, ina tabbatar miki da cewa shi zai fi ma kowa jin dadin canzawar ki Anty" ta kalleni da sauri, “da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi. Tace “to yanzu me kike so inyi?" nace “abu na farko daya kamata kiyi shine kije ki cire loop din jikinki, bayan hana haihuwa yana da side effects a jikinmu ba kadan ba, bana tantama kibar jikinki loop ne ya assasa miki ita" ta gyada kai cikin nuna yarda da abinda nace, “nima nayi tunanin haka. In Allah ya yarda gobe zan koma asibitin a cire min" nayi murmushin jin dadi, “we will do the other things later then... Bari inje in kwanta haka nan" na mata sai da safe na wuce.

Har na kusa kofata naji ta kira sunana, “Nafeesah!" na juya a hankali, “it was not bad opening up to you.." nayi murmushi sosai, “Anytime Anty" na shige dakin tare da rufo kofata na koma kan gado na kwanta. Tunanin yadda muka kare da Anty na dinga yi, na tsinci kaina da addu'ar Allah yasa ta dore a haka, Allah kuma ya bamu zaman lafiyar da a kullum nake mana addu'ah. Da haka barci ya dauke ni cike da mafarkai iri-iri, mafi yawa daga cikin su shine na wani kyakkyawan yaro da yake bina da tuffa a hannu, na tashi da dan murmushi a fuskata. Addu'a nayi na shafa a fuskata na tashi na fada toilet na dauro alwala nazo nayi sallah.

Da yake ranar Anty ta karbi girki, ban fita falo ba sai da karfe tara tayi. Yara sun tafi makaranta, dana tambayi Harira Anty Mubeenah tace tace a fada min ta tafi asibiti, nayi murmushi kawai. Abinci na zauna naci, nayi gefe da plates din a zuciyata ina raya lokacin barin Harira gidan yayi.

Lokacin da Anty ta dawo har dakina ta leko ta same ni, tace “sun rubuta min magunguna in sha na sati daya sai in koma a cire min" nace “to Allah yasa mu dace" tace “ameen."

Daga ranar alakar mu da Anty Mubeenah ta canza, su kansu yaran sun yi mamaki kuma sun ji dadin hakan kada ma dai Abbu yaji labari wanda nake updating din shi da duk abinda ke faruwa. Ni'imah ta sake haihuwar diya Mace, a ranar muka je muka yi barka ni da Anty Mubeenah. A cikin mota muna dawowa nayi shiru ina tunanin anya a duniya zan ma haihu kuwa? Na tuna ina cikin shekarar aure ta uku kenan zuwa hudu amma har yau shiru babu bayani ko batan wata ban taba yi ba. Mommy tace wai itama hakan ce ta faru da ita, sai a cikin shekararta ta biyar ne sannan ta samu cikina, nayi ajiyar numfashi a hankali ina addu'ar idan da rabona Allah ya kawo masu albarka.

Anty Mubeenah taje an cire mata loop din, sai dai ance sabida jimawar abin a jikinta babu wata kulawa irin yadda ya kamata, ya taba mata mahaifa saboda haka da kyar mahaifar ta iya daukar ciki nan gaba. Hankalinta ya tashi kwarai da jin haka ni na dinga kwantar mata da hankali har ta nutsu. Ni na bata shawarar shiga From My Kitchen Institute da yake Allah ya budawa mai makarantar Hadiza Dogon Daji ta bude reshe anan Kano bayan na Abuja, inda ta fara koyon salon girke girke ina kuma taimaka mata da wasu abubuwa. A gefe guda kuma na dora ta akan weight loss da slimming. Kullum muna gym muna aikin motsa jiki. Abbu ya dawo yayi sati daya ya tafi wata seminar inda daya dawo za a bashi VC.

Cikin wata daya kacal idan ba mugun sanin Anty Mubeenah kayi ba idan ka ganta a hanya ba zaka gane ta ba. Wannan kibar marar fasali da rashin gyara duk ya tafi babu shi, ta dawo tayi wani fresh da ita Masha Allah! Duk da dai har yanzu da sauran kibar amma ta ragu sosai. Musamman ta siya form din wata islamiyah anan bayan gidanmu inda take zuwa daukar karatu kowace rana da yamma, karfe hudu zuwa shida. Ko a yanzu kam Alhamdulillah! Zama na da kishiyata ya canza, idan ka ganmu zaka yi zaton cewa wasu shakikai ne ba kishiyoyi ba.

Result dinmu ya fita, sakamako yayi kyau sosai. Nayi clearance da komi, Abbu kadai nake jira ya dawo in nemi izinin shi in fara aiki da Lab din Aminu Kano Teaching Hospital.

Muna zaune akan dinning muna cin abinci, ranar Anty Mubeenah ce mai girki kuma ita ta dafa mana abincin da kanta don tuni muka sallami Harira bayan mun danka mata kudi masu tsoka da zata ja jari dasu, duk da cewa har yanzu dai sai a hankali amma she's improving sosai. Ta kalli plates dinmu, Jollop spaghetti da sauce din hanta, soyayyiyar agada, da coleslaw. Ita kuma nata taliyar ce kadai sai tulin vegetables akai, ta kai spoonful of cabbage bakinta ta taune ta hadiye da kyar, ruwa ta tsiyaya ta kai bakinta. “Nafeesah! This is a torture wallahi! Haba!! Wata na nawa bani da abincin daya wuce kabeji? Gaskiya na gaji haka nan wallahi, I want to eat chicken!!" ta fada da karfi tana watsa hannuwana sama kamar wata yarinya, aikuwa nan muka samu abin dariya, ni da yaran muka kwashe da dariya sosai, ta nuna mu da yatsa “dariya ma kuke yi koh? Just wait nauyina ya dawo 65, idan na fara cin nama a gidan nan..." Qaseem yace “Mommy, Anty Nafeesah tace ko kin kai 65 din sau daya zaki dinga cin nama a sati fa!" ta harare shi, “inji wa? Kai dai ku jira in rage nauyin, babu wanda zai hana ni cin nama" ni dariya ma ta hana ni magana. A haka dai muka gama cin abincin cikin raha, na taya Anty Mubeenah muka kwashe kayan muka kai kicin muka wanke, daga nan na koma daki na kwanta wai in dan runtsa kafin La'asar tayi.

Ihun yara na jiyo a falo suna ga Abbu, haba! Na dira daga kan gadon da sauri na fita. A karamin falo muka ci karo dashi, tsaye a tsakiyar su Hafsy cikin suits bakake da farar shirt, na danne dokin in rungume shi da naji naje gefen shi kawai na zauna ina murmushi. Sai da yaran suka gama murnar su ya basu chocolates da tarkace ya tura su dakinsu sannan ya juyo gare ni.

Nade ni yayi cikin jikin shi cikin tattausar rungumar nan tashi. Nima na mayar mishi da wadda tafi tashi taushi, mun jima a haka muna jin dumin jikin juna kafin na zare jikina daga nashi a hankali, na kalleshi ina dan murmushi, “ya hanya?" ya jingina kan shi da jikin kunya, “it was tiresome but Alhamdulillah tunda na iso lafiya" nayi murmushi “you must be kam... Yakamata ka watsa ruwa koh?" na mike da brief case dinshi a hannuna.

Ya mike shima yana sassauta neck tie din wuyan shi, daidai lokacin Anty Mubeenah ta fito daga dakinta. Sanye take da doguwar rigar Shadda wadda tabi jikinta sosai, now that I look at her very well, tana da diri da halittun jiki Masha Allah. Haka kawai naji wani abu ya makale min a wuya ganin yadda Abbu ya saki baki yana kallonta yayin da take kallon shi cike da so da kewa. Ganin kallon nasu ba mai karewa bane ba yasa na danyi gyaran murya sai lokacin suka dauke idanunshi a kan juna, na danne takaicin daya zo mun wuya nayi dan murmushi tare da cewa “dama wanka wai zai je yayi, amma tunda gaki bari in barku tare, inje in dan kwanta" na mikawa Anty brief case din, ban jira sun ce wani abu ba na shige dakina da sauri na maida kofar na rufe.

Numfashi na dinga ajiyewa da sauri kamar wadda tayi tsere, tabdijam! Idan har haka zan dinga ji idan naga Abbu tare da Anty Mubeenah to akwai matsala, lallai yakamata in san abin yi.

Da dare muka hadu a dinning wajen cin abinci, daga jin taste din abincin nasan cewa Anty really put her best effort don kuwa yayi dadi sosai, duk yadda taso taja Abbu da hira a wajen abun ya faskara har naji ta bani tausayi, sai dai wani sashe na zuciyata na raya min cewa kawai burga ce yake yi, amma a dokance yake da ita, hakan shi yake kara tunzura ni.

Bayan mun ci abincin muka hada kan komi muka kai kicin muka dawo falo, Abbu da yaran shi suna hirarrakin su, sai muka ja kujera ni da Anty Mubeenah muna tamu hirar har wajen karfe tara da rabi, na tashi na musu sai da safe na shige dakina.

Wanka nayi na dauro alwala, anan cikin bayin nayi shafa ina karfafawa kaina gwiwa daga munanan tunanika da zuciyata ke kitsa min, babu abinda ya canza, Abbu yana nan a yadda yake kamar yadda Anty Mubeenah take, nayi dashe a zuciyar Abbu wanda babu wata 'ya macen data isa ta dakusar min dashi, sai dai ta nemi wani gurbin tayi nata dashen, da wannan naji karfin gwiwa ya shige ni. Don haka koda na fito nayi tozali da Abbu akan gado, murmushi nayi naje gefen shi na zauna. Lafiya lau muka yi sallama dashi, na raka shi har bakin kofa ya tafi bayan ya manna min pecks a kumatu da goshina. Na maida kofar na rufe, kan gado naje na kwanta na janyo wayata nayi en dube-dube da chatting har dare yayi kafin na kashe wayar nayi addu'ar kwanciya barci na shafa. Filo na janyo na rungume a kirjina na rufe idanuna, can kasar zuciyata Istigfar na dinga janyowa da hailala saboda korar shaidanin dake saka min abubuwa a cikin raina...

~Lol! Su Malama Hajiya Mubeenah an dawo kan hanya fa! Wa yaji dadin canzawar ta kuwa? Ni dai naji
~N please ina baran addu'o'inku...
#TeamAbnaf
#OneLove





*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA...!*


*©Jeedderh Lawals*

*®Fikrah Writers Association* 🖊🖊



*60 FiNaLe*



Alhamdulillah! Rayuwa mai cike da inganci da zama lafiya muke shimfidawa mu da mijinmu. Mun hade kawunan mu waje guda domin samun kwanciyar hankalin mijinmu. Yes, akwai kishi, sai dai kishin zamani muke shimfidawa ba wai na dabbobi ba, kowa tana iyaka kokarinta wajen ganin ta faranta ran mijinta domin samun ragamar zuciyar shi don haka a takaice dai Abbu ya zama sha lelen mu.

Lokacin Hajji yazo, Abbu ya biya mana kujera mu duka banda Hafsy, muka je muka sauke farali. Bayan mun dawo naje Kaduna nayi kwana daya na dawo muka ci gaba da gudanar da rayuwar mu a nutse.


*****

Kallon shi nake yi idanuna na shekin bacin rai da tashin hankali, “ban gane ba? Kamar ya ba zan yi aiki ba, akan me??” tunda muka dawo daga aikin hajji na dame shi da maganar son fara aikina amma yayi biris dani, sai ranar ne ya bani amsa da cewa ai ba zai barni wae inyi aiki ba, duk wahalar dana sha!.

A nutse ya kalleni cikin sanyin murya mai cike da lallashi yace “to menene abin tada jijiyar wuya kuma? Kin dai san cewa ba tun yau ba nasha fada miki cewa bani son mata na su yi aiki, nafi so su zauna a gida su kula min da gidana da iyalina. Beside Nafeesah baki nemi komi kin rasa ba a gidannan, aikin me kuma zaki je kiyi saboda Allah?"

Na cure baki waje guda ina yamutsa fuska, “to ni nace ne dama saboda kudi zan yi aiki ne? Kawai sabida ina so inyi aikin ne, m bored to death! Baka barina ina fita ina ganin mutane sai abu mai muhimmancin gaske ya taso, baka barina inje gidanmu in musu kwanaki sai dai wuni.... Ni wallahi idan ba so ake yi mutum kadaici ya kashe shi ba a bar shi yayi aiki!"

Kallona yake yi baki a dage cike da mamaki, tun da muka yi aure iyakata da Abbu Nafeesah yi kaza, ince toh., ko kuma Nafeesah ba zaki yi kaza ba ince toh. Amma yau yaga gabadaya na wani canza ne, abinda bai taka kara ya karya ba, maganar aiki ba tun yau ba yayi making it very clear ba zai bar matar shi tayi aiki ba amma gashi ina tonon fada da maganar.

Na kawar da kaina daga kallon da yake min na mamaki, “a’ah! Yo mutum sai yaki fadin gaskiya haka kawai! Idab ma bazan yi aikin ba a dinga barina ina fita mana, amma kullum ni a garkame a gida kamar wata furzuna? Da yake ita er gaban goshi ce naga babu ranar banza da ba zata fita ba amma ko a jikin ka sai ni, me nayi maka ne saboda Allah??" kwalla ta ciko idanuna, da sauri na juya na shige dakina. Kan gado na kwanta ina ajiyar numfashi idanuna a lumshe. Kwana biyun nan zuciyata a wuyana take, kome aka yi da wanda ya kai da wanda bai kai bama jin haushin shi nake yi. Na dan ja siririn tsaki, meye ma na wani sako zancen Anty Mubeenah? Duk da cewa dai abin yana ci mun tuwo ne a kwarya, kun ganta nan kullum tana waje yawo, yawace-yawacen nan nata har lokacin bai ragu ba, karewa ma watarana sai ta fita sannan take fada mishi duk da cewa dai an samu saukin kin fada mishi da bata yi. To ni kuma Fisabilillah kullum ina garkame a gida, idan yara suka tafi school Anty ma ta fita ni kadai ake bari inyi ta gantali a cikin gida, abin ya dame ni sosai.

Ina jin lokacin da aka taba kofa alamun an shigo cikin dakin, bayan juya baya da nayi sai na lumshe idanu na. Ya zauna a gefen gadon da nake kwance, yace “wai Nafeesah me ke faruwa ne? U never go against my words n you never raise ur voice on me, naga maganar aikin nan fa tun ba yau ba na fada miki cewa ba zan iya barin mata ta tayi aiki ba. Mubeenah tana da degree akan computer science ni na hana ta aiki but in return sai na bude mata saloon din can, ba gashi yanzu komi ya zama even ba? I'll do the same to u, Dan Allah kar ki maida maganar nan ta zama babba ranmu ya baci Nafeesah!"

Nayi shiru kawai ina sauraronshi. A en kwanakin nan kwata-kwata zuciyata a wuya na take, abu da wanda ya kai da wanda bai kai ba sai inji raina ya baci, akwai ranar da ina jan jagira hannuna ya kubce ta bata mun fuska, wani irin bacin rai ya ziyarce ni a lokacin, duk abubuwan da suke kan dresser din sai dana yi wurgi dasu suka fado kasa, abin zai baku mamaki da dariya idan kuka ga yanda na tsaya a kansu ina wani huci kamar tsohuwar macijiya, sai daga baya da fushin ya tafi kuma na dawo ina dariya da tu'ajjibi. Akwai kuma ranar da kadan ya hana in mazge Hafsy saboda nayi abinci tace gishiri yayi yawa, bayan a hakikanin gaskiya taste din bakina ya bace nayi ta zabga uban gishiri a cikin abincin ni da kaina dama sai dana yi tunanin haka amma data fada sai naji haushi.

Abbu ya dan tabo ni tare da juyo ni ina fuskantar shi, shiru nayi ina kallon kyakkyawar fuskar shi, ina so in gano laifi ko aibu a cikin abubuwan daya fada amma na kasa. Ban san abinda yasa nake fada dashi akan maganar aikin nan ba, lokacin da nake gida har addu'ah nake yi akan Allah ya kawo min miji wanda zai tsaya min akan komi kamar yadda Daddy yayi wa mommy, gashi yanzu na samu amma kuma na rasa abinda yasa na kasa yarda da hakan, m behaving really strange kwana biyun nan, wasu bakin halaye dana kasa gane su.

“Nafeesah??! Talk to me mana uhm?? Bana so muyi fada akan maganar nan please, kin dai san babu abinda zaki nema a duniyar nan da ba zan kasa miki shi ba, ba zan gazawa hidimomin ki ko kadan ba kin ji? Kuma In shaa Allah ba zan taba bari kiyi dana sanin kin yin wannan aikin ba, ok?" kai na gyada mishi a hankali, yayi murmushi a hankali, “uwww thanks my baby..." ya sadda kanshi saitin fuskana zai yi rewarding dina da kiss, naja wata doguwar shakuwa data sa ya dakata yana kallona, daga haka kuma ba sai kakarin amai ba? Na tashi da gudu na shige bandaki, sai dana amayar da duk abubuwan dana ci a take, Abbu yana tsaye a gefena yana dan bubbuga bayana har na gama aman, ya taimaka min na wanke bakina ya kaini kan gado ya kwantar ya koma toilet din.

Kafin ya fito na dukunkune cikin bargo ina rawar sanyi sosai, hankali tashe ya tarairayo ni jikin shi yana taba wuya na, waya ya dauko ya kira family doctor dinmu, Doctor Salmah. Bayan kamar mintuna arba'in ta iso, lokacin zazzabin ya sauka sai jikina da yayi wani irin sanyi kamar an min duka, kasala duk ta lullube ni. Tayi duk wasu gwaje-gwaje da zata yi, daga karshe dai ta bani wata kwalba tace inje inyi fitsari a ciki, na dafa kafadar Anty Mubeenah muka shiga toilet, ta fita ta bar ni nayi fitsarin ina gamawa ta shigo muka koma dakin, Docta ta amsa kwalbar ni kuma na koma kan gado na kwanta, muka yi zuru-zuru muna kallonta tana saka strip a cikin kwalbar fitsarin.

Bayan kamar minti goma ta dago abin yadda duk zamu gani, bamu fahimci komi ba sai da muka ji tace “mashaa Allah!! Farfesa matar ka na da juna biyu!!" a rikice na kamo hannun Abbu na rirrike kamar zan tsinke mishi shi, ya kamo wuyana ya hada fuskata da tashi waje guda yana furta wasu addu'o'i da ake son mutum ya dinga furta su cikin halin tsananin farin ciki. Anty Mubeenah ta dafa kafadata ko ban fada ba nasan tana murna da abinda taji ne. Docta tayi er dariya ta fara tattara kayanta tana fadawa Abbu bata bincika ko watan nawa ba saboda haka ya kaini asibiti washegari a duba da kuma lafiyata data jaririn yace toh. Nan ta mana sallama ta tafi bayan Abbu ya mata kyautar da bai san adadinta ba don hannu kawai ya saka a cikin aljihun shi ya damko kudi ya mika mata.

Ranar kam naga tattali da kulawa ba daga mijina ba ba daga 'ya'yan mijina da en uwanshi ba, ba daga kishiyata ba ba daga Iyayena ba kada ma dai Daddy yaji labari. A ranar ya kirani shi da Mommy ban ma san wanda ya sanar dasu zancen cikin ba suka taya ni murna da addu'o'i iri-iri Mommy kuma yadda zan kula

Please Login or Register in order to submit comment