Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da scrunching hanci, “anya?? Akwai abinda na koya miki amma har yau kin kasa kwarewa" baki na daga zan yi musu kafin na tuna abinda yake nufi, da sauri na bude murfin motar na fita a kunyace, bayana ya biyo yana “tsaya mana baby" amma ban tsaya ba sai a cikin daki, ya shigo yana er dariya kasa-kasa, baki na turo ina kallonshi, ya tsaya a gefena tare da kamo fuskana ya rike, “fushi kika yi koh? Ai gaskiya na fada ko karya nayi?" na ciza lebena na kasa, “haka kace koh? Ni kuwa sai na baka mamaki" gira ya dage sama alamun yana challenging dina, “oh really? Bring it on then" murmushin mugunta na saki tare da matsawa gaban shi seductively ina kallon fuskar shi, ga kunya ina ji amma I don't want to lose don haka na jefa kunyar a cikin kwandon shara na rufe for the time being, in yaso daga baya na dauko ta sai in wanke...

Bayan kamar awa daya na fito daga bayi ina goge jikakken gashina da towel, yana zaune a gefen gadona yana kallona cikin murmushi. Naja kujera na zauna tare da jona dryer ina kafe gashin kaina, yayi gyaran murya, “I admit" na juya na kalleshi tare da yin murmushi cike da kunya, “na fada maka ai!" yayi er dariya “yes Babe, shi fa dayan?" idanu na zaro sosai, ya daga min gira yana er dariya, wani dan tuntu mai kama da soso na dauka na jefa mishi, ya cafe tare da komawa kan gadon rigingine ya kwanta, na girgiza kai tare da cigaba da goge gashina.

Cikin kwana biyu kuwa na kware sosai, yau da kaina na kai shi gidan Anty Mubeenah da yake ranar girki yake komawa hannunta, bata nan ma lokacin da muka je sai yaran, bayan mun gaisa da Harira na dauki yaran muka je gidan Anty Rahina data sha zazzabi kwana biyu muka duba ta, daga can muka wuce gidan Ni'imah dake ta laulayi, muka karasa gidan Anty Ameenah, a takaice sai da yamma na maida su gida har lokacin kuma Anty Mubeenah bata dawo ba. Na musu sallama na wuce gidana inda na tarda Zainab tana jirana.

**** ****

Bayan sati daya muka koma makaranta, da kaina nake tuka kaina zuwa lectures wata rana kuma Abbu ne yake kaini. Yanxu en class dinmu duk sun san wanda na aura, na share kwanaki kafin su daina tsokana, shakiyanci da taya ni murnar aure, a haka dai muka ci gaba da karatun mu.Yau Abbu zai yi wata tafiya zuwa birnin Ikko taron karawa juna sani, daga wannan taron ne muke fata za a bashi matsayin Professor idan ya dawo. Da yake kwana na ne ranar ni na taya shi hada kayan shi wadanda zai bukata. Tafiyar kwanaki shida ce zai yi. Ni na raka shi har airport, sai da naga tashin jirgin su sannan na koma gida cike da kewar Abbu na, har yau na kasa sabawa da rashin shi a kusa dani.

Kasancewar muna waya dashi, chatting, sometimes ma har video call, shi yasa ban ga tsayin kwanakin da yayi ba, kwanaki shidan na cika kuwa ya dawo, zai karasa kwana daya a gidana kafin ya koma gidan Anty Mubeenah. Na tare shi da murnata da tarin delicious abinci dana hada mishi kafin muka dire a gado inda muka nunawa juna tsananin kewar juna da muka yi. Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah.

*****

Muna gama lectures da misalin karfe biyar na ranar Alhamis, na fito daga class din a dan gajiye na nufi parking lot inda nayi parking Vibe dita, na bude murfin motar kenan zan shiga naji an kira sunana, “Malama Nafeesah??" na juya ina kallon matashin saurayin daya kira sunana cikin mamaki da alamun tambaya, nace “na'am, lafiya??" Wata envelope brown ya miko min, “sako ne?" na kalleshi “sako? Daga wa??" ya girgiza kai, “I was just asked to pass it to you" na jijjiga kai, hannu nasa na amshi envelope din tare da mishi godiya, “ok thanks" yayi nodding kan shi kawai ya juya ya tafi. Na bishi da kallo kafin na gyada kaina kawai na bude motar na shiga tare da mata key bayan na jefa envelope din a bayan motar, ina kokarin yin kwana na juya na dan kalli gefe na na dama kadan kafin na wuce.

Koda na isa gida wanka na fara yi tare da dora abinci naci, Abbu yana gidan Anty Mubeenah Zainab kuma taje gida da yake yanzu na saba da zama ni kadai. Da dare Abbu ya leko ya min sai da safe kafin ya tafi da yake sai washegari ne zai dawo gidana. Yana tafiya na kashe wutar gidan naje na kwanta. Haka kawai envelope din da aka bani ta fado min a rai, na tsinci gabana da faduwa sosai. A raina na raya sai washegari zan duba. Washegari Abbu ya dawo, da yake sai karfe goma nake da class bayan mun karya ya wuce dani makaranta. Da aka tashi sai na biyo adaidaita ya dawo dani gida don shi Abbu ya wuce masallaci.

Zan wuce ta gaban motar idanuna ya sauka a bayan motar na hangi envelope din nan, motar na bude na dauki envelope din na shige cikin gida, abincin rana na daura bayan na gama nayi wanka na kimtsa jikina na zauna jiran Abbu. Out of frustration na jira, na janyo envelope dinnan na bude. Hotuna suka fado daga ciki lokacin dana bude ta, na dauki hoto daya na bude. Abbu ne sanye da kayan dana gane su riga shirt brown mai bakaken lines da wando trouser baki, suna daga cikin kayan dana hada mishi lokacin da zai tafi Lagos. Yana zaune a wani waje kamar na shakatawa suna magana da what? Wata Mace ce amma ta juya bayan ta don haka babu fuska, na dan yamutse fuska tare da bude wani hoton, su dinne dai a waje guda amma a tsaye da alamu zasu tafi, na bude wani, ido na zaro ganin matar nan a jikin Abbuna!! Ya dora hannunshi akan kafadar ta, cikin rawar hannu na bude wani hoton... Da sauri na runtse idona ina jin ana min wani lugude a kirjina, Abbu shi da wata kwance a kan gado babu riga a jikin su, Abbu shi da wata kwance akan gado wata Watsattsiya tana shafa shi da filthy hannuwanta, Abbu na!! Abbu na.... Abbu dai mijina shi da wata akan gado.... Gado dai a kwance wata banzar bazara ta dora filthy mouth dinta akan precious and luscious lips din Abbu na!! Innalillaahi Wa Inna Ilaihi Raji'un..... Na kwala ihu tare da yin watsi da hotunan suka zube a tsakiyar dakin ko wanne yayi nashi wurin, wasu zafafan hawaye suka shiga zubo min a kan kumatuna..., does that mean Abbu has been lying to me?? Haba, biri yayi kama da mutum, sau tari na kan tambayi kaina taya Abbu mutum mai matsananciyar sha'awa yake iya rike kanshi daga matan banza bayan baya samun yadda yake so daga wajen matar shi?? Na yarda dashi, nayi amanna dashi, nayi zaton cewa idanun shi suna ga halalin sa ne, Ashe......!!

Ghen! Ghenn!! Ghennn!!! Toh fa!! Ga wata sabuwa inji en caca!! Me kuke tunanin zai faru da wannan hargitsi da rikici daya danno kai cikin rayuwar Auren su??
Wai shin! Me Nafeesah ya kamata tayi ne yanzu? Please comment so I'll know ur opinions....
Soooo, wattpadians!! Da alamu sakona ya iso gare ku, shi yasa nima na cika alkawari na ture karatun exam din gobe na muku typing, tunda ance kyan alkawari cikawa, so keep it up.... In shaa Allah Friday ok???
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare

*♡Jeedderh♡*
​NI DA ABOKIN BABA NA....!!!​



​©•°jeedderh Lawals°•​


​®°•Fikrah Writers Association•°​🖊🖊



_Soooo guys!! Alhamdulillah na gama exams dina lafiya.. Na gode sosai da addu‘o‘in ku a gare ni. Duk da haka I still have some things to take care of, saboda haka ba lallai ne ku dinga ganin posting dina kullum ba duk da cewa zan dinga iyaka kokari na ganin cewa kun samu posting akai-akai, so with this being said, can we continue??



*56*


Lokacin da aka kira sallar La'asar lokacin ne hankalina ya dawo cikin jikina, na tashi da kyar da bin bango ina jin jiri na shiga toilet nayi alwala na fito nayi sallah, akan abin sallah naci gaba da zama na kurawa hotunan dake watse a tsakiyar dakin idanu gabadaya kwalwata ta kasa nema min mafita akan abinda ya kamata inyi.

Nayi tunanin in jira Abbun ya dawo in kwashi hotunan in watsa mishi a fuska, wata zuciyar tace shake shi zan yi har sai ya gaya min gaskiyar abinda ya faru, wata tace kawai in tashi in bar mishi gidan shi bai kamata in ci gaba da zama da maha'inci ba, tunanika barkatai har ta kai ga bana fahimtar abinda zuciyoyina suke kullawa da warwarewa. Cikin wannan halin na jiyo karar mota alamun dawowar Abbu daga masallaci, na tashi da kyar naje bakin kofa na tsaya ina hangen shi yana fitowa daga cikin mota hannunshi dauke da leda, agogo na duba. Awowi uku da suka wuce ya kamata ace ya dawo gidan, ina ya tsaya? Na samu zuciyata da saka tunanika marasa dadi, ina kallon shi ya taho da waya makale a kunnenshi, at the last step da zai hada shi da kofar falon, wani tunani ya dar su a cikin raina. Abbu na ne fa? Abbu na dai the gentle and good man dana sani ba wani ba, mutumin dana zauna a gidan shi na tsayin watanni shida ba tare daya taba rike yatsan Hannuna idan ba mistake ba, da ace dan iska ne kamar yadda nayi zato anya zai iya kyale ni kuwa bayan da ace yaso ya lalata ni da tuni yayi hakan? Mutumin da ko bayan aurenmu sai daya jira da ixini na da komi kafin ya kusance ni?? Dana kara tuno wasu abubuwan sai na samu kaina da sake kallon hotunan idanuna na hango katon question akan kowannen su zuciyata na tamvaya na anya kuwa babu lauje a cikin nadi??.

Da sauri na koma na hau tattare hotunan na janyo drawer ta gefen gado na watsa su ciki tare da fadawa toilet da sauri na, dole in zauna in sake tunani kafin in yanke hukuncin abinda ya dace inyi, ina rufe kofar bayin naji shigowar Abbu dakin....

Ganin bana dakin yasa ya fita daga dakin tare da maida min kofar dakin ya rufe. Na kurawa kaina idanu a jikin mirror ina kallon reflection dina, kwalliyar da nayi ta hade da ruwa da hawaye ta maida ni kamar zombie. Ruwa da sabulu nasa na wanke fuskana na kara yin wata kwalliyar kafin na fita, akan kujera na gan shi a zaune. Yana ganina ya saki murmushi mai taushi, yayin da naji gabana ya fadi sosai, anya zan iya daurewa kuwa? Don a daidai lokacin zuciyata tana kitsa min in ci kwalar shi ne kawai. Na daure na kakalo murmushi wanda nasan ko fatar bakina bai gama hadewa bama, a sanyaye na karasa kusa dashi na dan duka tare da cewa “Abbu sannu da zuwa" ya amsa yana murmushi, “kin ga na dade koh?" na gyada mishi kai kawai, yace “wai gidan Rahina na biya, shine ta hado ni da kaya ma tace in kawo miki" ya miko min ledar daya shigo da ita na amsa tare da dubawa, turaren wuta ne sai wani kamar na tsuguno idan ban manta ba naga irin shi cikin kayayyakin da aka hado min daga gida. Na maida ledar na rufe tare da kallon shi nace “abinci?" ya lumshe idanu tare da gyada kai, “please, m hungry... Very" da ace zuciyana cikin kwanciyar hankali take da babu abinda zai hana ni kamo fuskar shi in bashi sumba a baki, a yanzu kam koda tunanin ya fado cikin raina I found it disgusting sosai. Sai kawai nayi wajen dinning table ban ko yi magana ba yayin da naji lokacin daya tashi ya biyo bayana.

Abincin na hau zuba mishi, gabadaya cikina a cushe yake nasan sam babu abinda zai shiga cikina a lokacin don haka na zuba mishi iya wanda zai iya ci kawai, ina gamawa na tura mishi su gaban shi na juya da niyar tafiya yayi saurin sa hannu ya riko hannuna, ji nayi kamar garwashi ya taba ni, kallona yayi sosai, “ina zaki je haka? Ba zaki ci abincin bane?" na girgiza kai tare da kallon shi, “naci tun dazu da naga baka dawo ba" ya kara kallona kamar wanda bai yarda da abinda nace ba kafin naga yayi murmushi tare da jan kujerar gefen shi tayi baya ya zaunar dani, “ok, zauna ki taya ni hira toh, kin san cewa dai bana jin dadin cin abinci idan ba kya gefena koh?".

Haka na zauna tare da kurawa kasan carpet din idanu ina ta saka da warwara, ban san lokacin daya gama cin abincin ba, ya juyo dani na fuskance shi, “baby, me ke damun ki ne?" ya fada cikin nuna damuwa da halin da rashin walwalata a gare shi, nima nasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi idan har nace wai zan iya pretending inyi behaving kamar yadda na saba.

Na girgiza kaina kawai, “babu komi Abbu, bana jin dadin jikina ne kawai" da sauri ya dora hannun shi akan goshina yaji babu zafi, ya dawo dashi wuya nan ma komi normal, yace “amma jikin ki lafiya lau... Are you sure ba sai mun je asibiti ba??" nayi saurin gyada kai, “m ok" yace “idan kin ji da wani abu don't hesitate fa, ki sanar dani" na gyada mishi kai, yayi murmushi tare da cewa “good girl" fuskana ya matso daidai tashi tare da kawo bakin shi saitin nawa, ina fahimtar abinda yake shirin yi nayi saurin kauda kaina gefe ta yadda leben shi ya kare da sauka akan kumatuna ba lebe na ba, ya dago ya kalleni cike da alamun tambaya, da sauri na tashi na tattara kayan da yayi amfani dasu na kai kicin. Wanke su nayi tare da dora abincin dare, ya leko kicin din ganin ina girki yazo ya kashe gas din, a hankali na dago na kalleshi amma ban yi magana ba, kafada ya daga cikin alamun tsokana “hey chill! Ba sai kinyi girki ba yau, zan fita in sayo mana abinci" sai kawai na juya na sauke tukunyar dana dora na zubar da ruwan tare da rabawa ta gefen shi na fita.

Ina gaban wardrobe dina ina shirya kayan ciki wadanda na ciro su daga ciki musamman saboda in dauke hankalina daga tunanika, Abbu ya sake shigowa dakin. Gefen gado ya samu ya zauna yayi tagumi tare da zuba min idanu wadanda seriously na dinga jin su a cikin jikina kamar me?? Kokari nake kawai naci gaba da aikina. Can kasan zuciyata ina so in mishi maganar, sai dai ina matukar tsoron abinda xai fito daga bakinshi, ina tsoron ya amsa min da ehh shine don a hakikanin gaskiya ban san ina zan jefa rayuwata idan hakan ta kasance ba.

Haka muka wanzu har aka kira sallar Magrib, Abbu ya tashi ya shiga toilet dina ya fito daure da alwala ya wuce masallaci, sai dana ga fitar shi sannan ne nima na dauro alwalar naxo na tada kabbarar sallah, anan kan sallayar na zauna bayan na gama ina laxumi har aka yi Isha'i nayi sallah. Tashi nayi na nade abin sallar, ina ta en kimtse-kimtse na wanda a zahirin gaskiya basu da amfani ina yi kawai don kada su dauke mun tunani, Abbu ya dawo daga masallaci. Dakin kawai ya leko yace in fita mu ci abinci. Na fita falon na same shi har ya fiddo plates waje, naje gefen shi na zauna kawai.

Gashin nama ya xuba mana cikin plate din da yoghurt a cikin cups, na sa cokali muka fara ci daga cikin kwano daya. Ba wai don wani abu ko yunwa nake cin abincin ba, kawai saboda bana so Abbu ya dame ni da korafi ne don a lokacin ko kadan bana so inyi magana, gabadaya raina a jagule yake. Abu na karshe da nake bukatar yi shine in kadaice a waje guda in nemi mafita a cikin rayuwata data aurena gabadaya.

Duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni jin dadin naman ba har ma ban san lokacin dana bude ciki naci naman sosai ba, sai dana ji cikina ya cika kafin na kora da yogurt din, lokacin Abbu ya ture kwanon gefe alamun ya koshi don haka na tattara kayan na kai kicin, sauran kayan duk na saka su a cikin freezer na fita falo. Abbu yana zaune akan kujera yana kallon labaran kasa, na shige shi zuwa dakinshi da yake yanzu yawancin kayana ma suna dakin don ragewa kaina wahalar je ka dawo daga wannan dakin zuwa wancan. Toilet na shiga nayi brush na fito na shirya cikin kayan barci tare da fesa en turaruka na kwanta. Not that barci nake ji ko kuma gajiya, kawai ina gujewa Abbu ne.

Misalin karfe tara Abbu ya shigo dakin, ina jin alamun shigowar shi na kara lafewa akan gado kamar mai barci. Ina ji ya gama duk abubuwan da zai yi kamar su brush, shafa turare, sa kayan barci da sauran su. Ina jin lokacin daya kashe wutar dakin kafin inji alamun hawan shi kan gadon, na kara sakankance jikina sosai. Ina jin lokacin daya janyo ni jikinsa, duk da ihun da naji ana min a kunne akan in kwace jikina sharewa nayi, bana so inyi abinda zai sa Abbu yayi zaton idanu na biyu. Ina jin shi yana lalubata wanda da da ne tashi zanyi koda barcin nake yi in shige cikin kirjin Abbuna mai fadi, yau kam ban yi hakan ba.

Bayan lokaci mai tsayi naji alamun yayi barci, a hankali na zare jikina daga nashi tare da juya mishi baya, wasu siraran hawaye suna gangaro min a kumatu, ban san yaushe barci ya kwashe ni ba. Da asubahi Abbu ya tashe ni daga barci ya wuce masallaci. Ina kan sallaya ina karatu lokacin daya dawo daga masallacin, kan gado ya hau ya kwanta rigingine, ban motsa daga inda nake ba har sai da gari yayi sha, na rufe al-qur'anin na mayar dashi inda ake ajiye shi na fita daga dakin. Kicin na shiga na fara shirya break fast.

Abbu ya shigo kicin din, ina tsaye ina wanke hanta a jikin sink, ya tsaya a daidai gefena na dama. Kwana daya kacal daga ni har shi mun yi wani zuru-zuru damu, hannu yasa ya kamo habata a kokarin shi nason mu hada ido, sai nayi kasa da nawa idanun na hana shi ganin kwayar idanu na. Muryar shi tayi kasa sosai cike da damuwa yace “hey, me ke faruwa da ke ne Nafeesah?" na kara yin kasa da kaina na kasa magana, ya kara matsowa kusa dani sosai har ina jin saukar numfashin shi a kaina, fuskana ya sake dagawa sama, “talk to me Nafeesah please..... Look at me" yadda yayi maganar kamar wanda yake rokona yasa na daga idanuna na kalli nashi idanun, tsananin damuwa da kulawa dana hanga a cikin idanunshi suka sa ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, sai dana ji dumin su akan kumatuna sannan na ankara...
Abbu ya ida hade er tazarar dake tsakaninmu tare da rungume ni kam a jikinsa, a hamkali ya kai hannu bayana yana shafawa a hankali alamun rarrashi, hakan ya kara karya min xuciya sosai... Na zagaye hannuwana a bayan shi tare da fashewa da kuka ba tare dana shiryawa hakan ba.....
#TeamAbnaf
#OneLove





*♡Jeeedderh♡*
​NI DA ABOKIN BABA NA....!!!​



​©•°jeedderh Lawals°•​


​®°•Fikrah Writers Association•°​🖊🖊


*57*


Bayana yake tapping a hankali ba tare da yayi magana ba, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri ban sani ba bacin rai ne ko tausayi na? Shi dai ya bar wa kan shi sani. Hannu yasa ya kashe gas din dana kunna, yaja hannuna ba musu na bi bayan shi muka fita daga cikin kicin din. Daki ya kaini ya zaunar dani a gefen gado yayin da shi kuma ya zauna a kasa a gabana ina fuskantar shi.

Sai dana gama shesshekar kukan da nake yi da komi, ya tashi yaje kan mirror ya dauko tissue ya miko min, hannu nasa na amsa na goge fuskata dashi. Wajen daya tashi ya koma ya zauna ya kalleni..., “ok, ina sauraronki. Fada min, me ya faru??".

Idanu na kura mishi cikin tunani, shin in gaya mishi ko kuwa in yi shiru? Shin in nuna mishi hotunan ko kuwa zan ci gaba da boyewa ne ina kwarar mu?? Ganin nayi shiru ba tare da nayi magana ba yasa ya kara matsowa gab dani, ya kamo hannuwana ya damke cikin nashi tare da dora su akan cinyata, murya can kasa wadda ta dakushe cike da damuwa yace “Kalle ni Nafeesah!" na dan yi hesitating na en dakikai kafin na daga kai a hankali na kalli kwayar idanun shi, take jikina yayi sanyi sosai, na kasa daurewa kallon tsananin kulawa, so da kauna da suke cikin idanun shi sai na kara yin kasa da kaina.

Yace “Nafeesah, idan ban manta ba na fada miki cewa babu boye sirri a tsakaninmu, ba zamu boyewa junan mu Abu ba komi tsananin munin shi kuwa, amma meye yanzu kike yi? You are hiding something from me Nafeesah, kin saka ni cikin damuwa gashi na rasa gane matsalar balle in magance miki ita, please tell me Nafeesah, tell me me ke damun ki??" rikon da yayi min a hannuna ya kara karfi, ajiyar zuciya na sauke a hankali. That's it! I couldn't do this anymore, kawai bari inji ta bakin shi in yaso komi ta fanjama shi kenan.

Naja numfashi a hankali tare da tashi cikin sanyin jiki bayan na zare hannuna daga cikin nashi, ya juya ya bini da kallo. Drawer din na bude na ciro hotunan cikin faduwar gaba na koma inda yake, sai dana lalubi gefen gado na zauna kafin na mika mishi hotunan, ya kalleni sosai kafin yasa hannu ya karba, na kura mishi idanu sosai ina so in ga yadda zai karbi ganin hotunan..

Idanun shi suka fito waje sosai kamar wadanda zasu fado kasa, nuna su yake yi da hannunshi kamar wani tababbe, da kyar ya iya kakaro sautin “Naffee..sah.... Daga ina??..." cikin rawar murya yana nuna min hotunan, na kura mishi ido ina kokarin karanta kalar tsoro dana gani a cikin idanuwan shi, na tsoron asirin shi ya tonu ne ko kuma na wani abu daban?? Nace “ba kai bane ba koh Abbu??" na kura mishi idanu cikin tsananin tsoron jin amsar da zata fito daga cikin bakin shi. Kai ya girgiza min da sauri, “bani bane ba Nafeesah., I promise you bani bane ba!".

Wani irin sanyi ya xiyarci zuciyana da gangan jikina gabadaya,

Please Login or Register in order to submit comment