Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ran shi wasai babu bacin rai a tattare dashi. Da yamma na lallaso shi da kyar muka je gidan Sadiya muka ga baby don da cewa Yayi wai ya za ayi in fara fita ina amaryar sati daya? Da kyar da jibin goshi ya bar ni bayan na dauki alkawarurruka da dama wadanda sirrin mu ne, daga can muka wuce ya fara koya min mota sai gab da magrib muka koma gida. Kwana biyu da yin haka visar mu ta fita kasashen ketare yawon bude ido (honey moon) ta fita. Da kaina na zauna na fitar da kasashe biyar wadanda nake matukar so da burin ziyarta a rayuwata. Muka fara shirye-shiryen tafiya amma fa bayan anyi sunan Sadiya.

~Daga yanzu ba zaku dinga ganin posting dina akai-akai ba gaskiya, mun koma school kuma things are somehow... Kun dai san lamurran en makaranta ina fata za ayi mun uziri?
#TeamAbnaf
#AnaTare





*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋



*53*


A rana ta uku da haihuwar na kara komawa gidan Sadiya daga can bayan Abbu yaje ya dauke ni da dare muka biya ta can babban gida gidan su Abbun muka gaida iyayen shi, Hajiya Siyama mutuniyar kirki ta amshe mu da hannu bibbiyu har da dan guntun fadanta wai me yasa ya barni na fara fita yanzu? Har tana karawa da cewa wai ai su a zamanin su amarya sai tayi rabin shekara kafarta bata taka kofar gidanta ba., na kama baki a raina na kara da lallai kuwa! Bayan mun gaisa ta saka mana albarka muka wuce sashen Hajja Fati itama muka gaida ta. Nan ta hada ni dasu tarkacen daddawa da sauran su. Mahaifinsu kuwa kwaryar zuma farar saka mai kyau ya bani, daga nan muka juya gida hannu riki-riki da tsaraba.
Ranar sunan kuwa da safe na tafi. Muna ta ayyuka da tsare-tsaren wajen da baki zasu zauna bayan falo. Sai bayan la'asar su Anty Mubeenah suka iso gidan ita da yaranta lokacin muna can bayan gidan muna suyar samosa wadda ake ba baki.
Ni'imah data kai wa su Anty Ameenah wadda muka soya ta dawo, ta daddabo ni tare da rada min “ga fa uwargidan ki can tazo!" naji kamar zuciyata zata faso kirjina saboda bugawar da tayi, ganin yadda nayi kuru-kuru da ido yasa tayi dariya, “haba babe cool mana, sai kace wadda zata cinye naman jikin ki?" nayi murmushin yake kawai.
Ni'imah ba zata gane halin da nake ciki ba, ba wai tsoron Anty Mubeenah nake ji ba, kawai ina fargabar yadda karon mu da ita zai kasance a matsayina na matar Abbu-Mijinta a halin yanzu, nasan ko kallon banza ba zan samu ba wannan karon, fatana daya mu rabu da ita lafiya ba tare da rayuka sun baci ba. Don haka nayi gefe daya da tunanin naci gaba da rolling din da nake yi.
Har inda muke Hafsy ta lalubo ni, nan ta zauna tana ta zuba min labarai har muka gama, aka shiga da wadanda muka yi ciki mu kuma muka shiga BQ muka yi wanka muka gyara jikinmu.
Wata uwar sun shadda muka saka a matsayin ankon suna, dark purple ta sha aikin pink din zare, Ya Allah! Zo kuga yadda na fita a cikin kayan nan. Kyawuna ya fita sosai kamar ka sace ni ka gudu, muka tsaya muka dan karkashe flashes kafin muka koma cikin gida. Bayan dogon hesitating da tunanin zanyi ko ba zan yi ba, daga karshe dai nayi sallama dakin maijego na shiga cikin dakiya duk da cewa zuciya na wani mayen tsere take yi a cikin kirjina.

Ina shiga muka hada idanu da ita kamar wadda take jiran isowa ta, ni da ita muka yi stilling a waje guda, ni na fargabar abinda zai je yazo ni yayin da a nata 6angaren ban san dalili ba.
Ta janye idanunta a kaina, yayin dana daga kafa da kyar na karasa shiga cikin dakin. Gefen gado kusa da maijego na zauna nesa da inda Anty Mubeenar ta zauna ita da kanwar ta Shakirah wadda sai dana zauna na kula da ita a wajen hakan ya kara min fargabata, a tunani na ko taron dangin cin kaniyata suka yi.
Da dan murmushina cike da yake na dubi inda take zaune nace “Anty Mubeenah ina yinin ku?" ta dage kai sama yadda kasan ba da ita nake ba, sai Shakirah ce ta amsa da er fara'arta har da cewa “su amare ne?, Ai naso lekawa har gidan naki mu gaisa Allah bai nufa ba tunda bamu samu zuwa biki ba, Allah ya sanya alkhairi!" na amsa da “Ameen" a hankali kuma a dan kunyace ina satar kallon inda Anty Mubeenah take a zaune koma ince a hakimce, to ta dare kan gado tare wani baje-baje yadda kuka san kan gadonta tana kallon kowa daya bayan daya kamar wasu bayinta ko irin en duniya dinnan da daurin kallabinta ture-ni-kaga-tsiya dinnan wanda ya fito da daddagaggiyar keyar ta gashi duk a cunkushe, sosai matar take bani mamaki. Kamar ta ace tana da saloon guda amma gashinta bashi da maraba da wata Inna ko Goggo a kauye wadda bata san menene ma'anar Relaxer, Shampoo ko Stretcher da stuffs dinnan ba.
Tashi tsaye tayi tana jan hannun Shakira tana magana kamar mai gunaguni, “Malama tashi mu tafi koh?" Shakirar ta maida ta ta zaunar tace “haba ke kuwa, ba mu jima da zuwa ba fa! Bari mu dan jima mana" ta koma ta zauna tana wasu guna-guni, fuskar nan tayi wani sha6ar babu kyawun gani, na kauda kallona daga gun su kafin cibi ya zama kari kuma.
Anty Ameenah ta shigo dakin, “Nafeesah kin ci abinci kuwa?" na dan girgiza mata kai, “A'ah Anty, bana jin yunwa ne" ta dan hade fuska, “a‘ah ban yarda ba, maza-maza tashi ki nemo abinci.... Ko don ma ina zuwa" ta juya ta fita daga dakin.
Tana fita su Hafsy su duka ukun suma suka shigo, dama kai tsaye Hafsy wajena ta taho, su kuma biyun sai da suka matso kusa sannan suka lura dani. Qaseem ne yayi tsallen murna ya karaso wajena shima yayin da Abdullahi yayi gefen mahaifiyar shi. Yaran suka zauna a gefena muka gaisa da Qaseem, na kalli inda Abdullahi yake zaune cikin er tsokana nace “su Abdullahi babu magana ne??" ya kalleni sosai kafin ya dauke fuskar shi ba tare da yayi magana ba. A take na sha jinin jikina, tun ranar da suka je gidana na kula da wasu canje-canje a tare dashi dama kawai ban yi tunanin wani abu bane mai girma amma yanzu kam, na hangi babban lamari a tare da yaron.

Muna nan Anty Ameenah ta dawo dakin hannunta dauke da plate shake da fried rice, coleslaw, da naman kaza a sama ta miko min plate din, na zare ido cike da mamaki na kalleta nace “Anty ina zan kai wannan abincin?" tace “cikin ki mana! Ni anya ma kuwa kina cin abinci yadda yakamata Nafeesah?" na sadda kaina kasa ina dan murmushi kawai. Ta zauna a gefen gado sai a lokacin ta kula dasu Mubeenah a zaune, Shakirah ce ta fara gaida ta, tayi dan murmushi ta amsa ta dauke kanta ga mayar da bakin da suke cikin dakin. Na jijjiga kai a hankali ina kara jinjina halin Mubeenah a cikin raina.
Ni dasu Hafsy muka fara cin abincin, har ga Allah turawa kawai nake yi. Ga rashin jin yunwa, ga tunanin sauyawar dabi'un Abdullahi a gare ni, abin ya daure min kai sosai. Muna cikin cin abincin naga ya tashi ya fita daga cikin dakin, da sauri na tashi na bi bayan shi.
A can bayan gidan wajen wasu shuke-shuke na same shi a zaune, ya kurawa shukokin idanuwa very lost in his thought, sai dana zauna a gefen shi sannan ya kula dani. Yayi saurin dauke kanshi ya sadda shi kasa. Dan murmushi nayi tare da gyara zama na sosai. Muka yi shiru muna kallon shukokin, can nace mishi.,
“Ka tsane ni koh Abdullahi?" da alamun tambayar tawa ta bashi mamaki sosai, da sauri ya dago ya kalleni yana girgiza kai alamun a'ah, sai dana sake ajiyar zuciyar relief a hankali kafin nace “kar ka boye min komi Abdullahi. Nasan cewa dama dole zaku tsane ni, nazo na aure muku mahaifi na zama kishiyar mahaifiyar ku, ko ba haka ba?" nan ma ya girgiza kai da sauri.
Nayi shiru tare da kura mishi idanu, idan ba haka bane ba to menene? Na juya na fuskance shi sosai tare da riko hannayen shi nace “to idan ba haka bane ba Abdullahi menene? Me yasa kake avoiding dina? Last time da kuka zo gidana dama haka kake sakewa kamar ni bakuwar ka ce wadda baka taba gani ba, you hurt my feelings you know... Now, gaya min, ni ce koh?" ya sake girgiza kai, a hankali kamar mai tsoron yin maganar yace “Abbu ne!!".
Na zaro ido cike da mamaki ina kallon shi, “Abbu da kan shi? Me ya maka? Fada min zan mishi magana kaji??" ya kura min idanu kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi maganar da tasa na kusa sakin fitsari a wando saboda tsananin mamaki. “cewa yayi baya son Mommyn mu!!" ya fada muryar shi na dan rawa yayin da idanun shi suka cika da hawaye.
Da gaske gabana ya fadi, duk wata kalma ta bace daga cikin kaina. Cikin sanyin jiki na kura mishi idanu nace “shi Abbu din ne ya fada maka haka da bakinsa?" yayi saurin girgiza kai, “a'ah, Mommy ya fadawa. Ni kuma lokacin naje dakin shi ince ya kai mu gidanki mu yini, shine naji yana gaya mata cewa baya son ta ke yake so!" na dafe saitin zuciyata dake bugawa, ba wai na jin dadin maganar ko fluttering ba, na takaici da wani dan tsillin jin haushin abinda Abbu yayi. A tunani na sai mazajen da basu san inda yake musu ciwo bane suke irin wadannan halaye, ashe ba haka bane.

A lokacin na fahimci cewa wasu iyayen su suke sa ‘ya‘yan su su tsani kishiyoyin iyayen su. Babu yadda za ayi ace a yabi wata ba uwar yaro ba, ko a fifita wata akan uwar yaro bai ji haushin abin ba koda uwar tashi bata da kyawun hali kuwa. Kamar dai abinda yake faruwa yanzu, wanda ba zan taba bari hakan ya faru ba. Mun gina amintacciyar rayuwa ni da yaran, they trust me, suna so na, suna girmama ni, ba zan taba bari hakan ya taba amintar mu ba.
Nace “shi yasa ka tsane ni kenan?" yayi shiru kan shi a kasa, “lokacin da naji labarin zaki auri Dad dinmu, frankly naji haushi. Me yasa muna kallon ki a matsayin yaya a gare mu zaki buge da auren Abbu? Daga baya kuma sai na fara tunanin hakan ai ba laifi bane ba, kuma zamu zama muna tare dake a koda yaushe saboda believe me muna son ki wallahi. Har lokacin da muka zo gidanki ina cikin confusion, daga karshe dai nazo nayi concluding cewa Kaddarar ki ce hakan don haka na kauda tunanin komi a cikin raina nayi niyar rungumar ki da zuciya daya. Saboda haka ne ma nayi niyar sa Abbu ya kaimu gidan ki mu yini in kuma baki hakurin abinda ya faru ranar farko da muka je gidan ki. Sai kuma na kare da jin maganganun dasu Abbun suke yi..., I was afraid! Naji tsoron cewa zaki iya sa wa Abbu ya tsani Mommy ya daina kula ta, muma yazo ya tsane mu ya daina son mu sai ke da baby idan kin haihu..., irin yadda Daddyn su abokina Ameer ya musu lokacin daya kara aure!".
Na fahimci irin tsoro da fargabar da yake ciki, na matsa tare da kamo hannun shi sosai. Nace “look Abdul, ni ba irin matar Baban su Ameer abokin ka bace kaji? Ba zan taba bari wani abun cutarwa yazo kusa da ku ba balle in cuce ku da kaina. Sannan Abbun ku yana son Mommyn ka kaji?" yaron ya kalleni sosai with so much hope in his eyes sai da naji kamar zan yi kuka. Fuskar shi ta washe da murmushi, “da gaske Anty Nafeesah?" na daga mishi kai da sauri, “sosai ma. Yafi son ta akai na ma. Kawai ranar ai ya fada min, yana so ne yaga abinda zata yi ne shi yasa yace haka. Wasa yake mata!!" na karasa maganar cikin cije baki.
Yayi ajiyar zuciya, “har naji dadi wallahi, da har na fara ji Abbu ya fara bani haushi!" da sauri nace mishi “kul! Kar ka sake maimaita irin haka kaji Abdul? Ko me iyayen mu suka mana bamu da damar jin haushin su a cikin ranmu kana jin mu? Duk abinda zasu yi suna da dalili don haka mu dinga musu uziri ka gane?" ya gyada kai cikin fahimta, “na gane. Nagode sosai Anty Nafeesah! Kiyi hakuri kuma" na shafa tattausar tattaurar sumar kanshi ina murmushi, “are we good now?" shima ya gyada kai yana murumushi. Nace “zo mu koma cikin gida kaga yamma tayi kila su Mommyn ka suna neman ka. Kada fa ka sanya damuwar komi a cikin ranka kaji?" ya gyada kai. Naja hannun shi muka tafi.
Aikuwa su Anty Mubeenah na waje suna neman shi, ganin mu tare fuskar ta ta danyi frowning da ban san ko na menene ba. Na daure duk da sanyin da gwiwa ta tayi muka karasa har gaban motar su, wanda kafin muje sun shige ciki, Abdullahi ya bude baya ya shiga na leka ta jikin taga ina musu Allah ya kiyaye hanya, Anty Shakira da yaran suka amsa cikin fara'ah yayin da mai gayya Mubeenah ta dauke kai gefe, ni dama nasan za a rina. Suka ja motar suka tafi, na sauke ajiyar zuciya a hankali na juya zuwa cikin gidan, lokacin an fara kiran Sallar Magriba.

Bayan Isha'i Abbu yazo ya dauke ni, na wa su Anty Ameenah sallama na tafi suna ta min godiyar hidimata a gare su, daga ta gangar jikina har ta jakata. Na bude murfin motar gefen mai zaman banza na zauna, Abbu ya kalleni da murmushi a fuskar shi. “ya ne baby?" na kakaro murmushin yake kawai, yayi zaton gajiya ce don haka ya tashi motar muka tafi.
Muna zuwa gidan na dafa mishi jollop din Spaghetti, ban zauna ci ba don cikina a cike yake already. Daki na shiga na watsa ruwa, na dauro alwala na yi sallar Isha'i tare da yin Shafa'i da Wutiri. Yan shafe-shafe nayi tare da zura kayan barci. Wando iya gwiwa da riga mai budadden wuya, har yau ban warke daga cuta ta ta jin suffocation idan na kwanta da riga ba, saukin dana samu shine Abbu baya ma bari na na kwana da riga, idan ya tafi gidan Anty Mubeenah ne nake amfani da riguna irin wadannan saboda ina sakewa a cikin su.
Nayi sallama a nutse na tura kofar dakin, yana kan sallaya yana Nafilfilin shi na duk dare daya saba yi. Na wuce kan gado tare da kwanciya na juya baya daga inda yake sallar na kalli bango zuciyana cike da sake-sake, ina so inyi mishi maganar ina kuma tsoron abinda zai auku ko yaje ya dawo, amma a ganina yin maganar kamar ya zama dole ne.
Ina jin lokacin daya gama sallar ya wuce gaban dresser yayi shafe-shafe da feshe-feshen turaruka kafin ya kashe wutar dakin. Ya hawo kan gadon ya kwanta a bayana tare da janyo ni jikinsa, hannunsa ya fara laluba na yayin daya kai bakinsa gadon bayana yana manna short short kisses zuwa bayan wuyana, kafin in lalubo hanyar yin protesting ya san yadda yayi ya batar min da hankali, da sauri na juya na sarkafe hannuwana a wuyan shi tare da sakar mishi jikina gabadaya, ina nufin mallaka mishi....

Yayi rigingine akan gado yana ajiyar numfashi, kaina yana kan kirjinshi yana shafa gashin kaina a hankali. “as usual, that was amazing baby, I love You!" ya fada tare da kissing din kaina. Ire-iren kalaman shi kenan a yawancin dararen ko ince lokutan da duk muka kasance tare dashi. Duk yadda naso kar inji dadin kalmar hakan bai yiwu ba, naji zakin ta tamkar zuma. Na kara shigewa cikin jikinshi tare da dora lebbana a tsakiyar kirjinshi na sakanni da basu fi biyar ba na kara maida kaina na kwantar a kirjin shi.
Wucewar mintuna masu dama, mun yi shiru ne kawai babu wanda yayi magana. Wata masaniya ta taba bani shawarar cewa lokuta irin wadannan wato lokutan bayan gama Auratayya, lokuta ne da suke kawo fahimtar juna da kara sa shakuwa a tsakanin ma'aurata, I tried, n it really works. Wani lokaci mu kan tattauna game da feature dinmu, rayuwar mu, idan ma da matsala sai mu tattauna akan ta mu warware ta. Na jefa mishi tambayar “me yasa kake so na Abbu?" maganar taje mishi a bazata saboda shirun da yayi na dan lokaci kafin yace “I don't really know, amma kyawawan halayen ki, kulawar ki a gare ni da tausasawar ki ina ji sune jigon abubuwan da suka ja ra ayina game da ke" nayi dan murmushi kawai, “I am sorry to say, but idan zaka rike son da kake min a cikin zuciyar ka zan fi son hakan" yayi shiru na dan lokaci kafin yace “saboda me?" nayi shrugging, “ina so in samu farin ciki mai dorewa da kai Abbu, ina so in rayu da iyalan ka cikin aminci da lumana da yarda da juna, idan kana fadawa kishiyata kana so na a gabanta me kake tunani hakan zai jawo min??" tashi zaune yayi sosai, nima na zauna tare da jan bargo na rufe jikina.
“me kike nufi? Kun hadu da Mubeenah a wajen suna ko? Me ta fada miki? Tana kokarin ta raba ni da wadda take so na ko? That..." nayi saurin katse shi, “ba ita bace, yes mun hadu da ita amma ko kalma daya bata hada mu da ita ba" ya kalleni sosai, “idan ba Mubeenah ba a wajen wa kika ji maganar?" nace “kayi hakuri, amma ba zan iya fada maka ba" ya kalleni, “daya daga cikin yaran ne koh?" shirun da nayi ne yasa ya gaskata zarginshi, hannu ya kai yana yamutsa sumar kan shi, “God!! Abinda nake jin tsoro kenan".
Na kara matsawa kusa dashi, “saboda haka ne nake so plssss ka daure, kada kayi sanadin da zai sa yaran su tsane mu daga ni har kai. Kaga hakan ba zai mana dadi ba" muryar shi cike da bacin rai “no way! Ita bata so na sai kuma ta hana ni son wanda yake so na??" nace “babu wanda ya hana ka son abinda ke son ka Abbu, amma kaje kana ihun kana son kishiyarta a gabanta da yayanta, hakan babu kyau. Zai jawo consequences masu dama wanda hakan ba zai mana dadi ba" ya dan girgiza kai, “I was angry!" nace “shi yasa Annabin mu SAW ya umarce mu da yin shiru idan muna cikin fushi, you should've just keep quite ko ka bar inda take lokacin da ranka ya fara baci. Ni dai don Allah kada ka sake yin hakan kaji Abbuna??!" na fada cikin sanyin murya mai dauke da roko, ya kura min idanu cikin duhun dakin kafin ya sake ajiyar zuciya., “naji! Na fahimta, hakan ba zai sake faruwa ba. Na gode, Allah ya miki albarka!" matsawa kusa dashi nayi na dare kan cinyar shi na kamo fuskar shi na rike cikin hannuna, “har kullum fahimtar ka a gare ni da saukin kan ka su suke kara saka min natsuwa da jin dadi Abbu na, Allah ya barmu tare ya kara mana son juna" yayi murmushi, “if you are that happy then show me!" ba bata lokaci na hade bakina da nashi. Kafin wani lokaci na tsinci kaina a karkashin shi, “you up to another round??!" ya fada hoarsely idanunshi na sheki da farin ciki da sha'awa, na daga baki zan bashi amsa but instead na buge da furta “Abbu....!!".

Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah, Zaynab ta dawo da yake idan ya tafi can ne take zuwa, ranar da zai dawo kuma sai ta koma gida. Naje gidan su Anty Ameenah na musu sallama har can babban gida sai da naje, ranar daya dawo gidana da dare jirginmu ya daga zuwa Las Vegas, Paris.

~Hii! Nasan kwana biyu zaku ce shiru babu labari na, kamar yadda na fada muku karatu ne ya sako ni gaba. On that note, nake so na baku hakuri saboda zaku ji ni shiru diff na wasu lokuta saboda exams da zan fara ranar wannan litinin din. But kar ku damu shaa, In shaa Allah ba zata dauke mu lokaci mai tsayi ba. Don haka ina baran addu'ah daga gare ku, In shaa Allah idan na dawo zamu daura ba tare da bata lokaci ba!. This January In Shaa Allah!!
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare





*♡Jeedderh♡*
h*NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋

In Dedication to *Beloved Anti Zee*



*54*


Cikin tsakiyar dare muka isa birnin Las Vegas, already mota daga hotel din da Abbu ya kama mana tana jiran mu a airport din, muka zuba abubuwan da muka taho dasu

Please Login or Register in order to submit comment