Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.πŸ₯°



*Alhamdulillah*
7/22/21, 12:08 AM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*7*


Tana shiga cikin sauri ta ciro kwalin wayar daga ledar, saida ta daka tsalle ta rumgume Asma'u tana murna ganin IPhone duk da k'aramar tashi ce, amma dai taji dad'i sosai da ganin wayar, Asma'u kam mamaki ne ya hanata magana sai kallonsu suna ta murna har da yin zaune tasa Salma turo mata abubuwa da dama har da hotunan data d'auka yanzu, suna idawa a gaggauce sukayi sallama da cewa sai sun zo ranar da za'a kawo kayanta, suna fita suka samu taxi ta nufi dasu unguwar yayar Asma'u.

Ko da suka je gidan basu wani jima sosai ba sai sak'on da Asma'u ta bawa yayar ta ta wanda uwar ta bata ta kawo sanda ta ji zasu taho, 05:50 suka baro gidan suka shiga takawa a k'afa dan isa bakin titi, dama idan aka kawoka ne kake samun mai kai ka har k'ofar gida, amma idan ba haka ba masu taxi basu cika kai kawo a layin ba.

Cikin fad'a Asma'u ta kalleta tace "Gaskiya Mimi kina ban haushi wasu lokutan, wai ke ba kya tsoron abin da zai je ya dawo ne?"

Yatsina fuska tayi tana d'an goge zufar data tsatsafo mata a hanci, kallonta tayi tace "Ba ma zaki kulani ba ko?"

Kallonta tayi ta sake yatsina mata baki tare da d'an mata gwalo ta sake d'auke kanta, jinjina kai tayi tace "Ba komai ki ci gaba, Allah na gani nayi iya k'ok'ari a kan ki Mimi, bana so k'awance na da ke ya zama irin k'awance da aka ambata ranar lahira mu had'u ni da ke muna zagin junanmu, ko kuma na rok'i da ki haska min gabana dan na tsallake sirad'i ko ke ki rok'i hakan, na fi so mu wuce a tare cikin aminci."

Wata bak'ar Prado ce ta sha gabansu ta tsaya wanda dole su ma suka tsaya cak, da sauri Asma'u ta rik'e hannun Mimi tana fad'in "Shikenan, Allah ya taimaku yasa ba cikin samarinki bane wani zai sace mu."

Kallonta Mimi tayi, saidai kafin tayi magana Ashraf ya zuro farar k'ararshi mai d'auke da takalmi k'afa ciki irin na matasan da suka san kansu wayayyu yan zamani k'irar polo, kafin suyi wani yunk'uri ya gama fitowa gaba d'ayanshi ya tura murfi da k'arfi ya rufe, a sanyaye ya shiga takowa gabansu yana cire bak'in glass d'in fuskarshi, gabanta ya tsaya cak yana mai k'arewa duk ilahirin jikinta kallo, faffad'an bakinshi mai d'auke da tsararun hak'ora ya bud'e ya nunota da yatsa kamar zai tsokale mata ido yace "Ke wacece da zaki wuce ta nan baki gaishe dani ba?"

Mimi da tun fitowarshi ta saki baki tana kallonshi, a take ta tambayi " *Wanene wannan*? Yaushe ya zo garin nan?"

Dan kam ita daga tsarinshi zuwa fatarshi da gyaran kanshi ya bayyana mata ba mai jin yaren hausa, zabarmanci, barbarci, tubanci, fulatanci ko buzanci bane, tunda take bata tab'a jin namiji ya birgeta a kallonshi ba sai yau, hasalima samarinta kallo d'aya take musu bata sake sha'awar kallonsu. Amma wannan sai take jin zata iya zaunawa tayi ta kallonshi ba zata k'osa ba ita kam. Sanda ya shiga nuna ta da yatsan nan a karo na farko a rayuwarta da taji a ranta zata shanye wulak'anci ta kuma had'e, dan wannan ba guy da zata ma rashin kunya bane, yanayinshi ma ya nuna mata zai iya tsinka mata mari, babbar asarar da zatayi kuwa bata wuce su rabu ba tare da yace yana son ta ba, dan gaskiya ita duk ajin shi da yanda ya birgeta ba zata tab'a sauko da k'anta k'asa tace tana son shi ba, ina! Ba zata iya ba, gwara idan sun rabu tayi takaicin rasashi a gaba kuma zata samu wani kamarshi ko wanda ya fi shi.

K'yasta yatsunshi yayi daf da fuskarta hakan ya sakata lumshe idonta da suka fara kawo ruwa sabida jimawa tana kallon abu d'aya, daidaita nutsuwarta tayi ta saka idonta a na shi sosai, hakan ya bashi damar sakar mata murmushi yace "Wasa nake miki, kin tsorata ne?"

Tarrr ta masa tana kallo inda a hankali ta shiga canza yanayin fuskarta daga shagala da mamaki har ta d'aure fuskar, kallo ne ta shiga yi masa irin na zuru d'in nan cikin jin haushi. D'an kallon Asma'u yayi da ita tayi galala take kallonshi yace mata "K'awarki bata magana ne?"

Da sauri ta zabura tace "Tana yi mana."

Kallon Mimi tayi ta sake jimk'e hannunta gam tana d'an motsa bakinta, a hankali ta sadda dubanta tayi k'asa da idonta tana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi mai sauti yace "Masha'Allah, dan Allah ya sunanki?"

Da sauri ta sake d'agowa ta kalleshi, dan Allah ya sunanki? Kamar wata 'yar talla ko kayan miya? Sama da k'asa ta harareshi tare da kaucewa ta rab'ashi zata wuce, da sauri ya sake tare gabanta yace "Dan Allah ki saurareni, ko na biyo bayanku ne har na ga gidanku?"

Asma'u ce tayi saurin cewa "A'a dan Allah ka rufa mana asiri, zaka sa a mana fad'a a gida."

Kallon Asma'u yayi yace "To in hakane ki sa k'awarki ta min magana mana."

Cike da tausayin kan ta ta sake kallon Mimi, numfashi kawai ta sauke dan bata ga abinda zaisa tayi maganar ba idan ba niyya tayi ba, sake matsowa yayi kusanta yana fad'in "Dan Allahana 'yan mata, ki taimaka ki fad'a min sunanki da unguwarku, nasan bai kamata na tsareku a kan hanya ba, amma babu yanda zan yi ne, ina ganinki naji zuciyata ta doka da k'arfi ta yanda ba zan juri ki sub'uce min ba."

Kallon Asma'u tayi ta mata alama da ido mu tafi, zata taka k'afarta yace "Ki fad'a min abinda zanyi mana da zai sa ki min magana, dan Allah kada ki bari ki kubce min *Naana*."

Kallon juna sukayi ido cikin ido, da sauri ta d'auke na ta saboda marayan kallon da yake mata, a marairaice yace "Ko sai na duk'a har k'asa ne?"

K'asa ta k'urawa ido ba tace komai ba, a hankali ya nemi zemewa ya durk'usa k'asa yana fad'in "Wannan ba kom..."

Ba ta barshi ya k'arasa ba tayi saurin kallonshi tare da fad'in "Maryam."

Da mamaki Asma'u ta kalleta jin ta fad'i cikakken sunanta yau ga saurayi, a iya saninta saidai ta fad'a maka Mimi amma ba zaka ji Maryam a bakinta ba. Mik'ewa yayi yana sakin murmushi tare da fad'in "Alhamdulillah, *Mimi*, suna mai dad'i."

D'an kumburo bakin da tayi yasa shi yin murmushi yace "Kina da aji, hakan kuma ya tabbatar min da na samu matar aure, fatana Rabbi ya dafa min kar ki k'i kulani a matsayin wanda zakiyi soyayya da shi ma bare aure."

Hannu yasa aljihu ya jawo tartsetsiyar wayarshi ya mik'o mata yana fad'in "Zan iya samun agajinki ta hanyar rattab'a min lambobin da zasu sadani da inda kike?"

Wani wallll! Tayi da ido tare da k'ura mishi ido, kunnenshi d'aya ya kama alamar ban hak'uri, fari tayi da ido hakan ya k'ara narkar dashi tare da fad'in "Ko na sake zubewa k'asa ne?"

Har yayi haramar zubewa k'asa tayi saurin fizgo wayar ta shiga saka mishi lambarta, mik'a mishi wayar tayi a hannu suna kallonshi ya saka suna kafin ya kalleta ya sumbaci wayar, irin kallon firgitarwar nan ta bishi da shi, shi kam murmushi yayi yace "Yanzu musaya ta fara shiga tsakanina da ke, a sannu sannu wata rana zamu gauraya mu zama babban iyali da zai tsiro da kyakyawa kuma hazik'an yara."

Kallon mamaki ta mishi shi kuma ko a jikinshi, saima rusunawa da yayi yace "Dan Allah zan iya saukeku inda zaku je?"

Asma'u ce ta girgiza kai tace "A'a gaskiya, an hanamu."

Kallonta yayi sannan ya kalli Mimi, cikin taushin murya yace "Hakan ne a ranki kema? Ba zaki shiga ba?"

A hankali ta lumshe idonta wanda suka sha mascara suka yi tsayi sosai alamar eh, jinjina kai yayi yana jinjina al'amarin wannan mai kama da jinin sarautar, idan da za'a barshi da hasashenshi sai yace 'yar k'usa ce a gwamnati sun samu matsalar abun hawa ne, dan duk da baya da sani akan suturar mata yasan kayan dake jikinta ba masu arha bane, ko da akwai mai arha to sai dai ko 'yan kunnenta dake k'anana sosai mak'ale a kunnen. Saidai a wajenshi kam ko ta kasance 'yar babba ko ta kasance 'yar takala wannan bai dameshi ba, tunda ya karyo kwana idonshi suka sauka a kanta ya ji zuciyarshi ta fizga a guje ta rakito duk wani abu daya shafeta ta killace da jin cewa zata dage a kan ta ko ma wacece ita.

Saida ya kalli k'wayar idonta ya daidaita gilashinshi da kyau ya manna mata shi a fuskarta, hakan kuma ba k'aramin kyau ya k'ara mata ba. Dariya yayi data fito da kyawunshi da kyau yace "Sai na kiraki, Mimi."

Da kallo ta rakashi sai Asma'u da tace "Dama kasan inkiyarta ce Mimi?"

Juyowa yayi yana shafa tarin sumar kanshi yace "Ban sani ba, amma duk mai sunan Maryam ina kiranta da Mimi, saboda sunan *mahaifiyata* ne."

A tare suka saki murmushi ita da Asma'u, haka kawai ta ji abinda ya fad'a ya sata nishad'i, da kallo suka bishi har ya shiga motar ya barsu nan tsaye. Kallonta Asma'u tayi sai taga har yanzu idonta na kan shi, da sauri cikin jin haushi ta cire gilashin daya saka mata tana fad'in "Malama ya tafi to sai ki kama bakin."

Da sauri Mimi ta kalleta sai kuma taja tsaki tare da k'watar gilashin ta saki murmushi ta kalleta tace "Dan Allah mutumin nan bai birgeki ba?"

Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an, tunda saurayinki ne."

Cike da damuwa tace "Ke ba haka nake nufi ba, ina nufin tsarinshi, kalamanshi, kyawunshi da kuma yanda ya iya shiga zuciya lokaci d'aya."

Galala Asma'u ta kalleta tace "To fa, da alama wannan kam shi ne *zakaran* da ya zubar da 'yan maza warwas a wajen Mimi."

Kallon gilashin hannunta tayi ta sake mayar dashi ga fuskarta ta kalli Asma'u ta d'aga mata gira tace "Ya kika gani dan Allah? Ya min kyau?"

D'aga mata gira tayi ita ma tace "Kinyi kyau kam sosai."

Hannunta ta kama cike da jin dad'i suka fara tafiya tana fad'in "Asma'u a rayuwata ban tab'a tunanin zan had'u da irin wannan namijin ba?"

Da mamaki ta kalleta tace "Me yasa? Naga ai burinki kenan samun irin wannan namiji."

Saida ta saki hannunta tace "Hakane, amma ni ban tab'a tunanin zan samu kyakyawa haka ba ai, to wai wanene shi?"

Ta fad'a tana kallon Asma'u, tab'e baki tayi ta d'aga kafad'a tace "Ina zan sani, sai ki bari idan ya kiraki ki tambayeshi."

Wani murmushi ta saki tare da d'agawa wani d'an taxi hannu tana fad'in "Ba ni zan tambayeshi ba, shi ne zai fad'a min."

K'ala Asma'u ba tace ba har suka k'arasa kusa da mai taxi, saida ta kalleta tace "Gida muka nufa yanzu ko kuma dai kina da sauran gurin zuwa ne?"

Murmushi ta mata tace "Gida zamu koma mana ke ma, magriba ta kusa ai."

Girgiza kai tayi ta kalli mai taxin tace "Tallague."

Jinjina kai yayi alamar su shiga, bud'ewa sukayi suka shiga inda ya jasu, wayar ta ciro a jakarta ta shiga saitata zuwa yanayin da take buk'ata, saida ta tabbatar komai ya mata kafin ta ciro wani k'yalle a jakarta a hankali ta shige goge kwalliyarta na fuskarta tana kallon madubi, saida ta goge duka kafin ta kwance d'aurin d'an kwalin ta saka a jaka ta ciro hijabinta ta saka, sak yanda ta fito daga gidan hakan yasa ta kallon Asma'u tace "Zasu gane wani abu?"

Girgiza kai tayi tare da juya mata baya tana kallon titi, tyab'e baki tayi tace "Asma'u kar kisa na fara tunanin ke 'yar bak'in cikina ce."

Ita ma juya gabanta tayi daga kallonta, a zaman kuramen nan suka isa gida, babu wacce tayi wa yar uwarta sallama kowace ta shiga gida dan suna da tabbacin zasu shirya zuwa gobe a makaranta.


*Sheikh*


Sauri yake sosai dan ya fita masallaci da sunyi sallah a d'ora karatu kasancewar masallacin na shi ne dake manne da gidan, haka kuma ga asibitinshi dake kallon gidanshi wacce yake d'aukar nauyin ma'aikatan ana duba mutane kyauta, kawai zaka ciri kati ne da d'an abun da baiyi tsamari ba, amma daga maganar rashin lafiyar da zata kwantar zuwa mata masu haihuwa da yara k'anana duk kyauta ake dubasu. Suna alwala amma ya cikashi da surutu, har suka fito daga ban d'akin dake cikin falon zasu fita yana fad'in "Ustaz kana ji na? Wallahi da gaske nake fad'a maka, dama na ce maka zanyi budurwa yau ba? To na yi yanzu aiki ya rage naka ka nemo min aurenta."

Hafsat dake jinsu tana neman tashi tsaye ne ta kalleshi tace "Wai auren wasa ne aka fad'a maka da za kace kayi budurwar yanzu kuma a nema maka aurenta?"

Da sauri ya kalleta yace "Aunty Hassy bari maganar nan dan Allah kada kisa mijinki ya baud'e min, wallahi daga ganinta tana da hankali da nutsuwa, wai kin ganta kuwa? Ga mugun aji yarinyar na tabbata ba kowa take kulawa ba."

Da sauri ya mayar da dubanshi ga sheikh zaiyi magana sai kuma ya yi shiru yana sunkuyar da kanshi saboda k'ura masa ido da yayi, a hankali cikin gyara ma hularsa zama da nad'in dake kanta na farin rawani yace "Kai yanzu har ka tabbatar da sahihancinta ne?"

A marairaice ya kalleshi yace "Allah kuwa sheikh, yarinyar daga ganinta sam alamunta da yanayinta ba suyi kama da na wacce zata iya cutar da kowa ba."

Juyawa sheikh yayi cikin takon hanzari ya nufi hanyar fita, da sauri shi ma ya bishi yana fad'in "Ustaz, indai kana so na kana son Hajia to ka nema min auren yarinyar nan."

Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace "Ta fad'a maka tana sonka ne? Ko kuma dole za'a mata?"

Da murmushi yace "A'a ba haka bane, dama amincewarka nake buk'ata kan zaka nema min auren na ta, idan na samu yarda daga gunka shikenan sai nayi yak'i dan k'wato zuciyarta."

A daidai zasu shiga masallack suna cire takalminsu yace "Allah yasa alkairi, zan nema maka auren nata idan nayi bincike na gane yar manyan mutane ce, akasin haka kuma zaka hak'ura da ita *Asas*, ka yarda?"

Jinjina kai yayi alamar to shikenan, shigewa sukayi cikin masallacin ana ta kiran sallah, lokacin tayar da sallah nayi ya shiga gaba dan jan su ba tare da mai jiyawar ba, da kan shi yake d'aga sauti yanda zai jiyar da kowa musamman daya zama ga lasipika.

Suna kammala sallah aka shiga shirye shiryen karatu, cikin k'ank'anin lokaci aka had'a komai kamar yanda aka saba inda masu d'auka ma ana watsawa a kafafen sadarwa da gidajen tv da redio kowa ya shirya. A nutse sheikh ya fara bud'e katarun da muk'addima kafin su tashi a inda suka tsaya. K'arfe 08:10 suka kammala dan ma an amsa tambayoyi kenan, yana mik'ewa zai fita yan agaji da masu tsaronshi d'aya daga ciki suka shiga kakkareshi suna son mutane su gyara ya wuce, gashi k'ofar da zata fitar da shi ta baya kuma mai sadashi da cikin gida ne, gashi kuma yana son fita shi kad'ai ba tare da 'yan koren nan ba. Sosai aka rufe hanyar fitar masu tsaro na ta k'ok'arin a bud'a hanya ya wuce, musamman matasa sune a sahun gaba kowa burinshi su gaisa wasu kuma takardar tambaya ce da su suna son sai sun bashi hannu da hannu.

Allah ne ya so shi ya rufe musu ido sanda ya kutsa ta cikinsu ya fice a masallacin ba tare da ma sanin jami'an ba, bai kuma tsaya komai ba yayi gaggawar fad'awa cikin gida, kai tsaye wajen motoci ya wuce inda ya d'auki wata jibgegiyar Honda crv ya danno hancinta waje sanda mai gadi ya bud'e mishi k'ofar yana bin shi da addu'a, har k'ofar gidan suka fito cigiya mmai gadi na fad'a musu sai hankalinsu ya kwanta tare da tunanin kuma ina ne sheikh zai tafi da baya buk'atarsu? A k'ofar gidan duk suka gyara tsayuwarsu da jiran ya dawo su tabbatar lafiya lau yake.


*Maryam*

Idar da sallarta kenan mahaifinsu ya shigo yana kiran sunanta, tasowa tayi daga kan tabarmar ta durk'usa kanta a k'asa tana fad'in "Abba gani."

Cikin fad'a ya shiga fad'in "Mimi me mahaifin yaron nan yake fad'a ne? Me ya had'aki da shi da suka ce sun hak'ura da tura kayan? Wani abu kika masa na rashin kunya ko?"

Girgiza kai tayi murya k'asa k'asa tace "Abba babu abinda na masa."

A tsawace yace "To me yasa suka ce sun fasa? Yace ke da kanki kika ce ba kya son shi."

Shiru tayi kanta a sadde ba tace komai ba, a zabure ya matso kamar zai daketa yana fad'in "Ba dake nake ba kina ji na?"

Da sauri ta d'ago tace "Abba ni bana son shi ne."

Baki sake ya shiga kallonta yace "Iyeeeeh! Ba kya son shi fa kika ce? Kuma kika kawo mana shi gidan nan har muka shiga maganarku."

Turo baki tayi tana kunkuni, da sauri ya k'arasa duk'awa ya d'auki takalminshi yana fad'in "Kinga 'yar butan uban nan..."

Da gudu ta shige d'aki tana fashewa da kukan shagwab'a, girgiza kai mamanta tayi tace "Allah ya kyauta."

Shi kam tsaki yayi tare da k'arasawa wajen Yaseen dake kwance yace "Har yanzu jikin nashi da zafi?"

A sanyaye ta sake tab'a goshin Yaseen tace "Da zafi malam, ko zamu kaishi asibiti ne? Ina tsoron zazzab'i wallahi musamman ma na dare."

A tausashe shi ma yace "Rabi'a ta ina zamu fara to? Abinda muka ci ma waccen ja'irar ce kika ce ta bayar da kud'in data samu a hannun yaron da muke tsammanin zai zama mijinta, yanzu kud'in taxi ma da zata kaimu asibitin kawai bana da shi."

Jinjina kai tayi kanta a k'asa, laluba aljihunsa yayi ya mik'o mata wasu canji yace "Kinga karb'i wannan, ba wa Mimi ta karb'o masa ko paracΓ©tamol ne ya sha zafin ya rage, bari naje gidan Iya Delu na ga idan malam na nan ba zai rasa wani taimakon da zai mana ba."

Hannu biyu tasa ta karb'a ta bishi da kallo har ya fita, a sanyaye ta k'wala kiran Mimi dake d'aki, tana fitowa da k'aton hibajinta fari na makaranta da tayi sallah da shi, kud'in ta mik'a mata tace "Inji mahaifinki ki siyo paracΓ©tamol a bawa Yaseen."

Karb'a tayi tare da komawa d'akin ta d'auko sabuwar wayarta da har yanzu bata bari kowa ya gani ba, ficewa tayi a gidan ba tare da ta kula kowa ba.


***************

Tsaye tayi bakin titin tana jiran shawagin ababen hawan ya tsagaita ta samu ta tsallaka dan ta isa ga mai shagon dake siyar da maganin, ta jima a wurin kafin tayi nasarar tsallakawa ta siyo ta juyo. Watak'ila Allah ne ya k'addara had'uwarsu, shiyasa ma ya fito shi kad'ai har ya buk'aci ruwa dan mak'oshin shi a bushe yake, gefe ya paka motar ya tsallaka titin ya siyo swan water, zai tsallako ya dawo ne ita kuma ta k'etara ta siyo maganin. Tunda ya ganta ya gane wacece, tsaf ya shaida kamanninta da ita ya had'u da ita na farko, babban abun da ya masa dad'i bai wuce ganinta da yayi a suffar daya fara ganinta a wurin sabkar nan ba, dan tun daga k'asa ya kalli k'afafunta da ake gani da k'yar saboda girman hijabin, gashi da k'yar take kallon gefe da gefe ba irin idonta a tsaye yake a kan titin bΓ’, dan har rintse ido take ko ta kawar da kanta idan wani abun hawan ya hasketa sosao. Hakan yasa ya ji cewa lallai 'yar babban gida ce (yar masu tarbiya).

Da kallo ya bita har ta wuce ta gefenshi ta siyo magani ta dawo bakin titi, yanzu haka tsakaninshi da ita bai fi tako biyar zuwa shida ba ya isar dashi gareta, amma tunanin rashin dacewar yi mata magana a kan titi, da kuma hangen ta yanda zata kalleshi yasa duk sai yaji gwiwarsa tayi sanyi. Amma dake zuciya da abinda take so kuma take muradi, sai yaji a ranshi ai kamar dama ce da zaka san asalin d'abi'ar dake lullub'e a cikin zumbulelen hijab d'in nan, hakan yasa shi takawa a nutse tare da d'an sakin jikinshi ya b'oye k'irarshi ta kakk'arfan dattijo har ya tsaya gefenta, shi ma kallon titin yayi cikin wata daddad'ar murya kuma sanyayya yace "Bayan nema miki amincin Allah, ko zaki iya kawo hannunki na k'etaraki?"

A hankali ta juyo tana yatsina fuska alamar za tayi halin na ta, amma ganin Sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif ya saka ta waro idonta tare da bud'e bakinta, murmushi ya sakar mata sanda suka had'a ido tare da cewa "Sannu."

Rufe bakinta tayi gam tare da yin k'asa da idonta, a hankali har ta sauke kanta k'asa tana d'an jujjuya kanta cikin siririyar murya tace "Assalama alaika, ina wuni?"


Da mamaki ya kalleta, mamakin shin bata ganeshi bane? Yasan dai fuskarshi ta gama garin nan da kewayenshi baki d'aya, ko baku da telebijin zaka iya ganinshi a telebijin d'in wasu, idan ba a nan ba kuma ga waya data game ko ina, wa'zinzikanshi masu tsayi da gajeru suna cikin wayoyin mutane dayawa, idan ka tara mutum goma zaiyi wuya ka kasa samun karatunshi a wayar mutum biyar ko ma sama da haka. Kowa yana son ya ganshi, kowa ya ganshi haba-haba yake da son su gaisa har su tattauna ko na minti d'aya ne, dan hakan ya zama abun alfaharin wani ko abun nishad'i.

Amma ita ta kalleshi da fari kamar zatayi mamaki amma kuma sai ta wani d'auke kai tace wai wani sannu a k'arshe. D'an d'auke kanshi yayi daga kanta ya kalli titi yace "Muje, karki yarda na barki a nan, hakan zai jawo miki kwana a bakin titin nan, ki saka k'afarki a inda na d'auke tawa."


Da sauri ta kalleshi da tunanin shi ne kuwa? To me zatayi? Tayi yanda yace ko kuma shi ma ta d'an gurza mishi ne kamar sauran? Wata zuciyar ce tace da ita "Malam ne fa! Kiyi yanda yace."

Sake kallonshi tayi ta kalli titin a hankali ta d'aga kan ta tana jinjina shi tace "...


Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.

Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA

Please Login or Register in order to submit comment